Aikin Allah a duniya yana nuna kamani mai-yawa tsakanin manyan canje canje daga sara zuwa sara. Kaidodin dangantakar Allah da mutane ba sa sakewa. Muhimman al’amura na yanzu suna da makamantansu a tarihi, kuma abinda ya faru da ekklesiya a zamanun baya yana da darussa masu tarin anfani ga lokacinmu. BJ 341.1
Babu gaskiyan da Littafin ya fi koyarwa a sarari kamar cewa Allah ta wurin Ruhunsa Mai-tsarki musamman yana bi da bayinsa a duniya cikin manyan canje canje da kan kawo ci gaban aikin ceto. Mutane kayan aiki ne a hannun Allah da yake anfani da su don cim ma manufofinsa na alheri da jin kai. Kowa yana da abin da zai yi, an ba kowa haske daidai da bukatun lokacinsa, isashe kuma don yin aikin da Allah Ya ba shi. Amma ba mutumin da komi darajan da Allah Ya ba shi, ya taba samun cikakkiyar ganewar babban shirin nan na ceto, ko ma cikakkiyar fahimtar manufar Allah game da aikin don zamaninsa. Mutane ba sa samun cikakken ganewar abin da Allah zai yi tawurin aikin da yake ba su, ba sa fahimtar dukan fannonin sakon da suke furtawa cikin sunansa. BJ 341.2
“Ka iya binchike har ka tone al’amura na Allah? Ka iya binchiken mai-iko duka sosai?” “Gama tunanina ba tunaninku ba ne, al’amuranku kuma ba al’amurana ba ne.” “Ni ne Allah kuma babu wani mai-kama da ni, mai-bayyana karshe tun daga mafarin, tun zamanin da kuma, al’amuran da ba a rigaya an aika ba tukuna.” Ayuba 11:7; Ishaya 55:8-9; 46:9-10. BJ 341.3
Ko annabawan da ana basu hasken Ruhu na musamman ma basu sami cikakkiyar fahimtar ma’anar ruyan da aka ba su ba. Akan dinga bayana ma’anan daga sara zuwa sara ne daidai da yadda mutanen Allah ke bukatar sakon da ke ciki. BJ 342.1
Game da ceton da aka bayana tawurin bishara, Bitrus ya rubuta cewa; “annabawan da suka yi annabcin alheri wanda ke zuwa a gareku suka yi bidassa, suka bincike kuma da himma; suna nema su sani ko wane loto ne ko kwa irin loto Ruhun Kristi da ke chikinsu yana nuna, sa’anda ya shaida a gaba ra’adai na Kristi, da daraja da za ta bi bayan su. Su kwa aka bayana masu, ba kansu ba ne, amma ku ne suka hidimta maku wadannan abu.” 1Bitrus 1:10-12. BJ 342.2
Amma ko dashike ba a ba annabawa cikakkiyar ganewar ababan da aka bayana masu ba, sun yi kokarin samun dukan hasken da Allah ya ga daman bayyanawa. Sun tambaya, suka bincika da himma, suna neman sanin lokaci da irin lokacin da Ruhun Kristi da ke cikinsu ya bayyana. Wannan darasi ne ga mutanen Allah a zamanin Kiristanci wadanda don anfaninsu aka ba bayinsa annabce annabcen nan. Ba ga wadanda aka bayana masu suka yi anfani ba, amma gare mu suka yi anfanin. Lura da tsarkakan nan na Allah yayin da suka yi bincike suka nema da himma game da ruyai da aka ba su daga sararakin da ba a rigaya an haifa ba. Gwada himmarsu da halin kyaliya da kamnatattu na sararakin baya suka rike kyautar Allah da shi. Wannan tsautawa ce ga kiwuya da kyaliyan da ake yi, ana wani cewa ba za a iya fahimtar annabce annabcen ba! BJ 342.3
Ko da shike tunanin mutane basu isa su san tunanin Allah ko su gane yadda manufofinsa ke aiki ba, duk da haka sau da yawa sabo da wani kuskure ko kyaliyarsu ne ba sa fahimtar sakonin Allah. Sau da yawa ra’ayoyin mutane da al’adu da koyaswoyin karya na yan Adam sukan makantar da tunanin mutane ta yadda da kadan kawai suke fahimtar muhimman ababan da Ya bayana cikin maganarsa. Haka ya kasance game da almajiran Kristi, har lokacin da mai-ceton ke tare da su ta jiki ma. Zukatansu sun shaku da zancen da mutane ko ina suka dauka cewa Masiyan dan sarki ne na duniya wanda zai daukaka Israila zuwa gadon sarautar mulkin dukan duniya, basu iya gane ma’anar maganarsa da ya yi annabcin wahalolinsa da mutuwarsa ba. BJ 342.4
