Da tarihin farko na mutum, Shaitan ya fara kokarin sa na rudin yan Adam. Shi wanda ya ta da tawaye a sama ya so ya sa mazaunan duniya su hada hannu da shi cikin yakinsa da gwamnatin Allah. Adamu da Hauwa’u sun yi farinciki cikin biyayya da dokar Allah, wannan kuma ya zama shaida kullum sabanin zargin da Shaitan ya yi a sama, cewa dokar Allah ta danniya ce kuma tana sabani da jin dadin halittunsa. Bugu da kari, Shaitan ya yi kishin kyakyawan gidan da aka shirya ma Adamu da Hauwa’u, marasa zunubi. Ya kudurta zai jawo faduwarsu, domin bayan ya raba su da Allah ya kuma kawo su kalkashin ikonsa, zai iya samun mallakar duniya ya kuma kafa mulkinsa a nan, inda zai yi sabani da Madaukaki. BJ 528.1
Da Shaitan ya bayana kansa da ainihin halinsa da an tare shi nan da nan, gama an rigaya an gargadi Adamu da Hauwa’u game da mugun magabcin nan; amma ya yi aiki cikin duhu ne, ya boye manufarsa, domin ya cimma burinsa. Sa’an da ya yi anfani da maciji, wanda a lokacin nan halitta ne mai-kyaun gani sosai, sai ya ce ma Hauwa’u: “Ko Allah ya che, baza ku chi daga dukan itatuwa na gona ba?” Farawa 3:1. Da Hawa’u ba ta shiga musu da majarabcin ba, da ba ta sami damuwa ba, amma ta shiga hira da shi ta kuwa shiga tarkon dabarunsa. Har yanzu ma haka ne ake rinjayar mutane da yawa. Su kan yi shakka suna musu game da umurnin Allah, kuma maimakon biyayya ga dokokin Allah, su kan karbi ra’ayoyin mutane, wadanda ke badda kaman dabarun Shaitan. BJ 528.2
“Sai machen ta che ma machijin, daga ‘ya’yan itatuwan gona an yarda mamu mu chi; amma daga ‘ya’yan itache wanda ke chikin tsakiyar gona, Allah Ya che, ba za ku chi ba, ba kwa za ku taba ba, domin kada ku mutu. Sai machijin ya che ma machen, Ba lallai za ku mutu ba; gama Allah ya sani ran da kuka chi daga chiki, ran nan idanun ku za su bude, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.” Aya 2-5. Ya ce za su zama kamar Allah, su sami hikimar da ta fi ta da, su kuma sami yanayin rayuwa da ya fi na da. Hawa’u ta amince da jaraba kuma ta wurin tasirinta, ta jawo Adamu cikin zunubi. Sun yarda da kalmomin macijin, cewa Allah bai nufi abinda ya fada ba; basu gaskata Mahalicinsu ba, suka ga kamar yana rage ‘yancin su ne kuma cewa za su iya samun hikima mai-yawa da daukaka tawurin ketare dokarsa. BJ 529.1
Amma mene ne Adamu, bayan zunubinsa, ya gane cewa kalmomin nan “chikin rana da ka chi, mutuwa zaka yi lallai” ke nufi? Ko ya ga cewa su na nufin abin da Shaitan ya ce masu ne, cewa za a kai shi cikin yanayin rayuwa mafi girma ne? In da haka ne, da ketare dokar Allah ya zama da riba sosai, da Shaitan kuma ya zama babban mai-taimakon zunubin mutum, za ya koma kasa daga inda aka ciro shi; “Gama turbaya ne kai, ga trubaya za ka koma.” Aya 19. Kalmomin Shaitan “Idanunku za su bude,” sun zama gaskiya ta hanya daya ne kawai; Bayan Adamu da Hawa’u sun yi ma Allah rashin biyayya, idanunsu sun bude, suka gane wautarsu; sun san mugunta, sun kuma dandana dacin sakamakon rashin biyayya. BJ 529.2
A tsakiyar Adnin ne itacen rai ya kasance, ‘ya’yansa kuma suna da ikon sa rai ya dawama. In da Adamu ya ci gaba da biyayya ga Allah, da ya ci gaba da cin yayan itacen rai, kuma da ya rayu har abada. Amma sa’an da ya yi zunubi, an raba shi da ci daga wannan itacen, ya kuma zama mai-mutuwa. Hukumcin Allah cewa, “turbaya ne kai, ga trubaya za ka koma,” yana Magana game da shudewar rai ne gaba daya. BJ 529.3
Rashin mutuwa da aka yi ma mutum alkawalinsa bisa sharadin biyayya, an rasa shi ta wurin ketare doka. Adamu bai iya mika ma zuriyarsa abinda shi bai mallaka ba; kuma da ba bege domin jinsin nan na ‘yan Adam da ya fadi, ba don Allah, tawurin hadayar Dansa, ya kawo masu yiwuwar samun rashin mutuwa ba. Sa’anda “mutuwa ta bi kan dukan mutane, da shi ke duka sun yi zunubi,” Kristi “ya haskaka rai da dawama tawurin bishara.” Romawa 5:12; 2Timothawus 1:10. Kuma tawurin Kristi ne kadai ana iya samun dawama. In ji Yesu: “Wanda yana ba da gaskiya ga Dan yana da rain a har abada; amma wanda ba ya yi biyayya ga Dan ba, ba za shi ganin rai ba.” Yohanna 3:36. Kowa zai iya mallakar albarkan nan idan ya bi sharuddan. Dukan “wandada ke bidan daukaka da girma da wanzuwa ta wurin hankuri chikin aikin nagarta,” za su sami “rai na har abada.” Romawa 2:7. BJ 530.1
