Cikin annabcin sakon malaika na fari na Ruya 14, an yi annabcin babban falkaswar addini kalkashin shelar kusantowar zuwan Kristi na biyu. An ga malaika yana firiya “a tsakiyar sararin sama, yana da bishara ta har abada wadda za ya yi shelatta ga mazamman duniya, ga kowane iri da kabila da harshe da al’umma.” “Da babban murya kwa” ya yi shelar sakon, cewa: “Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja; gama sa’ar hukunchinsa ta zo: ku yi sujada ga wanda ya yi sama da duniya da teku da mabulbulan ruwaye.” Ruya 14:6,7. BJ 353.1
Akwai muhimmanci game da cewa malaika ne mai-shelar gargadin nan. Ya gamshi Allah, ta wurin tsarki da daraja da karfin mai shelar sakon, ya bayana girman yanayin aikin da sakon zai aiwatar, da kuma iko da darajar da aikin zai kunsa. Kuma firiyar malaikan, “a tsakiyar sararin sama,” da babbar murya” da ake shelar gargadin da ita, da kuma shelar ta “ga mazamnan duniya”- “ga kowane iri da kabila, da harshe da al’umma - suna nuna sauri da kuma mamayewar duniya da aikin zai kunsa. BJ 353.2
Sakon kansa yana ba da haske game da lokacin da wannan aikin zai gudana. An ce shi wani sashi ne na “bishara ta har abada,” yana kuma shelar farawar hukumcin. An yi wa’azin sakon ceto a dukan sararaki; amma sakon nan wani sashi ne na bishara, wanda a kwanakin karshe ne kadai za a yi shelar sa, domin a lokacin ne kadai za a iya cewa sa’ar hukumcin ta zo. Annabce annabcen suna byayana al’amuran da za su kai ga farawar hukumcin, musamman ma littafin Daniel. Amma an bukaci Daniel ya kulle fannin nan na annabcinsa da ya shafi kwanakin karshe, ya kuma rufe shi da hatimi “har kwanakin karshe.” A wannan lokacin ne kadai za a iya shelar sako bisa ga cikawar annabce annabcen nan. Amma annabin ya ce, a lokacin karshen “mutane da yawa za su kai da kawo a guje, ilimi kuma za ya karu.” Daniel 12:4. BJ 353.3
Manzo Bulus ya gargadi ekklesiya kada ta yi zaton zuwan Kristi a zamaninsa. Ya ce: “Gama wannan sai riddan ta fara zuwa, mutumin zunubi kuma ya bayanu, dan hallaka,” kafin ranar ta zo. 11 Tassalunikawa 2:3. Sai bayan babban riddar, da lokacin nan mai-tsawo na mulkin “mutumin zunubi,” kafin mu fara neman zuwan Ubangijinmu. “Mutumen zunubin” wanda ake kuma ce da shi “kyamar lalata,” “dan hallaka,” mai-mugunta kuma, shi ne tsarin paparuma, wanda bisa ga annabci, zai yi mulkinsa har shekaru 1260. Wannan lokacin ya kare a 1798 ne. zuwan Kristi bai faru kafin lokacin ba. Gargadin Bulus ya kunshi har zuwa 1798. Bayan nan ne za a yi shelar sakon zuwan Kristi na biyu. BJ 354.1
Ba a taba ba da irin sakon nan a sararakin baya ba. Bulus bai yi wa’azinsa ba; ya kai hankulan yan’uwasa can gaba game da zuwan Ubangiji. Yan canji basu yi shelarsa ba. Martin Luther ya kai hukumcin har wajen shekara dari uku daga zamaninsa. Amma tun 1798 an bude littafin Daniel, sanin annabci ya karu, kuma da yawa sun yi shelar sakon nan na kusantowar hukuncin. BJ 354.2
Kamar abban Canjin nan na karni na sha shidda, wa’azin zuwan Kristi ya gudana a kasashen Kirista dabam dabam ne a lokaci daya. A Turai da Amerika, masu bangaskiya da addu’a sun yi nazarin annabcin, suka kuma sami shaida kwakwara cewa karshen kowane abu ya kusa. BJ 355.1
A 1821, shekara uku bayan Miller ya fassara annabcin da ya bayana lokacin hukuncin, Dr. Joseph Wolf ya fara shelar gagabtowar zuwan Ubangiji. An haifi Wolf a Jamus ne, Ba-yahudi ne, babansa kuma rabbi ne na Yahudawa. Yana dan saurayi ne ya karbi gaskiyar addinin Kirista. Yakan saurari hiran da akan yi a gidan babansa yayin da manyan Yahudawa ke magana game da bege da burin mutanensu, da darajar Masiya da ke zuwa da kuma mayaswar Israila. Wata rana da yaron ya ji an ambaci Yesu Ba-nazarat, sai ya tambaya ko wane ne shi. Aka amsa masa cewa “Wani Ba-yahudi ne mai-matukar baiwa, amma da shike ya yi da’awar cewa wai shi ne Masiyan sai hukumar Yahudawa ta masa hukumcin kisa.” Sai yaron ya tambaya, “Don me aka hallaka Urushalima, kuma don me muka zama kamammu?” Sai babansa ya amsa: “Domin Yahudawa sun kashe annabawa ne.” Nan da nan ya yi tunanin, “ko Yesun ma annabi ne, kuma Yahudawan suka kashe shi bai yi laifin komai ba?” Wannan tunanin ya yi karfi ta yadda ko da shike an hana shi shiga majami’ar Kirista, yakan rabe a waje, ya saurari wa’azin. BJ 355.2
