Na gaba cikin wadanda aka kira domin jagorantar ekklesiya daga duhun tsarin paparuma zuwa haken gaskiya mafi-tsabta shi ne Martin Luther. Ga himma, ga kwazo, ga dukufa, ba tsoro sai dai tsoran Allah, wanda ya yarda da Littafin kadai a matsayin tushen imanin addini, Luther ne mutumin zamanin sa, ta wurin sa Allah Ya yi aiki mai-yawa domin canza ekklesiya da kuma haskaka duniya. BJ 119.1
Kamar jakadun farko na bisharar, Luther ya taso daga talauci ne. Ya yi yarantakan shi a gidan wani talakan Jamus ne. Ta wurin aikin tonon ma’adini kowace rana, baban shi ya rika biyan kurdin makarantan shi. Ya so shi ya zama lauya ne; amma Allah Ya nufa Ya mai da shi magini a babban haikalin nan da ke tasowa a hankali cikin daruruwan shekaru. Wahala da kunci da tsananin horo ne makarantar da Allah Ya shirya Luther a ciki domin babban aikin da zai yi. BJ 119.2
Baban Luther mutum ne mai-karfin zuciya da kuzari kuma, mai-halin kirki, amintace mai-taurin zuciya, mara zagaye-zagaye kuma. Mai-aminci ne ga aikinsa, ko da me zai faru. Basirar sa ta sa bai yarda da tsarin zuhudun nan ba. Bai ji dadi ba, lokacin da Luther, ba da goyon bayansa ba, ya shiga zuhudu; kuma sai bayan shekara biyu uban ya shirya da dan nasa akan wannan, duk da haka kuma ra’ayin uban bai sake ba. BJ 119.3
Iyayen Luther sun kula da ilimin yayansu da horarwarsu sosai. Suka koya masu sanin Allah da bin kaidodin rayuwar Kirista. Dan ya kan ji uban yana addu’a cewa dan ya tuna sunan Ubangiji, wata rana kuma ya taimaka wajen ci gaban gaskiyarsa. Iyayen suka rika goyon bayan duk wani abin da ke iganta tarbiyya ko basirar yaran. Suka yi iyakar kokarinsu don shirya yaran domin rayuwa mai-anfani da kuma son ibada. Sabo da naciyarsu da ingancin halinsu, wani lokaci tsananinsu ya kan yi yawa; amma shi dan Canjin, ko da shi ke yakan san sun yi kuskure, yakan amince da horonsu. BJ 120.1
A makaranta inda aka kai shi tun yana karamin yaro, an rika cin zalin Luther. Talaucin iyayensa ya sa lokacin da ya je makaranta a wani gari, akwai lokacin da sai ya bi gida gida yana raira waka kafin ya sami abinci, wani lokaci kuma ya fama da yunwa. Koyaswoyin camfi na addini a zamanin suka cika shi da tsoro. Yakan kwanta da dare cike da bakin ciki, yana tunanin munanan ababan da za su faru nan gaba, da tsoro kuma yana tunanin Allah kamar azalumin Mai-sahri’a, Mara-tausayi, maimakon Uba na sama Mai-nasiha. BJ 120.2
Duk da haka, cikin manyan matsaloli da yawa, Luther ya ci gaba da himma don samun ingantaciyar tarbiyya da basiran da yake sha’awa. Ya yi kishin samun sani, halinsa na naciya da gaskiya kuma ya sa shi marmarin neman abu na kwarai maimakon mai-kyaun gani sama-sama kawai. BJ 120.3
Sa’an da a shekarar sa ta sha-takwas ya shiga Jami’ar Erfurt, yanayin rayuwarsa ya fi na yarantakarsa kyau. Iyayen sa ta wurin tsimi da kwazo sun iya biyan dukan bukatunsa a lokacin. Tasirin abokai na kirki kuma ya rage masa damuwar irin koyaswan da ya samu da farko. Ya shiga nazarin muhimman mawallafan litattafai, yana sah’awar tunaninsu, yana koyo kuma daga hikimarsu. Ko a kalkashin muguntar mallamansa na farko ma ya ba da alamar yin fice, da ababa suka kara kyau kuwa, tunaninsa ya kara inganci da sauri. Iya tuna abu, hangen nesa, azanci mai-kyau da kuma aiwatar da kudurorinsa sun sa nan da nan ya yi fice cikin abokansa. Ingancin basira ya nunar da ganewarsa, ya kuma ba shi tunani da ganewan da suka shirya shi domin tankiyar rayuwarsa. BJ 120.4
Tsoron Ubangiji ya kasance cikin zuciyar Luther ya kuma sa shi ya rike amincinsa ga manufarsa, wanda ya kai shi shiga kaskantar da kai a gaban Allah. Ya dogara ga taimako daga Allah, bai kuma fasa fara kowace rana da addu’a ba, yayin da zuciyarsa ke rokon bishewa da goyon baya kowane lokaci. Sau da yawa yakan ce: “Yin addu’a da kyau shi ne rabi mafi kyau na nazari.” BJ 121.1
Yayin da yake duba littattafai a dakin karatun jami’ar, Luther ya gano Littafin, na harshen Latin. Bai taba ganin irin littafin nan ba. Bai san akwai shi ba ma. Yakan ji ana karatu daga Bishara ko Wasiku a wurin sujada, sai ya dauka cewa Littafin kenan dukansa. Yanzu kuma ya ga dukan maganar Allah gaba dayansa. Da ban-mamaki ya bude shi, zuciyarsa tana bugawa, ya karanta ma kansa kalmomi na rai, loto loto yana cewa: “Da dai Allah zai ba ni nawa littafi irin wannan!” Malaiku na sama suna gefensa, haske daga kursiyin Allah kuma ya bayana tmanin gaskiya ga ganewarsa. Kullum yana tsoron yi ma Allah laifi, amma yanzu sanin yanayin sa na mai-zunubi ya zo masa fiye da duk yadda ya taba ji. BJ 121.2
Marmarin samun yanci daga zunubi da samun salama da Allah ya sa shi ya shiga rayuwar zuhudu. Nan aka bukace shi ya yi ayukan kaskanci, yana kuma bara gida gida. Shekarunsa sun kai inda a kan so bangirma sosai, wadannan ayuka na kaskanci kuwa suka ci masa mutunci sosai; amma ya jimre cin mutuncin, yana gani kamar wannan wajibi ne gare shi sabo da zunubansa. BJ 122.1
