Sa’anda za a janye kariyar dokokin mutane daga masu girmama dokokin Allah a kasashe dabam dabam a lokaci daya, za a yi yunkurin hallaka su. Sa’an da lokacin da aka sa a cikin dokan ya kusa, mutane za su hada baki domin su kawar da kungiyoyin nan da aka ki jini. Za a shirya murkushe su a dare daya, bugu daya da zai rufe muryar adawa da tsautawa. BJ 631.1
Mutanen Allah, wadansu a kurkuku, wadansu a boye cikin dazuzuka da duwatsu, suna da rokon tsaron Allah, yayin da a kowane gefe kungiyoyin mutane dauke da makamai, da zugin miyagun malaiku, suna shiryawa domin aikin kisa. Yanzu ne, a sa’a a karshe, Allahn Israila zai shiga tsakani domin tsiradda zababbunsa. In ji Ubangiji: “Ku kwa za ku yi waka kamar lokacin da ake yin idi mai-tsarki da dare: da murna kwa a zuchiya, kamar lokachin da akan tafi ... garin a zo da dutsen Ubangiji, watau dutsen Israila. Ubangiji kuma za ya sa a ji murya tasa mai-daraja, Ya nuna sabkowar hannunsa, tare da fushinsa mai-zafi, da harshen wuta mai-chinyewa; da tsawa da hadari, da duwatsun kankara.” Ishaya 30:29, 30. BJ 631.2
Da ihun nasara, da gori da zagi, garkuwan miyagun mutane suna gaf da rugawa kan masu adalci, sai ga duhu mai-nauyi da ya fi dare, ya sauko bisa duniya. Sa’an nan bakar gizo, mai-darajar kursiyin Allah, ta rufe sammai, kuma kaman ta kewaye kowace kungiyar addu’a. taron jama’an da suka fusata, nan da nan aka kama su ihun ba’arsu ya kare. Aka manta da wadanda su suka so su kashe. Da tsoro suka kalli alamar alkawalin Allah, suka kuma so da za a kare su daga haskensa. BJ 631.3
Mutanen Allah za su ji murya tana cewa: “Dubi sama,” kuma suna duban sama za su ga bakan gizon alkawalin. Za a raba bakaken gizagizai din nan da suka rufa sararin sama. Kuma kamar Istifanus, za su kalli sama da karfin hali har su ga darajar Allah da Dan mutum kuma yana zaune a kursiyinsa. A cikin yanayinsa na Allahntaka za su ga alamar kaskancinsa, daga lebunansu kuma za su ji rokon da zai gabatar a gaban Ubansa da malaiku masu-tsarki cewa: “Wadanda ka ba ni, ina so su zamna wurin da ni ke, tare da ni.” Yohanna 17:24. Kuma za a ji wata murya mai-dadi cike da murna, tana cewa: “Suna zuwa! Suna zuwa! masu-tsarki, marasa mugunta, marasa kazamta kuma. Sun kiyaye kalmar hakurina; za su yi tafiya chikin malaikun;” sai kuma lebunan wadanda suka rike bangaskiyarsu da gaske za su ta da kuwwar nasara. BJ 632.1
Da tsakar dare ne Allah zai bayana ikon Shi na tsirar da mutnensa. Rana za ta bayana, tana haskakawa cikin karfinta. Alamu da al’ajibai za su biyo bi da bi da hanzari. Miyagu za su kalli al’amarin da razana da mamaki kuma, yayin da masu adalci za su kalli alamar tsirarsu da murna. Kowane abu a halita, kaman ya kauce daga hanyarsa ne. Rafuka za su dena gudu. Manyan gizagizai masu kauri, masu duhu kuma, za su taso suna karo da juna. A tskiyar fushin sammai din akwai wani sarari mai-darajan gaske, ta inda muryar Allah kamar motsin ruwaye tana cewa: “An gama.” Ruya 16:17. BJ 632.2
Muryan nan za ta girgiza sammai da duniya. “Za a yi babban rawan duniya irin wanda ba a taba yi ba, tun kasancewar mutane a duniya, rawan duniya mai-girma, mai-karfi kuma.” Aya 17,18. Sararin sama kaman yana budewa yana rufewa kuma, daraja daga kursiyin Allah tana wucewa ciki. Duwatsu suna rawa kamar ciyawa a iska, kuma manya manyan duwatsu suna warwatsuwa ko ta ina. Akwai wani ruri kaman na guguwa da ke zuwa. Teku ya tuntsure, ya fusata. Za a ji karar mahaukaciyar guguwa kamar muryar aljannu da ke aikin hallaka. Dukan duniya za ta ja numfashi ta kumbura kamar rakuman ruwan teku. Fuskar duniyan tana tsagewa. Tussansa sai ka ce suna watsewa ne. Jerin duwatsu suna nutsewa. Tsibirai masu mazamna cikin su za su bata. Tashoshin jiragen ruwa da suka zama Kamar Sodom sabo da muguntarsu, za su nutse cikin ruwayen. An kuma tuna da Babila babba a gaban Allah, “domin a ba ta koko na ruwan anab na zafin hasalassa.” Manya manyan kankara, “kowane guda nauyinsa ya yi wajen talent daya,” su na aikinsu na hallaka. Aya 19,21. Biranen duniya masu alfarma za a rusar da su. Manyan gine ginen da mutanen duniya suka kashe arzikinsu domin su daukaka kansu akai su na rugujewa a idonsu, suna zama kango. Gidajen kaso su na rushewa, mutanen Allah kuma, wadanda aka kulle su sabo da sabo da imaninsu, za a yantar da su. BJ 632.3