Yana dan shekara bakwai kadai ya yi ma wani Kirista tsoho makwabcinsa fariyar nasarar Israila sa’anda Masiya zai zo, sai tsohon, a natse ya ce masa: “Ya kai yaro, zan fada maka ko wane ne ainihin Masiyan: shi ne Yesu Ba-nazarat, … wanda kakanin ka suka giciye, yadda suka yi da annabawa na da. Je gida ka karanta Ishaya 53, za ka kuwa gamsu cewa Yesu Kristi ne Dan Allah.” Ya kuwa je gida, ya karanta nassin, yana mamakin yadda ya acika dai dai kan Yesu Ba-nazarat. Ko maganar Kiristan nan gaskiya ce kam? Yaron ya tambayi babansa fasarar annabcin, amma irin shurun da aka masa ya sa bai sake magana a kan batun ba. Amma kuma wannan ya kara masa marmarin karin sani ne game da addinin Kirista. BJ 355.3
A gidan su na Yahudawa an hana shi sanin da ya bida, amma sa’anda yana dan shekara sha daya kacal ya bar gidan ubansa, ya shiga cikin duniya neman ilimi ma kansa, ya kuma zabi addininsa da aikin neman abin daman gari. Da farko ya zauna a gidan ya’uwa, amma nan da nan suka kore shi cewa mai-ridda ne, cikin talauci da kadaici kuwa dole ya yi rayuwarsa tare da baki. Ya rika zuwa wurare dabam dabam yana nazari, yana kuma koyar da Ibrananci don samun abin biyan bukata. Ta wurin wani mallaminsa dan Katolika, ya karbi addinin Romawa. Ya kuma dauki kudurin zama mai-wa’azi ga mutanensa, da wannan manufar, bayan yan shekaru, ya shiga neman iliminsa a “College of the Propaganda,” a Rum. A nan, halinsa na mai-fadin ra’ayinsa kai tsaye ya sa aka mai da shi mai bidi’a. A fili ya rika sokar kurakuran ekklesiya, yana kira cewa a yi gyara. Ko da shike da farko manyan ‘yan paparuma sun nuna masa soyayya ta musamman, daga baya an cire shi daga Rum, kalkashin kulawar ekklesiya ya rika zuwa wurare dabam dabam, har sai da ya bayana a fili cewa ba za su iya sa shi ya yarda da bautar tsarin Rum ba. BJ 356.1
Sai aka bayana cewa shi mara-gyaruwa ne, aka kuma ba shi dama ya je duk inda ya ga dama. Sai ya koma Ingila, ya rungumi Kin ikon paparuma, sa’an nan ya zama dan Ekklesiyar Ingila. Bayan makaranta na shekara biyu, ya fita a 1821, ya kama aikinsa. BJ 356.2
Yayin da Wolf ya karbi gaskiyar zuwan Kristi na farko a matsayin wanda “mai-bakinciki ne, ya saba da chiwuta,” ya ga cewa annabci ya bayana zuwansa na biyu da iko da daraja kuwa. Kuma yayin da ya yi kokarin jawo mutanensa wurin Yesu Ba-bazarat, cewa Shi ne wanda aka yi alkawali, da kuma nuna masu zuwansa na farko cikin kaskanci a matsayin hadaya don zunuban mutane, ya kuma koya masu game da zuwansa na biyu a matsayin sarki mai-kubutarwa. BJ 356.3
Ya ce: “Yesu Ba-nazarat, wanda aka soki hannuwansa da sawayensa, wanda aka kawo kamar dan rago zuwa mayanka, wanda Mai-bakinciki ne; ya saba da chiwuta, wanda bayan da an karbe sandar sarauta daga Yahuda, ikon doka kuma daga tsakanin sawayensa, ya zo da fari; zai zo na biyu a gizagizai na sama, da kafon malaiku kuma, zai kuma tsaya kan Dutsen Zaitun, kuma mulkin nan da aka ba Adamu bisa sauran halitta, ya kuma sallamar (Farawa 1:26; 3:17), za a ba Yesu. Za ya zama sarki bisa dukan duniya. Nishin halitta da makokinta za su dena, amma za a ji wakokin yabo da godiya,… Sa’an da Yesu zai zo cikin darajar Ubansa, da malaiku masu-tsarki, matattun da suka ba da gaskiya za su fara tashi. Tassalunikawa I, 4:16; Korrinthiyawa I, 15:32. Abinda Kirista ke kira tashin mattattu na farko ke nan. Sa’an nan al’ummar dabbobi za ta canja yanayinta (Ishaya 11:6-9), ta kuma koma kalkashin Yesu. Zabura 8. Salama za ta mamaye dukan halitta.” “Ubangiji, kuma zai sake duban duniya, Ya ce “Ga shi kwa, yana da kyau kwarai.” BJ 357.1
Wolf ya gaskata cewa zuwan Ubangjiji ya kusa, kuma bisa ga fasararsa ta annabcin wokatai, ya nuna cewa bambancin lokacin da shi ya zata Yesun zai dawo, da lokacin da Miller ya zata ‘yan shekaru kalilan ne kawai. Ga wadanda, bisa ga fadin Littafin cewa “Amma zanchen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani ba,” suna cewa bai kamata mutane su san komi game da kusantawar zuwan ba, Wolf ya amsa cewa: “Ubangijinmu Ya ce ba za a taba sanin rana ko sa’an ba ne? Ko bai ba mu alamun lokacin domin a kalla mu san kusantowar zuwansa, yadda akan san kusantowar bazara ta wurin zubawar ganyayen itacen baure ba? Matta 24:32. Ashe bai kamata mu taba sanin lokacin ba, alhali Shi kansa ya shawarce mu cewa mu karanta annabcin Daniel mu kuma gane shi? Kuma cikin Daniel din inda aka ce an kulle kalmomin har sai lokacin karshe, kuma da yawa za su kai da kawo (watau za su lura su kuma yi tunani game da lokacin), ‘ilimi kuma za ya karu’ (game da lokacin). Daniel 12:4. A nan, Ubangijinmu ba Ya nufin cewa ba za a san kusatowan lokacin ba, amma cewa daidai ranan da sa’ar ba wanda ya sani. Yana cewa ta wurin alamun wokatai za a sami isashen sanin da zai motsa mu mu shirya domin zuwansa, yadda Nuhu ya shirya jirgin. BJ 357.2
