A karhen shekara dubu din, Kristi zai sake dawowa duniya. Zai zo tare da rundunan fansassun da malaiku masu rufa masa baya. Yayin da yake saukowa da martaba mai-ban tsoro zai bukaci matattun miyagu su taso su karbi hallakarsu. Za su taso, babban runduna da ba mai-kirgawa, kamar yashin teku. Sun bambanta sosai da wadanda aka ta da su a tashin farko! An suturta masu- adalci da kuruciya, da kyau, mara mutuwa. Miyagu suna da burbushin ciwo da mutuwa. BJ 658.1
Kowane ido a wancan taron jama’an zai juye domin ya kalli darajar Dan Allah. Da murya daya rundunar miyagun za su ce: “Mai-albarka ne shi wanda yake zuwa chikin sunan Ubangiji!” Ba don suna kaunar Yesu ne za su yi wanan furcin ba. Karfin gaskiya ne zai tilasta kalmomin su fito daga lebunansu. Yadda miyagun suka shiga kabarbarunsu, hakanan ne kuma za su fito da kiyayya ga Kristi da kuma ruhun nan nasu na tawaye. Ba za su sami wata damar gyarta kurakuran halayensu na rayuwarsu ta da ba. Damar ba za ta anfane su ba. Rayuwar ketare doka ba ta sake zukatansu ba. Da za a ba su wani zarafi kuma, da za su yi anfani da shi yadda suka yi anfani da na farin ne, wajen kauce ma umurnin Allah da ta tayar da tawaye gare Shi. BJ 658.2
Kristi za ya sauko a kan Dutsen Zaitun ne, inda, bayan tashin Sa daga matattu, Ya hau, kuma inda malaiku suka maimaita alkawalin nan na dawowansa. Annabin ya ce: “Ubangiji Allahna, kuma za ya zo tare da dukan tsarkakansa.” “A chikin wannan rana kwa sawunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun, wanda ke fuskanta Urushalima wajen gabas, Dutsen Zaitun kwa za ya rabu a tsaka,… da kwari mai-girma kuma a tsakani.” “Ubangiji za ya zama sarki bisa dukan duniya; a chikin wannan rana Ubangiji daya ne, sunansa kuma daya ne.” Zechariah 14:5, 4, 9. Sa’an da Sabuwar Urushalima ta fito daga cikin sama, da ban sha’awan ta, za ta sauka a wurin da aka tsarkake, aka kuma shirya dominta ne, kuma Kristi, tare da mutanensa da malaikun, zai shiga Birni Mai-tsarkin. BJ 658.3
Yanzu Shaitan zai shirya babban yaki na karshe don neman daukaka. Sa’an da aka kwace ikonsa aka kuma yanke shi daga aikin sa na rudi, sarkin muguntan zai yi bakinciki, ya kuma damu; amma sa’an da aka ta da matattun miyagu, idan ya ga taron jama’a da ke gefensa, begen shi zai farfado, kuma zai yi himman cewa ba zai bar babban jayayyan ba. Zai tattara dukan mayakan batattu kalkashin tutarsa, ta wurin su kuma zai yi kokaarin aiwatar da shirye shiryensa. Miyagu kamammun Shaitan ne. Ta wurin kin Kristi, sun karbi shugabancin shugaban tawayen ke nan. Suna shirye su karbi shawrwarinsa, su yi abin da ya umurce su. Duk da haka bai yarda cewa shi ne Shaitan ba, sabo da rinto kawai. Yana ikirarin cewa shi ne sarki, ainihin mai-duniyar, wanda kuma aka kwace masa gadonsa ba bisa ga doka ba. Yana nuna kansa ga talakawansa rudaddu cewa shi mai-fansa ne, yana tabbatar masu cewa ikon shi ya fito da su daga kabarbaru, kuma ba da jimawa ba, zai kubutar da su daga zalunci mafi-muni. Da shike Kristi ba ya wurin, Shaitan zai aikata al’ajibai don tabbatar da maganarsa. Zai karfafa kamamu, ya kuma motsa kowa da ruhunsa da karfin sa kuma. Zai yi masu tayin shugabantarsu zuwa ga yaki da tsarkaka don karban mallakar Birnin Allah kuma. Da murnar mugunta zai ja hankula zuwa ga miliyoyin nan da aka tayar daga matattu ya ce a matsayin shi na shugaban su shi zai hambarar da mulkin ya kuma sake karban kursiyansa da mulkinsa. BJ 659.1
Cikin babban taron nan akwai tulin mutane da suka kasance kafin ruwan tufana; mutane masu girman jiki da tunani mai-kyau ainun, wadanda suka yarda da bishewar fadaddun malaiku, suka ba da dukan kwarewarsu da saninsu ga daukaka kansu; mutanen da al’ajiban aikin hannuwansu suka sa duniya ta mai da gwanintar tasu gumaka, amma kuma muguntarsu da miyagun kage kagensu sun kazantar da duniya suka kuma bata surar Allah, wanda ya sa Shi Ya shafe su daga fuskar halitta. Cikinsu akwai sarakuna da janar janar da suka yi nasara da al’aummai, jarumawa da basu taba kasa cin yaki ba, mayaka masu alfahari da buri, wadanda zuwansu kawai yakan sa al’aummai su yi rawan jiki. Sa’an da suka mutu kuma ai basu sake hali ba. Sa’an da suka fito daga kabari, za su ci aba da irin tunaninsu daidai inda suka tsaya. Za su ci gaba da son yakin da ya mallaki zukatansu lokacin da suka mutu. BJ 660.1