Kristi kansa ya rigaya ya aika da sako, “Zamanin Allah ya chika, mulkin Allah kwa yana nan: ku tuba ku ba da gaskiya ga bisharan.” Markus 1:15. Sakon nan daga annabcin Daniel 9 ne. Malaikan ya ce bakwai sattin da tara din za su kai har zuwa loton “Masiya sarki,” kuma da bege mai yawa almajiran suka yi jiran kafawar mulkin Masiyan a Urushalima domin shi yi mulkin dukan duniya. Sun yi wa’azin sakon da Kristi ya dauka masu, ko da shike su kansu basu fahimci ma’anar sa daidai ba. Yayin da ginshikin sanarwar su Daniel 9 ne, basu ga cewa aya ta biye ta nuna cewa za a datse Masiyan ba. Tun haifuwarsu tunanin su yana kan wata daukaka ta mulki na duniya, wannan kuwa ya rufe tunaninsu daga kalmomin annabcin da kalmomin Kristi ma. BJ 343.1
Sun cika aikinsu na mika ma al’ummar Yahudawa gaiyatar jinkai, sa’an nan, daidai lokacin da suka zata za su ga Ubangijinsu Ya hau gadon sarautar Dauda, suka ga an cafke Shi kamar mai-laifi, aka masa bulala, aka wulakanta Shi, aka hukumta Shi, aka kuma daga Shi a akan giciyen kalfari. Sanyin gwiwa da bakinciki kwarai suka cika zukatan almajiran duk sa’anda Ubangijinsu ke kwance cikin kabarin! BJ 343.2
Kristi ya zo daidai lokaci, kuma daidai yadda annabci ya ce. Kowane fannin aikinsa ya cika shaidar Littafin. Ya yi shelar sakon ceto, kuma Kalmarsa cike da iko ne. Zukatan masu jinsa sun shaida cewa sakonsa daga sama ne. Kalmar da Ruhun Allah sun shaida cewa sakon Dan daga Allah ne. BJ 344.1
Almajiran sun ci gaba da kaunarsu ga maigidansu. Amma duk da haka tunaninsu ya cika da rashin tabbaci. Cikin bakincikinsu basu tuna maganar Yesu da ta nuna cewa zai wahala Ya kuma mutu ba. Da Yesu Ba-nazarat ne ainihin Masiyan, da an sa su cikin bakinciki da cizon yatsa, tamboyoyin da suka dinga damunsu ke nan yayin da Mai-ceton ke kwance cikin kabarinsa, ran Assabat din nan tsakanin mutuwarsa da tashinsa. BJ 344.2
Ko da shike daren bakinciki ya cika masu bin Yesu din nan, duk da haka ba a rabu da su ba. In ji annabin: “Sa’anda na zamna a chikin dufum Ubangiji za ya zama haske a gareni… za ya fito da ni wajen haske, zan kwa duba adilchinsa.” “Ko dufu ma ba dufu ne gareka ba, amma dare yana haskakawa kamar rana; da dufu da haske gare ka duk daya ne.” Allah Ya ce: “Haske yana fitowa chikin dufu akan masu gaskiya.” “Zan kuma jawo makafi ta hanyar da basu sani ba, tafarkun da basu sani ba in bishe su; in mai da dufu haske a gabansu; karkatattun wurare kuma su zama sosai. Wadannnan abu zan yi, ba ni kwa bari ba.” Mikah 7:8,9; Zabuara 139:12; 112:4; Ishaya 42:4. BJ 344.3
Sanarwa da almajiran suka yi cikin sunan Ubangiji daidai ne ta kowace fuska, kuma al’amuran da ta nuna suna faruwa a lokacin ma. “Lokaci ya yi kuma mulkin Allah ya yi kusa,” shine sakon su. Da cikar bakwai sittin da tara na Daniel 9 din nan, da suka kai har ga Masiyan “Shafaffen, Kristi ke nan, Ya karbi shafewar Ruhu Mai-tsarki bayan baptismar da Yohanna ya yi masa a Urdun. Kuma “mulkin Allah” da suka ce ya kusa ya kafu ta wurin mutuwar Kristi. Mulkin nan ba na duniya ba ne yadda aka koya masu. Kuma ba mulkin nan mai-zuwa