Manzo Bulus cikin wasikar sa zuwa ga Tassalunikawa, ya ce za a yi babbar riddar da za ta kai ga kafawar mulikn paparuma. Ya ce rana ta Kristi ba za ta zo ba, “sai riddan ta fara zuwa, mutumen zunubi kuma ya bayanu, dan hallaka, shi wanda yana tsayayya, yana kwa daukaka kansa gaba da dukan abin da ake yi masa sujada, har yana zamne chikin haikalin Allah, yana shelar kansa shi Allah ne.” Biye da wannan kuma, manzon ya gargadi yan-uwan sa cewa “asiri na taka shari’a yana ta aikawa ko yanzu.” Tassalunikawa II, 2:3,4,7. BJ 48.1
Kadan da kadan dai, a sace, daga baya kuma har a bayane, bayan ya kara karfi har ya mallaki zukatan mutane, “asiri na taka shari’an” ya ci gaba da aikin sa na sabo. A hankali dai har al’adun kafirai ya kawo sassauci ga ruhun saka-saka. Amma da zaran tsanantawa ya tsaya, sarakuna da fadawan su kuma suka fara shigowa addinin Kiristanci, sai ekklesiya ta watsar da tawali’un Kristi da manzanin sa, ta rungumi fadin rai da fahariyar priestoci da shugabannin kafirai, ekklesiya ta sauya sharuddan Allah da koyaswoyin mutane, da al’adun su kuma. Tuban karya da Constantine ya yi, ya jawo farinciki sosai; sai duniya, yafe da kamanin adalci, ta shiga cikin ekklesiya. Sai kuma lalacewa ya habaka. Kafirci da ake gani kamar an rigaya an murkushe shi kuma sai ya sami nasara. Ruhun kafirci ya mallaki ekklesiya. Aka shigo da koyaswoyin kafirci da al’adun sa cikin addini da sujadar wadanda ke kiran kan su masu-bin Kristi. BJ 48.2
Garwayewar kafirci da Kiristancin nan ya kai ga tasowar “mutumen zunubi” wanda annabi ya ce yana tsayayya, yana kuma daukaka kan sa gaba da Allah. Wannan addinin babban alama ce ta ikon Shaitan da kokarin sa na neman hawa kan kursiyin domin shi yi mulkin duniya yadda ya ke so. BJ 49.1
Shaitan ya taba so ya gama hannu da Kristi. Ya zo wurin Dan Allah a jeji inda ya jarabce Shi, sai ya nuna masa dukan mulkokin duniya da darajar su, sa’an nan ya ce zai ba da dukan su a hannun Kristi idan har Ya amince da fifikon sarkin duhu. Kristi Ya tsauta ma majarabcin, Ya kuma tilasta masa gudu daga wurin. Amma Shaitan yana yin nasara sa’anda yake jarabtar mutum da abu dayan. Don samun riba da girma na duniya aka sa ekklesiya ta nemi goyon bayan manyan mutane na duniya kuma da shike ta musunci Kristi hakanan, aka rude ta har ta yarda da shugabancin wakilin Shaitan, watau bishop na Rum. BJ 49.2
Wata koyaswar Rum ita ce cewa wai paparuma ne shugaban ekklesiyar Kristi cikin dukan duniya, wanda ake gani, kuma wai an ba shi iko bisa bishop- bishop da pastoci da ke ko ina a duniya. Fiye da haka ma wai an ba paparuma lakabi irin na Allantaka. Ana ce da shi “Ubangiji Allah Paparuma,” an kuma ce shi mara-kuskure ne. Yana bidar ban girma daga kowane mutum. Abin da Shaitan ya bida inda ya jarabci Yesu, shi ne paparuma ke bida ta wurin ekklesiya Rum, kuma dimbin mutane suna shirye su ba shi girman. BJ 49.3
Amma masu tsoron Allah suna amsa wannan renin yadda Kristi Ya amsa ma magabcin ne: “Ka yi sujada ga Ubangiji Allahnka, shi kadai kuma za ka bauta masa” Luka 4:8. Allah bai taba cewa Ya nada wani mutum ya zama kan ekklesiya ba. Amma Koyaswar fifikon paparuma ta saba ma koyaswar Littafi. Paparuma ba zai taba samun iko bisa ekklesiyar Kristi ba, sai dai ta wurin kwace. BJ 50.1