Shaitan zai yi shawara da malaikunsa, sa’an nan sarakunan nan da jarumawa da mayakan nan za su dubi karfinsu da yawansu, sai su ce wai mayakan da ke cikin birnin ba su da yawa kamarsu, kuma za a iya yin nasar abisan su. Za su tsara shirye shiryensu na kwace wadata da darajar Sabuwar Urushalima. Nan take dukansu za su fara shiri domin yaki. Gwanayen masu aikin hannu za su kera makamai. Shahararrun shugabannin soja za su shirya kungiyoyin mayaka su karkasa su kamfani kamfani, sashi sashi. BJ 660.2
Daga karshe za a ba da umurni cewa a fara yakin, rundunan nan da ba mai-kirgawa kuma za ta taso, mayaka irin da ba a taba hadawa ba a duniya, kuma taron dakarun dukan sararaki tun da aka fara yaki a duniya ba za su kai yawan wannan rundunan ba. Shaitan shugaban mayaka zai shugabance su, malaikunsa kuma za su hada dakarunsu domin fadan nan na karshe. Akwai sarakuna da mayaka cikin rundunarsa, sauran jama’a kuma za su bi bisa ga kamfanoninsu, kowane dayansu kalkashin shugabansu. Bisa tsari za su ci gaba, suna ketare kwari da tudu zuwa Birnin Allah. Bisa umurnin Yesu, za a rufe kofofin Sabuwar Urushalima, mayakan Shaitan kuma za su kewaye birnin su shirya kai hari. BJ 660.3
Yanzu kuma Kristi zai bayana ga magabtansa. Can bisa birnin, a kan harsashe na zinariya, akwai kursiyi a sama da aka daga. A kan kursiyin nan Dan Allah yana zaune, kuma kewaye da Shi talakawan mulkinsa ne. Ikon Krisiti da martabansa, babu harshen da zai iya bayanawa, ba alkalami da zai iya kwatantawa. Darajar Uba Madawami za ta kewaye Dansa. Hasken kasancewarsa zai cika Birnin Allah ya kwarara, ya wuce kofofin, ya cika dukan duniya da walkiyarsa. BJ 661.1
Mafi-kusa da kursiyin akwai wadanda a da suka yi himma cikin aikin Shaitan, amma, kamar itace daga cikin wuta, aka fizge su, suka kuma bi Mai-cetonsu da dukufa sosai. Biye da su akwai wadanda suka kasance da halayen Kirista, inda karya da rashin aminci suka dawama, wadanda suka girmama dokar Allah lokacin da Kiristan duniya suka rika cewa dokan nan wofi ne, da kuma miliyoyi na dukan sararaki da aka kashe sabo da imaninsu. Bayan wannan akwai “taro mai-girma wanda ba mai-kirgawa, daga chikin kowane iri da dukan kabilu, da al’ummai da harsuna,…gaban kursiyin da gaban Dan ragon, suna yafe da fararen riguna, da ganyayen dabino chikin hannuwansu.” Ruya 7:9. Yakinsu ya kare, sun yi nasara. Sun yi tseren, sun kai wurin ladar. Ganyen dabinon da ke hannuwansu alama ce ta nasararsu, farar rigar kuma shaidaar adalci mara-aibi na Kristi wanda yanzu nasu ne. BJ 661.2
Fansassun za su ta da wakar yabo da za ta dinga amsa kuwa ko ina a sama, suna cewa: “Cheto ga Allahnmu wanda Ya zamna bisa kursiyin, da Dan ragon kuma.” Aya 10. Malaiku kuma za su hada muryoyinsu cikin yabo. Kamar yadda fansassu suka ga ikon Shaitan da muguntarsa, haka za su ga cewa ba wani ikon da ya isa ya ba su nasaran nan sai dai ikon Kristi. Cikin dukan rundunan nan mai-haskakawa, ba wanda ke gani Kaman da ikon kan shi ne ya yi nasara. Ba wanda ke maganar abin da suka yi ko wahalar da suka sha, amma kan maganar kowace waka ita ce ceto ga Allahnmu da Dan ragon kuma. BJ 661.3
A gaban taron mazamnan duniya da sama za a yi nadin sarauta na karshe na Dan Allah. yanzu kuma yafe da martaba da iko fiye da na kowa, Sarkin sarakunan zai fadi hukumci kan masu tawaye ga gwamnatinsa, ya kuma zartas da adalci kan wadanda suka ketare dokarsa suka kuma wulakanta mutanensa. In ji annabin Allah: “ Na ga kuma babban farin kursiyi da wanda ke zamne a bisansa, wanda duniya da sama suka guje ma fuskatasa; ba a kwa sami masu wuri ba. Na ga matattu kuma kanana da manya, suna tsaye a gaban kursiyin; aka bude littattafai: aka bude wani litafi kuma,litafin rai ke nan; aka yi ma matattu shari’a kuma bisa ga abin da aka rubuta chikin litatafai, gwalgwadon ayukansu.” Ruya 20:11,12. BJ 662.1
