Babban jayayyan nan tsakanin Kristi da Shaitan da ake yi, yanzu wajen shekaru dubu shidda kenan, ya kusa karewa; mugun kuma yana kara kokarinsa na bata aikin da Kristi ke yi a madadin mutum, ya kuma daure rayuka cikin tarkokinsa. Manufarsa ita ce ya rike mutane cikin duhu da rashin tuba har sai tsakancin Mai-ceton ya kare, kuma babu sauran hadaya domin zunubi. BJ 515.1
Idan ba a yi wani kokari na musamman don jayayya da ikonsa ba, sa’anda kyaliya ta mamaye ekklesiya da duniya, Shaitan ba ya damuwa; domin ba yiwuwar rasa wadanda yake rike su cikin bauta yadda ya ga dama. Amma sa’anda aka jawo hankula zuwa ababa na har abada, mutane kuma su na tambaya: “Menene zan yi domin in sami ceto?” ya kan nemi yadda zai gwada ikonsa da na Kristi, ya kuma rushe tasirin Ruhu Mai-tsarki. BJ 515.2
Littafin ya ce a wani lokaci sa’anda malaikun Allah suka zo su gabatar da kansu a gaban Ubangiji, Shaitan ma ya zo cikin taron. (Ayuba 1:6), ba domin shi durkusa a gaban Madawamin Sarkin ba, amma domin shi ci gaba da miyagun manufofinsa kan adilai. Da manufa dayan yake kasancewa sa’anda mutane suka taru don sujada ga Allah. Ko da shike ba a ganinsa, ya na aiki da dukan himma domin shi mallaki zukatan masu-sujadar. Kamar kwararren janar ya kan shimfida tsare tsarensa kafin lokacin. Yayin da yake ganin dan sakon Allah ya na binciken Littafin, ya kan lura da batun da za a gabatar ma mutanen. Sa’an nan yakan yi anfani da dukan dabarunsa da iyawarsa don mallakar al’amurata yadda sakon ba zai kai wurin wadanda yake rudinsu game da wannan batun ba. Wanda ya fi bukatar sakon za a nuna mashi wani sha’ani da ke bukatar kasancewarsa, ko kuma ta wata hanya a hana shi jin kalmomin da za su iya zama masa dalilin samun rai. Kuma, Shaitan ya na ganin bayin Ubangiji su na damuwa saboda duhun ruhaniya da ke mammayar mutane. Ya na jin addu’o’insu domin alherin Allah da iko domin rushe kangin kyaliya da rashin kulawa da kiwuya. Sa’an nan da sabuwar himma ya kan shiga aikinsa. Ya kan jarabci mutane da kwadayi ko kuma wani irin jin dadi, ta hakan kuma ya kangarar da tunaninsu domin su kasa jin ainihin ababan da suka fi bukatar sani. BJ 515.3
Shaitan ya sani sarai cewa dukan wanda zai iya sa shi ya bar yin addu’a da binciken Littafin zai rinjaye shi da hare harensa. Saboda haka yana kirkiro kowane irin abu da zai mallaki zuciya. A kullum akwai masu cewa su na bin Allah amma maimako su ci gaba domin su san gaskiyar, sai su yi himma wajen neman kuskuren bangaskiya ko aibin hali wajen wadanda ke da banbancin ra’ayi da su. Irinsu masu taimakon Shaitan ne sosai. Masu zargin yan-uwa su na da yawa, kuma kullum su na aiki sa’anda Allah ya na aiki, bayinsa kuma suna yi masa biyayya. Za su sa launin karya kan kalmomi da ayukan masu kaunar gaskiya da kuma biyayya gareta. Za su nuna cewa wai bayin Kristi mafi himma da kwazo da musunkai an rude su ne ko kuma masu yaudara ne su. Aikinsu ne bata manufofin kowane abin gaskiya da martaba, su labarta jitajita, su ta da zato cikin zukatan marasa kwarewa. Ta kowace hanya za su so su sa a ga abinda ke da tsarki da tsabta kamar kazamtace ne mai yaudara. BJ 516.1
Amma kada a rudi wani, game da su. Nan da nan za a iya gane ko ‘ya’yan wanene su, ko kwatancin wa suke bi, kuma ko aikin wa suke yi. “Bisa ga ‘ya’yansu za ku sansanche su.” Matta7:16. Tafarkinsu kama da na Shaitan, mugun makaryaci, “mai-saran yan-uwanmu.” Ruya 12:10. BJ 516.2
