Ga mutane da dama, mafarin zunubi da dalilin kasancewarsa ababa ne masu wuyan ganewa ainun. Su na ganin ayukan mugunta da munanan sakamakonta na kaito da hallakaswa, suna kuwa tambayan yadda aka yi ababan nan ke faruwa a kalkashin ikon wanda ya ke da hikima da iko da kauna marasa iyaka. Wannan asiri ne da ba su da bayaninsa. Cikin rashin tabbacinsu da shakkarsu, sun kasa ganin gaskiya da a ka bayana sarai sarai cikin maganar Allah, muhimmai ga ceto kuma. Akwai wadanda, cikin bincikensu game da kasancewar zunubi, su na kokarin binciken abin da Allah bai taba bayanawa ba; saboda haka ba sa samun amsar tambayoyin su; masu yawan shakka da zargi ba dalili, kuma suna anfani da wannan a matsayin hujjar kin maganar littafi mai-tsarki. Wadansu kuwa sun kasa samun cikakkiyar fahimtar babban matsalan nan, watau mugunta, sabo da abada da bahaguwar fasara sun duhunta koyaswar Littafin game da halin Allah da yanayin gwamnatinsa, da kaidodinsa na magance zunubi. BJ 489.1
Ba shi yiwuwa a bayana mafarin zunubi ta yadda za a ba da dalilin kasncewarsa. Duk da haka za a iya fahimtar abu da yawa game da mafarin zunubi da yadda a karshe za a gama da shi, a ba da cikakken bayanin adinin Allah da kaunarsa cikin magance mutunta da ya ke yi. Littafin yana koyar da cewa Allah ba Shi da hannu cikin shigowar zunubi; cewa ba a janye alherin Allah haka kawai ba, ba aibi a gwamnatin Allah da har za a ce ya janyo tasowar tawaye. Zunubi ya kutsa ne, kuma ba za a iya ba da hujjar kasancewarsa ba. Asiri ne, babu dalilinsa; idan aka ba da hujjar kasancearsa, an nuna cewa ba laifi ne ba ke nan. Idan aka sami hujjarsa ko a nuna sanadin kasancewarsa, ya dena zama zunubi ke nan. Ma’anar zunubi ita ce wadda aka bayar cikin maganar Allah: zunubi shi ne “ketaren shari’a, bayanuwar wata kaida ce mai-jayayya da babban dokan nan watau kauna, wadda ita ce tushen gwamnatin Allah. BJ 489.2
Kafin shigowar zunubi, akwai salama da farinciki ko ina a dukan halitta. Komi yana cikakkiyar jituwa da nufin Mahalici, kaunar Allah ita ce gaba, kaunar juna kuma ba son kai a ciki. Kristi kalma, haifaffe kadai na Allah, daya yake da Uban, daya cikin yanayi, da hali da manufa, shi kadai ne cikin duka halitta ya isa ya shiga cikin dukan shawarwarin Allah da manufofinsa. Ta wurin Kristi, Uban Ya y i aikin halittar dukan mazamnan sama. Ta wurinsa aka halici dukan abu, wadanda ke sama, ko kursiyai ne, ko mulkoki ne, ko ikoki ne, kuma dukan sama ta nuna biyayya ga Kristi yadda aka nuna ma Uban. BJ 490.1
Da shike dokar kauna ce harsashen gwamnatin Allah, farincikin dukan halitu ya danganta ga cikakkiyar jituwarsu da manyan kaidodinta na adalci ne. Allah yana bidar hidima ta kauna daga dukan halitunsa - biyayya da ta ke bulbulowa daga godiya sabo da halinsa. Ba Ya son biyayya dole, kuma yana ba kowa yancin zabi, domin su yi masa hidima ta yardar rai. BJ 490.2
