Shirin Allah game zaben ma’aikata don kawo canji a ekklesiya daidai yake da shirinsa domin kafa ekklesiya. Babban Mallami na saman Ya tsallaka manyan mutanen duniya, masu matsayi da mawadata, wadanda suka saba karban yabo da bangirma daga mutane. Sun rika alfarma da alfahari, suna fariya da giramansu ta yadda ba za a iya sifanta su su tausaya ma yan-uwan su mutane, su kuma zama abokan aikin Mutumin Nazareth din nan mai-tawali’u ba. Ga jahilan masunta masu faman nan na Galili aka yi kira cewa: “Ku biyo ni, ni kuwa in maishe ku masuntan mutane.”Matta 4:19. Almajiran nan masu tawali’u ne, masu karban koyaswa kuma. Karancin tasirin koyaswar karya ta zamaninsu a gare su ya sa Kristi Ya kara yin nasaran koyar da su da kuma horar da su don hidimarsa. Haka lokacin babban Canjin. Shugabannin Canjin masu tawali’u ne, mutanen da ba ruwan su da fahariyar matsayi da kuma tsananin ra’ayin priestanci. Shirin Allah ne Ya yi anfani da kananan kayan aiki don cim ma manyan manufofi. Ta haka ba za a daukaka mutane ba, sai dai Shi wanda Ya ke aiki ta wurinsu domin sun yarda su yi abin da ya gamshe Shi. BJ 169.1
Makonnni kalilan bayan haifuwar Luther a dakin mai-aiki a ramin ma’adini a Saxony, aka haifi Ulric Zwingli a gidan wani mai-kiwo a cikin duwatsun Alps. Abubuwa da suka kewaye wurin zaman Zwingli a kuruciyar sa, da horonsa na farko, sun shirya shi domin aikin shi nan gaba. Da shi ke ya girma cikin wurare masu asalin kyau da muhimmanci, masu girma na ban tsoro, hankalin sa ya saba tunanin girma da iko da martabar Allah, tun yana yaro. Tarihin ayukan sa na jaruntaka a kan duwatsun garinsu sun shafi burinsa tun samartakansa. Kuma a gefen kakansa mai- ibada, ya ji labaru daga Littafin da ita ma ta tsinto daga tatsuniyoyi da al’adun ekklesiya. Da marmarin gaske ya yi ayukan ubani da annabawa, da makiyaya da suka yi kiwon garkunan su a tuddan Falesdinu, inda malaiku suka yi magana da Mutumin Kalfari kuma. BJ 169.2
Kamar John Luther, baban Zwingli ya so ma dansa ilimi, ya kuwa tura shi makaranta tun da wuri. Tunanin shi ya girma nan da nan, tambaya kuma ta kasance, Ina za a sami mallamai masu kwarewa da za su koya masa. Yana dan shekara goma sha uku ya je Bern, inda akwai makaranta mafi inganci a Switzerland. Amma kuma a nan, wani hatsari ya taso da ya yi barazanar lalata burinsa. Ma’aikatan ekklesiya suka yi iyakar kokari su ja hankalin shi ya shiga gidan ‘yan zaman zuhudu. ‘Yan kungiyar zaman zuhudun Dominican da na Franciscan suka rika kishin juna game da samun farin jini. Sun yi kokarin samun wannan ta wurin adon da suka yi ma majami’unsu, da fahariyar iliminsu, da manyan sifofi masu kyau da al’ajiban da suka rika yi. BJ 170.1