Babban mai-rudin ya na da wakilai da yawa da ke shirye su gabatar da kowane irin kuskure domin su kama rayuka, ridda da aka shirya domin a gamsar da sha’awoyi da kwarewar wadanda ya ke so ya hallaka. Shirinsa ne ya kawo marasa gaskiya wadanda basu tuba ba cikin ekklesiya, domin su karfafa yin shakka da rashin ba da gaskiya, su kuma hana dukan masu marmarin ganin ci gaban aikin Allah su kuma ci gaba da shi. Da yawa da ba su da ainihin bangaskiya ga Allah ko maganarsa, suna amincewa da wadansu kaidodin gaskiya ana kuma ganin su kamar Kirista, ta hakanan kuma za su iya gabatar da kurakuransu kamar koyaswoyin Littafin. BJ 517.1
Koyaswan da ke cewa ko da menene a mutum ya gaskata ba damuwa, rudu ne na Shaitan ya san cewa gaskiya idan aka karbe ta cikin kauna, takan tsarkake ran mai-karban; sabo da haka a kullum ya na kokarin sauya ta da karya da tatsuniyoyi da wata bishara. Tun farko bayin Allah su na hamayya da mallaman karya, miyagu masu shuka karyan da ke kashe rayuka. Iliya da Irmiya da Bunlus, ba tsoro suka yi hamayya da masu juyar da mutane daga maganar Allah. Karimcin nan da ke gani kamar sahihiyar bangaskiya ba ta da muhimmanci bai karbu ga tsarkakan nan masu-kare gaskiya ba. BJ 517.2
Fassara mara inganci da ake yi ma Littafin, da ra’ayoyi masu karo da juna game da bangaskiya na addinin da ake samu cikin Kiristanci aikin babban magabcinmu ne domin ya rikita zukata don kada su gane gaskiya. Rashin jituwa da tsatsaguwa da ke tsakanin ekklesiyoyin Kirista kuma yawanci saboda an saba murda nassosi ne domin su goyi bayan ra’ayin da ake so. Maimakon binciken maganar Allah da zuciyar ladabi, domin a san nufinsa, da yawa suna neman sabon abu ne kawai, wanda babu kamarsa. BJ 517.3
Domin a tabbatar da koyaswoyin kuskure ko halayyan da suka saba ma Kiristanci, wadansu sukan dauke nassosi daga mahallinsu, ko su dauki rabin aya don tabbatar da ra’ayin nasu. Tare da dabarun Shaitan suna nutsar da kansu cikin guntayen batutuwan da suke murdawa don gamsar da bukatunsu na mutuntaka. Ta hakanan wadansu suke lalatar da maganar Allah. Wadansu kuma masu zurfin tunani, sukan yi anfani da misali da alama na Littafin, su fasarta su ta yadda za su gamsar da sha’awoyinsu, ba tare da kulawa da shaidar Littafin a matsayinsa na mai-fasarta kansa ba, sa’an nan su kan koyar da ganin damansu a matsayin koyaswar Littafin. BJ 518.1
Duk lokacin da aka shiga nazarin Littafin ba tare da ruhun addu’a da tawali’u da neman koyuwa ba, za a murda nassosi mafi sauki da mafi-wahala daga ainihin ma’anarsu. Shugabannin; ‘yan paparuma sukan zabi sassan Littafin da suka je daidai da manufarsu ne, su fasarta su yadda su ke so, sa’an nan su bayana ma mutane hakanan, yayin da su ke hana su nazarin Littafin da gane ma kansu gaskiyansa. Ya kamata a ba mutane dukan Littafin daidai yadda yake. Da bahaguwar koyaswar Littafin gara ma ba a koya masu Littafin ba gaba daya. BJ 518.2
