Duk inda aka yi wa’azin maganar Allah da aminci, sakamakon yakan hakikance cewa Allah ne tushen ta, Ruhun Allah ya kasance tare da sakon bayinsa, maganar kuma ta zama da iko. Masu zunubi suka ji an farfado da lamirinsu. Hasken da ke haskaka dukan wanda ya zo cikin duniya ya rika haskaka kowane lungun ransu aka kuma bayana boyayun ababa na duhu. Tunanin su da zukatansu suka tabu kwari. Suka amince cewa akwai zunubi da adalci da hukumci mai-zuwa. Suka sami dandanon adalcin Yahweh suka kuma ji tsoron bayanuwa cikin laifinsu da rashin tsabtarsu, a gaban mai binciken zukata. Cikin bakinciki suka yi kuka cewa, “Wa za ya kubutar da ni daga jikin nan mai-mutuwa?” Sa’an da aka bayana giciyen kalfari da hadayarsa domin zunuban mutane, suka ga cewa ban da halayan Kristi ba abin da ya isa ya yi kafara domin zunubansu; abin da kadai zai iya sasanta mutum da Allah kenan. Da bangaskiya tare da saukin kai suka karbi Dan rago na Allah, wanda ke dauke da zunubin duniya. Ta wurin jinin Yesu sun sami gafarar zunuban da suka wuce. BJ 458.1
Wadannan mutane suka haifi ‘ya’ya da suka cancanci tuba. Sun ba da gaskiya aka kuma yi masu baptisma, suka kuma taso domin yin tafiya cikin sabon rai, sabobin halitta cikin Kristi Yesu; ba domin sifanta kansu bisa ga sha’awoyi na da ba, amma bisa ga bangaskiya na Dan Allah su bi sawunsa, su kamanta halinsa, su kuma tsabtata kansu, kamar yadda Shi mai-tsabta ne. Ababan da suka ki da, yanzu suka so su, ababan da suka so da kuma, yanzu suka ki su. Masu-girman kai da nuna isa suka zama masu saukin-kai da taushin zuciya, marasa kunya, masu rashin hankuri suka zama natsatsu marasa gagara. Marasa tsarki suka zama masu bangirma, mashaya suka zama natsatsu, fasikai kuma suka zama masu tsabta. Ayukan banza na duniya aka kawar da su. Kirista suka dena bidar “ado na waje, watau su kitson gashi, da sa ado na zinariya, ko yafa tufafi masu kawa, amma, boyayyen mutum na zuchiya, chikin tufafi wadanda ba su lalachewa, na ruhu mai-ladabi mai-lafiya, abin da ke da tamani mai-girma a gaban Allah.” 1Bitrus 3:3,4. BJ 458.2
Hidimomin falkaswa sun rika jawo bimbini mai-zurfi da tawali’u, sun kunshi roko mai saduda da gaske ga mai-zunubi cikin tausayi saboda jinin Kristi da an saye su da shi. Maza da mata sun yi addu’o’i ga Allah domin ceton rayuka. An ga ‘ya’yan wadannan falkaswan cikin rayukan da ba su tsaya kan musun-kai da hadaya kadai ba, amma suka yi farinciki cewa suma sun isa su sha reni da gwaji sabo da Kristi. Mutane sun ga sakewa a rayukan wadanda suka furta sunan Yesu. Jama’a suka anfana ta wurin tasirinsu. Suka tattaro tare da Yesu, suka kuma shuka ga Ruhu, domin su girbe rai madawami. BJ 459.1
Game da su ana iya cewa: “Bachin zuchiya da aka yi ya kawo tuba.” “Gama bachin zuchiya irin da Allah ke sa ya kan aika tuba zuwa cheto, tuba mara-ladama; amma bakin zuchiya na duniya yana aika mutuwa. Gama wannan abu kansa, bakinzuchiya da aka yi maku irin da Allah ke sa, duba irin kaifin hankali da ya aika a wurinku, i, duba, wache irin kariyar kai, i, wane irin haushi, i, wane irin tsaro, i, wane irin bege, i, wache irin himma, i, wane irin daukar pansa! Ga kowane abu kuka nuna kanku kubutattu a chikin wannan matsala.” Korinthiyawa II, 7:9-11. BJ 459.2
Wannan sakamakon aikin Ruhun Allah ne. Sakewa it ace kadai shaidar ainihin tuba. Idan ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya kwace, kuma, ya furta zunubansa, ya kuma kaunaci Allah da yanuwansa ‘yan Adam, mai-zunubin nan zai sami tabbaci cewa ya sami salama da Allah. Irin sakamakon da suka biyo bayan lokutan falkaswa na addini kenan a shekarun baya. Bisa ga ‘ya’yan da suka haifar aka sani cewa Allah Ya yi masu albarkacikin ceton mutane da kyautata yanayin ‘yan Adam. BJ 459.3
Amma da yawa cikin hidimomin falkaswa na zamanin nan sun bambanta kwarai daga almun alherin Allah da suka biyo bayan aikin bayin Allah a zamanin da. Hakika akan ta da marmari sosai, da yawa sukan ce sun tuba, kuma akan zama membobibn ekklesiyoyi, duk da haka sakamakon ba wadanda za su sa a ga cewa karuwar rayuwar ruhaniya ba ne. Hasken da ya kan nuna na wani dan lokaci ya kan mutu nan da nan, ya bar duhun da ya fi na da. BJ 460.1