Game da yadda aka saba fassara annabci, Wolf ya rubuta cewa: “Yawancin ekklesiyar Kirista sun kauce daga bayananniyar ma’anar Littafin, suka koma tsari irin na ‘yan addinin Budhism, suka gaskata cewa farincikin ‘yan Adam nan gaba zai kunshi yawo ne a iska, suna kuma zato cewa duk inda aka ambaci Yahudawa ana nufin al’ummai ne, inda suka ga Urushalima kuma ekklesiya ke nan; idan kuma aka ambaci duniya, sama ke nan, sa’an nan zuwan Ubangiji ci gaban kungiyoyin masu-wa’azi ke nan; kuma hawa Dutsen gidan Ubangiji shi ne babban taro na Methodist.” BJ 358.1
Cikin shekaru ashirin da hudun nan daga 1821 zuwa 1845, Wolf ya yi tafiya sosai: a Afirka, ya ziyarci Masar da Habasha; a Asia, ya je Falesdinu da Syria da Persia da Bokhara, da Indiya. Ya kuma ziyarci Amerika, inda ya yi wa’azi a tsibirin Saint Helena. Ya isa New York cikin Agusta na 1837, kuma bayan ya yi magana a birnin, ya yi wa’azi a Filadelfiya da Baltimore, a karshe kuma ya ci gaba zuwa Washington. A nan, ya ce, “game da wata takardar roko da shugaba John Quicy Adams mai-barin gado ya kawo, a daya daga cikin Majalisun, Majalisar ta ka da kuriya gaba gadi ta ba ni izinin anfani da Zauren Majalisar don yin lacca ta, wadda kuwa na yi wata ranar Asabar, dukan ‘yan majalisar kuma suka girmama ni tawurin halartar laccar, da kuma bishop na Virginiya, da masu aikin bishara da mutanen Washington kuma. Membobin gwamnatin New Jersey, da Pennsylvania ma sun girmama ni hakanan, na ba da laccoci game da bincike na a Asia da kuma game da mulkin Yesu Kristi da kan sa.” BJ 358.2
Dr.Wolf ya rika tafiya a kasashe mafi-kauyanci da mugunta ba tare da tsaro daga hukumomin Turai ba. Ya jimre wahaloli ga hatsaruka kewaye da shi. An yi masa duka da sanduna, ga yunwa, aka sayar da shi kamar bawa, sau uku kuma aka masa hukuncin kisa, ya gamu da mafasa, wadansu lokuta kuma ya kusa mutuwa da kishirwa. An taba kwace duk abin da yake da shi, ya yi tafiyar daruruwan mil a kafa, yana ketare duwatsu, daskararriyar iska tana karo da fuskarsa, sawayensa kuma suka kangare saboda sanyi. BJ 359.1
Sa’an da aka gargade shi kada ya yi tafiya ba tsaro a cikin kabilu marasa mutunci, magabta kuma, “ya ce shi yana da makamai”, “watau addu’a, himma don Kristi, da amincewa da taimakonsa.” Ya ce: “An kuma tanada mani kaunar Allah da makwabci na a zuciyata, Littafi kuma yana hannuna.” Ya rika tafiya da Littafin, na harshen Ibrananci da na harshen Hellenanci ko ina ya je. Game da wata tafiyar sa ya ce: “Na rike budediyar Littafin a hannuna. Na ji a jiki na cewa karfi na yana cikin Litafin ne, kuma girmansa zai taimake ni.” BJ 359.2
Hakanan ne ya nace cikin aikinsa har sai da aka kai sakon hukumcin ga mutane da yawa a duniyan nan. Ya raba cikin harsunan Yahudawa da Turkawa da Parsiyawa, da Hindawa da kuma kabilu da jinsuna da yawa, kuma ko ina ya dinga shelar kusantawar mulkin Masiya. BJ 359.3
Cikin tafiye tafiyensa, a Bokhara ya tarar da wadansu makadiata masu nisa da suke koyar da sakon kusantowar zuwan Ubangiji. Larabawan Yamal, in ji shi, “suna da wani Littafi mai-suna Seera, wanda ke sanar da zuwan Kristi da mulkinsa cikin daraja, kuma suna begen cewa manyan al’amura za su faru a shekara ta 1840.” Ya ce: “A Yamal …. na yi kwana shidda da yayan Rechab. Ba sa shan barasa, ba sa shuka inabi, ba sa shuka iri, kuma suna zama a tents ne, suna kuma tuna nagarin tsohon nan Janadab, dan Rechab, na kuma tarar da ‘ya’yan Israila a cikinsu, yan kabilar Dan,… wadanda, tare da ‘ya’yan Rechab din, su ke begen zuwan Masiya cikin gizagizai na sama, da sauri.” BJ 359.4
Wani dan mishan ma ya tarar da irin wannan koyaswar a Tatary. Wani priest na Tatar ya tambayi dan mishan din ko yaushe ne Yesu zai sake zuwa. Sa’an da dan mishan din ya ce bai san komi game da wannan ba, priest din ya yi mamaki sosai game da wannan rashin sani daga mutumin da ke kiran kansa mai koyar da Littafin, sai ya bayana nasa bangaskiyar, bisa ga annabci, cewa Kristi zai zo wajien 1844 ne. BJ 360.1
