Annabi Daniel yace: “Ina nan ina dubawa, har na ga an kafa kursiyai, wani kuma wanda shi ke Mai-zamanin da yana zamne: tufafinsa fari fat kamar snow suke: gashin kansa kuma kamar tsatsabtar ulu, kursiyinsa harsunan wuta ne mai-chi. Rafi mai-kamar wuta ya tasa ya fito kuma daga gabansa: dubban dubbai kuma sun a yi masa hidima; zambar goma kuma so zambar goma suna tsaye a gabansa; aka kafa shari’a aka bude littattafai.” Daniel 7:9,10. BJ 476.1
Haka aka bayana ma annabin babban ranan nan mai-saduda da halayen mutane da rayuwarsu za su gurbana a gaban mai-shari’an dukan duniya, za a kuma ba kowane mutum gwalgwadon ayukansa. Mai-zamanin Da Allah Uba ne. Mai-zabura ya ce: “Tun ba a bullo da duwatsu, tun ba ka ko sifanta kasa da duniya, tun fil’azal kai ne Allah har abda.” Zabura 90:2. Shi tushen dukan kowane abu, mabulbulan kowace doka, Shi ne zai zama shugaban shari’ar. Malaiku masu tsarki kuma a matsayin ‘yan hidima da shaidu, da yawan su ya kai dubban dubbai da zambar goma so zambar goma, za su halarci zaman shari’ar. BJ 476.2
“Ga shi tare da gizagizan sama wani ya zo mai-kama da dan mutum ya zo kuma, har wurin mai-zamanun da, aka kawo shi a gabansa har ya yi kusa. Aka ba shi sarauta da daraja, da mulki, domin dukan al’ummai, da dangogi, da harsuna su bauta masa; sarautassa madauwamiya che, wadda ba za ta shude ba.” Daniel 7:13,14. Zuwan Kristi da a ke magana a kai a nan ba zuwansa na biyu a duniya ba ne. Zai zo wurin mai-zamanin Da a sama ne domin shi karbi sarauta da mulki, wanda za a ba shi a karshen aikin sa na matsakanci. Wannan zuwan ne, ba zuwan sa na biyu a duniya ba da annabci ya ambata cewa zai faru a karshen kwane 2300 din nan a 1844. Tare da malaiku na sama, babban priest na mu zai shiga wuri mafi tsarki inda za ya bayana a gaban Allah domin shi yi aikin shari’a ta bincike ya kuma yi kafara domin dukan wadanda suka cancanci kafara. BJ 476.3
A hidima ta misalin, wadanda suka zo gaban Allah da tuba da furta zunubi ne kadai wadanda aka gafarta zunuban su. Ta wurin jinin hadaya ta zunubi wanda aka yayafa a haikalin ne sukan shiga hidimar Ranar kafara. Hakanan a baban ranan nan na kafara ta karshe da shari’a ta bincike al’amuran da za a bincika na wadanda ke cewa su mutanen Allah ne kadai. “Shari’a za ta faru a kan gidan Allah; idan kwa a wajenmu ta faru, ina matukar wadanda basu bi bisharar Allah ba?” 1Bitrus 4:17. BJ 477.1
Littattafan da ke sama, inda a ke, rubuta sunaye da ayukan mutane, su ne za su nuna hukumcin da shari’ar ta yanka. Annabi Daniel ya ce: “An bude wani littafi kuma, littafin rai ke nan: aka yi ma matattu shari’a kuma bisa ga abinda aka rubuta chikin litattafai, gwalgwadon ayukan su.” Ruya 20:12. BJ 477.2
Littafin rai ya kunshi sunayen dukan wadanda su ka taba shiga bautar Allah, Yesu ya ce ma almajiransa: “Ku yi murna saboda an rubuta sunayenku chikin sama.” Luka 10:20. Bulus yana magana game da amintattun abokan aikinsa “wadanda sunayensu ke chikin littafin rai.” Filibbiyawa 4:3. Daniel yayin da yake kallon “kwanakin wahala irin da ba a taba yi ba” ya ce za a ceci mutanen Allah, “kowane daya wanda aka iske shi a rubuche chikin littafin.” Mai-ruyan kuma ya ce wadanda “an rubuta su chikin litafin rai na Dan rago” ne kadai za su shiga birnin Allah. Daniel 12:1; Ruya 21:27. BJ 477.3