An shirya Littafin ya zama mai-bishewa ne ga dukan masu son sanin nufin Mahalicinsu. Allah Ya ba mutane tabbataciyar kalmar annabci; malaiku har da Kristi kansa sun zo domin su sanar ma Daniel da Yohanna alamuran da dole za su faru jima kadan. Ba a bar ababan nan da suka shafi cetonmu cikin sirri ba. Ba a bayyana su ta yadda za su rudar da mai-neman gaskiya har su batar da ita ba. In ji Ubangiji ta bakin annabi Habakkuk: “Ka rubuta ruyan, ta fita a fili,… domin mai-karantawa shi yi a guje.” Hababuk 2:2. Maganar Allah a fili ta ke ga dukan masu-nazarinta da zuciyar addu’a. Kowane ainihin mai-gaskiya zai zo wurin hasken gaskiya. “Ana shibka haske domin masu adilchi.” Zabura 97:11. Kuma ba ekklesiyar da za ta ci gaba cikin adalci sai membobin ta suna neman gaskiya da himma kamar boyayyar dukiya. BJ 518.3
Ta wurin zancen ‘yanci, ko karimci, mutane ba sa ganin dabarun magabcinsu, yayin da kowane lokaci shi ya na kokarin cim ma burinsa ne. Idan ya yi nasarar sauya Littafin da ra’ayin mutane, za a kawar da dokar Allah, ekklesiyoyi kuma za su shiga bautar zunubi yayin da su ke cewa su na da ‘yanci. BJ 519.1
Ga mutane da yawa, binciken kimiyya ya zama la’ana. Aka ya yarda ambaliyar haske ta zubo ma duniya ta wurin sabobin ababa da kimiya da fasaha ke ganewa, amma ko manyan masana, in ba maganar Allah ke bishe su cikin bincikensu ba, sukan rikice cikin kokarinsu na bincika dangatakar kimiya da wahayi. BJ 519.2
Sanin mutuntaka ba cikakke ba ne, saboda haka yawanci basu iya daidaita ra’ayinsu na kimiya da batutuwan Littafin ba. Yawanci su na amincewa da ra’ayoyi da tunaninsu a matsayin tabbatattun batutuwan kimiya, su na kuma gani kamar ya kamata a gwada maganar Allah da koyaswoyin “ilimin da ana che da shi hakanan a karyache” Timothawus I, 6:20. Mahalici da aikace aikacensa sun fi karfin ganewarsu, kuma da shike basu iya bayana wadannan ta wurin dokokin halitta ba, akan maida tarihin Littafin abin shakka. Masu shakkar sahihancin Tsohon Alkawali da Sabon Alkawali sau dayawa su kan ci gaba su yi shakka cewa akwai Allah, har su mai da ikon Allah wai al’amarin halitta ne kawai. Da shike sun rabu da madogaransu, sukan shiga yawo cikin duwatsun kafirci. BJ 519.3
Ta hakanan yawanci su kan bata, Shaitan kuma ya rude su. Mutane su na kokarin fin Mahalicinsu hikima. Tunanin mutum ya na kokarin bincikawa da bayana asiran da ba za a taba bayanawa ba har abada. Da mutane za su iya bincikawa su gane abin da Allah ya sanar game da kansa da manufofinsa, da za su ga daraja da martaba da ikon Yahweh ta yadda za su gane kankantar kansu su kuma gamsu da abin da aka bayana masu da ‘ya’yansu. BJ 519.4
Babban rudun Shaitan ya sa mutane tunani da bimbini game da abin da Allah bai bayana ba, kuma bai nufa mu gane ba. Ta hakanan ne Lucifer ya rasa matsayin sa a sama. Bai gamsu ba da shike ba a fada masa dukan asiran manufofin Allah ba, ya kuma yi banza da abin da aka bayana game da aikinsa a babban matsayin da aka ba shi. Tawurin ta da rashin gamsuwan nan cikin malaikun da ke kalkashinsa kuma, ya jawo faduwarsu. Yanzu yana so ya cika zukatan mutane da ruhu dayan ya kuma kai su ga kin kula da umurnin Allah. BJ 520.1
