Daga farkon babban jayayyar a sama nufin Shaitan ne ya rushe dokar Allah. Don cimma burin nan ne ya shiga tawayen sa ga Mahalici, kuma ko da shi ke an kore shi daga sama, ya ci gaba da yakin a nan duniya. Manufan da yake bi kulluin ita ce rudin mutane, ta hakanan kuma shi sa su ketare dokar Allah. Ko ya yi wannan ta wurin kawar da dokar gaba daya ne ko kuma tawurin kin doka daya ne, a karshe dai sakamakon daya ne. Wanda ya ketare doka daya, ya rena dukan dokan ke nan; tasirinsa da kwatancinsa na zunubi ne; “ya zama mai-laifi ga duka ke nan.” Yakub 2:10. BJ 578.1
Don neman jawo reni ga dokar, Shaitan ya karkata koyaswoyin Littafin, kurakurai kuma sun shiga cikin ibadar dubbai masu cewa sun ba da gaskiya ga Littafin. Babban yaki na karshe tsakanin gaskiya da kuskure babban jayayyan nan da aka dade ana yi game da dokar Allah ne. Yanzu muna shiga wannan yakin ke nan, yaki tsakanin dokokin mutane da umurnin Yahweh, tsakanin addinin Littafin da addinin tatsuniya da al’ada. BJ 578.2
Wakilan da za su hada hannu sabanin gaskiya da adalci a wannan yaki suna aiki yanzu sosai. Magana mai-tsarki na Allah wanda aka mika mana ta wurin wahala da zub da jini, ba a ma ba shi muhimmanci sosai. Kowa zai iya samun Littafin amma mutane kalilan ne su ke karban shi a matsayin mai-bishewar rayuwarsu. Rashin aminci ya dawama sosai, ba cikin duniya kadai ba, har cikin ekklesiya. Da yawa sun ki koyaswoyin da suka kasance madogarar addinin Kirista. Manyan batutuwa na halitta da horarrun marubuta suka bayana, da faduwar mutum, da kafara, da kuma dawowar dokar Allah, Kirista da yawa suna kin, ko dukan su, ko sassansu. Dubban masu takama da hikimarsu da ‘yancinsu suna gani kamar amincewa da Littafin gaba daya kumamanci ne, suna gani kamar tabbacin baiwa da ilimi ne idan ana ba’a da Littafin ana kuma wasa da muhimman koaswoyinsa. Masu aikin bishara da yawa suna koya ma mutanensu, shehunan mallamai da sauran mallamai kuma suna koya ma dalibansu, cewa an canza ko kuma an soke dokar Allah, kuma wadanda ke gani kamar dokar tana aiki har yanzu, cewa ya kamata a yi biyayya gare ta, ana gani kamar ya kamata a rena su ne ko a yi ba’a da su. BJ 578.3
Tawurin kin gaskiya, ana kin tushen gaskiyan ne. Ta wurin tattake dokar Allah ana kin ikon mai-ba da dokan ne, mai da koyaswoyin karya gumki yana da sauki kamar sifanta gumki daga itace ko dutse ne. Ta wurin karyata halayyan Allah Shaitan yakan sa mutane su ga Allah da halin da ba nashi ba ne. Da yawa suna daukaka gumkin tunani a madadin Yahweh, yayin da kalilan ne su ke sujada ga Allah Mai-rai, yadda aka bayana shi cikin kalmarsa, cikin Kristi da cikin ayukansa na halitta. Dubbai suna mai da halitta allah, alhali suna kin Allahn halitta. Ko da shike ta wata hanya dabam ne, akwai bautar gumaka yau a cikin Kirista tabbas kamar yadda ta kasance cikin Israila ta da, a zamani Iliya. Allahn yawancin wadanda a ke gani masu hikima ne, da masu-zurfin tunani, da mawaka da ‘yan siyasa, da ‘yan jarida - allahn wayayyun ‘yan zamani, na kolejoji da jami’o’i da yawa, har ma, na wadansu makarantun koyar da tauhidi, ba da yawa suka fi Baal allan rana na Phoenicia ba. BJ 579.1