Da zaran an bude littattafan, idon Yesu kuma ya dubi miyagu, za su tuna kowane zunubi da suka taba yi. Za su ga daidai inda suka kauce daga hanyar tsabta da tsarki, nisan inda girman kai da tawaye suka kai su cikin ketarewar dokar Allah. Jarabobin da suka karfafa ta wurin aikata zunubi, albarkun da suka kawar, yan sakon Allah da aka rena, fadaka da aka ki ji, jiye jiyen kai da aka ki tawurin zukatan taurin kai da rashin tuba — duka za su bayana kamar an rubuta da harufofin wuta. BJ 662.2
A bisa kursiyin, za a ga giciyen, kuma kamar majigi za a nuna jarabawa da faduwar Adamu da matakai bi da bi na babban shirin fansa. Haifuwar Mi-ceton, rayuwarsa ta saukin kai da biyayya, baptismarsa a Urdun, azuminsa da jarabawarsa a jeji, aikinsa cikin jama’a inda ya bayana ma mutane albarkun sama mafi muhimmanci; ayukansa na kauna da jinkai, daren da yakan kwana addu’a da tsaro shi kadai a kan duwatsu; shirye shiryen masu-kishi, da mugunta da kiyayya don ayukansa na nagarta, wahalarsa mai-tsanani a Gethsemani sabo da zunuban duniya duka, bashewar shi a hannun masu-kisa, ababan ban tsoro na daren nan mai-ban-kyama, ga Shi fursuna mara-gardama, wanda almajiransa kaunatattu suka yashe Shi, da rashin ladabi aka bi da Shi titunan Urushalima, Dan Allah da aka kai Shi gaban Annas, aka gurbanar da Shi a fadar babban priest, a zauren shari’ar Bilatus, gaban matsoracin azalumin nan Hirudus, aka yi masa ba’a, aka zage Shi, aka zalunce Shi, sa’an nan aka yanka masa hukumcin kisa, za a nuna dukan wadannan. BJ 662.3
Yanzu kuma za a bayana ma taron jama’ar ababan da suka faru a karshe: Mai-shan wahalan a hanyarsa zuwa Kalfari; Sarkin sama a rataye kan giciyen; priestoci masu-girman kai da jama’a masu ba’a game da wahalarsa; duhun nan na musamman; duniya mai-lumfashi, fansassu na duwatsu, budaddun kabarbaru da suke nuna lokacin da Mai-fansa Ya ba da ransa. BJ 663.1
Al’amarin zai bayyana, daidai yadda al’amura suka kasance da. Shaitan da malaikunsa da talakawansa ba su da iko su kau da ido daga hoton aikinsu. Kowa zai tuna fannin da shi ya aikata. Hirudus, wanda ya karkashe yaran Baitalahmi, domin shi hallaka Sarkin Israila; yar banzan nan Herodiya wadda jinin Yohanna mai-baptisma ke kanta; Bilatus kumaman nan; sojoji masu-gori; prirestoci da shugabanni da taron jama’an nan da suka yi ihu cewa; “Jininsa a kan mu da ‘ya’yanmu!” - dukan su za su ga yawa laifinsu. A banza za su so su buya daga martabar fuskarsa da ta fi rana haske, yayin da fansassu za su jefa rawaninsu a sawayen Mi-ceton, suna cewa: “Ya mutu domi na!” BJ 663.2
A cikin fansassun akwai manzanin Kristi: jarumi Bulus, Bitrus mai-himma, Yohanna kaunatace mai-kauna, da amintattun yan’uwansu, tare da su kuma akwai babban rundunar wadanda aka kasha sabo da imaninsu, yayin da a bayan ganuwar, tare da kowane abu mai-ban kyama, wadanda suka tsananta masu ne, suka kai su kurkuku, suka kashe su kuma. Akwai Nero, mugun nan azalumi, yana kallon murna da farincikin wadanda ya taba azabta masu ya kuma ji dadin ganin azabarsu. Uwarsa za ta kasance a wurin domin ta ga sakamakon aikinta; ta ga yadda halin mugunta da ta ba dan ta, da fushin da tasirinta da kwatancinta suka karfafa, sun haifar da laifukan da suka sa duniya ta ji tsoro. BJ 663.3
Akwai prietoci da sauran ma’aikatan ‘yan paparuma da suka rika cewa su jakadun Kristi ne, amma suka yi anfani da zalunci don mallakar lamirin mutanen Kristi din. Akwai paparuma dabam dabam masu-girman kai da suka daukaka kansu fiye da Allah, suka kuma dauka cewa za su iya canja dokar Madaukaki. Su ma akwai lissafin da za su bayar ga Allah da ba za su so bayarwa ba. A kuraren lokaci za su ga cewa Shi Masanin komi yana kishin dokarsa, kuma babu yadda zai kubutar da mai-laifi. Za su sani yanzu cewa Kristi yana hada burinsa da na mutanensa da ke wahala, za su kuma ji karfin maganarsa cewa: “Da shike kuka yi wannan ga guda daya a chikin wadannan mafiya-kankanta ni kuka yi ma.” Matta 25:40. BJ 664.1
