Nassin da ya fi kowanne zama harsashe da kuma babbar madogarar imanin zuwan Yesu shi ne furcin nan cewa: “Y ache mani, Har yamma da sfiya guda alfin da dari uku: kana za a tsarkake wuri mai-tsarki.” Daniel 8:14. Dukan masu ba da gaskiya ga zuwan Ubangiji sun san kalmomin nan. Dubbai sun rika maimata kalmomin a matsayin ginshikin bangaskiyarsu. Kowa ya dauka cewa burinsu da begensu sun dangana ga al’amuran da aka yi annabcinsu a nassin ne. An nuna cewa kwanakin nan na annabci za su kare a bazarar 1844 ne. Tare da sauran Kirista, Adventist a lokacin sun dauka cewa duniya, ko kuma wani sashen sa ne haikalin. A ganewarsu, tsarkakewar haikalin shi ne tsabtatawar duniya tawurin wutar rana mai-girma ta karshe, kuma cewa wannan zai faru lokacin zuwan Kristi na biyu ne. Shi ya sa suka ce Yesu zai zo duniya a 1844. BJ 407.1
Amma lokacin ya wuce, Ubangiji kuma bai bayana ba. Masu-bi sun san cewa maganar Allah ba za ta yi kuskure ba, tilas fasarar da suka wa annabcin ne akwai kuskure, amma ina kuskuren yake? Da yawa sun yi gaggawar kauce ma matsalar tawurin kin cewa kwana 2300 din sun kare a 1844 ne. Ba su da wani dalili kuwa sai dai wai don Kristi bai dawo a 1844 yadda suka zata ba. Sun matsa cewa, da kwanakin annabcin sun kure a 1844, da Kristi ya dawo domin ya tsarkake haikalin tawurin tsabtata duniya da wuta; kuma cewa da shike bai dawo ba, kwanakin ne basu kare ba. BJ 407.2
Yarda da wannan ra’ayin zai zama kin yarda da lissafin annabcin wokatai da an rigaya an yi ne. An rigaya an gane cewa kwana 2300 din sun fara sa’an da umurnin Artaxerxes don mayaswa da gina Urushalima ya fara aiki ne a bazarar 457 BC. Idan aka fara a nan, akwai daidaituwa game da dukan al’amuran da aka yi annabcinsu a fasarar lokacin a cikin Daniel 9:25-27. Bakwai sittin da tara, shekaru 483 na farko daga cikin shekaru 2300 din, za su kai ga Masiya, Shafaffen, kuma baptismar Kristi da shafewar sa da Ruhu Mai-tsarki ya yi a A.D. 27 ya cika annabcin daidai. A tsakiyar bakwai na saba’in din, za a datse Masiya. Shekara uku da rabi bayan baptismar Kristi, an giciye Shi, a bazaran A.D. 31. Bakwai saba’in din, ko kuma shekara 490 na Yahudawa ne musamman. A karshen wannan lokacin al’ummar ta hatimce kin Kristi da ta yi, ta wurin tsananta ma almajiransa, manzamin kuma suka juya zuwa ga Al’ummai, a A.D. 34. Da shike shekaru 490 na farko na shekaru 2300 din sun kare, saura shekara 1810 kenan. Daga A.D 34, shekaru 1810 za su kai 1844. Malaikan ya ce: “Dukan al’amuran da annabcin ya ambata sun rigaya sun cika,” dai dai lokacin da aka ambata. BJ 408.1
Da wannan lissafin, komi ya je daidai bau shakka kuma, sai dai ba a ga cewa wani abin da ya je dai dai da tsarkake haikalin ya faru a 1844 ba. Idan aka ce kwanakin basu kare a lokacin ba za a birkitar da dukan batun ke nan a kuma warware ababan da an rigaya an tabbatar da su tawurin cikar annabci. BJ 408.2
