An shuka bishara a Bohemia tun karni na tara. An juya Littafin zuwa harshen mutanen, aka kuma rika yin sujada cikin harshen nasu. Amma yayin da ikon paparuma ke karuwa, haka kuma maganar Allah ta dinga shudewa. Gregory VII, wanda ya rigaya ya kuduri aniyar ladabtar da sarakuna, haka kuma ya shirya jefa mutane cikin bauta, kuma sabo da haka aka ba da dokar da ta hana sujada cikin jama’a da harshen Bohemianci. Paparuma ya ce: “Ya gamshi mai-cikakken iko a yi sujadarsa da yaren da ba a sani ba, yana cewa mugunta da bidi’a da yawa sun taso sabo da kin bin wannan kaidar.” Sabo da haka, Rum ta umurta cewa a kashe hasken maganar Allah a kuma kulle mutane cikin duhu. Amma Mai-sama Ya tanada wadansu hanyoyi dabam domin kiyaye ekklesiyarsa. Waldensiyawa da Albigensiyawa da yawa da zalunci ya kore su daga gidajensu a Faransa da Italiya, sun zo Bohemia. Ko da shike basu iya yin koyaswa a fili ba, sun rika yin aiki a boye. Ta haka aka rike ainihin imani daga karni zuwa karni. BJ 96.1
Kafin zamanin Huss akwai mutanen Bohemia da suka taso a fili suka nuna rashin ingancin ekklesiya da fasikancin mutanen. Aikin su ya ja hankulan mutane da yawa. Taron shuagbannin ekklesiya ya karu, aka kuma bude ma almajiran bishara zalunci. Sa’an da suka gudu zuwa dazuzuka da tsaunuka don yin sujada, sai sojoji suka rika farautar su, suka kashe da yawa cikin su. Bayan wani lokaci, sai aka umurta cewa a kone dukan wadanda suka bar sujada ta Rum, amma yayin da Kiristan suka ba da rayukan su, sun rika begen nasarar aikin su. Daya daga cikin masu-koyar da cewa ceto ta wurin Mai-ceton da aka giciye ne kadai, sa’an da yake mutuwa, ya ce: “Yanzu fushin magabtan gaskiya yana nasara kan mu, amma ba har abada ba ne, wani daga cikin talakawa zai taso; babu takobi ko iko; kuma ba za su iya nasara kan sa ba.” Zamanin Luther yana da nisa a lokacin; amma wani ya rigaya ya fara tashe, wanda shaidarsa game da Rum za ta motsa al’ummai. BJ 96.2
John Huss dan talaka ne, kuma cikin kurciyar sa mutuwar baban sa ta mayar da shi maraya. Uwar sa mai-ibada sosai ta ba ilimi da tsoron Allah muhimmanci matuka, ta so ta samo ma danta wannan gadon. Huss ya je makarantar lardin sune, daga nan ya je jami’ar Prague ta hanyar agaji. Maman shi ta je Prague din tare da shi; gwamruwan nan mai-talauci ba ta da guzuri mai-ma’ana da za ta ba danta, amma sa’an da suka kusa da babban birnin, ta durkusa a gefen saurayin nan mara uba, ta roka masa albarkar Uban su na sama. Da kadan uwan nan ta san yadda za a amsa addu’arta. BJ 97.1
A jami’ar, nan da nan Huss ya yi fice ta wurin kwazon sa da ci gaban sa maza maza. Hakanan, rayuwarsa mara-aibi, mai-saukin kai kuma da fara’arsa suka sa kowa ya girmama shi. Shi amintacen dan ekklesiyar Rum ne mai- kwazo wajen neman albarku na ruhaniya da ta ce tana bayarwa. Bayan ya gama jami’a, sai ya zama priest, ya kuma yi fice nan da nan, sai aka hada shi da fadar sarkin. An kuma mai da shi shehun mallami, daga baya kuma ya zama shugaban jami’ar, inda shi ya yi makarantar sa. Cikin shekaru kalilan, dalibin nan da ya yi makaranta ta wurin agaji ya zama mutumin da kasar sa ke alfahari da shi, sunan sa kuma ya zama sananne ko ina a Turai. BJ 97.2