Dukan miyagun duniya sun gurbana a gaban shari’ar Allah, da zargin cin amanar gwamnatin sama. Ba su da mai-kare su, ba su da hujja; za a kuma furta hukumcin mutuwa ta har abada a kansu. BJ 664.2
Yanzu zai bayana ga kowa cewa hakin zunubi ba ‘yancin kai da rai madawami ba ne, amma bauta ce, da hallaka da mutuwa. Miyagu za su ga abin da suka ki ta wurin rayuwarsu ta tawaye. Sun rena nauyin daraja lokacin da aka yi masu tayinta, amma yanzu suna sha’awar ta. Batace zai ce: “Da na mallaki dukan wannan, amma na zaba in nisantar da shi daga wuri na…. Na sauya salama da murna da girma, da rashin kirki da wahala.” Kowa zai ga cewa hana shi shiga sama daidai ne. Ta wurin rayuwarsu, sun rigaya sun bayana cewa: “ba ma son wannan mutumin [Yesu] ya yi mulki bisanmu.” BJ 664.3
Kaman a mafalki, miyagu za su kalli nadin sarautar Dan Allah. A hannuwansa za su ga allunan dokar Allah, umurnin da suka rena, suka ketare. Za su shaida ihun mamaki da murna da sha’awa daga cetattun; kuma yayin da amon sautin ke mamaye jama’a da ke bayan katangar birnin, duka, da murya daya za su ce: “Ayukanka masu girma ne, masu-ban al’ajibi, ya Ubangiji Allah Mai-iko duka; halullukanka kuma masu-adilchi ne, masu-gaskiya kuma, ya sarkin zamanai.”(Ruya 15:3); kuma za su yi rub da ciki, su yi sujada ga Sarkin rai. BJ 664.4
Shaitan zai shanye, yayin da yake kallon martraba da darajar Kristi. Shi wanda da can malaika ne, zai tuna daga inda ya fadi. Malaika mai-walkiya, “dan asubahi,” dubi yadda ya canja, ya lalace! Daga majalisa inda ake girmama shi, yanzu ba dama ya shiga wurin, har abada. Zai ga wani yanzu kusa da Uban, yana rufe darajansa. Ya rigaya ya ga rawanin da malaika mai-kwarjini ya sa a kan Kristi, ya kuma san cewa babban matsayin malaikan nan da na shi Shaitan ne. BJ 665.1
Zai tuna gidansa na lokacin rashin laifi, ga tsabta da salama da gamsuwa da yake da su kafin ya fara gunaguni kan Allah, da kuma kishin Kristi. Zarginsa da tawayensa da rudinsa don samun goyon bayan malaiku, taurin kansa wajen kin tuba lokacin da Allah zai iya gafarta masa, dukan wadannan za su bayana a gabansa. Zai tuna aikinsa cikin mutane, da sakamakonsa: kiyayyar mutane, hallakar rayuka, tasowa da faduwar mulkoki, hambarar da sarauta, tashe tashen hankula bi da bi, sabani, da canje canje. Zai tuna kokarinsa na hamayya da aikin Kristi, da kara nutsar da dan Adam kullum. Zai ga cewa kulle kullensa basu iya hallaka wadanda suka dogara ga Yesu ba. Sa’anda Shaitan ya dubi mulkinsa, da sakamakon famarsa, zai ga faduwa ne da lalacewa kadai. Ya sa jama’a sun gaskata cewa Birnin Allah zai yi saukin kamawa; amma kuma ya san cewa wannan karya ce. Akai akai, cikin babban jayayyar, an yi nasara da shi, aka kuma tilasta shi ya yarda da hakan. Ya san iko da martabar Madaukakin sosai. BJ 665.2
Manufar babban dan tawayen kullum shi ne ya ba da hujjar ayukansa, ya kuma nuna cewa gwamantin Allah ne ya jawo tawayen. Inda ya mai da dukan hankalinsa ke nan. Ya yi aiki da saninsa, bisa tsari kuma, ya kuma yi nasara sosai inda ya sa tulin jama’a suka yarda da labarinsa game da babban jayayyan da an dade ana yi. Shekaru dubbai, wannan sarkin laifin yana mai da karya gaskiya. Amma lokaci ya yi yanzu a karshe dai da za a yi nasara bisa karyar, a kuma bayana tarihin Shaitan da halinsa. Cikin babban kokarin shi na karshe don hambarar da Kristi, ya hallaka mutanensa, ya kuma karbi mallakar Birnin Allah, an fallasa babban mai-rudin gaba daya. Wadanda suka hada kai da shi za su ga faduwar aikinsa gaba daya. Masu-bin Kristi da malaiku masu biyayya, za su ga dukan iyakar kulle kullen Shaitan game da gwamnatin Allah. Shi ne dukan duniya za ta yi kyamarsa. BJ 666.1
Shaitan zai ga cewa tawayen shi ya sa bai cancanci shiga sama ba. Ya rigaya ya horar da kansa cikin yaki da Allah; tsabta, da salama da jituwar sama a gare shi za su zama azaba ne. Zarge zargensa game da jinkan Allah da adalcinsa sun kare yanzu. Renin da ya yi kokarin kawo ma Yahweh ya koma kansa dungum. Yanzu kuma Shaitan zai durkusa ya furta cewa hukumcinsa daidai ne. BJ 666.2