Yan Dominican na Bern sun ga cewa idan suka iya jan hankalin saurayin nan dalibi mai-baiwa, za su sami farin jini da daraja. Samartakansa da iya maganansa da iya rubutunsa kuma, da kuma baiwarsa ta iya waka da wake, za su fi dukan girman kai da fahariyarsu jan hankalin mutane zuwa hidimominsu, su kuma kara ma kungiyarsu kurdi. Ta wurin rudi da fadanci suka yi kokarin shawo kan Zwingli ya shiga kungiyarsu. Yayin da Luther ke makaranta, ya bizne kansa cikin daki a wurin da masu zaman zuhudu suke, kuma ya bata daga sauran duniya, in ba don Allah Ya kubutar da shi ba. Ba a yarda Zwingli ya shiga wannan matsalar ba. Ta wurin ikon Allah ubansa ya sami labarin kulle-kullen ma’aikatan ekklesiyar. Ba shi da niyyar barin dansa ya bi rayuwar zaman banza da rashin anfani na masu zaman zuhudu. Ya ga cewa anfanin sa nan gaba yana cikin hatsari, sai ya umurce shi ya dawo gida ban da jinkiri. BJ 170.2
An yi biyayya da umurnin; amma matashin bai iya gamsuwa da zaman kauyensu da dadewa ba, ya kuwa fara makarantarsa bayan wani lokaci kuma ya koma Basel, Wittenbach, mai-koyar da tsofofin yaruka na da. Yayin da yake nazarin Hellenanci da Ibrananci, ya taba samun Littafi Mi-tsarki, a haka kuma tsirkiyoyin hasken Allah suka haskaka tunanin daliban sa ta wurin koyaswarsa. Ya sanar da cewa akwai wata gaskiya da ta fi dabarun mallaman makaranta da na masu bin ussan ilimi dadewa da kuma anfani kwarai. Wannan da daddiyar gaskiyar it ace cewa mutuwar Kristi ce kadai fansar mai-zunubi. Kalmomin nan ne tsirkiyar farko da ta zo ma Zwingli, kafin wayewan gari ya zo masa. BJ 171.1
Ba da jimawa ba aka kira Zwingli daga Basel ya shiga aikin rayuwarsa. Wurin aikinsa na farko a majami’ar Alps ne, kusa da kauyensu. Da shike an shafe shi priest, ya “dukufa da dukan ransa ga neman gaskiya ta Allah, domin ya sani sarai yawan sanin da yake bukata game da wanda aka damka masa amanar garken Kristi,” in ji wani dan-uwansa dan Canji. Yayin da ya ci gaba da nazarin Littafi, bambanci tsakanin gaskiyarsu da riddar Rum ya ci gaba da kara bayanuwa gare shi. Ya ba da kansa ga Littafin a matsayin maganar Allah kadai isashiya mara kuskure. Ya ga cewa dole it ace kadai mai-fassara kanta. Bai isa ya fassara Littafi domin tabbatar da ra’ayi ko koyaswa da ya rigaya ya kulla a zuciyarsa ba, amma ya dauki kudirin koyo daga abin da Littafin ke koyarwa kai tsaye a bayyane. Ya nemi kowane taimako don samun cikakken ganewa adaidai na ma’anar ta, ya kuma roki taimakon Ruhu Mai-tsarki wanda zai bayana ma dukan wanda ya neme shi da gaske cikin addu’a kuma. BJ 171.2
Zwingli ya ce: “Littafi ya zo daga Allah ne, ba daga mutum ba, kuma ma Allah Mai-bayanawa zai ba ka ganewa cewa maganar daga Shi Allah ne. Maganar Allah ba za ta taba faduwa ba; tana da haske, ta na koyar da kanta, ta na bayana kanta, tana haskaka rai da dukan ceto, da laheri, ta kuma ta’azantar da mutum cikin Allah, ta ba shi saukin kai, domin ya musunci kansa, ya rungumi Allah kuma.” Zwingli da kansa ya tabbatar da gaskiyar kalmomin nongame da rayuwar sa ta wannan lokacin , daga baya ya rubuta cewa: “Sa’an da na fara ba da kai na gaba daya ga Littafi Mai-tsarki, bin ussan ilimi da ilimin tauhidi suka rika shawarta mani yin fada. A karshe tunani ya zo mani cewa, ‘Dole ka rabu da dukan masu karya ka koyi ma’anar Allah daga maganarsa mai-sauki kadai.’ Sa’an nan na fara rokon Allah haskensa, kuma Littafi ya fara kara saukin ganewa gare ni.” BJ 172.1
