Daya daga cikin gaskiya mafi saduda da daraja da aka bayana a Littafin shi ne na zuwan Kristi na biyu don karasa babban aikin nan na fansa. Ga mutanen Allah da suka dade cikin bakunci “ainihin wurin mutuwa da inuwatta,” aka ba da bege mai kawo murna cikin alkawalin bayyanuwarsa, wanda Shi ne tashin matattu, Shi ne rai, domin ya dawo da horraru gida. Koyaswar zuwan Yesu na biyu ita ce cibiya cikin Littafin. Daga ranan da Adamu da Hawa’u suka fita daga Adnin, masu bangaskiya suna sauraron zuwan Yesu domin ya karya ikon mai-hallakasuwan, ya kuma sake dawo da su paradise da suka rasa. Mutanen da masu tsarki sun yi sauraron zuwan Masiya cikin daukaka, domin cikar begensu. Enoch (Ahnuhu) na bakwai cikin zuriyar Adamu da Hawa’u, shi wanda ya yi tafiya da Allah har shekaru dari uku, aka ba shi damar hangen zuwan Mai-kubutarwan. Ya ce: “Ku duba ga Ubangiji ya zo da rundunan tsarkakansa, garin ya hukumta shari’a bisa dukan mutane.” Yahuda 14:15. Ayuba kuma a daren azabarsa, da cikakkiyar bangaskiya ya ce: “Gama na sami mai-pansana yana da rai, a karshe kuma za ya tsaya a bisa duniya.… Zan kwa gan shi, ni kai na, yana goya bayana, idanuna za su gan shi, ba kwa kamar bako ba.” Ayuba 19:25-27. BJ 297.1
Zuwan Kristi domin shigo da mulkin adalci ya motsa rubutu da yawa mafi ban sha’awa da aka yi a cikin Littafin. Annabawan suka rika magana game da shi cikin kalmomi masu walkiya da wutar samaniya. Mai-zabinta ya raira game da iko da martabar Sarkin Israila: “Allah ya bullo da haske daga chikin Sihiyona, na kamilin jamali. Allahnmu yana zuwa, ba kwa za ya yi shuru ba…. Za ya kira sammai daga bisa, za ya kira duniya kuma, domin ya yi ma mutanensa shari’a” Zabura 50:2-4. “Bari sammai su yi murna, duniya kwa ta yi farin zuchiya:… A gaban Ubangiji, gama yana zuwa: yana zuwa domin ya shara’anta duniya da adilchi, al’umai kuma da aminchinsa.” Zabura 96:11-13. BJ 298.1
In ji annabi Ishaya: “Ku falka ku raira waka, ku da ke zamne chikin turbaya: gama rabarka rabar haske che, kasa kwa za ta fitasda matattu.” “Ya hadiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh zaya shafe hawaye daga dukan fuskoki.” Za ya kuma kawasda zargin mutanensa daga dukan duniya: gama Ubangiji ya fadi. A ranan nan fa za ya che, Ga shi wannan Allahnmu ne; mun jirashe shi, za mu yi murna, mu yi farinchiki chikin chetonsa.” Ishaya 26:19; 25:8,9. BJ 298.2
Habakuk kuma, cikin wahayi mai-tsarki, ya hangi bayanuwarsa. “Allah ya zo daga Teman, mai-tsarki kuma daga dutsen Paran. Darajatasa ta rufe sammai, duniya kwa ta chika da yabonsa. Shekinsa yana kama da haske.” “Ya staya ya auna duniya; ya duba, ya kori al’umamai ya warwatsa su; madawaman duwatsu kuma suka warwatsu, tuddai na fil’azal suka sunkuya; tafarkunsa na tun zamanu ne.” “Har da ka hau dawakanka, bisa karusanka na cheto.” “Duwatsu suka gan ka, suka ji tsoro;…zurfafa suka furta murya, suka tada hannuwansu sama. Rana da wata suka tsaya kurum a mazamninsu; da ganin hasken kibawanka yayinda, suke tafiya, da shekin mashinka mai-walkiya.” “Ka fita domin cheton mutanenka, domin cheton shafaffenka.” Habakuk 3:3,4,6,8,10,11,13. BJ 298.3
Sa’anda an kusa raba Mai-ceto da almajiransa, ya ta’azantar da su cikin bakinchikinsu da tabbacin cewa za ya zo: “Kada zuchiyarku ta bachi;… A chikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa… zan tafi garin in shirya maku wuri, kadan na tafi na shirya maku wuri kuma, sai in sake dawowa, in karbe ku wurin kaina,” Yohanna 14:1-3. “Dan mutum za ya zo chikin darajassa, da dukan malaiku tare da shi.” “Sa’an nan za ya zamna bisa kursiyin darajassa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai.” Matta 25:31,32. BJ 299.1