Wanda kadai ya yi ma Adamu alkawalin rai cikin rashin biyayya babban mai-yaudaran nan ne. Kuma furcin da macijin ya yi ma Hauwa’u a Eden cewa: “Ba lallai za ku mutu ba.” Shi ne hudubar farko game da dawamar ran mutum. Duk da haka, wannan Magana wadda Shaitan ne tushenta, ana maimaita ta a majami’un Kirista, kuma yawancin yan Adam sun yarda da ita kamar yadda iyayen mu na farko suka yarda da ita. Hukumcin Allah cewa, “wanda ya yi zunubi shi za ya mutu” (Ezekiel 18:20), an mai da shi: Wanda ya yi zunubi ba za ya mutu ba, amma za ya rayu har abada. Abin mamaki ne yadda mutane ke maganar Shaitan suna kuma kin gaskata maganar Allah. BJ 530.2
Da bayan faduwar mutum an ba shi damar zuwa wurin itacen rai da ya rayu har abada, ta haka kuma da zunubi ya dawama. Amma cherubim da takobi mai-hasken wuta “sun tsare hanyar itache na rai.” (Farawa 3:24), kuma ba a ba ko mutum daya daga iyalin Adamu izinin wuce shingen nan har ya ci daga ‘ya’yan itace mai-ba da rai din ba. Sabo da haka ba mai-zunibi mara mutuwa. BJ 530.3
Amma bayan faduwar, Shaitan ya bukaci malaikunsa su yi kokari na musamman don koyar da cewa mutum mara mutuwa ne, kuma bayan an rudi mutane suka karbi karyan nan, sai su sa su su dauka cewa mai-zunubi zai rayu cikin wahala ta har abada. Yanzu sarkin duhu, ta wurin wakilansa, yana nuna cewa Allah azalumi ne mara gafara, cewa yana jefa dukan wadanda ba ya sonsu cikin lahira, yana kuma sa su dandana fushinsa har abada, kuma cewa yayin da suke fama da azaba mai-tsanani suna kuma birgima cikin wuta ta har abada, Mahalici zai dinga jin dadin kallonsu. BJ 531.1
Haka ne babban magabcin ke daukan halayyan da ya shafa ma Mahalici mai-kaunar ‘yan Adam. Mugunta shaidanci ne. Allah kauna ne, kuma dukan abin da ya halitta mai-tsabta ne, mai-tsarki, mai-ban sha’awa, har sai da babban dan tawaye na farko ya shigo da zunubi. Shaitan kansa ne magabcin da ke jarabtar mutum shi yi zunubi, sa’an nan ya hallaka shi in ya iya; sa’anda ya tabbatar da muguntarsa, sai ya yi murna da hallakan da ya jawo. In ya sami izni zai share dukan ‘yan Adam zuwa cikin kamarsa. Ba don shiga-tsakanin ikon Allah ba, ko dan Adam ko ‘yar Adam daya ba za su tsira ba. BJ 531.2
Shaitan yana so ya rinjayi mutane yau, yadda ya rinjayi iyayenmu na farko, ta wurin girgiza amincewarsu da Allah da sa su yin shakkan hikimar gwamnatinsa da adalcin dokokinsa. Shaitan da ‘yan sakonsa suna nuna cewa wai Allah ya fi su mugunta ma, domin su bada hujjar muguntarsu da tawayensu. Babban mai-yaudaran yana kokarin tura ma Ubanmu na sama mumunan mugun halin nan nasa, domin ya sa a ga kamar an yi masa rashin adalci sosai da aka kore shi daga sama don bai yarda da mai-mulkin nan mara adalci ba. Yana nuna ma duniya irin ‘yancin da za su mora kalkashin mulkinsa na tawali’un sabanin bautan da matsanantan dokokin nan na Allah ke dorawa kan mutane. Ta haka yana nasara wajen rudin mutane su janye biyayyarsu ga Allah. BJ 531.3
Ina yawan sabanin kauna da jinkai da adalci ma, da koyaswan nan cewa matattun miyagu suna shan azaba da wuta da kibritu a lahira mai-konawa har abada, cewa saboda zunuban gajerewar rayuwarsu a duniya, za su sha azaba duk tsawon rayuwar Allah. Duk da haka ana baza wannan koyaswar, kuma tana cikin kundin koyaswoyin Kirista da yawa. In ji wani masani; “Ganin azabar lahira zai kara farincikin tsarkaka har abada. Sa’an da suka ga wadansu masu yanayi iri daya da su, da aka kuma haife su ta hanya dayan, suna fama da irin wahalan nan, su kuma suka bambanta hakanan, za su gane yawan farincikin da su ke da shi.” Wani kuma ya ce: “Yayin da umurnin rashin gamsuwa ke cika har abada da fushi, hayakin azabarsu za ya yi ta hawa har abada, a idon wadanda aka yi masu jin kai, wadanda, maimakon bin tafarkin wahallalun nan za su ce, Amin, Halelluya! Yabo ga Ubangiji!” BJ 532.1
A cikin magabar Allah, ina ne ake samun wannan koyaswar? Fansassu a sama za su rasa tausayi da jinkai ne, har ma da juyayi na mutuntaka? Za a sauya wadannan da rashin kulawa da mugunta irin na marasa mutunci ne? Babu, babu; wannan ba koyaswar Littafin Allah ba ne. Masu koyas da ra’ayoyin nan da suka gabata, ko da shi ke masana ne, watakila kuma masu fadin gaskiya ne su, amma kuma Shaitan ya rude su da dabarunsa. Yakan sa sun kasa gane Littafin, ya ba maganar Allah kamanin fushi da mugunta irin na shi Shaitan, amma ba na mahalicinmu ba. “In ji Ubangiji Yahweh, na rantse da raina, ba ni da wani jin dadi chikin mutuwar mugu ba, gwamma dai shi mugun ya juyo ga barin hanyassa, shi yi rai; ku juyo dai, ku bar miyagun halulukanku; don mi za ku mutu? Ezekiel 33:11. BJ 532.2