Amma a wani fanni dabam ne Huss ya fara aikin canji. Shekaru da dama bayan ya zama prirest, aka sa ya zama mai-wa’azin ekklesiyar Baitalahmi. Wanda ya kafa wannan majami’an ya dinga koyar da cewa da harshe mutanen wurin ne za a rika koyar da Littafin. Duk da kin hakan da Rum ta yi, ba a dena kwata kwata ba a Bohemia. Amma akwai jahilci sosai game da Littafi, kuma laifuka mafi-muni suka mamaye mutane a kowane mataki. Huss ya kushe laifukan nan, yana anfani da maganar Allah domin tabbatar da kaidodin gaskiya da tsabta da shi yake koyarwa. BJ 98.1
Wani mutumin Prague, Jerome, wanda daga baya ya shaku da Huss sosai, ya dawo da rubuce rubucen Wycliffe daga Ingila. Sarauniyar Ingila da ta rungumi rubuce rubucen Wycliffe, gimbiyar Bohemia ce, kuma ta wurin tasirin ta ne aka baza rubuce rubucen dan Canjin ko ina a kasarta ta gado. Huss ya karanta su da maarmari; ya gaskata cewa mawallafin su Kirista ne na kwarai, kuma ya yarda da canje canjen da aka ce a yi. Kafin nan, Huss, ko da shike bai sani ba, ya rigaya ya shiga hanyar da za ta kai shi nesa daga Rum. BJ 98.2
Kusan lokacin nan, wadansu baki biyu suka shigo daga Ingila, masana ne da suka sami hasken, suka kuma zo domin su yi shelar sa a kasan nan mai-nisa. Da shike sun fara da zargin paparuma kai tsaye, nan da nan hukumomi suka hana su yin magana; amma da shike basu yarda su bar manufar su ba, suka canja dabarun su. Da shike kwararrun masu-zane da kuma wa’azi ne su, suka shiga anfani da kwarewar su. A wani wuri da kowa zai iya gani, suka zana hotuna biyu. Daya ya nuna shigowar Kristi Urushalima “Mai-tawali’u ne, yana tafiya bisa kan jaki” (Matta 21:5), almajiran Shi kuma suna bin Shi da kodaddun riguna, ba takalma. Daya hoton kuma ya nuna jerin gwanon paparuma; paparuma yana yafe da tufafinsa masu-tsada da rawaninsa, yana bisa kan doki mai-ado sosai, a gabansa ga masu busa kaho, manyan shugabannin ekklesiya cikin ado mai-tsada kuma suna bin sa. BJ 98.3
Wa’azin nan ya jawo hankulan koawane fanni na jama’a. Jama’a sun rika zuwa kallon zanen hotunan. Kowa ya gane sakon, da yawa kuma suka motsu da bambanci tsakanin tawali’u da saukin kan Kristi Mai-gidan, da fahariya da girman kan paparuma, mai-cewa wai shi bawan Kristi ne. An yi tashin hankali sosai a Prague, jima kadan kuma bakin suka ga cewa wajibi ne su tafi, sabo da tsaron lafiyar su. Amma ba a manta darasin da suka koyar ba. Hotunan sun sa Huss tunani sosai, suka kuma sa shi ya kara nazarin Littafi da rubuce rubucen Wycliffe da kyau. Ko da shike bai shirya karban canje canjen da Wycliffe ya shawarta ba, ya kara ganin ainihin halin paparuma, da Karin himma kuma ya kushe faharya da buri da lalacewar tsarin. BJ 99.1
Daga Bohemia hasken ya kai Jamus, domin tashe tashen hankula a Prague sun jawo sallamar daruruwan dalibai, ‘yan Jamus. Da yawa cikinsu sun rigaya sun sami Littafin su na fari daga wurin Huss, kuma daga dawowarsu suka yi shelar bisharar a kasarsu ta gado. BJ 99.2
An kai labarin aikin Prague din a Rum, nan da nan kuwa aka bukaci Huss ya bayana a gaban paparuma. Zuwan shi zai sa a ba da shi ga mutuwa tabbas. Sarikin Bohemia da sarauniyar, da jami’ar da masu-martaba da jami’an gwamnati, suka hada kai, suka roki paparuma cewa a bar Huss ya kasance a Bohemia, ya amsa zargin Rum ta wurin wakilinsa. Maimakon amincewa da wannan roko sai paparuma ya ci gaba, ya shar’anta Huss, ya iske shi da laifi, ya kuma ce Birnin Prague ma tana kalkashin horo, cewa ba za a yi hidimar ibada a cikinta ba kuma. BJ 99.3