Za a bude kabarbaru, “Da yawa kwa daga chikin wadanda su ke barci chikin turbayar kasa a su falka , wadansu zuwa rai na har abada, wadansu kuma zuwa kunya da reni mara matuka.” Daniel 12: 2. Dukan wadanda suka mutu cikin bangaskiyar malaika na uku za su fito daga kabari da daraja, domin su ji alkawalin Allah na salama da wadanda suka kiyaye dokarsa. “Su kuma wadanda suka soke shi.” (Ruya 1:7), wadanda suka yi ba’a ga azabar mutuwar Kristi, da kuma masu mafi-yawan jayaya da gaskiyarsa da mutanensa, za a tashe su su ganshi cikin darajarsa su kuma ga girmamawa da za a yi ma masu biyayya. BJ 633.1
Har yanzu dai, gizagizai suna rufe da sararin sama, amma rana takan ratsa loto loto, tana kama da idon ramuwa na Yahweh. Walkiya masu ban tsoro suna tsalle daga sammai, suna kunsa duniya cikin fallen wuta. A kan rurin tsawa, muryoyi da ba a gane su ba, masu ban tsoro kuma, suna bayana hallakar miyagu. Ba duka ne za su fahimce su sarai ba. Wadanda ba da dadewa ba, da garaje da fahariya da tumbe suka yi ta murnar zaluncin da suka yi ma mutanen Allah masu-kiyaye dokokinsa, yanzu mamaki ya cika su, suna rawan jiki sabo da tsoro. Ana jin ihunsu fiye da karar kasa da teku da iska. Aljannu za su yarda cewa Kristi Allah ne, su kuma yi rawan jiki a gaban ikonsa, yayin da mutane ke rokon karin jin kai, suna kuma damuwa game da jin kai, suna kuma fama cikin razana mai-tsanani. BJ 633.2
In ji annabawa na da, sa’an da suka hangi ranar Allah cikin wahayi mai-tsarki: “Ku yi ihu gama ranar Ubangiji ta kusa: misalin hallaka daga wurin Mai-iko duka.” Ishaya 13:6. “Ka shiga chikin dutse, ka buya chikin turbaya, daga gaban razanar Ubangiji, da darajar daukakassa. Za a sunkuyadda duban rai na mutum, ta da hanci na mutane kuma za ya sha kaskanchi; Ubangiji kadai kwa za ya daukaka chikin wannan rana. Gama za a yi ranar Ubangiji mai-runduna, a kan kowane mai-girman kai da mai-ta da hanchi, a kan kowane daukakakken abu kuma; za a kwa kaskantadda shi.” “A chikin ranan nan mutum za ya dauki gumakansa na azurfa, da gumakansa na zinariya, wadanda aka yi masa domin sujada ya yar ma jaba da jemage; domin ya shiga chikin ramummuka na duwatsu, da chikin tsatsaguwa na tsagaggun duwatsu kuma, daga gaban razanar Ubangiji da darajar daukakassa, sa’anda ya tashi garin girgiza duniya da karfi.” Isahaya 2:10 -12; 20, 21. BJ 634.1
Ta wurin wani tsago a gizagizan, wani tauraro zai haskaka wanda walkiyarsa ta karu ribi hudu, sabo da duhun. Yana ba amintattu bege da murna, wahala da fushi kuma ga masu ketare dokar Allah. Wadanda suka sadakar da komi sabo da Kristi, yanzu za su kasance da tsaro, boyayyu kamar cikin sirrin rumfar Ubangiji. An rigaya an gwada su, kuma a gaban duniya da masu rena gaskiya sun nuna shaidar kaunarsu ga Shi wanda Ya mutu dominsu. Babban canji ya zo kan wadanda suka rike amincinsu har a bakin mutuwa ma. An tsirar da su faraf daya daga mugun zaluncin mutane da suka juya suka zama aljannu. Fuskokinsu da suka nuna taraddadi da damuwa yanzu sun haskaka da mamaki da bangaskiya da kauna. Muryoyinsu suna tashi da wakar nasara cewa: “Allah mafakanmu ne da karfinmu, taimako ne na kurkusa chikin wahala. Domin wannan ba za mu ji tsoro ba, ko da duniya ta juya, ko a duwatsu sun motsu a chikin zuchiyar tekuna; ko da duwatsunsu suna ruri suna hauka, duwatsu suna rawa da kumburinsu.” Zabura 46:1-3. BJ 634.2
