“A komo bisa shari’an da shaidan! Idan basu fadi bisa ga wannan magana ba, hakika babu wayewan gari a garesu ba.” Ishaya 8:20. Ana nuna ma mutanen Allah Littafin a matsayin tsaronsu daga tasirin mallaman karya da ikon rudi na ruhohin duhu. Shaitan yana anfani da kowace dabara don hana mutane sanin Littafin, da shi ke kalamansa suna bayana rudinsa. A kowace falkaswar aikin Allah sarkin mugunta yakan kara himmar ayukansa, yanzu yana tayar da iyakar kokarinsa domin fama ta karshe tsakaninsa da Kristi da masu binsa. Babban rudi na karshe zai bayana a gabanmu ba da jimawa ba. Antichrist zai aikata al’ajiban a gabanmu. Jabun zai yi kama da ainihin sosai ta yadda ba zai yiwu a bambanta su ba sai ta wurin Littafin. Dole a gwada kowace shaida da kowace magana da shaidar Littafin. BJ 589.1
Za a yi hamayya da masu kokarin yin biyayya ga dukan dokokin Allah, a kuma yi masu ba’a. Za su iya tsayawa cikin Allah ne kadai. Dominsu jimre gwajin da ke gabansu, dole su gane nufin Allah yadda aka bayana cikin maganarsa, za su iya girmama Shi kawai idan sun sami kyakyawar fahimtar halinsa da gwamnatinsa da manufofinsa ne kadai, suka kuma yi anfani da su. Sai dai wadanda suka karfafa tunaninsu da gaskiya na Littafin ne kadai za su jimre babban fada na karshen. Ga kowane mai-rai gwajin zai zo: ko zan yi biyayya ga Allah maimakon mutane? Sa’ar hukumcin ma ta zo yanzu. Ko sawayenmu sun kafu bisa Dutsen maganar Allah da ba ta sakewa? Ko muna shirye mu tsaya da karfi mu kare dokokin Allah da imanin Yesu? BJ 589.2
Kafin giciyewarsa Mai-ceton ya bayana ma al’majiransa cewa za a kashe shi ya kuma sake tashi daga kabarin, kuma malaiku suna wurin domin su fassara kalmominsa ga tunanin almajiran da zukatansu. Amma almajiran suna begen kubutarwa daga bautar Romawa ne, kuma ba su iya yarda da tunanin cewa shi wanda dukan begen su ke kan sa zai yi mutuwar wulakanci ba. Kalmomin da ya kamata su ji sun fice daga tunaninsu; sa’an da lokacin gwaji ya zo kuwa, ya tarar ba su shirya ba. Mutuwar Yesu ta rushe begensu kaman bai gargade su kafin lokacin ba. Haka ne cikin annabci an bude mana a bayane abin da ke zuwa kamar yadda maganar Kristi ta bayana ma almajiran. Al’amuran da ke da nasaba da rufewar gafara da aikin shiryawa domin lokacin wahala suna bayane sarai. Amma da yawa ba su fahimci muhimman gaskiyan nan ba sai ka ce ba a taba bayana su ba. Shaitan yana kallo domin ya dauke kowace ganewa da za ta sa su zama da hikima zuwa ga ceto, kuma lokacin wahala zai same sub a a shirye ba. BJ 590.1
Sa’anda Allah Ya aika ma mutane fadaka masu muhimmincin da ya sa an nuna kamar malaiku masu firiya a tsakiyar sararin sama ne ke shelarsu, yana bidar kowane mai-tunani ya saurari sakon. Hukumci mai-ban tsoro da aka furta kan sujada ga bisan da gumkinsa (Ruya 14:9-11) ya kamata ya kai kowa ga nazarin annabci domin a san ko menene shaidar bisan, da yadda za a iya kin karban ta. Amma yawancin mutane suna kin sauraron gaskiya, suna komawa ga tatsuniyoyi. Manzo Bulus da ya hangi kwanakin karshe ya ce: “Gama kwanaki za su zo da ba za su daure da koyaswa mai-lafiya ba.” Timothawus II, 4:3. Wannan lokacin ya zo. Yawanci ba sa son gaskiya ta Littafin, da shi ke ta na tsoma baki cikin muradan zuciya ta zunubi mai-kaunar duniya; Shaitan kuma yana tanada rudin da su ke kauna. BJ 590.2