Malaikun da suka kasance a kan Dutsen Zaitun bayan tafiyar Kristi zuwa sama, sun maimaita ma almajiran alkawalin dawowansa: “Wannan Yesu wanda aka dauke shi daga wurinku aka karbe shi sama, kamar yadda kuka ga tafiyatasa zuwa chikin sama, hakanan za shi dawo.” Ayukan 1:11. Manzo Bulus kuma ya shaida cewa; “Gama Ubangiji da kansa za ya sabko daga sama, da kira mai-karfi, da muryar sarkin malaiku, da kafon Allah kuma.” Tassalunikawa 1 4:16. Annabin Patmos ya ce: “Ga shi yana zuwa tare da gajimarai; kowane ido kuma za ya gan shi.” Ruya 1:7. BJ 299.2
Zuwansa ne zai kawo “mayasda kowane abu, abin da Allah ya ambata ta bakin annabawansa masu tsarki wadanda ke tun farkon duniya.” Ayukan 3:21. Sa’anan za a karye mulkin mugunta, “mulkin duniya ya zama na Ubangijinmu da na Kristinsa: za ya yi mulki kuma har zuwa zamanun zamani.” Ruya 11:15. “Daukakar Ubangiji kuma za ta bayana, masu rai duka kuma za su ganta baki daya.” “Ubangiji Yahweh za ya sa adilchi da yabo su tsiro a gaban dukan-al’ummai za ya zama “kambi na daraja, da rawani na jamali ga ringin mutanensa.” Ishaya 40:5; 61:11; 28:5. BJ 299.3
Lokachin ne za a kafa mulkin Masiya mai-ban sha’awa da salama da aka dade ana begensa. “Ubangiji za ya ta’azantadda Sihiyona: ya ta’azantadda dukan kufaifanta, ya maida jejinta kamar Eden, hamadatta kuma kamar gonar Ubangiji.” “Daukaka ta Lebanon za a bayas a gareta, mafificiyar daraja ta Karmel da Sharon.” “Ba za a kara che da ke yasashiya ba: ba kwa za a kara fadin kasarki Risbewa ba, amma za a che da ke Daulata, kasarki kuma amrarriya.” “Kamar yadda ango yakan yi farinchiki da amarya, hakanan Allahnki za ya yi farinchiki da ke.” Ishaya 51:3; 35:2; 62:4,5. BJ 300.1
A dukan sararraki zuwan Ubangiji ne begen ainihin masu binsa. Alkawalin ban kwana na Mai-ceton a Dutsen zaitun, cewa zai sake zuwa, ya haskaka ma almajiransa gaba, ya cika zukatansu da murna da begen da bakinciki bai iya bicewa ba, wahaloli kuma basu iya duhuntawa ba. Cikin wahala da zalunci, “bayanuwar darajar Allahnmu mai-girma mai-cetonmu kuma Yesu Kristi” ne ta kasance “begen nan mai-albarka.” Sa’anda kristan Tassalunika suka cika da bakinciki, yayin da suke bizne kaunattatunsu da suka yi begen kasancewa a raye su ga zuwan Ubangiji, Bulus ya ja hankalinsu ga tashin matattu, da zai faru lokacin zuwan Mai-ceto. Sa’an nan matattu cikin Kristi za su tashi, a kuma wanzar da su tare da masu rai su sadu da Ubangiji a sararin sama. Ya ce: “Hakanan za mu zauna har abada tare da Ubangiji. Domin wannan fa ku yi ma junanku ta’aziya da wadannan Magana.” Tassalunikawa I, 4:16-18. BJ 300.2
A Patmos kaunatacen almajirin ya ji alkawalin, “ina zuwa da samri,” amsarsa kuma ta bayana addu’ar ekklesiya cikin dukan tafiyarta, “Amin: ka zo ya Ubangiji, Yesu.” Ruya 22:20. Daga kurkuku da wuraren kisa inda tsarkaka da wadanda aka kashe don bangaskiyarsu suka shaida gaskiya, ana samun furcin bangaskiya da begensu. Wani Kirista ya ce: “Da shike suna da tabbacin tashinsa, da kuma tashinsu lokacin zuwansa, saboda haka, suna raina mutuwa, suka kuma fi karfinta.” Sun yarda su je kabari domin su tashi ‘yantattu. Sun yi begen zuwan Ubangiji daga sama da darajar Ubansa, da zai kawo ma tsarkaka mulkinsa, Waldensiyawa ma sun yi marmarin wannan. Wycliffe ya yi begen bayanuwar Mai-fansa, begen ekklesiya. BJ 300.3
Luther ya ce: “Na tabbata cewa ranar hukumci za ta iso kafin cikar shekaru dari uku. Allah ba zai iya barin muguwar duniyan nan ta fi haka dadewa ba.” “Babbar ranar tana kusatowa da za a hambarar da mulkin haram.” BJ 301.1
In ji Melanchthon, “Tsohuwar duniyan nan ba ta yi nisa da karshen ta ba.” Calvin ya bukaci Krista kada su “yi jinkiri, suna marmarin ranar zuwan Kristi, rana mafi muhimmanci,” Ya kuma ce: “dukan iyalin amintattu zai yi jira don wannan ranar.” “Dole mu yi marmarin Kristi, dole mu nema, mu yi bimbini, har wannan babban ranar, sa’anda Ubangijinmu za ya bayana dukan darajar mulkinsa.” BJ 301.2