Wadanda ba sa so su amince da bayanannun gaskiya na Littafin, kullum su na neman tatsuniyoyi masu dadi ne da za su kwantar da lamiri. Idan suka rage yawan ruhaniya da musun-kai da kaskantarwar koyaswoyinsu, karbuwarsu ga mutane takan karu. Da shike su na ji kaman hikimarsu ta wuci cewa su yi binciken Littafin da zukatan tuba da addu’a da naciya domin bishewar Allah, bas u da tsaro daga rudu. Shaitan yana shirye ya biya muradin zuciya ya na kuma sauya gaskiya da rudunsa. Ta hakanan ne mulkin paparuma ya sami iko kan zukatan mutane; kuma ta wurin kin gaskiya domin ta kunshi daukan giciye, masu Kin ikon paparuma suna bin hanya dayan. Dukan masu-kyale maganar Allah domin bin sauki, domin kada su saba ma duniya, za su karbi ridda a matsayin gaskiyar addini. Wadanda su ka ki gaskiya da gangan za su karbi kowane irin kuskure. Wanda ke kyamar rudi daya, nan da nan zai karbi wani rudin kuma. Manzo Bulus, yayin da yake magana game da wadanda “ba su amsa kamnar gaskiya da za su tsira ba,” ya ce: “Sabili da wannan fa Allah ya na aika masu da aikawar sabo, har da za su gaskata karya; domin a hukumta shari’a bisa dukan wadanda ba su gaskata gaskiya ba, amma suka ji dadin rashin adilchi.” Tassalunikaya II, 2:10-12. Da irin kashedin nan a gabanmu ya kamata mu yi hankali da irin koyaswoyin da mu ke karba. BJ 520.2
Cikin dabarun Shaitan, mafi nasara shi ne koyasuwoyin karya da al’ajiban karya na ruhohi. Ya sake kama, ya zama kamar malaikan haske, ya na baza tarunsa inda ba a taba zato ba. Da mutane za su yi nazarin littafin Allah da himma cikin addu’a domin su gane shi, ba za a bar su cikin duhu su karbi koyaswoyin karya ba. Amma ya yin da su ke kin gaskiya, suna shiga farkon yaudara. BJ 521.1
Wata koyaswa mai hatsari kuma ita ce wadda ke musun Allahntakan Kristi, ta na cewa bai kasance ba kafin zuwan sa duniyan nan. Mutane da yawa masu cewa sun gaskata Littafin sun yarda da koyaswan nan, amma kuma a koyaswar ta saba ma furcin Mai-cetonmu game da dangantakarsa da Uban, da yayayin Allahntakansa da kasancewarsa kafin zuwansa duniya. Koyaswa ce da ke murda nassosi. Ta na rage ganewar mutum game da aikin ceto, ta kuma rage bangaskiya ga Littafin, cewa wahayi ne daga Allah. Wannan ya kara munin ta da wahalar yiyuwa a yarda da ita. Idan mutane su ka ki shaidar Littafin game da Allantakan Kristi, aikin banza ne yin mahawara da su game da batun, domin ba abin da za a bayana masu har su amince. “Mutum mai tabi’ar jiki ba shi karba al’amura na Ruhun Allah ba, gama wauta su ke a gare shi, ba shi kwa da iko shi san su, gama ana gwadassu chikin ruhaniya.” Korintiyawa I, 2:14. Duk mai wannan kuskuren ba zai iya samun sahihiyar fahimtar halin Kristi ko aikinsa ba, ko kuma babban shirin Allah domin fansar mutum. BJ 521.2
Wani kuskure mai-zurfin wayo da keta kuma shi ne wai Shaitan ba wani takamammen halitta ba ne; cewa wai Littafin ya na anfani da sunan ne kawai don bayana guggan tunani da muradan mutane. BJ 521.3
Koyaswan nan da a ke maimaitawa a manyan majami’u cewa zuwan Kristi na biyu zai zo ma kowane mutum shi kadai a lokacin mutuwarsa ne dabara ce ta kawar da tunanin mutane daga zuwansa zahiri cikin gizagizai na sama. Shekaru da dama Shaitan ya na cewa, “Ga shi, ya na chikin lolokai,” (Matta 24:23-26), rayuka da yawa kuma sun salwanta ta wurin yarda da rudanin nan. BJ 522.1