Bisahran da Zwingli ya yi wa’azin tab a daga Luther ya karba ba. Koyaswar Kristi ce. Zwingli y ace: “Idan Luther yana wa’azin Kristi, yana abin da ni ke yin a.wadanda ya kawo wurin Kristi sun fi wadanda ni na kawo yawa. Amma wannan ba komi ba ne. Ba zan amsa wata suna dabam da ta Kristi wanda ni sojansa ne ba, wanda Shi kadai ne kuma Sarki na. Ko kalma daya ban taba rubuta ma Luther ba, Luther kuma bai taba rubuta mani ko kalma daya ba; don me?... Domin a nuna yadda Ruhn Allah ba ya sabani da kansa da shike mu biyu din, ba tare da shawara da juna ba, muna koyar da koyaswar Kristi ba tare da wani sabani ba.” BJ 172.2
A shekara ta 1516, an gayyaci Zwingli ya je ya zama mai-wa’azi a gidan ‘yan zaman zuhudu a Einsiedeln. A nan ya ga kurakuran Rum kusa kusa, ya kuma yi tasiri ga dan Canjin da aka ji har can nesa da kauyensu na Alps. Cikin manyan ababan ban sha’awa a Einsiedeln akwai sifar budurwar, wadda aka ce tana da ikon yin al’ajibai. A kofar shiga unguwar masu zaman zuhudun, aka rubuta cewa: “A nan za a iya karban cikakkiyar gafarar zunubai.” Matafiya kowane lokaci suka dinga zuwa wurin budurwar; amma a babbar bukin tsarkaketa na shekara shekara, jama’a da yawa suka rika zuwa daga kowane bangaren Switzerland, har ma daga Faransa da Jamus. Zwingli da ya fusata da abin da ya gani, ya yi anfani da zarafin don shelar yanci ta wurin bishara ga bayin nan na camfi. BJ 172.3
Ya ce: “Kada ku zata cewa Allah Yana cikin haikalin nan, fiye da yadda yake a kowane wuri a duniya. Ko da wace kasa kake, Allah Yana kusa da kai, Yana kuma jin ka.... Meme ne anfanin tarin kalmomin da muke jibga ma addu’o’in mu? Wane iko ke a hula mai-ado, ko kai da aka aske suman sa gaba daya, ko doguwar riga, ko takalma masu adon zinariya?.... Allah Yana duban zuciya ne, kuma zukatan mu suna nesa da Shi.” Ya ce: “Kristi wanda aka taba ba da Shi a kan giciye, Shi ne hadaya da ta biya hakin dukan zunuban masu ba da gaskiya har abada.” BJ 173.1
Da yawa cikin masu jin sa basu so maganan nan ba. Ba su so a ce masu wai wahalar tafiyan nan ta su banza ce ba. Basu iya gane gafaran da aka ba su kyauta ta wurin Kristi ba. Sun gamsu da tsohuwar hanyan nan zuwa sama wadda Rum ta zana masu. Suka yi sanyin gwiwa game da rudewan da neman wata hanya dabamza ta kunsa. Ya fi masu sauki su dogara ga priestoci a paparuma, maimakon bidar tsabtar rai. BJ 173.2
Amma wata kungiya ta karbi labarin fansan nan ta wurin Kristi da farin ciki. Ababan da Rum ta umurta yi basu kawo salamar zuci ba, cikin bangaskiya kuma suka karbi jinin Mai-ceton a matsayin fansar su, wadannna suka koma gidajen su suka bayana ma wadansu kuma hasken da suka samu. Ta haka aka kai gaskiyar daga unguwa zuwa unguwa, gari zuwa gari, yawan masu zuwa wajen Budurwar kuma ya ragu sosai. Bayaswa kuma ta ragu sosai, haka kuma albashin Zwingli ya ragu, da shike daga baye-bayen nan ake biyansa. Amma wannan ya ba shi farin ciki ne kadai sa’an da ya ga cewa ikon tsananin ra’ayi da camfi yana raguwa. BJ 173.3