“Wane ne za ya rasa jin tsoro, ya rasa daukaka sunanka, ya Ubangiji.” Gama kai kadai Mai-tsarki ne; gama dukan al’ummai za su zo su yi sujada a gabanka; gama ayukanka masu-adlichi sun bayanu.” Aya 4. Yanzu kowane batu na gaskiya da karya cikin dadaddiyar jayayyan nan an rigaya an bayana shi. Sakamakon tawaye, da kawar da dokokin Allah sun rigaya sun bayyanu a gaban dukan halitu masu-tunani. An bayana ma dukan halitta bambanci da ke tsakanin yanayin mulkin Shaitan da gwamnatin Allah. Aikace aikacen Shaitan kansa sun rigaya sun yanka masa hukumci. Hikimar Allah da adalcinsa da nagartaarsa sun tabbata a bayyane. Za a ga cewa dukan ma’amalansa cikin babban jayayyan nan Ya yi su domin anfanin mutanensa har abada da kuma anfanin dukan duniyoyin da ya halitta. “Dukan ayukanka za su albarkacheka ya Ubangiji; tsarkakanka kuma za su albarkacheka.” Zabura 145:10. Tarihin zunubi zai tsaya har abada a matsayin shaida cewa kasncewar dokar Allah wajibi ne don farincikin dukan wadanda Ya halita. Da sanin dukan baatuttuwan babban jayayyar, dukan halita masu-biyayya da masu-tawaye, tare gaba daya za su ce: “Tafarkunka adalchi da gaskiya ne, Ya Sarkin tsarkaka.” BJ 666.3
A gaban dukan halita, an rigaya an bayana babban hadayan da Uban da Dan suka yi a madadin mutum lokacin da Kristi Ya dauki matsayin Shi, aka kuma daukaka Shi fiye da ikoki da kowace suna. Sabo da murnan da ke gabansa ne, cewa zai kai mutane da yawa ga daraja, shi ya sa ya jimre giciyen, ya kuma yi watsi da kunyar. Kuma ko da shike bakincikin da kunyar sun fi karfin ganewa, duk da haka, murnar da darajar sun fi. Zai dubi fansassu da aka sabunta cikin siffarsa, kowace zuciya dauke da cikakkiyar shaidar Allah, kowace fuska tana nuna kamanin Sarkinsu. Cikinsu zai ga sakamakon wahalar ruhunsa, zai kuma gamsu, sa’an nan cikin murya da ta kai dukan taron masu-adalci da na miyagu, zai ce: “Duba ga wadanda jini na ya sayo! Domin sun a sha wahala, dominsu na mutu, domin su kasance tare da ni har dukan sararaki har abada.” Sa’an nan wakar yabo za ta hau daga wurin masu fararen tufafin nan kewaye da kursiyin, cewa: “Dan rago wanda an kashe mai-isa ne shi karbi iko, da wadata, da hikima, da karfi, da daraja, da daukaka, da albarka.” Ruya 5:12. BJ 667.1
Ko da shike an matsa ma Shaitan ya amnice da adalcin Allah, ya kuma durkusa ma fifikon Kristi, halinsa ba zai sake ba. Ruhun tawaye, kamar babban ambaliyar ruwa, zai sake kwararowa. Cike da garaje, zai dauki kudurin cewa ba zai bar babban jayayyar ba. Lokaci ya zo domin fada na karshe da Sarkin sama. Zai ruga zuwa tsakiyar talakawan shi, ya yi kokarin motsa su da fushinsa, ya kuma ingiza su domin yaki nan take. Amma cikin miliyoyin nan da ya rude su zuwa cikin tawaye, ba wadanda yanzu za su yarda da mulkin shi. Ikon shi ya kare.Miyagun suna cike da kiyayya dayan da ke motsa Shaitan; amma za su ga cewa ba su da bege, ba za su iya yin nasara bisa Yahweh ba. Fushin su zai koma kan Shaitan da wakilansa cikin rudi, sa’an nan da fushin aljannu, za su juya kansu. BJ 667.2
In ji Ubangiji Yahweh: “Tun da ka mai da zuciyarka sai ka che zuchiyar Allah; ni ma ga shi sai in jawo maka baki masu ban tsoro na al’ummai: za su zare takobinsu su yi yaki da jamalin hikimarka, su kazantadda haskenka. Za su gangaradda kai har ramin.” “Na kwa hallaka ka, ya cherub, mai-rufewa, na raba ka da duwatsun wuta… na fyade ka, na mike ka a gaban sarakuna, su zuba maka ido…ka zama abin tsoro ba ka da sauran zama ba dadai.” Ezekiel 28:6-8, 16-19. BJ 668.1