Daga 1826, an fara wa’azin zuwan Kristi a Ingila. Aikin a can bai bi wani takamamen tsari kaman na Amerika ba, ba a koyar da ainihin lokacin zuwan ba, amma babban gaskiya na kusantowar zuwan Kristi da iko da daraja dai an koyar da shi sosai, kuma ba cikin masu musu da masu-ta da kayar baya kadai ba. Mourant Brock, wani mawallafi dan Ingila, ya ce wajen masu aikin bishara na Ekklesiyar Ingila sun rika wa’azin “wanan bishara ta mulkin.” A Birtaniya ma, an ba da sakon da ya nuna cewa 1844 ne lokacin zuwan Ubangiji. An dinga raba wallafafun rubuce rubuce daga Amerika game da zuwan Kristi din. Aka sake wallafa littafai da majallu a Ingila. A 1842 kuma, Robert Winter, haifaffen dan Ingila, wanda ya karbi bangaskiyar zuwan Kristi din a Amerika, ya dawo kasarsa ta gado don yin shelar zuwan Ubangiji. Da yawa suka hada hannu da shi cikin aikin, aka kuwa yi shelar sakon hukumcin a sassa da yawa na Ingila. BJ 360.2
A Amerika ta kudu, a tsakiyar kauyanci da tsafi, Lacunza, dan Spain, kuma dan kungiyar Jesuit, ya sami hanyar karanta Littafin, ta haka kuma ya sami gaskiyar dawowar Kristi da sauri. Da marmarin ba da gargadin, ga shi kuma yana so ya kauce ma horon daga Rum, sai ya wallafa ra’ayoyinsa da wata suna dabam da ya ba kansa wai “Rabbi Ben-Ezra,” yana nuna kansa wai tubabben Ba-Yahudi ne. Lacunza ya yi rayuwarsa a karni na sha takwas ne, amma wajen 1825 ne aka juya littafinsa da ta shigo London zuwa turanci. Wallafawar ta kara zurfafa sha’awa a Ingila game da batun zuwan Kristi na biyu din. BJ 361.1
A Jamus an rigaya an koyar da koyaswar a karni na sha takwas ta bakin Bengel, wani ma’aikacin bishara a ekklesiyar Lutheran, shahararren masani mai-ba yin sharhi game da aikin wadansu. Sa’anda ya gama makarantarsa, Bengel ya dukufa ga nazarin ilimin tauhidi, wanda ya je daidai da zuciyarsa ta son addini da kuma irin horon da ya samu tun kuruciyarsa. Kamar sauran samari masu-tunani, ya dinga fama da shakku da rashin fahimta na addini, ya kuma ambaci matsaloli da yawa da suka rika addabar zuciyarsu suka kuma sa samartakar sa ta zama masa da wahala. “ Da ya zama dan majalisar Warttemberg, ya ba da shawara cewa a ba kowa ‘yancin addini”. “Yayin da ya girmama ‘yancin ekklesiya, ya dinga shawarta cewa a ba duk mai son janyewa daga cikinta sabo da lamirinsa ‘yancin ficewa. “Har yau ana cin moriyar wannan ra’ayin a kasarsa ta gado.” BJ 361.2
Yayinda yake shirya wa’azi daga Ruya 21 ne hasken zuwan Yesu na biyu ya shigo zuciyar Bengel. Ya fahimci annabce annabcen littafin Ruya fiye da yadda ya taba fahimta. Sabo da yawan muhimmanci da darajar ababan da annabin ya gabatar, dole ya dakatar da binciken batun tukuna. A bagadi, batun ya sake zuwa masa a sarari da karfi kuma. Daga wannan lokacin ya dukufa wajen yin nazarin annabce annabcen, musamman game da karshen duniya, nan da nan kuma ya gane cewa sun nuna cewa zuwan Kristi ya kusa. Ranan da ya aza cewa ita ce ranar zuwan Kristi din ba ta yi nisa da shekaran da Miller daga baya ya aza cewa Kristi ba zai dawo ba. BJ 361.3
An baza rubuce rubucen Bengel ko ina cikin Kirista. Da yawa a jiharsa ta Wuttenberg sun amince da ra’ayoyinsa game da annabci, haka kuma, a wadansu sassan Jamus ma. Aikin ya cigaba bayan mutuwarsa, aka kuma ji sakon zuwan Kristi a Jamus daidai lokacin da yana jan hankula a wadansu kasashe. Ba da jimawa ba wadansu masu ba da gaskiya suka je Rasha, can kuma suka kafa kungiyoyi, kuma har yanzu ekklesiyoyin Jamus suna rike da bangaskiya game da kusatowar zuwan Kristi. BJ 362.1
Hasken ya kuma haskaka a Faransa da Switzerland. A Geneva inda Farel da Calvin suka baza gaskiyar Canjin, Gausen ya yi wa’azin zuwa na biyu din. Yayin da yake dalibi a makaranta, Gausen ya sadu da ruhun nan na dogara ga tunani maimakon bangaskiya ko wahayi, wanda ya mamaye Turai a karshen karni na sha takwas zuwa farkon karni na sha tara; kuma sa’an da ya shiga aikin bishara, bai san ainihin bangaskiya ba, har ma ya fi zama mai yawan shakka. A samartakarsa, ya yi sha’awar nazarin annabci. Bayan ya karanta littafin Rollin, mai-suna “Tarihin Zamanin Da,” hankalin sa ya koma littafin Daniel, ya kuma yi mamakin yadda annabcin ya cika daidai, bisa ga tarihi. Wannan ya zama shaida gareshi cewa Littafin hurare ne daga Allah, abin da kuma ya zama masa madogara cikin matsalolin rayuwa. Bai gamsu da koyaswoyin ra’ayin nan cewa tunani ya fi wahayi ko bangaskiya ba, kuma yayin da yake nazarin Littafin, ya sami bangaskiya mafi haske. BJ 362.2