Shugabanninn ekklesiya basu kasa sanin aikin da Zwingli yake yi ba, amma a wannan sa’ar basu dame shi ba. Da begen komo da shi gefensu, suka yi kokarin jawo shi ta wurin yi mashi balmar baka; ana haka kuma gaskiya tana samun shiga zukatan mutane. BJ 174.1
Aikin Zwingli a Einsieldeln ya shirya shi don babban fili, wanda zai shiga ba da jimawa ba. Bayan shekara uku a nan aka kiraye shi a zama mai-wa’azi a babban majami’ar Zurich. A lokacin, Zurich ne gari mafi muhimmanci a tarayyar Switzerland, kuma tasirin da aka kawo nan, za a ji shi ko ina. Masu bisharan da suka gayyato shi Zurick dai sun so su hana duk wani sabon abu, da sauri kuwa suka fada mashi aikin da zai yi. BJ 174.2
Suka ce: “Za ka yi iyakan kokari ka tara kurdaden sashin, komi kankantansu. Za ka gargadi masu bi, daga bagadi da kuma wurin-furta zunubinsu, su biya dukan zakkoki da baye baye, su kuma nuna soyayyarsu ga ekklesiya ta wurin baikonsu. Za ka yi kwazo wurin kara kurdin da ke shigowa daga wurin marasa lafiya, da jama’a, a takaice dai, daga kowane fannin ekklesiya.” “Game da ba da jibi, da wa’azi da kulawa da garken kuma, wadannan ma aikin mai-bisharan ne. Amma game da wadannan, kana iya samo wani a madadinka, musamman ma game da wa’azi. Kada ka ba kowa jibi, sai dai sanannu, kuma sai an bukaceka ka bayar; ba a yarda maka ka ba kowa ba tare da bambanta mutanen ba.” BJ 174.3
Zwingli ya saurari umurnin nan shuru, sa’an nan bayan ya nuna godiyarsa sabo da girmama shi da aka yi, da ba shi muhuimmin aikin nan, sai ya ci gaba ya bayana matakin da yake so ya dauka. Ya ce: “An dade ana boye ma mutane rayuwar Kristi. Zan yi wa’azi kan dukan bishara ta Matta...., bisa ga Littafin kadai, ina bayana zurfin ta, ina kuma gwada nassi da nassi, ina kuma neman fahimi ta wurin himma wajen addu’a. Ga daukakar Allah da yabon Dansa tilo, ga ainihin ceton rayuka da kuma ginuwarsu cikin imanin gaskiya ne zan kebe hidima ta.” Ko da shike wadansu shugabannin ekklesiyan basu amince da shirinsa ba, suka kuma yi kokarin hana shi bin shirin, Zwingli ya tsaya da karfinsa. Ya bayana cewa ba sabon tsari yake so ya kawo ba, amma tsohon tsarin da ekklesiya ta yi anfani da shi ne a zamanai na farko masu tsarki. BJ 174.4
Kafin nan an fara marmarin gaskiyan da ya koyar; mutanen kuma suka rika tururuwa da yawansu don sauraron wa’azinsa. Da yawa da suka dade da barin zuwa sujada suna cikin masu jinsa. Yakan fara hidima ta wurin karantawa da kuma fassara ma masu jinsa daga Bishara, game da rayuwa da koyaswa, da mutuwar Kristi. Nan ma, kamar a Einsiedeln, ya gabatar da maganar Allah a matsayin iko kadai mara aibi, mutuwar Kristi kuma a matsayin cikakkiyar hadaya ita kadai, ba wata kuma. Ya ce: “Wurin Kristi ne nike so in kai ku, wurin Kristi, ainihin tushen ceto.” Mutane iri iri, daga manyan gwamnati da masana, zuwa masu aikin hannu da talakawa, suka dinga tattaruwa wajen mai-wa’azin. Da sha’awa sosai suka saurari kalmominsa. Ba kyautar ceto kadai ya bayana ba, ya kuma tsauta ma mugunta da lalacewar zamanin, ba da tsoro ba. Da yawa suka rika dawowa daga majami’ar suna yabon Allah. Suka ce: “Wannan mutumin mai-wa’azin gaskiya ne. Shi ne zai zama Musan mu, domin ya shugabanci fitowar mu daga duhun Masar din nan.” BJ 175.1