Akwai littafin tunawa da aka rubuta a gaban Allah, inda aka rubuta, kyawawan ayukan “wadanda su ke jin tsoron Ubangiji, masu tunawa da sunansa.” Malachi 3:16. Kalmomin su na bangaskiya, ayukan su na kauna, suna rubuce a sama. Nehemiah ya yi magana game da wannan sa’an da ya ce: “Ka tuna da ni, ya Allahna,… kada kwa ka shafe aikin nagarta da na yi sabili da gidan Allahna.” Nehemiah 13:14. A chikin littafin tunawa na Allah ana rubuta kowane aikin nagarta. A cikinsa, kowace jaraba da aka yi nasara a kai, kowace mugunta da aka yi nasara da ita, kowace kalmar tausayi da aka furta, suna nan a rubuce, ba kuskure. Kuma kwane aikin sadakarwa, kowace wahala da bakinciki da aka jimre saboda Kristi yana nan a rubuce. Mai-zabura ya ce: “Kana lissafin yawache-yawachena; ka sa hawayena chikin garanka; ba a chikin litafinka su ke ba? Zabura 56:8. BJ 478.1
Ana kuma rubuta zunuban mutane. “Gama Allah za ya kawo kowane aiki wurin shari’a, da dukan aisirin rai, domin shi raba, ko nagari ne, ko mugu.” “Kowace maganar banza da mutane ke fadi, a chikin ranar shari’a za su ba da lissafinta.” Mai-ceton ya ce: “Bisa ga zantattukanka za ka barata, bisa ga zantattukanka kuma za a kashe ka.” Mai-wa’azi 12:14; Matta 12:36,37. Tunani da manufofi da ke cikin zuciya ma suna cikin rajista; gama Allah “za ya tone boyayyun al’amura na dufu, ya bubbude shawarwarin zukata a sarari.” Korinthiyawa I, 4:5. “Ga shi, a gabana yake a rubuche:… naku laifofi da laifofin ubanninku tare, in ji Ubangiji.” Ishaya 65:6,7. BJ 478.2
Aikin kowane mutum yana wucewa a gaban Allah mai-bincikewa kuma yana rubuce, ko aminci ne ko rashin aminci. A gefen kowace suna a litattafan sama ana rubuta kowace kalma mara dacewa, kowane aikin son kai, kowane aikin da aka ki yi, da kowane zunubi na boye. Ana rubuta kowace fadaka daga sama da aka kyale, lokaci da aka bata, zarafi da aka ki anfani da shi, tasiri da aka yi anfani da shi don alheri, ko mugnta, da dukan sakamakonsa, dukansu malaika yana rubutawa. BJ 479.1
Dokar Allah ce ma’aunin da za a yi anfani da ita don auna halaye da rayuwar mutane lokacin shari’a. Mai-hikima ya ce: “Ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama Allah za ya kawo kowane aiki wurin shari’a.” Mai-wa’azi 12:13.14. Manzo Yakub ya gargadi yan-uwansa: “Haka za ku yi Magana, haka za ku aika kuma, kamar mutane wadanda za a yi masu shari’a bisa ga shari’a ta yanchi.” Yakub 2:12. BJ 479.2
Wadanda a lokacin shari’a aka iske sun cancanta za su kasance cikin masu tashin adilai. Yesu ya ce: “Amma su wadanda an maishe su sun isa su kai wanchan zamani da tashi kuma daga matattu,… sun zama daidai da malaiku; yayan Allah su ke kwa, da shi ke yayan tashin matattu ne.” Luka 20:35,36. Ya kuma ce: “Wadanda sun yi nagarta za su fito zuwa tashi na rai.” Yohanna 5:29. Ba za a ta da matattun masu adalci ba sai bayan shari’a inda za a hukunta cewa sun isa tashi na rai. Sabo da haka ba za su kasance a wurin shari’an da kansu ba yayin da ake bincika halayensu daga litattafan, ana kuma hukumta su. BJ 479.3
Yesu za ya bayyana a matayin lauyansu, domin Ya yi roko a madadinsu a gaban Allah. “Idan kowa ya yi zunubi, muna da mai-taimako wurin Uba, Yesu Kristi mai-adalchi.” 1Yohanna 2:1. “Gama Kristi ba ya shiga chikin wani wuri mai-tsarki wanda aka yi da hannuwa ba, mai-kama da gaskiya ga zanchen fasali, amma chikin sama kanta, shi bayana a gaban fuskar Allah sabili da mu yanzu.” “Domin wannan kwa yana da iko ya yiwo cheto ba iyaka domin wadanda ke kusantuwa ga Allah ta wurinsa, da shike kullum a raye yake domin yin roko sabili da su.” Ibraniyawa 9:24; 7:25. BJ 479.4
