Sa’anda Yesu Ya bayana ma almajiransa abin da zai faru da Urushalima da kuma al’amura da suka shafi zuwansa na biyu, Ya kuma fada masu abin da zai faru da mutanensa da lokacin da za a dauke Shi daga wurinsu har zuwa dawowansa cikin daraja domin kubutarwarsu. Daga Zaitun, Mai-ceton Ya hangi matsalolin da za su abko ma ekklesiyar manzanin, jima kadan, idonsa kuma ya hangi munannan guguwa da za su addabi masu binsa a sararaki na biye, cike da duhu da zalunci. Cikin kalmomi kadan cike da ma’ana, Ya bayana ababan da shugabannin duniyan nan za su yi ma ekklesiyar Allah. Matta 24:9,21,22. Dole masu-bin Kristi su bi hanyan nan na kaskanci da reni da wahala da Mai-gidan Ya bi. Za a gwada ma dukan masu-bada gaskiya ga sunan Mai-fansar duniya kiyayyar da aka nuna masa su ma. BJ 38.1
Tarihin edkklesiyar farko ya shaida cikar maganar Mai-ceton. Ikokin duniya da na lahira suka tinkari Kristi ta wurin masu-binsa. Kafirci ya ga cewa idan bishara ta yi nasara za a kawar da masujadan sa da wuraren hadayun sa; don haka kafirci ya tattaro ikokin sa domin su hallaka Kiristanci. Sai fa aka fara tsanantawa. Aka kawar da Kirista daga mallakansu, aka kuma kore su daga gidajensu. Sun “sha kokuwa mai-zafi ta wahala” Ibraniyawa 10:32. Aka “auna wadansu da ba’a da dukan bulala, i, har da sarkoki da damri.” Ibraniyawa 11:36. Da yawa sun hatimce shaidarsu da jininsu. Shugabanni da bayi, mawadata da matalauta masana da jahilai duk an karkashe su ba tausayi. BJ 38.2
Tsanantawan nan tun lokacin Nero, wajen lokacin da aka kashe Bulus, ya ci gaba har dauruwan shekaru. Aka zargi Kirista da laifuka mafi-muni, aka kuma ce su ne sanadin manyan matsaloli — yunwa da annoba a duniya. Da shi ke an ki jininsu, ko wane lokaci akwai shaidun karya a shirye domin su bashe su. Aka hukunta cewa ‘yan tawaye ne su, magabtan addini, kwari kuma ga al’umma. Aka jefa da yawan su ga namomin jeji, ko uma an kone su a wuraren shakatawa. Wadansu an giciye su ne, aka kunsa wadansu cikin fatun namomin daji, sa’an nan aka jefa ma karnuka suka cinye su. Horon su ne yakan zama baban abin kallo lokacin bukukuwa. Jama’a da yawa sukan taru domin su sha kallo, suna dariyan azabarsu. BJ 39.1
Duk inda masu bin Kristi suka nemi mafaka, akan bi su kamar namun daji ne. Sukan nemi buya a kangaye ne, inda ba mutane. “Suka sha rashi; kuntatattu ne, wulakantattu (sun fi karfin darajar duniya), suna yawo a jeji, chikin duwatsu da kogai, da kwazanzaman kasa.” Ibraniyawa 11:33, 38. Koguna suka zama mabuyar dubbai. A kalkashin tuddai a bayan birnin Rum, aka tsaga dogayen ramuka masu tsawon gaske. Nan ne masu-bin Kristi suka rika bizne matattun su, kuma nan ne suka nemi mafaka idan aka zarge su, ana neman kama su. Sa’anda Mai-ba da rai zai falkas da wadanda suka yi aminci, da yawa da aka kashe su sabo da Kristi za su taso daga wadannan wuraren ne. BJ 39.2
Cikin tsanani mafi muni wadannan shaidu na Yesu sun rike bangaskiyarsu. Ko da shi ke an hana su sakewa, aka boye su daga hasken rana, suka rika zama cikin koguna, duk da haka basu yi gunaguni ba. Da kalmomin bangaskiya da hakuri da bege suka rika karfafa juna su jimre kunci da wahala. Rashin dukiya na duniyan nan bai iya tilasta su yin musun bangaskiyarsu ga Kristi ba. Jarabobi da tsanantawa suka zama matakai da suka rika kawo su kusa da hutunsu da ladar su kuma. BJ 40.1