Amma Allah yana so ya sami mutane a duniya da za su rike Littafin kadai a matsayin ma’aunin dukan koyuaswoyi da ginshikin kowane canji. Ra’ayin masana, ra’ayin kimiyya, kaidodi ko matakai na majalisun ekklesiyoyi, da duk yawansu da bambance bambancensu kamar ekklesiyoyin, da muryar masu rinjaye ko dayan wadannan ko ma dukansu bai kamata su zama shaidar sahihancin wani batu na imanin addini ba. Kafin a amince da kowace koyaswa ko umurni bari mu tabbatar cewa “in ji Ubangiji” ya goyi bayanta. BJ 591.1
Shaitan kowane lokaci yana kokarin jan hankali daga Allah zuwa mutum. Yana jan mutane su dubi bishops da pastoci da shehunan mallaman tauhidi a matsayin masu bishewarsu maimakon binciken Littafin domin gano ma kansu aikinsu. Sa’an nan tawurin mallakar zukatan shugabannin nan zai iya juya jama’a yadda ya ga dama. BJ 591.2
Sa’anda Kristi ya zo domin ya fadi kalmomi na rai, talakawa sun saurare shi da farinchiki, kuma priestoci da shugabanni da yawa sun gaskata shi. Amma shugabannin priestocin da manyan kasa suka dukufa wajen kushe koyaswoyinsa da warware su kuma. Ko da shi ke an kasa yin nasara da dukan kokarinsu na neman dalilan zargi a kansa, ko da shi ke kuma sun ji tasirin ikon Allah da hikimarsa cikin kalmominsa, duk da haka suka kulle kansu cikin rashin adalci, suka ki bayananniyar shaidar Masiyanan sa, domin kada a tilasta su zama almajiransa. Masu adawan nan da Yesu mutane ne da an rigaya an koya ma sauran mutane, tun suna yara, su daukaka su, kuma sun saba amincewa da mulkinsu ba jayayya. Suka tambaya, “Yaya aka yi shugabanninmu da marubuta masana ba su gasktata Yesu ba? Da shi ne Kristi din da mutane masu ibadan nan basu karbe shi ba? Tasirin irin wadnnan mallaman ne ya jawo al’ummar Yahudawa ta ki Mai-fansarsu. BJ 591.3
Har yanzu mutane da yawa masu nuna cewa su masu-ibada ne, suna nuna irin ruhun nan da ya motsa priestocin nan da shuganbannin nan. Suna kin binciken shaidar Littafin game da gaskiya na musamman domin zamanin nan. Su kan dubi yawansu da arziki da son da ake yi masu, sai su rena kalilan din nan matatalauta, marasa farinjini, masu imanin da ya raba su da sauran duniya. BJ 592.1
Kristi ya hangi cewa ikon da marubuta da Farisawa suka ba kan su ba zai kare sa’anda Yahudawa sun warwatsu ba. Ya hangi aikin daukaka ikon mutum don mulkin lamiri, wanda ya kasance mumunan la’ana ga ekkesiya cikin dukan sararaki. Sokarsa ga marubuta da Farsawa, da gardadinsa ga mutane, cewa kada su bi makafin shugabbanin nan, an rubuta su don fadaka ne ga sararaki da ke zuwa. BJ 592.2