An cika gudanar da falkaswa ta yadda an fi maida hankali ga ababa masu ban mamaki ko ban tsoro, ko ban tausayi. Wadanda suka tuba ta wurin wadannan ba sa sha’awar jin gaskiya ta Littafin, kuma ba su damu da shaidar annabawa da manzani ba. Idan hidima ta addini tana jawo hankali a yi tunani ne kawai, ba a kula ta. Ba sa jin gargadin maganar Allah game da rayuwarsu ta har abada. BJ 460.2
Ga kowane mai-tuba na gaskya, dangantaka da Allah da ababa na har abada ne za su zama muhimman ababa gare shi. Amma a shaharrarun ekklesiyoyi yau, ina ake samun ruhun mannewa ga Allah? Tubabbun ba sa barin girman-kan su da son duniya. Ba sa shirye su yi musun kai, su dauki giciyensu, su bi Yesu mai-tawali’u yanzu. Addini ya zama abin wasan kafirai da masu shakka domin da yawa masu addinin ba su san kaidodinsa ba. Ikon ibada ya kusa batawa daga ekklesiyoyi da yawa. Cin guziri na shan iska, nishadi, kyawawan gidaje, da burgewa sun kawar da tunani game da Allah. Filaye da kayan duniya da aikace-aikace na duniya ne suka mallaki tunanin mutane, kuma ababa masu anfani na har abada ba a ko kulawa da su ma. BJ 460.3
Ko da shike bangaskiya da ibada sun ragu sosai, akwai masu-bin Kristi na kwarai a cikin wadannan ekklesiyoyin. Kafin hukumcin Allah na karshe a akan duniya, za a iske falkaswar ibada irin ta da a cikin mutanen Ubangiji, irin da ba a taba gani ba tun zamanin manzani. Za a zubo da Ruhun Allah da ikonsa bisa ‘ya’yansa. A wancan lokacin mutane da yawa za su rabu da ekklesiyoyi inda kaunar duniyan nan ta dauki wurin kaunar Allah da maganarsa. Mutane da yawa za su karbi muhimman gaskiyan nan da Allah Ya sa a sanar a wannan lokacin domin shirya jama’a don zuwan Kristi na biyu. Magabcin yana so ya hana wannan aikin, kuma kafin lokacin wannan aikin ya zo, zai yi kokarin hana shi tuwurin fito da jabu. A ekklesiyoyin nan da zai iya kawowa kalkashin ikon sa, zai sa a ga kamar an zubo da albarkar Allah ta musamman, za a ga kamanin babbar sha’awar addini. Jama’a da yawa za su yi farinciki cewa Allah yana aikata al’ajibai domin su, alhali aikin na wani ruhu ne dabam. Cikin kamanin addini, Shaitan zai so ya fadada aikinsa cikin Krista. BJ 461.1
Cikin falkaswa da yawa da aka yi cikin shekaru hamsin da suka gabata, an iske irin ikokin nan da za su yi aiki cikin manyan ayukan da za a yi nan gaba. Akwai nuna murna da garwaya gaskiya da karya ta yadda za a rudi mutane. Duk da haka kada a yaudare ka. Bisa ga maganar Allah yana da sauki a gane yanayin kungiyoyin nan. Duk inda mutane suka rabu da shaidar Littafin, suka juya daga gaskiyan nan bayyanannu masu bidar musun kai da rabuwa da duniya, sai mu sani cewa ba albarkar Allah a wurin. Kuma tawurin ma’aunin da Kristi kansa Ya bayar, “Bisa ga yayansu za ku sansanche su” (Matta 7:16), a bayyane yake cewa wadanan hidimomin ba aikin Ruhun Allah ba ne. BJ 461.2
Cikin gaskiyar maganarsa, Allah Ya bayana kansa ga mutane. Ga dukan wadanda suka karbe su, gaskiyan nan garkuwa ce daga rudun Shaitan. Rabuwa da gaskiyan nan ne ya bude kofa ga muguntan da ke yaduwa yanzu cikin addinai na duniyan nan. An manta da yanayin dokar Allah da muhimmancinta. Rashin fahimtar yanayi da dawama da wajibtar dokar Allah ya haifar da kura-kurai game da tuba da tsarkakewa, ya kuma kai ga rage darajar ibada cikin ekklesiya. Wannan ne asirin rashin Ruhun Allah da ikonsa cikin falkaswan zamanin mu. BJ 462.1
Cikin dariku dabam dabam, akwai mutane sannanu cikin ibadarsu da suka amince da wannan batun. Shehun mallami Edwards A. Park, game da matsalolin addini yanzu ya ce: “Wani tushen damuwa shi ne kin aiwatar da dokar Allah da ake yi. A zamanun da, shugabannin addini ne suke bayana ainihin addini,… Shahararrun masu wa’azinmu sun dinga ba da martaba ga jawabansu ta wurin bin kwatancin mai-gidan, su na kuma girmama dokar da umurninta da gargadinta. Su kan kuma maimaita cewa dokan nan hoton rashin aibin Allah ne, kuma cewa mutumin da ba ya kaunar dokar, ba ya kaunar bishara ke nan; gama dokar, da bisharar ma, madubi ne mai-bayana ainihin halin Allah. Matsalan nan na rabuwa da dokar Allah tana jawo wata matsalar kuma, ta rena muguntar zunubi da girmansa da ikonsa. Girman dokar daidai yake da girman rashin biyayya gare shi, … BJ 462.2