Kamar bayin Allah na da, “aka kashe wadansu da duka, basu karbi pansarsu ba domin su ruski tashi mafi kyau.” Ibraniyawa 11:35. Wadannan suka tuna maganar Mai-gidansu cewa idan aka tsananta masu sabo da Kristi, sai su yi murna sosai domin ladar su a sama mai-yawa ce; domin haka aka wulakanta annabawa kafin su. Suka yi farincik cewa sun isa su sha wahala sabo da bangaskiyar su, suka raira wakoki har daga cikin wuta ma. Sa’an da suka dubi sama cikin bangaskiya sai suka ga Kristi da malaiku suna kallon su daga sama, suna kuma nuna amincewa da naciyarsu. Murya ta sauko masu daga kursiyin Allah ta ce: “Ka yi aminci har mutuwa, ni ma im ba ka rawanin rai.” Uya 2:10. BJ 40.2
Shaitan ya yi kokarin hallaka ekklesiyar Allah da karfi, amma a banza. Babban jayayyan nan inda almajiran Yesu suka ba da rayukan su bai kare ba sa’an da amintattun nan suka mutu cikin famar su. Ta wurin shan kaye suka yi nasara. An kashe ma’aikatan Allah amma aikin Sa ya ci gaba. Bishara ta ci gaba da yaduwa, masu karban ta kuma suna karuwa. Ta shiga wuraren da ko gaggafar Rum ma ba za ta iya zuwa ba. Wani Kirista ya ce ma masu wulakanta su: “Kuna iya kashe mu, ku azabta mu, ku hukumta mu ma....Rashin adalcin ku shi ne shaida cewa ba mu yi laifi ba.... muguntar ku kuma ba za ta taimake ku ba.” Wahalar su ma ta karfafa wadansu ne suka karbi sakon. “Kuna kashe mu, muna kara yawaita; jinin Kirista iri ne.” BJ 40.3
An kulle dubbai aka kuma kashe dubbai, amma wadansu kuma sun taso suka dauki wurin su. Wadanda aka kashe sabo da bangaskiyarsu sun zama tabbatattu na Kristi, Shi kuma Ya mai da su masu-nasara. Sun yi aikinsu, za su kuma karbi rawanin daraja sa’anda Yesu za ya zo. Wahalar Kirista ta jawo su kusa da juna, kusa da Mai-fansa kuma. Rayuwar su ta kyakyawar kwatanci, da shaidar mutuwar su, sun zama shaidar gaskiya a kullum, har inda ba a zata ba ma ‘ya’yan Shaitan suka rika barin bautar sa suna zama masu-bin Kristi. BJ 41.1
Sabo da haka Shaitan ya sake dabarar yakin sa da gwamnatin Allah ta wurin dasa tutar sa a cikin ekklesiyar Kirista. Idan har za a iya rudin masu bin Kristi su bata ma Allah zuciya, karfin su da karfin halin su da naciyar su za su lalace, zai kuma zama da sauki a kama su. Babban magabcin kuwa ya yi yunkurin anfani da dabara don samun abin da bai iya samu da karfi ba. Tsanantawa ya tsaya, a maimakon sa kuma aka kwadaita ma mutane kayan duniya. Aka sa masu bautar gumaka suka karbi wani bangaren adinin Kirista. Suka ce sun yarda Yesu Dan Allah ne kuma Ya mutu ya kuam tashi, amma basu yarda suna da zunubi ko bukatar tuba ko sakewar zuciya ba. Da shi ke sun yarda da wadansu koyaswoyin, sai suka bidi cewa Kirista ma su yarda da wadansu koyaswoyin su, wai domin duka a hada kai a kan bangaskiya ga Kristi. BJ 41.2
Yanzu ekklesiya ta shiga babban damuwa ken nan. Kurkuku da azaba da wuta da takobi basu yi muni kamar wannan dabarar ba. Wadansu Kirista suka tsaya da karfi suka ce ba za su sassauta addinin su ba. Wadansu kuma suka goyi bayan canja wadansu fannonin bangaskiyar, suka kuma hada kai da wadanda suka karbi wani bangaren Kiristanci, suna cewa watakila ta haka ne za su tuba. Wancan lokaci ne na bakinciki ga amintattu masu bin Kristi. Kalkashin rudu na Kiristancin karya, Shaitan ya rika shigowa cikin ekklesiya, domin shi lalata bangaskiyar su, shi kuma juya zukatan su daga maganar gaskiya. BJ 41.3