na har abada da za a kafa sa’anda “za a ba da sarauta da mulkin, da girman mulkokin da ke kalkashin sama, duka ga mutanen tsarkakan madaukaki” ba, ma mulkin nan na har abada inda “dukan mulkoki kuma za su bauta masa su yi biyayya da shi.” Daniel 7:27. Bisa ga Littafin, “mulkin Allah shi ne mulkin alheri da mulkin daukaka kuma. Bulus ya yi zancen mulkin alheri cikin wasika ga Ibraniyawa, bayan ya bayana Kristi, Matsakanci nan mai-tausayi da ke “tabuwa da tarayyar kumamancin mu.” Manzon ya ce: “Bari mu gusa fa gaba gadi zuwa kursiyi na alheri, domin mu karbi jin kai mu sami alheri.” Ibraniyawa 4:15,16. Kursiyin alheri yana nufin mulkin alheri ne, da shike kasancewar kursiyi yana nuna kasancewar mulki ne. Cikin misalansa da yawa Kristi Ya yi anfani da kalamin nan “mulkin sama” don bayana aikin alherin Allah kan zukatan mutane. BJ 344.4
Saboda haka kursiyin daraja shi ne mulkin daukaka, kuma mai ceto ya ambaci mulkin nan, cewa: “Amma saboda Dan mutum za ya zo chikin darajassa, da dukan malaiku tare da shi, sa’anan za ya zamna bisa kursiyin darajassa; a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai.” Matta 25:31,32. Mulkin nan na nan gaba ne. Ba za a kafa shi ba sai zuwan Yesu na biyu. BJ 345.1
An kafa mulkin alheri nan da nan bayan faduwar mutum. Lokacin da aka tsara shirin fansar ‘yan Adam. Ya kasance cikin shirin Allah tawurin alkawalinsa kuma, tawurin bangaskiya kuwa za a iya zama talakawansa. Amma ba a ainihin kafa shi ba sai da Yesu Ya mutu. Ko bayan shigarsa hidimarsa ta duniya Mai-ceton, saboda Ya gaji da taurin kai da rashin godiyan mutane, da Ya ga dama da Ya fasa hadayarsa ta Kalfarin. A Gethsemani, kokon wahalar ta raunana a hannunsa. A lokacin da Ya share zufan goshinsa, ya bar masu zunubi su hallaka cikin zunubinsu. Da Ya yi haka, da babu ceto domin fadaddun mutane. Amma sa’anda Mai-ceton ya bada ransa, ya kuma ce, “an gama,” lokacin ne aka tabbatar da cikar shirin fansa. An hakikance alkawalin ceto da aka yi ma Adamu da Hauwa’u masu zunubi a Adnin ke nan. Mulkin alheri, wanda ya kasance tawurin alkawalin Allah ne, ya kafu a lokacin. BJ 345.2
Ta hakanan mutawar Kristi, wadda almajiran suka dauka cewa ta murkushe begensu, ita ce ta tabbatar da bege har abada, ko da shike ta jawo masu sanyin gwiwa, ita ce makurar tabbacin cewa bangaskiyarsu daidai ne. Al’amarin da ya cika su da makoki da cizon yatsa, shi ne ya bude kofar bege ga kowane dan Adam, cibiyar rayuwa nan gaba da farinciki mara matuka na dukan amintattun Allah na dukan sararraki. BJ 346.1
Manufofin jin kai mara matuka sun rika cika, ko tawurin yankan burin almajaran ma, ko da shike alherin Allah da karfin koyaswar Kristi sun ribato zukatansu, duk da haka, garwaye da kaunarsu ga Yesu akwai girman kai da buri na son kai. Ko a zauren paskan, sa’an nan da mai-gidansu ya rigaya ya fara sunsuna giciyewarsa “makagara kuma ta tashi a tsakaninsu, ko wane ne ake maishe shi babba a chikin su.” Luka 22:24. Zukatansu suna cika da zancen rawani da kursiyi da daraja, alhali a gabansu ga kunya da azabar lambun Gethsamani, da dakin shari’a da giciyen kalfari. Girman kansu, da burin daraja ta duniya ne suka sa su manne ma koyaswar karya ta zamaninsu, suka kasa kula maganar Mai-cetonsu da ta nuna ainihin yanayin mulkinsa, da kuma radadinsa da mutuwarsa. Kurakuran nan kuma suka haifar da gwajin da aka bari ya faru domin yi masu gyara. Ko da shike almajiran sun yi kuskuren ma’anar sakonsu, suka kuma kasa cika begensu, duk da haka sun yi shelar gargadin da Allah ya ba su, Ubangiji kuma zai ba su ladar bangaskiyarsu ga dukan al’ummai. Domin shirya su don wannan aikin ne aka bari suka sha bakincikin nan. BJ 346.2
