Yanzu masu Kin mulkin paparuma suna girmama tsarin Romawa fiye da shekarun baya. A kasashen da tsarin Katolika ba ya ci gaba, ‘yan paparuma kuma suna taka tsantsan domin su sami tasiri, akwai karuwan kyaliya game da koyaswoyin da suka bambanta ekklesiyoyin da suka canja da tsarin paparuma din; ana kara baza ra’ayin nan cewa ai ba mu bambanta sosai ba game da muhimman ababa kamar yadda aka zata, kuma cewa sassauci kadan daga gefen mu zai kawo mu ga karin fahimtar juna da Rum. Akwai lokacin da masu Kin ikon paparuma suka daukaka ‘yancin lamiri kwarai. Sun koya ma ‘ya’yan su su guji tsarin paparuma, suka kuma gaskata cewa neman jituwa da Rum rashin biyayya ga Allah ne. Amma yanzu abin ya bambangta sosai! BJ 559.1
Masu-goyon bayan ‘yan paparuma suna cewa wai an bata ma ekklesiyarsu suna, masu Kin ikon paparuma kuma suna kokarin amincewa da wannan maganar. Da yawa suna koyar da cewa ba daidai ba ne a zargi ekklesiya ta yau da haramtattun halayya da muguntan da ta aikata lokacin mulkinta a zamanin jahiliya da duhu. Sun ba da hujja cewa zaluncin da ta yi, sakamakon jahilcin zamanin ne, suna kuma cewa tasirin wayewan zamani ya sake tunaninsu. BJ 559.2
Mutanen nan sun manta da’awar cewa wannan mulkin ta yi shekara dari takwas tana cewa ita ba ta kuskure? Maimakon dena wannan kirarinma, an karfafa shi ne a cikin karni na sha tara da himmar da ta fi ta da. Da shi ke Rum ta na cewa wai “ekklesiya ba ta taba yin kuskure ba, kuma ba za ta taba yin kuskure ba, bisa ga Littafin,” ta yaya za ta yi musun kaidodin da ta yi anfani da su a sarraki da suka gabata? BJ 560.1
Ekklesiyar paparuma ba za ta taba rabuwa da ikirarin ta na cewa ba ta kuskure ba. Tana nacewa cewa duk abin da ta yi na tsananta ma wadanda su ke kin dokin ta daidai ne, kuma ashe ba za ta maimaita ayukan nan ba idan ta sami zarafi? Bari gwamnatocin yanzu su janye hali da suka yi, a kuma mayar da Rum ga ikon ta na da, nan da nan za a farfado da zaluncin ta. BJ 560.2
Wani sannanen mawallafi ya yi Magana hakanan game da halin tsarin paparuma game da ‘yancin lamiri, da kuma hadaruka da ke barazana ga Amerika game da nasarar tsarin mulkinta. Ya ce: BJ 560.3
“Akwai wadanda ke so su mai da tsoron ekklesiyar Roman Katolika a Amerika kamar tsatsauran ra’ayi ne ko kuma yarantaka. Ba sa ganin komi a yanayin Roman Katolika da hakinta da ke sabani da tsare tsarenmu, kuma ba sa ganin wani abin tsoro game da girman da ta ke yi. bari mu gwada wadansu muhimman kaidodin gwamanatin mu da na ekklesiyar Katolika. BJ 560.4
“Kundin tsarin Amerika yana tabbatar da ‘yancin lamiri. Ba abin da ya fi wannan tamani muhimmanci. Paparuma Pius IX cikin wasikarsa ta 15 ga Agusta 1854 ya ce: ‘Munanan koyaswoyi ko suruce-surucen da ke goyon bayan ‘yancin lamiri kuskure ne cike da annoba, kwaro ne da ya kamata kowace kasa ta ji tsoronsa.’ A wasikarsa ta 8 ga Disamba, 1864 kuma paparuman nan dayan ya tsine ma wadanda ke goyon bayan ‘yancin lamiri da na addini,’ da kuma ‘dukan wadanda ke cewa bai kamata ekklesiya ta yi anfani da karfi ba.’ BJ 560.5
“Taushin muryar Rum a Amerika ba nuna cewa da ta sake hali ba ne. Tana saukin kai inda ba ta da yadda za ta yi ne. In ji Bishop Oconnor: ‘Ana jimre ‘yancin addini kawai har sai lokacin da za a iya aiwatar da akasinsa ba tare da wani hatsari ga ekklesiyar Katolika ba.’… Babban bishop na St. Louis ya taba cewa: ‘Ridda da rashin ba da gaskiya laifuka ne; kuma a kasashen Kirista, kamar a Italiya da Spain misali, inda dukan mutanen ‘yan Katolika ne, da kuma inda addinin Katolika muhimmin fanni ne na dokar kasar, akan hori laifukan nan kamar sauran lafiya’,… BJ 561.1
“Kowane cardinal da archbishop, da bishop a Ekklesiyar Katolika yakan dauki rantsuwar biyayya ga paparuma, inda akwai kalmomin nan: “Masu ridda, da masu kawo rabuwa, da ‘yan tawaye ga Ubangijin namu (watau paparuma), ko kuma magadansa, ni zan yi iyakar kokari na in zalunce su in yi sabani da su.” BJ 561.2
Gaskiya ce akwai Kiristan gaskiya a cikin ekklesiyar Katolika. Dubbai cikin wannan ekklesiyar suna bauta ma Allah iyakar hasken da suka samu ne. Ba a barinsu su karanta maganarsa, sabo da haka kuwa ba su san gaskiyan ba. Basu taba ganin bambaci tsakanin ibada mai-rai daga zuciya da bukukuwa da hidimomi kawai. Allah yana kallon irinsu da idon tauisayi, ko da shike suna da ilimi cikin addini mai-rudi da ba ya gamsarwa. Za ya sa tsirkiyoyin haske su ratsa duhun da ya kewayesu. Za ya bayana maishe gaskiya da ke cikin Yesu, kuma da yawa za su zabi kasancewa tare da mutanensa. BJ 561.3
