Littafi ya bayana dangantaka tsakanin duniyan da a ke gani da wanda ba a gani, da hidimar malaikun Allah, da wakilcin miyagun ruhohi, kuma ba a iya raba ababan nan da tarihin ‘yan Adam. Kin gaskata cewa akwai miyagun ruhohi ya na karuwa ne, sa’an nan wadansu kuma su na koyar da cewa malaiku masu tsarkin nan masu “hidima sabili da wadanda zasu gaji cheto” (Ibraniyawa 1:14), wai ruhohin matattu ne. Amma Littafin ya na koyar da kasancewar malaiku, nagargaru da miyagu, yana kuma cikakken tabbaci cewa malaiku ba ruhohin matattu ba ne. BJ 508.1
Kafin halittar mutum, akwai malaiku, domin lokacin da aka kafa harsashen duniya. “tamrarin safiya suka yi waka, dukan ‘ya’yan Allah kwa suka yi sowa don farinchiki.” Ayuba 38:7. Bayan faduwar mutum, an aiki malaiku su tsare itacen rai, tun kafin mutum da ya ya mutu. Bisa ga yanayi, malaiku sun fi mutane, gama mai-zabura ya ce mutum da kadan ya gaza malaiku. (Zabura 8:5). BJ 508.2
Littafin ya fada mana yawa da iko da darajar mazamnan sama, da dangantakarsu da gwamnatin Allah, da kuma dangantakarsu da aikin fansa. “Ubangiji ya kafa kursiyinsa a chikin sammai; mulkinsa kwa ya na bisa kowa.” Annabin kuma ya ce: “Na ji murya malaiku da yawa kewaye da kursiyin.” Su na jira a dakin sarkin sarakuna, malaiku “karfafa masu-iko” “masu hidima na sa, wadanda ke aika yardassa,” suna “kasa kunne ga muryar maganatasa.” Zabura 103:19-21; Ruya 5:11. Masu hidiman da Daniel ya gani su dubban dubbai ne, zambar goma kuma so zambar goma. Manzo Bulus ya ce rundunarsu “ba ta kidayuwa,” Daniel 7:10; Ibraniyawa 12:22. A matsayin su na ‘yan sakon Allah su na kaiwa da komowa “sai ka che hasken walkiya.” (Ezekiel 1:14), darajarsu mai walkiya, firiyarsu da saurin gaske. Malaikan da ya bayana a kabarin Mai-ceton wanda “siffarsa tana kama da walkiya, tufassa kuma fara fat kamar snow.” Ya sa masu tsoron kabarin suka yi rawan jiki don tsoro,” su ka zama kamar matattu.” Matta 28:3.4. Sa’anda Sennacherib sarkin Assyria ya rena Allah, ya kuma yi masa sabo, ya kuma yi ma Israila barazanar hallaka, “A daren nan fa ya zama malaikan Ubangiji ya fita, ya buga mutum zambar dari da tamanin da biyar chikin sansanin Assyriyawa.” Ya datse dukan jarumawa, da manya da shugannin.” Daga mayakan Sennacherib. “Ya fa kama garinsa da kunya.” Sarakuna II, 19:35; Labarbaru II, 32:21. BJ 508.3
Ana aikan malaiku ne da sakonin jinkai zuwa ga ‘ya’yan Allah. Zuwa ga Ibrahim, da alkawaran albarka, zuwa kofokin Sodom, domin su ceci Lot adali daga hallaka ta wuta; zuwa ga Iliya, yayin da yake gaf da hallaka sabo da yunwa da gajiya a jeji; zuwa ga Elisha, da karusai da dawaki na wuta, kewaye da kankanin garin nan inda magabta su ka kewaye shi, zuwa ga Daniel, yayin da ya ke bidar hikimar Allah a fadar kafirin sarki, ko kuma inda aka bar shi ya zama abincin zakuna; zuwa ga Bitrus, wanda ke jiran mutuwa a kurkukun Hirudus, zuwa ga fursunonin nan a Filibbi; zuwa ga Bulus da abokansa a daren guguwan nan a kan teku; domin a bude tunanin Karnilius don karban bishara; domin a tura Bitrus da sakon ceto zuwa ga ba-al’umi, hakanan ne malaiku masu tsarki suka yi ma mutanen Allah hidima cikin dukan sararraki. BJ 509.1