Kowane zarafi ya samu yakan shiga nazari, yana hana kan shi barci, da kyar ma yakan sami damar cin abinci. Fiye da komi, yakan ji dadin nazarin maganar Allah. Ya sami wani Littafi da aka daure da tsarka a jikin bango, kuma sau da yawa yakan je wurin. Sa’an da ya kara sanin zunubinsa, ya yi kokarin samun gafara da salama ta wurin ayukansa. Ya yi rayuwa ta fama sosai, yana azumi, yana kwana gani, ya yi ma kansa bulala ma wai domin shi danne muguntarsa ta mutumtaka, wadda kuma rayuwar zuhudu ta kasa magancewa. Bai yi shakkar yin kowace sadakar da za ta kawo masa tsabtar rai da zai sa ya sami karbuwa ga Allah ba. Daga baya ya ce: “Da ni dan zuhudu ne mai-son addini, na kuma bi kaidodin kungiya ta filla filla. Da wani dan zuhudu zai iya zuwa sama ta wurin ayukansa, da ni na samu.... Da na kara ci gaba cikin zuhudu, da na kai kai na har ga mutuwa.” Ta wuin wannan rayuwar, karfin sa ya kare, ya kuma fama da tsanani, bai kuwa warke daga wannan ba har mutuwar sa. Amma duk da famarsa, zuciyarsa bat a hu ta ba. Daga baya ma har ya kusan sallamar da komai. BJ 122.2
Sa’anda Luther ya ga kamar ba shi da bege, Allah ya tanada masa aboki mai-taimako kuma. Mai-ibadan nan Staupitz ya bayana ma Luther maganar Allah, ya kuma bukace shi ya bar tunani game da kansa, ya dena tunanin horo mara iyaka sabo da ketarewar dokar Allaha, ya dubi Yesu Mai-ceto Mai-gafarar zunubai. “Maimakon azabtar da kan ka sabo zunubanka, ka jefa kanka cikin hannuwan Mai-fansa. Ka amince da Shi da adalcin rayuwarsa, da kafarar mutuwarsa.... saurari Dan Allah. Ya zama mutum domin ya ba ka tabbacin alherin Allah ne.” “Ka yi kaunar Shi wanda Ya fara kaunarka.” Kalmominsa sun yi tasiri ga tunanin Luther sosai, bayan fama da kurakurai da ya dade da su, ya iya gane gaskiyar, salama kuma ta zo zuciyarsa. BJ 122.3
An nada Luther priest, aka kuma kira shi ya zama shehun mallami a Jami’ar Wuttenburg. Nan ya shiga nazarin Littafi cikin harsunan asali na Littafin. Ya fara koyarwa game da Littafin, ya bayana ma jama’a da yawa littafin Zabura da Wasikun, da Bishara, har suka fahimta. Abokinsa Staupitz ya roke shi ya hau bagadi, ya yi wa’azin maganar Allah. Luther ya yi jinkiri, yana ganin kansa bai isa ya yi ma mutane Magana a madadin Kristi ba. Bayan doguwar mahawara ne ya yarda da shawarar abokin. Kafin nan ya rigaya ya kware a sanin Littafin, alherin Allah kuma ya kasance a kansa. Iya maganan sa ya jawo hankulan masu jinsa, yadda ya bayana gaskiyan a fili da karfi kuma, ya sa sun fahimta suka kuma yarda, kwazonsa kuma ya taba zukatansu. BJ 123.1
Luther dai dan ekklesiyar Rum ne, bai ko yi tunanin barin ta ba. Cikin shirin Allah sai aka sa shi ya ziyarci Rum. Ya yi tafiyarsa a kafa, ya rika kwana a mazamnan ‘yan zuhudu a hanyarsa. Ya yi mamakin wadata da kyau da holewan da ya gani a wani gidan ma’aikatan ekklesiya. Sabo da makudan kurdi da suke da shi, ‘yan zuhudun suka zauna a manyan gidaje, masu-kyau sosai, suna saye da tufafi mafi-tsada, suna kuma cin abinci mai-kyau sosai. Luther cikin fushi ya gwada wannan da rayuwarsa ta kunci da musun kai, da wahala. Zuciyar sa ta damu kwarai. BJ 123.2
Daga baya ya hangi birnin daga nesa. Sai ya durkusa a kasa, da babban murya kuma ya ce, “Rum mai-tsarki, na gaishe ki!” Ya shiga birnin, ya ziyarci ekklesiyoyin, ya saurari labaru na ban mamaki ta bakin priestoci da ‘yan zuhudu, ya kuma yi dukan al’adun da akan yi. Ko ina, ya ga wurare da suka cika shi da mamaki da kyama ma. Ya ga cewa akwai zunubi cikin ma’aikatan ekklesiya. Ya ji priestoci suna ba’a ta rashin kunya, ya kuma yi kyamar rashin tsabtar ransu, har a lokacin mass ma. Yayin ma’amalar sa da yan zuhudu da mutanen gari, ya sadu da barna da fasikanci. Duk inda ya je ya sadu da abin kyama ne maimakon tsarki. In ji shi, “Ba wanda zai yi zaton irin zunubi da aikin mugunta da ake yi a Rum; sai an gani an kuma ji za a gaskata. Sabo da haka sun cika cewa ‘Idan akwai lahira an gina Rum a kan ta ne: rami mara-matuka ce ita, daga inda kowane irin zunubi ke fitowa.’ ” BJ 123.3
Ta wurin wata doka, paparuma ya yi alkawalin wata gafara ga dukan wadanda za su hau “Matakalan Bilatus,” inda aka ce Mai-ceto mu Ya bi Ya sauko daga dakin shari’ar, wai kuma ta hanyar ban al’ajibi aka dauki matakalan daga Urushalima zuwa Rum. Wata rana Luther yana hawan matakalan nan da zuciya daya, sai faraf daya murya kamar tsawa ta ce masa: “Amma mai-adilchi da bangaskiya za ya rayu.” Romawa 1:17. Ya tashi tsaye ya bar wurin maza maza cikin kunya. Nassin nan bai taba rasa karfin ikon sa ga rayuwar Luther ba kuma. Daga lokacin ya kara ganin wautar dogara ga ayukan mutum domin samun ceto, ya kuma ga cewa tilas a ba da gaskiya kullum ga Kristi. An bude idanunsa, kuma ba za a sake rufe su ba, game da rudi na tsarin paparuma. Sa’an da ya juya fuskarsa daga Rum, ya juya zuciyarsa ma, kuma daga wannan lokacin, rabuwar ta dinga karuwa ne, har ya rabu da ekklesiyar paparuma kwatakwata. BJ 124.1
Bayan dawowansa daga Rum, Luther ya sami digiri na likata a fannin addini a Jami’ar Wuttenburg. Yanzu yana da yancin dukufa ga Littafi fiye da duk wani lokaci da ya gabata. Ya yi alkawalin yin nazari a hankali da kuma yin wa’azin maganar Allah da aminci, ba furcin su paparuma da koyaswoyinsu ba, duk tsawon ransa kuwa. Yanzu shi ba kawai dan zuhudu ba ne ko kuma mallami, amma mai-izinin koyar da Littafi ne. Kalmomin nan sun girgiza tushen daukakar paparuma. Sun kunshi muhummin kaidar Canjin. BJ 124.2
Luther ya ga hadarin daukaka tunanin mutane bisa maganar Allah. Ba tsoro ya soki rashin gaskiyan mallaman makaranta, ya kuma yi hamayya da ussan ilimi da tauhidin da ya dade yana tasiri kan mutane. Ya soki irin koyaswoyin, cewa ba su da anfani, kuma suna da hatsari sosai, sai ya so ya juya tunanin masu jinsa daga karyar masanan ussan ilimi da masanan tauhidi zuwa gaskiya ta har abada, wadda annabawa da manzani suka bayana. BJ 125.1