Ekklesiyar Rum ta kebe ma priestocinta ne ‘yancin fassara Littafin. A kan cewa ma’aikatan bishara ne kadai sun iya bayana maganar Aallah, ana hana sauran mutane Littafin. Ko da shi ke canjin ya ba da Littafin ga kowa duk da haka kaidan nan da Rum ta rike tana hana jama’a da yawa a ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma bincika Littafin don kansu. Ana koya masu su karbi koyaswoyinta yadda ekklesiya ta fassara su; kuma akwai dubbai da ba su isa su karbi wani abu ba, komi yadda Littafin ya bayana shi, idan ya saba ma koyaswar ekklesiyarsu. BJ 592.3
Duk da cewa Littafin ya cika da gardadi game da mallaman karya, mutane da yawa suna shirye su ba da kiyayewar rayukansu ga masu aikin bishara. Yau akwai dubban masu addini da ba za su iya ba da wata hujjar bangskiyan da su ke da ita ba sai da cewa shugabannin addininsu ne suka koya masu hakanan. Su kan wuce koyaswoyin Mai-ceton basu kula ba ma, su kuma ba da cikakkiyar amincewa ga maganar pastocinsu. Amma ko pastocin ba sa kuskure? Yaya za mu mika rayukanmu ga bishewarsu in ba mun sani ne daga maganar Allah cewa masu kai haske ne su ba? Rashin karfin halin rabuwa da hanyar da duniya ta saba da ita yakan sa mutane da yawa su bi matakan masana, kuma sabo da rashin son bincikawa da su ke da shi, suna kara dauruwa da sarkokin kuskure ne. Suna gani cewa gaskiya don zamanin nan tana bayane a Litafin, kuma su na jin ikon Ruhun Mai-tsarki cikin shelarta da a ke yi; duk da haka suna yarda hamayyar masu bishara ta juya su daga hasken. Ko da shi ke tunaninsu da lamirinsu sun yarda, rudaddun mutanen nan basu isa su yi tunani dabam da na paston ba, don haka ana sadakar da ra’ayin kansu da muradan zukatansu ga rashin ba da gaskiya da girman kai da kiyayyar wadansu. BJ 592.4
Hanyoyin da Shaitan ke aiki ta wurin tasirin mutane don daure mutane suna da yawa. Yana rike jama’a da yawa wurinsa tawurin manna su da kirtanin soyayya ga masu gaba da giciyen Kristi. Ko da mene ne dangantakan nan, na iyaye ne, na ‘ya’ya ne, na aure ne, ko na zama da jama’a ne, sakamakon daya ne, masu hamayya da gaskiya su na anfani da ikonsu don mulki bisa lamiri, kuma rayukan da aka rike hakanan ba su da isashen karfin hali ko ‘yancin kai da za su yi bayayya ga bangaskiyar kansu. BJ 593.1
Gaskiya da darajar Allah ba su rabuwa; ba shi yiwuwa garemu, da Littafin kusa da mu, mu girmama Allah tawurin ra’ayoyi na kuskure. Da yawa sun a cewa wai ba abin da ka gaskata ne muhimmin ba, muddan dai rayuwarka daidai ne. Amma abin da aka gaskata ne yake sifanta rayuwar. Idan muna iya samun haske da gaskiya, kuma muka ki anfani da zarafin ji da na ganin shi, mun ki shi ke nan, mun zabi duhu maimakon haske. “Akwai wata hanya wadda ta ke da alamar kirki ga mutum, amma matukatatta tafarkun mutuwa che.” Misalai 16:25. Rashin sani ba hujja ce don kuskure ko zunubi ba, idan akwai dukan zarafin sanin nufin Allah. Mutum yana tafiya sai ya kai wani wuri inda akwai hanyoyi da yawa da allo na bishewa da ke nuna inda kowace hanya ta nufa. Idan ya rabu da allon bishewan, ya bi hanyar da ya ga ta dace mashi, ko da gaske yake yi, ba mamaki ya iske cewa bai bi hanyar da ta dace ba. BJ 593.2