Knox ya ce: “Ba Ubangiji Yesu ya dauki nman mu zuwa sama ba? Kuma ba zai dawo ba? Mun san cewa za ya dawo, da sauri kuma.” Ridley da Latimer da suka ba da rayukansu saboda gaskiya sun yi begen zuwan Ubangiji, cikin bangaskiya. Ridley ya rubuta: “Babu shakka duniya, na gaskata, don haka ni ke fadi, ta kusa karshenta. Tare da Yohanna bawan Allah bari mu yi kuka cikin zukatanmu ga mai-cetonmu Kristi, Ka zo, Ubangiji Yesu, ka zo.” Baxter ya ce: “Tunanin zuwan Ubangiji yana da dadi da farinciki gareni.” Aikin bangaskiya da halin tsarkakansa ne su yi kaunar bayanuwarsa, su kuma nemi bege mai albarkan nan.” Idan mutuwa ce magabci na karshe da za a hallaka lokacin tashin matattu, za mu ga yadda ya kamata masu ba da gaskia su yi marmari su kuma yi addu’a sosai domin zuwan Kristi na biyu, sa’anda za a yi wannan cikakkiyar nasara ta karshe.” BJ 301.3
Ban da bayana yadda Kristi za ya dawo da dalilin zuwansa, annabci ya ba da alamun da za su nuna cewa ya kusa. Yesu ya ce: “A chikin rana da wata da tamrari za a ga alamu.” Luka 21:25. “Rana za ta yi dufu, wata ba za ya ba da haskensa ba, tamrari suna ta fadowa daga sama, ikokin da ke chikin sammai za su raurawa. Sa’an nan za su ga Dan mutum yana zuwa chikin gizagizai tare da iko mai-girma da daukaka.” Markus 13:24-26. Mai-ruya ya bayana alamar farko ta zuwan Yesu na biyu din: “Sai ga babban rawan duniya; rana kuma ta koma baka kamar gwado na gashi, wata kuma gudansa ya zama kamar jini.” Ruya 6:12. BJ 302.1
An ga alamun nan kafin farkon karni na sha tara. Don cika annabcin nan na 1755 an yi rawan duniya mafi muni da aka taba sani. Ko da shike an cika kiran shi rawan duniyan Lisbon, ya kai yawancin Turai da Afirka da Amerika. An ji shi a Greenland da West Indies da tsibirin Madeira, a Norway da Sweden da Birtaniya da Ireland kuma. Ya rufe a kalla mil miliyan hudu murabbai. A Afirka girgizan ya yi tsanani yadda ya yi a Turai. Ya hallaka wuri mai yawa a Algiers; kuma kusa da Morocco, ya hadiye wani kauye mai mutum dubu takwas zuwa dubu goma. Wani babban rakumin ruwa ya share gabar Spain da Afirka, ya jawo hallaka mai yawa a birane. BJ 302.2
A Spain da Portugal ne girgizar ta fi karfi. A Cardiz, rakumin ruwan aka ce bisan sa ya kai kafa sittin. Duwatsu, “wadansu mafi girma a Portugal, suka raunana kwarai kamar ma daga tushensu, wadansun su kuma suka bude a samansu, suka rarrabu suka yayage, abin al’ajibi, manyan bangarorinsu kuma suka gangara zuwa kwarin da ke kewaye. An ce harsunan wuta sun rika fitowa daga duwatsun nan.” BJ 302.3
A Lisbon, “an ji karar tsawa a kalkashin kasa, jima kadan kuma wata girgiza mai-karfi ta rusar da yawancin birnin cikin misalin minti shida, mutum dubu sittin suka hallaka. Da farko teku ya ja da baya, ya bar yashin gabar, sa’annan ya dawo, ya hau kafa hamsin ko fiye da ainihin yadda ya saba kaiwa.” Cikin sauran ababan ban mamaki da aka ce sun faru a Lisbon, lokacin bala’in, akwai nutsewar wani masaukin jiragen ruwa da aka gina da kurdi mai yawa. Mutane da yawa sun taru a wurin don fakewa daga baraguzan rushe rushe; amma faraf daya wurin ya nutse da dukan mutanen, kuma ko gawa daya bai taba fitowa kan ruwan ba.” BJ 303.1
“Motsin rawan duniyar ke da wuya, nan da nan kowace ekklesiya da gidan masu zaman zuhudu, da kusan kowane babban ginin gwamnati da fiye da daya daga cikin hudu na gidaje suka rushe. Kamar sa’oi biyu bayan matsannacin motsin, wuta ta kama wurare daban dabam ta rika ci kuma da karfi sosai har kusan kwana uku, har birnin ya zama kango gaba daya. Rawan duniyan ya faru a rana ce mai tsarki, yayin da majami’u da gidajen ma’aikatan ekklesiya sun cika da mutane, kalilan daga cikinsu ne kuwa suka tsira. “Razanar mutanen ta wuce misali. Ba wanda ya yi kuka; ya fi karfin hawaye, sun rika gudu nan da can, a rikice da tsoro da mamaki, suna kuka cewa duniya ta kare. Uwaye suka manta ‘ya’yansu, suka rika gudu cike da gumaka masu alamar giciye. Cikin rashin sa’a mutane da yawa sun gudu zuwa majami’u don neman tsaro; amma a banza aka bude farantin jibi; a banza aka rika rungumar bagadi; gumaka da pristoci da mutane suka kone tare a lokaci daya.” An kiyasta cewa mutum dubu tasa’in ne suka mutu a wannan ranar. BJ 303.2