Sakon da yakan bayar ma jama’an da suka gaskata shi yana da daraja sosai. Ba su taba jin irin koyaswan nan ba. Albishir na kaunar Mai-ceto, tabbacin gafara da salama ta wurin jinin kafararsa, sun ba su murna da bege mara karewa. A Wittenburg an kunna wani haske wanda zai kai karshen duniya, kuma zai rika kara haskakawa har karshen lokaci. BJ 125.2
Amma haske da duhu ba za su iya daidaituwa ba. Tsakanin gaskiya da kuskure akwai sabani mara boyuwa. Goyon bayan dayan sabani ne da na biyu din. Mai-ceton mu da kansa Ya ce: “Na zo ba domin in koro salama ba, amma takobi.” Matta 11:34. Shekaru kadan kuma bayan an fara Canjin, Luther ya ce: “Allah ba Ya bishe ni, yana ingiza ni ne zuwa gaba. Yana dauke ni. Ni ba mai-gidan kai na ba ne. Ina marmarin zaman hutu; amma ana jefa ni cikin tsakiyar hargitsi da juyin dan wake.” Yanzu an kusa a roke shi ya shiga hamayyar kenan. BJ 125.3
Ekklesiyar Rum ta yi kasuwanci da alherin Allah. Teburan masu canja kurdi (Matta 12:12) sun kasance a gefen bagadin ekklesiya, iska kuma ta cika da surutun masu saye da sayarwa. Kalkashin cewa wai ana tara kurdi don gina majami’ar Saint Peter a Rum aka rika tallan gafarar zunubi! Amma hanyar da aka dauka don cika burin Rum ta haifar da bugu mafi saurin kisa ga ikonta da girmanta. Wannan ne ya haifar da magabcin tsarin paparuma mafi himma, mafi nasara kuma. BJ 126.1
Hafsan da aka nada ya gudanar da jarin gafaran nan a Jamus, mai suna Tetzel, an rigaya an hukumta shi sabo da laifuka ga jama’a da kuma laifuka ga dokar Allah; amma bayan ya tsere ma horo don laifukansa, sai aka dauke shi aikin ci gaba da munanan laifofin nan na paparuma. Ba kunya ya dinga maimaita karyan, yana ba da labarun karya domin a rudi jahilai masu saukin rudi, masu camfi kuma. Da suna da maganar Allah da ba a rude su hakanan ba. Domin a rike su kalkashin ikon paparuma ne, domin a kara iko da wadatar shugabanci kansu ne aka hana su Littafin. BJ 126.2
Yayin da Tetzel ya shiga garin, wani masinja yakan wuce gabansa yana sanarwa: “Alherin Allah da Uba Mai-trsarki yana gaban gidanku.” Mutane kuma suka marabci makaryacin nan kamar Shi Allah kan Sa ne Ya sauko wurinsu daga sama. Aka kafa wannan ciniki a cikin ekklesiya, Tetzel kuma yakan hau bagadi ya sanar cewa gafaran da ake sayarwa it ace kyauta mafi girma daga Allah. Ya ce ta wurin takardun nan nasa na shaidar gafara dukan zunuban da mai saye zai so ya sake aikatawa za a gafarta masa, kuma wai ba ya bukatar tuba ma. Fiye da wannan, ya tabbatar ma masu jinsa cewa gafara tana da ikon ceto ba kan masu rai kadai ba, har da matattu; cewa da zaran kurdin ya taba gindin tasar sa, ruhun wanda aka ba da kurdin a madadinsa zai tsere daga purgatory ya je sama. BJ 126.3
Sa’an da Simon Magus ya sayi ikon yin al’ajibai daga wurin manzanin, BItrus ya amsa masa: “Azurfarka ta lalace da kai, tun da ka aza a ran ka za ka sami kyautar Allah da kurdi.” Ayuka 8:20. Amma dubbai suka karbi tayin Tetzel da suari ma. Zinariya da azurfa suka rika kwararowa cikin baitulmalinsa. Ceto da za a iya saye da kurdi ya fi saukin samu da wanda ke bukatar tuba da bangaskiya da kokarin kin zunubi da yin nasara da shi kuma cikin natsuwa. BJ 127.1
Masana a cikin ekklesiyar Rum sun yi jayayya da koyaswan nan na sayar da gafara, kuma akwai da yawa da basu yarda da rudin nan da ya saba ma hankali da ruya ba. Ba ma’aikacin ekklesiya da ya isa ya yi jayayya da mugun cinikin nan, amma zukatan mutane sun far damuwa, da yawa kuma suka fara tambaya ko Allah ba zai iya bin wata hanya don tsarkake ekklesiyar Sa ba? BJ 127.2
Luther, ko da shi ke dan tsarin paparuma ne, na kwarai kuwa, ya cika da kyamar sabon da masu sayar da gafaran nan suka dinga yi. Da yawa daga majami’an da yake sujada sun sayi takardun shaidar gafaran, kuma suka fara zuwa wurin paston su suna furta zunuban su, suna kuma zaton zai yafe masu, ba don sun tuba ba, amma domin sun sayi gafara. Luther ya hana yafewar, ya kuma gargade su cewa in ba sun tuba suka sake rayuwarsu ba, za su mutu cikin zunuban su. Cikin mamaki suka koma wajen Tetzel da kukan cewa mai-karban furcin zunubansu ya ki takardun shaidar gafaran da shi Tetzel ya sayar masu; wadansu ma suka ce a mayar masu da kurdinsu. Tetzel ya fusata sosai. Da la’ana iri iri, mafi muni, ya sa aka kunna wuta a wuraren taron jama’a, sa’an nan ya sanar da cewa shi “ya karbi umurnin daga paparuma cewa ya kone dukan masu-ridda da suka yi jayayya da takardun gafararsa mai-tsarki.” BJ 127.3
Luther yanzu kuma ya shiga aikinsa na jarumin gaskiya, ba tsoro. Akan ji muryarsa daga bagadi yana kashedi da gaske. Ya bayana ma mutane munin zunubi, ya kuma koya masu cewa ba zai yiwu ma mutm, ta wurin ayukansa, ya rage munin laifin zunubinsa ko kuma ya kauce ma horon ba. Ba abin da zai iya ceton mai-zunubi sai tuba ga Allah da bangaskiya ga Kristi. Ba za a iya sayen alherin Allah ba; kyauta ce. Ya shawarci mutanen kada su sayi takardun shaidar sayen gafaran nan, amma cikin bangaskiya su dubi Mai-fansa da aka giciye. Ya ba da labarin kokarinsa a banza don samun ceto ta wurin kaskantar da kai da wahalar da kai, ya kuma tabbatar ma masu jinsa cewa ta wurin rabuwa da kansa, da kuma ba da gaskiya ga Kristi ne ya sami salama da farin ciki. BJ 128.1