Amma akwai wani da ya zaba ya bata yancinsa. Zunubi ya sami asali a wurinsa ne, shi wanda, bayan Kristi, Allah Ya girmama shi fiye da kowa, wanda kuma ya fi kowa cikin mazamnan sama iko da daraja. Kafin faduwarsa, Lucifer ne na farko cikin cherubim, mai-tsarki mara kazanta. “Abinda Ubangiji Yahweh ya fadi ke nan: ba ka rage komi ba, chike da hikima, kamiltache ne ga wajen jamali. A chikin Eden ka ke, gonar Allah; kowane dutse mai-daraja ya zama marufinka,… kai ne cherub shafaffe, mai-rufewa; na kafa ka a bisa dutse mai-tsarki na Allah; tafiyarka, kai da kawowa, a tsakiyar duwatsun wuta. Tun ran da aka haliche ka kamiltache ne kai a chikin dukan al’amuranka, har ran da aka iske rashin gaskiya a chikinka.” Ezekiel 28:12-15. BJ 490.3
Ya kamata Lucifer ya kasance cikin alherin Allah, kamnatace wadanda dukan rundunan malaiku za su girmama shi su kuma kaunace shi, yana anfani da kyawawan gwanintan shi don taimakon wadansu da daukakar Mahalicinsa. Amma, in ji annabin, “Zuchiyarka ta daukaka sabada jamalinka: hasken ranka ya bata hikimarka.” Aya 17. Kadan da kadan, Lucifer ya zama mai-son daukaka kansa. “Tun da ka mai da zuchiyarka sai ka che zuchiyar Allah.” “Ka che,… zan daukaka kursiyina, bisa tamrarin Allah; zan zamna bisa dutse na taron jama’a,… in hau chan bisa madaukakan hadura; in maida kai na kamar Mai-iko duka.” Aya 6; Ishaya 14:13,14. Maimakon kokarin daukaka Allah cikin soyayya da biyayyar halitunsa, kokarin Lucifa shi ne jawo su su bauta masa su kuma yi masa biyayya shi kansa. Kuma sabo da kiyashin darajan da Uban Ya ba dansa, wannan sarkin malaikun ya yi kokarin samun ikon da Kristi ne kadai ke da yancin mallakarsa. BJ 491.1
Dukan sama ta yi murnar bayana darajar mahalicin da kjuma nuna yabonsa. Kuma sa’anda a ke girmama Allah hakanan ba komi sai salama da murna. Amma wata muryar sabani ta lalata jituwar saman. Bautar kai da daukakar kai, sabanin shirin Mahalicin, sun jawo alamun mugunta cikin zukatan da daukakar Allah ce ta ke da fifiko a ciki. Majalisun sama suka roki Lucifer. Dan Allah Ya bayana masa girma da nagarta da adalcin mahalicin, da kuma yanayin tsarki na dokarsa da rashin sakewarta. Allah da kansa ya rigaya ya kafa tsarin sama; kuma idan lucifa ya kance masa, zai ci mutumcin mahalicinsa ke nan ya kuma kawo ma kansa hallaka. Amma kashedin nan da aka bayar cikin kauna da jinkai marasa iyaka sun jawo ruhun tirjiya ne kawai. Lucifa ya bar kishin Kristi ya dawoma, har ya nace da sabaninsa. BJ 491.2
Alfarman darajarsa ta haifar da son daukaka. Lucifer bai ga cewa manyan girmamawa da aka yi masa kyauta ne daga Allah ba, don haka bai ga dalilin da zai gode ma mahalicin ba. Ya yi alfahari da walkiyarsa da girmansa, har ya yi burin zama daidai da Allah. Mazamnan sama sun kaunace shi suka kuma girmama shi. Malaiku sun rika marmarin aiwatar da umurninsa, kuma an suturta shi da hikima da daraja fiye da dukansu. Duk da haka Dan Allah ne babban sarkin sama da aka amince da Shi, wanda ikonsa da iyawansa daya ne da na Uban. Duk wata shawara a sama, Kristi yana ciki, amma ba a yarda Lucifa ya shiga shawarar Allah ba. Sai shi wannan babban malaikan ya tambaya: “Don me Kristi ke da fifikon? Don me a ke daukaka Shi hakanan gaba da Lucifer?” BJ 492.1