“Dangane da matsalolin da an rigaya an ambata akwai kuma hadarin rena adalcin Allah. Masu wa’azi yanzu sun cika son raba adalcin Allah da kaunarsa, a nutsar da kauna maimakon daukaka shi. Sabon yayin koyaswar addini yana raba abinda Allah ya hada ne. Dokar Allah nagarta ce ko mugunta? Nagarta ce. Ashe adalci nagarta ne, da shike shi adalci aiwatar da doka ne. Daga halin rena dokar Allah da adalcinsa, da rena girman da illar rashin biyayya, mutane nan da nan su kan shiga halin rena alherin da ya tanada kafara domin zunubi.” Ta hakanan bishara ta kan rasa anfanin ta da muhimmancinta a zukatan mutane, jima kadan kuma za su so ma su kawar da Littafin kan sa. BJ 462.3
Mallamai da yawa na addini suna koyar da cewa wai Kristi tawurin mutuwarsa ya warware dokar, kuma wai daga yanzu mutane suna da ‘yanci su dena boyayya gare ta. Akwai wadanda ke koyar da cewa dokan ma karkiya ce mai-tsanani, kuma sabanin bautar dokar, su na koyar da wani ‘yanci da ake samu kalkashin bisharar. BJ 463.1
Amma ba haka manzani da annabawa suka mai da dokar Allah ba. In ji Dawuda: “Zan yi tafiya kuma a sake; gama na bidi shaidun ka.” Zabura 119:45. Manzo Yakub wanda ya yi rubutunsa bayan mutuwar Kristi, ya kira dokoki goman “shari’an nan basarauchiya” da kuma “cikakkiyar shari’a, sahri’a ta yanchi.” Yakub 2:8; 1:25, mai-ruya kuma, shekaru hamsin bayan giciyewar, ya furta albarka kansu wadanan da ke wankin tufafinsu, dominsu sami iko su zo wurin itachen rai, su shiga kuma ta kofofi chikin birni.” Ruya 22:14. BJ 463.2
Zancen cewa Kristi tawurin mutuwarsa ya warware dokar Ubansa ba shi da tushe. Da zai yiwu a canja dokar ko kuma a warware shi, da bai zama wajibi ga Kristi ya mutu domin ya ceci mutum daga horon zunubi ba. Mutuwar Kristi, maimakon warware dokar, yana tabbatar da cewa ba za a iya sake ta ba ne, Don Allah ya zo domin “ya daukaka shari’a, ya maishe ta abin kwarjini” ne. Ishaya 42:21. Ya ce: “Kada ku zache na zo domin in warware Attaurat,” “Har sama da duniya su shude, ko wasali daya ko digo daya ba za su shude daga Attaurat ba.” Matta 5:17,18. Game da kansa kuma ya ce: “Murna ni ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika shari’arka tana chikin zuchiya ta.” Zabura 40:8. BJ 463.3
Dokar Allah, daga yanayinsa mara sakewa ne. Bayani ne na manufa da halin mai-ba da shi. Allah kauna ne, dokarsa kuma kauna ce. Muhimman kaidodinta biyu su ne kaunar Allah da kaunar mutane. “Kamna fa chikar shari’a che.” Romawa 13:10. Halin Allah adalci ne da gaskiya haka kuma yanayin dokar sa yake. Mai-zabura yace:“Shari’arka kuma gaskiya che.” “Dukan dokokin ka adilchi ne.” Zabura 119:172. Manzo Bulus kuma ya ce: “Shari’a tsatsarka che, doka kuma tsatsarka che mai-adilchi kwa, tagari che.” Romawa 7:12. Wannan dokar da ke bayana tunanin Allah da nufinsa dole za ta dawama kamar mai ba da ita. BJ 464.1
Aikin tuba da tsarkakewa ne su sasanta mutane da Allah ta wurin kawo su ga daidaituwa da kaidodin dokarsa. A cikin farko an halici mutum cikin surar Allah. Ya kasance cikin cikakkiyar daidaituwa da yanayin Allah da dokarsa kuma; an rubuta kaidodin adalci a zuciyarsa. Amma zunubi ya raba shi da mahalicinsa. Bai sake kasancewa cikin surar Allah ba. Zuciyarsa ta dinga yaki da kaidodin dokar Allah. “Domin himmatuwar ji ki gaba che da Allah, gama ba ta chikin biyayya da shari’ar Allah ba, ba ta iya kwa.” Romawa 8:7. Amma “Allah ya yi kamnar duniya, har abada Dansa, haifaffe shi kadai” domin mutum ya sasanta ga Allah. Tawurin adalcin Kristi za a iya mayas da mutum ga daidaituwa da Mahallicinsa. Dole a sabonta zuciyarsa tawurin alherin Allah; dole ya mallaki sabon rai daga sama. Wnnan canjin ne sabuwar haihuwa, wanda idan ba shi, Yesu ya ce “ba za ya shiga mulkin Allah ba.” BJ 464.2
Matakin farko don sasantawa da Allah shi ne amincewa an yi zunubi. “Zunubi shi ne ketaren shari’a” “Gama tawurin shair’a a ke sanin zunubi.” 1Yohanna 3:4; Romawa 3:20. Domin ya ga laifinsa, dole mai-zunubi ya gwada halinsa da babban ma’aunin adalci na Allah. Madubi ne da ke nuna cikar halin adalci ya kuma sa shi ya gane aibin na sa halin. BJ 464.3
Dokar ta na bayana ma mutum zunubansa, amma ba ta tanada magani. Yayin da ta na alkawalin rai ga mai-biyayya, ta na bayana cewa mutuwa ce rabon mai-ketarewa. Bisharar Kristi ce kadai za ta iya kubutar da shi daga kazantarwar zunubi. Dole ya tuba ga Allah, wanda dokarsa ce na ketare; ga kuma bada gaskiya ga Kristi da hadayarsa ta kafara. Ta hakanan ya ke samun gafarar zunubai da suka wuce, ya kuma zama mai-yanayi irin na Allah. Sai yaron Allah ne, da shike ya karbi ruhun karbuwa ta yadda ya ke cewa: “Abba, Uba.” BJ 464.4