Yayin da Tetzel ya ci gaba da cinikinsa, da rashin imaninsa, Luther ya shirya jayayya mafi dacewa game da kurkuran nan. Nan da nan dama ta samu. Majami’ar Wittenburg ta mallaki sifofi da yawa da akan nuna ma mutane a wadansu ranaku masu tsarki, sa’an nan akan ba da cikakkiyar yafewar zunubi ga dukan wadan da suka zo majami’a ranan, suka kuma furta zunubansu. Don haka, wadannan ranakun mutane da yawa sukan taru a wurin. Daya daga cikin muhimman ranakun nan, watau bukin Dukan Tsarkaka ta kusato. Kwana guda kafin ranar bukin, Luther, cikin jerin mutanen da ke tafiya zuwa majami’ar, ya manna wata walka kunshe da dalilai guda tasa’in da biyar da suka nuna kurakuran koyaswar cinikin gafarar. Ya bayana cewa yana shirye ya kare dalilan nan washegari a jami’a, idan akwai wadanda ke shirye su kushe su. BJ 128.2
Ra’ayoyin nasa sun ja hankalin duniya. An karanta su akai akai ta kowace fuska. An zaburar da jami’a da birnin kuma kwarai. Ra’ayoyin nan sun nuna cewa ba a taba ba paparuma, ko kuma wani mutum ma, ikon gafarta zunubi ko yafe horonsa ba. Tsarin gaba daya rudi ne, dabarar Shaitan don hallaka rayukan wadanda suka gaskata rudinsa. An kuma nuna a fili cewa bisharar Kristi ce tamani mafi-girma ga ekklesiya, kuma alherin Allah da aka bayana a ciki kyauta ce ga dukan mai-bidar ta tawurin tuba da bangaskiya. BJ 129.1
Ra’ayoyin Luther sun bukaci mahawara, amma ba wanda ya isa ya ta da mahawarar. Ababan da ya fada sun yadu ko ina a Jamus cikin kwanaki kadan, kuma cikin makoni kadan suka kai duk inda Kirista suke. Manyan Romawa da suka gane suka kuma yi bakin cikin zunubin da ya mamaye ekklesiyar, amma ba su san yadda za su tsayar da shi ba, sun karanta ra’ayoyin Luther da murna sosai, suka gane muryar Allah a ciki. Sun gane cewa Allah Ya sa hannu domin Ya tsayar da ci gaban zunubin da ke bulbulowa daga Rum. ‘Ya’yan sarakuna da Majistarori suka yi murna a boye cewa za a tsayar da tsarin nan da ya hana daukaka kara daga hukumcin Rum. BJ 129.2
Amma jama’a masu kaunar zunubi sun tsorata domin an share dabarun da suka kwantar masu da rai. Ma’aikatan ekklesiyar da aka hana su goyon bayan zunubi suka kuma ga hanyar samun kurdin su za ta rufu, suka fusata, suka kuma nace za su ci gaba da ayukan su. Luther ya gamu da masu zargi da sun rigaya sun fusata. Wadansu suka ce ya yi gaggawa da rashin tunani. Wadansu suka zarge shi da ganganci, cewa ba Allah ne Ya ba shi umurni ba, amma girman rai da zafin kai ne suka tura shi. Ya amsa da cewa: “Wane ne bai san cewa duk wanda ya kawo sabon ra’ayi akan gan shi kamar mai-girman kai ne, mai-neman ta da fitina ba?... Don me aka kashe Kristi da dukan adilai da aka kashe? Domin an gan su kamar masu rena hikimar zamaninsu ne, kuma domin sun fito da sabobin ra’ayoyi ba tare da neman shawarar masanan tsofofin ra’ayoyin ba.” BJ 129.3
Ya kuma ce: “Duk abin da ni ke yi zan yi ne, ba ta wurin hikimar mutane ba, amma ta wurin bishewar Allah. Idan aikin na Allah ne, wa zai tsayar da shi? Idan ba na Allah ba ne, wa zai ci gaba da shi? Ba nufi na ba, ko nasu ko namu; amma nufinka, ya Uba Mai-tsarki, wanda ke cikin sama.” BJ 130.1
Ko da shi ke Ruhun Allah ne ya motsa Luther ya far aikinsa,ya gamu da tankiya sosai. Zarge zargen magabtansa, da karyarsu game da manufofinsa, da karyarsu game da halinsa da burinsa, sun abko masa kamar ambaliya; sun kuwa shafi aikinsa. Ya dauka cewa shugabanni na makaranta da na ekklesiya za su hada kai da shi don samun canji. Kalmomin karfafawa daga manyan mutane sun ba shi bege da murna. Sai ya ga kamar rana ta haskaka ma ekklesiya. Amma kafafawa ta koma reni da zargi. Manya da yawa na ekklesiya da na kasa sun gamsu da ra’ayoyinsa; amma suka ga karban koyaswoyin zai kunshi manyan canje canje. Wayar da kan mutane da kuma canja su zai rage ikon Rum, ya tsayar da dubban kurdade da ke shigowa baitulmalinta yanzu, ta haka kuma zai rage bushasha da almubazzaarancin shugabannin tsarin paparuma. Ban da haka, koya ma mutane yin tunani da aikatawa kamar masu hankali, suna duban Kristi kadai don cetonsu, zai hambarar da gadon sarautan paparuma, ya kuma lalata nasu ikon. Don haka suka ki sanin da Allah Ya ba su, suka kuma jera kansu don jayayya da Kristi da gaskiyar kuma a wurin yin jayayya da mutumin da ya aiko domin wayar da kansu. BJ 130.2
Luther ya raunana sa’an da ya dubi kansa , mutum daya sabain ikoki mafi girma na duniya. Wani lokaci yakan yi shakka ko da gaske Allah ne Ya bishe shi ya ja daga da ikon ekklesiya. Ya rubuta cewa: “Wane ne ni in ja da martabar paparuma, wanda a gabansa ...sarakunan duniya da duniyar kan ta ke rawan jiki?... Ba wanda zai iya sanin wahalan da zuciya ta ta sha cikin shekaru biyu na farkon nan, da kuma irin yankan kauna da na shiga.” Amma ba a bar shi ya karai gaba daya ba. Sa’an da ya rasa goyon bayan mutane, yakan dubi Allah kadai, ya gane kuma cewa zai iya dogara ga hannun nan Mai-cikaken iko. BJ 131.1
Luther ya rubuta ma wani abokin Canjin cewa: “Ba za mu iya fahimtar Littafin ta wurin nazari ko basira ba. Wajibi ne ka fara da addu’a. Ka roki Ubangijji cikin jinkansa Ya ba ka ganewar gaskiyar maganarsa. Ba wani mai-fasarar maganar Allah kamar wanda Ya wallafa ta, gama Shi da kan Sa Ya ce, ‘Allah zai koya ma dukansu’ kada ka yi begen komi daga aikinka, daga ganewar kanka: ka dogara ga Allah kadai, da kuma tasirin Ruhunsa. Ka gaskata wannan da shi ke maganar wanda ya gogu ne.” Wannan darasi ne mai muhummanci kwarai ga wadanda ke ji cewa Allah Ya kiraye su domin su bayyana ma wadansu muhimman gaskiya na wannan zamani. Gaskiyan nan za su ta da magabtakan Shaitan da masu kaunar tatsuniyoyin da ya kirkiro. Cikin sabani da ikokin mugunta akwai bukatar wani abu fiye da karfin basira da hikimar mutum. BJ 131.2