“Gama dukan kayan mayaki chikin rigimar yaki, da tufafi mirginannu chikin jini, za su zama na konewa, abinchin wuta.” “Gama Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai, yana hasala da da duka rundunassu: ya hallaka su sarai, ya bashe su ga kisa.” “Za ya zubo da tarkuna bisa masu mugunta; wuta da kibiritu da iska mai-kuna su ne za su zama rabon kokon su.” Ishaya 9:5; 34:2; Zabura 11:6. Wuta za ta sauko kasa daga wurin Allah cikin sama. Duniya za ta tsage. Makaman da aka boye cikinsu za a fitar. Harsunan wuta masu konewa za su bullo daga kowane kogo. Duwatsu kansu suna konewa da wuta. Ranar ta zo da za ta kuna kamar tanderu. Rundunan za su narke da kuna mai-zafi, duniya kuma da ayukan da ke cikin ta za su kone. Malachi 4:1; Bitrus II, 3:10. Fuskar duniya za ta zama kamar narkakkiyar dunkule guda, ta zama koramar wuta. Lokacin hukunci ne da hallakawar marasa biyayya ga Allah- “ranar daukan pansa ta Ubangiji ke nan, shekara ta sakaiya che chikin mahawara ta Sihiyona.” Ishaya 34:8. BJ 668.2
Miyagu za su karbi ladansu a duniya. Misalaii 11:31. “Za su zama tattaka; ranan da ke zuwa kuma za ta kokone su, in ji Ubangiji mai-rudauna.” Malachi 4:1. Za a hallaka wadansu, kamar faraf daya ma, yayin da wadansu za su sha wahala kwanaki da yawa. Za a hori kowa “gwalgwadon ayukansu” ne. Da shike an rigaya an juye ma Shaitan zunuban masu-adalchi a kansa, za a sa Shi ya sha wahala ba domin tawayen shi kadai ba, amma domin dukan zunuban da ya sa mutanen Allah suka yi. Horon shi zai zarce na wadanda ya rude su. Bayan dukan wadanda sun fadi sabo da rudinsa sun mutu, shi zai ci gaba da rayuwa yana shan wahala. Cikin wutar tsarkakewar a karshe za a hallaka miyagu, tushe da reshe. Shaitan ne tushen, masu- bin shi ne ressan. An kamala dukan horon duka; an cika dukan sharuddan adalci, sama da kasa kuma da suke kallo, zasu shaida adalcin Yahweh. BJ 669.1
Aikin hallakan Shaitan ya kare. Shekara dubu shida yana yin abin da ya ga dama, yana cika duniya da kaito, yana jawo bakinciki ko ina cikin dukan halitta. Dukan halitta ta yi kishi ta kuma fama da azaba. Yanzu za a tsirar da halitar Allah har abada daga kasancewar Shaitan da jarabobinsa. “Dukan duniya tana zamne a huche; fashe da rairawa suke yi.” Ishaya 14:7. Kuma ihun yabo da nasara zai tashi daga dukan halittta masu biyayya. “Murya ta babban taro,” “kamar muryar ruwaye masu yawa kuma, kamar muryar tsawa mai-karfi kuma, suka che, Halellujah: gama Ubangiji Allahnmu Mai-iko duka yana mulki.” Ruya 19:6. BJ 669.2
Yayin da duniya ke kunshe cikin wutar hallaka, masu-adalci suna zaune cikin Birni Mai-tsarkin. Mutuwa ba ta da iko kan wadanda suke cikin masu tashin matattu na fari. Ko da shike Allah wuta mai-cinyewa ne ga miyagu, ga mutanensa kuwa, Shi rana ne da garkuwa kuma. Ruya 20:6.; Zabura 84:11. BJ 669.3
“Na ga sabuwar sama da sabuwar duniya kuma: gama sama ta fari da duniya ta fari sun shude.” Ruya 21:1. Wutar da za ta cinye miyagu za ta tsarkake duniya. Za a share kowane burbushin la’anar. Babu wata lahira mai-konawa har abada da za ta dinga tuna ma fansassu wannan sakamakon na zunubi. BJ 670.1
Abin tunawa daya ne kadai ya rage: Mai-fansar mu zai kasance da alamun giciyewarsa har abada. A bisa kansa da aka kuje, a gefensa, da hannuwansa, da sawayensa ne kadai akwai alamun mugun aikin da zunubi ya yi. “Shekinsa yana kama da haske; kalkali suna fita daga hannunsa; ikonsa kwa a rufe yake.” Habakuk 3:4. A gefen nan nasa da jinin da ke sasanta Allah da mutum ke fitowa ne darajar Mai-ceton take, can ne ikonsa ke rufe. Da shike Mai-girma ne, wanda zai yi ceto, ta wurin hadayar fansa, domin wannan yana da ikon da zai zartas da adalci kan wadanda suka rena jinkan Allah. Kuma alamun kaskancinsa su ne bangirmansa mafi-yawa; har abada raunukan Kalfari za su nuna yabonsa, su bayana ikonsa. BJ 670.2
“Ke fa ya hasumiyar garke, tudun diyar Sihiyona, a gare ki za ya zo; I, mulkin zamanin da za ya zo.” Mikah 4:8. Lokacin da tsarkaka suka yi begensa da marmari, tun da takobin wutan nan ya hana Adamu da Hawa’u shiga Adnin, lokacin ya zo, lokacin “pansar abin mulki na Allah.” Afisawa 1:14. Duniyan da aka fara ba mutum, cewa mulikin shi ne, ta bashe shi cikin hannuwan Shaitan, kuma duk da dadewa da ta yi a hannun Shaitan, an rigaya an dawo da ita ta wurin shirin fansa. Dukan abin da ka rasa ta wurin zunubi, an mayar. “Gama hakanan Ubangiji Ya fadi… mai-sifanta duniya, mai-yinta kuma; shi wanda ya kafa ta, ya haliche ta ba wofi ba, ya kamanta ta domin wurin zama.” Ishaya 45:18. Ainihin shirin Allah don halitar duniya ya cika, da shike duniyar ta zama wurin zaman fansassu har abada. “Masu-adilchi za su gaji kasan, su zamna a chikinta har abda.” Zabura 37:20. BJ 670.3