Amma Allah Ya rigaya Ya jogaranci mutanensa a babban aikin nan na batun zuwan Yesu. Ikonsa da darajarsa sun kasance tare da aikin, kuma Shi ba zai bar aikin ya kare cikin duhu da cizon yatsa ba, har a rena shi cewa karya ce. Ba zai bar maganarsa cikin shakka da rashin tabbaci ba. Ko da shike da yawa sun rabu da lissafin su na da, game da lokaci na annabci, suka kuma musunci sahihancin aikin da aka yi bisa ga lissafin lokaci na annabcin, wadansu basu yarda su rabu da matsayi na bangaskiya da ayuka da aka tabbatar tawurin Littafin da kuma shaidar Ruhun Allah ba. Sun gaskata cewa sun yi anfani da nagargarun kaidodin fassara wajen yin nazarin annabcin, kuma cewa wajibi ne gare su su rike gaskiyan da sun rigaya sun samu, su kuma ci gaba da nazarin Littafin. Da naciya cikin addu’a suka sake duba ra’ayoyinsu suka kuma yi nazarin Littafin domin su gano kusurensu. Sa’an da basu ga kuskure game da lissafinsu na lokatan annabci ba, aka bishe su zuwa ga karin binciken haikalin. BJ 408.3
Cikin bincikensu sun gane cewa babu shaida daga Littafni da ya nuna cewa duniya ce haikalin, amma a cikin Littafin sun iske cikakken bayanin haikalin, da yanayinsa, da inda yake da hidimominsa, shaidar Littafin kuma ya kasance bayananne, isashe kuma ta yadda bai bar wata alamar tambaya ba. Manzo Bulus cikin littafin Ibraniyawa ya ce: “Amma ko alkawali na fari yana da farillai na hidimar Allah, da wuri mai-tsarki nasa, na duniyan nan. Gama da akwai mazamai shiryayye, na farin ke nan, inda ke fitilla, da teble, da gurasa ta nunawa, ana kwa che da ita wuri mai-tsarki. Bayan labule na biyu kuma, sai mazamni wanda ana che da shi mai-tsarki na tsarkaka, yana da bagadin turare na zinariya, da sanduki na alkawali rufaffe ko ina da zinariya, inda akwai kasko na zinariya da manna a chiki, da sandar Haruna wadda ta yi tofu, da kuma alluna na akawali, a bisansa kuma cherubim na daraja suna inuwantadda mazamni na jinkai.” Ibraniyawa 9:1-5. BJ 409.1
Haikalin da Bulus ke magana akai wanda Musa ya gina ne, bisa ga umurnin Allah domin shi zama wurin zaman madaukaki a duniya. “Bari kuma su yi mani mazamni mai-tsarki domin in zauna a chikinsu.” (Fitowa 25:8), umurnin da aka ba Musa ke nan yayin da yake kan Dutsen tare da Allah. Israilawa suna tafiya cikin jeji ne, aka kuma tsara haikalin ta yadda za a iya tafiya da shi daga wani wuri zuwa wani wuri, duk da haka gini ne mai-kyau sosai. Bangonsa shaifi-shafi ne da aka lulluba da zinariya aka kuma kama da azurfa, jinkan kuma jerin ababa ne misalin labule, waje fatu, ciki kuma linen mai-laushi da aka masa ado da zanen hotunan cherubin. Ban da haraba ta waje din da ta kunshi bagadin hadaya ta konawa, haikalin kansa yana da sassa biyu: wuri mai-tsarki da wuri mafi-tsarki, aka raba su da kyakyawan labule mai kauri sosai; irin labulen ne ma aka rufe kofar wuri na farin da shi. BJ 409.2
A wuri mai-tsarkin akwai sandar kyendur a kudu, da fitilunsa bakwai masu haskaka haikalin dare da rana; arewa akwai tebur na gurasar nunawa; kafin labulen da ya raba tsakanin wuri mai-tsarki da mafi-tsarki kuma akwai bagadin zinariya na turare, daga inda girgijen kamshi, da addu’o’in Israila, ke hawa sama zuwa wurin Allah. BJ 410.1
A wuri mai-tsarkin akwai sandukin, akwatin katako ne da aka lulluba da zinariya, inda aka ajiye alluna biyu na dutse da Allah ya rubuta Dokoki Goma akai ke nan. A bisa sandukin, abin da kuma ya zama marufin sandukin, shi ne mazamnin jinkai, gwanin kyau, wanda cherubim biyu ke tsaye a kansa, kowanne a kusurwarsa, kuma da zallan zinariya aka kera su. A wannan wurin, kasancewar Allah yana ganuwa ta girgijen daraja tsakanin cherubim din ne. BJ 410.2