Amma tsarin Romawa bai kara jituwa da Kristi yanzu fiye da duk wani lokaci cikin tarihinsa ba. Ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma suna cikin bakin duhu sosai, ba don haka ba da sun gane alamun zamanun. Ekklesiyar Rum ta yi nisa cikin shirye shiryenta da matakan aikin ta. Tana anfani da kowace dabara don fadada tasirinta, ta kuma kara ikonta don shiryawa saboda mumunan yaki da fada mai-zafi domin mallakar duniya, a sake dawowa da zalunci, a kuma warware duk abinda Kin ikon paparuma ya yi. Katolika tana ci gaba ta kowace fuska. Duni karuwar yawan majami’unta a kasashe masu Kin ikon paparuma. Dubi farinjinin kolejojinta da makarantun addininta a Amerika, inda masu Kin ikon paparuma ke zuwa don samun ilimi. Dubi yaduwar tsafi a Ingila da yawan komawa ekklesiyar Katolika da a ke yi. Ya kamata ababan nan su ta da taraddadin dukan masu kishin kaidodin bishara. BJ 561.4
Masu Kin ikon paparuma sun sa hannu cikin tsarin paparuma, sun kuma amince da wadansu ababa, suka yi sassauci kan wadansu al’amura, har ‘yan paparuman kansu suna mamaki, suka kuma kasa gane dalili. Mutane suna rufe idanunsu daga ainihin halin ekklesiyar Rum da hatsarin da za a iya fuskanta daga samun fifikonta. Ya kamata a falkar da mutane domin su yaki ci gaban wannan babban magabcin ‘yancin addini da sauran ‘yanci. BJ 562.1
Masu Kin ikon paparuma da yawa suna tsammanin cewa addinin Katolika ba shi da ban-sha’awa, kuma cewa sujadarta mara armashi ce, kuma bukukuwa marasa ma’ana. Wannan kuskure su ke yi. Ko da shike ekklesiyar Rum ta kafu kan rudi ne, ba wani kauyanci ne mara fasali ba. Hidimar addinin ekklesiyar Rum hidima ce mai-ban sha’awa. Adonta da hidimominta su kan ja hankulan mutanen su kuma rufe muryar hankali da lamiri. Ido yakan yi sha’awar kyawawan majami’u da jerin gwano masu-ban sha’awa da bagadin zinariya, da dakunan ibada masu ado, da kyawawan hotuna, da sassaka masu tamani; duka suna jan hankulan masu son abu mai-kayu. Kunne ma yakan ji abu mai-dadi. Muzikan na musamman ne, da sautin molon, da amon muryoyi da yawa sukan cika majami’un ekklesiyar, kuma baza su kasa cika zuciyar mutum da sha’awa da bangirma ba. BJ 562.2
Wannan kyau da shagali da hidima masu ban sha’awa da ido ke gani alama ce ta lalacewa daga ciki. Addinin Kiristi baya bukatar irin ban sha’awan nan. Cikin hasken da ke haskakawa daga giciyen ainihin Kiristanci yana bayanuwa cikin tsabta da ban-sha’awa da babu ado daga waje da zai kamanta ainihin tamaninsa. Kyaun tsarki ne, ruhun tawali’u da natsuwa, su ke da tamani ga Allah. BJ 562.3
Walkiyar salo ba lallai alamar kyakyawan tunani ba ne. Sau da yawa akan iske iya zane da yawan wayewa cikin ‘yan duniya masu mumunan sha’awa. Shaitan ya cika anfani da su don su mutane su manta wajibai na rai, su manta rayuwa ta rashin mutuwa da ke zuwa nan gaba, su juya da mai-taimakonsu mara-iyaka, su kuma yi rayuwa domin wannan duniyan kadai. BJ 563.1
Addinin abin da ake gani kawai yana da ban sha’awa ga zuciyar da ba ta tuba ba. Shaguli da al’adar sujadar Katolika yana jan-hankali sosai ta yadda yana rudin mutane da yawa, har su ga kamar ekklesiyar Rum ce kofar sama. Ba wanda ke da kariya daga tasirinta sai wadanda suka dasa kafafunsu da karfi bisa tushen gaskiya, wadanda ruhun Allah ke sabonta zukatansu kuma. Dubbai da ba su da ainihin sanin Allah za su karbi kamanin ibada ba tare da ikonta ba. Irin addinin da yawancin mutane ke so ke nan. BJ 563.2
Da’awar ekklesiya cewa tana da ‘yancin gafara ta kan sa Romawa su ji kamar suna da ‘yanci su yi zunubi, kuma hidimar furta laifi. Kafin ta yi gafarar ma tana ba da daman yin zunubi. Wanda ya durkusa a gaban mutum faddade kamarsa, ya kuma bayana masa asiran tunanin zuciyarsa, yana nakasa mutumtakansa da kuma kowane tunanin zuciyarsa ne. Ta wurin bayana zunuban ransa ga priest, wanda mai-kuskure ne, mai-zunubi, mai-mutuwa, wanda sau da yawa barasa da anishuwa sun rigaya sun lalata shi, matsayin halin mai-tuban yakan ragu, har ma ya kazamtu tawurin wannan. Tunaninsa game da Allah yakan ragu zuwa kamanin fadadden mutum, gama priest din yana matsayin wakilin Allah ne. Furta laifin mutum ga mutum din nan ne mabulbular boye daga inda yawancin mugunta ne da ke kazamtar da duniya, tana kuma shirya ta don hallaka ke bulbulowa. Duk da haka ga mai-son jin dadi, ya fi masa dadi ya furta zunubinsa ga mai-mutuwa kamarsa da ya bude ransa ga Allah. Yanayin mutuntaka ya fi jin dadin shan wahala don samun gafara maimako rabuwa da zunubi; wahal da jiki da toka da kayayuwa da sarkoki ya fi giciyewar sha’awoyin jiki sauki. Kayan da zuciyar mutumtaka ke shirye ya dauka maimakon durkusa ma karkiyar Kristi, yana da nauyi. BJ 563.3