Tsoron kada a sa abin gadon ya zama kamar ba na ruhaniya ba, ya sa mutane da yawa sun mai da abin gadon da muke gani namu ne ya zama na cikin ruhaniya kadai. Kristi Ya tabbatar ma almajiransa cewa Ya je domin Ya shirya masu wurin zama ne a gidan Uban. Wadanda sun karbi koyaswoyin maganar Allah ba za su jahilci zancen wurin zama na sama ba. Duk da haka, “ido ba ya gani ba, kunne ba ya ji ba, ba ya shiga zuchiyar mutum ba, dukan iyakar abin da Allah Ya shirya ma wadanda ke kamnassa.” Korinthiyawa I, 2:9. Harshen mutumtaka bai isa ya bayana ladan masu- adalci ba. Wadanda za su gan shi ne kadai za su san shi. Tunanin mutum ba zai iya fahimtar darajar Paradise na Allah ba. BJ 670.4
A cikin Littafin, ana ce da gadon cetattu “kasa” ne. Ibraniyawa 11:14-16. A can Makiyayi na sama zai kai tumakinsa mabulbulan ruwayen rai. Itacen rai zai ba da yayansa kowane wata, ganyen itacen kuma domin warkarwar al’ummai ne. akwai rafuka da ruwansu yana gudu kullum, mai-haske sarai, a gefensu kuma itatuwa masu ganyaye suna jefa inuwarsu kan hanyoyi da aka shirya domin fansassu na Ubangiji. A can budaddun filayen sukan zama tuddai masu-kyau a wadansu wurare, duwatsun Allah kuma sukan nuna bisansu masu ban-sha’awa. A wadannan filayen salaman, a gefen rayayyun rafukan nan, mutanen Allah da suka dade suna bakunci, suna kai da kawowa, za su sami gidansu. BJ 671.1
“Mutane na za su zamna a chikin mazamni na salama, a chikin tabbatattun mazamnai, da chikin mazamnai na hutawa.” “Ba za a kara jin labarin kwache a kasarki ba, ko kisbewa, ko hallaka a chikin iyakanki: amma za ki kira ganuwarki cheto, kofofinki kuma yabo.” “Za su gina gidaje, kuma za su zamna a chiki, su yi gonakin annab kuma, su chi anfaninsu. Ba za su yi gini wani ya zamna ba: ba za su dasa, wani ya chi ba;… zababuna kuma za su dade suna jin dadin aikin hannuwansu.” Ishaya 32:15; 60:18; 65:21,22. BJ 671.2
A can, “Jeji da kekadadiyar kasa za su yi farinchiki; hamada kuma za ta yi murna ta yi fure kamar rose.” “Maimakon kaya, itachen fir za ta tsiro; maimakon dakwara kuma myrtle za ya tsiro.” “Kerkechi za ya zamna tare da dan rago, damisa kuma za ta kwanta tare da dan akuya;… dan yaro kwa za ya bishe su.” “Ba za su yi chiwutaswa ba; ba kwa za su yi barna ko ina chikin dutsena mai-tsarki ba,” in ji Ubangiji. Ishaya 35:1; 55:13; 11:6,9. BJ 671.3
Azaba ba za ta iya kasancewa a yanayin sama ba. Ba za a sake samun hawaye ko biso, ko makoki ba. “Mutuwa kwa ba za ta kara kasanchewa ba; ba kwa za a kara yin bakin-zuchiya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shude.” “Wanda yake zaune a chiki ba zai che, Ina chiwo ba: mutanen da ke zaune a wurin za a gafarta masu zunubansu.” Ruya 21:4; Ishaya 33:24. BJ 672.1
Akwai Sabuwar Urushalima, babban birnin sabuwaar duniyar da aka darajanta, “kambi jamali a chikin hannun Ubangiji, dajiyar sarauta kuma a chikin hannun Allahnki.” “Shekinta yana kama da dutse mai-tamani mafifici, sai ka che jasper, garai kamar crystal.” “Al’aummai kuma za su yi yawo chikin haskenta; sarakunan duniya kuma suna kawo darajassu chikinta.” In ji Ubangiji: “Zan yi farin chiki domin Urushalima kuma, in yi murna domin mutanena.” “Mazamnin Allah yana wurin mutane, za ya zamna tare da su kuma, za su zama al’umma nasa, Allah kuma da kansa za ya zamna tare da su, ya zama Allahnsu.” Ishaya 62:3; Ruya 21:11,24; Ishaya 65:19; Ruya 21:3. BJ 672.2