Sa’anda ya bar wurinsa a gaban Allah, Lucifer ya ci gaba ya baza ruhun rashin gamsuwa a cikin malaikun. Ya yi aiki cikin sirri, da fako kuma ya boye ainihin manufarsa kalkashin kamanin girmamawa ga Allah, ya yi kokarin ta da kiyayya ga dokokin da ke aiki kan mazamna na sama, yana nuna cewa dokokin suna da takura ba dalili. Da shike yanayinsu masu-tsarki ne, ya roka cewa malaikun su bi muradin zukatan su. Ya so ya ja ma kansa tausayi tawurin nuna cewa wai Allah Ya yi masa rashin adalci tawurin ba Kristi mafificiyar daraja. Ya ce cikin neman karin iko da daraja ba firmama kansa ya ke so ba, amma yana neman ya tabbatar ma dukan mazamnan sama yanci ne, domin tawurin wannan su cimma yanayin rayuwa mafi-girma. BJ 492.2
Allah cikin jinkansa Ya yi hakuri da Lucifer da dadewa. Ba a rage masa girma nan da nan ba lokacin da ya fara tunanin rashin gamsuwa, ko ma lokacin da ya fara bayana zarge zargen shi na karya ga malaiku masu biyayya. An bari ya kasanche a saman da dadewa dai. Akai akai an rika yi masa tayin yafewa idan ya tuba, ya yi biyayya. An yi duk wani kokari na kauna da hikima mara iyaka domin a nuna masa kuskurensa. Kafin nan ba a taba samun ruhun rashin gamsuwa ba a sama. Lucifer kansa da farko ma bai san inda ya nufa ba; bai gane ainihin yanayin tunaninsa ba. Amma sa’an da aka bayana cewa ba dalilin rashin gamsuwarsa, Lucifer ya gane cewa ba shi da gaskiya, cewa batutuwan Allah daidai ne, kuma ya kamata ya amince da hakan a gaban dukan sama. Da ya yi haka, da ya ceci kansa da malaiku da yawa. A lokacin bai rigaya ya janye biyayyarsa ga Allah kwata kwata ba. Ko da shike ya rabu da matsayinsa na cherub mai-rufewa, duk da haka da ya yarda ya koma ga Allah, ya amince da hikimar Allah, ya kuma gamsu da matsayin da an bar shi cikin babban shirin nan na Allah, da an mayar da shi matsayinsa. Amma girman kai ya hana shi amincewa. Ya nace yana kare matakinsa, cewa ba ya bukatar tuba, ya kuma dukufa wajen babban jayayyarsa sabanin Mahalicinsa. BJ 492.3
Yanzu ya mai da dukan kwarewar tunanin son yin rudu, domin shi sami goyon bayan malaiku da ke kalkashin ikonsa. Ko kashedi da shawaran da Kristi ya ba shi ma ya tankware shi don taimaka ma dabarunsa. Ga wadanda kauna da amincinsu su ka manna su gare shi, Shaitan ya ce ba a yi masa adalci ba, ba a girmama matsayinsa ba, kuma ana so a takaita ‘yancinsa. Daga canja kalmomin Kristi ya kai ga canja tasa maganar da yin karya kai tsaye, yana zargin Dan Allah da shirin ci masa mutunci a gaban mazaunan sama. Ya kuma so ya yi karya cewa akwai wata damuwa tsakaninsa da malaiku masu biyayya ga Allah. Ya zargi dukan wadanda bai iya rudinsu su bi shi ba, da cewa wai basu damu da sha’anonin da suka shafi mazaunan sama ba. Ya zargi masu biyayya ga Allah da aikin da shi kansa ya ke yi. Don neman tabbatar da zarginsa na cewa Allah Ya yi masa rashin adalci, ya shiga canja kalmomin Mahalicin. Ya shiga rikitar da malaiku da rudu game da manufofin Allah. Ababa masu saukin ganewa ya mai da su na asiri, kuma ta wurin dabarunsa ya rikitar da maganar Allah. Kasancewarsa tare da hukumar sama ta kara ma karyarsa da karfi ta yadda malaiku da yawa su ka hada kai da shi wajen yi ma Allah tawaye. BJ 493.1