`Kuma, hikimar duniya ta na koyar da cewa addu’a ba ta da muhimmanci. ‘Yan kimiyya suna cewa ba yadda za a sami sahihiyar amsar addu’a; cewa wannan zai zama ketarewar doka, cewa al’ajabi ne, kuma wai ba al’ajibai ma. Su na cewa akwai kafaffun dokoki da ke iko da dukan halitta, kuma Allah kansa ba ya yi wani abin da ya saba ma dokokin nan. Ta haka suna nuna cewa Allah kansa ya na kalkashin dokokinsa, sai ka ce Allah ba shi da ‘yanci game da yadda dokokin su ke aiki ke nan. Irin koyaswan nan ya na sabani da shaidar Littafin. Ko Kristi da almajiransa ba su aikata al’ajibai ba? Mai-ceton nan Mai-tausayi har yau ya na da rai, ya na shirye kuma ya ji addu’ar bangaskiya kamar yadda ya yi lokacin da ya ke duniya. Mutuntaka ya na hada kai da wanda ya wuci ikon dan Adam. Shirin Allah ne tawurin amsa addu’ar bangaskiya, Ya ba mu abin da in da ba mu roka ba, ba zai ba mu ba. BJ 522.2
Koyaswoyin karya a cikin Kirista ba su lissaftuwa. Ba shi yiyuwa a kiyasta miyagun sakamakon cire daya daga cikin shaidun da maganar Allah ta kafa. Masu gwada yin haka ba gaskiya daya kadai su ke ki ba. Yawanci su kan ci gaba su na kawar da kaidodin gaskiyan, daya bayan daya, har sai sun zama ainihin kafirai. BJ 522.3
Abinda da Shaitan ya ke so ya faru ke nan. Ba abin da ya ke so kamar bata amincewa da Allah, da maganarsa da a ke yi. Shaitan ne shugaban kungiyar dukarun masu shakka, kuma ya na aiki da matukar ikonsa don rudin mutane su bi bayansa. Shakka ya zama abin da a ke yayi. Jama’a da yawa su na ganin maganar Allah da rashin yarda domin ta na tsauta ma zunubi, ta na kuma hukumta shi. Wadanda ba sa so su yi biyayya da bukatunta su kan yi kokarin watsar da ikonta. Sukan kranta Littafin, ko kuma su saurari koyaswoyinsa kawai domin su sami aibi daga Littafin ko wa’azin ne. Da yawa su na zama kafirai domin su sami hujjar kin aikin da ya kamata su yi ne. Wadansu su kan yi ta zarge zarge sabo da girman kai ne da kiwuya. Da shike son jiki ya hana su yin fice tawurin gwanancewa kan wani abu mai-daraja da ke bukatar kokari da musun-kai, su so su yi suna cewa suna da mafificiyar hikima, tawurin zargi ga sakon Littafin. Akwai ababa da yawa da tunanin mutum ba zai iya ganewa ba sai da taimakon hikimar Allah, don haka su kan soki irin ababan nan. Akwai wadanda ke gani kaman gwaninta ne a tsaya a gefen rashin ba da gaskiya da shakka da rashin aminci. Amma a kalkashin kamanin son gaskiya za a ga cewa irin mutanen nan amincewa da kai da kuma fahariya ne ke motsa su. Da yawa su na jin dadin neman wani abu daga Littafin da zai rudar da tunanin wadansu. Wadansu su kan yi soka da zargi su kuma bi ra’ayi da son jayayya kawai. Ba sa gane cewa tawurin haka su na rikitar da kansu ne cikin tarkon Shaitan. Amma da shike sun bayana rashin ba da gaskiyarsu a fili, suna ji kamar dole ne su ci gaba da rike wannan matsayin. Ta wurin wannan su kan hada kai da arna su kuma rufe ma kansu kofofin mulkin Allah. BJ 523.1
Allah Ya ba da isashen shaidan cikin Littafin, cewa Littafin maganarsa ce. Muhimman gaskiya da suka shafi fansar mu a bayane su ke a fili. Ta wurin taimakon Ruhu Mai-tsarki da a ka yi ma masu nemansa da gaske alkawalinsa, kowane mutum zai iya gane ma kansa koyaswoyin gaskiyan nan. Allah Ya ba mutane kakarfan harsashe da za su kafa bangaskiyarsu akai. BJ 523.2