Yayin da kalmomin amincewan nan mai-tsarki ke hawa zuwa wurin Allah, gizagizan za su koma baya, za a kuma ga sammai cike da taurari, da mafificiyar daraja sabanin duhun sarari mai-fushin da ya kewaye su ta kowane gefe. Darajar birnin sama din tana kwararowa ta budaddun kofofin nan ne. Sa’an nan za a ga hannu rike da alluna biyu na dutse da aka rufe su tare. In ji annabin: “Sammai za su ba da labarin adilchinsa; gama Allah mai-shari’a ne da kansa.” Zabura 50:6. Doka mai-tsarkin nan, adalchin Allah, da aka yi shelarta cikin tsawa da wuta daga Sinai a matsayin maibishewar rayuwa, yanzu za a bayana shi ga mutane a matsayin kaidar hukumci. Hannun zai bude allunan, za a kuma ga umurnin dokoki goma din da aka rubuta kaman da alkalamin wuta. Kalmomin suna bayane ta yadda kowa zai iya karanta su. Tunani zai falka, za a shafe duhun camfi da ridda daga kowace zuciya, kuma kalmomi goman nan na Allah, gajejjeru, bayanannu, masu iko, za a gabatar da su ga ganin dukan mazamnan duniya. BJ 635.1
Ba shi yiwuwa a bayana tsoro da bakincikin wadanda suka tattake dokoki masu-tsarki na Allah. Ubangiji Ya ba su dokarsa; da sun gwada halayensu da dokan nan su kuma sansance aibin halayensu tun da sauran zarafin tuba da canjin hali; amma domin a sami karbuwar duniya, suka kawar da umurnin dokokin, suka kuma koya ma wadansu su ketare su. Sun yi kokarin tilasta mutanen Allah su kazantar da Assabbat dinsa. Yanzu dokan nan da suka rena yana hukunta su. A fili sun gane cewa ba su da hujja. Su suka zabi wanda za su yi masa sujada. “Sa’an nan za ku komo, ku rarrabe tsakanin adili da mugu, tsakanin wanda yake bauta ma Allah da wanda ba ya bauta masa ba.” Malachi 3:18. BJ 635.2
Magabtan dokar Allah, daga shugabannin addini har zuwa mafi kankana cikinsu, za su sami sabuwar fahimtar gaskiya da abin da ya kamata su yi. A makare za su ga cewa Asabbat na doka ta hudu ne hatimin Allah Mai-rai. A makare za su ga ainihin yanayin assabbat din nan nasu na karya da harsashen yashi da su ke ta gini a kai. Za su gane cewa suna ta fada da Allah ne. Mallamai na addini sun kai rayuka ga hallaka da sunan cewa suna bishe su zuwa paradise ne. Sai ranar karshe ta lissafi ne za a ga girman alhakin mutanen da ke aiki mai-tsarki da kuma munin sakamakon rashin amincinsu. Cikin rai na har abada ne kadai za mu iya kiyasta munin hasarar mai-rai daya. Abin tsoro ne abin da Allah za y ace masa: Rabu da ni, mugun bawa. BJ 636.1
Za a ji muryar Allah daga sama ya na bayana rana da sa’ar zuwan Yesu, yana kuma mika ma mutanensa alkawali na har abada din. Kamar kuwwar tsawa mafi-karfi, kalmominsa za su gangaro duniya. Israila ta Allah tana ji, da idanunsu sama. Za a haskaka fuskokinsu da darajarsa, za su kuma haskaka kamar fuskar Musa lokacin da ya sauko daga Sinai. Miyagu ba za su iya kallonsu ba. Kuma sa’an da za a furta albarka bisa wadanda suka girmama Allah ta wurin kiyaye Assabbat nasa da tsarki, za a yi babban ihun nasara. BJ 636.2
Ba da jimawa ba, karamin bakin girgije zai bayana ta gabas, girmansa kamar tafin hannun mutum. Girgijen da zai kewaye Mai-ceton ne, wanda kuma daga nesa za a ga kamar yana da duhu ne. Mutanen Allah za su san cewa wannan alaman Dan mutum ne. Cikin zama shuru za su kalle shi yayin da yake kusantowa duniya, yana kara haske da daraja, har sai ya zama babban farin girgije, gindinsa mai-daraja kamar wuta mai-konawa, samansa kuma bakan-gizon alkawalin. Yesu yana hawa a matsayin babban Mai-nasara. Yanzu ba mutum mai-bakinciki ba da zai sha koko mai-daci na kunya da kaito, zai zo, Mai-nasara a sama da kasa, domin ya hukumta masu rai da matattu. “Mai-aminchi da Mai-gaskiya,” “chikin adilchi kwa yake yin shari’a da yaki kuma.” Kuma, “Rundunan yaki kwa wadanda ke chikin sama” (Ruya 19:11, 14) suka bi Shi. Da wakoki masu amo na sama malaiku masu-tsarki da ba za a iya lissafta su ba, za su bi shi. Sararin sama dai kaman ya cika da masu hasken- “dubu goma sau dubu goma, da dubban dubbai.” Babu alkawalin dan Adam da zai iya bayana wannan al’amarin; ba tunanin mutum da zai iya fahimtar ban-sha’awarsa. “Daraja tasa ta rufe sammai, duniya kwa ta chika da yabonsa. Shekinsa yana kama da haske.” Habakuk 3:3. Sa’an da girgijen ya kara kusantowa, kowane ido zai ga Sarkin rai. Babu rawanin kaya a kan nan mai-tsarki, amma rawanin daraja ke zaune a kan nasa. Fuskarsa ta fi rana haskakawa. A bisa rigatasa da bisa chinyatasa kuma yana da suna a rubuche, SARKIN SARAKUNA DA UBANGIJIN IYAYENGIJI.” Ruya 19:16. BJ 636.3