Wace riba Allah zai samu in mun yarda cewa shi yana jin dadin kallon azaba mara karewa, cewa yana farinciki da ihu da birgima da zage zagen wahalalun halitun da Shi ya ke rike da su a cikin wutar jahannama? Ko munanan suruce surucen nan za su yi dadin ji a kunnen Mai-kauna mara-matuka? Ana koyar da cewa wahal da miyagu har abada zai nuna yadda Allah Ya ki jinin zunubi da shi ke mugunta ce mai-hallaka salama da odan dukan halitta. Wannan sabo ne mai-ban tsoro! Sai ka ce don Allah Ya ki jinin zunubi ne ya sa a ke yinsa. Bisa ga koyaswoyin masanan nan, ci gaba da azabatarwa ba tare da begen jin kai ba tana haukatar da masu zunubin kuma yayin da su ke bayana fushinsu ta wurin zage zage da sabo, suna kara yawan laifinsu ke nan har abada. Ba za a kara darajar Allah tawurin damuwa da ci gaba da karuwar zunubi hakanan har abada ba. BJ 533.1
Tunanin mutum ba zai iya kiyasta yawan illan da koyaswan nan na azaba har abada ya jawo ba. Addinin Littafin, cike da kauna da nagarta, da yalwar tausayi ya kazamtu da camfi ya kuma yafa tsoro. Idan mun dubi kamanin karyan da Shaitan ya shashafa ma halin Allah, ko za mu yi mamakin yadda ake tsoron Mahalicinmu Mai-jin kai, har ma ana kinsa? Munanan ra’ayoyi da ake koyarwa a majami’u ko ina a duniya sun haifar da miliyoyin masu shakka da kafirai. BJ 533.2
Koyaswar azaba ta har abada tana cikin koyasuyoyin da su ke cikin ruwan anab na fasikancin Babila da ta sa dukan al’ummai su sha. Ruya 14:8; 17:2. Abin mamaki ne cewa ma’aikatan Kristi sun yarda da riddan nan suna kuma koyar da shi a bagadi. Sun karbe ta daga Rum ne, yadda suka karbi Assabbat na karyan. Gaskiya kam, manyan nagargarun mutane sun koyar da ita, amma a lokacin, haske game da batun nan bai zo masu, kamar yadda ya zo mana ba. Alhakinsu game da hasken da su ke da shi ne kadai a zamaninsu; mu za mu ba da lissafin hasken zamanin mu. Idan mun juya daga shaidar maganar Allah, muka karbi koyaswoyin karya wai don iyayenmu sun koyar da su, za mu fadi cikin hukumcin Babila, muna sha daga ruwan anab na fasikancinta kenan. BJ 533.3
Da yawa da basu yarda da koyaswar azaba ta har abada ba, suna wata kuskuren dabam kuma. Sun ga Littafin ya nuna cewa Allah mai-kauna da tausayi ne, kuma basu yarda cewa zai iya jefa halitunsa cikin wutar jahannama mai-konawa har abada ba. Amma da shike sun dauka cewa rai baya mutuwa, sai suka dauka cewa a karshe za a ceci dukan ‘yan Adam kenan. Da yawa sun dauka cewa kowace barazanar Littafin an shirya ta ne domin ta razanar da mutane su yi biyayya; amma ba za a aiwatar da barazanar a zahiri ba. Don haka mai-zunubi zai iya rayuwar holewa, ya ki kulawa da umurnin Allah, duk da haka kuma ya dauka cewa Allah zai karbe shi. Irin koyaswar gangancin nan game da jin kan Allah ba tare da kula adalcinsa ba, takan gamsar da zuciyar jiki ta mutumtaka ta kuma karfafa miyagu cikin zunubansu. BJ 534.1
Don nuna yadda masu cewa za a ceci dukan mutane su ke murda nassosi don tabbatar da koyaswoyinsu, furcinsu ma kawai ya isa. A wajen janaizan wani saurayi mara addini, wanda ya mutu nan take bayan ya gamu da hatsari, mai-wa’azin ya zabi nassin nan game da Dauda ne, cewa: “Ya hankura domin Ammon da shi ke ya rigaya ya mutu.” Samaila II, 13:39. BJ 534.2
Mai-maganan ya ce: “Sau da yawa ana tambaya ta, me zai faru da wadanda sukan bar duniya cikin zunubinsu, su mutu watakila ma da jinin zunibin da suka aikata a rigarsu, basu wanke ba ma, ko kuma suka mutu kamar yadda saurayin nan ya mutu bai taba furta bangaskiya ko ya dandana addini ba. Mun gamsu da nassosin; amsarsu za ta magance matsalar. Amnon mai-zunubi ne matuka; bai tuba ba, mashayi ne shi, kuma cikin buguwarsa aka kashe shi. Dawuda annabin Allah ne; ai ya san ko Amonon zai wahala ne ko zai ji dadi ne a duniya mai-zuwa. Mene ne zuciyarsa ta ce?” Ran sarki Dawuda kwa ya yi marmarin shi bi Absalom: gama ya hankura domin Amnon, da shi ke ya rigaya ya mutu.” Aya 39. BJ 534.3
“Kuma me za a gano daga kalmomin nan? Bai nuna cewa ba zancen whala ta har abada ba cikin addininsa? Haka mu ke gani, nan kuma mun gano koyaswar da ke goyon bayan ra’ayin nan mai-gamsarwa, mai-wayewa, mafi-nuna kauna, cewa a karshe za a sami salama da tsabta ko ina. Ya hakura, ganin cewa, dansa ya mutu. Kuma don me? Domin ta wurin idon annabci ya hangi gaba ya ga dan nan nesa daga dukan jarabobi, an kubutar da shi daga bautar zunubi aka tsarkake shi daga dukan rubansa, kuma bayan an ba shi isashen tsarki, da wayewa, an karbe shi cikin taron ruhohi masu farinciki da ke can sama. Ta’aziyarsa kawai ita ce cewa tawurin cire kaunatacen dansa daga yanayin zunubi da wahala na yanzu, ya je inda za a zuba ma rayuwarsa ta duhu lumfashi mafi-daraje na Ruhu Mai-tsarki, inda za a bude ma tunaninsa hikimar sama da murna mai dadi na kauna mara matuka, ta hakanan kuma a shirya shi da yanayin tsatsarka, ya ji dadin hutu da gado na sama. BJ 535.1