Duk da haka zukatan ba su isa su sami cikakkiyar fahimtar shirye shiryen Allah da manufofinsa ba. Ba yadda za mu gane Allah tawurin nemansa. Bai kamata mu yi gaggawar bude labulen da ya boye martabarsa da shi ba. Manzon ya ce: “Ina misalin wuyan binchiken shari’unsa al’amuransa kuma sun fi gaban a bi sawu!” Romawa 11:33. Za mu iya fahimtar yadda ya ke bi da mu, da manufofin da ya ke da su, domin mu gane kaunarsa da jinkansa marasa matuka da ke hade da iko mara iyaka. Ubanmu na sama ya na bi da kowane abu cikin hikima da adalci ne, kuma bai kamata mu yi rashin gamsuwa da rashin amincewa ba, amma mu durkusa cikin yarda ta bangirma. Za ya bayana mana yawan manufofinsa da ya kamata mu sani ne, fiye da wannan kuma,mu amince da ikonsa mara iyaka, da zuciyarsa cike da kauna. BJ 524.1
Yayin da Allah Ya ba da isashiyar shaidar bangaskiya, ba zai taba kawar da dukan hujjar rashin ba da gaskiya ba. Dukan masu neman hujjojin shakka za su samu, kuma wadanda su ka ki karban maganan Allah su kuma yi biyayya gareshi, wai har sai an kawar da kowace jayayya da shakka, ba za su taba samun haske ba. BJ 524.2
Rashin amincewa da Allah ya na samuwa ne daga zuciyar da ba ta tuba ba, wadda ke gaba da Allah. Amma Ruhu Mai-tsarki ne Ya ke jawo bangaskiya, kuma za ta girma yadda ke sha’awarta ne. Ba wanda zai iya samun karfi cikin bangaskiya ba tare da yin kokari da himma ba, rashin bangaskiya ya kan yi karfi idan ana karfafa shi ne, kuma idan mutane, maimakon tunani kan shaidun da Allah Ya bayar don karfafa bangaskiyarsu, suka yarda suka shiga yin tambayoyi da soke soke ba dalili, za su ga shakkunsu kullum sun tabbata. BJ 524.3
Amma masu shakkar alkawaran Allah, su na kuma kin yarda da tabbacin alherinsa, su na kin grimama Shi ne, kuma tasirinsu, maimakon jawo wadansu wurin Kristi, ya na koransu ne daga wurinsa, su itatuwa ne marasa ba da ‘ya’ya da su ke baza ressansu masu yabanya nesa, sun a rufe hasken rana daga sauran shuke shuke, suna kuma sa su yakwanewa su na mutuwa kalkashin sanyin inuwar. Aikin mutanen nan zai bayana a matsayin shaida mara karewa game da su. Su na shuka irin shakka da rashin yarda da za su haifar da girbi dole. BJ 524.4
Akwai hanya daya tak da ya kamata masu so a kubutar da su daga shakka su bi. Maimakon zargi da soka ba dalili game da abinda ba su fahimta ba, bari su saurari hasken da ke haskaka su yanzu, za su kuwa sami karin haske. Bari su yi kowane aikin da aka bayana ga ganewarsu, za a kuwa sa su iya ganewa su kuma aikata ababan da su ke shakkarsu yanzu. BJ 525.1
Shaitan zai iya kawo jabu wanda ya yi kama da ainihin sosai, ta yadda zai rudi wadanda su ka yarda a rude su, wadanda ke so su ki musun-kan nan da hadaya da gaskiyar ke bida; amma ba shi yiwuwa gare shi ya rike mutum daya kalkashin ikon sa, wanda da gaske ya ke marmari, ko ta halin kaka, ya san gaskiyar. Kristi ne gaskiya da “Haske mai-gaskiya wanda yana haskaka kowane mutun, yana zuwa chikin duniya.” Yohanna 1:9. An aiki Ruhu Mai-gaskiya Shi bishe mutane zuwa dukan gaskiya. Kuma bisa ikon Dan Allah an ce: “Ku nema, za ku samu.” “Idan kowane mutum yana da nufi shi aika nufin Allah, shi za ya sani ko abin da nike koyaswa na Allah ne.” Matta 7:7; Yohanna 7:17. BJ 525.2
Masu bin Kristi sun san kadan ne daga shirye shiryen da Shaitan da rundunansa ke kagowa game da su. Amma shi wanda ke zaune a sammai zai warware dukan dabarun nan domin cika shirye shiryensa. Ubangiji yana barin mutanensa su shiga wahalar jaraba, ba don yana jin dadin wahalarsu da azabarsu ba, amma domin matakin nan muhimmin ne ga nasararsu a karshe. Ba zai iya, bisa ga darajarsa, ya kare su daga jaraba ba, gama ainihin manufar jarabarsu ita ce don shirya su ki dukan jarabobin mugunta. BJ 525.3
