Yan Canjin Ingila, yayin da suka watsar da koyaswoyin Rum, sun rike siffofinta da yawa. Sabo da haka, ko da shike an ki ikon Rum da koyaswarta, an shigar da al’adunta da bukukuwanta cikin sujadar Ekklesiyar Ingila. An rika cewa wai wadannan ababa ba batutuwan lamiri ba ne, cewa ko da shike Littafin bai umurta a yi su ba, saboda haka kuma wauta ne su, duk da haka ba a hana su ba, don haka kuma su kansu ba mugunta ba ne. Kiyaye su ya rage banbancin da ya raba ekklesiyoyin da suka canja daga Rum, aka kuma ce wai za su taimaka wajen sa Rum ta karbi bangaskiyar masu Kin ikon paparuma. BJ 287.1
Ga masu ra’ayin mazan jiya da masu son daidaitawa, wadannan ra’ayoyin sun nuna kamanin gaskiya. Amma akwai wata kungiya da bata yarda hakan ba. Zancen cewa al’adun nan “suna iya cire bambancin da ke tsakanin Rum da canjin” dalili ne da ya sa bai kamata a ci gaba da al’adun ba. Sun ga al’adun kamar alamun bautan da suka fito daga ciki wanda kuma basa sha’awar komawa ciki. Sun yi tunanin cewa Allah ya tanada kaidodin sujadarsa cikin maganarsa, kuma mutane ba su da yanci su kara a kansu ko su rage daga cikin su. Farkon babban riddar ita ce neman tokarar ikon Allah da ta ekklesiya. Rum ta fara da hana abin da Allah bai hana ba, ta kuma karasa da hana abinda Ya umurta a sarari. BJ 287.2
Da yawa sun yi sha’awar komawa tsarki da saukin kan ekklesiyar farkon, sun mai da yawancin kafaffun al’adun Ekklesiyar Ingila tamkar al’adun bautar gumaka, kuma ba za su iya hada kai da su cikin sujada ba. Amma ekklesiyar, da goyon bayan hukumomin kasa, ba ta yarda da bambancin ra’ayi game da al’adunta ba. Akwai dokar da ta tilasta halartar sujada, ta kuma haramta duk-wani taron sujada ba tare da iznini ba, wanda ya yi kuma a jefa shi a kurkuku, ko a kore shi a kasar, ko a kashe shi. BJ 288.1
A farkon karni na sha bakwai sarkin da ya fito hawa gadon sarautar Ingila ya sanar da niyyarsa ta sa masu ra’ayin tsabtata adini su “yi sauron ekklesiya ko a kore su daga kasar, ko ma abinda ya fi haka muni,” Sa’an da aka rika farautarsu, ana zaluntarsu, anakuma tura su kurkuku, basu ga alamar gyara nan gaba ba, da yawa kuma suka yarda cewa ga dukan wadanda ke son bauta ma Allah bisa ga lamirinsu, Ingila ba wurin zama ba ne. Wadansu karshen ta suka bidi mafaka a Holland. An fuskanci wahaloli da hasara da kurkuku kuwa. Aka rushe manufofinsu, aka kuma bashe su a hannun magabtansu. Amma naciya ta yi nasara a karshe, suka kuma sami mafaka a jamhuriyar Holland. BJ 288.2
Garin gudunsu, sun bar gidajen su da dukiya, da hanyar rayuwarsu. Suka zama baki a kasar bakunci, cikin mutane masu harshe dabam da al’adu dabam. Dole suka shiga sabobin hanyoyin neman abin zaman gari da ba su taba gwadawa ba. Mutane da duk rayuwarsu manema ne, yanzu suka fara koyon kanikanci. Amma da farinciki suka amince da sabon yanayinsu, maimakon zaman banza da gunaguni. Ko da shike talauci ya dinga damun su, sun gode ma Allah da albarkun da ya masu, suka yi farinciki da yancin sujadarsu, ba fitina. “Sun san su baki ne, basu damu da komai ba sosai, amma suka dubi sama kamnataciyar kasarsu, suka kwantar da hankulansu.” BJ 288.3
Cikin hijira da wahala kaunarsu da bangaskiyarsu sun kara karfi. Suka gaskata alkawuran Ubangiji, shi kuwa bai yashe su a lokacin bukatar su ba. Alaikunsa sun kasance tare da su don karfafa su da taimaka masu, suka tokare su kuma. Sa’anda kuma hannun Allah ya nuna masu ketaren teku, kasa inda za su kafa kasar kansu, su kuma bar ma ‘ya’yansu gadon ‘yancin ibada, suka ci gaba, ba da shakka ba, inda Allah Ya bi da su. BJ 289.1