Amma ko da shike da farko an karbi aikin sa da babbar sha’awa, daga bisani jayayya ta taso. Masu zaman zuhudun suka shirya hana aikinsa da kushe koyaswoyinsa. Da yawa suka rika masa ba’a da reni; wadansu kuma suka shiga zagi da barazana. Amma Zwingli ya jumre da hakuri, yana cewa: “Idan muna so mu jawo miyagu zuwa wurin Yesu Kristi, dole mu rufe idanun mu daga abubuwa da yawa.” BJ 175.2
Wannan lokacin, wata kungiya ta shigo don kara ci gaban canjin. Aka aiki wani mai suna Lucian da wadansu rubuce rubucen Luther zuwa Zurich, ta wurin wani abokin sabuwar bisahrar a Basel, wanda ya shawrta cewa sayar da litattafan anan zai zama babban hanyar baza hasken. Ya rubuta ma Zwingli cewa: “Ka tabbatar ko wannan mutumin yana da isashen hikima da kwarewa; in haka ne, ya kai rubuce rubucen Luther daga birni zuwa birni, daga gari zuwa gari, daga kauye zuwa kauye, har ma daga gida zuwa gida, cikin mutanen Swiss, musamman ma bayanin fassara Luther din ta addu’ar Ubangiji da ya rubuta don marasa ilimin tauhidi. Kara saninsu zai jawo kin cinikinsu.” Ta haka ne hasken ya sami hanyar shiga. BJ 176.1
Lokacin da Allah ke shirin karye sarkokin jahilci da camfi, lokacin ne Shaitan yakan yi aiki da dukan ikonsa don kunsa mutane cikin duhu, kuma don kara daure sarkokinsu da karfi. Yayin da mutane ke tasowa a kasashe dabam dabam don mika ma mutane gafara da barataswa ta wurin jinin Kristi, Rum ta ci gaba da karin karfi don bude kasuwar ta ko in cikin Kirista, tana tallan gafara sabo da kurdi. BJ 176.2
Kowane zunubi da farashisa, aka kuma ba mutane lasin na yin zunubi kyauta, muddan dai baitulmalin ekklesiya zai cika sosai. Ta haka kungiyoyi biyu din suka ci gaba, daya tana tallan gafara don kurdi, dayan kuma tana shelar gafara ta wurin Kristi, Rum tana ba da lasin na zunubi tana kuma samun kurdin shiga; yan canjin suna kushe zunubi, suna kuma nuna Kristi a matsayinsa na kafara da mai-kubutarwa. BJ 176.3
A Jamus, an damka cinikin takardun shaidar gafara a hannun priestocin kungiyar Dominican ne, kalkashin Tetzel. A Switzerland, an ba da cinikin a hannun ‘yan Franciscan ne, kalkashin shugabancin Samson, mai-zaman zuhudu, dan Italiya. Samson ya rigaya ya yi ma ekklesiya aiki mai-kyau inda ya tara makudan kurdi a Jamus da Switzerland da suka isa su cika baitulmalin paparuma. Yanzu kuma ya rika yawo a Switzerland yana jawo jama’a da yawa, yana tsotse kurdaden talakawa, yana kuma jan kyaututtuka masu tsada daga mawadata. Amma tasirin Canjin ya rigaya ya kai inda ya rage yawan kasuwancin, ko da shike bai tsayar da shi ba gaba daya. Zwingli, dai yana Einsiedeln lokacin da Samson, jima kadan bayan da ya shigo Switzerland, ya taho da kayan jarinsa a wani makusancin gari. Da aka fada ma Zwingli abin da ya kawo shi, nan da nan ya je domin ya yi jayayya da shi. Basu sadu ba, amma Zwingli ya yi nasarar fallasa karyar priest din ta yadda ya kama shi dole ya koma wani gari dabam. BJ 176.4