Yawancin Kirista sun yarda daga baya suka sassauta matsayin su, aka kuwa sami wani hadin kai tsakanin Kiristanci da kafirci. Ko da shike masu bautar gumaka sun ce sun tuba, suka kuma hada kai da ekklesiya, sun ci gaba da bautar gumakan su, sai dai sun sake abin da suke masa sujada ne zuwa surar Yesu ko ta Maryamu ko tsarkaka. Bautar gumaka da aka kawo cikin ekklesiya hakanan ta ci gaba da mummunan aikinta. Koyaswoyi marasa kyau da camfe-camfe da bukukuwan gumaka suka sami shiga cikin bangaskiyar ekklesiya da sujadar ta. Sa’anda masu bin Kristi suka hada kai da masu bautar gumaka, addinin Kirista ta lalace, ekklesiya kuma ta rasa tsabtar ta da ikon ta. Amma akwai wadanda rudin nan bai batar da su ba. Suka rike amincin su ga Tushen gaskiya suka kuma yi sujada ga Allah kadai. BJ 42.1
A kullum, masu cewa suna bin Kristi su kan kasu kashi biyu ne. Yayin da kashi daya su kan yi nazarin rayuwar Mai-ceton su kma yi kokarin gyarta kurakuransu ta yadda za su bi gurbinsa, kashi na biyu din sukan yi banza da gaskiyan da ke bayana kurakuran nasu ne. Ko lokacin da ekklesiya ta fi karfi ma ba ta kunshi amintattu ne kadai ba. Mai-cetonmu Ya koyar da cewa kada a karbi masu-zunubin ganganci cikin ekklesiya; amma kuma Ya hada masu-raunin halaye cikin mutanen Sa, Ya ba su dandanon koyaswar Sa da kwatancin Sa, domin su sami damar ganin kurakuran su su kuma gyarta su. Cikin manzani goma sha biyu din akwai mazambaci. Ba don raunin halin Yahuda ne aka karbe shi ba, sai dai duk da an san da raunin halin nasa aka dai karbe shi. Aka hada shi da almajiran domin ta wurin fadakarwa da kwatanciin Kristi, ya koyi halin Kiristanci, ta hakanan kuma ya ga kurakurnsa, ya tuba, kuma, ta wurin alherin Allah, a tsarkakae rayuwar sa cikin biyayya ga gaskiya. Amma Yahuda bai yi tafiya cikin hasken da aka ba shi ba. Ta wurin aikata zunubi ya gayyato jarabobin Shiatan. Miyagun halayyan sa suka bayana. Ya ba da zuciyar sa ga ikokin duhu, yakan ji fushi sa’an da an tsauta masa sabo da kurakuran sa, ta haka kuma har ya kai inda ya aikata babban laifin nan na bashe Mai-gidan shi. Haka dukan wadanda ke son zunubi yayin da suke boyewa a kalkashin inuwar cewa wai su masu-bi ne, sukan ki jinin wadanda ke nuna masu zunubin su. Sa’an da sun sami dama, kamar Yahuda, za su ba da wadanda cikin kauna suka nuna masu kuskuren su. BJ 42.2
Manzanin sun sadu da wadanda cikin ekklesiya suka nuna cewa masu-bi ne su, alhali suna aikata zunubi. Hananiya da Safiratu sun yi rudi, suka nuna kamar sun ba da komi ga Allah, alhali sun ajiye ma kansu wani abu. Ruhu Mai-tsrki Ya bayana ma manzanin ainihin halin makaryatan nan, hukumcin Allah kuma ya kawar da wannan aibi daga tsabtar ekklesiya. Wannan shaida na Ruhun sani na Kristi cikin ekklesiya ya zama abin razana ga munafukai da miyagu. Ba su iya dadewa tare da wadanda ke wakiltar Kristi kullum cikin halin su da manufofin su ba; kuma yayin da jarabobi da tsanantawa suka abko ma masu bin Sa, wadanda suka kuduri aniyar barin komi sabo da gaskiya ne suka yarda su zama almajiran Sa. Sabo da haka, muddan tsanani ya ci gaba, ekklesiya ta ci gaba cikin tsabtar ta. Amma sa’an da an dena tsautawa, tubabbu marasa gaskiya ne da naciya suka rika shigowa, kofa kuwa ta budu ma Shaitan da shi ke ya sami wurin sa kafa. BJ 43.1