Sa’anda an bude littattafan a lokacin shari’a rayuwan dukan wadanda suka ba da gaskiya ga Yesu zai zo gaban Allah domin bincike. Kuma daga wadanda suka fara rayuwa a duniya Mai-taimakonmu zai gabatar da maganar kowace sara bi da bi, zai kuma karasa da masu-rai. Zai ambaci kowane suna, a bincika kowace magana, da kyau. Za a karbi sunaye, za a ki sunaye kuma. Wadanda su ke da zunuban a littafin, wadanda ba su tuba sun bari an kuma gafarta ba, za a share sunayensu daga littafin rai, kuma za a share rubutattun nagargarun ayukansu daga littafin tunawa na Allah. Allah ya ce ma Musa: “Wanda ya yi zunubi gareni duka, shi ne zan shafe daga chikin litafina.” Fitowa 32:33. Annabi Ezekiel kuma ya ce: “Amma lokachin da adili ya juya ga barin adilchinsa, ya yi ta aikin mugunta,… ba za a tuna da ayukansa na adilchi da ya yi ko daya ba.” Ezekiel 18:24. BJ 480.1
Dukan wadanda sun tuba da gaske daga zunubi, tawurin bangaskiya kuma suka amshi jinin Kristi ya zama hadayar kafararsu, an rubuta yafewa a sunansu a cikin litattafan sama, da shike sun zama masu cin moriyar adalcin Kristi, an kuma iske halayyansu sun je daidai da dokar Allah, za a shafe zunubansu, su kansu kuma za a ga sun isa samun rai na har abada. Ubangiji ta bakin annabi Ishaya Ya ce: “Ni, i, ni ne na shafe laifofinka sabili da kaina; ba ni kwa kara tuna da zunubanka ba.” Ishaya 43:25. Yesu ya ce: “wanda ya yi nasara za a yafa shi hakanan da fararen tufafi; ba ni kwa shafe sunansa daga chikin litafin rai ba dadai, zan kuma shaida sunansa a gaban Ubana, da gaban malaikunsa.” “Ko wanene fa da za ya shaida ni a gaban mutane, shi zan shaida a gaban Ubana wanda ke chikin sama kuma. Amma dukan wanda za ya yi musun sani na a gaban mutane, shi zan yi musunsa a gaban Ubana wanda ke chikin sama kuma.” Ruya 3:5; Matta 10:32,33. BJ 480.2
Hankali mafi-zurfi da mutane kan ba hukumcin kotunan duniya dan kankanin alama ne na hankalin da kotunan sama za su jawo sa’anda sunayen da aka rubuta a littafin rai za su bayana gaban mai-shari’an duniya domin bincike. Matsakancin yana roko cewa a gafarta zunuban dukan wadanda su ka yi nasara ta wurin bangaskiya cikin jininsa, a mayas da su gidansu na Adnin, a kuma daura masu rawanin sarauta tare da shi. Mikah 4:8. Shaitan cikin kokarinsa na rudin ‘yan Adam da jarabtarsu ya so ya lalata shirin Allah don halitar mutum; amma yanzu Kristi yana roko cewa a aiwatar da shirin kamar mutum bai taba faduwa ba. Yana roko ma mutanensa yafewa da barataswa cikakku, da rabo cikin darajarsa da kujera a kursiyinsa kuma. BJ 480.3
Yayinda Yesu yake roko domin mutanensa, Shaitan yana zarginsu a gaban Allah cewa masu ketare doka ne su. Mai-rudun ya so ya ja su zuwa shakka, ya sa su dena amincewa da Allah, su raba kansu da kaunarsa, su kuma ketare dokarsa. Yanzu kuma yana nuna rayuwan da su ka yi da aibin halayensu, da rashin kamaninsu da Kristi, wanda ya rage darajar mai-fansarsu, da dukan zunuban da ya jarabce su su ka aikata, saboda wadannan kuma yana cewa su bayinsa ne. BJ 481.1