Bayan shekara ashirin da biyar, alama ta biye da annabci ya ambata ta bayyana-duhuntawar rana da wata. Abin da ya sa wannan ya fi daukan hankali shi ne cewa an ambaci ainihin lokacin cikawarta. Cikin hirar Mai-ceton da alamjiransa a Dutsen Zaitun, bayan Ya bayana lokacin jaraba ga ekklesiya mai-tsawon nan, shekaru 1260 na zaluncin paparuma, inda ya ce za a takaita kuncin - Ya ambaci wadansu al’ammura da za su rigayi zuwansa, Ya kuma fadi lokacin da na farkon zai faru: “Amma a chikin wadannan kwanaki, bayan wannan kunchi, rana za ta yi dufu, wata ba za ya ba da haskensa ba.” Markus 13:24. Kwana ko shakaru 1260 din sun kare a 1798 ne. Shekara ashirin da biyar kafin nan, zalunci ya kusa tsayawa gaba daya. Bayan wannan zaluncin, bisa ga maganar Kristi, rana za ta duhunta. Ran 19 ga Mayu, 1780, an cika wannan annabcin. BJ 304.1
“Kusan gaba daya ba abinda ya fi ranan duhun nan na 19 ga Mayu, 1780, inda ba dalili kawai sama da sarari ko ina a New England ya yi duhu.” BJ 304.2
Wani mazamnin Massachusets da aka yi abin a idonsa ya bayana al’amarin kamar haka: “Da safe rana ta fito da haske, amma nan da nan ta rufu. Gizagizai suka duhunta, daga cikinsu kuma, da suka kara duhu da ban tsoro, walkiya ta haskaka, tsawa ta buga, ‘yar ruwan sama kadan kuma ta fado. Kusan karfe tara, gizagizan suka rage duhu, suka zama kamar kalan jan karfe, kuma hasken da ba a saba gani ba ya canja kasa da duwatsu da itatuwa da gine gine da ruwa da mutane. Mintoci kadan bayan wannan, wani babban bakin girgije ya rufe dukan sararin sama, sai dai karamar layi a gefe, wuri kuma ya yi duhu kamar yadda yakan kasance karfe tara na dare da damina …. “Tsoro, damuwa da fargaba suka cika zukatan mutane a hankali. Mata suka tsaya a kofa, suna kallon duhun; maza suka dawo daga gonakinsu, kafinta ya bar kayan aikinsa, makeri ya bar makera, mai-shago ya bar kantarsa. Matafiya suka sauka a gidan gona da ya fi kusa. Aka rufe makarantu, ‘yan makaranta kuma da rawan jiki suka ruga zuwa gida. Kowa ya dinga tambaya, “Me ke faruwa ne?” Kamar dai mahaukaciyar guguwa ce za ta abko ma kasar, ko kuma kamar ranar karshen komi kenan. BJ 304.3
“An yi anfani da kyandir ko ina, wurtar muruhu ta haskaka Kaman ana duhun dare inda ba wata da bazara.… Kaji suka koma wurin kwanansu, suka yi barci, shanu suka tattaru a wurin kwanansu, kwadi suka rika kara, tsuntsaye suka raira wakokin su na yamma, jemage suka rika firiya ko ina. Amma dan Adam ya san cewa dare bai yi ba. BJ 305.1
“Dr. Nathanael Whittaker, paston ekklesiyar Tabernacle a Salem, ya rika yin sujada a majami’ar, ya kuma yi wa’azi inda ya nace cewa duhun nan ya wuce ikon dan Adam. A wadansu wurare da yawa ma an taru. Nassosin da aka karanta a wurin kowane taro duka masu nunawa ne cewa duhun nan cikan annabci ne... Duhun ya fi yawa jima kadan bayan karfe sha daya ne.” A yawancin sassan kasar, ya yi yawa da rana, ta yadda mutane basu iya fadin lokaci tawurin duba agogo ba, ko cin abinci, ko yin ayukan su na gida ma basu yiwu ba, sai da hasken kyandir….. BJ 305.2
“Yawan wuraren da duhun nan ya kai ba na kullum ba ne. An gan shi har can Famentta. Ta yamma ya kai har kurewar Connecticut, har Albany ma. Ta kudu, an gan shi a gabar teku, ta arewa kuma har duk inda kasar Amerika ta kai.” BJ 305.3