Babu kuskuren Kirista da ya fi saba ma ikon Allah, kuskuren da ya fi saba ma tunani kai tsaye, wanda sakamakonsa ya fi muni kamar koyaswar zamani da ke bazuwa da sauri, cewa wai dokar Allah ta dena aiki kan mutane. Kowace kasa tana da dokokinta da ke bidar biyayya da ban-girma; ba gwamnatin da za ta iya kasancewa in ba dokokin, kuma ko za a taba tunanin cewa Mahalicin sama da kasa ba shi da dokar da ke mulkin wadanda Ya halitta? Bari a ce manyan shugabannin ekklesiya suna koyarwa a fili cewa dokokin kasarsu da ke tabbatar da ‘yancin yan kasa ba wajibi ba ne, cewa suna takaita ‘yancin mutane, sabo da haka kuma bai kamata a yi biyayya gare su ba, ko za a bar shuganbannin nan su dade a aikinsu? Amma ko kyale dokokin kasashe ya fi tattake dokokin Allah, tushen gwamnati, muni? BJ 580.1
Da zai fi dacewa ga alummomi su soke dokokinsu, su yarda ma mutane su yi abin da sun ga dama, maimakon shugaban dukan halitta ya soke dokarsa, Ya bar duniya ba ma’aunin da zai hukunta mai-laifi ya kuma baratar da mai-biyayya. Ko mun san sakamakon soke dokar Allah? An taba gwadawa. Ababan da suka faru a Faransa a lokacin kafircinta ba kyaun gani. Lokacin an nuna ma duniya cewa yin watsi da hanin da Allah Ya dora zai sa a karbi shugabancin azalumi mafi-mugunta. Idan aka kawar da ma’aunin adalci, an bude ma sarkin mugunta hanya ke nan ya kafa ikonsa a duniya. BJ 580.2
Duk inda aka ki dokokin Allah, zunubi baya kama da zunubi, kuma adalci ba ya zama abin sha’awa. Wadanda suka ki mika kai ga gwamnatin Allah ba za su iya mulkin kansu ba sam. Ta wurin munanan koyaswoyinsu suna shuka ruhun rashin bangirma cikin zukatan yara da matasa, kuma sakamakon wannan shi ne jama’a marasa bin doka, masu son nishadi kawai. Yayin da ake dariyan wautar masu biyayya ga dokokin Allah, jama’a suna karban yaudarar Shaitan da marmari. Suna bin sha’awa, suna kuma aikata zunuban da suka jawo ma kafirai hukumci. BJ 580.3
Masu koya ma mutane su rena dokokin Allah suna shuka rashin biyayya ne domin su girbe rashin biyayya. Bari a kawar da halin da dokar Allah ta dora gaba daya, nan da nan kuma za a rabu da dokokin mutane. Da shike Allah Ya hana rashin aminci, kiyashi, karya da yaudara, mutane suna shirye su tattake dokokinsa domin suna hana su ci gaba a duniya. Amma sakamakon watsar da umurnin nan zai zama abin da bas u zata ba. Idan dokar ba ta aiki,don me za a ji tsoron ketarewa? Duniya za ta kasane ba tsaro. Mutane za su kwace dukiyar makwabtansu da karfi, masu karfi ne kuma za su fi arziki. Ba za a girmama rai kansa ba ma. Alkawalin aure ba zai kasance garkuwa da zai tsari iyali ba kuma. Mai-karfi, in ya ga dama sai ya dauki matar makwabcinsa da karfi. Zai kawar da doka ta biyar tare da ta hudu. Yara ba za su yi shakkar dauke ran iyayensu ba, idan wannan zai sa su sami muradum zukatansu. Duniya da ta waye za ta zama matattarar mafasa da masu-kisan gilla, kuma salama da hutu da farinchiki za su watse daga duniya. BJ 581.1