Yayin da magabta suka dogara ga al’ada ko kuma furcin paparuma ko ikonsa, Luther yakan nuna masu Littafin ne kawai. Nan ne akwai zantattukan da ba za su iya kushewa ba, don haka bayin nan na camfi suka bidi jininsa, yadda Yahudawa suka bidi jinin Kristi. Suka ce: “Mai-ridda ne. Babban cin amana ne a bar kazamin mai-riddan nan da rai har tsawon sa’a guda nan gaba. Bari a kafa dakalin da za a rataya shi maza maza!” Amma fushinsu bai cinye Luther ba. Allah Yana da aiki dominsa, aka kuwa aiko malaikun sama domin su tsare shi. Amma da yawa da suka karbi hasken daga wurin Luther sun gamu da fushin Shaitan, ba tsoro suka fuskanci azaba da mutuwa. BJ 131.3
Koyaswoyin Luther sun jawo hankulan masu tunani ko ina a Jamus. Daga wa’azin sa da rubuce rubucensa haske ya rika fitowa yana haskaka dubban mutane. Bangaskiya mai-rai ya fara daukan wurin matacen tsarin al’adun nan da ya rike ekklesiya da dadewa. Mutane suka fara shakkar camfe camfen ekklesiyar Rum. Shingen wariya sun fara watsewa. Maganar Allah da Luther ya rika gwada kowace koyaswa da ita, kamar takobi ne mai-kaifi biyu; yana yanka hanyar sa zuwa zukatan mutanen. Ko ina marmarin ci gaban ruhaniya ya fara tasowa. Ko in aka sami yunwa da kishin adalci irin da ba a taba gani ba da dadewa. Idanun mutane da aka dade ana nuna masu al’adun mutane da matsakanta na duniya, yanzu kuma sun fara juyawa cikin tuba da bangaskiya zuwa wurin Kristi, Shi wanda aka giciye. BJ 132.1
Jawowar hankalin nan ya kara tsoratar da mahukumatan tsarin paparuma. Luther ya sami sammaci cewa ya je Rum don amsa tuhumar ridda. Umurnin ya cika abokansa da tsoro. Sun san hadarin da ke kansa a birnin nan da ya riga ya shawu da jinin amintattun Yesu. Suka ki yarda da tafiyarsa Rum, suka ce a tuhume shi a Jamus. BJ 132.2
Daga bisani an yarda da wannan shirin, aka zabi jakadan paparuma ya ji tuhumar. Cikin umurnin da paparuma ya ba jakadan, an ce an rigaya an sanar da cewa Luther mai-ridda ne. Don haka aka umurci jakadan ya zarga ya kuma hukumta, ban da jinkiri. Idan ya nace, har kuma jakadan ya kasa kama jikin Luther din, an ba shi dama “ya hana shi zuwa ko ina a Jamus; ya kora, ya la’anta, ya kuma ware dukan wadanda suka yarda da shi.” Bayan haka, paparuma ya umurci jakadan nasa, domin dai a batar da annoban riddan, ya ware duka, komi girman su a ekklesiya ko a kasar, ban da sarkin, wadandan duk suka ki kama Luther da masu binsa, su tura su ga ramuwar Rum. BJ 132.3
Nan ne aka bayana ainihin ruhun tsarin paparuma. Babu ko alamar Kiristanci ko kaidar adalci ma a cikin takardar umurnin. Luther yana da nisa sosai daga Rum; bai sami dammar bayana matsayinsa ba, duk da haka kafin a bincika tuhumarsa, an hukumta cewa shi mai-ridda ne, a rana dayan kuma aka tsauta masa, aka tuhume shi, aka hukumta shi, aka kuma iske shi da laifi; kuma mai-karyan kiran kansa uba mai-tsarki, makadaici, madaukaki, mai-iko, mara-kuskre, a kasa ko ekklesiya, shi ne ya yi haka. BJ 133.1
A awannan lokaci da Luther ya bukaci goyon baya da shawarar abokan gaskiya, Allah Ya aiko Melanchthon zuwa Wittenberg. Matashi ne mai-kamewa, hikimarsa da yawan iliminsa, da iya maganansa sun hadu da tsabtar halin sa da nagartarsa, suka jawo ma Melanchthon farin jini da ban girma. Kyaun baye bayensa bai fi halinsa na tawali’u karbuwa ba. Nan da nan ya zama almajirin bisharar, kuma abokin Luther mafi aminci da mai-goyon baya mafi tamani, tawali’unsa da hankalinsa da natsuwansa suka rika jan linzamin jaruntakar Luther da karfin halinsa. Haduwarsu cikin aikin ta kara ma Canjin karfi ta kuma karfafa Luther sosai. BJ 133.2
An zabi Augsburg ne inda za a yi shari’ar, Luther kuma ya kama hanya da kafa zuwa wurin. An ji masa tsoro sosai. An rigaya an yi barazana a fili cewa za a kama shi a kashe shi a hanya, kuma abokansa suka roke shi kada ya je. Har ma sun roke shi ya bar Augsburg na wani lokaci, ya nemi mafaka a wurin wadanda za su kare shi. Amma ya ki barin wurin da Allah Ya sa shi. Dole zai ci gaba da rikon gaskiya da aminci, komi hare haren da ke zuwa masa. Maganarsa it ace: “Ni kamar Irmiya ne, mutum mai-fama da kuma yawan hamayya; amma yayin da barazanan nan ke karuwa, haka murna ta take yawaita.... Sun rigaya sun bata daraja ta da suna na. Abu daya kawai ya rage; jikin nan nawa mara-martaba: su dauke shi; ta haka za su takaita rayuwa ta, na tsawon sa’o’i kalilan. Amma ruhu na kam, ba za su iya daukewa ba. Duk wanda ke so ya yi shelar maganar Allah ga duniya, dole ya yi tsammanin zai iya mutuwa ko wane lokaci.” BJ 133.3
Labarin isowar Luther Augsburg ya gamsar da jakadan paparuma sosai. Fitinannen mai-riddan nan da ya ja hankalin dukan duniya ya shigo kalkashin ikon Rum, jakadan kuma ya kudurta cewa ba zai tsira ba. Luther bai samo ma kansa kariya ba. Abokan shi sun gargade shi kada ya halarci wurin shari’an ba tare da tsaro ba, su kansu kuma suka so su samo masa tsaron daga wurin sarki. Jakadan ya so ya tilasta Luther ya janye ra’ayinsa, ko kuma ya sa a a kai shi Rum, domin a yi masa yadda aka yi ma Huss da Jerome. Sabo da haka ta wurin wakilan sa, ya yi kokrain sa Luther ya bayana ba tare da kariya ba, domin ya yi abin da ya ga dama da shi. Luther kuwa ya ki yin hakan. Sai da ya karbi takardar shaidar kariyar sarki kafin ya bayana a gaban jakadan paparuman. BJ 134.1