“Cikin batutuwan nan, za a gane cewa mun gaskata cewa ceton sama bai danganta ga wani abin da za mu iya yi a wannan rayuwar ba ne; kuma ba kan wata sakewar zuciya yanzu ba ce, ko kuma bangaskiya na yanzu, ko addinin da ake bi yanzu,” BJ 535.2
Hakanan ne ma’aikacin Kristi din nan ya maimaita karyan da macijin ya furta a Adnin cewa “Ba lallai za ku mutu ba.” “Ran da kuka chi daga chiki, ran nan idanunku za su bude, za ku zama kamar Allah,” ya ce komi munin zunubin mutum: da mai-kisa, da barawo, da mazinaci, bayan mutuwa za a shirya su domin shiga salama mara-matuka. BJ 535.3
Kuma daga mene ne mai-murda nassosin nan ya sami ra’ayinsa? Daga magana daya inda Dawuda ya bayana danganarsa ga nufin Ubangiji. Ransa “ya yi marmarin shi bi Absalom; gama ya hankura domin Amnon, da shi ke ya rigaya ya mutu.” Da shi ke zafin bakincikinsa ya ragu a hankali, tunaninsa ya koma daga wurin mamacin zuwa wurin rayayyen dan, wanda ya kori kansa don tsoron horo sabo da laifinsa. Kuma shaidar ke nan da ake anfani da ita cewa da zaran mashayi da mazinacin nan Amnon ya mutu nan da nan a ka kai shi mazamna na salama, inda za a tsarkake shi a shirya shi don ma’amala da malaiku marasa zunubi! Wannan tatsuniya ce mai-gamsarwa kam, shiryayya da kyau domin gamsar da zuciya ta jiki na mutumtaka; wannan koyaswar Shaitan ce, kuma tana cika aikinsa da kyau. Ko ya kamata mu yi mamaki cewa mugunta tana yawaita sabo da wannan koyaswar? BJ 535.4
Hanyar da mallamin karyan nan ya bi misali ne na wadansu da yawa. Akan raba wadansu kalmomin Littafin daga sauran nassin da yawanci yakan nuna cewa ainihin ma’anar ta saba ma fasarar da ake bayarwa; sa’an nan akan murda guntayen nassosin tabbatar da koyaswoyin da ba su da tushe cikin maganar Allah. Shaidar da aka yi anfani da ita don nuna cewa Amnon mashayi yana sama zance ne kawai da ya saba ma bayyananiyar koyaswar Littafin cewa mashayi ba zai gaji mulkin Allah ba. Korintiyawa I, 6:10. Hakanan ne masu shakka da marasa ba da gaskiya su kan juya gaskiya ta zama karya. Ann kuma rudin jama’a da yawa ta wurin dabarunsu, a lallaba su su yi barci cikin zaman lafiya irin na mutumtaka. BJ 536.1
Da gaskiya ne cewa rayukan mutane su kan wuce kai tsaye ne zuwa sama da zaran an mutu, da za mu gwammaci mutuwa maimakon rai. Koyaswan nan ta sa mutane da yawa sun kashe kansu. Sa’anda kamuwa ko rikicewa ko yankan buri ya fi karfinsu, su kan ga kamar ya fi masu sauki su yanke rayuwarsu su tashi zuwa salamar duniya ta har abada kawai. BJ 536.2
Allah Ya shaida cikin maganarsa cewa zai hori masu ketare dokarsa. Masu rudin kansu cewa jin kansa ya yi yawa ta yadda ba zai iya aiwatar da hukumci kan mai-zunubi ba, su dubi giciyen Kalfari ma kawai mana. Mutuwar Dan Allah shaida ce cewa “hakin zunubi mutuwa ne,” cewa kowace ketarewar dokar Allah dole zai gamu da ramuwarsa. Kristi mara-zunubi ya zama zunubi sabo da mutum. Ya dauki laifin ketarewar, da boyewar fuskar Ubansa, har sai da zuciyarsa ta karye, ransa kuma ya fice. An yi dukan hadayan nan domin a fanshi masu zunubi ne. Ba wata hanya dabam kuma da za a iya kubutar da mutum daga horon zunubi. Kuma kowane mutumin da ya ki zama mai-hannu cikin kafaran da aka tanada da tsada hakanan dole zai dauki laifi da horon zunubi a jikinsa. BJ 536.3
Bari mu dubi abin da Littafin ke koyarwa game da marasa imani da marasa tuba, wadanda masu cewa za a ceci kowane mutum ke cewa suna sama, a matsayin tsarkakan malaiku masu farinciki. “Ni ba shi daga chikin mabulbulan ruwa na rai kyauta.” Ruya 21:6. Alkawalin nan ga masu kishi ne kawai-sai masu jin cewa suna bukatar ruwan rai, suna kuma neman shi fiye da dukan sauran ababa, za a ba su.” “Wanda ya yi nasara za ya gada wadannan abu, in zama Allahnsa kuma, shi zama da na.” Aya 7. Nan ma an ba da sharudda. Domin mu gaji dukan abu, dole sai mun ki zunubi mu ka yi nasara da shi kuma. BJ 537.1
Tawurin annabi Ishaya, Ubangiji ya bayana cewa: “Ku ambaci mai-adilchi, ku che, Dadi za ya ji.” “Kaiton mai-mugunta! Wuya za ya sha; gama aikin hannuwansa za a saka masa.” Ishaya 3:10,11. Mai-hikiman yace: “Mai-zunubi ya yi mugunta sau dari, har ma ya dade a duniya, duk da haka na sani lallai, wadanda ke tsoron Allah za su zama lafiya, masu-iabda ke nan; amma babu lafiya ga miyagu.” Mai-wa’azi 8:12,13. Bulus kuma ya sahida cewa mai-zunubi yana tanada ma kansa “fushi chikin ranar fushi da bayannuwar hukumchi mai-adilchi na Allah, shi da za ya saka ma kowane mutum gwalgwadon ayukansa;” “tsanani da azaba a kan kowane ran mai-aika mugunta.” Romawa 2:5,6,9. BJ 537.2