Yayin da ya ci gaba da binciken annabci, ya kai inda ya gaskata cewa zuwan Ubangiji Ya kusa. Sabo da muhimancin gaskiyan nan, ya yi sha’awar kawo shi gaban mutane, amma ra’ayin nan cewa annabce annabcen Daniel asirai ne da ba za a iya fahimta ba ya kawo masa cikas. A karshe dai ya kudurta kai bisharar a Geneva, zai kuma fara da yara, tawurinsu kuma zai jawo hankulan iyayen. BJ 362.3
Daga baya ya ce: “Ina so a gane, ba don kankantan muhimmancinsa ba ne, amma sabo da yawan anfaninsa ne na so in bayana shi hakanan, na kuma sanar da shi ga yara. Na so a saurare ni, na kuma ji tsoron cewa ba za a saurare ni ba idan na fara da manya tukuna.” “Sabo da haka na kudurta farawa da kananan. Ni kan tara yara; idan yawansu ya karu, idan an ga suna sauraro, sun ji dadi, suna sha’awa, suna ganewa har ma su fassara batun, na tabbata ba da jimawa ba zan sami kungiya ta biyu, su manya kuma za su ga cewa ya kamata su zauna su yi nazari. Idan aka yi haka, an yi nasara.” BJ 363.1
Kokarin ya yi nasara. Yayin da yake ma yaran jawabi, manya sukan zo su ji. Kowane dakin taro na majami’arsa yakan cika da masu-sauraro. Cikinsu akwai masana da masu-matsayi, da baki da ke ziyartar Geneva; ta hakanan aka kai sakon wadansu sassan. BJ 363.2
Wannan nasarar ta karfafa Geneva, sai ya wallafa darussan sa, da niyyar karfafa nazarin litattafan annabci a ekklesiyoyi masu karshen Faransa. Ya ce: “Wallafa koyaswa da aka yi ma yara yana ce ma manya ne da ke kin kula littattafan a kan cewa wai ba za a iya gane su ba, ‘Yaya ba za a iya fahimtarsu ba, tun da yaranku suna fahimtarsu?’ ” Ya kara da cewa: “Na yi sha’awa kwarai in sa sanin annabce annbcen ya zama abin sha’awa ga mutanenmu, idan zai yiwu.” “A gani na ba nazarin da ya fi biyan bukatun zamanin.” “Ta wurin wannan ne za mu shirya domin kuncin da ke zuwa ba da jimawa ba, mu kuma yi tsaro, mu jira Yesu Kristi.” BJ 363.3
Ko da shike Gausen yana daya daga cikin shahararrun masu-wa’azi da harshen Faransa, bayan wani lokaci an dakatar da shi daga aikin bishara a kan cewa ya yi anfani da Littafin don koyar da matasa, maimakon wata takardar koyarwa mara takamemmen matsayi game da bangaskiya, wadda ekklesiya ke anfani da ita. Daga bisani ya zama mai koyarwa a makarantar ilimin tauhidi, ran Lahadi kuma yakan ci gaba da aikinsa na koyar ma matasa Littafin. Rubuce rubucensa game da annabci ma sun ja hankula sosai. Daga aikin sa na shehun mallami zuwa mawallafi da mai-koyar da yara, ya yi shekaru da yawa yana tasiri kwarai, ya kuma yi aiki sosai wajen jawo hankulan mutane da yawa ga nazarin annabce annabcen da suka nuna cewa zuwan Ubangiji ya kusa. BJ 364.1
A Scandinavia ma an yi shelar sakon zuwan Kristi, aka kuma ta da sha’awar mutane da yawa. Da yawa suka falka daga kyaliyarsu, suka furta suka kuma rabu da zunubansu, suka kuma bidi gafara a cikin sunan Kristi. Amma masu aikin bishara na ekklesiyar kasar sun yi jayayya da aikin, kuma tawurin su aka jefa wadansu masu wa’azin sakon cikin kurkuku. A wurare da yawa inda aka hana masu-shelar zuwan Ubangiji hakanan, Allah Ya aika da sakon ta hanyar al’ajibi, tawurin yara kanana. Da shike yara ne, dokar kasa ba ta iya hana su ba, aka kuma yarda masu suka yi magana babu tsangwama. BJ 364.2
Yawancin aikin, talakawa ne suka yi, kuma a gidajen masu aikin ne mutane suka rika taruwa don jin gargadin. Yara masu wa’azin ma kauyawa ne. Wadansu basu fi shekara shida ko takwas ba, kuma yayin da rayuwarsu ta shaida cewa suna kaunar Mai-ceton, kuma suna kokarin rayuwar biyayya ga umurnin Allah, sun nuna irin basira da kwarewa da ake samu daga saransu ne kawai. Amma sa’anda suke tsaye a gaban mutane, yakan bayana a fili cewa wani iko fiye da kwarewarsu ta mutuntaka ne ke aiki a cikinsu. Muryarsu da hallayyansu sukan sake, da iko mai-saduda kuma su kan ba da gargadi game da hukumcin, suna anfani da kalman nassin cewa, “Ku ji tsoron Allah, ku ba Shi daraja; gama sa’ar hukumshinsa ta zo.” Sun tsauta ma zunuban mutanen, ba fasikanci da mugunta kadai ba, amma suka tsauta ma son abin duniya da koma-bayan ruhaniya, suka kuma gargadi masu jinsu su yi sauri su guji fushi da ke zuwa. BJ 364.3
Mutanen sun rika sauraro da rawan jiki. Ruhun Allah ya yi magana da zukatansu. Da yawa suka fara binciken Littafin da sabon marmari mai-zurfi, marasa kamewa da fasikai suka canja, wadansu suka rabu da rashin gaskiyansu, kuma aka yi aikin da ya yi anfani ta yadda ko ma’aikatan ekklesiyar kasar dole suka yarda cewa hannun Allah na cikin aikin. BJ 365.1