Bisa ga al’adarsu, Romawan sun so su ja hankalin Luther ta wurin nuna kamanin tawali’u. Jakadan a cikin hirarsu, ya nuna kamanin abota sosai; amma ya bukaci Luther ya yarda da ikon ekklesiya kawai ba hamayya ko tambaya. Bai san halin mutumin da yake magana da shi ba. Cikin amsarsa Luther ya nuna ban girman sa ga ekklesiya, burin sa na tabbatar da gaskiya, shirinsa don amsa kowace tambaya game da ababan da ya koyar, ya kuma mika koyaswoyinsa ga binciken wadansu fitattun jami’o’i. Amma kuma ya ki yarda da bukatar jakadan cewa ya janye ba tare da ya nuna masa kuskurensa ba. BJ 134.2
Martaninsa kawai ita ce: “Ka janye, ka janye!” Luther ya nuna cewa matakin da ya dauka daidai yake da Littafi ya kuma nace cewa ba zai musunci gaskiya ba. Sa’an da jakadan ya kasa amsa maganar Luther, sai ya dinga tura masa ashar, da ba’a, da fadanci, yana surkawa da wadansu maganganu daga al’ada da furcin ubanin ekklesiya, amma bai ba Luther damar yin magana kuma ba. Da ya ga taron ba zai haifar da komi ba, a karshe Luther ya sami iznin mika amsarsa a rubuce. BJ 135.1
Ya rubuta ma wani abokin sa cewa: “Ta wurin yin haka, wulakantace ya kan sami riba kashi biyu: na daya, watakila za a ba wadansu abin da aka rubuta din su duba; na biyu kuma mutum yakan sami damar taba lamirin wani azalumi mai-fadin rai da yawan magana, wanda da zai fi karfin ka da maganganu irin na manya kawai.” BJ 135.2
Ya gabatar da gajeruwar bayani a fili, mai-karfi kuma, na ra’ayoyinsa cike da nassosin Littafin da suka goyi bayan ra’ayoyin. Bayan ya karanta takardar bayanin, sai ya mika ma jakadan, shi kuwa ya jefa ta a gefe da reni, yana cewa tarin kalmomin banza ne kawai da ba su dace ba. Luther kuwa ya fusata, sai ya ba shi amsa daga al’adu da koyaswoyin ekklesiya, ya kuwa nuna kurakuran jakadan. BJ 135.3
Sa’an da jakadan ya ga ba zai iya amsa koyaswar Luther ba, ya kasa kame kansa, cikin fushi kuma ya ta da murya ya ce: “Ka janye! ko kuma in aika da kai Rum, inda za ka bayana a gaban masu shari’an da aka zaba su yi shari’arka. Zan ware ka da dukan magoya bayanka, da dukan wadanda daga baya za su karbe ka, zan kuma cire su daga ekklesiya.” A karshe cikin fushi ya ce: “Ka tuba, ko kuma kada ka dawo kuma.” BJ 135.4
Nan da nan Luther ya fice tare da abokansa, sa’anda ya nuna cewa ba zai taba janyewa ba. Ba abin da jakadan ya nufa kenan ba. Ya rigaya ya rudi kansa cewa ta wurin anfani da karfi zai razana Luther ya yi biyayya, yanzu kuwa da aka bar shi tare da masu goyon bayansa, ya dube su daya bayan daya, yana mamakin kasawar dabarunsa. BJ 136.1
Kokarin Luther a wannan karo ya haifar da sakamako masu kyau. Tarin jama’a da suke wurin sun sami zarafin gwada mutum biyu din nan don kansu, ko wane irin ruhu ne suka nuna, da kuma kafri da gaskiyar matsayin da suka dauka. Bambancin ya yi yawa! Luther mai-saukin kai da tawali’u da karfi, ya tsaya cikin karfin Allah, a gefen gaskiya; wakilin paparuma kuwa, ga ji cewa shi wani abu ne, ga son duniya, ga alfarma, ga rashin kima, ba shi kuma da goyon baya daga Littafin, amma ya yi ta ihu da naciya cewa: “Ka janye ko kuwa a aika da kai Rum domin a hore ka.” BJ 136.2
Duk da cewa Luther ya rigaya ya sami kariya, yan ekklesiyar Rum din nan sun so su kama shi su sa shi a kurkuku. Abokansa suka ce masa, tun da zamansa a Augsburg din ba anfani kuma, gara kawai ya koma Wittenberg maza maza, kuma a yi hankali sosai kada a gane abin da yake shirin yi. Sabo da haka ya bar Augsburg kafin wayewan gari, a kan doki, daga shi sai mai-nuna masa hanya wanda majistare ya ba shi. Da rashin tabbachi, a boye ya wuce ta titunan birnin cikin duhu. Magabta masu tsaro da zalunci suna shirin hallaka shi. Ko zai tsere ma tarkokin da aka shirya masa? Wannan lokaci ne na fargaba da addu’a sosai. Ya kai wata karamar kofa a ganuwar birnin. Aka bude masa, tare da mai-bishe shi, ba matsala. Da zaran sun fita sai suka kara hanzari, kuma kafin jakadan ya san cewa Luther ya gudu, ya rigaya ya wuce inda masu tsananta masa za su iya kama shi. An ka da Shaitan da ‘yan sakonsa. Mutumin da suka zata yana kalkashin ikonsu ya rigaya ya tafi, ya tsere kamar tsuntsu daga tarkon mai-farauta. BJ 136.3
Sa’an da jakadan ya sami labarin tserewar Luther, ya cika da mamaki da fushi kuma. Ya dauka zai sami lada mai yawa sabo da hikimar sa da naciyarsa wajen ladabtar da mai- damun ekklesiyan nan; amma begen sa bai yiwu ba. Ya bayana fushinsa cikin wasikarsa zuwa ga Fredrick mai-zaben Saxony, inda ya bukace shi ya tura Luther zuwa Rum, ko kuma ya kore shi daga Saxony. BJ 137.1
Don kare kansa, Luther ya bidi jakadan ko kuma paparuma ya nuna masa kuskurensa daga Littafi, ya kuma yi alkawalin rabuwa da koyaswoyin sa idan har an nuna cewa sun saba ma maganar Allah. Ya kuma gode ma Allah cewa har shi ma an ga ya cancanta ya wahala sabo da imani. BJ 137.2
A lokacin mai-zaben bai rigaya ya san koyaswoyin da aka canja ba, amma ya yi sha’awar gaskiya da karfi da saukin maganar Luther; kuma in ba an nuna kuskuren Luther ba, Fredrick ya kudurta zai zama mai-kare shi. Cikin amsar sa ga wasikar jakadan, ya rubuta cewa: “Da shi ke Likita Martin ya bayana gabanka a Augsburg, ya kamata ka gamsu. Ban zata za ka yi kokarin sa shi ya janye ba, sai bayan ka nuna masa kuskurensa. Ba wani masani a yankin mu da ya fada mani cewa koyaswar Luther ta saba ma imani, ko Kiristanci, ko kuma ridda ce ba.’ Dan sarkin kuma ya ki tura Luther zuwa Rum, ko kuma shi kore shi daga kasarsa.” BJ 137.3