Akwai kamani sosai tsakanin ekklesiyar Rum da ta Yahudawa ta lokacin zuwan Kristi na fari. Yayin da Yahudawa suka dinga tattake kowace kaidar dokar Allah a boye, sun dinga kiyaye umurninta a bayane, suna jibga mata sharudda da al’adu da suka sa biyayya ta zama da zafi da wahala kuma. Yadda Yahudawa su ka ce suna girmama dokar haka ne Romawan ke cewa suna girmama giciyen. Suna daukaka alamar wahalokin Kristi alhali cikin rayuwarsu suna kin Kristi din. BJ 564.1
‘Yan paparuma suna manna giciye a majami’unsu da bagadinsu da rigunansu. Ko ina ana ganin alamar giciyen. Ko ina ana girmama ta a daukaka ta. Amma ana bizne koyaswoyin Kristi kalkashin tulin al’adu marasa ma’ana da fassaran karya da yawan bukatu. Kalmomin mai-ceton game da Yahudawa sun fi cancantar shugabanin ekklesiyar Roman Katolika ma, cewa: “I, su kan damra kaya masu nauyi, masu-wuyan daukawa kuma, su dibiya ma mutane a kafadu; amma su da kansu basu yarda su ko motsa su da yatsansu ba.” Matta 23:4. Ana rike masu bi cikin fargaba kullum suna tsoron Allahn da suka yi masa laifi, alhali da yawa cikin shugabannin ekklesiya suna rayuwa cikin jin dadi da sha’awa. BJ 564.2
Sujada ga siffofi, rokon tsarkaka da daukaka paparuma, dabarun Shaitan ne don jawo hankulan mutane daga Allah da Dansa. Domin tabbatar da hallakarsu, yana, kokarin juya hankulansu daga wanda ta wurinsa ne kadai zasu iya samun ceto. Zai mai da hankulansu ga duk wani abin da za a iya sauyawa a madadin shi wanda ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kwa in ba ku hutawa.” Matta 11:28. BJ 564.3
Kokarin Shaitan kullum shi ne karyata halin Allah, da yanayin zunubi da ainihin batutuwan da babban jayayyan nan, ta kunsa. Karyarsa tana rage nauyin bukatar kiyaye dokar Allah ta ba mutane damar yin zunubi. A lokaci dayan, yana sa su sha’awar tunani mara kyau game da Allah, ta yadda suna daukan shi da tsoro da kiyayya maimakon kauna. Ana danganta Allah da muguntar da ke halin Shaitan ne, sai a kunsa shi cikin tsarin addini, a bayana shi tawurin salon sujada. Ta haka ana makantar da zukatan mutane, Shaitan kuma yakan rike su su zama wakilansa don yin yaki da Allah. Tawurin mumunan fahimtar halin Allah, an sa al’ummai na kafirai suka gaskata cewa wajibi ne a ba da hadayar mutane domin samun karbuwa ga Allah, kuma an aikata munanan zalunci kalkashin salo iri iri na bautar gumaka. BJ 565.1
Ekklesiyar Roman Katolika da ta hada ayukan kafirci da Kiristanci, kuma kamar kafirin, ta na karyata halin Allah, ta shiga ayukan zalunci masu ban-kyama. A zamanin fifikon Rum akwai dabarun zalunci da suka tilasta amincewa da koyaswoyinta. Akwai itacen nan mai-tsini inda ake kashe wadanda suka ki yarda da ikonta. Akwai kashe kashe da ba za a iya sanin yawan su ba, sai sa’ar hukumci ta bayana su. Shugabannin ekklesiya kalkashin mai-gidansu Shaitan sun rika nazarin yadda za su kirkiro hanyoyin yin zalunci mafi girma ba tare da dauke ran mutunin ba. A lokata da yawa a kan dinga maimaita konawar, har iyakar inda mutumin zai iya jimrewa, har inda mai-faman yakan gwammaci mutuwa. BJ 565.2
Abinda ya faru da masu jayayya da Rum ke nan. Ga membobin, takan ba da horo na bulala, ko yunwa mai tsanani, ko kuma wahalrwa ta jiki kowace iri. Don samun alherin Allah, masu tuba sukan ketare dokokin Allah tawurin ketare dokokin halitta. Aka koya masu su raba dangantakan da Allah ya hada domin ya kyautata bakuncin mutum a duniya. Makabarta tana cike da miliyoyin mutane da suka kashe rayuwarsu a banza wai suna kokarin danne soyayyar jikunansu, su kawar da kowane tunanin tausayin sauran halittatu, cewa Allah ba ya so. BJ 565.3