“Da mai-fasikanchi, da mutum mai-kazamta, da mutum mai-sha’awa, watau mai-bautan gumaka ke nan, duk basu da gadon komi chikin mulkin Kristi na Allah.” Afisawa 5:5, “Ku nemi salama da dukan mutane, da tsarkakewa wadda babu mutum da za shi ga Ubangiji im ba tare da ita ba: Ibraniyawa 12:14. “Masu-albarka ne wadannnan da ke wankin tufafinsu, domin su sami iko su zo wurin itachen rai, su shiga kuma ta kofofi chikin birni. Daga waje da karnuka, da masu-sihiri, da fasikai, da masu-kisan kai, da masu-bautan gumaka, da dukan wanda yana kamnar karya yana kwa aikata ta.” Ruya 22:14,15. BJ 538.1
Allah ya ba mutane bayanin halinsa da na hanyar da yake bi da zunubi. “Ubagiji, Allah ne chike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinkai da gaskiya, yana tsaron jinkai domin dubbai, yana gafarta laifi da sabo da zunubi; ba shi kubutadda mai-laifi ko kadan.” Fitowa 34:6,7. “Za ya hallaka dukan miyagu.” “Masu-zunubi fa za a hallaka su gaba daya: za a datse karshen miyagu.” Zabura 145:20; 37:38. Za a yi anfani da karfin gwamnatin Allah da ikonsa don kwantar da tawaye; duk da haka dukan nuna adalci tawurin ramuwa ba zai saba ma halin Allah na jin kai da tsawon jimrewa da kauna ba. BJ 538.2
Allah baya tilasta mutuwa ba ya son biyayya irin na bayi. Yana so halitunsa su kaunace Shi domin ya cancanci kauna ne. Yana so su yi masa biyayya domin sun gane hikimarsa, da adalci da kaunarsa ne. Kuma wadanda ke da kyakyawar ganewar halayyan nan za su kaunace Shi domin suna sha’war halayyan nasa ne. BJ 538.3
Halayyan alheri da jinkai da kauna da Mai-ceton mu Ya koyar Ya kuma kwatanta hoto ne na halin Allah da nufinsa. Kristi ya bayana cewa bai koyar da komi ba sai abinda ya karba daga wurin Ubansa. Kaidodin gwamnatin Allah suna da cikakkiyar jituwa da umurnin mai-ceton cewa “Ku yi kaunar magabtanku.” Allah yana aiwatar da hukumci kan miyagu, domin dukan halitta ta anfana, har ma domin wadanda aka hukumta din su anfana ne. Zai ba su farinciki idan zai iya yin hakan bisa ga dokokin gwamnatinsa da adalcin halinsa ne. Yana kewaye su da alamun kaunarsu, yana ba su sanin dokarsa, ya kuma bi su da tayin jin kansa; amma suna rena kaunarsa, su wofinta dokarsa, su kuma ki jin kansa. Yayin da kullum suna karban baye bayensa, suna cin mutuncin mai-bayarwan; sun ki Allah domin sun san yana kyamar zambansu. Ubangiji yana tsawon jimrewa da zunubansu; amma sa’ar hukumcin za ta zo a karshe, sa’an da za a tabbatar da karshensu. Ko a lokacin shi zai daura ‘yan tawayen nan a jikinsa ne? Zai tilasta su yin nufinsa ne? BJ 538.4
Wadanda suka zabi Shaitan ya zama shugabansu, suka kuma kasance kalkashin ikonsa ba su shirya shiga wurin Allah ba. Girman kai, yaudara, anishuwa da zalunci sun kafu cikin halayensu. Za su iya shiga sama su kasance tare da wadanda suka rena suka kuma ki jininsa a duniya? Gaskiya ba za ta taba burge makaryaci ba. Tawali’u ba zai gamsar da mai-daga kai da girman kai ba; tsabta ba za ta karbu ga mara-kirki ba. Kauna zalla ba ta burge mai-son kai. Wane irin jin dadi ne sama za ta iya ba wadanda sun dukufa cikin son kai da kayan duniya? BJ 539.1
Da wadanda suna rayuwar tawaye ga Allah za su iske kansu a sama faraf daya, su ga yanayin cikakken tsarki da ke wurin, yadda kowa yana cike da kauna, kowace fuska tana walkiya da farinciki, ga muzika mai dadi yana daukaka Allah da Dan ragon, haske mara iyaka kuma yana zubowa kan fansassu daga fuskar shi wanda ke zaune kan kursiyin, ko su ga wadanda zukatansu ke cike da kiyayya ga Allah da gaskiya da tsarki, za su iya cudanya da taron mutanen da ke sama su kuma sa baki cikin wakokin yabon su? Za su iya jimre darajar Allah da Dan ragon? Babu, babu, an ba su shekaru na damar samun halayya irin na sama, amma basu taba horar da tunanin su ya kaunaci tsarki ba; basu taba koyon harshen sama ba, yanzu kuma lokaci ya kure. Rayuwar tawaye ga Allah ta sa ba su cancanci sama kuma ba. Tsabtar sama da tsarkinta da salamar ta za su zama wuta mai-cinyewa. Za su so su gudu daga wuri mai-tsakin nan. Za su gwammaci hallaka, domin su buya daga fuskar wanda ya mutu domin shi fanshe su. Karshen miyagu ya tabbata bisa ga sabon su ne. Rashin kasancewarsu ganin daman su ne, kuma adalci ne da jinkan Allah. BJ 539.2