Mai-zaben ya ga cewa akwai lalacewar halayyan kirki a kasar. An bukaci babban aikin canji mai-girma. Tsarin nan mai-tsada da wuyan ganewa kuma, na horon laifi, ba zai zama da anfani ba idan mutane sun yi biyayya ga umurnin Allah da bukatun lamirin da ke da sani. Ya ga cewa Luther yana kokari ne ya cim ma wannan manufar, ya kuma yi farin ciki a boye cewa wata koyaswa mafi kyau tana shigowa ekklesiya. BJ 137.4
Ya ga kuma a matsayin sa na shehun mallamin jami’a Luther yana nasara sosai. Shekara guda ce kadai ta wuce bayan ya manna ra’ayoyinsa a babban majami’an nan , amma yawan masu zuwa ekklesiyar Bukin Dukan Tsarkakan nan a Rum ya ragu sosai. Rum ta rasa masu sujada, da baiko kuma, amma wata kungiya ta dauki wurinsu, masu zuwa Wittenberg kenan, ba don yin sha’awar sifofin ta ba, amma dalibai masu neman sani. Rubuce rubucen Luther sun ta da sabon marmarin Littafin, ko ina kuma ba daga Jamus kadai ba, amma daga wadansu kasashe ma dalibai suka rika tururuwa. Samarin da farkon zuwan su Wittenberg kenan suka “daga hannuwan su sama, suka yabi Allah da Ya sa hasken gaskiya ya haskaka daga birnin nan, kamar daga Sihiyona a zamanun da, daga inda kuma ya yadu zuwa kasashe mafi nisa.” BJ 138.1
Luther a lokacin nan bai gama tuba daga kurakuran tsarin paparuma ba. Amma yayin da ya gwada Littafi da dokokin paparuma da kundin tsarin mulkinsu, ya cika da mamaki. Ya ce: “Ina karanta dokokinsu paparuma, kuma...ban san ko paparuma ne .............................. din nan da kansa ba ko mazon Kristi, an bata sunan Kristi aka kuma giciye Shi a cikin su.” Duk da haka a wannan lokacin Luther mai-goyon bayan Ekklesiyar rum ne, kuma ba ya tunanin cewa zai taba rabuwa da ita. BJ 138.2
Rubuce rubucen Luther da koyaswarsa sun ci gaba da yaduwa cikin Kirista. Aikin ya yadu har Switzerland da Holland. Kofen rubuce rubucensa suka kai Spain. A Ingila an karbi koyaswoyinsa kamar maganar rai. Maganar ta kai Belgium da Italiya ma. Dubbai sun rika falka daga barcinsu mai-kama da mutuwa, zuwa murna da begen rayuwa ta bangaskiya. BJ 138.3
Rum ta kara damuwa game da hare haren Luther, kuma wadasu masu matukar gaba da shi, har da likitoci a jami’o’in Katolika, suka ce duk wanda zai kashe dan zuhudu mai-tawayen nan bai yi zunubi ba. Wata rana wani bako da ya boye karamar bindiga a kuntun sa ya je wurin Luther, ya tambaye shi don me yake tafiya shi kadai hakanan. Sai Luther ya amsa masa: “Ni ina hannun Allah ne. Shi ne karfi na da garkuwa ta. Mene ne mutum zai iya yi mani?” Da bakon ya ji wannan, sai jikin shi ya yi sanyi, ya gudu kamar yana gudun malaikun sama. BJ 139.1
Rum ta nace sai ta hallaka Luther; amma Allah Shi ne kariyarsa. An ji koyaswoyinsa ko ina, “a kauyuka da gidajen ma’aikatan ekklesiya...a gidajen fadawa, a jami’o’i, da kuma gidajen sarakuna.” Kuma manyan mutane suka rika tasowa ko ta ina suna goyon bayan kokarinsa. BJ 139.2
Wajen wannan lokacin ne Luther, bayan ya karanta rubuce rubucen Huss, ya gane cewa babban gaskiyan nan na kubutarwa ta wurin bangaskiya wadda shi kansa ke kokarin koyarwa, Huss ma ya yarda da shi. Luther ya ce: “Ashe dukan mu, Bulus da Augustine da ni, almajiran Huss, ne amma ba mu sani ba!” ya ce: “Allah zai kama duniya da laifin cewa an yi mata wa’azin gaskiya shekaru dari da suka wuce amma aka kona gaskiyar!” BJ 139.3
Cikin wani roko ga sarkin Jamus da fadawansa a madadin Canjin Kiristanci, Luther ya rubuta game da paparuma cewa: “Abin ban kyama ne a ga mutumin da ke kiran kansa wakilin Kristi yana nuna girma da kyau na ban mamaki wanda babu sarkin da ke da irinsa, kamanin Yesu matalauci ko Bitrus mai-tawali’u kenan? In ji su wai shi ne Ubangijin duniya! Amma Kristi, wanda shi ya ce yana wakilta Ya ce, ‘Mulki na ba na wannan duniya ba ne. Ko mulkin wakili zai iya zarce na mai-gidansa?” BJ 139.4
Game da jami’o’in, ya rubuta cewa: “Ina tsoro watakila jami’o’in za su zama kofofin lahira fa. In ba sun yi kokarin fassara Littafi da kyau, suna kuma zana shi cikin zukatan matasa ba. Ban shawarci wani ya sa yaran sa inda Littafi ba shi da fifiko ba. Kowace makarantar da ba a binciken maganar Allah lallai za ta lalace.” BJ 139.5
Nan da nan aka kai sakon nan ko ina a Jumus, ya kuma yi tasiri sosai a kan mutane. Kasar gaba daya ta motsu, jama’a da yawa suka tashi suka goyi bayan canji. Magabtan Luther cike da neman ramuwa suka roki paparuma shi dauki matakai na karshe a kan Luther. Aka umurta cewa nan da nan a hana koyaswoyinsa. Aka kuma ba da masu goyon bayansa kwana shida su janye ko kuma a ware su. BJ 140.1
Wannan ya zama babban damuwa ga Canjin. Da dadewa hukumcin warewa na Rum yana razana sarakuna; ya cika manyan kasashe da kaito da hallaka kuma. Wadanda aka ware su din akan rika kyamarsu da tsoronsu; akan raba su daga yin ma’amala da yan-uwa, a mai da su masu ketare doka da ya kamata a yi farautar su a kawar da s u. Luther ya san guguwar da ke fuskantar sa; amma ya nace, ya dogara ga Kristi shi zama taimakon sa da garkuwarsa. Da bangaskiya tare da karfin hali ya rubuta cewa: “Abin da ya kusa faruwa ban sani ba,...Bari naushin ya bugi inda ya ga dama, bana tsoro. Ko ganye ma ba ya faduwa sai da yardar Ubanmu. Ai kuwa zai fi lura da mu! Mutuwa don maganar Allah ba komai ba ne, tun da Kalman da ya zama nama Shi ma ya mutu. Idan mun mutu tare da Shi za mu rayu tare da Shi; kuma idan mun dandana abin da shi Ya dandana kafin mu, za mu kasance inda Shi yake mu kuma zauna tare da Shi har abada.” BJ 140.2