A wancan zamanin, irin hukumcin nan yakan ta da hankula ko ina. Aka tsara hidimomin da aka hana, ta yadda za a razana mutanen nan da ke ganin paparuma kamar wakilin Allah kansa, mai-rike mabudan sama da lahira, da kuma ikon jawo horo, na jiki da na ruhaniya. Akan dauka cewa an rufe kofofin sama daga kowane wurin da aka kakaba masa wannan horon; kuma har lokacin da paparuma ya ga dama ya cire takunkumin, mutanen nan ba za su iya shiga wuraren salama ba. Alamar wannan masifa ita ce dakatar da dukan hidimomin addini. Akan rufe dukan majami’u; a kan daura aure a harabar masujadar ne. Matattun da akan hana bisonsu a wurin da aka kebe, akan bizne su babu hidimomin biso, a cikin lambatu ko a daji. Ta hakanan Rum ta yi kokarin mallakan lamirin mutane. BJ 100.1
Birnin Prague ya cika da tashin hankali. Jama’a da yawa suka zargi Huss cewa shi ne sanadin dukan matsalolin, suka kuma bidi cewa a ba da shi ga ramuwar Rum. Don kwantar da tarzumar, dan Canjin ya koma kauyen haihuwarsa. Ya rubuta ma abokansa da ya bari a Prague: “Idan na juye daga tsakanin ku, domin bin kwatancin Yesu Kristi ne, domin kada in ba masu-mugun nufi dama su ja ma kansu hukumci na har abada, kuma kada in zama ma masu-ibada sanadin bala’i da zalunci. Na janye kuma don gudun kada priestoci marasa imani su dade suna hana wa’azin maganar Allah a cikinku; amma ban yarda maku ku ki gaskiyar Allah wadda ni ke shirye in mutu sabo da shi ba.” Huss bai dena aikace aikacensa ba, amma ya dinga zagaya kauyukan kewaye yana wa’azi ga jama’a. Ta hakanan hanyoyin da paparuma ya bi don danne bisharar sun kara fadada bishra ne kuma. “Gama ba mu da iko mu yi komi sabanin gaskiya ba, sai domin gaskiya.” Korinthiyawa II, 13:8. BJ 100.2
“Zuciyar Huss a wannan lokacin aikin nasa ya cika da tankiya mai-tsanani. Ko da shike ekklesiya ta nemi rufe shi da hare harenta, bai rabu da ikonta ba. Har wancan lokacin dai, ekklesiyar Rum ce amaryar Kristi, paparuma kuma, wakilin Allah, mataimakinsa kuma. Abin da Huss ke yaki akai shi ne yin anfani da iko yadda bai kamata ba, ba kaidar kan ta ba. Wannan ya jawo sabani sosai tsakanin ganewarsa da lamirinsa. Idan ikon nan daidai ne, mara-kuskure kuma, yadda shi ya gaskata, ta yaya shi ya ga ya kamata ya ki yin biyayya gare ta? Ya ga cewa yin biyayya zunubi ne; amma don me yin biyayya ga ekklesiyar da ba ta kuskure zai kai ga haka? Damuwan da ya kasa magancewa kenan; shakkar da ta dinga zaluntar sa ke nan kowace sa’a. Amsar da ta fi kusa gamsar da shi, ita ce cewa abin ya faru ne kamar yadda ya faru lokacin Mai-ceton, sa’an da priestocin ekklesiya suka zama miyagu, suna anfani da ikon da doka ta ba su domin aikata ababa ba bisa doka ba. Wannan ya sa shi ya dauka a zuciyarsa cewa umurnin Littafi da aka bayar ta wurin ganewa su ne ya kamata su yi mulki bisa lamiri; watau Allah da ke magana cikin Littafi Shi ne Mai-bishewa mara- kuskure kadai, ba ekklesiya da ke Magana ta wurin priestoci ba.” BJ 101.1