Ekklesiyar Rum tana zargin sauran ekklesiyoyi da laifin ridda, cewa sun baude daga ekklesiya ta gaskiyar. Amma su Katolikawa ne suka yi wannan laifin. Su suka saukar da tutar Kristi, suka rabu da “bangaskiya wadda aka taba ba tsarkakan.” Yahuda 3. BJ 50.2
Shaitan ya sani sarai cewa Littafi zai sa mutane su gane rudinsa, su kuma fi karfin ikonsa. Ta wurin wannan ne Mai-ceton duniya ma Ya yi nasara da shi. Ga kowane hari, Kristi Ya yi anfani da garkuwa ta gaskiya, cewa, “An rubuta.” Idan har Shaitan zai tabbatar da ikon sa a kan mutane ya kuma tabbatar da ikon paparuma, dole sai ya hana mutanen sanin Littafi. Littafi yakan daukaka Allah ya kuma sa mutane daidai matsayin su; shi ya sa dole Shaitan ya danne ya kuma boye gaskiyar Littafin. Matakin da ekklesiyar Rum ta dauka ke nan. An hana yaduwar Littafi har tsawon daruruwan shekaru. Aka kuma hana mutane karanta shi ko ajiye shi a gidajensu ma, priestoci kuma suka rika fassara Littafi ta yadda zai tabbatar da rudinsu. Ta haka aka sa kusan ko ina aka dauka cewa paparuma ne wakilin Allah a duniya, mai-iko bisa ekklesiya da kasa. BJ 50.3
Da shi ke an kau da mai-gano kuskure, Shaitan ya yi abin da ya ga dama. Annabci ya ce mulkin paparuma “za ya nufa ya sake zamanu da shari’a kuma.” Daniel 7:25. Domin samo ma tubabbu daga kafirci wani abu a madadin bautar gumaka, ta haka kuma a karfafa jabun Kiristancin nan nasu, sai aka shigo da girmamawar sifofi cikin sujadar Kirista a hankali, a hankali. Daga baya wani kudurin majalisa ya tabbatar da wannan bautar gumakar. Don kalmasa wannan batancin, Rum ta yi yunkurin cire doka ta biyu daga dokokin Allah, ta kuma raba doka ta goma kashi biyu domin dokokin su cika goma. BJ 50.4
Ruhun daidaitawa da kafirci ya bude hanya domin a kara rena ikon Allah. Shaitan, ta wurin lalatattun shugabannin ekklesiya, ya taba doka ta hudu kuma, ya kuma yi kokarin watsar da Assabbat din, ranar da Allah Ya albarkace ta Ya kuma tsarkake ta (Farawa 2:2,3), a maimakon ta kuma ya so ya girmama bukin da kafirai ke yi, wai bukin babban ranar rana. Da farko dai ba a bayyane aka so a yi canjin ba. A karni na fari dukan Kirista sun kiyaye Assabbat ne. Sun girmama Allah, suna kuma gaskata cewa dokar sa ba mai-sakewa ba ce; suka rika kare kaidodinta. Amma sannu a hankali, Shaitan ya yi aiki ta wurin wakilan sa don cim ma manufar sa. Domin a jawo hankulan mutane zuwa Lahadi, sai aka mai da shi bukin tunawa da tashin Kristi daga matattu. Aka rika hidimomin ibada a ranar; duk da haka an mai da ita ranar shakatawa ce, yayin da ake kiyaye Assabbat. Domin shirya hanya don aikin da ya shirya yi, Shaitan ya sa Yahudawa kafin zuwan Kristi, su jibga ma Assabbat nauyin bukatu masu-yawa ta yadda kiyaye shi ya zama abu mai-wuya. Bayan wannan sai yanzu kuma ya bata mata suna, wai ranar yahudawa ce. Yayin da yawancin Kirista suka ci gaba da kiyaye Lahadi a matsayin bukin farin ciki, sai Shaitan ya sa suka mai da Assabbat ranar azumi, ranar bakin ciki, domin mutane su nuna kiyayyar su ga Yahudanci. BJ 51.1