Bayan Ibraniyawa sun zauna a Kan’ana, an sanya wannan mazamnin da haikalin Solomon, wanda, ko da shike gini ne kafaffe, babba kuma, ya bi daidai gwajin mazamnin nan ne irin kayan da ke cikinsu kuma iri daya ne. Hakanan ne haikalin ya kasance, ban da lokacin da ya kasance kango a lokacin Daniel, har sa’an da Romawa suka rushe shi a A.D. 70. BJ 410.3
Wannan ne kadai haikalin da ya taba kasancewa a duniya, bisa ga Littafin. Bulus ya ce da shi haikali na alkawalin fari. Amma ko sabon alkawalin bas hi da haikali ne? BJ 410.4
Sa’anda suka koma littafin Ibraniyawa kuma, masu neman gaskiyan suka iske cewa zancen kasancewar haikali na biyu ko na sabon alkawali yana kunshe cikin maganan nan na Bulus, cewa: “Amma ko alkawali na fari yana da farillai na hidimar Allah, da wuri mai-tsarki nasa na duniyan nan.” Ba shakka Bulus ya rigaya ya ambaci wannan haikalin, inda ya ce: “Kwayar magana chikin abinda muke fadi kenan: muna da wannan irin babban priest, wanda ya zamana ga hannun daman a al’arshen madaukaki chikin sammai, mai-hidiman wuri mai-tsarki da na mazamnai na gaske, wanda Ubangiji ya kafa, ba mutum ba.” Ibraniyawa 8:1,2. BJ 411.1
A nan an bayana haikali na sabon alkawali. Haikali na fari mutum ne ya kafa shi, Musa ne ya gina shi; wannan kuwa Ubangiji ne Ya kafa shi, ba mutum ba. A wancan haikalin, priestoci na duniya ne suka rika hidimarsu, a wannan kuwa Kristi, Babban priest namu ne yake hidima a hannun dama na Allah. Da can akwai haikali daya ne a duniya, dayan kuma yana sama ne. BJ 411.2
Bayan haka, haikalin da Musa ya gina ya bi wani fasali ne. Ubangiji ya umurce shi: “Bisa ga fasalin abin da na nuna maka duka, fasalin mazamnin, da fasalin kayansa duka, hakanan za ku yi shi.” An kuma ba da fadaka cewa: “Ku lura fa ka yi su bisa ga fasalinsu, wanda aka nuna maka chikin Dutsen.” Fitowa 25:9, 40. Bulus kuma ya ce haikali na farin “misali ne domin wannan zamani; a tafarkinsa fa ana mika baye-baye da hadayu,” watau wurare masu-tsarki “misalin ababan da ke chikin sama” ne; cewa priestocin da suka mika baye-baye bisa ga doka sun yi hidima “misalin abuabuwa na sama” ne; kuma cewa “Kristi ba ya shiga chikin wani wuri mai-tsarki wanda aka yi da hannuwa ba, mai-kama da gaskiya ga zanchen fasali; amma chikin sama kanta shi bayana a gaban fuskar Allah sabili da mu yanzu.” Ibraniyawa 9:9, 23; 8:5; 9:24. BJ 411.3
Haikalin da ke sama, inda Kristi ke hidima a madadinmu, shi ne babban asalin, wanda haikalin da Musa ya gina ya misalta. Allah Ya sa Ruhunsa a kan maginan haikali na duniyan. Kwarewan da aka nuna wajen gina shi ya nuna cewa hikima ne daga Allah. Kowane bango yana da kamanin zinariya ne, yana kuma walkiya da hasken kyandir na fitillu bakwai din nan na sandar kyandir din. Tebur na gurasa ta nunawa da bagadin turare ta rika walkiya kamar tsabar zinariya. Kyakyawan labulen nan da ya kasance silin, shafe da zanen hotunan malaiku cikin launi daban-dabam ya kara ma ginin ban sha’awa. Kuma bayan labule na biyu din akwai Shekinah mai- daraja wanda shi ne darajar Allah da ake gani, wanda babban priest ne kadai zai iya shiga wurinsa ya kuma ci gaba da rayuwa. BJ 412.1