Kamar ruwan Tufana, wutar babban ranan tana bayana hukumcin Allah ne cewa miyagun ba su da magani. Ba sa so su ba da kai ga mulkin Allah. Sun zabi tawaye, kuma sa’anda rai ya kare, lokaci ya kure da za a juya tunaninsu, daga zunubi zuwa biyayya, daga kiyayya zuwa kauna. BJ 540.1
Tawurin barin ran Kayinu mai-kisankai, Allah Ya ba duniya kwatancin sakamakon barin mai-zunubi ya rayu ya ci gaba da zunubi ba sassauci. Ta wurin tasirin koyaswar Kayinu da kwtancinsa, zuriyarsa da yawa chikin duniya, kuma kowache shawara ta tunanin zuchiyassa mugunta che kadai kullayaumi. “Duniya kwa ta bachi a gaban Allah, duniya kuma ta chika da zalumchi.” Farawa 6:5, 11. BJ 540.2
Cikin jin kai ga duniya, Allah Ya shafe miyagun mazamnanta a lokacin Nuhu. Cikin jin kai ya shafe mazamnan Sodom. Ta wurin ikon yaudarar Shaitan, masu aikata zunubi suna samun tausayawa da sha’awa, ta haka kuma kullyaumi suna kai wadansu ga tawaye. Haka ya kasance lokacin Kayinu da lokacin Nuhu, da kuma lokacin Ibrahim da Lot; inda yake a lokacin mu. Cikin jin kai ga dukan halitta ne a karshe Allah za ya hallaka masu kin alherinsa. BJ 540.3
“Hakin zunubi mutuwa ne; amma kyautar Allah rai na har abada ce tawurin Kristi Yesu Ubangijin mu.” Romawa 6:23. Yayin da da rai gadon masu adalci ne, mutuwa ladar miyagu ce. Musa ya bayana ma Israila cewa: “Duba a gabanku na sa rai da nagarta, mutuwa da mugunta.” Kubawar Sharia 30:15. Mutuwa da ake magana a nassosin nan ba wadda a ka furta ma Adamu ba ce, domin dukan ‘yan Adam suna shan horon zunubinsa. Mutuwa ta biyu ce a ke bambanta ta da rai madawami. BJ 541.1
Sanadiyar zunubin Adamu mutuwa ta bi kan dukan ‘yan Adam. Kowa yana zuwa kabari. Kuma ta wurin tanadin shirin ceto, za a kawo kowa daga kabarinsa. “Za a yi tashin matattu na masu-adalci da na marasa-adilchi.” “Gama kamar yadda chikin Adamu duka suna mutuwa, hakanan chikin Kristi duka za su rayu.” Ayukan 24:15; Korintiyawa I, 15:22. Amma an bambanta tsakanin kashi biyu na masu tashin. “Dukan wadanda suna chikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma; wadanda sun yi nagarta su fito zuwa tashi na rai, wadanda sun yi mugunta, zuwa tashi na shari’a.” Yohanna 5:28,29. Wadanda aka ga sun cancanci tashi na rai masu albarka ne, masu-tsarki. “Mutuwa ta biyu ba ta da iko bisansu.” Ruya 20:6. Amma wadanda basu sami gafara, ta wurin tuba da bangaskiya ba dole za su karbi horon zunubi, watau “hakin zunubi.” Za su sha horo, kowa da tsawon horonsa da zurfin horonsa kuma dabam, “gwalgwadon aikinsa,” amma za su karasa da mutuwa ta biyu. Da shi ke ba shi yiwuwa ma Allah, daidai da adalcinsa da jinkansa, ya ceci mai-zunubi cikin zunubinsa, zai hana shi kasancewarsa, wanda zunubansa suka hana shi, wanda kuma shi kansa ya nuna cewa bai cancance shi ba. Wani nassi ya ce: “Gama in an jima kadan, sa’an nan mai-mugunta ba shi; hakika da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kwa za ya kasance ba.” Wani kuma ya ce za “su zama sai ka che basu taba kasanchewa ba.” Zabura 37:10; Obadiah 16. Yafe da rashin daraja, za su nutse zuwa cikin bata, ba bege har abada. BJ 541.2
Hakanan ne za a kawo karshen zunubi da dukan hallaka da kaito da ya haifar, mai-zabura ya ce; “Ka hallakadda miyagu, ka shafe sunansu har abada abadin. Abokan gaba sun kare sarai, sun zama kango har abada.” Zabura 9:5,6. Yohanna cikin Ruya, sa’anda ya hangi gaba zuwa yanayi na har abdada ya ji wata wakar yabo ta dukan halitta, wadda ko kuskure daya babu. An ji kowace halitta sama da duniya tana ba Allah dukan daraja. Ruya 5:13. Lokacin babu batacen rai ko daya balle a yi ma sunan Allah sabo ma, yayin da batattu suke birgima cikin azaba mara karewa; ba wahallu a lahira da za su garwaye ihunsu da wakokin cetattu. BJ 542.1
Koyaswar cewa matattu sun san abin da ke faruwa ta kafu kan babban kuskuren nan ne cewa rai ba ya mutuwa, koysawar da ke sabani da koyaswoyin Littafin da bisira da kuma tausayi da juyayinmu na ‘yan Adam. Bisa ga koyaswar, fansassu a sama sun san duk abin da ke faruwa a duniya, kuma musamman ma da abokansu da suka bari a duniya. Amma ta yaya matattu za su yi farincikin sanin matsalolin masu rai, su ga zunuban da kaunatattunsu ke aikatawa, su kuma gan su suna jimre dukan bakinciki da yankan buri da azabar rayuwa? Ina yawan salamar sama da wadanda ke famar zagayar ‘yan-uwansu a duniya za su ji? Kuma dubi munin koyaswan nan cewa da zaran lumfashi ya bar jiki a kan jefa ran mara tuba cikin wutar jahannama nan da nan! Wane irin zurfin bakin ciki za a jefa wadanda ke ganin abokansu suna wucewa zuwa kabari ba shiri, su shiga madawamin kaito da zunubi! Da yawa sun shiga tabin hankali sabo da wannan tunanin. BJ 542.2