A gabansa “dukan fuskoki fa sun komo fari;” tsoron bakin ciki na har abda zai fada ma masu kin jin kan Allah. “Zuchiya tana narkewa, guwawu suna bugun juna, ... fuskokin dukansu kwa suna fari.” Irmiya 3:6; Nahum 2:10. Masu adalci za su yi kuka da rawan jiki suna cewa: “Wa zai iya tsayawa?” Wakar malaikun za ta tsaya, kuma wuri zai yi shuru na ban tsoro har wani lokaci. Sa’an nan za a ji muryar Yesu yana cewa: “Alherina ya ishe ku.” Za a haskaka fuskokin adilai, murna kuma za ta cika kowace zuciya. Malaiku kuma za su kara amo su yi waka kuma yayin da suje kara kusatowa duniya. BJ 637.1
Sarkin sarakuna zai sauko a kan girigjen, yafe da harshen wuta mai-ci bal-bal. Za a nade sammai tare kamar walkar takarda, duniya za ta yi rawan jiki a gabansa, kuma za a gusar da kowane dutse da tsibiri daga wurinsa. “Allahnmu yana zuwa, ba kwa za ya yi shuru ba: wuta za ta chi a gabansa, za ta yi hauka kuma kwarai kewaye da Shi. Za ya kira sammai daga bisa, za Ya kira duniya kuma domin Ya yi ma mutanensa shari’a.” Zabura 50:3,4. BJ 637.2
“Sarakunan duniya kuma, da hakimai, da jarumawa, da attajirai, da masu-karfi, da kowane bawa da da, suka buya chikin ramummuka da pannun duwatsu; suna che ma duwatsu da pannu, Ku fado mana, ku rufe mu daga fuskar wanda Ya zamna bisa kursiyin, daga hasalaar Dan ragon kuma: gama babban rana ta hasalassu ta zo, wa ke da iko shi tsaya kuma?” Ruya 6:15-17. BJ 638.1
Ba’an reni zai tsaya. Lebuna masu-karya za su yi shuru. Surutun makamai, hayaniyar yaki “chikin rigimar yaki da tufafi mirginannu chikin jini (Ishaya 9:5), za su taya. Ba abin da ake ji yanzu sai muryar addu’a da karar kuka da makoki. Kukan zai fito daga lebunan da dazun nan ke ba’a ne. “Babban rana ta hasalassa ta zo; wa ke da iko shi tsaya kuma?” miyagu suna roko a bizne su a kalkashin duwatsu, maimako su sadu da fuskar Shi wanda suka rena suka kuma ki. BJ 638.2
Muryar da ke shiga kunen matattu, sun sani. Sau da yawa amonta ya dinga kiran su zuwa tuba. Sau da yawa sun rika jinta cikin rokon wani aboki ko dan’uwa ko Mai-fansa ma. Ga masu kin alherinsa ba muryar da ta fi hukumtawa da tsautawa kamar muryar da ta dade ta na roko cewa: “Ku juyo dai ku bar miyagun halulukanku; don mi za ku mutu?” Ezekiel 33:11. In ji Yesu: “Da shike na yi kira, kun ki; na mika hannuna, ba wanda ya kula; amma kun wakala dukan shawarata, ba ku yarda da tsautawata ba ko kadan” Misalai 1: 24, 25. Muryan nan za ta tuna masu ababa da za su so da an shafe su - gargadin da suka rena, gayyatan da suka ki, zarafin da suka wofinta. BJ 638.3
Akwai wadanda suka yi ma Kristi ba’a lokacin da aka wulkanta Shi. Da karfi mai-motsa zuciya za a tuna masu kalmomin nan na Kristi lokacin da babban priest ya yi masa tambaya, inda Ya ce: “Gaba nan za ku ga Dan mutum a zamne a hannun daman na iko, yana zuwa kuma bisa gizagizan sama.” Matta 26:64. Yanzu suna ganin Shi cikin darajarsa, amma basu rigaya sun gan Shi a hannun daman iko ba. BJ 639.1
Wadanda suka rena furcinsa cewa Shi ne Dan Allah za su yi shuru yanzu. Akwai Hirudus mai-fahariyan nan da ya yi ma sarautar Kristi ba’a, ya kuma sa sojojin da ke masa ba’a suka sa masa rawanin sarauta. Akwai ainihin mutanen da suka sa masa wata riga da hannun su, suka sa masa rawanin kaya a goshinsa mai-tsarki, a hannunsa kuma suka sa sandar sarauta ta ba’a, suka kuma durkusa a gabansa cikin ba’a na sabo. Mutanen nan yanzu za su kau da fuska daga kallon da yake yi masu, su kuma so su gudu daga darajar kasancewarsa. Wadanda suka buga kusoshi a hannuwansa da kafafunsa, da sojan da ya soki gefensa, za su dubi alamun nan da razana da juyayi kuma. BJ 639.2
A sarari priestoci da sarakuna za su tuna al’amuran Kalfari. Cikin tsoro mai-yawa za su tuna yadda cikin murna irin na Shaitan suka ce: “Ya chechi wadansu, ya kasa cheton kansa. Sarkin Israila ne shi; shi sabko daga gichiye yanzu, mu kwa mu a ba da gaskiya gare shi. Yana dogara ga Allah; bari ya cheche shi yanzu, idan yana son sa.” Matta 27: 42,43. BJ 639.3