Nufin Allah ne cewa a ba da sakon zuwan Mai-ceton a kasashen Skandivavia, kuma sa’an da aka rufe muryoyin bayinsa, Ya sa Ruhunsa cikin yara domin a gama aikin. Sa’anda Yesu Ya kai kusa da Urushalima tare da jama’a da ke farinciki, suna rairawa ta nasara da ganyayen dabino kuma a hannayen su, suna shelar cewa Shi ne Dan Dawuda, Farisawa masu kishin nan suka ce mashi Ya sa su yi shuru; amma Yesu ya amsa cewa dukan wannan cikar nabbabci ne, kuma idan wadannan suka yi shuru duwatsu za su ta da murya. Mutanen, sabo tsoron priestoci da shugabannin, suka dena shelar ta su yayin da suka shiga Urushalima, amma bayan haka yara a harabar haikalin suka daga wakar, suna kada ganyayen dabino, kuma suka rika cewa: “Hossana ga Dan Dawuda!” Matta 21:8-16. Sa’anda Farisawa cikin fushi suka ce masa: “Kana jin abin da wadannan su ke fadi?” Yesu Ya amsa: “I, ba ku taba karantawa ba, daga chikin bakin jarirai da masu shan mama ka chika yabo?” Kamar yadda Allah Ya yi ta wurin yara a lokacin zuwan Krisiti na farkon, haka kuma Ya yi ta wurinsu game da ba da sakon zuwansa na biyu. Dole maganar Allah ta cika, cewa za’a yi shelar zuwan Mai-ceton ga dukan mutane, da harsuna, da al’ummai. BJ 365.2
William Miller da abokan aikinsa ne aka ba su wa’azin gargadin Amerika. Wannan kasar ta zama cibiyar babban aikin shelar zuwan Yesu. A nan ne annabcin sakon malaika na fari ya fi cika kai tsaye. Rubuce rubucen Miller da abokansa sun kai kasashe masu nisa. Duk inda ‘yan mishan suka shiga a duniya, an aika da labarin zuwan Kristi da sauri. Ko ina sakon bishara ta har abada ya bazu cewa; “Ku ji tsoron Allah, ku ba Shi daraja, gama sa’ar hukumcinsa ta zo.” BJ 366.1
Shaidar annabcin da ya nuna kamar Kristi zai zo a bazarar 1844 ne ya shiga tunanin mutanen sosai. Yayin da sakon ya je daga jiha zuwa jiha, ko ina aka ta da sha’awar mutane. Da yawa sun yarda cewa fasarar annabcin game da lokaci daidai ne, kuma suka sallamar da ra’ayin su suka karbi gaskiyar. Wadansu ma’aikatan bishara suka bar ra’ayoyin darikunsu, suka bar albashinsu, da ekklesiyoyinsu, suka hada kai wajen shelar zuwan Yesu. Amma masu aikin bishara kalilan ne fa suka karbi sakon nan, sabo da haka an bar ma masu sa kai ne yawancin aikin. Manoma suka bar gonakinsu, makanikai suka bar kayan aikinsu, yan tireda suka bar kayan jarinsu, masu-aikin gwamnati suka bar matsayinsu; amma duk da haka yawan mutanen ya kasa idan aka gwada da aikin da za a yi. Yanayin ekklesiya mara bin Allah da duniya da ke kwance cikin mugunta ya dami masu tsaron, suka kuma yarda suka jimre aiki da rashi da wahala, domin su kirawo mutane zuwa tuba da ceto. Ko da shike Shaitan ya yi jayayya da su, aikin ya ci gaba, dubbai kuma suka karbi gaskiyar zuwan Kristi din. BJ 366.2
Ko’ina an ji shaidar, ana gargadi ga masu zunubi, ‘yan duniya da ‘yan ekklesiya, cewa su gudu daga fushin da ke zuwa. Kamar Yohanna mai-baftisma, wanda ya share ma Kristi hanya, masu wa’azin sun sa gatari a gindin itatuwa suka bukaci mutane su fito da ‘ya’ya fa masu-isa tuba. Gargadinsu ya banbanta da tabbacin salama da zsaman lafiya da aka dinga ji daga majami’u da yawa; kuma duk inda aka ba da sakon, ya motsa mutanen. Shaidar Littafin kai tsaye da Ruhu mai-tsarki ya bayana, ya jawo ganewa kwarai. Masu addini suka falka daga gamsuwarsu ta karya, suka ga koma-bayansu, da son duniya da rashin bangaskiyansu, da fadin ransu da kuma son kansu. Da yawa suka bidi Ubangiji da tuba da tawali’u. Kaunar duniya ta koma kaunar sama. Ruhun Allah Ya sauko kansu, kuma da zukata da aka tausasa aka kuma rinjaya, suka sa hannu cikin shelar cewa; “Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja, gama sa’ar hukumcinsa ta zo.” BJ 367.1
Masu zunubi cikin kuka suka ce: “Mene ne zan yi domin in sami ceto?” Masu rashin gaskiya suka nemi mayas da abinda suka karba tawurin rashin gaskiyan. Dukan wadanda suka sami salama cikin Kristi suka yi sha’awar ganin wadansu ma sun sami albarkar. Zukatan iyaye suka koma ga yayansu, zukatan ‘ya’ya kuma ga iyayensu. Aka kawar da shingen girman kai. An furta laifuka da gaske ‘yan gida kuma suka yi aiki don ceton kaunatattu na kusa da su. Sau da yawa akan ji addu’a da gaske da ake ma wani. Ko ina rayuka cikin bakinciki suka dinga rokon Allah. Da yawa sun dinga addu’a duk dare don samun tabbacin cewa an gafarta zunubansu, ko kuma don tubar yan-uwa ko makwabta. BJ 367.2