Sa’a daya zuwa biyu kafin yamma, haske ya bayana kadan bayan bakin duhun nan na ranan, rana kuma ta fito, ko da shike bakar raba mai-nauyi ta rage hasken ranan. “Bayan faduwar rana, gizagizan suka sake dawowa, nan da nan kuma wuri ya yi duhu.” “Kuma duhun daren bai kasa na rana ban mamaki da ban tsoro ba; ko da shike akwai kusan cikakken wata, ba a iya ganin komi ba sai da haske wanda mutum ne ya harhada, wanda idan aka gani daga gidaje makwabta da wadansu wurare daga nesa, suka nuna kamar ta duhun Masar wadda ta kusa ta gagari haske wucewa.” Wani wanda aka yi abin a idonsa ya ce: “Dole a lokacin na yi tunani cewa da an nade kowane abu mai ba da haske cikin dukan duniya da wani abinda haske ba zai wuce ta cikin sa ba, ko kuma a batar da duk ababa masu ba da hasken ma, da duhun ba zai fi wanda aka yi ba.” Ko da shike da karfe tara na daren, wata ta kai cikarta, “ba ta yi wani anfani wajen korar duhun ba.” Bayan tsakar dare duhun ya watse, wata kuma sa’anda ya fara ganuwa, ya zama kamar jini. BJ 305.4
A tarihi ana ce da 19 ga Mayu, 1780 “Ranar Duhu” ce. Tun lokacin Musa ba wani lokacin duhu da ya kai wannan zurfi da fadi da dadewa. Yadda wadanda aka yi a idonsu suka bayana shi, al’amarin daidai ne da kalmomin Ubangijimu ta bakin annabi Joel, shekara dubu biyu da dari biyar kafin cikawar su. Ya ce: “Rana za ta juya ta zama dufu wata kuma za ya zama jini, kamin babbar rana mai-ban razana ta Ubangiji ta zo. Joel 2:31 BJ 306.1
Kristi ya ce ma mutanensa su lura da almun zuwansa, su kuma yi farinciki yayinda za su ga alamun Sarkinsu da ke zuwa. Ya ce: “Amma sa’anda wadannan al’amura sun soma faruwa, ku duba bisa, ku ta da kanku; gama pasarku ta kusa.” Ya nuna ma masu binsa itatuwa masu fitarda furanni da bazara, Ya ce: “Sa’anda suna tofuwa, kukan gani, kun sani kuma chikin rayukanku bazara ta kusa. Hakanan kuma, lokochin da kun ga wadannan al’amura suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya kusa.” Luka 21:28, 30, 31. BJ 306.2
Amma sa’anda ruhun tawali’u da dukufa ya zama ruhun girman kai da al’adu, kaunar Kristi ta yi sanyi. Da mutanen Allah suka tsunduma cikin son duniya da holewa sai suka manta umurnin Mai-ceton game da alamun bayanuwarsa. Aka manta batun zuwan sa na biyu din. Aka dinga karkata fasarar nassosin da suka shafi zuwan na sa har ya kai inda aka manta da shi ma, musamman a ekkleisiyoyin Amerika. ‘Yanci da holewa da jama’a suka samu, burin samun wadata da busar iska, dukufa ga neman kurdi, gaggawar neman suna da iko, sun sa mutane suka mai da hankullansu da begensu ga kayan rayuwa na yanzu, suka kuma nisantar da zancen ranan nan da al’amuran rayuwan nan za su shude. BJ 307.1
Sa’anda Mai-ceton Ya bayana ma masu bi ga alaman zuwansa, Ya yi annabcin koma baya da za a samu gaf da komowansa. Kamar kwanakin Nuhu, za a shagala cikin ayukan duniya da son jin dadi - saye da sayarwa, shuka, gine-gine, aure da auraswa- an manta Allah da rai da ke zuwa. Ga masu rai a wannan lokaci, gargadin Kristi shi ne: “Amma ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku ba labari kamar tarko.” “Amma a kowane loto sai ku yi tsaro, kuna yin roko ku sami ikon da za ku tsere ma dukan wadannan al’amuran da za su faru, ku tsaya kuma a gaban Dan mutum.” Luka 21:34, 36. BJ 307.2
Maganar Mai-ceton, cikin littafin Ruya ta yi annabcin yanayin ekklesiya a wannan lokacin: “Kana da suna mai-rai ne, amma matache ne.” Ga wadanda suka ki tashi daga gamsuwa da rashin kulawansu an ba da gargadi cewa: “Idan fa baka yi tsaro ba, ina zuwa da kamar barawo, ba kwa za ka san sa’an da zan afko maka ba.” Ruya 3:1,3. BJ 307.3