A bayane za su tuna misalin nan na Mai-ceton game da manoman da suka ki ba ubangijinsu anfanin gonansa, suka wulakanta bayinsa suka kuma kashe dansa. Za su kuma tuna hukumcin da su kansu suka furta cewa: Ubangijin gonan zai hallaka miyagun mutanen nan. Cikin zunubi da horon mutanen nan marasa aminci, priestoci da dattibai za su ga abin da su kansu suka yi da hallakar da ta cancance su. Wani ihun kuma zai taso yanzu. Fiye da ihun da aka cika titunan Urushalima da su, cewa: “A giciye shi, a gichiye shi,” yanzu wata muryar tsoro da makoki ce za ta taso tana cewa: “Shi ne Dan Allah! Shi ne Masiya na gaskiyan!” za su so su gudu daga wurin Sarkin sarakunan. A banza za su so su buya a cikin kogunan kasa da ta tsatsage lokacin hargitsin. BJ 639.4
Cikin rayuwar dukan masu kin gaskiya, wani lokaci lamiri yakan falkas da su, zuciya takan tuna masu da rayuwarsu ta riya, sai rayuwarsu ta cika da nadama ta banza. Amma wadannan ba komi ba ne idan aka gwada da nadamar wancan rana da “tsoro ya afka masu kamar hadari,” sa’an da “masifarku ta chi maku kamar guguwa.” Misalai 1:27. Wadanda suka so su hallaka Kristi da amintattunsa, yanzu za su ga darajan da ke kansu. A tsakiyar razanar su za su ji muryoyin tsarkaka cikin farin ciki suna cewa: “ga shi wannan Allahnmu ne; mun jirache shi, za ya cheche mu.” Ishaya 25:9. BJ 640.1
Cikin rawan duniya da walkiya, da rurin tsawa, muryar Dan Allah za ta kirawo tsarkaka da ke barci. Za Ya dubi kabarbarun adilai, sa’an nan, da hannayensa sama, zai ce: “Ku falka, ku falka, ku falka, ku da kuke barci cikin turbayar, ku tashi kuma!” Ko ina cikin duniya, matattu za su ji wannan muryar, kuma wadanda suka ji za su rayu. Dukan duniya kuma za ta amsa da takawar babban rundunar mayakan kowace al’umma, da dangi, da harshe, da jama’a. Daga kurukun mutuwa za su zo, yafe da daraja mara mutuwa, suna cewa: “Ya mutuwa ina nasarakki? Ya mutuwa, ina karinki? Korinthiyawa I, 15:55. Sa’an nan adilai da ke raye, da adilai da aka ta da su daga matattu za su hada muryoyinsu cikin dogon ihu na murnar nasarar.” BJ 640.2
Duka za su fito daga kabarbarun da kamaninsu, daidai yadda su ke lokacin da suka shiga kabarin. Adamu da zai kasance cikinsu dogo ne da surar martaba, amma a sura zai kasa Dan Allah da kadan. Zai bambanta sosai da mutanen sararakin baya; cikin wannan fanni za a nuna yawan lalacewar ‘yan Adam. Amma duka za a tashi sabobi da kuzarin samartaka ta har abada. A cikin farko, an halici mutum da kamanin Allah ne, ba a hali kadai ba, amma duk da siffa da kamani. Zunubi ya bata ya kuma so ya lalata suran nan na Allah gaba daya; amma Kristi Ya zo domin Shi mayas da abin nan da aka rasa. Za Ya canja jikunan nan namu kazamtattu Ya kuma sifanta su kamar jikinsa na daraja. Suran nan mai-mutuwa mai-lalacewa kuma, mara ban sha’awa, wanda zunubi ya kazamtar, zai zama mara aibi, kyakyawa mara mutuwa kuma. Za a bar dukan illoli da nakasa a cikin kabari. Sa’an da an mayas da su wurin itacen rai a Adnin tsarkaka za su fita (Malachi 4:2) zuwa siffar dan Adam cikin darajarta ta halitta. Za a cire burbushin zunubi da suka ragu, sa’an nan amintattu na Kristi za su bayana cikin kyau na Ubangiji Allahnmu, a tunani da ruhu da jiki za su zama da sura mara aibi irin na Ubangijinsu. Fansa ke nan mai-ban al’ajibi! wanda an dade ana zancensa, an dade ana begensa, an yi bimbininsa da bege mai- yawa, amma ba a taba fahimtarsa duka ba. BJ 640.3
Za a canja tsarkaka masu-rai faraf daya, da kyaftar ido. Da muryar Allah za a darajanta su; yanzu za a ba su rashin mutuwa, kuma tare da tsarkaka da aka ta da su za su wanzu domin su sadu da Ubangijinsu a sararin sama. Malaiku za su kai kananan yara wurin uwayensu. Abokai da mutuwa ta raba su da dadewa za a sada su, babu rabuwa kuma, wakokin murna kuma za su hau zuwa birnin Allah. BJ 641.1
A kowane gefen karusar girgijen akwai fukafukai, a kalkashinsa kuma akwai garegare masu rai, kuma yayin da karusar ke haurawa, garegaren suna cewa: “Mai-tsarki,” fukafukin kuma, yayin da suke motsi, suna cewa, “Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki, Ubangiji Allah Madaukaki.” Fansassu kuma za su yi ihu su ce, “Haleluya!” yayin da karusar ke ci gaba zuwa sabuwar Urushalima. BJ 641.2