Allah Ya ba mu maganarsa domin mu san koyaswoyinta mu sani ma kan mu abin da yake bukata daga gare mu. Sa’an da masanin Attaurat din nan ya tambayi Yesu cewa; “Mi zan yi domin in gaji rai na har abada?,” Mai-ceton Ya kai hankalinsa wurin Littafin, Ya ce: “Mi ke a rubuche a chikin Attaurat?, yaya ka ke karantawa?” Rashin sani ba zai zama hujja ga matasa ko tsofoffi ba ko kuma ya ‘yantar da su daga horon da ya cancanci masu ketare dokar Allah, da shike a hannunsu akwai amintaciyar gabatarwar dokan da kai’dodinta da sharuddanta. Manufofi masu kyau kadai basu isa ba, yin abin da mutum ke gani daidai ne ko abin da pasto ya ce daidai ne kadai bai isa ba. Batun ceton ransa ake, kuma ya kamata ya bincike Littafin da kansa, komi karfin ra’ayinsa, komi tabbacin da yake da shi cewa ma’aikacin bisharan ya san gaskiya, wannan ba tushe ba ne. Yana da taswira da ke nuna kowace alama cikin tafiya zuwa sama, kuma bai kamata ya yi bara-da-ka ko kame-kame game da wani abu ba. BJ 594.1
Babban aiki kuma aiki mai-girma ga kowane mai-tunani shi ne ganowa daga Littafin ko mene ne gaskiya, sa’an nan ya yi tafiya cikin haske ya kuma karfafa saura su bi kwatancinsa. Ya kamata kowace rana mu yi nazarin Littafin a natse, muna auna kowace magana muna kuma gwada nassi da nassi. Da taimakon Allah ya kamata mu sifanta ra’ayinmu don kanmu domin za mu amsa ma kanmu a gaban Allah. BJ 594.2
Gaskiyan da Littafin ya bayana a fili, an jawo su cikin shakka da duhu, ta hannun masana wadanda, da son nuna cewa suna da hikima sosai, suke koyar da cewa Littafin yana da ma’ana mai-wuyan ganewa, ma’ana na sirri na ruhaniya wanda ba a gani daga harshen da aka yi anfani da shi. Mutanen nan mallaman karya ne. Irinsu ne Yesu ya ce suna da “Rashin sanin litattafai da ikon Allah.” Markus 12:24. Ya kamata a fassara harshen Littafin bisa ga ma’anarsa na bayane ne, sai dai in an yi anfani da alama ko kamani. Kristi ya yi alkawali cewa; “Idan kowane mutum yana da nufi shi aika nufin Allah, shi za ya sani ko abin da ni ke koyaswa na Allah ne.” Yohanna 7:17. Da mutane za su dauki Littafin daidai yadda take rubuce, da dai ba mallaman karya masu batar da mutane suna rikita tunaninsu, da an yi aikin da zai sa malaiku su yi murna ya kuma kawo dabban dubbai da yanzu su ke yawo cikin kuskure zuwa garken Kristi. BJ 594.3
Ya kamata mu yi anfani da dukan tunaninmu cikin nazarin Littafin mu kuma ingiza tunaninmu ya fahimci muhimman ababa na Allah, kuma ba za mu taba manta cewa ainihin ruhun mai-koyon irin ruhun yaro ne na saukin horuwa da biyayya. Ba za a iya magance matsalolin Littafin ta hanyoyin da ake anfani da su don magance matsalolin ilimi ba. Bai kamata mu shiga nazarin Littafin da irin dogara da kai da ake shiga fannin kimiyya da shi ba, amma da ruhun tawali’u da koyuwa don samun sani daga Allah. In ba haka ba miyagun malaiku za su mankantar da tunaninmu su kuma taurara zukatanmu ta yadda gaskiya ba za ta yi tasiri gare mu ba. BJ 595.1