Yawan ban-sha’awan haikali na duniyan ya nuna ma ‘yan Adam darajar haikalin nan na sama inda Kristi ke hidima dominmu a gaban haikalin Allah. Wurin kasancewar sarkin sarakuna, inda dubban dubbai ke masa hidima, zambar goma so zambar goma kuma suna tsaye a gabansa (Daniel 7:10), wancan haikalin, cike da darajar kursiyi na har abada, inda Seraphim, masu lura da shi, da fuskokinsu a rufe don bangirma, suka iske cewa gini mafi kyau da ‘yan Adam suka taba yi, don kankanin hoto ne na girman haikalin sama da darajarsa. Dun da haka an kyoyar da muhimman gaskiya game da haikalin sama da babban aikin da ake yi a wurin domin fansar mutum tawurin haikali na duniyan ne, da hidimominsa. BJ 412.2
Wurare masu-tsarki na haikalin sama an misalta su da wurare biyu na haikali na duniyan. Sa’anda cikin ruya aka nuna ma manzo Yohanna haikalin sama, ya ga “fitilla bakwai ta wuta kuma suna chi a gaban kursiyin,” Ruya 4:5. Ya ga malaika “yana rike da kasko na zinariya; aka ba shi turare da yawa, domin ya zuba shi tare da addu’o’in tsarkaka a bisa bagadi na zinariya wanda ke gaban kursiyin.” Ruya 8:3. BJ 412.3
A nan an yarda ma annabin ya ga wurin farko na haikalin da ke sama, can kuma ya ga fitillu bakwai na wuta da bagadi na zinariya, wanda kyandir na zinariya da bagadin turare na haikalin duniya suka misalta. Kuma, “Aka bude haikalin Allah da ke chikin sama” (Ruya 11:19), sai ya duba cikin labulen da ke ciki ya dubi wuri mafi-tsarki. A nan ya ga “sandukin alkawalinsa,” wanda akwati mai-tsarkin nan da Musa ya gyara domin a sa dokar Allah a ciki ya misalta. BJ 412.4
Don haka, wadanda suka yi ta nazarin batun suka sami tabbaci ba shakka cewa akwai haikali a sama. Musa ya yi haikali na duniyan bisa ga kwatancin da aka nuna masa ne. Bulus ya koyar da cewa kwatancin shi ne ainihin haikalin da ke cikin sama, Yohanna kuma ya shaida cewa ya gan shi a sama. BJ 413.1
A cikin haikali na sama, wurin kasancewar Allah, kursiyinsa yana kafe cikin adalci da shari’a. A wuri mai-tsarki akwai dokarsa, babban kaidar cancanta wada tawurin ta ake gwada dukan ‘yan Adam. Sandukin da ya kunshi allunan dokan an rufe shi da mazamnin jinkai, wanda a gaban shi ne Kristi yake roko da jininsa a madadin mai-zunubi. Ta hakanan aka bayana hadewar adalci da jinkai cikin shirin fansar ‘yan Adam. Wannan hadewar, hikima mara matuka kadai ya iya kirkirowa, kuma iko mara matuka kadai ya iya aiwatarwa; hadewa ne da ya cika dukan sama da mamaki da girmamawa kuma. Cherubim na haikali na duniya da suke duban mazamnin jin kai, da bangirma, suna misaltar sha’awan da rundunan sama ke kallon shirin fansa da shi ne. Wannan asirin jin kai ne da malaiku ke sha’awar kallo, cewa Allah yana iya yin adalci, yayin da yake kubutar da mai-zunubi da ya tuba, yana kuma sabonta dangantakarsu da fadadun ‘yan Adam, cewa Kristi zai iya sunkuyawa ya daga tulin jama’a daga rami mara matuka na hallaka, ya suturta su da sutura mara aibi na dalcin kansa, domin su hadu da malaiku da basu taba faduwa ba, su kuma kasance har abada tare da Allah. BJ 413.2