Idan muna so mu fahimci zaluncin Shaitan, wanda ya yi daruruwan shekaru yana nunawa, ba cikin wadanda basu taba jin labarin Allah ba, amma a tsakiyar Kiristanci, kuma ko ina, sai mu dubi tarihin Romawa kawai. Tawurin tsarin nan na rudi sarkin muguntan yana cim ma manufarsa ta kawo reni ga Allah da bakinciki ga mutum. Kuma yayin da mu ke ganin yadda yake badda kamaninsa yana kuma cika aikinsa ta wurin shugabannin ekklesiya, ya kamata mu gane dalilin da ya sa yana kiyayya da Littafin. Idan aka karanta Littafin nan, jinkan Allah da kaunarsa za su bayana, za a ga cewa bai aza ma mutane wadannan manyan nauyin ba. Abin da yake bida kadai shi ne zuciyar tuba da ruhun tuba mai-tawali’u. BJ 566.1
Kristi bai ba da kwatanci cikin rayuwarsa na cewa mutane su kulle kansu cikin gidajen zuhudu domin a cancanci sama ba. Bai taba koyar da cewa dole a danne kauna da tausayi ba. Zuciyar Mai-ceton ta cika da kauna. BJ 566.2
Idan mutum yana kara kusantuwa da samun cikakken halin kirki, tunaninsa zai kara kaifi, kuma zai kara fahimtar zunubi, kuma zai kara tausaya ma wahallalu. Paparuma yana da’awar cewa shi ne wakilin Kristi, amma yaya halinsa yake idan aka gwada shi da na Mai-ceton? Ko an san Kristi da jefa mutane cikin kurkuku ko wurin kisa wai don basu yi masa biyayya a matsayin Sarkin sama ba? Ko an taba jin muryarsa yana hukumcin kisa ga wadanda basu karbe shi ba? Saboda mutanen wani kauyen Samariyawa su ka nuna masa reni, manzo Yohanna ya fusata sosai, har ya tambaya: “Ubangiji kana so mu umurchi wuta ta sabko daga sama ta chinye su?” Yesu Ya dubi almajiransa da tausayi, ya tsauta ma ruhun fushinsu Ya ce, “Dan mutum ba ya zo domin hallaka rayukan mutane ba, amma domin ya cece su ne.” Luka 9:54,56. Dubi bambancin ruhun da Kristi ya nuna da ruhun mai-cewa wai shi ne wakilinsa. BJ 566.3
Yanzu ekklesiyar Rum tana nuna ma duniya cewa tana da adalci, tana rufe zaluncin ta da neman gafara. Ta suturta kanta da riguna irin na Kristi, amma ba ta sake ba. Kowace kaidar tsarin paparuma ta sararaki na da, tana nan yanzu. Har yanzu ana rike da koyaswoyin da aka kago a zamanin jahiliya. Kada kowa ya rudi kansa. Tsarin paparuma da masu Kin ikon papruma ke shirye su girmama yanzu shi dayan ne wanda ya yi mulkin duniya a kwanakin canjin, lokacin da mutanen Allah suka tashi tsaye, suka sa kansu cikin hadari suka fallasa zunubin ta. BJ 567.1
Tana da griman kai da zaton nan da suka aza ta bisa sarakuna da ‘ya’yan sarki ta kuma mallaka ma kanta ababa da Allah kadai Ya isa ya mallaka. Ruhunta na kama-karya da zalunci yana nan daidai da na lokacin da ta murkushe ‘yancin ‘yan Adam ta kuma kashe tsarkakan madaukaki. BJ 567.2
Tsarin paparuma dai abin da annabci ya ce zai kasance ne, watau riddar kwanakin karshe. Tassalunikawa II, 2:3,4. Takan dauki yanayin da zai fi biya mata bukata ne, amma kalkashin canje-canjen kamaninsa kamar hawainiya tana boye dafin macijin nan mara sakewa. “Bai kamata a amince da masu ridda ba, ko ma wadanda a ke tsammanin sun yi ridda,” in ji ta. Ko ya kamata mulkin nan da ya yi shekaru dubu yana zubar da jinin tsarkaka ya karbu a matsayin wani sashe na ekklesiyar Kristi? BJ 567.3
Ba kawai ba ne a kasashen da suka ki ikon paparuma ana cewa wai yanzu Katolika ba ta bambanta sosai da ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma ba kamar da. An sami canji kam, amma canjin ba na tsarin paparuman ba ne. Tsarin Katolika, hakika, ya yi kama da yawancin Kin ikon paparuma na zamanin nan, da shike Kin ikon paparuma ya lalace sosai daga na zamanin ‘yan Canjin. BJ 567.4
Yayin da ekklesiyoyin masu Kin ikon paparuma ke neman goyon bayan duniya, kaunar karya ta makantar da idanunsu. Suna gani kamar daidai ne su gaskata cewa kowace mugunta nagarta ce, kuma ba shakka a karshe za su gaskanta cewa kowace nagarta mugunta ce, maimakon kare bangaskiyar da aka taba ba atsarkaka, yanzu suna tuba ma Rum saboda ra’ayinsu mara-kyau game da ita, suna rokon gafara sabo da matsanancin ra’ayinsu. BJ 567.5
Da yawa har ma da masu goyon bayan Rum suna ganin karamin hatsari daga ikonta da tasirinta. Da yawa suna cewa duhun da ya mamaye tunani da halin kirki a zamanin jahaliya ya taimaka wajen baza koyaswoyinta da camfe canfenta da danniyarta, kuma cewa Karin tunani na wannan zamani, da yaduwan sani da karuwar ‘yanci a sha’anin addini suna hana tasowar rashin hakuri da zalunci. Tunanin ma cewa wannan abu zai kasance an mai da shi abin ba’a. Gaskiya ne, cewa haske mai-yawa ta fannin addini da halin kirki da tunani. A cikin budadiyar maganar Allah haske daga sama yana haskaka duniya. Amma a tuna cewa yawan hasken da aka bayar, yawan duhun wadanda suka lalata shi suka kuma ki shi. BJ 568.1