Yawancin sassan Littafin da masana ke cewa asiri ne, ko kuma su wuce su wai ba su da anfani, suna cike da gargadi ga wanda aka koya masa a makarantar Kristi. Wani abin da ya sa da yawa masanan tauhidi ba su da ganewa sarai na maganar Allah shi ne, su kan rufe idonsu ga ababan da ba sa so su aikata. Ganewar gaskiya ta Littafin ta dangana, ba lallai kan yawa da kuma kwarin tunanin da aka yi anfani da shi cikin binciken ba ne kamar kyakyawar manufa da himmatuwa wajen neman adalci. BJ 595.2
Bai kamata a taba in nazarin Littafin ba addu’a ba. Ruhu Mai-tsarki ne kadai zai iya sa mu mu ji muhimmancin ababan da ke da saukin fahimta, ko kuma ya hana mu fizgo gaskiya masu wuyan ganewa. Aikin malaikan sama ne su shirya zuciya ta yadda za ta fahimci maganar Allah ta yadda za mu yi sha’awar kyaunta, mu koyu daga gardadinta, ko kuma motsu mu kuma karfafa daga alkawuranta. Ya kamata mu mai da addu’ar mai-zabura addu’armu, cewa: “Ka bude mani idanu na, domin in duba al’ajibai daga chikin shari’arka.” Zabura 119:18. Jarabobi su kan yi kaman ba za a iya yin nasara da su ba saboda, tawurin rashin yin addu’a da nazarin Littafin, wanda aka jarabce shi ba zai iya tuna alkawuran Allah ya kuma tare Shaitan da makamai na Littafin ba. Amma malaiku su na kewaye da wadanda ke shirye a koyar da su ababan ruhaniya; kuma lokacin bukata. Don haka “Sa’an da magabchi ya shigo kamar rigyawa, ruhun Ubangiji za ya kafa tuta, ya yi gaba da shi.” Ishaya 59:19. BJ 595.3
Yesu ya yi ma almajiransa alkawali cewa: “Amma mai-taimako, watau Ruhu mai-tsarki, wanda Uban za ya aiko a chikin sunana, za ya koya maku abu duka, ya tuna maku kuma dukan abin da nafada maku.” Yohanna 14:26. Amma dole sai an rigaya an ajiye koyaswoyin Kristi a zuciya domin Ruhu Mai-tsarki ya tuna mana a lokacin wahala. Dawuda ya ce: “Na boye maganarka chikin zuchiyata, domin kada in yi maka zunubi.” Zabura 119:11. BJ 596.1
Dukan wadanda ke kaunar rai na har abada ya kamata su yi hankali da shigowar shakka. Za a kai hari ga ainihin madogaran gaskiyar. Ba zai yiwu a boye ma habaici da yaudarar miyagun koyaswoyin nan masifa na kafircin zamani ba. Shaitan yakan sifanta jarabobinsa daidai da kowane sashi. Yakan tinkari jahilai da ba’a ko reni, amma yakan gwada masu ilimi da musu na kimiyya ne da babu ‘yancin zurfin tunani, wadanda ya shirya domin ta da rashin amincewa ko rena Littafin. Har matasa marasa kwarewa ma su kan yi kokarin ta da shakka game da muhimman kaidodin Kiristanci, kuma rashin imanin matasan nan duk da rashin zurfinsa, yana da tasirinsa. Ta hakanan ana sa mutane da yawa su yi ma imanin ubaninsu ba’a, su kuma rena Ruhun alheri. Ibraniyawa 10:29. Rayuka da yawa da suka yi alkawalin daukakar Allah da albarka ga duniya sun la’antu da warin rashin imani. Dukan masu amincewa da fahariyar matakan tunanin mutum suka kuma ga kamar za su iya fassara asiran Allah har su kai ga gaskiya ba tare da taimakon hikimar Allah ba, sun nannadu cikin tarkon Shaitan ke nan. BJ 596.2