A Zurich, Zwingli ya yi wa’azi da himma sabanin masu jarin gafaran nan; kuma da Samson ya kusa da wurin, wani masinja daga majalisa ya same shi da sako cewa ana bukatar shi ya wuce ne. Daga baya ta wurin dabara ya shiga garin, amma aka kore shi, ko gafara daya bai sayar ba; ba da dadewa ba kuma ya bar Switzerland. Canjin ya sami karin karfi sa’anda annoba, ko Babbar Mutuwa, da ta abka ma Switzerland; a shekara ta 1519 ta bayana. sa’anda mutane suka gamu da mai-hallakaswa, fuska da fuska, da yawa suka ji yadda gafaran da suka saya ya tabbata banza mara anfani; suka kuma yi sha’awar tabbatacen harsashe domin bangaskiyarsu. Zwingli a Zurich ya harbu da ciwo; ya kai inda begen warkewar sa ya kare, labari kuma ya kai ko ina cewa ya mutu. Cikin wannan mawuyacin halin ma begen sa da karfi halinsa basu ragu ba. Ya rika duban giciyen Kalfari yana dogarawa ga cikakkiyar kafara ga zunubi. Sa’an da ya dawo daga kofofin mutuwa, ya yi wa’azin bishara da himma fiye da duk yadda ya taba yi; kalmominsa kuma suka fito da iko na ban mamaki. Mutanen suka marabci paston su kaunatace da farin ciki, paston da aka dawo masu da shi daga bakin mutuwa. Su kansu sun fito jinyar marasa lafiya da masu mutuwa, suka kuwa ji tamanin bishara yadda basu taba ji ba. BJ 177.1
Zwingli ya kara fahimtar gaskiyar bisharar, ya kuma dandana a jikinsa cikakken ikonta na sabuntawa. Faduwar mutum da shirin fansa ne kawunan magana da ya mai da hankalinsa akai. Ya ce: “Cikin Adamu, dukan mu matattu ne, nutsatsu cikin lalacewa da hukumci.” “Kristi.... Ya sayo mana fansa mara karshe.... Azabarsa, hadaya ce ta har abada, mai-ikon warkarwa kuma har abada; tana gamsar da adalcin Allah har abada a madadin dukan wadanda suka dogara gare ta da bangaskiya mai-karfi mara kaduwa.” Duk da haka ya koyar a fili cewa mutane ba su da yancin ci gaba da zunubi wai don alherin Kristi. “Duk inda akwai bangaskiya ga Allah, akwai Allah, kuma duk inda Allah Yake, akwai himma da ke ingiza mutane su yi nagargarun ayuka.” BJ 178.1
Sha’awar saurarom wa’azin Zwingli ta kai inda har majami’ar ma takan cika da jama’a masu son sauraronsa, har ta kasa. Kadan da kadan dai ya rika bayana masu gaskiya. Ya yi hikima da bai fara da ababan da za su ba su mamaki har su ta da kiyayya ba. Aikinsa dai shi ne jawo hankalin su zuwa koyaswoyin Kristi, domin su zama masu saukin kai tawurin kaunar Kristi din, ya kuma nuna masu kwatancin Kristi; kuma yayin da za su karbi kaidodin bisharar, za a hambarar da camfe camfensu ba jinkiri. BJ 178.2