Yesu bai bada hujja domin zunubansu ba, amma yana nuna hakurinsu da bangaskiyarsu, kuma yana rokon gafara dominsu, yana nuna ma Uban da malaiku masu-tsarki hannuwansa da aka huda, yana cewa; na san su da sunayensu. Na rubuta su a tafin hannuwana. “Hadayu na Allah karyayyen ruhu ne; karyayyar zuchiya mai-tuba ba za ka rena ta ba, ya Allah.” Zabura 51:17. Ga mai-zargin mutanensa kuma ya ce: “Ubangiji shi tsauta maka, ya Shaitan, i, Ubangiji wanda ya zabi Urushalima shi tsauta maka; wannan ba konannen itace ba ne da aka chiro daga chikin wuta?” Zakariya3:2. Kristi zai suturta zabbabunsa da adalchin kansa, domin ya gabatar da su ga Ubansa “ekklesiya mai-daraja, ba tare da aibi ko chira ko kowane abu misalin wadannan.” Afisawa 5:27. Sunayensu suna rubuce cikin littafi na rai, game da su kuma an ce: “Za su yi tafiya tare da ni a yafe da fari; gama sun isa.” Ruya 3:4. BJ 481.2
Ta haka ne za a tabbatar da cikawar sabon alkawalin nan: “Zan gafarta muguntassu, bani kwa kara tuna da zunubinsu ba.” “A chikin wadannan kwanaki, a loton nan kuma, in ji Ubangiji, za a nemi a ga laifin Israila, a rasa; za a nemi a ga zunubban Yahuda, ba za a iske ba.” Irmiya 31:34; 50:20. “A chikin ranan nan dashe na Ubangiji za ya yi jamali ya yi daraja, anfanin kasa kuma za ya kasanche kyakyawa mai-ado domin wadanda su ke tsira na chikin Israila. Za ya zama kuma shi wanda ya rage chikin Sihiyona, da shi wanda ya wanzu chikin Urushalima, za a che da shi mai-tsarki, watau kowane dayan da aka rubuta shi chikin masu-rai na Urushalima.” Ishaya 4:2,3. BJ 482.1
Aikin shari’a ta bincike da shafewar zunuban nan za a kamala shi kafin zuwan Ubangiji na biyu. Da shike za a sharanta matattu daga ababan da aka rubuta cikin litattafan ne, ba zai yiwu a shafe zunuban mutane ba sai bayan shari’ar, inda za a bincika rayuwarsu. Amma manzo Bitrus ya fada a fili cewa za a shafe zunuban masu ba da gaskiya “domin hakanan wokatan wartsakewa daga wurin Ubangiji su zo; domin kuma shi aiko Kristi.” Ayukan 3:19,20. Sa’an da shari’ar binciken ta kare, Kristi za ya zo, ladarsa kuma tana tare da shi da zai ba kowa gwalgwadon ayukansa. BJ 482.2
A hidima ta kwatanci, babban priest, bayan ya yi kafara domin Israila, yakan fito ya albarkaci jama’a. Hakanan Kristi a karshen aikinsa na Matsakanci, za ya bayana kuma, ban da zunubi, zuwa ceto (Ibraniyawa 9:28), domin Ya alabrkaci mutanensa da ke jira, da rai madawami. Kamar yadda priest yayin da yake cire zunubai daga haikalin yakan furta su a bisa kan bunsurun Azazel, hakanan Kristi zai jibga dukan zunuban nan a kan Shaitan tushen zunubi, mai-ingizawa a aikata shi kuma. A kan kai bunsurun Azazel, dauke da zunuban Israila, can cikin wata kasa inda babu kowa ne (Levitikus 16:22), hakanan Shaitan, dauke da laifin dukan zunuban da shi ya sa mutanen Allah su ka yi, za a kange shi har shekaru dubu a duniyan nan, wadda a lokacin kango ne, babu kowa a ciki, a karshe kuma zai sha cikakken horon zunubi cikin wutan da zai hallaka dukan miyagu. Ta hakanan babban shirin nan na fansa zai cika sa’anda aka kawar da zunubi aka kuma kubutar da dukan wadanda suka kasance a shirye su rabu da mugunta. BJ 482.3
A lokacin da aka shirya domin hukuncin-karshen kwana 2300 din a 1844 aikin bincike da shafawar zunubai ya fara. Dukan wadanda suka taba dauka ma kansu sunan Kristi dole za a bincika su sosai. Za a hukunta mattattu da masu rai daga ababan da aka rubuta a cikin littattafan, bisa ga ayukansu. BJ 483.1