An bukaci falkas da mutane daga hatsarinsu, domin su shirya ma al’amuran da suka danganci rufewar gafara. Anabcin Allah ya ace: “Gama ranar Ubangiji mai-girma che, mai-ban razana kwa; wa ke da iko ya jimre da ita?” Wa zai tsaya sa’anda ya bayana, Shi “wanda tsarkin idon sa ya fi gaban duban mugunta,” Ga wandanda ke kuka cewa, “Ya Allah na, mun sanka,” amma suka ketare alkawalinsa, suka kuma bi wani allah, suna boye zunubi a zukatansu, suna nuna kaunar tafarkun rashin adalci, a gare su rana ta Ubangiji za ta zama “dufu kwarai ma, babu haske a chiki ko kadan.” Hosea 8:2, 1; Zabura 16:4; Amos 5:20. Ubangiji ya ce: “Za ya zama kwa a loton nan, zan yi binchiken Urushalima da fitillu, in hukumta mutanen da ke zamne lubus, masu-chewa chikin zuchiyassu, Ubangiji ba za ya aika nagarta ba, ba kwa za ya aika mugunta ba.” Zaphaniah 1:12. “Zan fori duniya kuma domin muguntassu, da miyagu kuma saba da laifofinsu: zan sa alfarmar masu griman kai ta dena, in kaskantar da alfarmar mutane masu ban tsoro kuma.” Ishaya 13:11. “Ko azurfassu ko zinariyassu ba za su iya chetonsu ba,” “Wadatassu za ta zama ganima, gidajensu kuma risbewa.” Zaphaniah1:18, 13. BJ 308.1
Sa’anda annabi Irmiya ya hangi wannan lokaci mai-ban tsoro, ya ce: “Chiwo ni ke ji har chikin zuchiyata:…ban iya zama shuru ba, domin ka ji karar kafo, hargitsin yaki, ya raina. Ana hiran hallaka a kan hallaka.” Irmiya 4:19,20. BJ 308.2
“Wannan rana ranar hasala che, ranar wahala da kumchi, ranar kadaichi da risbewa, ranar dufu da gama gira, ranar hadura masu-zurfi da dufu baki kirin, ranar kafo da ihu.” Zaphaniah 1:15,16. “Duba ga ranar Ubangiji tana zuwa;… garin a mai da kasa kango, a kuma hallaka masu-zunubin da ke chiki, su kare” Ishaya 13:9. BJ 308.3
Sabo da babbar ranan nan maganar Allah da babban murya tana kiran mutanensa su falka daga barcinsu na ruhaniya su bidi fuskarsa da tuba da kaskantar da kai: “Ku busa kafo chikin Sihiyona, ku buga ihu chikin dutse na mai-tsarki; bari dukan mazamnan kasa su yi rawan jiki; gama ranar Ubangiji tana zuwa, har ma ta yi kusa.” “A tsarkake jama’a, a tattara dattibai, a tattara yara:… bari ango shi fita dakinsa, amarya kuma daga chikin lolokinta. Bari priest masu- hidimar Ubangiji, su yi kuka tsakanin haraba da bagadi,” “Ku juyo mani da dukan zuchiyarku, tare da azumi da kuka da bakinchiki: ku tsaga zukatanku ba tufafin ku ba, ku juyo wurin Ubangiji Allahnku: gama shi mai-alheri ne chike da juyayi, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinkai.” Joel 2:1; 15-17, 12, 13. BJ 309.1
Domin shirya jama’a su tsaya a rana ta Allah, an yi babban aikin canji. Allah Ya ga cewa da yawa cikin masu-cewa su nasa ne ba sa shiri don rai na har abada, kuma cikin jinkansa Ya shirya aiko da sakon da zai falkas da su daga barci ya sa su shirya domin zuwan Ubangiji. BJ 309.2
Ruya 14 ya ambaci wannan gargadin. Nan ga sako mai-sassa uku da aka ce malaiku ne suka sanar wanda kuma zuwan Dan mutum ya bi nan da nan domin girbe duniya. Gargadi na farkon yana ba da sanarwar hukumci da ke zuwa. “Annabin ya hangi malaika yana firiya a tsakiyar sararin sama, yana da bishara ta har abada wadda za a yi shellatta ga mazamnan duniya, ga kowanne iri da kabila da harshe da al’umma; da babbar murya kwa ya che, ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja; gama sa’ar hukmchinsa ta zo; ku yi sujada ga wanda ya yi sama da duniya da teku da mabulbulan ruwaye.” Ruya 14:6,7. BJ 309.3
Sakon nan aka ce wani bagangare ne na “bishara ta har abada.” Ba malaiku aka ba su aikin shelar bisharar ba, mutane ne aka ba su. An bukaci malaiku su bi da wannan aikin. Su ke lura da aikace aikace na ceton mutane, amma bayin Kristi a duniya ne suke anihin shelar bisharar. BJ 310.1
Amintattun mutane da suka yi biyayya ga ruhun Allah da koyaswoyoyin maganarsa ne masu-shelar kashedin nan ga duniya. Su ne wadanda suka ji “maganar annabchi wadda aka fi tabbatasda ita,” a fitilla mai-haskakawa chikin wuri mai-dufu, har gari yawaye, tamraro na assubahi kuma ya fito.” II Bitrus 1:19. Sun rika neman sanin Allah fiye da boyayyun dukiya, suka dauka cewa “ya fi chinikin azurfa kyau, ribatta kuma tafi suhihiyar zinariya.” Misalai 3:14. Ubangiji kuma ya bayana masu muhimman al’amura na mulkin. “Asirin Ubangiji ga masu tsoron sa yake; za shi kwa nuna masu wa’adinsa.” Zabura 25:14. BJ 310.2