Yanzu yana da ‘yanci ya ketare dokar Allah ke nan? Bulus ya ce: “Tawurin bangaskiya fa muna mai da shari’a wofi? Dadai! Ba haka ba, tabbatadda shari’a mu ke yi.” “Dadai! Mu da muka mutu ga zunubi, kaka za mu kara rayuwa a chiki?” Yohanna kuma ya ce: “Gama kamnar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban chiwo ba.” Romawa 3:31; 6:2; 1Yohanna 5:3. Chikin sabuwar haihuwar, ana kawo zuciya ga jituwa da Allah, yayin da ake sasanta ta da dokarsa. Sa’an da wannan babban canji ya faru cikin mai-zunubi, ya wuce daga zunubi zuwa cikin rai ke nan, daga zunubizuwa tsarki, daga ketare doka, da tawaye zuwa biyayya. Tsohuwar rayuwar rabuwa da Allah ta kare; sabuwar rayuwar sasantawa da bangaskiya da kauna ta fara. Sa’an nan “wajibin sharia” za “ya chika a wurinmu, mu wadanda ke tafiya ba bisa ga tabi’ar jiki ba, amma bisa ga ruhu.” Romawa 8:4. Sa’an nan maganar mutumin za ta zama: “Ina kamnar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.” Zabura 119:97. BJ 465.1
“Shari’a ta Ubangiji chikakkiya che, ta na mayas da rai.” Zabura 19:7. Idan ba doka mutane ba za su sami ganewar tsabta da tsarkin Allah ko ganewar laifinsu da rashin tsabtarsu ba. Ba su da ainihin sanin zunubi kuma ba sa jin bukatar tuba. Da shike ba sa ganin batawarsu na masu ketare dokar Allah, ba sa gane bukatarsu ta jinin kafara na Kristi. Ana karban begen ceto ba tare da sakewar zuciya ko rayuwa ba. Sabo da haka tuba mara zurfi ya yi yawa, kuma jama’a suna shiga ekklesiya alhali ba su taba haduwa da Kristi ba. BJ 465.2
Koyaswoyin kuskure game da tsarkakewa da ke tasowa daga rabuwa da dokar Allah suna da tasiri mai yawa cikin ayukan addini na zamanin nan. Koyaswoyin nan karya ne, kuma sakamakonsu akwai hatsari sosai, kuma karbuwan da su ke samu ko ina ya sa ya zama wajibi ga kowa shi sami kyakyawar fahimtar abin da Littafin ke koyarwa game da wannan batun. BJ 466.1
Ainihin tsakkakewa koyaswa ce ta Littafin. Manzo Bulus, cikin wasikarsa zuwa ga ekklesiyar Tasslunikawa ya ce: “Gama nufin Allah ke nan, tsarkakewar ku.” Sa’an nan ya yi addu’a cewa: “Allah kwa da kansa na salama, shi tsarkake ku sarai.” Tassalunikawa I, 4:3; 5:23. Littafin yana koyar da abin da ake nufi da tsarkakewa, a bayane da kuma yadda ake samunsa. Mai-ceton ya yi addu’a don almajiransa: “Ka tsarkake su chikin gaskiya: maganarka ita che gaskiya.” Yohanna 17:17. Bulus kuma yana koyar da cewa masu-ba da gaskiya za a tsarkake su tawurin Ruhu Mai-tsarki: (Romawa 15:16). Mene ne aikin Ruhu Mai-tsarki? Yesu ya ce ma almajiran; “Amma sa’an da shi, Ruhu na gaskiya, ya tafo, za ya bishe ku chikin dukan gaskiya.” Yohanna 16:13, Mai-zabura kuma ya ce: “shari’ar ka gaskiya ce.” Ta wurin maganar Allah da Ruhunsa ne ake bude ma mutane muhimman kaidodin adalci da ke kunshe cikin dokarsa. Kuma da shike dokar Allah mai-tsarki ce, da adalci da nagarta, kuma hoton rashin aibin Allahtaka ne, ya nuna cewa halin da aka samu tawurin biyayya ga dokar zai zama hali mai-tsarki. Kristi cikakken kwatanci ne na irin wannan halin.” Yace: “Na kiyaye dokokin Ubana.” “Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” Yohanna 15:10; 8:29. Ya kamata masu bin Kristi su zama kamarsa - tawurin alherin Allah su sami halaye da suka je daidai da kaidodin dokar sa mai-tsarki. Tsarkakewa bisa ga Littafin ke nan. BJ 466.2
Za a iya aiwatar da aikin tawurin bangaskiya ga Kristi ne kadai, tawurin ikon Ruhun Allah a cikinmu. Bulus ya fadakar da masu ba da gaskiya cewa: “Ku yi aikin chetonku da tsoro da rawan jiki, gama Allah ne yana aiki a chikinku da za ku yi nufi har ku aika kuma, zuwa abinda ya gamshe shi.” Filibiyawa 2:12,13. Kirista zai ji jarabar zunubi, amma zai yake shi kullum. Inda ake bukatar taimakon Kristi ke nan. Kumamacin mutuntaka yakan hadu da karfin Allahntaka, bangaskiya kuma ta kan ce: “Godiya ga Allah wanda ya ke ba mu nasara tawurin Ubangijinmu Yesu Kristi.” Korinthiyawa I, 15:57. BJ 466.3