Mutane kowane iri sun dinga halartar kowane taron wa’azin, mawadata da matalauta, manya da kanana, sabo da dalilai dabam dabam, da taraddadi, suka so su ji ma kansu koyaswar zuwan Kristi na biyu din. Ubangiji ya hana ruhun jayayya yayin da bayinsa suka bayana dalilin bangaskiyar su. Wani lokaci mai-wa’azin yana da kumamanci, amma Ruhun Allah Ya ba da iko ga gaskiyarsa. An ji kasancewar malaiku masu tsarki a wuraren taron nan, kuma aka kara masu bangaskiya da yawa. Yayin da aka maimaita shaidun kusantowar zuwan Kristi, jama’a da yawa suka rika sauraro shuru. Sai kace sama da duniya suna saduwa da juna. An ji ikon Allah a kan tsofoffi da yara da matasa. Mutane suka bidi gidajensu da yabo a lebunan su, sautin farincikin kuma ya cika ko ina cikin daren. Duk wadanda suka halarci taron ba za su taba manta abinda ya gudana ba. BJ 367.3
Shelar takamammen lokacin zuwan Kristi ya jawo jayayya sosai daga mutane da yawa, daga kowane sashi, daga masu wa’azi zuwa yan banza marasa tsoron Allah ma. Kalmomin annabci sun cika cewa: “Cikin kwanaki na karshe masu-ba’a, suna bin nasu sha’awoyi, suna chewa, ina alkawalin tafowassa? Gama tunda randa ubanni suka kwanta barci, dukan al’amura suna nan kamar yadda suke tun farkon halitta. Bitrus II 3:3,4. Da jayayya game da koyaswar zuwansa na biyu din; su dai basu yarda da takamammen lokacin ba ne. Amma idon Allah ya karanta zukatansu. Basu so su ji maganar zuwan Kristi don shar’anta duniya cikin adalci ba ne. Su bayi marasa aminci ne, ayukansu ba za su jimre binciken Allah ba, suka kuwa ji tsoron saduwa da Ubangijinsu. Kamar Yahudawa lokacin zuwan Kristi na farkon, su ma ba sa shirye su tarbi Yesu din. Ban da kin sauraron bayanai daga Littafin ma, suka kuma yi ma masu-bidar Ubangiji ba’a. Shaitan da malaikunsa suka ji dadi, suka wurga ma Kristi ba’ar a fuskarsa da fuskar malaikunsa masu tsarki cewa mutanen nasa ma ba sa kamanarsa, har ma ba sa son bayyanuwarsa. BJ 368.1
Masu kin batun zuwan Yesu sukan dogara ga furcin nan ne. “Ba wanda ya san rana ko sa’a. Nassin ya ce: “Amma zanchen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani ba, ko malaiku na sama, ko Da, sai Uban kadai.” Matta 24:36. Wadanda ke neman Ubangiji suka fassara nassin daidai a bayane, amma masu jayayya da su suka yi anfani da nassin ta yadda bai kamata ba. Yesu ya fadi kalmomin nan a cinin hirarsa da almajiran ne a kan Dutsen Zaitun bayan ya bar haikalin, bari na karshe. Almajiran sun tambaya: “Mi ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” Yesu Ya ba su alamu, ya kuma ce. “Lokacinda kun ga wadannan al’amura duka, ku sani ya yi kusa, har bakin kofa.” Aya 3, 33. Ba yadda za a sa wani furcin Yesu ya rushe wani furcin nasa kuma. Ko da shike ba wanda ya san rana ko sa’ar zuwansa, an umurce mu mu san lokacin da zuwan ya kusa. An kuma koya mana cewa rashin kulawa game da sanin kusantowar zuwan sa zai zama da hatsari garemu kamar yadda ya zama ma mutanen lokacin Nuhu da basu san ambaliyar ta zo ba. Kuma misalin da ke cikin suran nan din, wanda ya bambanta amintacen bawa da bawa mara aminci, ya kuma bayana kaiton wanda ya ce a zuciyarsa; “Ubangiji na yana jinkiri,” ya nuna ta yadda Kristi zai mai da wadanda zai tarar da su suna tsaro, suna kuma koyar da batun zuwansa da kuma wadanda ke kinsa. Ya ce: “Ku yi tsaro fa, wannan mai-albarka ne wanda Ubangijinsa sa’anda ya zo za ya iske shi yana yin haka.” Aya 42, 46 “Idan fa ba ka yi tsaro ba, ina zuwa da kamar barawo ba kwa za ka san sa’an da zan afko maka ba.” Ruya 3:3. BJ 368.2
Bulus ya yi magana game da wadanda bayanuwar Ubangiji tana zuwa misalin barawo da dare. “Suna chikin fadin, kwanchiyar rai da lafiya, sai ga hallaka farap daya ta abko masu,… ba kwa za su tsira ba ko kadan.” Amma ya kara, ga wadanda suka saurari gargadin Mai-ceton: “Amma ku yan-uwa ba chikin dufu kuke ba da ranan nan za ta tarshe ku kamar barawo; gama ku duka yayan haske ne, yayan rana kwa: mu ba na dare ba ne, ba kwa na dufu ba.” Tassalunikawa I, 5:2-5. BJ 369.1