Ba masanan tauhidi ne suka fahimci gaskiyan nan, suka kuma yi shelarta ba. Da sun yi aminci, suka dukufa cikin addu’a da nazarin Littafin, da sun san likacin daren, da annabce anabcen sun bayana masu al’amuran da za su faru. Amma basu dauki matsayin nan ba, aka kuma ba ma su tawali’u sakon. In ji Yesu: “Ku yi tafiya tun kuna da haske, domin kada dufu ya chim maku.” Yohanna 12:35. Wadanda ke juyawa daga hasken da Allah a bayar ko kuma suka ki neman Shi lokacin da za su iya samun Shi, za a bar su cikin duhu. Amma Mai-ceton ya ce: “Wanda yana biyo na ba za shi yi tafiya cikin dufu ba, amma za ya sami hasken rai.” Yohanna 8:12. Duk wanda da, zuciya daya ke kokarin yin nufin Allah, yana kuma bin hasken da an rigaya an bayar, za ya sami Karin haske, a gare shi za a aiko da wani tauraro mai-walkiyar sama domin bishe shi zuwa dukan gaskiya. BJ 310.3
Lokacin zuwan Kristi na farko, priestoci da marubuta na Birni Mai-tsarkin, wadanda aka ba su amanar maganar Allah, ya kamata da sun gane alamun zuwan Yesu. Anabcin Mikah ya ambaci wurin da za a haife shi; Daniel ya fadi lokacin zuwansa, Mikah 5:2; Daniel 9:25. Allah Ya ba shugabanin Yahudawa annabce annabcen nan; ba su da hujjar rashin bayana ma mutane cewa zuwan mai-ceton ya kusa. Jahilcinsu sakamakon kyaliya ne. Yahudawa sun rika gina ababan tunawa da annabawan Allah da aka kashe amma kuma tawurin girmama manyan mutane na duniya sun rika daukaka Shaitan ne. Yayin da neman matsayi da iko ya dauke hankalinsu, suka manta darajan da sarkin sama ke mika masu. BJ 311.1
Yakamata da dattiban Israila cikin marmari suka rika nazarin wuri da lokaci da yanayin abin nan mafi girma a tarihin duniya, watau zuwan Dan Allah domin fansar mutum. Ya kamata da dukan mutane sun yi tsaro suna jira domin su zama na farko da za su marabci Mai-fansar duniya. Amma, ga shi, a Baitalahmi, gajiyayyun matafiya daga Nazareth su biyu suka bi duk tsawon titin garin har kurewar gabas, a banza, suna neman mafaka da wurin kwana. Ba inda aka karbe su. A wani dakin shanu suka sami mafaka, kuma nan ne aka haifi Mai-ceton duniya. BJ 311.2
Malaikun sama sun ga darajan da Dan Allah yake da shi tare da Uban, kafin halittar duniya, kuma da marmari sosai suka rika begen bayanuwarsa a duniya a matsayin al’amarin da ke cike da mafificin farinciki ga dukan mutane. Aka sa malaiku suka kai labari mai dadin nan ga wadanda ke shirye su karbe shi su kuma sanar da shi da farinciki ga mazamnan duniya. Kristi Ya sunkuya domin shi dauka ma kansa yanayin mutuntaka; za ya dauki nauyi mai-ban tausayi yayinda zai mai da ransa hadaya don zunubi; duk da haka malaiku sun so da ko cikin kaskantarwarsa ma Dan Allah shi bayana a gaban mutane da martaba da darajan da suka cancanci halinsa. Ko manyan mutane za su taru a babban birnin Israila don marabtarsa? Ko tulin malaiku za su gabatar da shi ga masu begen zuwan nasa? BJ 311.3
Malaika ya ziyarci duniya domin ya ga wadanda ke shirye su tarbi Yesu. Amma bai ga alamun jira ba. Bai ji muryar yabo da nasara cewa lokacin zuwan Masiyan ya yi kusa ba. Malaikan ya yi shawagi kewaye da birni mai-tsarkin da haikalin, inda kasancewar Allah ta dinga ganuwa har zamanu, amma ko a nan ma rashin kulawan ne ya tarar. Priestoci cikin alfarmarsu da holewarsu suna mika kazamattun hadaya a haikalin. Farisawa da manyan muryoyi suna ma mutane jawabi ko kuma addu’o’i na girman kai a gefen tituna. A gidajen sarakuna da wuraren taron masana da makarantun mallaman Yahudawa, duka basu damu da al’amarin nan da ya cika sama da murna da yabo ba - cewa Mai-fansar mutane ya kusa bayanuwa a duniya. BJ 312.1