Bayan tashinsa, Yesu ya bayyana ga almajiransa a hanyar Imwasu, kuma “tun daga Musa da dukan annabawa, chikin dukan littattafai yana fasalta masu al’ammura na bisa kan sa.” Luka 24:27. Zukatan almajiran suka motsu. Bangaskiya ta taso. Suna sake samun bege mai rai, tun ma kafin Yesu Ya bayana kansa garesu. Nufinsa ne Ya ba su ganewa, Ya kuma kafa bangaskiyarsu ga tabbataciyar Kalmar annabci. Ya so gaskiya ta kafu da karfi cikin zukatansu, ba kawai don shaidarsa da kansa ba, amma domin tabbataciyar shaidar da dokar alamu da kamani da kuma annabce annabce na Tsohon Alkawali suka bayyana ne. Ya zama wajibi masu bin Kristi su sami bangaskiya mai basira ba domin kansu kadai ba, amma domin su kai ma duniya sanin Kristi. Kuma matakin farko don ba su wannan sanin shi ne cewa Yesu ya kai hankulan almajiran zuwa ga “Musa da dukan annabawa.” Shaidan da Mai-ceton ya bayar ke nan game da muhimmancin Tsohon Alkawali, bayan tashinsa daga matattu. BJ 347.1
An kawo sakewa sosai ga zukatan almajiran, sa’anda suka sake kallon fuskar Mai-gidansu! Luka 24:32. Ta hanya mafi inganci, sun same shi, wanda Musa cikin shari’ar da kama annabawa suka rubuta. Rashin tabbaci, da bacin rai, da cizon yatsa, sun kauce, tabbaci da bangaskiya suka shigo. Shi ya sa bayan komawarsa sama suka kasance cikin haikali kullum suna yabon Allah. Mutane, da shike mutuwarsa kadai suka sani, sun zata za su ga bakinciki da rudani a fuskokinsu, amma murna da nasara suka gani. Almajiran nan sun sami shiri sosai don aikin da ke gabsu. Sun rigaya sun wuce gwaji mafi tsanani, suka kuma ga yadda, sa’anda bisa ga ganin mutum, sun rasa komi, maganar Allah ta cika daidai. Daga nan, mene ne kuma zai rage bangaskiyarsu, ko kuma ya sa kaunarsu ta yi sanyi? Cikin tsananin bakin ciki, sun sami karfafawa sosai, “anchor na rai, tabbatachen bege mai-tsayawa.” Ibraniyawa 6:18,19. Sun rigaya sun shaida hikimar Allah da ikonsa, suka kuma “kawas da shakka ba mutuwa, ba rai, ba malaiku, ba sarautai, ba al’amuran yanzu, ba al’amura na zuwa, ba ikoki, ba tsawo, ba zurfi, ba kwa wani halitaccen abu, da za ya iya raba mu da kamnar Allah, wanda ke chikin Kristi Yesu Ubangijin mu.” Suka ce: “Cikin dukan wadannan al’amuran, mun fi gaban masu-nasara tawurin wanda ya kamnache mu.” Romawa 8:38,39, 37. “Amma maganar Ubangiji ta tabbata har abada.” 1 Bitrus 1:25. Kuma “wa za ya koyas? Kristi Yesu ne ya mutu, I kwa, har yatashi daga matattu, yana hannun dama na Allah, yana yin roko kuma sabili da mu.” Romawa 8:34. BJ 347.2
In ji Ubangiji, “Mutane na kuma ba za su kumyata ba dadai.” Joel 2:26. “Kuka ta na sabka da dare amma murna ta kan zo da safe.” Zabura 30:5. Sa’anda almajiran nan suka sadu da Mai-ceton a ranar tashinsa, zukatansu kuma suka kuna daga cikin su yayinda suke jin maganarsa, sa’anda suka kalli kai da hannaye da sawayen da aka kuje domin su; sa’anda, kafin hawan sa sama Yesu Ya kai su har Baitanya, Ya kuma daga hannuwansa sama Ya yi masu albarka, Ya ce masu “Ku tafi chikin duniya duka, ku yi wa’azin bishara,” Ya kuma kara da cewa: “Ga shi kwa ina tare da ku