Ko miyagun mutane ko aljannu ba za su iya hana aikin Allah ba, ko kuma su rufe shi daga kasanchewa da mutanensa, idan da zukatan tuba da saukin kai, za su furta su kuma rabu da zunubansu, cikin bangaskiya kuma su karbi alkawuransa. Kowace jaraba, kowane tasiri mai-hamayya, bayananne ko na sirri, za a iya kin sa, “Ba ta wurin karfi ba, ba kwa tawurin iko ba, amma tawurin ruhuna, in ji Ubangiji Mai-runduna.” Zakariya 4:6. BJ 526.1
“Gama idanun Ubangiji suna bisa masu-adilchi, kunnuwansa kuma suna bude ga jin rokonsu:… Wanene shi da za ya yi maku ta’adda kuma, idan kuna da himma domin nagarta?” 1Bitrus 3:12,13. Sa’anda Balaam, don kwadahin arziki, ya yi duba game da Israila, kuma tawurin hadaya ga Allah ya so ya jawo la’ana kan mutanensa, Ruhun Allah Ya hana muguntan da ya so ya ambata, dole kuma Balaam ya ce: “Ya ya zan la’anta wadanda Allah ba Ya la’anta ba? Yaya zan yi kirarin reni ga wadanda Ubangiji ya yi ba?” “Bari in mutu irin mutuwar mai-adilchi, bari karshena ya zama kamar nasa!” Bayan an sake yin hadaya kuma annabin nan mara-biyayya ga Allah ya ce: “Ga shi na karbi umurni in sa albarka; shi ya albarkache, ni kwa ba ni da iko in juyas. Ba ya ga mugunta a chikin Yakub ba, baya kwa ga shiririta chikin Israila ba; Ubangiji Allahnsa yana tare da shi, sowa su ke yi domin sarki.” “Ba wani magani da za ya chiwuchi Yakub; ba wani dabo da za ya chiwuchi Israila; yanzu fa za a bayana ma Yakub da Israila abin da Allah ya aika!” Duk da haka an shirya wurin hadaya, so na uku, Balaam kuma ya sake kokarin la’antawa. Amma daga lebunan annabin, ba da sonsa ba, Allah Ya bayana ci gaban zababbunsa, ya kuma tsauta ma wauta da muguntar magabtansu. Ya ce: “Mai-albarka ne dukan wanda ya albarkace ka, la’antache ne dukan wanda ya la’antadda kai.” Littafin Lissafi 23:8,10,20,21-23; 24:9. BJ 526.2
Mutanen Israila a wannan lokacin suna biyayya ga Allah, kuma muddan sun ci gaba suna biyayya ga dokarsa, ba wani iko a duniya ko lahira da zai yi nasara bisan su. Amma la’anan da ba a ba Balaam damar furtawa kan mutanen Allah ba, a karshe ya yi nasara ya furta shi akansu ta wurin rinjayarsu zuwa cikin sunubi. Sa’anda suka ketare dokokin Allah, suka raba kansu da Shi, aka kuma bar su su ji ikon mai-hallakaswan. BJ 526.3
Shaitan ya sani sarai cewa mutum mafi-kumamanci da ke cikin Kristi ya fi karfin rundunonin duhu, kuma ya san cewa idan ya bayana kansa a fili, za a tare shi, a ki shi. Saboda haka yakan nemi janye mayakan giciyen daga mafakarsu, yayinda yake boye yana jira tare da dakarunsa, suna jira su hallaka duk wanda ya shiga yankinsa. Ta wurin dogara ga Allah da biyayya ga dukan dokokinsa ne kadai za mu iya samun tsaro. BJ 527.1
Ba wanda ke da rashin hatsari, na rana daya ko sa’a guda in ba addu’a. Musamman, ya kamata mu roki Ubangiji hikimar fahimtar maganarsa. A nan an bayana dabarun majarabcin da hanyoyin da za a iya nasaran kansa. Shaitan kwararre ne wajen fadin nassosi, yana ba da fasara ta sa garesu ta yadda ya ke so ya sa mu tuntube. Ya kamata mu yi nazarin Littafin da tawali’un zuciya, kada mu taba manta dogararmu ga Allah. Yayin da dole ne a kullum mu yi hankali da dabarun Shaitan, ya kamata mu yi addu’a cikin bangaskiya kowane lokaci cewa: “Kada ka kai mu chikin jaraba.” BJ 527.2