Nazarin Littafin tare da addu’a zai nuna ma masu-kin ikon Rum ainihin halin tsarin paparuma ya kuma sa su su ki shi, su kuma rabu da shi, amma da yawa suna gani kamar suna da wayo sosai ta yadda basa ji kamar suna bukatar bidar Allah domin a bishe su zuwa gaskiya. Ko da shike suna fahariya da wayewarsu, sun jahilci Littafni da ikon Allah ma. Dole su sami wata hanyar lallabar lamirinsu, sabo da haka suna bidar abin da ke da mafi-kankantar ruhaniya, abin da ke kaskantarwa kuma. Abin da suke nema shi ne hanyar mance Allah da za a ga kamar hanyar tunawa da shi ne. Tsarin paparuma tana shirye ta gamsar da dukan wadannan. Tana shirye don mutane kashi biyu da suka mamaye kusan dukan duniya, watau wadanda za a cece su bisa ga isar su, da wadanda za a cece su cikin zunubansu. Asirin ikonsu ke nan. BJ 568.2
An rigaya an nuna cewa ranar duhun tunani yakan taimaka ma nasarar paparuma. Za a kuma nuna cewa ranar babban hasken tunani ma zai taimaka ma nasarar paparuman. A sararakin da suka gabata, lokacin da mutane ba su da maganar Allah, kuma ba su san gaskiya ba, an hyi masu rufa-ido, aka kuma kama dubbai da ba su ga tarkon da aka dana masu ba. A zamanin nan akwai da yawa da idanunsu sun rufu da walkiyar zato da kimiyyar karya, har ba sa iya ganin tarkon, suna kuwa shiga cikinsa sai ka ce an rufa masu ido. Allah ya shirya cewa mutum ya rike tunaninsa kamar kyauta daga wurin mahalicinsa da zai yi anfani da shi cikin hidimar gaskiya ta adalci, amma sa’anda girman kai da buri suka shirya zuciyan mutane kuma suka daukaka tunaninsu fiye da maganar Allah, a lokacin nan tunani zai yi ta’adi fiye da wanda jahilci zai yi. Ta hakanan kimiyar karya ta yau, wadda ke rage bangaskiya ga Littafin, zai yi nasara wajen shirya hanyar karban ikon paparuma da ayukansa kamar yadda hana sani ya yi nasara wajen bude mata hanyar biyan bukatunta a zamanin jahiliya. BJ 568.3
Cikin al’amuran da ke gudana yanzu a Amerika don samo ma fannonin ekklesiya da ayukan ta goyon bayan kasa, masu Kin ikon paparuma suna bin matakan ‘yan paparuma ne. Har ma suna bude kofa ne ma ‘yan paparuma su sake samun fifikon da suka rasa a tsohuwar duniya. Abin da ke kara ma wannan yankuri muhimmanci kuma shi ne cewa babban burin da ake da shi shi ne tilasta kiyayewar Lahadi, al’ada da Rum ta fara, tana kuma cewa ita ce shaidar ikonta. Ruhun tsarin paparuma ne ruhun daidaituwa da al’adun duniya. Daukaka al’adun mutane fiye da dokokin Allah shi ne yake mamaye ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma, yana kuma kai su ga daukaka Lahadi wanda ‘yan paparuma suka yi kafin su. BJ 569.1
Idan mai-karatu zai gane dabarun da za a yi anfani da su cikin hayayyan da ke zuwa, zai bukaci tunawa ne kawai da dabarun da Rum ta yi anfani da su a sararakin da sun gabata. Idan mai-karatun yana so ya san yadda ‘yan paparuma da hadin kan masu Kin mulkin paparuma za su yi da masu-kin kayaswoyinta, ya dubi irin ruhun da Rum ta nuna game da Assabbat da masu kiyaye shi. BJ 569.2
Dokokin sarakuna, da majalisu na bai daya, da haikalin ekklesiya da ake tabbatarwa tawurin ikon kasa, matakai ne ta inda bukin kafirai ya sami matsayin girmamawa cikin Kiristanci. Matakin farko da ya tabbatar da kiyaye Lahadi shi ne dokar da Constantine ya kafa a AD 321. Dokan nan ta bukaci ‘yan alkarya su huta a “rana mai-tsarki ta rana,” amma ya ba kauyawa dama su ci gaba da ayukan su na noma. Ko da shike dokar kafirci ce babban sarkin ya tabbatar da ita bayan ya karbi Kiristanci a suna kawai. BJ 570.1
Da shike umurnin sarauta bai kai ikon Allahntaka ba, Eusebius, wani bishop mai-neman goyon bayan ‘ya’yan sarauta, wanda kuma aboki na musamman ne mai-fadanci kuma ga Constantine, ya dinga baza wani ikirari cewa Yesu ya mayar da Assabbat zuwa Lahadi. Ba aya ko shaida ko daya daga Littafin da ya tabbatar da sabuwar koyaswar. Eusebius kansa ya amince cewa karya ce, ya kuma nuna ainihin masu kirkiro canjin. Ya ce: “Dukan ababan da suka wajibta a yi ran Assabbat, mu mun mayar da su ranar Ubangiji.” Amma zancen Lahadin nan, ko da shi ke ba shi da tushe, ya karfafa mutane tattake Assabar na Ubangiji. Dukan masu son daukakar duniya sun amince da Lahadin. BJ 570.2