An bayana aikin Kristi na matsakanci a cikin annabcin nan mai-ban sha’awa na Zechariah game da shi “wanda sunansa zuriya ne.” In ji annabcin: “Shi kansa za ya gina haikalin Ubangiji; za ya dauki daraja, ya zamna kuma ya yi mulki a bisa kursiyinsa; za ya zama priest a bisa kursiyinsa; shawarar salama kuma za ta zama tsakanin su biyu.” Zechariah 6:12,13. BJ 413.3
“Za ya gina haikalin Ubangiji.” Ta wurin hadayarsa da tsakancinsa, Kristi ne harsashe da kuma maginin ekklesiyar Allah. Manzo Bulus ya nuna cewa Shi Kristi “babban dutse na kusurwa ne; a chikinsa kwa dukan gini, sassadadde ne, yana hawa yana zama haikali mai-tsarki chikin Ubangiji, a chikinsa kwa an gina ku tare domin ku zama mazamnin Allah chikin Ruhun.” Afisawa 2:20-22. BJ 414.1
“Za ya dauki daraja.” Darajar fansar fadadiyar jinsin ‘yan Adam ta Kristi ce. Cikin dukan sararaki har abada wakar fansassu za ta kasance: “A gare shi wanda yake kamnarmu, ya kwanche mu kuma daga zunubanmu chikin jininsa,… a gare shi daukaka da mulki har zuwa zamanun zamanai.” Ruya 1:5,6. BJ 414.2
Za “ya yi mulki a bisa kursiyinsa, za ya zama priest a bisa kursiyinsa. Yanzu dai ba bisa kursiyin darajarsa ba, mulki na daraja bai zo ba tukuna. Sai aikinsa na matsakanci, ya kare ne Allah ya “za ya ba shi kursiyi na Ubansa Dawuda,” mulki wanda ba shi da matuka. Luka 1:32,33. A matsayinsa na priest, yanzu Kristi yana zaune da Uban a kursiyinsa. Ruya 3:21. Tare da Allah a kan kursiyin akwai Shi wanda “ya dauki bakinchikinmu, da kayan chiwutanmu ya nawaita,” wanda “an jarabche shi a kowache fuska kamarmu, sai dai banda zunubi,” domin Ya sami “iko ya taimaki wadanda ake jarabtassu.” “Idan kowa ya yi zunubi, muna da mai-taimako wurin Uba.” Ishaya 53:4; Ibraniyawa 4:15; 2:18; 1Yohanna 2:1. Tsakancinsa na jikin da aka huda ne, na rayuwa mara aibi. Hudaddun hannayen da hudadden gefen da kafafun da aka kuje, suna roko a madadin fadadden mutum, wanda aka sayi fansarsa da tamani mara iyaka hakanan. BJ 414.3
“Shawarar salama kuma za ta zama tsakaninsu biyu.” Kaunar Uban da ita Dan shi ce mabulbulan ceto domin batacen al’umma. Kafin tafiyarsa, Yesu ya ce ma almajiransa: “Kuma ban che maku ni yi addu’a ga Uba domin ku ba; gama Uba da kansa yana kamnarku.” Yohanna 16:26,27. “Allah yana chikin Kristi yana sulhunta duniya zuwa kansa.” Korinthiyawa II, 5:19. Kuma cikin hidima a haikali na sama, “shawarar salama za ta zama tsakaninsu biyu.” “Allah ya yi kamnan duniya, har ya ba da Dansa haifaffe shi kadai domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalache amma ya sami rain a har abada.” Yohanna 3:16. BJ 414.4
Littafi ya amsa tambayan nan, Mene ne haikalin? sarai. Kalman nan haikali a Littafin da farko yana nufin wurin zaman nan na Allah da Musa ya gina ne, misalin ababa na sama; na biyu kuma ainihin mazamnin Allah a sama, wanda na duniyan ya misalta. A mutuwar Kristi hidimar farillai ya kare. Ainihin haikalin Allah a sama shi ne haikalin sabon alkawalin. Kuma da shike annabcin Daniel 8:14 ya cika a wannan yanayin ne, haikalin da yake magana akai shi ne haikali na sabon alkawali. A karshen kwana 2300 din nan a 1844, an yi daruruwan shekaru ba haikali a duniya. Saboda haka annabcin nan “Har yamma da safiya guda alfin da dari uku; kuma za a tsarkakar wuri mai-tsarki” yana magana game da haikali na sama ne. BJ 415.1