Kafin shigowa Birnin Allah, Mai-ceton zai ba masu binsa shaidar nasara ya kuma nada su da lambobin sarautarsu. An jera su, siffar murabba’i ne kewaye da Sarkinsu wanda siffarsa, a martaba ta zarce ta tsarkaka da ta malaiku, fuskansa kuma yana haskaka su cike da kauna. Ko ina cikin rundunan fansassu da yawansu ba mai iya kirgawa, idanunsu suna kallon Shi ne. Kowane ido yana duban darajarsa, Shi wanda aka bata fuskarsa fiye da na kowane mutum, siffarsa kuma aka ba ta fiye da ta ‘ya’yan mutane. Bisa kawunan masu nasaran, Yesu da hannun damansa zai aza rawanin daraja. Akwai rawani domin kowa da sabon sunansa a kai (Ruya 2:17), da rubutu mai-cewa “Tsarki ga Ubangiji.” Za a sa ma kowa dabinon nasara da giraya mai-walkiya ahannunsa. Muzika mai-dadi kwarai. Dadi da ya wuce misali zai cika kowace zuciya, za a kuma ta da kowace murya cikin yabo da murna, cewa: “A gareshi wanda yake kamnarmu, ya kwanche mu kuma daga zunubanmu chikin jininsa, ya sa mu mu zama mulki, mu zama priest ga Allahnsa da Ubansa; a gareshi daukaka da mulki har zuwa zamanun zamanai.” Ruya 1:5,6. BJ 641.3
A gaban fansassu, ga birni mai-tsarkin. Yesu za ya bude kofofi masu adon, al’umman da suka kiyaye gaskiyar kuma za su shiga ciki can za su ga Paradise na Allah, da gidan Adamu kafin ya yi zunubi. Sa’an nan muryan nan da ya fi duk wata muzika da kunen masu mutuwa sun taba ji, zai ce: “Yakinku ya kare,” “Ku zo, ku masu albarka na Ubana, ku gaji mulkin da an shirya dominku tun kafawar duniya.” BJ 642.1
Yanzu addu’ar Mai-ceton domin almajiransa ta cika, cewa: “Wanda ka ba ni, ina so su kazance wurin da ni ke.” “Marasa aibi chikin mafifichin farin zuchiya a gaban bayanuwar darajassa” (Yahuda 24), Kristi za ya mika ma Uban wadanda aka saya da jininsa, yana cewa: “Ga ni nan, da yayan da ka ba ni.” “Wadanda kai ka ba ni, na kiyaye su.” Dubi dai al’ajiban kauna mai-fansa! Dadin wannan sa’ar sa’anda Uba mara iyaka, sa’an da Ya dubi fansassun, zai ga kamaninsa, an rigaya an kawar da illar zunubi, burtuntunansa kuma an cire, ‘yan Adam kuma sun sake jituwa da Allah! BJ 642.2
Da kauna wadda ta wuce misali, Yesu zai marabci amintattun zuwa murnar Ubangiji. Murnar Mai-ceton ita ce ganin rayukan nan a mulkin, wadanda aka cetas ta wurin azabarsa da kaskancinsa yayin da suke gani cikn cetattun, wadanda aka kawo wurin Kristi ta wurin addu’o’insu da hadayarsu ta kauna. Yayin da su ke taruwa kewaye da babban farin kursiyin nan, murna da ta fi karfin bayanawa za ta cika zukatansu, sa’an da suka ga wadanda suka kawo ma Kristi, suka kuma ga daya ya samo wadansu, dukansu aka kawo su wurin hutawa, inda za su ajiye rawaninsu a sawayen Yesu, su kuma yabe Shi har abada. BJ 643.1
Yayin da ake marabtar fansassu cikin birnin Allah, za a yi ihu na yabo sabo da nasara, Adamun nan biyu sun kusa saduwa. Don haka Allah yana tsaye, hannuwansa a mike domin karban uban zuriyar mu — mutumin da Shi Ya halitta, wanda ya yi ma Mahalicinsa zunubi, wanda sabo da zunubinsa kuma Mai-ceton ke dauke da alamun giciyewarsa. Sa’an da Adamu zai ga alamun kusoshin, ba zai fadi a kirjin Ubangijinsa ba, amma cikin kaskantar da kai, zai fadi a sawayensa ne, yana cewa; “Ka isa, ka isa, Dan rago da an kashe!” A hankali Mai-ceton zai daga shi, ya kuma ce mashi ya sake kallon gidan nan na Adnin daga inda da dadewa aka kore shi. BJ 643.2
Bayan korarsa daga Adnin, rayuwar Adamu a duniya ta cika da bakinciki. Kowane ganye da ke bushewa, kowace dabbar hadaya, kowace burtuntuna a kyakyawar fuskar halitta, kowane la’ani ga tsarin mutum, yakan tuna ma Adamu da zunubinsa. Azabar nadama ta yi muni sa’an da ya ga zunubi yana karuwa, kuma akan amsa masa fadakarsa da zargin cewa shi din ne sanadin zunubi. Da tawali’u da hakuri, ya sha horon zunubi har kusan shekara dubu. Da aminci ya tuba daga zunubinsa, ya kuma mutu cikin begen tashin matattu. Dan Allah Ya fanshi kasawar mutum da faduwarsa; yanzu kuma ta wurin aikin kafara za a mayas da Adamu ga mulkinsa na fari. BJ 643.3