Sa’anda tsarin paparuma ya kafu sosai, an ci gaba da aikin daukaka Lahadi. Da farko, mutanen sukan shiga aikin gona idan basu je masujada ba, aka kuma ci gaba da kiyaye rana ta bakwai a matsayinta na Assabbat. Amma a hankali an yi canji. Aka hana masu aikin ekklesiya yin hukumci game da kowace jayayyar da ba ta addini ba ce a ranan Lahadi. Ba da jimawa ba, aka umurci dukan mutane, komi matsayinsu, su dena aiki in ba haka ba su biya tara in ba barori bane, ko kuma su sha bulala in barori ne. Daga baya aka umurta cewa a hori masu-arziki ta wurin kwace rabin gidajensu. A karshe kuma idan duk da haka basu dena ba, sai a mai da su bayi. Talakawa kuma sai a kore su kwatakwata daga kasar. BJ 570.3
An kuma yi anfani da al’ajibai. “Daya daga cikin al’ajiban shi ne cewa wai wani manomi da ya shirya nome gonarsa ran Lahadi ya share garmarsa da wani karfe, sai karfen ya manne cikin hannunsa, ya kuma yi shekaru biyu yana tafiya da karfen, yana fama da zafi da kunya masu yawa kuwa.” BJ 571.1
Daga baya paparuma ya ba da umurni cewa kowane priest na masujada ya gargadi masu-ketare Lahadi ya kuma koya masu su rika zuwa masujaida su yi addu’o’insu, kada su jawo ma kansu da makwabatansu mumunan bala’i. BJ 571.2
Wata majalisar ekklesiya ta gabatar da zancen da har masu Kin ikon paparum ma sun yi anfani da shi, cewa wai da shike walkiya ta kashe wadansu yayin da su ke aiki ran Lahadi, wannan ya nuna cewa Lahadi din ne Assabbat. Priestocin suka ce: “Rashin jin dadin Allah game da yadda basu kula ranan nan ba a bayane yake.” Sai aka roka cewa priestoci da pastoci da sarakuna da ‘ya’yan sarakuna, da dukan amintattu su “yi anfani da iyakar kokarinsu domin a dawo da darajar ranar, kuma, don anfanin Kiristanci, a kara himmar kiyaye ta saboda lokaci mai-zuwa. BJ 571.3
Da shike umurnin majalisu sun kasa, aka bukaci hukumomin kasa su ba da doka da za ta razana zukatan mutane ta kuma tilasta su su dena aiki ran Lahadi. A wani taron Synod da aka yi a Rum aka jaddada dukan kudurorin da aka taba dauka, da karin karfi da bangirma. Aka kuma hada su cikin dokar ekklesiya, hukumomin kasa kuma suka zartas da su, kusan ko ina a cikin Kirista. BJ 571.4
Har da haka dai rashin nassin da ya goyi bayan kiyaye Lahadi ya ci gaba yana jawo rudewa, sosai. Mutane suka yi shakkar ikon da mallamansu ke da shi na kawar da umurnin Yahweh cewa “Rana ta bakwai Assabbat ne ga Ubangiji Allahnka,” domin su girmama ranar rana. Don cika gibin nan na rashin shaidar Littafin, ya zama dole a nemi wadansu dalilai. Wani mai himmar goyon bayan Lahadi, wanda kusan karshen karni na sha biyu ya ziyarci ekklesiyoyin Ingila, ya gamu da jayayya daga amintattun shaidun gaskiya; kuma kokarin sa ya kasa haifar da komi ta yadda ya bar kasar na wani lokaci, ya nemi wadansu hanyoyin tabbatar da koyaswoyinsa kuma. Sa’anda ya dawo, an cika gibin, daga nan kokarinsa ya yi nasara. Ya zo da wata takarda da ya ce daga Allah kansa ne, wadda ta kunshi umurnin da a ke bukata don kiyaye Lahadi, da barazana masu-ban tsoro don razana marasa biyayya. Wannan takardar, mara daraja, aka ce ta fado daga sama ne, kuma wai an same ta a Urushalima ne, a kan bagadin Saint Simon a Golgotha. Amma, a gaskiya, fadar paparuma a Rum ce inda ta fito. Tsarin paparuma cikin dukan sararaki takan amince da yaudara don kawo ci gaban ikon ekklesiya. BJ 572.1
Takardar ta hana aiki daga sa’a ta tara, watau karfe uku, ran Asabar da rana, har zuwa fitar rana ran Litinin; aka kuma ce al’ajibai da yawa sun tabbatar da ikonta. Aka ba da labari cewa mutanen da suka yi aiki har sun zarce lokacin da aka yarda masu an hore su da ciwon shan inna. Wani mai nika da ya yi kokarin nika masaransa, maimakon garin masara ya ga jini ne ke kwararowa, injin kuma ya tsaya ko da shike ruwan da ke juya injin ya ci gaba da zubowa. Wata mace da ta sa kullun burodi a tanderun wutan gasa burodin, ta iske shi danye lokacin da ta fitar da shi, ko da shike tanderun yana da zafi sosai. Wata da ta shirya kullum burodin domin gasawa a sa’a ta tara, amma ta ajiye shi sai ran Litinin, washegari ta iske cewa an mai da shi dunkule-dunkule, kuma ikon Allah ya gasa su. Wani mutum da ya gasa burodi bayan sa’a ta tara ranan Asabar, washegari ya iske cewa jini yana fita daga cikinsa. Ta wurin irin kulle-kullen nan ne masu goyon bayan Lahadi su ka yi kokarin tabbatar da tsarkinsa. BJ 572.2