Allah cikin hikimarsa Ya bar Shaitan ya ci gaba da aikinsa, har sai da ruhun rashin gamsuwa ya kai ga tawaye kai tsaye. Wajibi ne tsare-tsarensa su cika, domin kowa ya ga yanayinsu da sakamakonsu. An daukaka Lucifer sosai; mazaunan sama sun kaunace shi sosai, tasirinsa a kansu kuma yana da karfi. Gwamnatin Allah ya kunshi mazaunan sama, har da na dukan duniyoyin da ya halitta; Shaitan kuma ya dauka cewa idan ya iya jawo malaikun sama suka yi tawaye tare da shi, zai iya daukan sauran duniyoyin ma. Ya yi anfani da dabaru da zamba wajen gabatar da ra’ayinsa ta yadda zai cimma burinsa. Gwanin rudi ne shi, kuma tawurin boye kansa cikin karya ya sami nasara. Har malaiku masu biyayya ga Allah ma ba su iya fahimtar halinsa gaba daya ko kuma su ga inda aikinsa ya nufa ba. BJ 494.1
An girmama Shaitan sosai, dukan ayukansa kuma sun cika da asiri ta yadda ya zama da wahala a bayana ma malaiku ainihinyanahin aikinsa. Ba don an bar zunubi ya cika girmansa ba, da ba a gane cewa mugun abu ne ba. Kafin nan, ba zunubi a dukan halittar Allah, halittu masu tsarki kuma basu san yanayinsa da muguntarsa ba. Ba su iya gane muggan sakamakon kawar da dokar Allah ba. Da farko Shaitan ya boye aikinsa ta wurin nuna cewa yana biyayya ga Allah. Ya ce wai yana karfafa daukaka ga Allah ne, da karkon gwamnatinsa da jin dadin dukan mazaman sama. Yayin da ya ke cusa rashin gamsuwa cikin zukatan malaikun da ke tare da shi, ya yi yadda za a ga kaman yana kokarin kawar da rashin gamsuwan ne. Sa’anda ya yi canje canje cikin tsarin Allah da dokokin gwamnatinsa, ya yi da karyan cewa canje canjen nan wajibi ne don tabbatarda jituwa a sama. BJ 494.2
Cikin aikinsa na magance zunubi, Allah ya na anfani da adalci da gaskiya ne. Shaitan ya na iya anfani da ababan da Allah ba zai iya anfani da su ba, watau balmar baka da rudi. Ya rigaya ya yi kokarin kayryata maganar Allah, ya kuma yi ma gwamnatin Allah batanci a gaban malaiku, ya na cewa wai Allah bai yi adalci ba da ya kafa ma mazaunan sama dokoki, cewa biyayya da Allah ke bida daga hallittunsa neman daukakan kansa ne kawai. Saboda haka, dole a nuna ma mazaunan sama da na dukan duniyoyi cewa gwamnatin Allah tana da adalci, dokarsa kuma mara-aibi ne. Shaitan ya nuna kamar shi kansa ya na nema ya karfafa ci gaban dukan halitta ne. dole kowa ya gane ainihin halin mai-kwacen nan. Aka ba shi lokaci domin ya bayana kansa ta wurin miyagun halayyansa. BJ 495.1
Shaitan ya zargi dokar Allah da gwamnatinsa da laifin jawo rashin jituwa, wanda aikin shi Shaitan din ne ya jawo. Ya ce kowace mugunta sakamakon mulkin Allah ne. Dole a bar aikinsa ya hukumta shi, da farko Shaitan ya ce shi ba tawaye ya ke yi ba. Dole a bari dukan halittu su ga tonon asirin makaryacin. BJ 495.2
Ko sa’an da aka ce ba zai iya ci gaba da kusancewa a sama ba, Allah bai hallaka Shaitan ba. Da shike Allah yana karban hidima ta kauna ce kadai, dole biyayyar halitunsa ta kasance bisa ga yarda da adalcinsa da kaunarsa. Mazaunan sama da na sauran duniyoyi ai da basu iya ganin adalcin Allah da jinkansa ba, in da ya hallaka Shaitan a wancan lokacin. Da an shafe shi daga halitta nan take, da ana yi ma Allah hidima don tsoro ne, ba don kauna ba. Da ba a rushe tasirin mai-rudun gaba daya ko kuma a kawar da ruhun tawaye gaba daya ba. Dole a bar mugunta ta nuna. Domin dukan haitta ta anfana, dole Shaitan ya girmar da kaidodinsa har su nuna, domin dukan halita su ga ainihin yanayin zarge zargen da ya yi ma gwamantin Allah da jinkansa da rashin sakewar dokarsa kuma. BJ 495.3