Allah Ya bar jarabobi suka abko ma mutanensa domin a shirya su cika nufinsa domin su. An kaskantar da ekklesiya domin a daukaka ta. Allah yana gaf da nuna ikonsa a madadin su, ya ba duniya wata shaida kuma cewa ba zai bar wadanda suka amince da Shi ba. Ya shirya al’amura ta yadda fushin Shaitan da dabarun miyagun mutane za su kawo ci gaban daukakarsa su kuma kawo mutanen Sa wurin tsaro. Zalunci da hijira sun bude hanyar yanci. BJ 289.2
Sa’anda ya zama masu dole su rabu da Ekklesiyar Ingila, masu son tsarkin ekklesiyar suka dauki alkawali, kamar yantattun mutanen Ubangiji, za su “yi tafiya tare cikin dukan hanyoyinsa da aka sanar masu ko kuma za sanar masu.” Ainihin ruhun kaidar Kin ikon paparuma kenan. Da wannan manufan ne matafiyan nan suka bar Holland zuwa sabuwar duniya. Pastonsu John Robinson, wanda Allah ya hana shi tafiya tare da su, cikin jawabinsa na ban kwana dasu ya ce ma yan hijiran: BJ 289.3
“Yan’uwa, yanzu za mu rabu, kuma Ubangiji ne Ya san ko zan sake ganin fuskokinku kuma. Amma ko Ubangiji Ya shirya haka ko babu, na gardade ku a gaban Allah da malaikunsa masu tsarki, ku bi ni daidai iyakar inda na bi Kristi kadai. Idan Allah Ya bayyana kansa gareku ta wurin wani kayan aikinsa kuma, ku kasance a shirye ku karbe shi kamar yadda kuka kasance a shirye ku karbi kowace gaskiya daga hidimata, gama na tabbata cewa Ubangiji yana da karin gaskiya da hasken da zai bayyana daga maganarsa mai-tsarki.” BJ 289.4
“Ni kuma, na damu sosai game da yanayin ekklesiyoyin canjin, yadda suka kai wani zamani na addini, suka kuma kasa ci gaba fiye da lokacin canjinsu. Luthawa basu iya wuce abinda Luther ya gani ba, Calvinawa kuma, kun ga sun tsaya cik, inda shahararren mutumin Allahn nan da bai ga dukan ababa ba ya bar su. Wannan abin bakin ciki ne sosai, domin ko da shike su haske ne da ya haskaka a zamaninsu, duk da haka basu shiga cikin dukan hikimar Allah ba, amma da suna da rai yanzu da sun kasance a shirye su rungumi karin haske kamar yadda suka karbi na farkon. BJ 290.1
“Ku tuna alkawalin ekklesiyarku, inda kuka yarda za ku yi tafiya cikin dukan hanyoyin Ubangiji da aka sanar da ku ko kuma za a sanar da ku. Ku tuna yarjejjeniyarku da Allah da juna kuma, cewa za ku karbi kowane haske da gaskiya da za a nuna maku daga rubutaciyar maganarsa, amma ku yi hankali, ina rokon ku, game da abinda za ku karba kamar gaskiya, ku gwada shi ku kuma auna shi da sauran nassosin gaskiya kafin ku karbe shi, gama ba shi yiwuwa duniyar Krista ta fito ta fito kwanan nan daga irin bakin duhun nan na kin Kristi, a ce kuma an sami cikakken haske a lokaci daya.” BJ 290.2
Marmarin yancin lamiri, ne ya motsa matafiyan suka dauki kasadar doguwar tafiyan nan na ketarewar teku, suka jimre wahalolin jeji, kuma da albarkar Allah, suka shuka harsashen al’umma mai-girma a Amerika. Amma duk da amincinsu da tsaron Allah da suke da shi matafiyan basu rigaya suka fahimci babban kaidar ‘yancin addini ba. Su basu kasance a shirye su ba wadansu ‘yancin nan da suka sha wahalar samo ma kan su ba. Kalilan ne ke daga shahararun masana da masu halin kirki na karni na sha bakwai suka ainihin gane muhimmiyar kaidan nan, wadda ta fito daga Sabon Alakawali, wadda ta yarda da cewa Allah ne kadai mai shar’anta bangaskiyar “yan adam.” Koyaswar cewa Allah Ya ba ekklesiya damar mallakar lamiri, ta kuma sansance ridda har ta hore shi, daya daga cikin kurakurai masu zurfi na tsarin paparuma ne. Yayin da ‘yan canjin suka ki koyaswar Rum, ba su rabu da ruhun rashin hakuri ba. Bakin duhun