Amma tambaya mafi-muhimmanci ba a amsa shi ba tukuna: Mene ne tsarkakewar haikalin? Tsohon Alkawali ya ambaci hidimar tsarkakewa game da haikali na duniya. Amma ko akwai wani abu a sama da ke bukatar tsarkakewa ahaikali na sama? Cikin Ibraniyawa 9 ana koyar da batun tsarkakewar haikalin duniya da na sama. Ya ce: “Saura kadan sai in che dukan abu, bisa ga shari’a da jini akan tsarkake shi, kuma im ba zubawar jini, babu gafara. Ya wajaba fa a tsarkake misalan al’amuran da ke chikin sama da wadannan abu; amma na sama da kansu da hadayu wadanda sun fi wadannan kyau. (Ibraniyawa 9:22,23), watau jinin Kristi. BJ 415.2
Tsarkakewar, a hidimar alamu da na ainihin ma dole da jini ake yin sa: a hidimar alamun da jinin dabbobi, a hidimar ainihin kuwa da jinin Kristi. Bulus ya ce dalili shi ne cewa im ba zubawar jini babu kafara, kafara, ko kuma kawas da zunubi shi ne aikin da za a gudanar. Amma ta yaya za a danganta zunubi da haikali, ko na sama ko na duniya? Za a iya gane wannan ta wurin duba hidima ta alamun, gama priestoci da suka yi hidima a duniya sun yi hidimarsu “misalin abubuwa na sama da inuwassu” ne. Ibraniyawa 8:5. BJ 415.3
Hidimar haikali na duniya ta kunshi fannoni biyu ne; priestocin sukan yi hidima kowace rana a wuri mai-tsarki, amma sau daya kwace shekara baban priest yakan yi aiki na musamman na tsarkakewar haikalin.Kowace rana mai-zunubi da ya tuba yakan kawo hadayarsa kofar haikalin, kuma sa’an da ya aza hannunsa bisa kan hadayar, yakan furta zunubansa, ta hakanan kuma ya dauke su daga wurinsa ya zuba kan hadaya mara laifin. Sa’an nan akan yanka hadayar. Manzon ya ce “im ba zubawan jini” babu kafarar zunubi. “Gama ran nama yana chikin jini.” Leviticus 17:11. Dokar Allah da aka karya ta bukaci ran mai-ketarewan. Priest yakan dauki jinin, alamar ran mai-zunubi da ya rasa, wanda hadayar ke daukan laifinsa, zuwa cikin wuri mai-tsarki ya yayyafa shi a gaban labulen, wanda a bayan shi akwai sandukin da ke kunshe da dokan da mai-zunubin ya ketare. Ta wurin wannan hidimar akan dauke zunubin tawurin jinin, a zuba shi a haikalin a misalce. A wadansu lokuta ba a zuba jinin a wuri mai-tsarki, amma priest yakan ci naman ne kamar yadda Musa ya umurci ‘ya’yan Haruna cewa Allah “ya kwa ba ku ita domin ku dauki zunubin jama’a,” Leviticus 10:17. Bukukuwan biyu sun misalta daukewar zunubi daga mai-zunubi da ya tuba, zuwa haikalin. BJ 416.1
Irin aikin da aka dinga yi kenan kowace rana duk shekara. Ta hakanan akan mayar da zunuban Israila ga haikalin, kuma ya zama wajibi a yi aiki na musamman don cire su. Allah Ya umutra cewa a yi kafara domin kowane sashi na wurare masu-tsarkin. “Za ya yi kafara domin wuri mai-tsarki, domin laifofinsu kuma, watau dukan zunubansu ke nan; hakanan kuma za ya yi domin tent na taruwa, wanda ke zamne tare da su a chikin tsakiyar kazamtarsu. An kuma bukaci yin kafara domin bagadin, domin a “tsabtadda shi, ya tsarkake shi kuma daga kazamta na yayan Israila.” Leviticus 16:16, 19. BJ 416.2