Yanzu ma koyaswar cewa an ‘yantar da mutane daga biyayya ga dokar Allah ta nakasa tunanin halin kirki ta kuma bude ambaliyar zunubi a duniya. Rashin bin doka da rashawa suna kwararo mana kamar igiyar ruwa mai-nutsarwa. Shaitan yana aiki cikin iyali. Tutarsa tana kadawa har cikin iyalan Kirista. Akwai kishi da mugun zato, riya, rashin jituwa, tashin hankali, cin amana, da biyan muradin sha’awa. Dukan tsarin kaidodi da koyaswoyin addini da ya kamata su zama harsashe da ginshikin rayuwar jama’a, yana kaduwa ne, ya kusan faduwa zuwa hallaka. Masu aikata munanan laifuka, sa’anda aka kai su kurkuku sabo da laifukansu, sau da yawa akan ba su kyautuka da kulawa sai ka ce sun yi wani fice. Ana labarta halayensu da laifofinsu. Masu watsa labarai sukan labarta muguntansu dalla-dalla, ta haka kuma su sa wadansu shiga aikata yaudara, fashi, da kisa; Shaitan kuma yakan ji dadin nasarar dabarunsa. Yawaitar mugunta, daukan rai barkatai, yawaitar rashin kamewa da kawane nau’in zunubi, ya kamata su falkas da dukan masu-tsaron Allah su nemi sanin abin da za a iya yi don tsayar da mugunta. BJ 581.2
Kotuna suna rashawa da cin hanci. Shugabanni suna kwadayin abin da za su samu suna kuma son sha’awa da jin dadi. Rashin kamewa ya duhunta tunanin mutane da yawa, ta yadda Shaitan yana mallakarsu. Ana rudar da masu-shari’a ana kuma ba su cin hanci. Maye da holewa da kishi da kowane irin rashin gaskiya suna cikin wadanda ya kamata su tabbatar da kiyaye dokoki. “Adalchi yana tsaye daga nesa; gama gaskiya ta fadi a chikin hanya, adilchi kuma ba ya iya shigowa ba.” Ishaya 59:14. BJ 582.1
Zunubi da duhun ruhaniya da suka kasancewa a kalkashin mulkin Rum sakamakon danne Littafin ne da ta yi; amma ina za a sami sanadin rashin aminci, da kin dokar Allah, da kuma lalacewa da aka samu a kalkashin hasken bishara a zamanin ‘yancin addini? Yanzu da Shaitan ba zai sake iya rike duniya kalkashin mulkinsa tawurin hana Littafin ba, ya koma ga wadansu dabaru don cim ma manufa dayan. Hana amincewa da Littafin yakan cika burinsa ya kuma bata Littafin kansa. Ta wurin koyar da cewa dokar Allah ba ta aiki yana sa mutane su ketare ta kamar ma basu san ta ba. Yanzu kuma, kamar da, ya yi aiki ta wurin ekklesiya domin ci gaba da nufinsa. Kungiyoyin addini na yau sun ki jin gaskiya mara dadi da ake gabatarwa cikin Littafin, kuma cikin yaki da gaskiyan sun amshi fasara suka kuma dauki matsayin da ke baza iri na shakka. Da shi ke sun manne ma kuskuren paparuma na cewa matattu sun san abin da ke faruwa, sun ki abin da shi ne kadai garkuwa mai-kariya daga sihiri. Koyaswar azaba ta har abada ta sa mutane da yawa sun bar gaskata Littafin. Kuma yayin da a ke iza mutane su kiyaye doka ta hudu, akan tarar cewa tana umurta cewa a kiyaye Assabbat na rana ta bakwai ne, kuma don kwace kansu daga abin da ba sa so su yi, shahararrun malamai da yawa suna cewa dokar Allah ta dena aiki. Ta hakanan suna watsar da dokar da kuma Assabbat tare. Sa’anda aikin inganta Assabbat ke ci gaba, kin dokar Allahn nan don ana so a rabu da bukatun doka ta hudu zai kusan mamaye duniya. Koyaswoyin shugabannin addini sun bude kofa domin rashin aminci, da sihiri, da kuma rena doka mai-tsarki ta Allah, kuma kan shugababbin nan ne nawaya mai-ban tsoro ta rataya sabo da zunubin da ake yi a cikin Kirista. BJ 582.2