Ba alama cewa ana sa rai Kristi zai zo, kuma ba shiri domin sarkin rai. Cikin mamaki dan sakon saman zai koma sama kenan da labari mai-ban kuyan, sai ya ga wadansu makiyaya suna tsaron tumakinsu da dare, kuma yayin da suke kallon sammai cike da taurari, suna bimbinin annabcin Masiyan da ke zuwa duniya, suna kuma begen zuwan Mai-fansar duniya. Wannan kam suna shirye su karbi sakon daga sama. Nan da nan kuwa malaikan ya bayana, yana shelar labari mai-kyau na babban murna. Darajar sama ta cika dukan wurin, wata kungiyar malaiku da ba a iya kirgawa ba ta bayana, kuma kamar murnar ta fi karfin mutum daya ya kawo daga sama, tulin muryoyi suka shiga raira wakar da dukan al’ummai na cetattu za su raira wata rana: “Alhamdu ga Allah a chikin mafi daukaka, a duniya kuma salama wurin mutane.” Luka 2:14. BJ 312.2
Labarin nan na Baitalahmi darasi ne babba. Yana tsauta ma rashin bangaskiyarmu da faharyarmu da isarmu. Yana mana kashedi mu yi hankali, kada saboda kyaliyarmu mu ma mu kasa gane almun zamanai, har mu kasa sanin ranar ziyartarmu. BJ 313.1
Ba a duwatsun Yahudiya, ko kuma cikin makiyaya ne kadai malaikun suka iske masu begen zuwan Masiyan ba. A kasar kafirai ma an iske masu nemansa; masu hikima ne, mawadata masu martaba, shehunan gabas. Cikin nazarin halitta, shehunan nan sun iske Allah cikin aikin hannuwansa. Daga Littafi na Yahudawa sun ga cewa wani Tauraro zai taso daga Yakub kuma da marmari mai-yawa suka jira zuwansa, shi wanda zai zama “Ta’aziya ta Israila” da kuma “Haske domin bayananuwa ga Al’ummai,” da kuma “kawo cheto har iyakachin duniya.” Luka 2:25,32; Ayukan 13:47. Masu neman haske ne su, kuma haske daga kursiyin Allah ya haskaka sawayen su. Yayin da priestoci da mallami na Urushalima, wadanda aka zaba su zama wakilan gaskiyar da masu koyar da ita ke fama cikin duhu, taruraron da Allah ya aika ya bi da alumman nan zuwa inda aka haifi Sarkin. BJ 313.2
Ga “wadanda suke sauraronsa” ne Kristi “za ya sake bayanuwa ban da zunubi… zuwa cheto.” Ibraniyawa 9:28. Kamar labarin haihuwar Mai-ceton, ba a ba shugabannin addini amanar sakon zuwansa na biyu ba. Sun kasa rike dangantakarsu da Allah, suka kuma ki haske daga sama; sabo da haka ba sa cikin wadanda manzo Bulus ya ce masu, “Amma ku, yan’uwa ba chikin dufu kuke ba, da ranan nan za ta tarshe ku kamar barawo: gama ku duka yayan haske ne, yayan rana kwa; mu ba na dare ba ne, ba kwa na dufu ba.” Tasssalunikawa I, 5:4,5. Masu tsaro a kan ganuwar Sihiyona ne ya kamata su fara samun labarin zuwan mai-ceton, na farko da zasu ta da murya su bayana cewa Ya kusa, na farko da za su gargadi mutane su shirya domin zuwansa. Amma sun yi sake, suna mafalkin salama da zaman lafiya, yayinda mutanen ke barci cikin zunubansu. Yesu ya ga ekklesiyarsa, kamar itacen bauren nan mara ‘ya’ya, yafe da ganyaye na rudu kawai, amma ba ‘ya’ya. Sun rika kiyaye al’adun addini, amma ba ruhun ainihin tawali’u da tuba da bangaskiya wanda shi ne kadai zai iya sa ibadarsu ta karbu ga Allah. Maimakon halayya na Ruhu, an rika nuna girman kai, da burga da son kai, da danniya. Ekklesiya mai koma baya ta rufe idanunta ga alamun zawanun. Allah bai rabu da su, ko kuma ya bar amincinsa ya kare ba, amma su sun rabu da shi, suka kuma raba kansu da kaunarsa. Da shike sun ki cika sharuddan, ba a cika alkawaran a garesu ba. BJ 313.3
Haka sakamakon rashin fahimta a kuma yi anfani da haske da tasirin da Allah ya bayar. Idan ekklesiya ba ta bi umurninsa, ta karbi kowace tsirkiyar haske, ta yi dukan aikin da aka bayyana ba, addini zai tabarbare, ya zama kiyayewar al’adu kadai, ruhun ainihin ibada kuma shi bata. Tarihin ekklesiya ya rika bayana gaskiyan nan akai akai. Allah yana bidar ayukan bangaskiya da biyayya da suka je daidai da albarku da zarafin da Ya bayar. Biyayya tana bukatar sadakarwa ta kuma kunshi giciye; kuma dalili kenan masu bin Kristi da yawa suka ki karban hasken daga sama, kuma kamar Yahudawa na da, basu san lokacin ziyartar su ba. Luka 19:44. Sabo da girman kansu da rashin bangaskiyarsu, Ubangiji Ya tsallaka su ya kuma bayana gaskiyarsa ga wadanda kamar makiyayan Baitalmi da Shehunan Gabas, suka yi amfani da dukan hasken da suka samu. BJ 314.1