Sannu a hankali canjin ya ci gaba a Zurich. Cikin fushi magabatansa suka tayar da jayayya. Shekara guda kafin nan, Luther, mai-zaman zuhudun Wittenberg, ya ce ya ki ma paparuma da babban sarki a Worms, yanzu kuma komi ya nuna kamar za a maimaita tsayayyan nan da koyaswar paparuma a Zurich ma. An dinga kai ma Zwingli hare hare akai akai. A cibiyoyin ‘yan paparuma loto loto an dinga kai almajiran bishara wurin kisa, amma wannan bai isa ba, dole a kashe Zwingli mai koyar da ridda. Sabo da haka bishop na Constance ya tura wakilai uku zuwa majalisar Zurich, yana zargin Zwingli da koya ma mutane su ketare dokokin ekklesiya, wannan kuwa yana barazana ga salama da oda. Ya ce idan aka kawar da ikon ekklesiya dukan duniya za ta shiga rashin zaman lafiya. Zwingli ya amsa cewa shekara hudu yana koyar da bishara a Zurich, amma Zurich din ya fi kowane gari cikin tarayar zaman lafiya. Ya ce: “Wannan bai nuna cewa Krisitanci ne ya fi tabbatar da tsaroba?” BJ 178.3
Wakilan sun rigaya sun shawarci yan majalisar wadda suka ce cikin ta kadai ake samun ceto. Zwingli ya amsa: “Kada wannan zargi ya dame ku. Harsashen ekklesiya shi ne Dutse dayan, Kristi dayan da Ya ba Bitrus sunansa domin ya karbe Shi da aminci. A kowace al’umma duk wanda ya ba da gaskiya da dukan zuciyarsa cikin Ubangiji Yesu, za ya karbu ga Allah. Wannan a gaskiya ita ce ekklesiyar, wadda cikin ta kadai ake samun ceto.” Sakamakon wannan taron, daya daga cikin wakilan bishop din ya karbi sabuwar bangaskiyar. BJ 179.1
Majalisar ta ki daukan mataki akan Zwingli, Rum kuma ta yi shirin sabon hari. Sa’an da aka fada masa kulle kullen magabatansa, Zwingliya ce: “Bari su zo; ina tsoron su kamar yadda dutsen gefen kogi ke tsoron igiyoyin rowan da ke kalkashin sawayensa.” Gaskiya ta ci gaba tana yaduwa. A Jamus magoya bayanta da suka damu sabo da bacewar Luther, suka ta’azantu kuma sa’an da suka ga ci gaban aikin a Switzerland. BJ 179.2
Sa’an da Canjin ya faru a Zurich, aka fi ganin sakamakonsa a raguwar mugunta da ci gaban oda da jituwa. Zwingli ya rubuta: “Salama tana da mazauninta a garinmu, ba fada, ba riya, ba kishi, ba tashin hankali. Daga ina irin hadin kan nan zai fito in ba daga wurin Ubangiji, da koyaswar mu da ke cika mu da ‘ya’yan salama da ibada ba?” BJ 179.3
Nasarorin Canjin sun hanzuga yan Rum, suka kara kokarin hambarar da shi. Ganin kankantar abin da zalunci ya samo game da danne aikin Luther a Jamus, suka shirya tasam ma Canjin ta wurin anfani da makaman da canji ke anfani da su. Za su yi mahawara da Zwingli, su kuma tabbatar sun yi nasara ta wurin zaben wurin mahawaran da alkalan mahawaran, su da kansu. Idan kuwa suka sami Zwingli sau daya a kalkashi ikon su, za su tabbatar cewa bai tsere masu ba. Idan aka gama da shugaban, za a iya murkushe kungiyan nan da nan. Amma fa an boye wannan shirin da kyau sosai. BJ 179.4
An shirya za a yi mahawaran a Baden ne; amma Zwingli bai hallara ba. Majalisar Zurich da ta gane kulle kullen yan paparuma, da kuma ganin yawan kisan magoya bayan bishara da ake yi a wuraren yan paparuma, suka hana paston nasu sa kansa cikin wannan kasadar. A Zurich, yana shirye ya sadu da dukan wadanda Rum za ta aika; amma zuwa Baden, inda aka fito zub da jinin masu bi, sabo da gaskiya, zai zama zuwa wurin mutuwa kenan. Aka zabi Oecolampadius da Haller su wakilci yan Canjin, yayin da Dr. Eck tare da likitoci masana da priestoci da yawa za su wakilci Rum. BJ 180.1