Muna raye a zamani mafi ban tsoro na tarihin duniyan nan. Kadarar yawancin jama’an duniya ya kusa tabbatuwa. Lafiyar mu nan gaba da kuma ceton sauran rayuka sun dangana ga abin da mu ke yi yanzu ne. Muna bukatar bishewar Ruhun gaskiyar. Ya kamata kowane mai-bin Kristi ya tambaya da gaske; “Ubangiji, me ka ke so in yi?” Muna bukatar kaskantar da kanmu a gaban Ubangii da azumi da addu’a, mu kuma yi bimbini kan maganarsa, musamman kan batutuwan hukumcin. Ya kamata yanzu mu bidi rayayyen dandano mai-zurfi game da al’amuran Allah. Ba mu da lokacin da za mu bata. Al’amura muhimmai suna faruwa kewaye da mu, muna filin Shaitan ne. Kada ku yi barci, masu-tsaro na Allah; magabcin yana boye kusa, yana shirye a kowane lokaci, ko za ka shagala ka yi gyangyadi, domin ya tasam maka ya mai da kai abincinsa. BJ 597.1
Da yawa suna kuskure game da ainihin yanayinsu a gaban Allah. Suna tafa ma kansu game da ababa marasa kyau da ba sa yi, su kuma manta nagargarun ababa masu kyau da Allah ke bukata daga gare su, amma ba su yi ba. Cewa su itatuwa ne a lambun Allah kawai bai isa ba. Ya kamata su cika bukatarsa ta wurin haihuwar ‘ya’ya. Yana bidar lissafi daga wurinsu sabo da kasawansu su yi dukan alheran da ya kamata su yi ta wurin karfafawar alherinsa. A litattafan sama an rubuta su a matsayin masu bata kasa. Duk da haka ko wadannan din ma begensu bai kare kwata kwata ba. Ga wadanda suka wofinta jin kan Allah suka kuma wulakanta alherinsa, zuciyarsa mai-kauna mai-jinkirin fushi yana roko dai. “Domin wannan an che, ka falka, kai da ka ke barchi, ka tashi daga chikin matattu, Kristi kwa za ya haskaka bisa gareka. Ku duba fa a hankali yadda ku ke yin tafiya,… kuna rifta zarafi, tun da shi ke miyagun kwanaki ne.” Afisawa 5:14-16. BJ 597.2
Sa’an da lokacin gwajin zai zo, za a bayana wadanda suka mai da maganar Allah kaidar rayuwarsu. Da damina ba bayanannen bambanci tsakanin itatuwa masu ganye kowane lokaci da sauran itatuwan, amma sa’anda iskar rani ta hura, masu-ganye kowane lokacin ba sa sakewa, yayin da sauran itatuwan a kan kakkabe ganyensu. Hakanan ba za a iya bambanta mai-zuciya ta karya daga ainihin Kirista ba yanzu, amma lokaci ya kusa da bambancin zai bayyana. Bari sabani ya taso, bari matsanancin ra’ayi da rashin sassauci su sake yawaita, bari a fara zalunci, masu zuciya biyu-biyu da masu riya kuwa za su kadu su kuma bar imanin; amma ainihin Kirista zai tsaya da karfi kamar dutse, bangaskiyarsa ta kara karfi, begensa ya kara haske, fiye da lokacin ci gaba. BJ 598.1
Mai-zaburan ya ce: “Shaidunka su ne abin tunawa gareni.” “Ta wurin dokokinka ni ke samun fahimi; domin wannan fa na ki kowache hanyar karya.” Zabura 119:99,104. BJ 598.2
“Mai-farin zuchiya ne mutum wanda yake samun hikima.” “Gama za ya zama kamar itachen da aka dasa a bakin ruwaye, wanda yana mika sawayensa a wajen kogi, ba za ya ji tsoro sa’anda zafin rana ke zuwa ba, amma ganyayensa za su yi kore, babu abinda za ya dame shi a shekaran fari, ba kwa za ya dena ba da yaya ba.” Misalai 3:13; Irmiya 17:8. BJ 598.3