da tsarin paparuma ya kunsa Kiristanci ciki a lokacin mulkin nan nasa mai-tsawo, bai gama shudewa ba a lokacin. In ji wani jagaban Pastocin Massacusetts, ya ce: “Hakuri da juna ne ya mai da duniya masu sabani da Kristi, kuma ekklesiya bata taba samun damuwa game da horon masu ridda ba.” Makauratan suka yi wata doka cewa membobin Ekklesiya ne kadai za su iya yin magana a gwamnatin kasar. Aka kafa ekklesiya ta kasa, aka kuma bukaci dukan mutane su hada hannu don biyan bukatun masu aikin bishara, majistarori kuma aka ba su ikon ladabtar da masu ridda. Ta hakanan ikon kasa ya kasance a hannun ekklesiya. Ba da jimawa ba wadannan matakai suka haifar da sakamakonsu, watau zalunci. BJ 290.3
Shekaru sha daya bayan an kafa kasar makaurata ta farko, Roger Williams ya zo Sabuwar Duniyar. Kamar matafiyan farkon, ya zo ne don ya mori ‘yancin addini, amma ba kamar su ba, shi ya ga abinda kalilan ne daga cikinsu suka gani a zamaninsa, cewa ‘yancin nan na kowa ne kuma ba za a iya kwace shi ba. Shi mai neman gaskiya ne da himma, kuma kamar Robinson, ya gaskata cewa ba shi yiwuwa a ce an rigaya an sami dukan haske daga maganar Allah. Williams ne “mutum na farko a Kristancin zamani da ya kafa gwamnatin kasa kan koyaswar ‘yancin lamiri da daidaiton ra’ayi a doka.” ‘Ya ce aikin majistare ne ya hana aikata laifi, amma ba ya mallaki lamiri ba. Ya ce: “Majistarorin za su iya yanke hukunci game da haki tsakanin mutum da mutum, amma sa’anda suka yi kokarin umurta alhakin da ke wuyar mutum ga Allah, sun yi kuskure, kuma akwai hadari; gama a bayane yake cewa idan majistare yana da ikon nan, zai iya umurta wadansu ra’ayoyi ko koyaswoyi yau, gobe kuma ya canza su, kamar yadda sarakuna daban dabam da paparuma da majalisa daban dabam na ekklesiyar Rum suka yi a Ingila, ta yadda imani zai zama tarin rudani kawai.” BJ 291.1
Halartar sujadar ekklesiya ya zama dole a lokacin, in ba haka ba akwai biyan tara ko zuwa kurkuku. “Williams yaki dokar cewa ba ta da ma’ana, doka mafi muni a Ingila ita ce wadda ta umurta halartar sujada a majamiu. Ya ce tilasta mutane saduwa da wadanda koyaswar su ba daya ba ta kawar da hakokinsu ne a sarari, tilasta kafirai da wadanda zuwa sujada tare da jama’a daidai yake da bidar riya daga gare su.… Ya kara da cewa, ‘kada a tilasta ko wani yin sujada ko ci gaba da sujada ba da yardarsa ba.’ Masu hamayya da shi cikin mamakin koyaswoyinsa suka ce: ‘Kai! Ashe ma’aikaci bai isa ajiyarsa ba?’ Ya amsa: “I, daga wadanda suka ba shi aikin.?” BJ 292.1
An martaba Roger Williams aka kuma kaunace shi a matsayin amintacen ma’aikacin bishara, mai baye baye na musamman, mai aminci da kauna ta gaskiya; duk da haka ba a iya jimre yadda ya ki zancen ikon majistarori kan ekklesiya, ya kuma bidi ‘yancin addini ba. Aka ce anfani da wannan sabuwar koyaswar zai “gurguntar da asalin kasar da gwamnatinta.” Aka masa hukumcin kora daga kasar, a karshe kuma don kada a kama shi, dole ya gudu cikin sanyin guguwan lokacin dari, zuwa kurmin daji, BJ 292.2
Ya ce: “Har mako sha hudu na sha fama cikin mawuyacin yanayi, ban san abinci ko wurin kwanciya ba.” Amma “hankaku sun rika ciyar da ni a dajin,” kuma ya rika samun mafaka a ramin wani itace. Ta haka ya ci gaba da gudu cikin kankara da jeji inda ba hanya, har sai da ya sami mafaka wajen wata kabilar Indiyawa da ya sami yarda da amincewarsu yayin da yake kokarin koya masu gaskiyar bishara. BJ 292.3