Cikin farinciki zai dubi itatuwan da ya so da, ainihin itatuwan da shi kansa da yakan diba a lokacinsa na murna da rashin laifi. Zai ga anab din da hannuwansa suka gyara, ainihin furanin da yakan ji dadin lura da su. Zuciyarsa za ta tuna ainihin yanayin; zai gane cewa hakika wannan Adnin ne aka mayar, da kyau ma fiye da lokacin da aka kore shi daga ciki. Mai-ceton zai kai shi wurin itacen rai, Ya tsinka Ya ba shi ya ci. Zai duba kewaye da shi ya ga taron iyalinsa fansassu suna tsaye a Paradise na Allah. Sa’an nan zai jefa rawaninsa mai-walkiya a sawayen Yesu ya fadi a kirjinsa ya rungumi Mai-fansar. Zai taba girayar zinariyar, sama kuma za ta amsa kuwwar wakar nasarar, cewa: “Na kirki ne, na kirki ne, na kirki ne Dan ragon da an kashe, yana raye kuma!” Iyalin Adamu za su amsa wakar, su kuma jefa rawaninsu a sawayen Mai-ceton yayin da suke durkusawa a gabansa cikin sujada. BJ 644.1
Malaikun da suka yi kuka lokacin faduwar Adamu, suka kuma yi farinciki sa’an da Yesu bayan tashinsa ya hau sama, bayan ya bude kabarin domin dukan wadanda za su ba da gaskiya ga sunansa, za su kalli wannan sake saduwar. Yanzu za su ga cikawar aikin fansa, za su kuma hada muryoyinsu cikin wakar yabon. BJ 644.2
A kan tekun madubi a gaban kursiyin, wanda yake kaman an garwaya shi da wuta, cike da darajar Allah, za a yi taruwar wadanda suka sami nasara kan bisan, da kan gumkinsa, da kan shaidarsa, da kan lamban sunansa. Tare da Dan ragon a kan Dutsen Sihiyona, rike molon Allah, zambar dari, da zambar arba’in da hudu din nan da aka fanshe su daga cikin mutane za su tsaya, a wurin kuma za a ji kamar muryar ruwaye masu- yawa, kamar rurin babbar tsawa kuma, za a ji “muryar masu molo suna kada molonsu.” Za su kuma raira “Sabuwar waka” a gaban kursiyin, wakan da ba wanda zai iya koyonsa sai dai mutum zambar dari da zambar arba’in da hudun din. Wakan Musa da Dan ragon ne, wakar tsira. Ba wanda zai iya koyonsa sai mutum zambar dari da zambar arba’in da hudun nan; da shike wakar abin da ya faru da su ne, wanda bai taba faruwa da wadansu ba. “Su ne su kan bi Dan rago inda Ya tafi duka.” Wadanda aka fyauce su daga duniya, daga cikin masu rai, ana ce da su “nunan fari ga Allah da Dan rago.” Ruya 15:2,3; 14:1-5. “Su ne wadanda suka fito daga chikin babban tsanani;” sun rigaya sun wuce lokacin wahala irin da ba a taba ji ba tun da aka yi al’umma; sun jimre azabar lokacin wahalar Yakub; sun rigaya sun tsaya ba matsakanci lokacin zubowar hukumcin Allah. Amma an tsiradda su, gama sun “wanke rigunansu, suka faranta su chikin jinin Dan ragon kuma.” “A chikin bakinsu ba a iske karya ba: marasa aibi ne su” a gaban Allah. “domin wannan suna gaban kursiyin Allah; suna masa bauta kuma dare da rana cikin haikalinsa: shi kuma wanda Ya zamna bisa kursiyin za ya inuwantadda su.” Sun rigaya sun ga duniya yadda yunwa da annoba sun lalatar da ita, rana kuma ta na da iko ta kone mutane da zafi mai-yawa, su kansu kuma sun jimre wahala da yunwa da kishirwa. Amma “Ba za su kara jin yunwa ba, ba kwa za su kara jin kishirwa ba; rana kuma ba za ta buge su ba, ko kowane irin zafi: gama Dan rago wanda ke chikin tsakiyar kursiyin za ya zama makiyayinsu, za ya bishe su kuma wurin mabulbulan ruwaye na rai: Allah kuma za ya share dukan hawaye daga idanunsu.” Ruya 7:14-17. BJ 644.3
Cikin dukan sararaki akan ilimantar da zababbu na Allah a kuma horar da su cikin makarantar gwaji. Sun yi tafiya cikin matsatsun hanyoyi a duniya; an tsarkake su cikin tanderun azaba. Sabo da Yesu sun jimre adawa da kiyayya da bata suna. Sun bi Shi cikin yake yake munana; sun sha musun kai da yankan buri. Ta wurin abin da ya faru da su sun gane muguntar zunubi da ikonsa da laifinsa, da kaitonsa; kuma suna kallon shi da kyama. Sanin hadaya mara-matuka da aka yi domin magance zunubi zai ladabtar da su ga ganin kan su, ya kuma cika zukatansu da godiya da yabo da wadanda basu taba faduwa ba ba za su iya faimta ba. Suna kauna da yawa domin an gafarta masu da yawa. Da shike sun zama da rabo cikin wahalolin Kristi, sun cancanta su zama da rabo cikin darajarsu. BJ 645.1