Amma babu jituwa tsakanin Sarkin haske da sarkin duhu, kuma ba za a taba hada kan mabiyan su ba. Sa’an da Kirista suka yarda su hada kai da wadanda basu tuba gaba daya ba daga kafirci, sun shiga wata hanya ce da ta rika kara nisantar da su daga gaskiya. Shaitan ya yi murna cewa ya rudi mutane da yawa masu bin Kristi. Sa’an nan ya kawo dukan ikon sa a kan su; ya sa suka wulakanta wadanda suka kasance da aminci ga Allah. Ba wanda ya fi sanin yadda za a saba ma koyaswar Kirista kamar wadanda sun taba zama masu-kare ta; sai wadannan Kirista da suka yi ridda, tare da abokan su masu hadawa da kafirci, suka kallafa yakin su a kan fannonin koyaswar Kristi mafiya muhimmanci. BJ 44.1
Sai da aka tsaya da gaske domin masu aminci su tsaya da karfi sabanin rudi da kazamtan da aka shigo da su cikin ekklesiya. Ba a karbi Littafi a matsayin ma’aunin gaskiya ba. Aka ce zancen ‘yancin addini ridda ce, aka kuma ki jinin masu-karfafa batun. BJ 44.2
Bayan an dade ana jayayya mai-tsawo, amintattun nan suka kudurta rabuwa da ekklesiyan nan mai-ridda, idan ta ki barin bautar gumaka. Suka ga cewa rabuwa ya zama dole idan har za su yi biyayya ga maganar Allah. Ba za su amince da kurakurai da ke iya jawo masu hallaka ba, har su kafa kwatancin da zai sa bangaskiyar ‘ya’yansu da jikokinsu cikin hatsari ba. Don tabbatar da salama da hadin kai, sun yarda su yi duk wata yarjejjeniyar da ta je daida da aminci ga Allah; amma suka ga cewa bai kamata su rabu da aminci wai domin a sami salama ba. Idan har sai an sallamar da gaskiya da adalci domin a sami hadin kai, to sai dai a ci gaba da bambanci, ko yaki ma. BJ 44.3
Da za a farfado da kaidodin da suka motsa amintattun nan a cikin zukatan mutanen Allah, da ekklesiya da duniya ma sun gyaru. Akwai kyaliya sosai game da koyaswoyin da suka kasance madogaran Kiristanci. Ana koyas da cewa wai ba su da muhimmanci sosai. Wannan lalacewan yana karfafa wakilan Shaitan, domin koyaswoyin karya da amintattu a zamanai da suka gabata suka sadakar da rayukan su domin su hana, sai ga shi yanzu dubban masu kiran kan su masu-bin Yesu suna girmama irin wadannan koyaswoyin. BJ 45.1
Kiristan zamanin farko mutane ne na musamman ainun. Halin su mara-abin zargi, da bangaskiyar su mara-sanyi zargi ne kullum da ya rika hana mai-zunubi salama. Ko da shi ke ba su da yawa, kuma ba su da arziki ko matsayi ko sarauta, sun kasance abin ban razana ga miyagu, ta wurin halayen su da koyaswoyin su. Don haka miyagu suka ki jinin su kamar yadda Kayinu ya ki jinin Habila. Dalilin da ya sa Kayinu ya kashe Habila shi ne dalilin da ya sa miyagu suka karkashe mutanen Allah. Da dalili dayan ne Yahudawa suka ki giciyayyen Mai-ceeton- domin tsarki da tsabtar halinsa sun rika tsauta ma son kansu da muguntarsu kuma. Daga zamanin Kristi har zuwa yau, amintattun almajiransa suna jawo kiyayya da magabtakan masu-zunubi. BJ 45.2