A farkon karni na hudu, sarki Constantine ya ba da umurnin da ya mai da Lahadi ranar buki ta dukan kasar Rum. Kafiran kasar sa suka tsarkake ranar ranan, Kirista kuma suka girmama ta; nufin sarkin ne ya hada kan kafirci da Kiristanci. Bishop bishop na ekklesiya ne kuwa suka shawarce shi ya yi hakanan, wadanda sabo da dogon buri da neman mulki suka ga cewa, idan kafirai da Kirista suna kiyaye rana daya, wannan zai kara sa kafirai su karbi Kiristanci da suna kawai, ta haka kuma ikon ekklesiya da darajar ta za su karu. Amma yayin da aka sa wadansu Kirista masu- tsoron Allah suka fara ji kamar Lahadi yana da tsarki kadan, duk da haka suka rike ainihin Assabbat a matsayin sa na mai-tsarki na Ubangiji, suka kiyaye shi kuma bisa ga doka ta hudu. BJ 52.1
Mai-rudin bai kamala aikin sa ba dai. Ya kudura tattara Kiristan duniya kalkashin mulkin sa, ya kuma yi mulki ta wurin wakilan sa, paparuma, wanda ya ce shi ne wakilin Kristi. Ta wurin kafirai masu-rabin tuba da shugabannin addini masu-dogon buri, da kuma masu bi da ke kaunar duniya, ya cim ma manufar sa. An rika taronin majalisu loto loto, inda manyan shugabannin ekklesiya daga dukan duniya sukan taru. A kusan kowane taro akan kara danne Assabbat da Allah Ya kafa, yayin da ake kara daukaka Lahadi. Ta haka aka karfafa bukin kafirai a matsayin rana ta Allah, Assabbat na Littafi kuma aka ce da shi al’adar Yahudanci, masu kiyaye shi kuma aka ce la’antattu ne. BJ 52.2
Babban mai-riddan ya daukaka kan sa “gaba da dukan abin da ake ce da shi Allah, ko abin da ake yi masa sujada.” Tassalunikawa II, 2:4. Ya yi yunkurin canza dokar Allah da ke nuna ma dukan yan Adam Allahn gaskiya Mai-rai. Cikin doka ta hudu an bayana Allah a matsayin Mahalicin sammai da duniya, ta haka kuma aka bambanta shi daga dukan allolin karya. A matsayin abin tunawa da halitta ne aka tsarkake rana ta bakwai ta zama ranar hutu. An shirya ta ne ta rika tuna ma mutane cewa Allah ne tushen rayuwa wanda kuma za a yi masa sujada da bangirma. Shaitan yana kokarin juyo mutane daga biyayya ga Allah da dokar Sa; sabo da haka yana mai da hankalinsa ga yin sabani da dokan da ke nuna Allah a matsayin Sa na Mahalici. BJ 52.3
Kiristan da suka ki ikon paparuma yanzu suna cewa tashin Kristi ran Lahadi ne ya mai da Lahadin Assabbat. Amma babu nassin da ya ce haka. Kristi ko manzanin basu ba ranan wannan darajar ba. Kiyaye Lahadi ga Kirista yana da tushe daga “asiri na taka shari’an” ne (Tassaluniawa II, 2:7) wanda ko a zamanin Bulus ma ya rigaya ya fara aikin sa. Ina ne, kuma yaushe ne Ubangiji Ya yarda da wannan kage na paparuma? Wane kyakyawan dalili za a bayar don canjin da Littafi bai goyi bayan sa ba? BJ 53.1
Cikin karni na shida, paparuma ya rigaya ya kafu sosai. Rum ne cibiyar mulkin sa, aka kuma ce bishop na Rum ne kan dukan ekklesiya. Kafirci ya ba paparuma wuri. Dragon ya ba bisan “ikonsa da kursiyinsa da hukumchi mai-girma.” Ruya 13:2. Yanzu ne kuma farkon shekaru 1260 na danniyar paparuma da aka yi annabci cikin litattafan Daniel 7:25; Ruya 13:5-7. Aka tilasta Kirista, ko su sadakar da amincin su su yarda da shugabancin paparuma, ko kuma su karasa rayuwar su cikin kurkuku ko kuma a kashe su. Lokacin ne maganar Yesu ta cika cewa: “Amma har da iyaye, da yan-uwa, da abokai za su bashe ku: a chikin ku kuma za su kashe wadansu. Za ku zama abin ki ga dukan mutane sabili da sunana.” Luka 21:16,17. Tsanantawa ta abko ma amintattu da muni fiye da duk wanda aka taba yi, duniya kuma ta zama babbar filin daga. An yi daruruwan shekaru ekklesiyar Allah tana fakewa a boye. In ji annabin: “Machen kwa ta gudu zuwa chikin jeji, inda Allah Ya rigaya Ya shirya mata wurin da za a yi mata kiwo a chan, kwana dubu da metin da satin.” Ruya 12:6. BJ 53.2