Littafin yana nunawa a fili cewa aikin tsarkakewa ba na lokaci daya ba ne. Sa’anda a lokacin da ya tuba, mai-zunubi ya kan sami salama da Allah tawurin jinin kafarar, rayuwar Kiristancin ya fara ma ke nan kawai. Yanzu za ya ci gaba ne “zuwa chikakken mutum,” ya girma “Zuwa misalin tsawon chikar Kristi.” In ji Manzo Bulus: “Amma abu daya ni ke yi, ina manta abubuwan da ke baya, ina kutsawa zuwa wadanda ke gaba, ina nache bi har zuwa ga goni, ina kaiga ladan nasara na madaukakiyar kira ta Allah chikin Kristi Yesu.” Filibiyawa 3:13,14. Bitrus kuma ya bayana mana matakan da tawurinsu ne ake samun tsarkakewa. Ya ce: “Sai ku kara ba da kokari, chikin bangaskiyarku kuma, ku kawo halin kirki; chikin halin kirki kuma ilimi; chikin ilimi kuma kamawa, chikin kamewa kuma hankuri, chikin son-yanuwa kuma kamna,… gama idan kun yi wadannan abu, ba za ku yi tuntube ba dadai.” Bitrus II, 1:5-10. BJ 467.1
Wadanda suka sami tsarkakewa bisa ga Littafin za su nuna ruhun tawali’u. Kamar Musa, sun hangi martabar tsarki mai ban tsoro, suna kuma ganin rashin cancantar kansu sabanin tsabta da mafificiyar cikar Allah mara iyaka. BJ 467.2
Annabi Daniel kwatanci ne na tsarkakewa na kwarai. Rayuwarsa mai-tsawon nan ta cika da hidima ta kirki ga mai-gidansa. Shi “Kamnatache kwarai” ne (Daniel 10:11) na Allah. Duk da haka, cewa shi mai-tsarki ne mara-aibi kuma, annabin nan mai-tsarki ya hada kansa da ainihin masu-zunubi na Israila ya yin da ya ke roko a gaban Allah a madadin mutanensa, ya ce: “Ba mu zuba maka godon mu sabili da adilchin kanmu ba, amma sabili da manyan jiyejiyenkanka.” “Mun yi zunubi, mun aika mugunta.” Ya ce kuma: “Ina nan ina chikin magana, ina addu’a, ina furta zunubi na da zunubin mutanena.” Kuma sa’anda daga baya Dan Allah ya bayana, domin ya ba shi umurni, Daniel ya ce: “Jamali na ya juya a chikina ya zama ruba, ba ni da ringin karfi.” Daniel 9:18, 15,20; 10:8. BJ 467.3
Sa’anda Ayuba ya ji muryan Ubangiji daga cikin babban guguwa, ya ce: “Raina yana tagumi a chikina.” Ayuba 42:6. Sai lokacin da Ishaya ya ga darajar Ubangiji, ya kuma ji cherubim suna cewa “Mai-tsarki, Mai-tsarki ne, Ubangiji Mai-runduna” ne, ya ta da murya ya ce, “Kaitona! Gama na lalache.” Ishaya 6:3,5. Bulus bayan an fyauce shi zuwa sama ta uku ne, ya kuma ji ababan da bashi yiwuwa mutum shi furta, ya ce shi ne, “Koma bayan baya chikin tsarkaka duka.” Korinthiyawa II, 12:2-4, Afisawa 3:8. Yohanna kamnatacen nan da ya jingina a kirjin Yesu, ya ga darajarsa, shi ne ya fadi kamar matace a sawayen malaikan. Ruya 1:17. BJ 468.1
Ba wani daukakan kai, babu fahariyar cewa an kubuta daga zunubi ga wadanda ke tafiya a inuwar giciyen Kalfari. Su kan san cewa zunubinsu ne ya jawo azabar da ta karya zuciyar Dan Allah, kuma wannan tunanin zai sa su rena kan su. Wadanda sun fi kusa da Yesu sun fi gane kumamanci da yawan zunubin ‘yan Adam, kuma begensu kadai shi ne adalcin mai-ceto wanda aka giciye ya kuma tashi. BJ 468.2
Irin tsarkakewan da ke tashe a cikin addinin duniya yanzu yana tattare da ruhun girmama kai da rabuwa da dokar Allah, wanda ya nuna cewa tsarkakewan ya saba ma addini na Littafin. Masu wannan koyaswar suna koyar da cewa tsarkakewa abu ne na lokaci daya, farap daya, wanda tawurin bangaskiya kadai su ke samun cikakken tsarki. Su kan ce, “Kaba da gaskiya kawai, albarkar ta zama taka ke nan.” Wai ba a bidar wani kokari kuma daga wurin mai ba da gaskiyan.” A lokaci dayan kuma su na musun ikon dokar Allah, suna cewa wai an yantar da su daga takalifin kiyaye dokokin. Amma ko zai yiwu mutane su zama tsarkaka, bisa ga nufin Allah, da halinsa, ba tare da jituwa da kaidodin da ke bayana yanayinsa da nufinsa, suna kuma nuna bin da ke gamsar da shi ba? BJ 468.3
Son addini mai-sauki wanda ba ya bukatar kokari, ko musun kai, ko rabuwa da wawutar duniya, ya mai da koyaswar bangaskiya da bangaskiya kadai ya zama koyaswa mai farinjini sosai, amma mene ne maganar Allah ke cewa? In ji manzo Yakub: “Yan’uwana, idan mutum ya che yana da bangaskiya, amma ba shi da ayuka, mi ya anfana? Ko wannan bangaskiya ta iya chetonsa?... Amma ko za ka sani ya mutumen wofi, bangaskiya ba tare da ayuka bakarariya che? Ko ba tawurin ayuka uban mu Ibrahim ya barata ba, yayinda ya mika Ishaku dansa bisa bagadi? Ka gani fa bangaskiya ta aika tare da ayukansa, ta wurin ayuka kuma bangaskiya ta chika,… Kun gani fa ta wurin ayuka mutum ya barata, ba ta wurin bangaskiya kadai ba.” Yakub 2:14-24. BJ 469.1