Sa’an da umurnin paparuma ya kai wurin Luther, ya ce: “Na rena shi, na kuma yake shi, cewa rashin imani ne, karya ne kuma, ... Kristi da kansa ne ake hukumtawa a wurin.... ina farin ciki in sha wahalolin nan sabo da dalili mafi kyau. Na rigaya na fara jin karin yanci ma a cikin zuciyata; da shi ke yanzu na san cewa paparuma ne magabcin Kristi, kuma gadon sarautarsa na Shaitan kansa ne.” BJ 140.3
Duk da haka umurnin Rum din ya yi tasiri, kurkuku, azaba da takobi makaman ta na tilasta biyayya kenan. Marasa karfin zuciya da masu camfi suka yi rawan jiki game da dokan nan na paparuma; kuma ko da shi ke ana tausaya ma Luther, da yawa sun ce ba za su sa rai cikin kasada wai sabo da canji ba. Bisa dukan alamu dai, aikin Luther ya kusan karewa. BJ 141.1
Amma Luther bai ji tsoro ba dai. Rum ta rika tsitsine masa, duniya kuma ta na kallo, da tabbaci cewa Luther zai hallaka, ko kuma a tilasta shi ya karai. Amma da karfin gaske, ya mayar ma Rum da hukumcin nata a fili, kuma ya bayana aniyarsa ta rabuwa da Rum din har abada. A gaban taron dalibai, likitoci da ‘yan kasa, Luther ya kona umurninn paparuma, da dokokin ekklesiyar, da wadansu rubuce rubuce da suka karfafa ikon paparuman. Ya ce: “Magabta na, ta wurin kona litattafai na, sun iya bata gaskiyan da ke cikin tunanin mutane, suka hallaka rayukansu kuma; dalilin kenan ni ma na rama ta wurin kona littattafansu. Babbar kokawa ta fara kenan. Kafin yanzu ina wasa ne kawai da papruma. Na fara aikin nan cikin sunan Allah ne; za a karasa shi ban da ni, da girman sunan Allah kuma.” BJ 141.2
Ga zarge zargen magabtansa da suka rika yi masa ba’a game da rashin karfin famar tasa, Luther ya amsa: “Wa ya san ko Allah bai zabe ni, ya kira ni ba, kuma idan bai kamata su ji tsoron wannan ba, ta wurin rena ni su na rena Allah da kansa ne? Musa ne kadai lokacin Fitowa daga Masar; Iliya shi kadai ne a zamanin mulkin sarki Ahab; Ishaya shi kadai ne a Urushalima; Ezekiel ne kadai a Babila;... Allah bai taba zaben babban priest ko wani mai-martaba shi zama annabinsa ba; amma ya zabi mutanen da aka rena ne, har da Amos dan kiwo ma. A kowace sara tsarkaka sukan tsauta ma manya, da sarakuna da yarimai, da preistoci da masu-hikima, a bakin ransu.... Ban ce ni annabi ne ba; amma ina cewa ne ya kamata su ji tsoro domin ni kadai ne, su kuma suna da yawa. Na tabbatar da wannan, cewa maganar Allah tana tare da ni, kuma ba ta tare da su.” BJ 141.3
Amma da wuyan gaske ne Luther ya dauki matakin karshe na rabuwa da ekklesiyar. Wajen wannan lokacin ne ya rubuta cewa: “Kowace rana ina kara jin wahalar rabuwa da tarbiyyan da mutum ya koya a kuruciyarsa. Ya zafe ni sosai, ko da shi ke ina da goyan bayan Littafi, cewa ni kadai in yi jayayya da paparuma, in kuma bayana cewa shi ne magabcin Kristi. Wadanne irin damuwoyi ne zuciyata ba ta shiga ba? Sau nawa ina ma kaina tamabayan nan da tsarin paparuma sun cika yi ma kansu, cewa: ‘Kai kadai ne mai-hikima? Watau dukan sauran mutane suna kuskure kenan? Yaya zai kasance idan ya zamana cewa kai ne mai-kuskuren, kuma kana jawo rayuka da yawa cikin kuskuren ka, har su kuma su hallaka har abada?’ Haka na dinga fada da kai na da Shaitan kuma, har sai da Kristi, ta wurin maganarsa mara kuskure, ya karfafa zuciya ta sabanin shakkun nan.” BJ 142.1
Paparuma ya rigaya ya yi ma Luther barazana zai ware shi idan ya ki janyewa, sai kuma aka cika barazanar. Sabon umurni ya fito da ya sanar da rabuwar Luther daga ekklesiyar Rum, yana cewa Luther la’antace ne tun sama, haka ma dukan wadanda suka karbi koyaswarsa, la’antattu ne an shiga ainihin fadan ke nan. BJ 142.2
Dukan wadanda Allah Ya ba su aikin gabatar da gaskiyar sa da ta je daidai da zamanin su sukan gamu da jayayya. A zamanin Luther akwai gaskiya ta lokacin. Gaskiya mai-muhimminci musamman ga wancan zamanin; akwai gaskiya ta yanzu domin ekklesiya ta yau. Shi wanda yake yin komi bisa ga nufinsa, Ya ga ya kamata ya sa mutane a yanayi dabam dabam, Ya kuma ba su aikin da ya dace da zamanin da su ke raye da kuma yanayin da Ya sa su a ciki. Idan suka ga muhimmincin hasken da Ya ba su, za a kara bude masu filayen gaskiya a gabansu. Amma yawanci yau ba su fi ‘yan tsarin paparuma da suka yi hamayya da Luther son gaskiya ba. Akwai son karban ra’ayoyi da al’adun mutane maimakon maganar Allah yau kamar sararakin da suka gabata. Kada masu-shelar gaskiya yau su zata za a karbe su da marmari fiye da ‘yan canji na da. Babban jayayya tsakanin gaskiya da kuskure, tsakanin Kristi da Shaitan, zai kara zafi har zuwa karshen tarihin duniya. BJ 142.3
Yesu Ya ce ma almairansa: “Da na duniya ne ku, da duniya ta yi kamnar nata; amma domin ku ba na duniya ba ne, amma ni na zabe ku daga chikin duniya, sabada wannan duniya tana kinku. Ku tuna da Magana wanda na fada maku, Bawa ba ya fin Ubangijinsa girma ba. Idan suka yi mani tsanani, su a yi maku tsanani kuma; idan suka kiyaye maganata, su a kiyaye taku kuma.” Yohanna 15:19, 20. Ta wancan gefen kuma Ubangijin mu Ya bayana a fili cewa: “Kaiton ku lokachin da dukan mutane za su yabe ku! gama hakanan ubanninsu suka yi ma makaryatan annabci.” Luka 6:26. Ruhun duniya yau bai fi na zamanin da can jituwa da Ruhun Kristi ba, kuma masu wa’azin maganar Allah da tsarkinta ba za a karbe su da amincewa da ta fi ta da din ba. Irin jayayyan zai iya canzawa, kiyayyar za ta zama a boye domin da zurfin wayo ake yin ta; amma magabtaka dayan ake yi, kuma za ta ci gaba har karshen lokaci. BJ 143.1