Sau daya a shekara, a babban Ranan Kafara, priest yakan shiga wuri mafi-tsarki don tsarkake haikalin. Aikin da akan yi a wurin ne yakan kamala hidimomin shekaran. A ranar kafara bunsuru guda biyu ne akan kawo kofar tent, a jefa kuri’a a kansu, “daya domin Ubangiji, dayan domin Azazel.” Aya 8. Bunsurun da karu’ar Ubangiji ta fadi a kansa akan yanka shi a matsayin hadaya ta zunubi domin mutanen. Priest kuma zai kawo jininsa cikin labulen, ya yayyafa shi bisa kan bunsuru mai-rai, ya furta dukan muguntar ‘ya’yan Israila a bisansa, da dukan laifofinsu, watau zunubansu duka; za ya sa su a bisa kan bunsurun, kana ya sallame shi zuwa jeji ta hannun wani mutum wanda aka sanya, bunsuru kuma za ya dauka ma kansa dukan muguntassu, ya kai zuwa chikin kasa inda babu kowa.” Aya 21, 22. Bunsurun Azazel din ba ya dawowa sansanin Israila kuma, mutumin da ya kai shi jejin kuma yakan wanke kansa da tufafinsa da ruwa kafin ya koma cikin sansanin. BJ 417.1
An shirya dukan hidimar ta yadda za a nuna ma Israilawa tsarkin Allah da yadda yake kyamar zunubi; kuma domin a nuna masu cewa ba za su iya saduwa da zunubi har su kasance ba aibi ba. Akan bukaci kowane, mutum ya auna rayuwarsa yayin da ake aikin kafaran. Akan dakatar da kowane aiki, kuma dukan Israilawa sukan uni kaskantar da kan u ne a gaban Allah, da addu’a da azumi, da bincikewar zuciya. BJ 417.2
Hidimar farillai din tana koyar da muhimman gaskiya. Akan karbi wani a madadin mai-zunubi; amma jinin hadayan ba ya share zunubin. Saboda haka aka tanada hanyar zubar da zunubin a haikalin. Ta wurin hadayar jini mai-zunubi yakan amince da ikon dokan ya furta laifinsa na ketare dokar, ya kuma bayana bukatarsa ta gafara ta wurin bangaskiya ga Mai-fansa da ke zuwa; amma tukuna ba a kubutar da shi daga hukumcin shari’a ba. A ranar kafara, babban priest, bayan ya karbi hadaya daga jama’a yakan shiga wuri mafi-tsarki da jinin hadayan nan, ya kuma yayyafa shi a kan mazamni na jinkai, daidai kan dokan, domin shi gamsar da sharuddan dokar. Sa’an nan, a yanayinsa na matsakanci, yakan dauki zunuban a ransa ya fitar da su daga haikalin. Sa’anda ya aza hannuwansa bisa kan bunsurun Azazel, yakan furta dukan zunuban a kansa, alamar mayar da su daga shi kansa zuwa bunsurun kenan. Sa’an nan bunsurun yakan tafi da su, akan kuma dauka cewa har abada an raba su da mutanen ke nan. BJ 418.1
Haka ne aka rika hidimar “misalin abubuwa na sama da inuwassu.” Kuma abin da aka yi cikin misali a hidimar haikali na duniya ana yinsa zahiri a hidimar haikalin sama. Bayan komawarsa sama, Mai-ceton mu Ya fara aikin sa na babban priest namu. In ji Bulus; “Kristi baya shiga wani wuri mai-tsarki wanda aka yi da hannuwa ba, mai-kama da na gaskiya ga zanchen fasali; amma chikin sama kan ta, shi bayana a gaban fuskar Allah sabili da mu yanzu.” Ibraniyawa 9:24. BJ 418.2
Hidimar priest cikin dukan shekaran a wuri na fari na haikalin a cikin labulen, wanda shi ne kofa, ya kuma raba tsakanin wuri mai-tsarki da harabar ta waje, yana misaltar aikin hidima da Kristi Ya shiga yi da zaran ya koma sama. Aikin priest ne a hidima ta kowace rana shi gabatar ma Allah jinin hadaya na zunubi, da kuma turare da yakan tashi zuwa sama tare da addu’o’in Israila. Hakanan ne Kristi ya yi anfai da jininsa a gaban Uban a madadin masu zunubi, ya kuma gabatar masa a gabansa, tare da turaren adalcin kansa, addu’o’in masu ba da gaskiya da suka tuba. Haka aikin hidima a wuri na fari na haikali na sama yake. BJ 418.3