A Scotland, kamar Ingila, an sami karin goyon bayan Lahadi ta wurin hada shi da wani sashi na Assabbat. Amma lokacin da aka ce a kiyaye da tsarki ya bambanta. Wata doka daga sarkin Scotland ta ce “Asabar daga sha biyu na rana ya kamata a kiyaye shi da tsarki,” kuma wai daga wannan lokacin har Litinin da safe kada wani ya yi wani sha’ani da ba na addini ba. BJ 573.1
Amma duk da kokarin tabbatar da tsarkin Assabbat, ‘yan paparuma kan su sun amince a fili da sahihancin Assabbat din. Cikin karni na sha shida, wata majalisar ‘yan paparuma a sarari ta ce; “Bari dukan Kirista su tuna cewa Allah ya tsarkake rana ta bakwai, kuma ba Yahudawa kadai ba, dukan masu-cewa suna sujada ga Allahsun karbe ta suna kuma kiyaye ta, ko da shi ke mu Kirista mun sake Assabbat din nasu zuwa Rana ta Ubangiji.” Wadanda suka taba dokar Allah b a u kasa sanin yanayin abin da su ke yi a lokacin ba. Da gangan suka aza kansu bisa Allah. BJ 573.2
An ba da kyakyawan misalin manufar Rum game da wadanda basu yarda da ita ba a zalunci mai-tsawo da zub da jini da aka yi ma Walensiyawa, wadanda cikin su akwai masu kiyaye Assabbat. Wadansu ma sun wahala hakanan sabo da amincinsu ga doka ta hudu ne. Tarihin ekklesiyoyin Habasha da Abyssiniya abin tunawa ne musamman. A tsakiyar bakincikin Sarrarakin Duhun nan, duniya ta manta da Kiristan Afirka ta Tsakiya, kuma sun yi daruruwan shekaru suna morar ‘yancin addininsu. Amma a karshe, Rum ta sami labarin kasancewarsu, nan da nan kuwa aka rudi babban sarkin Abyssiniya ya amince cewa paparuma ne wakilin Kristi. Ya amince da wadansu ababan kuma. Aka ba da dokar hana kiyaye Assabbat, wanda bai yi biyayya ba kuwa ya sha horo mai-tsanani. Amma zaluncin paparuma nan da nan ya yi tsamanin da ya sa mutanen Abyssiniya suka yi himmar kubutar da kansu daga gare shi. Bayan mumunan yaki aka kori Romawan daga garuruwan Abyssiniya, aka kuma mayar da bangaskiya ta da. Ekklesiyoyin sun yi farinciki da ‘yancin su kuma basu taba manta darasin da suka koya game da rudi da matsanancin ra’ayi da ikon danniya na Rum ba. Suka gamsu da kasancewa su kadai, sauran Kirista basu san da su ba. BJ 573.3
Ekklesiyoyin Afirka sun rike Assabbat kamar yadda ekklesiyar paparuma ta rike shi kafin ta cika riddar ta. Yayin da suka kiyaye rana ta bakwai don biyayya ga dokar Allah, suka bar yin aiki ranan Lahadi bisa ga al’adar ekklesiya. Sa’an da ta sami mafificin iko, Rum ta tattake Assabbat na Allah domin ta daukaka na ta, amma ekklesiyoin Afirka da ke boye har kusan shekaru dubu basu shiga wannan riddar ba. Sa’an da aka jawo su kalkashin ikon Rum, an tilasta su su kawar da Assabbat na gaskiya su daukaka na karyan, amma da zaran sun dawo da yancin su sai suka koma biyayya ga doka ta hudu. BJ 574.1
Labarum nan suna bayana magabtakan Rum game da Assabbat na gaskiya da masu kiyaye shi, da hanyar da take anfani da ita don daukaka na ta assabbacin da ta kirkiro. Maganar Allah tana koyar da cewa za a maimaita al’amuran nan sa’anda yan Roman Katolika da masu Kin ikon paparuma za su hada kai don daukaka Lahadi. BJ 574.2
Annabcin Ruya 13 ya bayana cewa mulkin da bisa mai-kahoni irin na dan rago ke misaltawa zai sa duniya da dukan mazamna cikinta su yi sujada ga tsarin paparuma, wanda nassin ya misalta da damisa. Bisa mai kahoni biyu din zai kuma “che ma wadanda ke zamne a duniya, su yi gunki ga bisan.” Kuma bugu da kari, za ya umurci kowa “kanana da manya, mawadata da matalauta, yaya da bayi,’ su karbi shaidar bisan. Ruya 13:11-16. An rigaya an nuna cewa Amerika ce mulkin da bisa mai-kahoni irin na dan ragon ke misaltawa, kuma cewa za a cika annabcin nan ne lokacin da Amerika za ta tilasta kiyaye Lahadi, wanda Rum ke cewa amincewa ne da fifikon daukakanta. Amma ba Amerika ce kadai za ta yi biyayyan nan ga Rum ba. Tasirin Rum cikin kasashen da suka taba amincewa da mulkin ta har yanzu ba a rushe shi ba. Annabci kuma ya ce za a mayar mata da ikonta. “Na ga dayan kawunansa sai ka ce an yi masa bugun ajali; sai kuma bugunsa na ajali ya warke, dukan duniya fa tana mamaki da bisan.” Ruya 13:3. Bugun ajalin shi ne faduwar paparuwa a 1798. Bayan wannan, in ji annabin, “bugunsa na ajali ya warke.” Dukan duniya fa tana mamaki da bisan.” Bulus ya bayana a fili cewa “mutumin zunubin” zai ci gaba har sai zuwa na biyu din. Tassalunikawa II, 2:3-8. Har karshen lokaci zai ci gaba da aikin rudi. Mai-ruya kuma ya ce, game da tsarin paparuman dai: Dukan mazamanan duniya kuma za su yi masa sujada, kowane wanda ba a rubuta sunansa tun kafuwar duniya chikin Littafin rai,” Ruya 13:8. Cikin Tsohuwar Duniya da Sabuwar Duniya, paparuma zai sami mubaya’a cikin darajanta Lahadi da ake yi, wanda tushensa ikon Ekklesiyar Rum ne kadai. BJ 574.3