Shaidar maganar Allah ba ta yarda da wannan koyaswa mai-kasada na bangaskiya ba tare da ayuka ba. Bangaskiya ba za ta sami karbuwar Allah ba, sai dai in ta cika sharuddan samun jinkai, in ba haka ba bangaskiyan nan ganganci ne, da shike ainihin bangaskiya yana da tushe a alkawura da tanade-tanaden Littafin ne. BJ 469.2
Har kuma suna rudin kansu cewa za su iya zama masu-tsarki yayinda suke ketare daya daga cikin umurnin Allah da gangan. Aikata zunubi da gangan ya kan bice muryan Ruhu ya kuma raba mutum da Allah. “Zunubi shi ne ketaren shari’a,” Kuma “Dukan wanda yake aika zunubi (ketaren shari’a) ba ya taba ganinsa ba, ba ya sonshi kuma.” Yohanna I, 3:6. Ko da shike Yohanna cikin wasikunsa yana magana da yawa game da kauna, duk da haka bai yi jinkiri ba wajen bayana ainihin yanayin wadanda ke cewa an tsarkake su alhali suna rayuwar ketare dokar Allah. “Wanda ya che, Na san shi, amma ba ya kiyaye dokokinsa ba, makaryachi ne, gaskiya kwa ba ta chikinsa ba; amma wanda yana kiyaye maganarasa, a chikinsa lallai kamanr Allah ta chika.” 1Yohanna 2:4,5. Wannan shi ne ma’aunin da’awar kowane mutum. Ba za mu iya kiran wani ma-tsarki, ba tare da an auna shi da ma’auni mai-tsarkin nan daya kadai na Allah, a sama da duniya ba. Idan mutane ba sa jin nauyin dokar Allah; idan suka kankantadda da umurnin Allah suka wofinta shi, idan sun ketare daya daga mafi-kankantan dokokin nan, suka kuma koya ma mutane hakanan, za su zama marasa martaba a ganin Allah, za mu iya ganewa kuma cewa da’awansu ba su da tushe. BJ 469.3
Kuma idan mutum ya ce bashi da zunubi kan shi ma wannan shaida ce cewa mutumin yana nesa da tsarki. Don ba shi da ainihin ganewar tsabta da tsarki mara matuka na Allah ne, ko kuma ganewar abin da ya wajibta masu son jituwa da halinsa su zama ne, domin mutumin fahimci ainihin tsabta da daukakar halin Yesu, da kuma tsananin muguntar zunubi ba ne, zai sa shi ya dauka cewa shi mai-tsarki ne. Yawan nisansa daga Kristi, da kuma yawan rashin ganewarsa na halin Allah da sharuddan sama suna daidai da yawan adalcinsa,. BJ 470.1
Tsarkakewa da aka shimfida cikin Littafin ya kunshi mutum dungum din sa ne: ruhu da rai, da jiki. Bulus ya yi ma Tassalunikawa addu’a cewa “ruhunku da ran ku da jikinku su zama a kiyaye sarai, ba abin zargi lokachin zuwan Ubangijinmu Yesu Kristi.” Tassalunikawa I, 5:23, ya kuma rubuta ma masu bada gaskiya cewa: “Ina rokonku fa, yan’uwa bisa ga jiyejiyenkai na Allah, ku mika jikunanku hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karba ga Allah, bautarku mai-ruhaniya ke nan.” Romawa 12:1. A zamanin Israila ta da, akan bincika kowane hadaya da aka kawo ma Allah, idan aka ga wani la’ani ko wata illa a jikin dabban, akan ki ta, domin Allah ya umurta cewa hadaya ta kasance mara aibi. Saboda haka ana umurta Kirista su mika jikunansu “hadaya mai-rai mai-tsarki abin karba ga Allah.” Domin yin wannan, dole su kiyaye kan su cikin yanayi mafi kyau. Duk wani abin da ke raunana karfin jiki ko karfin tunani ya kan hana mutum bautar mahalicinsa kuma ko Allah zai ji dadin wani abin da bai kai iyakar kokarinmu ba? Kristi ya ce: “Za ka kaunachi Ubangiji Allahnka da dukan zuchiyarka.” Wadanda ke kaunar Allah da dukan zuciya za su so su ba shi hidima mafi kyau na rayuwarsu, kuma za su yi ta kokarin yin anfani da kowane yanayinsu ga jituwa da dokokin da za su taimaka masu iya yin nufinsa, ba za su raunana ko su kazantar da hadayan da za su mika ma Uban su na sama ta wurin kwadayi ko yawan son dadi ba. BJ 470.2
Bitrus yace: “Ku hanu daga sha’awoyi na jiki wadanda ke yaki da rai.” Bitrus I, 2:11. Kowane zunubi da aka yi ya kan kangarar da tunani ya kashe ganewa na ruhaniya, kuma maganar Allah ko Ruhunsa ba za su yi tasiri sosai ga zuciyar ba. Bulus ya ce ma Korinthiyawa: “Bari mu tsarkake kanmu daga dukan kazamtar jiki da ta ruhu, muna kamala tsarki chikin tsoron Allah. Korinthiyawa II, 7:1. Kuma tare da diyan Ruhun — “Kamna (ne), farinchiki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminchi, tawali’u,” ya hada “kamewa” Galatiyawa 5:22,23. BJ 471.1