kulluyomi” (Markus 16:15; Matta 28:20), sa’anda a ranar Pentecost mai-taimakon da aka yi alkawalin sa Ya sauka aka kuma ba da iko daga sama, rayukan masu bada gaskiya kuma suka yi murna da sanin kasancewar Ubangijinsu da ya koma sama, sa’an nan ne su, ko da shike hanyarsu ta bi ta hanyar hadaya da mutuwa ma, sa’an nan ne da sun sauya hidimar bishara ta alherinsa da “rawanin adalci” da za a karba lokacin zuwansa, da daukakar kursiyi na duniya, wadda ita ce da begen almajirancinsu, Shi “wanda yake da iko shi aikata kwarai da gaske gaba da dukan abin da muke roko ko tsammani,” Ya rigaya Ya ba su murnar kawo ‘ya’ya da yawa wurin daraja, da murna mai-yawa da “nauyin daraja” wanda Bulus Ya ce “kunchinmu mai-sauki, wanda ke na lokaci kadan,” bai isa a gwada da shi ba. BJ 348.1
Dandanon almajiran da suka yi wa’azin “bishara ta mulkin” a zuwan Kristi na fari, ya sami na biyu dinsa a dandanon wadanda suka yi shelar zuwan sa na biyu. Kamar yadda almajiran suka yi wa’azi cewa: “zamani ya chika, mulkin Allah kwa yana nan,” haka ne Miller da abokansa suka yi shela cewa lokacin annabci mafi tasawo, kuma na karshe, da Littafin ya ambata ya kusan karewa, cewa hukumcin ya kusa, kuma za a shigo da mulki na har abada-din. Wa’azin almajiran game da lokaci ya danganci bakwai sab’in din nan na Daniel 9 ne. Sakon da Miller da abokansa suka bayar ya sanar da karewar shekara 2,300 na Daniel8:14 ne, wanda suka kunshi bakwai saba’in din. Kowane wa’azin ya shafi wani fanni dabam ne na annabci dayan. BJ 349.1
Kamar almajirai na farkon, William Miller da abokansa basu fahimci cikakkiyar ma’anar sakon da suka kai ba. Kurakurai da suka dade cikin ekklesiya sun hana su kaiwa ga kyakyawar fasarar wani muhimmin fannin annabcin. Saboda haka, ko dashike sun yi shelar sakon da Ubangiji Ya ba su su kai ma duniya, duk da haka tawurin rashin fahimtar ma’anarsa, suka sha yankan buri. BJ 349.2
Domin fassara Daniel 8:14, “Har yamma da safiya guda alfin da dari uku; kana za a tsarkake wuri mai-tsarki” Miller ya yi anfani da ra’ayin nan da ya fi karbuwa ne a zamanin, cewa duniya ce haikalin, ya kuma dauka cewa tsarkakewar hailakin shi ne tsarkakewar duniya da wuta lokacin zuwan Ubangiji. Saboda haka da ya gane karshen kwana 2,300 din sai ya dauka cewa lokacin zuwan Yesu na biyu ke nan. Kuskuren shi karban ra’ayin nan ne cewa duniya ce haikalin. BJ 350.1
Cikin tsarin kamani, wanda inuwar hadayar Yesu da priesthood na sa, tsarkakewar haikalin ne hidima ta karshe da babban priest yakan yi a hidimominsa na shekara. Shi ne aikin karshe na kafarar, watau cirewar zunubi daga Israila. Inuwa ce ta aikin karshe na hidimar Babban priest namu a sama, wajen sharewa ko cirewar zunuban mutanensa da aka rubuta a littattafai na sama. Wannan hidimar ta kunshi aikin bincike, aikin hukumci; kuma zai rigayi zuwan Kristi cikin gizagizai na sama da iko da kuma daraja mai yawa; gama zai zo bayan an rigaya an gama hukumcin ne. In ji Yesu: “Haki na yana tare da ni kuma, da zan saka ma kowane mutum gwalgwadon aikinsa.” Ruya 22:12. Wannan aikin hukumcin ne, gaf da zuwansa na biyu din. Sakon malaika na fari na Ruya 14:7 yana shelar cewa: “Kuji tsoron Allah, ku ba shi daraje, gama sa’ar hukumcinsa ta zo.” BJ 350.2