Akan ba kowane mai-bin Kristi malaika shi zama waliyinsa, masu-tsaron nan na sama suna tsaron masu-adalchi daga ikon mugun. Shaitan kansa ya gane hakan lokacin da ya ce: “A banza ne Ayuba yake tsoron Allah? Ba ka kewaye da shinge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da ya ke da shi, a kowane sassa?” Ayuba 1:9,10. Mai-zabura ya bayana ta yadda Allah ke tsaron mutanensa, inda ya ce: “Malaikan Ubangiji ya na kafa sansani a kewaye da masu tsoronsa. Ya na tseradda su kuma,” Zabura 34:7. Game da masu-ba da gaskiya gareshi, Mai-ceton Ya ce: “Ku yi hankali kada ku rena wani a chikin wadannan kankanana; gama ina che maku, chikin sama kullum malaikunsu suna duban fuskar Ubana.” Matta 18:10. Malaikun da aka sa su yi hidima ma ‘ya’yan Allah kullum su na da hanyar zuwa wurinsa. BJ 509.2
Muggan ruhohi da aka halice su da farko ba zunubi, da yanayinsu da iko da darajarsu daidai ne da na malaiku masu tsarki da yanzu ke hidimar Allah. Amma da shike sun fadi tawurin zunubi sun hada kai don rena Allah da hallaka mutane, da shike sun hada kai don rena Allah da hallaka mutane. Da shike sun hada kai da Shaitan cikin tawayensa, aka kuma kore su tare daga sama, cikin dukan sararaki su na hada kai da shi cikin yakinsa da Allah. Littafi yana bayana mana gangaminsu da gwamnatinsu, da kungiyoyinsu, iri iri, da wayansu da dabarunsu, da kuma muggan shirye shiryensu sabanin salamar mutane da farincikinsu. BJ 510.1
Tarihin Tsohon Alkawali ya kan ambaci kasancewarsu da wakilcinsu; amma lokacin da Kristi ke cikin duniya ne miyagun ruhohi su ka nuna ikonsu sarai sarai. Kristi ya zo domin shiga cikin shirin fansar mutum, Shaitan kuma ya kudurta nuna ‘yancinsa na mallakar duniya. Ya yi nasarar kafa bautar gumaka ko ina a duniya ban da Palestine. Ga kasa da ya kadai da ba ta yarda da mulkin Shaitan duka ba, Kristi Ya zo domin ya ba mutanen hasken sama. A kasan nan ikoki biyu masu gaba da juna sun yi jayayya game da fifiko. Yesu Ya mika hannuwansa na kauna, yana gayyatan dukan masu so, su sami gafara da salama cikinsa. Rundunan duhu sun ga cewa ba su da iko mara-iyaka, suka gane kuma cewa idan aikin Kristi ya yi nasara, mulkinsu zai kare ba da jimawa ba. Shaitan ya yi ta fushi kamar zakin da aka daure da sarka ya kuma ci gaba da nuna ikonsa a kan jikunan mutane da rayukansu. BJ 510.2
Sabon Alkawali ya bayana a fili cewa aljannu su kan shiga cikin mutane. Wadanda aka wahal da su hakanan ba azabar ciwon jikunansu kadai suke sha ba. Kristi Ya na da cikakkiyar ganewar abinda yake fuskanta, Ya kuma gane kasancewa kai tsaye da kuma wakilcin miyagun ruhohi. BJ 511.1