Duk da haka, mutanen nan suna cewa lalacewa da ke yaduwa da saurin nan sakamakon bata abinda suke kira “Assabbat na Kirista” ne, kuma wai tilasta kiyaye Lahadi zai inganta halayyan kirki cikin jama’a. Ana wannan zancen, musamman a Amerika, in da aka yi wa’azin Assabbat na gaskiyan. A nan, aikin kamewa, daya daga cikin canje canje mafi muhimminci, akan garwaya shi da koyaswar Lahadi, masu koyar da zancen Lahadin kuma sukan ce suna kokari ne su kara ci gaban jama’a, kuma wadanda suka ki hada kai da su akan zarge su da cewa magabtan shirin kamewa ne. Amma hada yunkurin tabbatar da kuskure da wani aikin wanda shi kansa yana da kyau, ba zai canja kuskuren ba. Za mu iya badda kamanin guba tawurin garwaya ta da abinci mai-kayu, amma ba za mu sake yanayinsa ba. Sabanin haka ma, dafin zai kara zama da hatsari da shike ana iya cinsa cikin rashin sani. Wata dabarar Shaitan ita ce garwaya karya da daidai gaskiyar da za ta sa a yarda da ita. Shugabannin inganta Lahadin za su iya koyar da canje canjen da mutgane ke bukata, kaidodi da suka je daidai da Littafin, duk da haka da shike tare da su akwai abin da ya saba ma dokar Allah, bayinsa ba za su hada kai da su ba. Ba abinda zai halatta masu soke dokokin Allah domin umurnin mutane. BJ 583.1
Ta wurin kurakurai biyu din nan, rashin mutuwar mai-rai da tsarkin Lahadi, Shaitan zai kawo mutane kalkashin rudinsa. Yayin da na farkon yana kafa tushen sihiri, na biyu din yana hada dankon amincewa da Rum. Masu Kin mulkin paparuma a Amerika ne za su jagoranci mika hannu zuwa ketaren teku su kama hannun sihiri; za su ketare rami mara matuka su kama hannu da mulkin Rum, kuma kalkashin tasirin hadin kan nan na sassa uku, kasan nan za ta bi matakan Rum wajen tattake ‘yancin lamiri. BJ 584.1
Da shi ke sihiri ya fi kwaikwayon Kiristanci a suna na zamanin nan, yana da karfin rudi da kuma jawowa cikin tarko. Shaitan kansa zai tuba, bisa ga yanayin al’amuran zamanin. Zai bayana da kamanin malaikan haske. Tawurin wakilcin sihiri, za a aikata al’ajibai, za a warkar da marasa lafiya, za a kuma yi ababa na ban mamaki zahiri. Kuma da shike ruhohin za su ce suna da bangaskiya ga Littafin suna kuma girmama ekklesiya, za a yarda da aikinsu a matsayin bayana ikon Allah. BJ 584.2
Layin bambanci tsakanin masu cewa su Kirista ne da marasa addini yanzu ba shi da yawa. Membobin ekklesiya suna kaunar abin da duniya ke kuana, kuma suna shirye su hada hannu da su, Shaitan kuma ya kuduri aniyar hada su wuri daya, ta hakanan kuma shi karfafa shirinsa tawurin tura kowa cikin harkar sihiri. ‘Yan paparuma masu alfahari da al’ajibai a matsayin alamar ekklesiya ta gaskiya, nan da nan ikon nan mai-aikata al’ajibai zai rude su, masu-Kin ikon paparuma kuma, da shike sun rigaya sun yi watsi da garkuwar gaskiya, su ma za a rude su. ‘Yan paparuma da masu Kin ikon paparuma da ‘yan duniya duka za su karbi surar ibada ba tare da ikonta, za su kuma ga wannan hadin kan kamar babban yunkuri ne na tubar da duniya da kuma shigo da shekaru dubun da suka dade suna jira. BJ 584.3
Ta wurin sihiri Shaitan yana bayanuwa da kamanin mai-taimakon ‘yan Adam, yana warkar da cututtukan mutane, yana kuma cewa wai ya kawo wani sabon tsarin ibada ta addini, amma kuma yana aikin hallakaswa ne. Jarabobinsa suna kai jama’a da yawa ga hallaka. Rashin kamewa yana kawar da tunani; fasikanchi da tashin hankali da zub da jini sukan biyo baya. Shaitan yana jin dadin yaki, domin yana ta da fushi mafi-muni, ya kuma tura mutane zuwa mutuwa cikin zunubansu. Nufinsa ne ya zuga al’ummai zuwa yaki da juna, domin ta hakanan zai iya karkata tunanin mutanen daga shiryawa don rana ta Allah. BJ 585.1