Zuwa wurin ne bangaskiyar almajiran Kristi ta bi su yayin da ya haura sama suna hallon tafiyarsa. Nan ne begensu ya kasance. “Wanda muna da shi kamar anchor na rai, tabbatachen bege mai-tsayawa, mai-shiga kuma chikin abin da ke chikin labulen; inda Yesu kamar shugaba ya shiga dominmu, da ya rigaya ya zama babban priest har abada.” “Ba kwa ta wurin jinin awaki da yan maruka ba, amma tawurin jini nasa, ya shiga so daya dungum chikin wuri mai-tsarki, bayan da ya jawo pansa ta har abada.” Ibraniyawa 6:19, 20; 9:12. BJ 419.1
Har karni sha takwas aikin kafaran nan ya ci gaba wuri na farko a haikalin. Jinin Kristi ya rika roko a madadin masu bada gaskiya, yana samo masu gafara da karbuwar Uban, duk da haka zunubansu sun kasance a cikin littattafan da aka rubuta su. Kamar yadda a hidimar tshohon haikalin akan yi aikin kafara a karshen shekara, hakanan kafin kamalawar aikin Kristi na fansar mutane akwai aikin kafara domin kawas da zunubi daga haikalin. Hidiman da ya fara ke nan a karshen kwana 2300 din. A wancan lokacin, bisa ga annabcin Daniel, Babban Priest namu Ya shiga wuri mafi-tsarki domin aiwatar da sashin karshe na aikinsa mai-saduda, watau tsarkake haikalin. BJ 419.2
Kamar yadda a da akan jibga zunuban mutanen a kan hadaya ta zunubin, tawurin bangaskiya, kuma tawurin jinin hadayan akan zubar da shi a haikalin, bisa ga alama, hakanan ne a sabon alkawalin, tawurin bangaskiya, ana jibga zunuban masu tuba a kan Kristi, a kuma zuba su zahiri a haikali na sama, kuma kamar yadda akan tsarkake haikali na duniya tawurun cire zunuban da suka kazamtar da shi, hakanan ne za a ainihin tsarkake na saman tawurin sharewan zunuban da aka rubuta a wurin. Amma kafin a yi wannan, sai an bincika littattafan domin a sansance wadanda, ta wurin tuba daga zunubi da bangaskiya ga Kristi, sun cancanci moriyar kafararsa. Sabo da haka tsarkakewar haikalin ta kunshi bincike, wanda kuwa wani fanni ne na hukumci. Dole a yi wannan aikin kafin zuwan Kristi domin shi fanshi mutanensa, domin sa’an da zai zo, ladarsa na tare da shi da zai ba kowa gwalgwadon aikinsa. Ruya 22:12. BJ 419.3
Saboda haka wadanda suka bi hasken kalmar annabcin suka ga cewa maimakon zuwa duniya a karshen kwana 2300 din a 1844, Kristi ya shiga wuri mafi-tsarki na haikalin sama ne domin shi aiwatar da aikin kamalawar kafara domin shirya zuwansa. BJ 420.1
An kuma ga cewa, yayin da hadaya ta zunubin ta misalta Kristi a matsayin sa na hadaya, babban priest kuma ya misalta Kristi a matsayin matsakanci, bunsurun Azasel ya misalta Shaitan ne, tushen zunubi, wanda a kansa ne za a jibga zunuban masu ainihin tuba. Sa’anda babban priest, ta wurin yin hadaya ta zunubi, ya cire zunubai daga haikalin, yakan jibga su a kan bunsurun Azazel ne. Sa’anda Kristi, ta wurin jinin kansa, ya cire zunuban mutanensa daga hailaki na sama a karshen hidimarsa, za ya jibga su a kan Shaitan ne wanda a lokacin aiwatar da hukumcin, dole zai dauki dukan horon. Akan kai bunsurun Azazel din wata kasa inda ba kowa ne, ba kuwa zai sake dawowa cikin Israilawa ba. Hakanan ne za a kori Shaitan har abada daga wurin Allah da mutanensa, za a kuma share shi kwata kwata daga kasancewa. Sa’anda za a hallaka zunubi da masu-zunubi a karshe. BJ 420.2