Tun tsakiyar karni na goma sha tara, daliban annabci a Amerika suna ba da wannan shaida ga duniya. Cikin al’amuran da ke aukuwa yanzu ana ganin ci gaba da hamzari zuwa cikar annabcin nan. Ga mallamai masu Kin ikon paparuma akwai ikirari dayan game da goyon bayan Allah ga kiyayae Lahadi, da kuma rashin shaida daga Littafin, kaman na shugababbin tsarin paparuma da suka kirkiro al’ajibai don cika wurin umurni daga Allah. Kirarin cewa ana zubo da hukumcin Allah kan masu ketare Assabbat na Lahadi zai sake faruwa, yanzu ma an fara iza shi. Kuma yunkurin tilasta kiyaye Lahadi ya fara samun goyon baya. BJ 575.1
Dabarun Ekklesiyar Rum da wayonta abin mamaki ne. Ta iya karanta abin da zai faru. Tana daukan lokacinta, da sanin cewa ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma yi mata mubaya’a tawurin amincewa da Assabbat na karyan nan, cewa kuma suna shirin tilasta ta ta hanyar da ita ma ta yi anfani da ita can baya. Wadanda suka ki hasken gaskiya za su bidi taimakon wannan mulkin mai-cewa ba ta kuskure, don daukaka abin da ita ta kirkiro. Nan da nan za ta taimaki masu Kin ikon paparuma cikin wannan aikin. Wa ya fi shugabannin ‘yan paparuma sanin yadda za a bi da marasa biyayya ga ekklesiya? BJ 576.1
Ekklesiyar Roman Katolika ko ina a duniya wata babbar kungiya ce kalkashin mulkin paparuma, wadda kuma aka tsara ta don cimma manufofin paparuma. Miliyoyin membobinta a kowace kasa a duniya, ana umurta su su mika kansu don biyayya da paparuma ne. Ko da wace kasa suke, ko kuma wace irin gwamnati ke mulkinsu, ana bidar su da su, girmama ikon ekklesiya fiye da dukan sauran hukumomi; ko da sun yi rantsuwar yin biyayya ga kasa, duk da haka a bayan wannan akwai rantsuwar biyayya ga Rum da ke wanke su daga duk wani alkawali da ya saba ma burinta. BJ 576.2
Tarihi yana shaida kokarinta na kutsa kanta cikin al’amuran kasashe; kuma idan ta sami wuri ta ci gaba da manufofinta, ko da ‘ya’yan sarakuna da sauran mutane za su hallaka ma. Cikin shekara ta 1204 paparuma Innocent III ya sa Peter II, sarkin Arragon rantsuwa da ta ce: “Ni Peter, sarkin Arragonawa, na yi alkawali zan kasance da aminci kullum ga Ubangiji na paparuma Innocent III, da magadansa Katolikawa, da Ekklesiyar Rum, da aminci kuma in rike kasata cikin biyayya gare shi, ina kare Ekklesiyar Katolika, ina kuma tsananta ma masu ridda.” Wannan ya je daidai da korafin nan game da ikon paparuma “cewa doka ta ba shi dama ya saukar da sarakuna,” kuma “cewa zai iya kubutar da talakawa daga yin biyayya ga shugabanni marasa adalci.” BJ 576.3
A tuna kuma, Rum tana alfaharin cewa ba ta taba canjawa. Kaidodin Gregory VII da na Innocent III har yanzu su ne kaidodin Ekklesiyar Roman Katolika. Kuma da tana da iko da ta yi aiki da su da tsanani kamar yadda ta yi cikin sararraki da suka wuce. Masu Kin ikon paparuma basu san abin da suke yi ba sosai sa’anda su ke so su karbi taimakon Rum cikin aikin daukaka Lahadi. Yayin da suke naciya wajen cimma burinsu, Rum tana kokarin sake tabbatar da ikonta, ta sake mayar da daukakanta da ta rasa. Bari a kafa kaida a Amerika cewa ekklesiya za ta iya yin anfani da ikon kasa, cewa za a iya tilasta ayukan ibada ta wurin dokokin kasa, a takaice dai, cewa ikon ekklesiya da na kasa zai mallaki lamiri, nasarar Rum kuwa za ta tabbata a wannan kasar. BJ 577.1
Maganar Allah ta ba da kashedi game da hatsarin da ke zuwa; idan an ki ji, masu Kin ikon paparuma za su kuwa gane ainihin manufofin Rum, a kurerren lokaci kuwa, don ba za su iya kauce ma tarkon ba. Tana girma shuru zuwa samun iko. Koyaswoyinta suna tasirinsu a majalisun dokoki, cikin majami’u, da cikin zukatan mutane, tana tara manya manyan gine ginenta a wuraren sirri inda za a maimaita zaluncinta na da. A sace ba tsammani kuma tana karfafa dakarun ta don ci gaba da manufofinta, sa’an da lokaci ya yi da za ta kai hari. Abin da take bukata kawai shi ne zarafi mai-kyau, kuma yanzu ma an rigaya an fara ba ta. Ba da jimawa ba za mu gani mu kuma ji ko mene ne manufar Rum din. Dukan wanda zai gaskata ya kuma yi biyayya da maganar Allah zai sami zargi da zalunci. BJ 577.2