Shaitan yana kuma aiki ta wurin halitta don tara girbinsa na rayuka da basu shirya ba. Ya rigaya ya yi nazarin asiran dakunan gwajin halitta, yana kuma anfani da dukan ikonsa don mallakar halitta duk inda Allah ya yarda masa. Sa’anda aka bar shi ya jarabci Ayuba, nan da nan aka share garkunan shanu da na tumaki, bayi, gidaje da ‘ya’ya, damuwa daya bayan daya kamar kyaftar ido. Allah ne yake kare halitunsa yana kange su daga ikon mai-hallakaswan. Amma Kirista sun rena dokar Yahweh; kuma Ubangiji zai yi daidai abinda Ya ce zai yi - zai janye albarkunsa daga duniya ya kuma cire tsaronsa daga wadanda ke tawaye ga dokarsa suna kuma koya ma wadansu, suna tilasta su yin haka. Shaitan yana mulki kan dukan wadanda Allah bai tsare su mausamman ba. Zai taimaki wadansu, ya ba wadansu ci gaba domin ya ci gaba da manufofinsa, zai kuma kawo ma wadansu wahala ya kuma sa su ji kamar Allah ne yake wahal da su. BJ 585.2
Yayin da yake bayanuwa ga ‘ya’yan mutane kamar babban mai-maganin da zai iya warkar da dukan cututtukansu, za ya kawo ciwo da bala’i, har sai an rushe manyan birane suka zama kango. Ko yanzu ma yana aiki. Cikin hatsaruka da masifu na teku da na kasa, cikin gobara, cikin guguwa masu karfi da mahaukatan iskoki tare da kankara, da ambaliya da munanan iskan ruwa masu barna, da igiyoyin ruwan teku masu fushi, da rawan duniya, ko ina, ta hanyoyi dubu kuma, Shaitan yana nuna ikonsa. Yakan share anfanin gona da ya fara nuna, sai yunwa da wahala su biyo. Yana zuba ma iska wani guba mai-kisa, dubbai kuma sukan hallaka saboda annobar. Ababan za su rika kara yawaita da halaka. Hallaka za ta abko ma mutane da dabbobi. “Kasa tana makoki tana yaushi,” “madaukaka na wajen jama’a suna kasala. Kasa kuma ta kazamtu kalkashin mazamnanta; saboda sun ketare dokokin, sun sake farilla, sun ta da madawamin alkawali.” Ishaya 24:4,5. BJ 585.3
Sa’an nan babban mai-yaudaran zai so ya nuna ma mutane cewa masu bautar Allah ne su ke jawo wahalolin nan. Wadanda suka jawo fushin Allah za su zargi wadanda biyayyarsu ga dokokin Allah tana tsauta ma masu ketare dokokin, cewa su ne suka jawo masu masifun. Za a ce mutane suna yi ma Allah laifi ta wurin ketare assabbat na Lahadi, cewa zunubin nan ya jawo masifu da ba za su kare ba har sai an tilasta kiyaye doka ta hudu, wanda ke lalatar da kiyayewar Lahadi, su ne ke wahal da mutanen, suna hana su dawowa ga alherin Allah da ci gaba a duniya. Ta hakanan zargin da aka yi ma bawan Allah a da, za a maimaita shi, kuma sabo da dalilai tabbatattu ma. “Ya zama kwa, sa’anda Ahab ya hangi Iliya, Ahab ya che masa, kai ne, kai mai-wahal da Israila? Ya amsa, Ba ni na wahalda Israila ba, amma kai ne da gidan ubanka, da shi ke kun rabu da dokokin Ubangiji, ka kwa bi Baalim.” 1Sarakuna 18:17,18. Sa’anda aka ta da fushin mutanen tawurin zarge zargen karya, za su dauki mataki game da jakadun Allah daidai irin wanda Israila mai-ridda ta dauka game da Iliya. BJ 586.1
Ikon aikata al’ajibai da aka nuna tawurin sihiri zai yi tasiri sabanin wadanda suka zabi biyayya ga Allah maimakon mutane. Sadarwa daga ruhohi zai ce Allah ya aike su su nuna ma masu-kin Lahadi kuskurensu, su kuma tabbatarda cewa ana biyayya ga dokokin kasa kamar dokokin Allah. Za su yi bakincikin muguntar da ke cikin duniya su kuma goyi bayan shaidar mallaman addini cewa lalacewar halayen kirki sakamakon bata Lahadi ne. Fushin da za a zuga sababinin dukan wadanda suka ki shaidar su mai-yawa ne. BJ 586.2