Hawan ekklesiyar Rum kan karagar mulki ne ya zama mafarin Zamanin Duhu. Sa’an da ikon ta ya karu, duhun yakan karu. Aka dauke bangaskiya ga Kristi aka mayar wurin paparuma. Maimakon dogara ga Dan Allah don gafarar zunubi da ceto na har abada, mutane suka dogara ga paparuma, da priestoci da ya zaba su wakilce shi. An koya masu cewa papruma ne matsakancin su a duniya, kuma wai ba mai zuwa wurin Allah sai ta wurin sa; kuma, wai shi yana matsayin Allah ne gare su sabo da haka dole a yi masa biyayya. Kauce ma umurnin sa yakan zama dalilin horo mai-tsanani kan jikuna da rayukan masu-laifin. Ta wurin wannan aka juya tunanin mutane daga Allah zuwa fadaddun mutane masu kuskure, masu mugunta, har zuwa wurin Shaitan kan sa wanda ya cika nufin sa ta wurin su. Aka boye zunubi cikin rigar adalci. Sa’an da an danne maganar Allah har mutum ya mai da kan sa madaukaki, ba abin da zai faru sai dai zamba da rudi da zunubi. Daukaka dokokin mutum da al’adun sa ya jawo rubewa da yakan faru sa’an da aka kawar da dokar Allah. BJ 54.1
Wadannan kwanaki ne na wahala ga ekklesiyar Kristi. Amintattu kalilan ne a lokacin. Akwai dai shaidu na gaskiya, amma wani lokaci kuskure da camfi sukan so su sami fifiko, addini na gaskiya kuma yakan kusan bacewa daga duniya. Ba a ganin bishara kuma a lokacin, amma addini na karya ya dinga yaduwa, aka rika damun mutane da wahaloli. BJ 54.2
An koya masu su dogara ga paparuma a matsayin matsakancin su, su kuma dogara ga ayukan su domin kafarar zunubi. Aka bukace su su rika tafiya mai-nisa, da ayukan neman gafara, da sujada ga tsofofi, da gina majami’u da wuraren hadaya, da biyan kurdade masu yawa a ekklesiya, wai domin a kawar da fushin Allah ko kuma a sami alherin Sa; sai ka ce Allah kamar mutane ne da zai fusata kan kananan ababa, ko kuma a kwantar Masa da zuciya ta wurin ayukan neman gafara! BJ 54.3
Ko da shi ke zunubi ya karu ko cikin shugabannin ekklesiyar Rum ma, duk da haka farin jinin ta ya rika karuwa. Kusan karshen karni na takwas, ekklesiyar Rum ta koyar da cewa wai a sararrakin farko na ekklesiya, bishop-bishop na Rum suna da ikon da suke manna ma kansu. Don tabbatar da hakan, dole a kirkiro wata hanya, uban karya kuwa ya nuna masu yadda za su yi. Shugabannin addini suka kirkiro rubuce rubucen karya. Aka fito da dokokin karya, wadanda ba a taba jin labarin su ba, duk da suna cewa wai paparuma ne madaukaki tun farkon zamanai. Ekklesiyar da ta ki gaskiya kuwa nan da nan ta yarda da wannan rudin. BJ 55.1
An zalunci amintattun maginan nan kan tushen gaskiyan (Korinthiyawa I, 3:10,11), aka kuma hana su aiki yayin da koyaswar karyan ke bata masu aiki. Kamar masu gini kan ganuwar Urushalima a zamanin Nehemiah, wadansu sun kasance a shirye su ce, “karfin masu daukan kaya ya lalace, ga kwa da kasa barkatai tuli; har da mun kasa gina ganuwa.” Nehemiah 4:10. Sabo da sun gaji da tsanani, da rudi da zunubi, da kowace matsala da Shaitan ya iya kawowa don hana ci gaban aikin su, wadansu amintattun magina suka yi sanyin gwiwa; kuma domin salama da zaman lafiya sabo da dukiyar su da rayukan su, suka kauce daga tushe na gaskiyan. Wadansu da basu damu da muguntar magabtan su ba suka ce: “Kada ku ji tsoronsu, ku tuna da Ubangiji wanda shi ke mai-girma, mai-ban razana.” Nehemiah 4:14; kuma suka ci gaba da aikin, kowa da takobinsa a maran sa. Afisawa 6:17. BJ 55.2