Zunjuban da ba a tuba daga gare su aka rabu da su ba, ba za a yafe a kuma shafe su daga litattafan ba, amma za su zama shaida akan mai-zunubin a rana ta Allah. Ko da hasken rana ne, ko cikin duhun dare ne ya aikata, muggan ayukansa, a bayane suke a gaban mai-shari’an. Malaikun Allah sun shaida kowane zunubi, sun ka kuma rubuta shi ba kuskure. Ana iya boye zunubi, a rufe shi, a yi musun shi a luluba shi daga sanin uba ko kuwa mata, da yara, da abokai, watakila mai-zunubin ne kadai ya san ya aikata, amma a bayane yake a gaban mazamnan sama. Duhun dare, da sirrin kowace dabarar rudu, basu isa su lulluba ko tunani daya ba daga wurin Allah. Allah yana da cikakken rahoton kowane rashin adalci da kowane rashin gaskiya. Kamanin ibada ba ya rudinsa. Ba Ya kuskuren sansance halin mutum. Masu mugunta a zuciya za su iya rudin wadansu, amma Allah yana zarce kowane rudu Ya karanta rayuwa ta cikin mutum. BJ 483.2
Wannan abin tsoro ne. Kowace rana tana da rahoton ta a littattafan sama. Kalmomin da aka taba fadi, ayukan da aka taba aikatawa, ba za a iya janye su ba. Malaiku sun yi rajistan nagarta da mugunta duka. Mayaki mafi shahara a duniya ba zai iya janye rahoto ko na rana daya ba. Ayukanmu da kalmominmu, har ma da manufofin zukatanmu suna da anfaninsu game da sansance matsayinmu, ko mai-kyau ko mara kyau. BJ 483.3
Ko da mu mun manta ma za a yi anfani da su don kubutarwa ko hukuntawa. Halin kowa yana bayane a sarari da aminci cikin littattafan sama. Duk da haka ba a cika kula rahoton nan da mazamana sama za su duba ba. In da za a cire labulen da ke raba abinda ake gani da wanda ba a gani a duniyan nan, ‘yan Adam kuma su ga malaika yana rubuta kowace kalma da al’amari da dole za su sake saduwa da su a lokacin shari’a, da ba a furta wadansu kalmomin, da kuma ba a aikata wadansu ayukan. BJ 484.1
A lokacin shari’ar za a bincika anfanin da ake yi da kowane talent, yaya mu ka yi anfani da jarin da Allah Ya ba mu rance? Ko mun kyautata kwarewan da aka ba mu amana ta hannu da zuciya da kwakwalwa domin daukakar Allah da alabrka ga duniya? Yaya mu ka yi anfani da lokacinmu da alkalaminmu, da muryarmu, da kurdinmu, da tasirinmu? Me mu ka yi ma Kristi, a matsayin matalauci da wahalalle da maraya da gwamruwa? Allah Ya mai da mu masu rikon maganarsa mai-tsarki, me muka yi da haske da kuma gaskiyan da aka ba mu domin mu sa mutane su zama da hikima zuwa ceto? Furcin cewa muna da bangaskiya cikin Kristi kawai ba shi da wani anfani, kaunan da ake nunawa tawurin ayuka ne kadai ke da anfani. Duk da haka kauna ce kadai ke sa ayuka su zama da anfani a ganin Allah. Duk abinda aka yi saboda kauna, komi kankantansa a ganin mutane, Allah ya kan karba Ya ba da ladansa. BJ 484.2
Boyayyen son kan mutane yana bayane a litattafan sama, a ciki ma an rubuta ababan da ya kamata a yi ma mutane amma ba a yi ba, da ababan da Mai-ceto Ya ce a yi amma aka manta. Can kuma za a ga yadda sau da yawa aka ba Shaitan lokaci da tunani da karfin da ya kamata a yi anfani da su domin Yesu. Abin bakinciki ne rahoton malaikun nan a sama. Masu tunani, masu cewa suna bin Kristi, sun dukufa neman kayan duniya ko jin dadin duniya. Ana kashe kurdi da lokaci da karfi domin jin dadi, da nuna isa; amma lokaci kadan a ke anfani da shi don addu’a da binciken Littafin da kaskantar da kai da furta zunubi. BJ 484.3
Shaitan yana kirkiro dabaru da yawa don mallakar tunaninmu, domin kada mu yi binbinin aikin da ya kamata mu fi saninnsa. Ya ki jinin muhimman gaskiya da ke bayana hadaya ta kafara da matsakanci mai-cikakken iko. Ya san cewa a gareshi wajibi ne ya kawar da tunanin mutane daga Yesu da gaskiyarsa. BJ 485.1