Ko da shike Zwingli bai halarci taron ba, an ji tasirinsa. ‘Yan paparuma ne suka zabi dukan sakatarorin, aka kuma hana sauran yin rubutu, wanda ya yi kuma a kashe shi. Duk da haka Zwingli ya sami rahotun komi da aka fada a Baden kowace rana. Wani dalibi da ya kasance a wurin taron ya dinga rubuta mahawaran da aka yi kowace rana. Wadansu dalibai biyu kuma suka dauki nauyin kai ma Zwingli rahotanin nan, tare da wasikun Oecolamoadius kowace rana a Zurich. Zwingli yakan amsa tare da shawarwari. Yakan rubuta wasikun sa d a dare ne, daliban kuma sukan kai ma Oecolampadius da safe. Don kada masu tsaron birnin su gane su, daliban sukan zo da kwandunan kaji a kawunansu, akan kuma bar su su wuce ba matsala. BJ 180.2
Ta haka Zwingli ya ci gaba da yakinsa da magabtansa. Miconius ya ce: “Ya yi aiki ta wurin bimbininsa da kwana ganinsa, da shawararin da ya rika turawa Baden, fiye da yadda ya yi ta wurin mahawara da kansa a tsakanin magabtansa.” BJ 181.1
Magabtan, cike da begen nasara, sun zo Baden cikin tufafinsu mafi tsada, cike da ado. Sun rika shakatawa suna cin abinci iri iri masu tsada, ga ababan sha na musamman. Suka rika sauke nauyin aikinsu na ekklsiya ta wurin annashuwa. Sabanin wannan sai ga ‘yan Canji, wadanda mutane suka gan su kamar da kadan suka fi masu-bara da karancin abincin su ya sa ba sa dadewa a wurin cin abincin. Sa’an da mai-gidan dakin da Oecolampadius ke haya ya leka shi kowace rana, yakan gan shi yana nazari ne ko kuma addu’a, cikin mamaki kuwa ya ce wannan mai-riddan, ko ba komai dai yana ibada. BJ 181.2
A wurin taron, “Eck da girman kai ya hau bagadi da aka masa ado sosai, amma Oecolampadius ya sa sutura mara tsada, aka tilasta mashi ya zauna a gaban magabcin sa kan wata yar kujerar katako mara baya.” Babban muryan nan na Eck da yawan tabbacinsa, basu taba barin shi ya karai ba. Himmar sa ta karu sabo da begen zinariya da yin suna, domin an ce ladar mai-kare bangaskiyar kurdi ne mai-yawa. Sa’an da ya rasa abin fadi na kwarai, sai ya shiga zagi har da rantsuwa. BJ 181.3
Oecolampadius, cikin saukin kai da ganin kasawar kansa, ya yi shakkar shiga mahawarar, ya kuma shige ta da cewa: “Ban amince da wani ma’auni ba sai maganar Allah.” Ko da shike mai-hankali ne da bangirma, mutum ne shi mai kwarewa da naciya kuma. Yayin da ‘yan Rum din suka dogara ga al’adun ekklesiya, dan Canjin ya manne ma Littafi babu kaucewa. Ya ce: “Al’ada ba ta da iko a Switzerland din mu, sai dai bisa ga kundin tsarin dokokin kasar; yanzu fa, a sha’anin bangaskiya Littafi ne kundin tsarin dokokin mu.” BJ 181.4
Bambanci tsakanin mutum biyu masu mahawaran nan ya yi tasiri. A karshe, yan paparuma sun dauka cewa sun yi nasara. Yawancin wakilan sun goyi bayan Rum, Majalisar kuwa ta furta cewa an ka da ‘yan Canjin, ta kuma ce su da shugabansu Zwingli an yanke su daga ekklesiya. Amma sakamakon taron ya nuna ko wane ne ya yi riba. Mahawarar ta haifar da kwarin gwiwa ga aikin masu kin ikon paparuma, kuma ba da jimawa ba bayan wannan, manyan biranen Bern da Basel suka bayana cewa su ‘yan Canji ne. BJ 182.1