Ta hakanan aka nuna cewa Littafin bai ba mutane damar kasancewa cikin jahilci game da kusantowar zuwan Kristi ba. Amma wadanda suka so hujjar kin gaskiya suka rufe kunnuwasu, kuma masu ba’a, har ma da masu kiran kansu ma’aikatan bishara suka ci gaba da maimaita kalmomin nan “Ba wanda ya san rana ko sa’a.” Sa’anda mutane suka falka, suka fara neman hanyar ceto, shugabannin addini suka shiga tsakaninsu da gaskiyar, suna nema su kwantar da hankulansu ta wurin fassara maganar Allah a karkace. Marasa aminci suka hada kai cikin aikin mai-rudun nan, suna cewa, salama, salama, alhali Allah bai ba da salama ba. Kamar Farisawa a zamanin Kristi, da yawa sun ki shiga mulkin sama da kansu, suka kuma hana masu shiga. Za a bidi jinin mutanen nan daga hannunsu. BJ 370.1
Mutane mafi tawali’u da dukufa cikin ekklesiyoyin ne suka fara karban sakon. Wadanda suka yi nazarin Littafin ma kansu dole suka ga kuskuren ra’ayoyi da mutane suka fi karba game da annabci, kuma duk inda tasirin masu aikin bishara bai shafi mutanen ba, sukan gwada koyaswar zuwan Kristi da Littafin ne kawai su ga cewa Allah ne tushen koyaswar. BJ 370.2
Da yawa yan’uwansu marasa ba da gaskiya ne suka tsananta masu. Domin su rike matsayinsu a cikin ekklesiya, wadansu suka yarda su yi shuru game da begensu; amma wadansu sun ga cewa aminci ga Allah ya hana su boye gaskiyan da shi yaba su amanarta. An cire wadansu daga zumuncin ekklesiya don kawai sun bayyana bangaskiyar su game da zuwan Kristi. Gare su, kalmomin annabin sun zama da anfani sosai, cewa, “Yan’uwanku wandanda sun ki ku, su wadanda suka yasda ku sabili da sunana, sun che, Bari Ubangiji shi daukaka, domin mu ga farincikiku; amma su za su kumyata.” Ishaya 66:5. BJ 370.3
Malaikun Allah sun yi ta kallon sakamakon gargadin. Sa’anda yawancin ekklesiyoyi suka ki sakon, malaiku suka juya cikin bakinciki. Amma akwai da yawa da ba a rigaya an gwada su ba game da gaskiyar zuwan Kristi din. Da yawa mazasu da ko matansu, ko iyayensu, ko yaransu ne suka rude su, suka kuma sa suka gaskata cewa sauraron koyaswoyin Adventist na zuwan Kristi din ma zunubi ne. Aka sa malaiku tsaron mutanen nan da aminci domin wani hasken kuma zai haskaka su daga kursiyin Allah. BJ 370.4
Da marmari kwarai wadanda suka karbi sakon suka saurari zuwan mai-cetonsu. Lokacin da suka zata zai zo ya yi. Sun kai wannan sa’ar da saduda cikin natsuwa suka huta cikin sadarwa mai-dadi tare da Allah, kwatancin salamar da za su samu nan gaba. Duk wanda ya dandana begen nan da amincewan nan ba zai iya manta sa’o’in jiran nan ba. Makonni kafin lokacin, an dakatar da yawancin harkokin duniya. Ainihin masu-bada gaskiyan suka bincika kowane tunanin zuciyarsu da kyau kamar lokacin mutuwarsu ta iso sauran sa’o’i kadan kawai. Kowa ya ga bukatar tabbacin cewa yana shirye don saduwa da Mai-ceton; fararen tufafinsu, tsabtar rai ne -halayen da aka tsrakake daga zunubi ta wurin jinin kafara na Kristi. Ina ma ace da har yanzu cikin mutanen Allah akwai wannan ruhun binciken zukatan, irin himman bangaskiyan nan. Da sun ci gaba suna kaskantar da kansu hakanan a gaban Ubangiji, suka kuma kai roke rokensu a kujerar jin kai, da suna da dandano mai-yalwar anfani fiye da wanda suke da shi yanzu. Akwai karancin addu’a, karancin amincewa, cewa an yi zunubi, kuma rashin bangaskiya na kwarai yana hana mutane da yawa alherin da mai-fansarmu ya tana da mana. BJ 371.1
Allah Ya shirya gwada mutanensa. Hannunsa Ya rufe wani kuskuren fasarar wokatan annabcin. Adventist basu gane kuskuren ba. Kuma masanan abokan hamayyansu ma basu gane ba. Yan hamayyan suka ce: “Lissafin ku na wokatan annabcin daidai ne. Wani babban al’amari yana gaf da faruwa, amma ba abin da Miller ke fadi ba ne, tubar duniya ne, amma ba zuwan Kristi na biyu ba ne.” BJ 371.2
Lokacin da aka zata zai zo din ya wuce, Kristi kuma bai bayana don kubutar da mutanensa ba. Wadanda da ainihin bangaskiya da kauna suka nemi Mai-cetonsu, sun yi cizon yatsa mai daci sosai. Duk da haka an rika cika manufofin Allah. Ya gwada zukatan masu cewa suna sauraron bayanuwarsa ne. Cikinsu akwai da yawa da tsoro ne kawai ya motsa su. Furcin bangaskiyarsu bai shafi rayuwarsu ko zukatansu ba. Sa’anda al’amarin da aka yi tsammaninsa bai faru ba, mutanen nan suka ce basu sami yankan buri ba, basu taba gaskatawa ma cewa Yesu zai zo ba. Suna cikin wadanda suka fara yi ma bakincikin masu-bada gaskiyan ba’a. BJ 372.1
Amma Yesu da dukan rundunan sama sun dubi amintattun da aka gwada su, ko da shike sun sami yankan buri. Da an bude labulen da ke raba tsakanin duniyan da ake gani da wanda ba a gani, da an ga malaiku suna kusatowa wurin amintattun nan suna kuma ba su kariya daga hare-haren Shaitan. BJ 372.2