Duk da hurarrun nassosin nan, dubi yawan Kirista da ke nakasa kan su cikin neman arziki ko bautar salo ko yayi, dubi yawan masu rage darajar mazantakansu irin na ibada, ta wurin zarin ci da shan giya, da haramtaceyar anishuwa. Kuma ekklesiya, maimakon tsawatarwa, sau da yawa ta kan karfafa muguntar, ta wurin anfani da kwadayi da son riba ko son jin dadi don nema ma baitulamalinta kurdi, maimakon yin anfani da kaunar Kristi. Da Yesu zai shiga ekklesiyoyi na yau ya ga bukukuwa da hidimomi marasa tsarki da ake yi a ciki da sunan addini, ko ba zai kori masu kazantarwan nan yadda ya kori masu canjin kurdi da haikalin ba? BJ 471.2
Manzo Yakub ya ce hikima daga sama, “da fari dai mai-tsarki ne.” Da ya sadu da wadanda ke rike da sunan Yesu a lebuna, kazamtattu da taba da ta bata lumfashinsu, da jikunansu masu wari, suna kuma bata iskar sama, suna tilasta na kusa da su shaker gubar - da manzon ya sadu da halin nan da ke sabani da tsabtar bishara, ashe da bai ce halin nan na yan duniya ne, na rashin imani, halin iblisanci ba? Bayin taba ma su cewa an tsarkake su sarai, suna zancen begensu na zuwa sama, amma maganar Allah tana bayana cewa “ba kwa wani abu mara tsarki da za ya shiga ko kadan.” Ruya 21:27. BJ 471.3
“Ko ba ku sani ba jikinku haikali ne na Ruhu Mai-tsarki wanda ke chikinku, wanda kun karba daga wurin Allah? Ku kwa ba na kan ku ba ne; gama aka saye ku da tamani; ku daukaka Allah fa chikin jikinku.” Korinthiyawa I, 6:19,20. Shi wanda jikinsa haikali ne na Ruhu Mai-tsarki ba zai zama bawan wani halin banza ba. Lafiyarsa ta Kristi ce, wanda ya saye shi da farashin jini. Dukiyarsa ta Ubangiji ce. Ta yaya zai kubuta daga laifi idan ya watsar da wannan jarin da aka ba shi amana? Kirista kowace shekara su na kashe kurdi mai-yawa wajen ababa marasa anfani, alhali rayuka suna hallaka saboda maganar rai. Ana yi ma Allah kwace wajen zakkoki da sadakoki, yayin da su ke kashe dukiya wajen biyan kwadayin jikunansu fiye da abinda su ke bayarwa don taimaka ma matalauta ko bishara. Da dukan masu cewa suna bin Kristi tsarkakakku ne, da maimakon kashe dukiyarsu akan jin dadi mara anfani ko mai cutarwa ma za su sa ta cikin baitulmalin Ubangiji, Kirista kuma da sun kafa kwatancin kamewa, da musun-kai, da sadakar da kai. Sa’an nan ne za su zama hasken duniya. BJ 472.1
Duniya ta nutse cikin son jin dadi. “Sha’awa ta jiki, da sha’awa ta ido,” da fahariyar rai suna mallakar yawancin mutane. Amma masu-bin Kristi suna da kira mafi tsarki. “Ku fito daga chikinsu, ku ware, in ji Ubangiji, kada ku taba kowane abu mara-tsarki.” Bisa ga maganar Allah muna da ‘yanci mu ce tsarkakewa ba za ta kasance sahihiya ba, idan ba ta haifar da rabuwa da ayukan zunubi da sha’awoyin duniya ba. BJ 472.2
Ga wadanda suka cika sharuddan nan, “Ku fito daga chikinsu ku ware,… kada ku taba kowane abu mara-tsarki,” alkawalin Allah shi ne: “Ni ma in karbe ku, in zama Uba gareku, ku za ku zama ‘ya’ya maza da mata gareni, in ji Ubangiji Mai-iko duka.” Korinthiyawa II, 6:17,18. Zarafi da takalifin kowane Kirista ne ya sami mawadacin dandano mai-yawa cikin al’ammuran Allah. Yesu Ya ce: “Ni ne hasken duniya; wanda yana biyona ba za shi yi tafiya chikin dufu ba, amma za ya sami hasken rai.” Yohanna 12:8. “Amma tafarkin mai-adilchi yana kama da hasken ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa chikakkiyar rana.” Misalai 4:18. Kowane matakin bangaskiya da biyayya yana kawo mutum zuwa dangantaka na kusa kusa da hasken duniya, wanda babu duhu a cikinsa ko kadan. Tsirkiyoyin hasken Ranar Adilchi suna haskaka bayin Allah, su kuma ya kamata su bayana tsirkiyoyin na sa. Kamar yadda taurari su ke fada mana cewa akwai babban haske a sama wanda darajarsa ce ta ke sa su haskakawa, hakanan ne ya kamata Kirista su sa a gane sarai cewa akwai Allah a bisa kursiyin dukan halitta wanda halin sa ya isa yabo da kwaikwayawa. Albarkun Ruhunsa, da tsarki da tsabtar halinsa za su bayana cikin shaidunsa. BJ 472.3
Bulus cikin wasikarsa zuwa ga Kolosiyawa ya bayana manyan albarkun da ake ba ‘ya’yan Allah. Ya ce: “Ba mu fasa yin addu’a da roko dominku ba, ku chika da sanin nufinsa chikin dukan hikima mai-ruhaniya da fahimi kuma, da za ku yi tafiya wadda ta chanchanta ga Ubangiji, kuna gamshe shi sarai, kuna ba da yaya chikin kowane kyakkyawan aiki, kuna karuwa kuma chikin sanin Allah; karfaffafu da dukan iko, bisa ga ikon daukakarsa, zuwa dukan hankuri da jimrewa tare da farinchiki.” Kolosiyawa 1:9-11. BJ 473.1