Hanyar Shaitan a fadan karshen nan da mutanen Allah daya take da wadda ya bi a farkon babban jayayyar a sama. Ya ce wai yana neman ci gaban zaman lafiyan gwamnatin Allah ne, alhali yana iyakar kokarinsa ne ya tabbatar da rushewarsa. Kuma wannan aikin ne ya ce malaiku masu biyayya ke yi. Hanyar rudin nan ne ta mamaye tarihin Ekklesiyar Rum. Ta ce ita ce ke wakiltar sama, alhali tana kokarin daukaka kanta fiye da Allah tana kuma so ta canja dokarsa. Kalkashin mulkin Rum wadanda suka mutu saboda amincinsu ga bishara an zarge su cewa masu-aikata mugunta ne, aka ce suna hada kai da Shaitan, aka kuma bi kowace hanya don rufa su da kunya, don a sa mutane da su kansu ma su ga kamar su ne masu-laifi mafi-muni. Haka zai kasance yanzu, yayin da Shaitan ke so ya hallaka masu girmama dokar Allah, za sa a zarge su da ketare doka, cewa su masu rena Allah ne suna kuma jawo hukumci ga duniya. BJ 587.1
Allah ba ya taba tilasta lamiri ko zuciya, amma Shaitan kullum, domin neman mallakar wadanda ba zai iya rudinsu ba, yana tilastawa ne ta wurin zalunci. Ta wurin tsoro ko tilastawa yana kokarin mallakar lamiri, ya kuma samo ma kansa biyayya daga mutane. Don cimma wannan, yana aiki ta wurin hukumomin addini da na kasa, yana zuaga su su tabbatar da dokokin mutane maimakon dokar Allah. BJ 587.2
Za a zargi masu girmama Assabbat na Littafin cewa magabtan doka da oda ne su, masu rushe halayyan kirki na jama’a, suna jawo hargitsi da lalacewa, da kuma hukumcin Allah bisa duniya. Za a ce da kyawawan halayensu matsanantan halaye, da taurin kai, da rena hukuma. Za a zarge su da rashin biyayya ga gwamnati. Masu wa’azi da suka ki biyayya ga dokar Allah za su bayana a bagadi cewa Allah ne ya umurta a yi biyayya ga hukumomin kasa. A majalisun dokoki da kotunan shari’a za a zargi masu-kiyaye doka a kuma hukumta su. Abinda basu fada ba za a ce sun fada; za a karkata manufofinsu a ba su ma’ana mafi muni. BJ 588.1
Sa’anda ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma suka ki bayanai masu-goyon bayan dokar Alllah, za su so su rufe bakunan wadanda ba za su iya ka da su ta wurin Littafin ba. Ko da shike suna rufe idonsu daga batun, yanzu suna daukan wata hanya da za ta kai ga zaluntar wadanda suka ki yin abin da sauran Kiristan duniya ke yi, suna kuma amincewa da sharuddan Assabbat na paparuma. BJ 588.2
Masu martaba na ekklesiya da na kasa za su hada hannu su ba da toshiya ko su rinjayar ko su tilasta dukan mutane su girmama Lahadi. Da shi ke babu goyon bayan Allah za a kafa dokoki na danniya. Toshiya ta siyasa tana lalata kaunar adalci da girmama gaskiya; kuma har a Amerika ma mai-‘yanci, shugabanni da masu-yin dokoki, don neman goyon bayan jama’a, za su amince da sabuwar dokar da za ta tilasta kiyaye Lahadi. ‘Yancin lamiri, wanda da wahala sosai aka samo shi, ba za a girmama shi kuma ba. A yakin da ba da jimwa ba za a yi, za mu ga kwatancin kalmomin annabin cewa: “Sai dragon ya hasala da gaske da machen, ya tafi kuma domin shi yi yaki da sauran zuriyanta, wadanda su ke kiyaye dokokin allah, suna rike da shaidar Yesu.” Ruya 12:17. BJ 588.3