Sa’an da bayan wani lokaci hayanniyar Prague ta ragu, Huss ya koma majami’arsa ta Baitalahmi, ya ci gaba da wa’azin maganar Allah da karfin himma, da karfin zuciya kuma. Magabtan sa masu kwazo ne da iko kuma, amma sarauniya da fadawa da yawa abokan sa ne, mutane da yawa kuma suka goyi bayansa. Da yawa da suka gwada koysawoyinsa marasa aibi da rayuwarsa mai-tsarki da munanan koyaswoyin da Romawan suka koyar, da fasikanci da son kurdinsu, sai suka ga cewa ya fi kyau su goyi bayansa. BJ 101.2
Kafin nan, Huss shi kadai ne ya yi ta aikinsa, amma yanzu, Jerome, wanda a Ingila ya karbi koyaswoyin Wycliffe, shi ma ya shiga aikin Canjin. Daga nan su biyu din suka hada kai cikin rayuwarsu, kuma a mutuwa ma basu rabu ba. Jerome mai-madaukakiyar iyawa ne, ga iya magana ga sani kwarai; amma Huss ya fi shi halayya na gari. Halin shi na natsuwa ya rika rage gaggawar Jerome wanda cikin tawali’u yakan bi shawarwarinsa. Kalkashin aikinsu tare, canjin ya yadu da sauri. BJ 101.3
Allah Ya bar haske mai-yawa ya haskaka zukatan mutanen nan zababbu, Ya bayana masu kurkuran Rum da yawa; amma basu karbi dukan hasken da aka ba duniya ba. Ta wurin bayin nan nasa, Allah Ya jawo mutane daga duhun addinin Rum; amma akwai manyan matsaloli da suka fuskanta, kuma Ya bi su daga mataki zuwa mataki yadda suka iya jimrewa. Basu shirya karban dukan hasken a lokaci daya ba. Kamar dukan hasken tsakar rana ga wadanda suka dade cikin duhu, da an nuna masu hasken gaba daya, da ya kore su. Don haka Ya bayana ma shugabanin kadan kadan, yadda mutanen za su iya karban shi. Daga karni zuwa karni wadansu amintattun ma’aikata suka bi baya don jagorantar mutane cikin hanyar canji. BJ 102.1
Rashin jituwa ya ci gaba cikin ekklesiyar. Paparuma uku suka yi ta hamayyar neman fifiko, wannan kuwa ya cika Kiristanci da laifuka da hayanniya. Zage zage basu ishe su ba, suka hada da makamai ma. Kowane dayansu ya shiga sayen makamai da tara sojoji; dole a sami kurdi kuma ai; don haka aka shiga sayar da kyautukan ekklesiya da matsayi da albarkun ekklesiya. Prietocin ma, don kwaikwayon manyansu, suka shiga sayar da ababan nan da yakin kaskantar da abokan hamayyansu da inganta ikon kansu kuma. Da karfin zuciya Huss ya kushe ababan ban kyaman nan da aka dinga yi da sunan addini; mutanen kuma suka zargi shugabannin ekklesiyar Rum din cewa su ne sanadin wahalolin da suka mamaye Kiristanci. BJ 102.2
Birnin Prague kuma ya shiga wata hayanniyar. Kamar zamanun baya, an zargi bawan Allah cewa: “Kai mai-wahal da Israila.” Sarakuna I, 17:18. Aka sake sa birnin cikin horo,Huss kuma ya koma kauyen haihuwarsa. Shaidar da aka rika bayarwa da mainci a majami’arsa ta Baitalahmi ta kare. Ya shiga yin magana ga dukan Kirista, kafin ya ba da ransa ya mutu a matsayin Shaidan gaskiya. BJ 103.1
Domin magance muguntar da ke dauke hankalin Turai, aka shirya taron majalisa ta bai daya a Constance. Babban sarki Sigismund ne ya bukaci a kira taron, ta wurin daya daga cikin paparuman nan uku masu-hamayya da juna, John XXIII. Paparuma John din bai so a yi taron nan, ba, halin sa kuwa ba wanda zai so a bincika ne ba, ko da malalatan yan bisharan zamanin ne za su yi binciken. Amma bai isa ya ja da umurnin Sigismund ba. BJ 103.2