Wadanda suka yi shelar sakon nan sun ba da sakon da ya kamata a lokacin da ya kamata. Amma kamar yadda lamajiran farko suka fada, “lokacin ya cika, kuma mulkin Allah yana nan,” bisa ga annabcin Daniel 9, ba tare da fahimtar cewa an yi annabcin mutuwar Masiyan a nassi dayan ba, don haka Miller da abokansa sun ji wa’azin sakon bisa ga Daniel 8:14 da Ruya 14:7 ne, suka kuma kasa gane cewa akwai wadansu sakoni kuma cikin Ruya 14 din, da su ma za a ba da su kafin zuwan Ubangiji. Yadda almajiran suka yi kuskure game da mulkin da za a kafa a karshen bakwai saba’in din, haka Adventist suka yi kuskure game da al’amarin da zai auku a karshen kwana 2,300 din. A duk lokutan biyu, an rike kurakurai da yawancin mutane suka amince da su, kurakuran kuma suka boye gaskiyar daga tunaninsu. Dukansu sun cika nufin Allah wajen kai sakon da ya so su kai, kuma dukansu, ta wurin kuskuren fasarar sakonsu, suka sha yakan buri. BJ 350.3
Duk da haka, Allah Ya cimma manufarsa tawurin bari da Ya y i aka ba da gargadin yadda yake. Babbar ranar ta kusa, kuma cikin ikonsa, aka kawo mutanen wajen gwaji game da ainihin lokaci, domin a bayana masu abin da ke zukatansu. An shirya sakon domin gwadawa da tsarkakewar ekklesiyan ne. An kai su inda za su gane ko zukatan su na wurin wannan duniyan ne ko kuma wurin Kristi da sama. Sun ce suna kaunar Mai-cetonsu, yanzu kuma ya kamata su hakikance kaunar ta su, ko suna shirye su sadakar da begen su da burinsu na duniya, su kuma marabci zuwan Ubangijinsu da farin ciki? An shirya sakon domin su iya sansance ainihin yanayin ruhaniyarsu ne; an aiko da shi cikin jin kai ne domin a falkas da su, su nemi Ubangiji cikin tuba da tawali’u. BJ 351.1
Kuma, ko da shike yankan burin sakamakon rashin fahimtarsu ta sakon da suka bayar ne, an yi anfani da yankan burin ya zama alheri. Ya gwada zukatan wadanda suka ce sun karbi gargadin. Ko saboda yankin burinsu za su watsar da abin da suka sani, su yi watsi da amincewar su ga maganar Allah? Ko kumacikin addu’a da tawali’u, za su nemi gano inda suka yi kuskuren fahimtar muhimmancin annabcin ne? Nawa ne suka motsu sabo da tsoro, ko buri? Nawa ne masu zuciya biyu biyu da kuma rashin bangaskiya? Da yawa sun ce suna kaunar bayanuwar Ubangiji. Sa’anda aka bukace su su jimre ba’a da renin duniya, da gwaji da jinkiri da kuma yankan burin, ko za su musunci bangaskiyarsu? Da shike basu gane yadda Allah ke bi da su ba, ko za su kawas da gaskiyan shaidar maganarsa? BJ 351.2
Wannan gwajin zai bayyana karfin wadanda, da ainihin bagaskiya suka yi biyayya ga abinda suka gaskata cewa shi ne koyaswan Maganar Allah da Ruhunsa. Zai koya masu hatsarin karban ra’ayoyin mutane da fassararsu, maimakon barin Littafin ya fassara kansa. Ga masu bangaskiya rikicewa da bakin ciki da kuskurensu ya jawo zai kai ga gyaran da ake bukata. Za su kai ga Karin nazarin annabcin. Zai sa a koya masu su kara binciken harsashen bangaskiyarsu, kuma su ki duk wani abu, komi yawan Kiristan da suka yarda da shi, wanda ba shi da tushe a ainihin maganar Allah. BJ 352.1
Ga wadannan masu bangaskiyar, kamar almajirai na farkon, abin da a lokacin gwaji ya yi duhu, ga ganewarsu daga baya za a bayana shi a sarari. Sa’anda suka ga karshen komi, za su san cewa, duk da gwajinsu da kurakuransu suka haifar, manufofinsa dominsu suna cika a hankali. Za su gane tawurin dandano mai-albarka cewa Shi mai-tausayi na kwarai, Mai-jinkai kuma, cewa dukan tafarkunsa “rahama ne da gaskiya ga irin wadanda su ke masu kiyaye alkawalinsa da shaidunsa.” BJ 352.2