Tawayen Shaitan darasi ne ga dukan halitta na dukan sararaki, shaida ce kuma har abada ta yanayin zunubi da mumunan sakamakonsa. Sakamakon mulkin Shaitan kan mutane da malaiku zai nuna sakamakon kawar da mulkin Allah. Zai shaida cewa zaman lafiyan dukan halittun Allah da dokarsa ne, ta hakanan tarihin mumunan tawayen nan za ya zama madawamin tsaro ne ga dukan tsarkaka, domin kada a rude su game da yanayin zunubi, a kuma cece su daga aikata zunubi, da shan horonsa. BJ 496.1
Har karshen jayayyan nan a sama, babban mai kwacen nan ya ci gaba da cewa yana da gaskiya. Sa’anda aka sanar da cewa dole za a kore shi da dukan masu-goyon bayansa daga sama, sai shugaban tawayen nan ya bayana reninsa ga dokar Mahalici, kai tsaye. Ya maimaita ra’ayinsa cewa malaiku ba sa bukatar a nuna iko a akansu, amma a bar su su bi nufin kansu, wanda kullum zai bishe su daidai. Ya soki dokokin Allah cewa suna rage masu ‘yanci, ya kuma bayana cewa niyyarsa ce ya tabbatar da sokewar doka; cewa idan aka ‘yantar da rundunan sama daga wannan kangin, za su shiga yanayin rayuwa mafi daukaka da daraja. BJ 496.2
Ruhun nan da ya ta da tawaye a sama har yanzu yana ta da tawaye a duniya. Abin da Shaitan ya yi da malaiku, ya ci gaba da yinsa tare da mutane. Ruhunsa yana mulki yanzu cikin ‘yan tawaye. Kamar Shaitan din, suna so su rushe shingayen dokar Allah suna kuma yi ma mutane alkawalin ‘yanci ta wurin ketare sharuddan doka. Har yanzu tsautawa zunubi ya na ta da ruhun kiyayya da tirjiya. Sa’an da aka bayana sakonin fadaka na Allah, Shaitan ya kan sa mutane su ba da hujja ma kansu, su kuma nemi goyon bayan wadansu cikin tafarkinsu na zunubi. Maimakon gyarta kurkuransu, su kan ta da fushi ne kan mai-fadakarwan, sai ka ce shi ne kawai matsala. Daga kwanakin Habila zuwa lokacinmu, irin ruhun da a ke nunawa ke nan game da masu kokarin nuna munin zunubi. BJ 497.1
Tawurin karya dayan da ya yi a sama game da halin Allah, wanda ya sa aka mai da shi azalumi mai-danniya, Shaitan ya koya ma mtum zunubi. Da shike ya yi nasara hakanan kuma, ya ce kuntatawa na rashin adalci da Allah ya yi ne ya kai ga faduwar mutum, kamar yadda ya kai ga tawyensa. BJ 497.2
Amma Madauwamin kansa Ya bayana halinsa: “Ubangiji, Ubangiji Allah ne cike da juyayi, mai-adalchi kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jin kai da gaskiya; yana tsaron jin kai domin dubbai, yana gafarta laifi da sabo da zunubi; ba shi kubutadda mai-laifi ko kadan.” Fitowa 34:6,7. BJ 497.3
Tawurin korar Shaitan daga sama Allah Ya bayana adalcinsa Ya kuma tabbatar da darajar kursiyinsa. Amma sa’anda mutun ya yi zunubi ta wurin amincewa da rudun mai-riddan nan, Allah Ya ba da shaidar kaunarsa ta wurin ba da Dansa haifaffe tilo domin ya mutu saboda fadaddun ‘yan Adam. Cikin kafarar an bayana halin Allah. Babban darasin giciyen yana koya ma dukan halitta cewa hanyar zunubi da Lucifer ya dauka ba laifin gwamnatin Allah ba ne ko kadan. BJ 497.4