Bayan wadansu watani, ya kai gabar tekun Narragansett inda ya kafa harsashen kasar farko a zamanin nan da ta fara amincewa da ‘yancin addini. Babbar kaidar kasar Roger Williams ita ce “cewa kowane mutum shi sami ‘yancin yin sujada ga Allah bisa ga hasken lamirinsa.” ‘Yar karamar kasarsa Tsibirin Rhode (Rhode Island), ta zama mafakar wulakantattu, ta kuma karu, ta ci gaba har sai da kaidodin tushenta, watau ‘yancin kasa da na addini, suka zama ginshikin Jamhuriyar Amerika. BJ 293.1
Cikin wannan babbar tsohuwar takarda da kakaninmu suka zana a matsayin kaidar ‘yanci, watau Sanarwar ‘Yancin Kai, suka sanar cewa: “Mun amince cewa gaskiyan nan a bayane suke, cewa an halici dukan mutane daidai ne; cewa mahalicinsu ya ba su wadansu ‘yanci da ba za a iya karabewa ba; cewa cikinsu akwai rai, ‘yanci, da neman farinciki.” Kundin Tsarin Dokokin kuma a sarari ya lamunci cewa ba za a keta lamirin mutum ba. Ya ce: “Ba za a taba bidar gwadawa ta addini a matsayin sharadin samun wani mukami na kusa a haddadun Jihohin Amerika ba.” “Majalisa ba za ta yi wata doka game da kafawar addini, ko hana ‘yancin bin addinin ba.” BJ 293.2
“Masu tsara Kundin Tsarin Dokokin sun gane madawmiyar kaidan nan cewa dangantakar mutum da Allah ya fi karfin dokokin mutane, kuma hakkokin sa na addini ba za a iya karbewa ba. Ba sai an yi tunani kafin a tabbataar da wannan ba, yana hammatar mu, mun kuma san shi. Wannan sani, wanda baya kula dokokin mutane, shi ne dinga karfafa mutane da ake kashewa don ibadarsu, yayin da ake zaluntarsu, ana kuma kashe su. Suka ji cewa alhakinsu ga Allah ya fi karfin dokokin mutane, kuma mutum bai isa ya yi iko bisa lamirin su ba. Kaida ce da ake haifar dan Adam da shi, wadda ba abin da zai kankare shi.” BJ 293.3
Sa’anda labari ya bazu cikin kasashen Turai, na wata kasa inda kowane mutum zai iya cin moriyar aikinsa ya kuma bi abin da lamirinsa ke fada masa, dubban mutane suka yi turruwa zuwa Sabuwar Duniyar. “Massacusetts, tawurin doka ta musamman, ta yi tayin kyautar maraba da taimako daga gwamnati ga Kiristan kowace kasa da za su ketare tekun Atlantic “don tsere ma yake yake ko yunwa, ko kuma danniyar azalumansu.” Ta haka masu gudun da marasa gata suka zama bakin kasar, bisa ga doka.” Shekaru ashirin daga ranan da aka fara zuwa suka sauka a Plymouth, wajen mutum dubu ashirin suka sauka a England (Sabuwar Ingila). BJ 294.1
Domin cimma manufarsu, “suka gamsu da dan abin da ya isa ya rike su, tawurin rayuwar tsimi, da yin aiki. Basu bidi komi daga kasar ba sai dai sakamakon aikinsu. Ba abin da ya rude su….Suka gamsu da ci gaban kasarsu a hankali amma ba tsayawa. Da hakuri suka jimre wahalolin jejin, suna ban-ruwa ga itacen ‘yanci da hawayensu, da kuma zufan fuskansu, har sai da tsaiwarsa ta yi zurfi cikin kasar.” BJ 294.2
Littafi ne ya zama harsashen bangaskiya, tushen hikima, da takardar sharuddan ‘yanci. An rika koyar da kaidodinsa da himma a gidaje da makarantu da majmi’u, sukamakonsa kuma ya nuna halin tanadi da na basira da tsarki da kamewa. Mutum zai iya yin shekaru a garin masu son tsabtar addinin nan, “kuma ba zai ga mashayi, ko ya ji rantsuwa, ko ya sadu da mai-bara ba.” Sun nuna cewa kaidodin Littafin ne suka fi tabbatar da girman al’umma. Kananan kasashen nan a rarrabe da juna, suka girma suka zama tarayyar jihohi masu karfi, duniya kuma cikin mamaki ta ga salama da ci gaban “ekklesiya mara paparum da kasa mara sarki.” BJ 294.3
Amma Karin mutane suka rika zuwa kasar Amerika, sabo da dalilai da suka bambanta da na matafiyan farkon. Ko dashike ainihin bangaskiya da tsabta sun nuna ikon sifantawa mai yawa, duk da haka tasirin ta ya rika raguwa akai akai sa’anda yawan masu zuwa sabo da dalilan abin duniya kadai ya dinga karuwa. BJ 294.4