A birnin Allah babu dare. Ba wanda zai bukaci hutawa. Ba za a gaji da aikata nufin Allah da raira yabon sunansa ba. Kullum za mu rika jin sabontakar safiya ne, kullum kuma mu kasance nesa da karewar safiyar. “Ba su kwa da bukatar hasken fitilla, ko hasken rana ba; gama Ubangiji Allah za ya ba su haske.” Ruya 22:5. Wata walkiya mara-dauke ido za ta rufe hasken rana, haskenta kuwa zai fi na tsakar rana. Darajan Allah da na Dan ragon za su yi ma Birni Mai-tsarkin ambaliyar haske mara-shudewa. Fansassu za su rika tafiya cikin darajar yini mara matuka inda ba rana. BJ 672.3
“Ban ga haikali a chiki ba: gama Ubangiji Allah Mai-iko duka da Dan rago su ne haikalinta.” Ruya 21:22. Mutanen Allah za su sami zarafin sadarwa da Uban da Dan. “Gama yanzu chikin madubi mu ke gani a zauranche.” Korinthiyawa I, 13:12. Muna ganin kamanin Allah da ke nunawa sai ka ce a madubi, cikin ayukan halita da dangantakarta da mutane, amma sa’an nan za mu gan shi fuska da fuska ba tare da wani labule a tsakani ba. Za mu tsaya a gabansa, mu ga daarajar fuskarsa. BJ 672.4
Can fansassu za su sani kamar yadda su ma za a san su. Can ne kauna da tausayi da Allah da kan Shi ya shuka cikin mutm za su sami ainihi da mafi-dadin bayanuwarsu. Sadarwa mai-tsabta da rayuka masu-tsarki, rayuwar ma’amala mara sabani da malaiku masu —albarka da kuma amintattu na dukan sararaki wadanda suka wanke tufafinsu, suka mai da su fari cikin jinin Dan ragon, dangantaka na ruhaniya da suka hada “kowane iyali chikin sama da duniya” Afisawa 3:15 — wadannan duka za su taimaka wajen hada farincikin fansassun. BJ 673.1
Can, zukata marasa mutuwa, masu murna kuma, za su yi bimbini game da al’ajiban ikon halita, da asiran kauna ta fansa. Ba za a iske mugun magabci mai-rudi da zai jarabci wani ya manta Allah ba. Kowane sani zai zama ingantace, kowace kwarewa za ta karu. Samun sani ba zai gajiyar da tunani ba, ko kuma ya kare kuzari ba. Can za a gudanar da al’amura mafi-girma, a cim ma manufofi mafiya-kyau, a cika buri mafi girma: duk da haka sabobin ababa za su taso da za a so a yi su, sabobin al’ajibai kuma da za a yi sha’awarsu, sabobin gaskiya da za a fahimta, sabobin manufofi da za su ingiza zuciya da ruhu da jiki. BJ 673.2
Dukan halita ko ina za su kasance domin fansassu su yi nazarinsu. Da shike mutuwa ba za ta yi masu takunkumi ba, za su rika firiya babu gajiya zuwa duniyoyi nesa, duniyoyin da suka yi bakincikin wahalolin dan Adam, suka kuma ta da wakokin murna game da labarin rai da aka fansa. Da murnan da ba za a iya bayanawa ba, ‘ya’yan duniya za su shiga cikin murna da hikimar masu rai da basu fadi ba. Za su raba dukiyar sani da ganewa da suka samu cikin zamanai bisa zamanai da suka yi suna bimbinin aikin hannun Allah. Da gani garai za su kalli darajar halita — rana da taurari, dukansu bisa ga matsayinsu, suna kewaye kursiyin Allah. Bisa kowane abu, daga mafi kankanta zuwa mafi girma, an rubuta sunan Mahalici a kai, kuma cikin dukansu an bayana wadatar ikonsa. BJ 673.3
Kuma shekaru mara-matuka, yayin da suke wucewa, za su kawo ganewa mafi wadata da daraja game da Allah da Kristi. Kamar yadda sani ke karuwa, haka kauna da ban girma da farin ciki za su karu. Yawan sha’awar halin Allah zai zama daidai da yawan saninsa da mutane suka yi ne. Sa’an da Yesu zai bude masu wadatar fansa da muhimman nasarori cikin babban jayayya da Shaitan, zukatan fansassu za su motsu da Karin kuzari da himma, kuma da karin murna mai-yawa za su kada girayan zinariya, su hada kai, su kara babban wakar yabon. BJ 674.1
“Kuma kowane halitacen abu wanda ke chikin sama, da bisa duniya, da kalkashin duniya, da bisa teku, da dukan abin da ke chikinsu, na ji su suna chewa, Ga wanda yake zamne bisa kursiyin, ga Dan rago kuma, albarka, da daraja, da daukaka, da mulki, har zuwa zamanun zamanai.” Ruya 5:13. BJ 674.2
Babban jayayyar ta kare. Zunubi da masu-zunubi babu su kuma. Dukan halitta tana da tsabta. Jituwa da murna daya ke cikin dukan halita. Daga wurin Shi wanda Ya halici duka, rai da haske da murna ke fitowa zuwa ko ina cikin sarari mara-iyaka. Daga kwayar halita mafi-kankanta zuwa duniya mafi-girma, dukan ababa, masu rai da marasa rai, cikin kyaunsu mara —duhu da murnarsu cikakkiya, suna cewa, Allah kauna ne. BJ 674.3