Misalin yawansu da iko da muguntarsu, da kuma ikon jin kan Kristi shi ne labarin Littafin na warkar da masu alajannun nan na Gadara. Wahalallun mahaukatan nan da suka fi karfin kowane kangi, suna birgima, suna kumfa, da fushi, su ka cika wuri da kukansu, suna ji ma kansu raunuka, suka kuma zama hatsari ga duk wanda ya je kusa da su. Jikunansu lalatattu jina-jina, da tunaninsu da ya kauce, sun gamsar da Shaitan hakanan. Daya daga cikin aljannun da ke cikin mahaukatan ya ce: “Sunana Tuli ne; gama muna da yawa.” Markus 5:9. A sojan Romawa, tuli guda ya kan kunshi tsakanin sojoki dubu uku zuwa dubu biyar ne. Rundunonin Shaitan ya na kuma karkasa su kampani-kampani ne, kuma kampani dayan da aljannun nan ke ciki ba su kasa tuli guda ba. BJ 511.2
Bisa ga umurnin Yesu miyagun ruhohin suka fice daga mutanen nan, suka bar su suna zaune a natse a sawayen Mai-ceton, rinjayayyu, cikin hankalinsu da ladabi kuma. Amma an yarda ma aljannun suka share zuwa cikin teku; kuma ga mazamanan Gadara, garken aladun ya fi masu albarkan da Kristi ya bayar, suka roki Mai-warkarwan ya tafi. Sakamakon da Shaitan ya so ya samu kenan. Ta wurin zargin Yesu da laifin jawo masu hasara, ya ta da tsoro na son kai cikin mutanen, ya kuma hana su sauraron maganarsa. Kullum Shaitan ya na zargin Kirista cewa su ne sanadin hasara da rashin sa’a da wahala, maimakon amincewa cewa shi da wakilansa ne sanadin. BJ 511.3
Amma ba a kawar da manufofin Kristi ba. Ya bar miyagun ruhohin suka hallaka aladun don tsauta ma Yahudawan nan ne da su ke kiwon dabbobin nan marasa tsabta don neman kurdi. Ba don Kristi ya hana aljannun ba, da sun tsunduma makiyayan aladun da masu aladun cikin tekun, tare da aladun. Kiyaye makiyayan da masu aladun sabo da ikonsa da ya yi anfani da shi cikin jinkai ne domin kubutar da su. Ban da haka, an bar wannan al’amari ya faru domin almajiransu shaida muguntar ikon Shaitan kan mutum da dabba ne, Mai-ceton Ya so masu-binsa su sami sanin magabcin da za su sadu da shi, domin kada ya rude su ya kuma rinjaye su da dabarunsa. Nufinsa ne kuma cewa mutanen yankin nan su ga ikonsa na karye kangin Shaitan da kuma kubutar kamanun Shaitan din. Kuma ko da shike Yesu kansa Ya tafi, mutanen da ya kubutar da su ta wurin al’ajibin nan sun kasance a wurin domin su bayana jinkan wanda ya taimake su. BJ 512.1
An kuma rubuta wadansu al’amura masu kama da wannan cikin Littafin. Diyar macen nan Ba-surofinikiya ta wahala sosai da aljani, Yesu kuwa ya fitar da shi tawurin kalmarsa. Markus 7:26-30. “Wani mai-aljan, makafo da bebe,” (Matta 12:22); wani saurayi mai-ruhu na bebanci, wanda “so da yawa kwa ya kan jefa shi chikin wuta, da chikin tapkunan ruwa kuma, domin ya hallaka shi,” (Markus 9:17-22); mahaukacin nan da cikin fama da “ruhun aljani mai-kazamta” (Luka 4:33-36), wanda ya rikitar da salamar Assabbat a haikali na Kafarunhum -dukansu Mai-ceton nan Mai-tausayi ya warkar da su. A kusan kowane al’amari, Kristi ya yi magana da aljanin kamar halitta mai-wayo. Mai-ceton nan mai-tausayi Ya yi magana da al’janin kamar wanda ke da ganewa, yana umurtarsa shi fito daga cikin mutumin, kuma kada ya sake hallaka shi. Sa’anda masu-sujada a Kafarnahum suka ga ikonsa mai-girma, “mamaki ya abko masu duka, suka yi zanche da junansu, suka che: Wache magana che wannan? Gama da hukumchi da iko yana umurnin kazaman ruhohi, suna kwa fito.” Luka 4:36. BJ 512.2