Ka’idan da masu zuwan farkon suka kafa, cewa membobin ekklesiya ne kadai za su iya jefa kuri’a ko su rike matasyi a gwamnatin kasar ta haifar da munanan sakamako sosai. Da an dauki matakin nan a matsayin hanyar kiyaye tsabtar kasar ne, amma sai ya jawo lalacewa ga ekklesiya. Da shike addini ne sharadin yin zabe da samun matsayi da yawa, domin son samun abin duniya kawai, suka hada kai da ekklesiya ba tare da sakewar zukatansu ba. Ta hakanan, ekklesiyoyin suka cika da mutanen da basu tuba ba; kuma ko cikin ma’aikatan ekklesiya ma an iske wadanda ban da ma kurkuran koyaswa da suke da shi, basu ma san ikon sabuntawa na Ruhu Mai-tsarki ba. Wannan kuma ya sake nuna miyagun sakamakon kokarin gina ekklesiya tawurin anfani da gwamnatin kasa, da kokarin anfani da ikon duniya don taimaka ma bisharar wanda ya ce: “Mulki na ba daga nan yake ba.” Yohanna 18:36. Tun zamanin Constantine, har zuwa yau, ana wannan kuskuren kuwa. Hadin kan ekklesiya da kasa, komi kankantarsa, yayin da ake gani kamar yana kawo duniya kusa da ekkleisya, yana ainihin jawo ekklesiya kusa da duniya ne. BJ 295.1
Muhimman kaidodin da Robinson da Roger Williams suka koyar, cewa gaskiya tana ci gaba ne, cewa Kirista ya kamata su kasance a shirye su karbi dukan hasken da zai haskaka daga magana mai-tsarki na Allah, zuriyarsu da suka biyo baya sun manta gaba daya. Ekklesiyoyin Amerika masu Kin ikon paparuma da na Turai ma, ga su dai sun sami tagomashi da suka karbi albarkun Canjin, amma suka kasa ci gaba da bin hanyar canji. Ko da shike amintattun mutane kalilan sun taso loto loto, suka yi shelar sabuwar gaskiyar, suka kuma bayana kuskuren da aka dade ana yi, yawanci, kamar Yahudawan zamanin Kristi, ko yan paparuman zamanin Luther, sun gamsu da irin bangaskiyar iyayensu, da kuma irin rayuwar iyayen na su. Don haka, addini ya sake lalacewa, ya zama al’ada, kurakurai kuma da camfe camfe da ya kamata da su kawas da su inda ekklesiya ta ci gaba da tafiya cikin hasken maganar Allah, aka rike su aka kuma so su. Ta hakanan ruhun da canjin ya kawo ya mutu a hankali, har sai da ka kai ga bukatar canji cikin ekklesiyoyin masu Kin ikon paparuma, kusan yadda aka bukata a ekklesiyar Rum a zamanin Luther. Aka iske son abin duniya, da sanya koyaswoyin maganar Allah da ra’ayoyin ‘yan Adam, irin na wancan zamanin. BJ 295.2
Bazawar Littafin sosai a farkon karni na sha tara, da yawan hasken da wannan ya haskaka duniya da shi, ba a bi shi da ci gaban sanin gaskiya ko addini na aikatawa daidai da hasken da aka samu ba. Shaitan bai iya hana mutane maganar Allah kamar zamanin da ba; an rigaya an kai ta inda kowa zai iya samu, amma domin dai cim ma burinsa, ya sa mutane da yawa basu ba shi muhimmanci sosai ba. Mutane suka dena binciken Littafin, sabo da haka kuwa suka ci gaba suna yarda da fasarar karya, suna anfani da koyaswoyi marasa tushe daga Littafin. BJ 296.1
Da ya gaza murkushe gaskiya tawurin zalunci, Shaitan ya koma ga sassauci da ya kai ga ridda da kafawar Ekklesiyan Rum. Ya sa Kirista suka hada kai da wadanda son abin duniya ya mai da su kamar masu bautar gumaka. Sakalamakon wannan hadin kai bai bambanta da na zamanin da ba; girman kai da almubazzaranci suka karu a sunan addini, ekklesiyoyi suka lalace. Shaitan ya ci gaba bata koyaswoyin Littafin, al’adu kuma suka habaka. Ekklesiya ta karfafa al’adun maimakon goyon bayan imani, wanda aka bayar ga tsarkaka so daya dungum. “Ta haka aka rage darajar kaidodin da yan Canjin suka wahala sosai a kai. BJ 296.2