Ruhun nan na kiyayya da sabanin ne yakan motsa magabtan Allah kowace sara, kuma akan bukaci tsaro da aminci iri dayan daga bayin Sa. Jawaban Kristi ga almajiran farko sun shafi masu bin Sa na kowane lokaci har karshen lokaci. Ya ce: “Abin da ni ke che maku, ina che ma duka: ku yi tsaro.” Markus13:37. BJ 55.3
Duhun ya dinga karuwa. Bautar sifofi ta yadu. Aka dinga kunna wutar kyandir a gaban sifofi, ana addu’a gare su. Al’adu mafi-muni suka yawaita. Camfi ya mallaki zukatan mutane har ma suka kasa yin tunani da kyau. Sa’an da priestoci suka zama masu son nishadi da annishuwa da toshi, dole masu-bin kwatancin su su rude cikin jahilci da lalacewa. BJ 56.1
Wani matakin ci gaban paparuma kuma shi ne lokacin da paparuma Gregory VII ya yi shelar rashin aibin ekklesiyar Rum. Ya ce ekklesiyar bata taba kuskure ba, kuma ba za ta taba yi ba, bisa ga Littafi, in ji shi. Amma ba a ambaci inda Littafin ya ce haka ba. Paparuman ya kuma ce yana da iko ya saukar da sarakuna, kuma ba wanda ya isa ya warware duk wani umurnin da shi ya bayar, amma shi yana da iko ya warware umurnin sauran mutane. BJ 56.2
Misalin ha’incin wannan paparuman shi ne abin da ya yi ma sarkin Jamus, Henry IV. Ya ware sarkin daga ekklesiya, sa’annan ya sauke shi daga saurautar. Don tsoron barazanar yarimomin sa, Henry ya ga wajibi ne ya nemi sulhu da Rum. Tare da matar sa da wani aminin sa, Henry ya ketare tsaunukan Alps da tsakar rani lokacin matukar sanyi, domin shi kaskantar da kan sa a gaban paparuma. Sa’an da ya haura dakin da Gregory yake hutawa, sai aka kai shi wani zaure, ba tare da dogarawan sa ba, nan ne fa, cikin sanyin rani, ba hula ko takalmi, kuma sanye da riga mara kauri, ya jira izinin ganin paparuma. Sai da ya cika kwana uku yana azumi da tuba kafin paparuma ya yafe masa. Duk da haka ma sai da ya jira izinin paparuma kafin ya koma sarautar sa. Gregory kuma ya rika fariya cewa yana da ikon ladabtar da girman kan sarakuna. BJ 56.3
A fili, ga bambanci tsakanin girman kan paparuma da tawali’un Kristi wanda ke roko a kofar zuciya domin a ba Shi damar shiga domin ya ba da gafara da salama, wanda kuma Ya koya ma almajiran Sa cewa: “Kuma dukan wanda yake so ya zama na fari a chikinku, bawanku za ya zama.” Matta 20:27. BJ 57.1
Sararraki na biye an rika samun karin kurakuran koyaswa daga Rum. Tun kafin kafuwar mulkin paparuma ma, koyaswoyin kafiran masana sun sami tasiri cikin ekklesiya. Da yawa da suka ce sun tuba, sun ci gaba da kaidodin kafircin su, suka kuma koya ma wadansu, domin su kara tasirin su a cikin kafirai. Ta haka aka shigar da munanan kurakurai cikin addinin Kirista. Daya daga cikin su ita ce koyaswar cewa wai mutum ba ya mutuwa, kuma matacce ma ya san abin da ke faruwa. A kan wannan koyaswan ne Rum ta kafa al’adar ta na rokon tsarkaka da kuma daukaka ga Maramu. Daga nan ne ma koyaswan nan ta azabtarwa har abada ga marasa tuba ta taso. BJ 57.2
Sa’an nan kuma aka shirya hanya don wata koyaswar kafirci kuma wadda Rum ta ba shi suna purgatory, wadda ake anfani da ita don razana jama’a. Ta wurin wannan koyaswa ana cewa wai akwai wani wurin azaba inda wadanda basu cancanci wuta a lahira har abada ba za su sha horo don zunuban su, daga nan kuma, bayan an tsarkake su, sai a shigar da su sama. BJ 57.3