Magadan Allah sun zo daga kauyuka, daga kurukuku, daga wuraren horo, daga duwatsu, daga hamada, daga kogunan kasa, daga kogunan teku. A duniya sun sha talauci da azaba da zalunci. Miliyoyi sun je kabari a wulakance domin sun ki su amince da rudin Shaitan. Kotunan kasa suka hukaumta su cewa su masu-laifi mafi muni ne. Amma yanzu “Allah mai-shari’a ne da kansa.” Zabura 50:6. Yanzu za a warware hukumcin duniya. “Za ya kuma kawasda zargin mutanensa” Ishaya 25:8. “Za a che da su Jama’a mai-tsarki, Pansassu na Ubangiji.” Ya rigaya Ya umurta “a ba su dajiyar fure maimakon toka, mai na farin chiki maimakon makoki, mayafi na yabo maimakon ruhu na nauyi.” Ishaya 62:12; 61:3. Ba za su kasance kamammu masu shan azaba, a warwatse, wulakantattu kuma ba. Daga nan za su kasance tare da Ubangiji har abada. Za su tsaya a gaban kursiyin, yafe da tufafi masu —tamanin da mutane da aka fi girmamawa a duniya basu taba sa irinsu ba. Za a daura masu rawani masu daraja da ba a taba daura ma wani sarki a duniya ba. Kwanakin azaba da kuka sun kare har abada. Sarkin daraja Ya shafe hawaye daga dukan fuskoki; an cire kowane dalilin bakin ciki. Da ganyen dabino a hannuwan su za su raira wakar yabo mai-dadi; kowace murya za ta raira har sai wakar ta cika kowane wuri a sama, suna cewa: “Cheto ga Allahnmu ne, wanda ya zamna bisa kursiyin, ga Dan ragon kuma.” Kuma dukan mazamnan sama za su amsa su ce: “Amin: albarka da daukaka da hikima, da godiya da daraja, da iko da karfi, ga Allahnmu har zuwa zamanun zamanai.” Ruya 7: 10,12 . BJ 646.1
Cikin rayuwarmu a duniyan nan, za mu iya fara gane batun fansa ne kawai. Da ganewar mu mai-iyaka, za mu iya bimbini kan kunya da darajar, rai da mutuwar, adalci da jinkan da suka sadu a giciyen ne; duk da haka, komi yawan tunanin mu baza mu iya fahimtar duk cikar ma’anar fansa ba. Kadan kawai ake fahimtar tsawo da fadi da zurfin kauna mai-kawo fansa. Ba za a sami cikakkiyar fahimtar shirin fansa ba, ko ma sa’anda fansassu sun ga yadda ake ganinsu, suka kuma san yadda aka sansu: amma har cikin dukan sarraki har abada sabobin gaskiya za su ci gaba da bayanuwa ga zukatan mutane. Ko da shike bakinciki da azaba da jarabobin duniya za su kare, za a kuma cire sanadinsu, mutanen Allah za su ci gaba da sanin farashin cetonsu. BJ 647.1
Giciyen Kristi ne zai zama kimiyyar fansasssu da wakarsu har abada. Cikin darajar Kristi za su ga giciyewar Kristi. Ba za a taba manta cewa Shi wanda Ya halitta, Ya kuma rike dukan duniyoyi, Kaunatace na Allah, Martabar sama, Shi wanda malaiku suka yi murmnar girmama Shi, Ya kaskantar da kansa domin Shi daukaka mutum fadadde, cewa Ya dauki laifin zunubi da kunyarsa, da boyewar fuskar Ubansa, har sai da kaiton bataciyar duniya suka karya zuciyarsa, suka kuma murkushe ransa a giciyen Kalfari. Cewa Mahalicin dukan duniyoyi, Mai-rike da dukan kadara, ya ajiye darajarsa, Ya kuma kaskantar da kansa sabo da kaunar mutum da yake yi zai ci gaba da ba dukan halitta mamaki da sha’awa har abada. Dukan al’ummomin cetattu za su dubi mai-cetonsu su kuma kalli daraja mara matuka ta Uban, suna haskakawa a fuskarsa, yayin da sue kallon kursiyinsa wanda daga har abada zuwa har abada ne, sun kuma san cewa mulkinsa ba zai kare ba, za su kuwa barke da wakar murna cewa: “Ya isa, Ya isa, Dan ragon da an kashe, Ya kuma fanshe mu zuwa ga Allah da jininsa mafi-daraja.” BJ 647.2
Asirin giciyen zai bayana dukan sauran asiri cikin hasken da ke kwararowa daga Kalfari za su zama da ban sha’awa gwanin kyau kuma. Jin kai da tausayi da kaunar iyaye za su hadu da tsarki da adalci da iko. Yayin da mu ke kalon martabar kursiyinsa, da daukakarsa za mu ga halinsa yadda Ya bayana shi da ban sha’awa, mu kuma gane ma’anar lakabin nan “Uban mu.” BJ 648.1
Za a ga cewa Shi wanda hikimarsa ba ta da iyaka, bai iya fito da wani shiri domin cetonmu ba, sai dai giciyewar Dansa. Diyyar hadayan nan ita ce murnar cika duniya da fansassun mutane masu-tsarki da murna, marasa mutuwa kuma. Sakamakon yakin Mai-ceton da ikokin duhu abin murna ce ga fansassu wadda ke kawo daukaka ga Allah har abada. Kuma hakanan ne tamanin rai har ma Uban Ya gamsu da farashin da aka biya; Kristi kansa kuma, sa’an da Ya kalli sakamakon babban hadayar tasa ya gamsu. BJ 648.2