Wadanda ke so su mori anfanin tsakonin mai-ceton, kada su bar wani abu ya tsoma baki cikin kokarin su na cikakken tsarki a tsoron Allah. Maimakon bata lokaci wajen jin dadi da nuna isa da neman abin duniya, sai a yi anfani da lokacin don naciya wajen addu’a da nazarin maganar gaskiya. Ya kamata mutanen Allah su fahimci batun haikali da shari’a ta bincike da kyau. Kowa yana bukatar sanin matsayi da aikin Babban priest dinsa. In ba haka ba, ba zai yiwu masu su yi bangaskiyar da ya wajibta a wannan lokaci ko kuma su dauki matsayin da Allah ya shirya masu su dauka ba. Kowane mutum akwai rai da zai kawo ga ceto ko kuma ya batar. Kowa yana da shari’a a gaban Allah. Dole kowa ya fuskanci babban Mai-shari’an fuska da fuska. Don haka wajibi ne kowa ya dinga bimbinin lokacin nan da za a fara shari’ar a kuma bude litattafai, sa’anda tare da Daniel, dole kowane mutum shi tsaya a cikin rabonsa a karshen kwanaki. BJ 485.2
Dukan wadanda sun sami haske game da batutuwan nan ya kamata su shaida gaskiyan da Allah Ya ba su. Haikali na sama shi ne cibiyar aikin Kristi a madadin mutane. Ya shafi kowane mai-rai da ke duniya, yana bayana shirin fansa, ya kawo mu har karshen lokaci, yana bayana batun nasaran nan game da jayayya tsakanin adalci da zunubi. Wajibi ne kowa ya bincika ababan nan da kyau ya kuma iya ba da amsa ga duk wanda ya tambaye su dalilin begen da ke cikinsu. BJ 485.3
Shiga tsakanin da Kristi ke yi a madadin mutum a haikalin sama wajibi ne ga shirin ceto daidai da mutuwarsa a kan giciye. Ta wurin mutuwarsa ya fara aikin nan da bayan tashinsa ya koma sama domin ya karasa. Dole ta wurin bangaskiya mu shiga bayan labulen, “inda Yesu kamar shugaba ya shiga dominmu” Ibraniyawa 6:20. Can ne haske daga Kalfari ke haskakawa. Can ne za mu sami karin haske game da asiran fansa. An aiwatar da ceton mutum da tamani mai-tsada mara matuka ga sama, hadayar da aka yi daidaita ke da fadin bukatun dokar Allah da aka ketare. Yesu ya bude hanya zuwa kursiyin Uban, kuma ta wurin tsakancinsa za a mika ma Allah ainihin burin dukan masu zuwa wurinsa cikin bangaskiya. BJ 486.1
“Wanda ya rufe laifofinsa ba za ya y i albarka ba, amma dukan wanda ya fade su, ya kwa rabu da su za ya sami jinkai.” Misalai 28:13. Wadanda ke boye zunubansu, suna kuma ba da hujja game da zunuban nasu, in da sun san yadda Shaitan ke jin dadinsu, yana yi ma Krisit da malaiku masu tsarki ba’a saboda halin nan nasu, da za su hanzarta fadin zunubansu su kuma rabu da su. Ta wurin lahani a halin mutum Shaitan yakan yi kokarin mallakar dukan tunanin, kuma ya san cewa idan ana rike da lahanin nan, shi zai yi nasara. Saboda haka kullum yana kokarin rudin masu bin Kristi da dabarunsa da ba za su iya nasara da su ba. Amma Yesu yana roko a madadinsu da hannayensa da aka huda, da kujajjen jikinsa, kuma yana ce ma dukan wadanda za su bi shi: “Alherina ya ishe ka.” Korintiyawa II, 12:9. “Ku dauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u me. ,ao-kaskantar zuchiya; za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauki che, kaya na kuma mara nauyi.” Matta 11:29,30. Don haka kada wani ya dauka cewa ba za a iya magance lahaninsa ba. Allah zai ba da bangaskiya da alheri don yin nasara da su. BJ 486.2