Wadanda aljannu ke cikinsu akan ce suna cikin yanayi na wahala sosai; amma ba kowanne ne haka ba. Domin a sami ikon da ya fi na mutum, wadansu sun nemi tasirin Shaitan. Irinsu basu sami damuwa da aljannun ba. Irin su sun hada da masu ruhun sihiri, kamar su Simon Magus, Alima mai-sihiri, da budurwan nan da ta rika bin Bulus da Sila a Fillibi. BJ 513.1
Ba wadanda suka fi fuskantar hadarin tasirin muggan ruhohi kamar wadanda, duk da shaidu da yawa kai tsaye daga littafin, su ke musun kasancewar Iblis da malaikunsa. Muddan dai ba mu san dabarunsu ba, suna da riba a kanmu; mutane da yawa suna sauraron shawarwarinsu yayin da suka gani kamar su na bin hikimar kansu ne. Shi ya sa, yayin da muka kusanto karshen lokaci, sa’anda Shaitan ke aiki da dukan ikonsa domin rudu da hallaka, yana yayata ra’ayin nan ko ina cewa ba Shaitan din ma. Yana so ne ya boye kansa da hanyoyin da ya ke tafiyar da aikinsa. BJ 513.2
Ba abin da mai-yaudaran nan ya fi tsoro kamar cewa mu gane dabarunsa. Ta wurin boye halinsa da manufofinsa ya sa ana daukansa da wasa ta yadda ana masa ba’a ne da reni kawai. Ya kan ji dadi idan ana nuna cewa shi abin dariya ne ko kyama, mumuna wanda rabinsa dabba ne, rabi kuma mutum. Yakan ji dadi in ya ji wadanda ke gani kamar su na da wayo da sani sosai su na wasa ko ba’a da sunansa. BJ 513.3
Domin ya boye kansa da kyau ne ya sa ake tambaya ko ina cewa: “Ko akwai wani halitta hakanan?” Amincewa da masu addini ke yi da ra’ayoyin da ke karyata shaidar Littafin, shaida ce ta nasarar Shaitan. Kuma domin Shaitan zai iya mallakar wadanda ba su san da tasirinsa ba ne ya sa maganar Allah ta ba mu misalai da yawa na aikin muguntarsa, ta kuma bayana mana ikokin sana sirri, ta hakanan kuma ta sa mu cikin tsaro daga hare harensa. BJ 514.1
Ikon Shaitan da muguntarsa da na rundunansa za su iya razana mu ba don za mu iya samun mafaka da kubuta cikin mafificin ikon mai-fansarmu ba. Mukan kulle gidajen mu da makullai don tsaron dukiyarmu da rayukanmu daga miyagun mutane, amma ba mu cika tunanin miyagun malaikun da kowane lokaci su ke neman hanyar zuwa wurinmu, wadanda kuma a cikin karfin kanmu ba mu da hanyar kariya daga hare harensu. Idan aka yarda masu za su iya kawar da zukatanmu, su lalata jikunanmu su kuma azabtar da su, su hallaka dukiyarmu da rayukanmu kuma. Abin da ke masu dadi kawai shine wahala da hallaka. Abin tsoro ne yanayin wadanda ke kin umurnin Allah su na yarda da jarabobin Shaitan, har lokacin da Allah zai ba da su ga ikon muggan ruhohi. Amma masu bin Kristi su na lafiya kullum a kalkashin tsaronsa. Ana aikawa da malaiku masu-matukar karfi domin su tsare su. Mugun ba zai iya kutsawa da shingen da Allah Ya kewaye mutanensa da shi ba. BJ 514.2