Muhimman manufofin majalisarsu ne magance rashin-jituwa da ke cikin ekklesiya, a kuma kawar da ridda. Sabo da haka, aka kira masu-jayayyan nan da paparuma, su biyu din, su bayana a gaban majalisar, har da jagoran sabobin ra’ayoyin nan, John Huss. Mutum biyu na farkon, sabo da tsaron lafiyarsu, basu hallara da kan su ba, amma wakilan su sun hallara. Paparuma John da ake gani shi ne ya kira taron majalisar, ya hallara da shakku, yana zato cewa babban sarkin yana shirin tube shi ne, yana kuma tsoron za a abincike shi sabo da miyagun ayukansa da suka kunyatar da mulkin paparuma, da kuma laifukan da suka karfafa mulkin. Duk da haka ya shiga birnin Constance din da shagulgula sosai, tare da ma’aikatan ekklesiya da fadawa ma. Dukan ma’aikatan eklesiya da masu-martaban birnin, da ‘yan kasa da yawa, sun fita suka marabce shi. Bisa kansa akwai babban laima na zinariya da manyan majistaroti hudu suka rike. Aka rike gurasar cin jibi a gabansa, tufafi masu tsada da shugabannin ekklesiyan suka sa kuma sun ba da sha’awa. BJ 103.3
Ana haka, wani matafiyin ma yana kusatowa Constance. Huss ya san da hadarukan da ke barazana gare shi. Ya rabu da abokansa, kaman ba zai sake saduwa da su ba, ya ci gaba da tafiyar sa da tsammanin cewa za ta kai shi ga mutuwa. Duk da haka, ya karbi takardar kariya wurin sarkin Bohemia, da wata kuma wurin babban sarki Sigismund. Yayin da yake cikin tafiyar tasa, ya yi dukan shirye shiryensa da tsammanin yiyuwar mutuwarsa. BJ 103.4
Cikin wata wasika da ya rubuta ma abokansa a Prague, ya ce: “‘Yan-uwa na, zan tafi tare da takardar kariya daga wurin sarki, in sadu da magabta na masu-yawa, masu neman kashe ni kuma…. Daga baya na dogara ga Allah mai-cikakken iko ne, da Mai-ceto na; na gaskata zai ji addu’o’in ku na naciya, cewa zai cika baki na da dabararsa da hikimarasa, domin in yi tsayayya da su; kuma cewa zai ba ni Ruhunsa Mai-tsarki Shi karfafa ni cikin gaskiyarsa domin, da karfin zuciya, in fuskanci jarabobi da kurkuku, in ta kama ma, har da mutuwa ta azaba. Yesu Kristi ya wahala sabo da kaunatattuns; sabo da haka kuma, ko ya kamata mu yi mamakin cewa Ya bar mana kwatancinsa, domin mu ma mu jimre dukan ababa da hakuri sabo da ceton mu? Shi Allah ne, mu kuma halitattunsa ne; Shi ne Ubangiji, mu kuma bayinsa; Shi ne Mai-gidan duniya, mu kuma masu-mutuwa ne, abin tausayi, duk da haka Ya wahala! Sabo da haka don me mu ma ba za mu wahala ba, musamman ma idan wahalar sabo da tsarkakewar mu ne? Sabo da haka kaunatattu, idan mutuwa ta za ta kara darajarsa, ku yi addu’a ta zo da sauri, cewa kuma Ya taimake ni jimre dukan masifu na da aminci. Amma idan ya fi kyau in dawo cikin ku, bari mu yi addu’a ga Allah in dawo babu aibi, watau kada in danne wasali daya na gaskiyar bisharar, domin in bar ma yan-uwa na kwatanci gwanin kyau da za su bi. Sabo da haka watakila ba za ku sake ganin fuska ta a Prague ba; amma idan nufin Allah Mai-cikakken iko ne Ya dawo da ni wurin ku, bari mu ci gaba da karin karfin zuciya cikin sanin dokarsa da kaunar ta kuma.” BJ 104.1