An kuma kirkiro wata koyaswar domin Rum ta yi riba daga tsoro da laifukan masu bin ta. Akan yi ma dukan wadanda suka yi ma paparuma yake-yaken sa na neman fadada mulikinsa, ko horon magabtansa, ko hallaka masu-musun daukakarsa, alkawalin gafarar zunubansu na da da na yanzu da na nan gaba. Aka kuma koyar da cewa ta wurin biya ma ekklesiya kurdi, za su ceci kansu daga zunubi, su kuma kubutar da rayukan matattun abokan su da ke fama cikin azabar wuta. Ta wannan hanya ma Rum ta cika baitulmalinta, ta kuma iya biyan bukatun ma’aikatan ta da anishuwan su. BJ 58.1
An kuma sauya jibin Ubangiji da wata hadaya da ake ce da ita mass. Priestocin ekklesiyar katolika sun rika cewa wai ta wurin al’adar su ta mass, sukan juya gurasa da rowan anab su zama ainihin jikin Yesu da jinin Sa. Da sabo, cike da rashi kunya, suka yi ikirarin cewa suna da iko su halici Allah, Mahalicin komi. Aka bukaci Kirista, a bakin ran su, su rantse cewa sun ba da gaskiya ga koyaswan nan na ridda. Dimbin mutane da suka ki kuwa, an kone su da wuta. BJ 58.2
A karni na goma sha uku, an kafa wani Bincike, wani tsari mafi-muni cikin dukan dabarun ekklesiyar Rum. Shaitan ya hada hannu da shugabannin ekklesiyar Rum. A majalisar su, Shaitan da malaikun sa suka mallaki tunanin miyagun mutane, a tsakanin su kuwa malaikan Allah, wanda ba su gan shi ba, ya dinga rubuta kudurorinsu, yana kuma rubuta tarihin ayukansu da idon mutum ba zai so ya gani ba. “Babila babba” kuma “tana maye da jinin tsarkaka.” Guntayen gababuwan miliyoyin mutanen da aka kashe sun dinga kai kara wurin Allah domin ramuwa kan Rum. BJ 58.3
Mulkin paparuma ya zama azalumin duniya. Sarakunan duniya kanana da manya suka rika biyayya ga dokokinsa. Ya zama kamar kadarar mutane a duniya, ko dawama ma, tana hannunsa ne. An yi daruruwan shekaru ana amincewa da dokokin Rum, ana bin al’adun ta, ana kuma yin bukukuwan ta. An rika darajanta priestocin ta, ana biyan bukatun su a yalwace. Ekkelesiyar Rum ba ta taba samun maraba, ko ban sha’awa ko iko irin na wannan lokacin ba. BJ 59.1
Amma “tsakar ranar paparuma tsakar daren duniya ne.” Kusan ma da mutane da priestoci kan su basu san Littafi ba. Kamar Farisawa na da, shaugabannin ekklesiyar paparuma suka ki jinin hasken da kan bayana zunuban su. Da shike an cire dokar Allah wanda shi ne ma’aunin adalci, suka yi mulki ba kadada, suna aikata mugunta ba sassauci. Zamba da handama da fasikanci suka dawama. Mutane basu damu su yi kowane laifi ma ba don dai su sami arziki ko matsayi. Fadar paparuma da ta kowane priest suka zama cibiyoyin shaye shaye. Wadansu paparuma-paparuma suka aikata laifukan da har shugabanni na duniya ma suka so su saukar da su sabo da munin laifukan nasu. An yi daruruwan shekaru Turai bai sami ci gaban ilimi ko wayewa ba. Kiristanci kuma ya sami nakasa na tarbiyya da na bishara. BJ 59.2
Yanayin duniya a zamanin ikon Rum ya zama abin tsoro wanda ya cika maganar annabi Hosea daidai cewa: “Mutane na sun lalace domin rashin ilimi: tun da ka ki ilimi ni ma za ki ka.... tun da ka manta da shari’ar Allahnka, ni kuma zan manta da yayanka.” “Babu gaskiya, ko jinkai, ko sanin Allah a kasar. Babu komi sai rantsuwa da cin amana, da kisa da sata, da aikin zina. Sukan pasu, jini kuma yana taba jini.” Hosea 4:6,1,2. BJ 59.3