Yanzu muna cikin babban ranar kafaran nan ne. A hidimar farillai, yayin da babban priest ke yin kafara don Israila, akan bukaci kowa ya wahal da ransa tawurin tuba daga zunubi da kaskantar da kai a gaban Ubangiji, domin kada a datse su daga jama’ar. Hakanan kuma dukan wadanda ke so a iske sunayensu cikin littafin rai, ya kamata tun yanzu, cikin yan kwanaki kalilan da sun rage masu, su wahal da rayukansu gaban Allah ta wurin bakinciki domin zunubi da tuba na gaskiya. Dole a yi binciken zuchiya cikin aminci sosai; dole a rabu da ruhun sakacin da Kirista da yawa ke yi. Akwai yaki sosai a gaban dukan masu so su danne miyagun halayyan da ke neman ka da su. Aikin shirin na kai da kai ne. Ba kungiya-kungiya ne za a cece mu ba. Tsabta da himmar wani ba za su cika ma wani mara halayyan nan gibinsa ba. Ko da shike dukan al’ummai za su gurbana a gaban Allah domin shari’a, za ya bincika rayuwar kowane mutum a natse dalla dalla kamar wannan mutumin ne kadai a duniya. Dole a gwada kowane mutum a tarar ba shi da aibi ko lahani, ko kuma wani abu hakanan. BJ 486.3
Al’amran da su ka danganci aikin karshe na kafarar masu muhimminci ne sosai. Yanzu ana shari’an a haikali na sama. Shekaru da dama ana wannan aikin. Ba da jimawa ba, ba wanda ya san lokacin za a kai kan shari’ar masu rai. Rayuwar mu za ta zo wurin Allah domin bincike. A wannan lokacin fiye da kowane lokaci ya kamata kowane mutum a ji fadakar Mai-ceton cewa: “Ku yi lura ku yi tsaro, ku yi addu’a; gama ba ku san lokachin da sa’a take ba.” Markus 13:33. “Idan fa ba ka yi tsaro ba, ina zuwa da kamar barawo ba kwa za ka san sa’an da zan afko maka ba.” Ruya 3:3. BJ 487.1
Sa’an da aikin shari’a ta binciken ya kare, an sansance rabon kowa ke nan, ko rai ko mutuwa. Za a rufe gafara gaf da bayanuwar Ubangiji cikin gizagizai, na sama. Kristi cikin Ruya, sa’an da Ya hangi wannan lokacin, Ya ce; “Wanda shi ke mara-adalchi, bari shi yi ta rashin adilchi; wanda shike mai-kazamta kuma, a kara kazamtadda shi; wanda shi ke mai-adilchi kuma, bari shi yi ta adilchi; wanda shi ke mai-tsarki kuma, a kara tsarkake shi. Ga shi, ina zuwa da samri; hakina yana tare da ni kuma, da zan saka ma kowane mutum gwalgwadon aikinsa.” Ruya 22:11,12. BJ 487.2
Masu adalci da miyagu za su ci gaba da rayuwa cikin jiki mai-mutuwa suna shuka da gine-gine, suna ci suna sha, ba tare da sanin cewa a haikali na sama an rigaya an fadi hukumcin karshe wanda ba za a taba sakewa ba. Kafin ambaliyar, bayan Nuhu ya shiga jirgin, Allah ya rufe shi a ciki, ya kuma rufe masu fajirci a waje; amma har kwana bakwai, muanen ba da sanin cewa hallakarsu ta tabbata ba, su ka ci gaba da rayuwarsu ta rashin kulawa da son annishuwa, suna ba’a ga r hukumcin da ke zuwa. Mai-ceton Ya ce; “Hakanan kuma bayanuwar Dan mutum za ta zama.” Matta 24:39. Shuru dai, ba zato ba tsammani, kamar barawo da tsakar dare, sa’ar za ta zo da za a tabbatar da rabon kowane mutum, sa’anda za a janye tayin jinkai na masu laifi. BJ 488.1
“Ku yi tsaro fa,… kada ya iske ku kuna barci da zuwansa ba labari.” Markus 13:35,36. Abin tausayi ne yanayin wadanda sun gaji jira su ka koma ga sha’awoyin duniya. Sa’anda mai-jari ya mai-da hankali ga neman riba, mai-kaunar jin dadi kuma yana neman nishadi, yayin da yar gaye ta ke kwalliyarta, watakila a wannan sa’ar ce Mai-shari’ar dukan duniya zai bayana hukumcin: “An auna ka chikin mizani, an iske ka ka gaza.” Daniel 5:27. BJ 488.2