Mene ne littafin ke fadi game da ababan nan? Dauda Ya ce mutum bai san komi ba in ya mutu: “Lumfashinsa ya kan fita, ya kan koma turbayassa kuma; a chikin wannan rana shawarwarinsa sukan lalache.” Zabura 146:4. Solomon ya ba da shaida dayan: “Gama masu-rai sun san za su mutu, amma matattu basu san komi ba.” “Kamnarsu duk da kiyayyarsu, da kishinsu, yanzu sun kare; basu kwa da wani rabo har abada a chikin komi da a ke yi a chikin duniya.” “Babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, chikin kabari inda za ka.” Mai-wa’azi 9:5,6,10. BJ 542.3
Sa’anda aka amsa addu’ar Hezekiah ta wurin tsawaita ransa da shekara goma sha biyar, sarkin ya raira ma Allah wakar yabo sabo da girman jinkansa. Cikin wakar, ya ba da dalilin murnarsa; “Gama kabari ba shi da iko shi yi yabonka, mutuwa ba ta iya daukaka ba. Wadanda suna gangarwa chikin rami basu iya begen gaskiyarka ba. Mai-rai, mai-rai, shi ne za ya yi yabonka, kamar yadda ni ke yi yau.” Masana da yawa suna koyar da cewa matattun tsarkaka suna sama yanzu, cikin salama suna yabon Allah da harshe mara mutuwa, amma Hezekiah bai ga matattu da irin darajan nan ba. Mai-zabura ya yarda da maganarsa. Ya ce: “Gama chikin mutuwa babu tunawa da kai; a chikin lahira wa za ya yi maka godiya?” “Matattu ba su yabon Ubangiji ba, babu mai-yabonsa kuma chikin masu-gangarawa wurin shuru.” Zabura 6:5. 115:17. BJ 543.1
A ranar Pentecost Bitrus ya ce Dawuda “ya mutu, aka bizne shi, kabarinsa kwa a wurin mu yake har wayau.” “Gama Dawuda ba ya hau zuwa chikin sammai ba.” Ayukan 2:29,34. Kasancewar Dawuda cikin kabari har sai tashin matattu ya tabbatar da cewa matattu ba sa zuwa sama da zaran sun mutu. Ta wurin tashin matattu ne kawai, da kuma cewa Kristi ya tashi, Dawuda zai iya zama a hannun daman Allah. BJ 543.2
Bulus kuma ya ce: “Gama idan ba a ta da matattu, ba a ta da Kristi kuma: idan kwa ba a ta da Kristi ba, bangaskiyarku kuma banza che: har yanzu ku na chikin zunubanku. Har wadannan ma da sun yi barchi chikin Kristi sun lalache.” Korintiyawa I, 15:16-18. Idan an yi shekara dubu hudu matattun masu adalci suna zuwa sama kai tsaye da zaran sun mutu, ta yaya Bulus zai ce idan ba tashin matattu “wadannan ma da sun yi barchi chikin Kristi sun lalache”? Ba anfanin tashin matattu ke nan. BJ 543.3
Game da yanayin matattu, Tyndale ya ce: “Na furta a sarari, cewa ban gamsu cewa sun rigaya sun sami cikakkiyar daraja da Kristi ke ciki ba, ko wadda malaikun Allah ke ciki ba; ba kuma bangaskiya ta ke nan ba, domin da haka ne, da wa’azin tashin matattu ya zama aikin banza.” BJ 544.1
Hakika, begen albarka mara matuka da zaran an mutu ya kai ga rabuwa da koyaswar Littafin game da tashin matattu. Game da wannan Dr. Adam Clarke ya ce: “Kirista na da sun ba da muhimmanci ga koyaswar tashin matattu fiye da yanzu. Kaman yaya? Manzanin sun dinga nanata shi, suna ingiza masu bin Allah su yi kwazo, da biyayya da fara’a, tawurin koyaswan nan. Magadansu a wannan zamani kuma ba su cika ambaton shi ba. Manzani sun yi wa’azinsa, Kirista na da kuma sun gaskanta; haka mu ke wa’azinsa, haka kuma masu sauraronmu su ke gaskatawa. Ba wata koyaswar bishara da aka fi karfafawa kamar wannan; kuma ba koyaswar da aka fi yi mata kyaliya a zamanin nan kamar wannan! BJ 544.2
Wannan ya ci gaba har sai da gaskiyan nan na tashin matattu ta kusan shudewa Kirista kuma suka manta da ita. Don haka, wani shahararren mawallafi na addini cikin sharhinsa game da maganar Bulus cikin Tassalunikawa I, 4:13-18 ya ce: “Sabo da kowane dalili na ta’azantarwa, koyaswar rashin mutuwar masu-adalchi yana sauya mana duk wata koyaswa da ba a tabbatar ba game da zuwan Ubangijinmu na biyu. Da zaran mun mutu, Ubangiji ya zo mana. Abin da ya kamata mu yi tsaro mu jira ke nan. Matattu sun rigaya sun wuce zuwa daraja. Ba sa jiran haho kafin hukuncinsu da alabrkarsu.” BJ 544.3
Amma gaf da tafiyar a daga almajiransa, Yesu ba ya ce masu za su zo wurinsa jima kadan ba. “Gama zan tafi garin in shirya maku wuri” Ya che; “kadan na tafi na shirya maku wuri ni ma, sai in sake dawowa, in karbe ku wurin kaina.” Yohanna 14:2,3. Bulus kuma ya kara fada mana cewa; “Ubangiji da kansa za ya sabko daga sama, da kira mai-karfi, da muryar sarkin malaiku, da kafon Allah kuma; matattun da ke chikin Kristi za su fara tashi; sa’an nan mu da mu ke da rai, mun wanzu, tare da su za a fyauche mu zuwa chikin gizagizai, mu tarbi Ubangiji a sararin sama; hakanan za mu zamna har abada tare da Ubangiji.” Ya kara da cewa: “Domin wannan fa ku yi ma junanku ta’aziya da wadannan magana.” Tassalunikawa I, 4:16-18. Dubi yawan bambanci tsakanin kalmomin ta’aziyan nan da na wani mai-wa’azin nan da mun rigaya mun karanta can baya! Shi ya ta’azantar da abokan mamacin da tabbacin cewa, komi munin zunubin mamacin, da zaran ya ja lumfashinsa na karshe a nan, za a karbe shi cikin malaikun. Bulus yana jan hakulan ya-uwan ga zuwan Ubangiji nan gaba, sa’anda za a bude kabarbura, matattun da ke cikin Kristi kuma za a tashe su zuwa rai madawami. BJ 545.1