Ta yaya kenan za a ce da bishara sakon salama? Sa’an da Ishaya ya yi annabcin haihuwar Masiya, ya ba shi lakabin “sarkin salama.” Sa’an da malaikun suka sanar ma makiyaya cewa an haifi Kristi, sun raira cewa: “Alhamdu ga Allah chikin mafi-daukaka, a duniya kuma salama wurin mutanen da yake murna da su sarai.” Luka 2:14. Akwai kamanin sabani tsakanin annabce annabcen nan da maganar Kristi cewa: “Na zo ba domin in koro salama ba, amma takobi.” Matta 10:34. Amma idan an fahimce su da kyau, bayanai din sun je daidai da juna. Bishara sakon salama ce. Kiristanci tsari ne wanda idan aka karba aka yi biyayya da shi, zai kawo salama da jituwa da farinciki ko ina a duniya. Addinin Kristi zai hada kan dukan masu karban koyaswoyin sa. Manufan Kristi shi ne sasanta mutane da Allah, da juna kuma. Amma duniya kan ta tana kalkashin Shaitan, magabcin Kristi. Bishara tana ba su kaidodin rayuwa da suka bamabnta da halayen su, suna bijire mata. Sun ki jinin tsabtar ta da ke nuna munin zunuban su, suna kuma tsananta ma wadanda su ke bayana masu sharuddan ta. Da shi ke gaskiyan da take kawowa tana jawo kiyayya ne ya sa aka ce bishara ta na kawo takobi. BJ 45.3
Asirin da ke sa adilai su sha tsanani a hannun miyagu yana da ban mamaki kwarai ga masu kankantar bangaskiya. Wadansu ma sukan so su janye bagaskiyar su ga Allah wai don yana barin miyagun mutane su ci gaba, yayin da ake wulakanta nagargarun mutane masu halin kirki. Akan tambaya cewa: Yaya Mai-adalci da jinkai, Mai-matukar iko kuma, zai bari a yi rashin adalci a duniya? Wannan tambaya ce da ba ruwan mu da ita. Allah ya ba mu isashen shaidar kaunarsa, kuma bai kamata mu yi shakkar adalcinsa ba, da shi ke ba za mu iya gane al’amuransa ba.Yesu Ya ce ma almajiransa: “Ku tuna da maganata wadda na fada maku, Bawa ba ya fi Ubangijinsa girma ba. Idan suka yi mani tsanani, za su yi maku tsanani kuma.” Yohanna 15:20. Yesu Ya wahala domin mu, fiye da yadda duk wani mai-binsa zai iya wahala ta wurin muguntar miyagu. Wadanda ake bidar su su jimre azaba da kisa suna bin sawun Dan Allah ne. BJ 46.1
“Ubangiji ba mai-jinkiri ba ne ga zanchen alkawalinsa.” Bitrus II, 3:9. Ba Ya manta ‘ya’yansa, amma Ya kan bar miyagu su bayana ainihin halin su, domin kada su yaudari wadanda su ke son bin Sa. Kuma ana sa adilai cikin azaba domin a tsarkake su ne, domin kwatancin su ya nuna muguntar marasa ibada; kuma domin naciyar su ta nuna muguntar marasa ibada da marasa ba da gaskiya. BJ 47.1
Allah yakan bar miyagu su ci gaba, kuma su nuna magabtakar su da Shi, domin sa’anda sun cika ma’aunin zunubinsu, kowa zai ga adalcinsa da jinkansa, yayin da ake hallaka su. Ranar ramuwarsa tana gagabtowa, sa’anda dukan masu-ketare dokarsa da masu wulakanta mutanensa za su gamu da sakamakon ayukansu; sa’an da kowace mugunta ko rashin adalcin da aka yi ma amintattun Allah zai sami sakamakonsa, sai ka ce Kristi ne da kansa aka yi masa muguntar. BJ 47.2
Akwai kuma wata muhummiyar tambaya da ya kamata ta ja hankalin ekklesiyoyi yau. Manzo Bukus ya ce: “Dukan wadanda su ke so su yi rai mai-ibada chikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” Timothawus II, 3:12. Idan haka ne, don me tsanani ya yi sanyi yanzu? Dalilin kadai shi ne cewa ekklesiya ta rungumi kaidar duniya, sabo da haka kuma ba ta tayar da sabani. Addinin zamanin mu yau ba irin mai-tsabta da tsarkin nan ne na zamanin Kristi da manzaninsa ba. Sabo da ruhun gama-hunnu da zunubi ne, domin an yi wasa da muhimman gaskiyan maganar Allah, don akwai karancin ainihin ibada a cikin ekklesiya, shi ya sa Kiristanci ke da farin jini a duniya. Bari a falkas da irin bangaskiya da ikon nan na ekklesiyar farko, za a kuwa ta da ruhun tsanantawa, za a kuma sake kunna wutar tsanani. BJ 47.3