Cikin jayayya tsakanin Kristi da Shaitan, lokacin hidimar Mai-ceto a duniya, an bayana halin babban mai-yaudaran nan. Ba abinda ya iya tumbuke Shaitan daga soyayyar malaikun sama da dukan halitta kamar yadda yakinsa da Mai-fansar duniya ya yi. Sabon nan na sa, inda ya ce ma Kristi shi yi masa sujada, da gangancin karfin halinsa da ya kai Kristi kan wani dutse mai-tsawo kwarai da kan hasumiya ta haikali, da muguwar manufar da ta bayana sa’anda ya bukaci Yesu ya fadi daga makurar tsawon hasumiyar haikalin, da muguntan da ya dinga farautar Kristi da ita ko ina, ya na zuga zukatan priestoci da mutane domin su ki kaunar Kristi, a karshe kuma su ta da murya su na cewa. “A giciye shi! A giciye shi!” - dukan wannan ya sa dukan halitta ta yi mamaki da fushi. BJ 498.1
Shaitan ne ya sa duniya ta ki Kristi. Sarkin mugunta ya yi anfani da dukan ikonsa da dabarunsa domin shi hallaka Yesu; domin ya ga cewa jinkan Mai-ceton da kaunarsa da tausayinsa da tawali’unsa suna bayana ma duniya halin Allah. Shaitan ya yi jayayya game da kowace magana da Yesu ya yi, ya kuma yi anfani da mutane su ka zama wakilansa don cika rayuwar Mai-ceton da wahala da bakinciki. Dabarunsa da karyan da ya yi anfani da su don hana aikin Yesu, da kiyayan da ya nuna tawurin yayan rashin biyayya, da zarge-zargen da ya yi kan Shi wanda rayuwarsa ta nagarta babu kamarta, duk sun taso ne daga son ramako. Wutan kiyashi da mugunta da kiyayya da ramako sun habaka a Kalfari kan Dan Allah, yayin da dukan sama ke kallo shuru da kyama. BJ 498.2
Sa’anda aka kamala hadayar, Kristi ya je sama, ya ki soyayyar malaiku tukuna, har sai bayan da ya gabatar da rokon nan cewa: “Wadanda ka bani, ina so su zamna wurin da ni ke, tare da ni. Yohanna 17:24. Sa’an nan da matukar kauna da iko Uban ya amsa daga kursiyinsa cewa: “Bari dukan mallaiku na Allah su yi masa sujada.” Ibraniyawa 1:6. Cin mutuncin da aka yi ma Yesu ya kare, hadayarsa ta cika, aka ba shi suna da ta fi kowace suna. BJ 498.3
Yanzu laifin Shaitan ya tabbata ba hujja. Ya rigaya ya bayana ainihin halinsa na makaryaci mai-kisa kuma. Aka ga cewa ruhun nan da ya yi mulkin ‘ya’yan mutane wadanda ke kalkashin ikonsa da shi, in da an ba shi damar mallakar mazaunan duniya da ya yi anfani da ruhu dayan ne. Ya yi ikirarin cewa ketare dokar Allah zai kawo yanci da girmammawa, amma aka ga cewa ya haifar da bauta ne da kaskanci. BJ 499.1
Zarge zargen Shaitan na karya game da halin Allah da gwamnatinsa sun bayana da ainihin yanayinsu. Ya zargi Allah da neman daukaka kansa ne kawai da yake bidar biyayyar halitunsa, ya kuma ce yayin da Mahalicin ke bidar musun kai daga wurin halita, shi kansa Mahalicin ba ya musun kai, kuma ba ya sadakar da komi. Yanzu ga shi an ga cewa domin ceton duniya ta zunubi sarkin dukan halitta ya yi hadaya mafi girma da kamna kan iya yi, gama “Allah yana chikin Kristi yana sulhunta duniya zuwa kansa.” Korintiyawa II, 5:19. An kuma ga cewa yayin da Lucifer ya bude kofa domin shigowar zunubi tawurin son girma da neman daukakarsa, Kristi Ya kaskantar da kansa, ya yi biyayya har mutuwa, domin shi hallaka zunubi. BJ 499.2