Ya kuma rubuta game da fatarsa cewa ‘yan-uwa da ke Afisus su fahimci girman gatancin Kirista. Ya bayana masu iko da sani na ban mamaki da za su iya samu kamar ‘ya’yan Madaukaki. Gatarsu ce “a karfafa (su) da iko tawurin Ruhunsa chikin mutum na chiki,” su zama “dasassu ne kafaffu kuma chikin kamna,” su “ruska tare da dukan tsarkaka, ko minene fadin da ratar da tsawon da zurfin kamnar Kristi, ku sani kuma kamnar Kristi wadda ta wuce gaban a san ta.” Amma addu’ar manzon ta kai makurar gatar, inda ya yi addu’a cewa: “domin ku chika har zuwa dukan chikar Allah.” Afisawa 3:16-19. BJ 473.2
Nan an bayana girman matsayin da za mu iya kaiwa ta wurin bangaskiya cikin alkawuran Ubanmu na sama, sa’an da mun cika sharuddansa. Ta wurin cancantar Kristi, muna da hanyar zuwa kursiyin iko Mara-iyaka. “Wanda baya kebe Da na sa ba, amma ya bashe shi domin mu duka, kaka za ya rasa ba mu abu duka kuma tare da shi a yalwache?” Romawa 8:32. Uban Ya bada Ruhunsa ga Dansa a yalwace, mu ma kuma za mu iya samun moriyar cikar Ruhun. Yesu ya ce: “Idan ku fa da kuke miyagu kun san yadda za ku ba yayanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga wadanda su ke rokonsa?” Luka 11:13. “Idan kun roke ni komi a chikin sunana, ni yi wannan.” “Ku yi roko, za ku karba, domin farinchikinku ya chika.” Yohanna 14:14; 16:24. BJ 474.1
Yayin da rayuwar Kirista za ta kasance ta tawali’u, bai kamata ta cika da bakinciki ba. Gatancin kowa ne ya yi rayuwa ta yadda Allah zai gamsu, Ya kuma yi masa albarka. Ba nufin Ubanmu na sama ne mu taba kasancewa kalkashin hukumci da duhu ba. Ba shaidar tawli’u idan ana tafiya da kai a sunkuye amma zuciya cike da tunanin son kanmu. Za mu iya zuwa wurin Yesu a tsarkake mu, mu kuwa tsaya gaban shari’a, ba kunya ko nadama. “Babu hukumci fa yanzu ga wadanda ke cikin Kristi Yesu, wadanda ke tafiya, ba bisa jiki ba, amma bisa ga Ruhu.” Romawa 8:1. BJ 474.2
Tawurin Yesu, fadaddun ‘ya’yan Adamu suna zama ‘ya’yan Allah. “Gama shi mai-tsarkakewa da su wadanda aka tsarkake su duk daga mafari daya ne; domin wannan fa a gare shi ba wani abin kunya ba ne shi che da su yan’uwa.” Ibraniyawa 2:11. Ya kamata rayuwar Kirista ta zama ta bangaskiya, ta nasara, da murna cikin Allah. “Gama kowane haifaffe daga wurin Allah yana yin nasara da duniya; nasara wadda ta chi duniya ke nan, bangaskiyarmu.” 1Yohanna 5:4. Nehemiah bawan Allah ya ce: “Farinchiki na Ubangiji shi ne karfinku.” Nehemiah 8:10. Bulus kuma ya ce: “Ku yi farinchiki chikin Ubangiji kullayomi; sai in sake chewa, ku yi farinchiki.” “Ku yi murna kullum; ku yi addu’a ba fasawa; chikin kowane abu a ba da godiya; gama shi ne nufin Allah gareku chikin Kristi Yesu.” Filibiyawa 4:4; 1Tassalunikwa 5:16-18. BJ 474.3
Irin ‘ya’yan tuba da tsarkakewa irin na Littafin ke nan; kuma don Kirista suna daukan muhimman kaidodin adalci da aka bayana cikin dokar Allah da rashin kulawa ne ya sa ba a cika ganin ‘ya’yan nan na tuba da tsarkakewa ba. Shi ya sa aikin nan mai-zurfi na Ruhun Allah da ya rika samuwa wajen falkaswa na shekarun da bai cika ganuwa sosai ba yanzu. BJ 475.1
Tawurin dubawa muke sakewa. Kuma sa’anda ake rabuwa da umurnin nan masu-tsarki inda Allah ya bude ma mutane cika da tsarkin halinsa, zukatan mutane kuma suna jawuwa zuwa koyaswoyi da ra’ayoyin mutane, ba abin mamaki ba ne aka iske raguwar ainihin ibada cikin ekklesiya. Ubangiji ya ce: “Sun yashe ni, ni mabulbular ruwaye masu rai, sun gina ma kansu runduna hadaddu, wadanda ba su rike ruwa ba.” Irmiya 2:13. BJ 475.2
“Mai-albarka ne mutum wanda ba ya bi ta shawarar miyagu ba,… Amma marmarinsa chikin shari’a ta Ubangiji yake, kuma a chikin shari’assa yakan rika tunani dare da rana. Za ya zamna kamar itachen da aka dasa a magudanar ruwaye wanda yana ba da yayansa a chikin kwanakinsa; ganyensa ba ya yi yaushi ba, kuma chikin iyakar abinda yake yi za shi yi albarka.” Zabura 1:1-3. Sai an mayas da dokar Allah ga ainihin matsayinsa ne za a iya samun falkaswar bangaskiya da ibada na da cikin mutanensa. In ji Ubangiji, “Ku tsaya a chikin hanya sosai, ku gani, ku tambayi hanyoyi na da inda hanyar kirki ta ke, ku yi tafiya a chiki, za ku sami hutawa domin rayukanku.” Irmiya 6:16. BJ 475.3