Kafin a shiga wuraren zaman tsarkaka, dole sai an bincika rayuwarsu, halayensu da ayukansu kuma za su bayana a gaban Allah domin bincike. Za a shar’anta kowa bisa ga ababan da aka rubuta cikin littattafan ne, a kuma ba su lada gwalgwadon ayukansu. Ba lokacin da an mutu a ke shari’an nan ba. Lura da maganar Bulus: “ya sanya rana, inda za ya yi ma duniya duka shari’a mai-adilchi ta wurin mutum wanda ya kadara; wannan fa ya ba da shaidassa ga mutane duka, yayinda ya tashe shi daga matattu.” Ayukan 17:31. A nan manzon ya bayana a sarari cewa an ayyana lokaci musamman domin sha’anta duniya. BJ 545.2
Yahuda ya yi zancen lokaci dayan. Yace: “Malaiku kuma wadanda ba su rike matsayi nasu ba, amma suka rabu da nasu wurin zama, ya tsare su chikin madawaman sarkoki a chikin dufu zuwa hukumchin babbar ranar.” Ya kuma maimaita kalmomin Enock cewa: “Ku duba ga Ubanguji ya zo da rundunan tsarkakansa, garin ya hukumta shari’a bisa dukan mutane.” Yohanna ya ce ya “ga matattu kuma, kanana da manya suna tsaye a gaban kursiyin, aka bude litattafai,… aka yi ma matattu shari’a kuma bisa ga abinda aka rubuta chikin litattafai.” Ruya 20:12. BJ 545.3
Amma idan matattu suna morar dadin sama yanzu ko kuma, suna birgima cikin wutar jahannama, wane anfani ne hukumci zai yi kuma? Koyaswoyin maganar Allah game da muhimman batutuwan nan a bayane suke, kuma ba sabani tsakaninsu, kowane mutum zai iya fahimtarsu. Amma wane mai-fadin gaskiya ne zai ga adalci ko hikima cikin ra’ayin da ake bazawa yanzu? Ko masu-adalchi, bayan an bincika shari’arsu, za su sami amincewan nan cewa; “Madalla kai bawan kirki mai-aminchi,… ka shiga chikin farinzuchiyar Ubangijinka,” alhali tuntuni ma suna kasancewa tare da shi, watakila ma har tsawon sararaki masu yawa? Ko za a kira miyagu daga wurin azaba domin su karbi hukumci daga wurin Mai-shari’an dukan duniya, cewa: “Ku rabu da ni ku la’antattu, zuwa chikin wuta ta har abada?” Matta 25:21,41. Wace irin ba’a ke nan! Wofinta hikimar Allah da adalcinsa kawai! BJ 546.1
Koyaswar rashin mutuwar mai-rai ta na cikin koyaswoyin karya da Rum ta aro daga kafirci ta kawo cikin addinin Kirista. Martin Luther ya danganta ta da tatsuniyoyi miyagu da aka hada cikin dokokin Rum. Game da furcin Solomon cikin Mai-wa’azi cewa matattu basu san komi ba, Luther ya ce: “wani wuri ke nan da ya nuna cewa matattu basu san komi ba. Ya ce ba alhaki, ba kimiya, ba sani, ba hikima a wurin. Solomon ya ce matattu suna barci, kuma ba sa jin komi sam. Gama matattu suna kwance a wurin, ba sa kirga kwanaki ko shekaru, amma idan aka tashe su, za su ga kamar barcin minti daya kadai suka yi.” BJ 546.2
Ba inda Littafin ya ce masu adalci su kan je wurin ladarsu, ko kuma miyagu sukan je wurin horonsu lokacin mutuwa. Ubanin iyaye da annabawa basu ba da wannan tabbacin ba, Kristi da manzanin basu ba da alamar hakan ba. Littafin yana koyar da cewa matattu ba sa zuwa sama nan da nan. Yana nuna cewa suna barci ne har sai tashin mattattu. Tassalunikawa I, 4:14; Ayuba 14:10-12. Ranar da “igiyar azurfa ta katse, tasar zinariya kuma ta fashe” (Mai-wa’azi 12:6), tunanin mutum yakan lalace. Wadanda ke gangarawa kabari shuru su ke. Ba su san komi kuma game da abin da ake yi a duniya ba. Ayuba 14:21. Hutu mai-albarka don gajiyayyun adilai! A gare su lokaci komi tsawo ko gajartarsa dan guntun lokaci ne. “Gama kafo za shi yi kara, matattu kuma za su tashi marasa-rubuwa,… Amma sa’anda wannan mai-rabuwa ya rigaya ya yafa rashin ruba, wannan mai-mutuwa kuma ya yafa rashin mutuwa, sa’an nan wannan batun da aka rubuta za ya tabbata cewa an hadiye mutuwa a nasarche.” Korintiyawa 15:52-54. BJ 546.3
Yayinda aka kirawo su daga barcinsu mai-nauyi, za su fara tunani daga inda su ka tsaya ne. Abu na karshe da suka sani shi ne abin da ya kashe su; tunani na karshe shi ne cewa suna faduwa zuwa kalkashin ikon kabari. Sa’an da su ka tashi daga kabari, za a maimaita tunanin su na farko mai tarin murna cikin ihun nan na nasara cewa: “Ya mutuwa, ina nasarakki, ya mutuwa ina karinki?” Aya 55. BJ 546.4