Allah Ya bayana kyaman da yake ma halayyan tawaye. Dukan sama sun ga an bayana adalcinsa ta wurin hukumta Shaitan da kuma fansar mutum. Lucifer ya rigaya ya ce idan dokar Allah ba ta sakewa, kuma ba za a iya cire horonta ba, dole za a hana kowane mai-laifi samun alherin Mahalici ke nan. Ya ce an kai masu zunubi inda ba za su iya samun fansa ba, saboda haka kuma su abincinsa ne na halal. Amma mutuwar Kristi ta ba mutum goyon bayan da ba wanda zai iya kawarwa. Horon dokar ya fadi a kansa ne, Shi wanda yake daidai da Allah, sai mutum ya sami ‘yancin karban adalcin Kristi, kuma tawurin rayuwar tuba ya yi nasara, yadda Dan Allah ya rigaya ya yinasara, bisa ikon Shaitan. Ta hakanan Allah mai-adalci ne, kuma mai-kubutar da dukan masu ba da gaskiya ga Yesu. BJ 499.3
Amma ba domin fansar mutum ne kadai Kristi ya zo duniya ya sha wahala har ya mutu ba. Ya zo domin Ya “chichika” dokan ne ya kuma mai-da shi abind daraja. Ba kawai domin mazaunan duniyan nan su dauki dokar yadda ya kamata ba ne, amma domin Ya bayana ma dukan duniyoyin dukan halitta ne cewa dokar Allah ba ta sakewa. Da za a iya kawar da bukatun dokar, da Dan Allah bai bukaci ba da ransa domin kafarar ketarewar ta ba. Mutuwar Kristi ta na tabbatar da rashin sakewar dokar. Kuma hadayan da kaunar Uban da Dan ta sa suka yi, domin a fanshi mutum, ta na nuna ma dukan halitta cewa adalci da jinkai ne harsashen dokar Allah da gwamnatinsa. BJ 500.1
Sa’an da a karshe za a zartas da hukumci za a ga cewa ba hujja domin zunubi. Sa’anda Mai-shari’an dukan duniya zai tambayi Shaitan, “Don me ka yi mani tawaye, ka kuma kwace mani ‘ya’yan mulki na? Mai-kirkiro zunubin ba zai sami hujjan da zai bayar ba. Kowane baki zai rufu, kuma dukan rundunan tawaye za su rasa abin fadi. BJ 500.2
Yayin da giciyen Kalfari ke bayana cewa dokar ba ta sakewa, yana kuma bayana ma duniya cewa hakin zunubi mutuwa ne. Cikin kalmomin karshe na Mai-ceton, cewa: “An gama,” an kada kararrawar mutuwar Shaitan. Babban jayayyan da aka dade ana yi ya zo karshensa, aka kuma tabbatar da kawar da zunubi a karshe. Dan Allah Ya shiga kabari “domin tawurin mutuwa shi wofinta wanda yake da ikon mutuwa, watau Shaitan.” Ibraniyawa 2:14. Burin Lucifer na daukakar kansa ya sa shi ya ce: “Zan daukaka kursiyina bisa tamrarin Allah,… in mai da kaina kamar Mai-iko duka.” Allah ya ce: “Na maishe ka toka a kasa, ba ka da sauran zama ba dadai.” Ishaya 14:13,14; Ezekiel 28:18,19. Sa’an da “rana tana zuwa, tana kuna kamar tanderu; dukan masu girman kai, da dukan wadanda ke aikin mugunta za su zama tattaka, ranan da ke zuwa kuma za ta kokone su, in ji Ubangiji mai-runduna, har da ba za ta bar masu tushe ko reshe ba.” Malachi 4:1. BJ 500.3
Dukan hailitta sun zama shaidu game da yanayin zunubi da sakamakonsa. Kuma hallakawarsa, wanda in da tun farko aka yi shi, da zai jawo ma malaiku tsoro ya kuma jawo ma Allah rashin daraja, yanzu kuwa zai bayana kaunarsa ne a gaban dukan halitta masu murnan yin nufinsa, wadanda kuma dokarsa tana cikinsu. Mugunta ba za ta kara bayanuwa ba kuma. Maganar Allah ta ce: “Wahala ba za ta taso so biyu ba.” Nahum 1:9. Dokar Allah da Shaitan ya ce karkiyar bauta ce, za a girmama ta a matsayin dokar ‘yanci. Halitta da an rigaya an gwada an kuma tabbatar, da za a sake juya ta daga biyayya ga Shi wanda an rigaya an bayana halinsa kwata kwata a gabansu, cewa kauna ce mara matuka da hikima mara iyaka ba. BJ 501.1