Cikin wata wasika kuma, zuwa ga wani priest da ya zama almajirin bishara, Huss ya yi magana da tawali’u mai-zurfi game da kurakuransa, yana zargin kansa “da jin dadin sa tufafi masu-tsada, da kuma bata sa’o’i masu anfani, yana yin ababa marasa anfani.” Sa’an nan ya kara gargadin cewa: “Bari darajar Allah da ceton rayuka su cika zuciyarka, ba mallakar duniya da gidaje da filaye ba. Ka yi hankali da yi ma gidan ka ado fiye da zuciyarka; kuma fiye da komi, ka lura da gini na ruhaniya. Ka yi ibada da tawali’u game da matalauta, kuma kada ka kashe dukiyar ka ta wurin bukukuwa. Idan ba ka sake rayuwar ka, ka rabu da almubazzaranci ba, ina tsoro cewa za a hore ka sosai, kaman ni kai na…. ka san koyaswa ta, da shike ka karbi koyaswata daga kuruciyarka; don haka ba anfani in kara rubuta maka. Amma ina kira gare ka, bisa ga alherin Ubnagijinmu, kada ka yi kwaikwayo na cikin duk wani aikin banza da ka ga na fada a ciki.” A bayan wasikar, ya kara da cewa: “Ina rokon ka aboki na, kada ka bude hatimin nan har sai ka sami tabbaci cewa na mutu.” BJ 104.2
Cikin tafiyarsa, Huss ya ga alamun yaduwar koyaswoyinsa ko ina da kuma goyon bayan da aikinsa ya samu. Mutanen sun rika tururuwa domin su sadu da shi, kuma a wadansu garuruwa, majistarorin suka yi masa rakiya a titunansu. BJ 105.1
Sa’an da Huss ya kai Constance, sai aka ba shi cikakken yanci. Paparuma ya kara masa tsaro da kansa, bayan takardar kariya da babban sarki ya ba shi. Amma ta wurin ketare wadannan umurnin kariyar, ba da jimawa ba, aka kama dan Canjin, bisa ga umurnin paparuma da shugabannin ekklesiyar Rum, aka jefa shi cikin wani kurkuku mai ban kyama. Daga baya aka kai shi wani babban daki a ketaren kogin Rhine inda aka rike shi a matsayin fursuna. Daga baya ma, paparuman da cin amanarsa bata anfane shi komi ba, an kai shi kurkuku dayan. An tabbatar da laifofin sa da yawa masu-ban kyama a gaban majalisa, ban da kisan kai da sayar da ababa na ruhaniya, da zina, da “zalunci da bai kamata a ambata ba ma.” Don haka majalisa da kanta ta umurta aka raba shi da rawaninsa, aka kuma jefa shi cikin kurkuku. Masu takaran zama paparuma ma an sauke su, aka zabi sabon paparuma. BJ 105.2
Ko da shike laifofin paparuman sun fi wadanda Huss ya taba zargin priesetoci da aikatawa, ya kuma bukaci cewa a yi canji a kansu, duk da haka, majalisa dayan da ta sauke paparuman, ta ci gaba ta murkushe dan Canjin. Sa Huss a kurkuku da aka yi, ya ta da fushi sosai a Bohemia. Mutane da yawa masu-martaba da iko suka rubuta ma majilisar rashin amincewarsu da wannan rashin adalcin. Babban sarkin, wanda bai ji dadin ketarewar takardar kariyan da ya bayar ba, bai goyi bayan tuhumar Huss ba. Amma magabtan Huss sun nace, suka dage. Suka ja hankalin babban sarkin ga zancen bambance bambance da ababan da yake tsoro da kwazon sa ga ekklesiya. Suka yi mahawara masu-tsawo sosai don nuna cewa “bai kamata a cika ma masu-ridda alkawlin da aka yi masu ba, ko ma wadanda ake zato sun yi ridda, ko da an ba su takardar kariyan da babban sarki ko sarakuna suka bayar.” Ta hakanan ne suka yi nasara. BJ 106.1
Rashin lafiya, da zaman kurkuku sun nakasa Huss, sabo da danshi da warin kurkukun sa sun jawo masa zazzabin da ya kusan kashe shi, daga baya aka kawo shi gaban majalisar. Yana fama da sarkoki ya tsaya gaban babban sarkin, wanda da aka yi alkawalin ba Huss kariya bisa ga daraja da kyakyawan amincinsa, shi babban sarkin. Duk lokacin tuhuman nan naas mai-tsawo, Huss ya rike gaskiya, a gaban shugabannin ekklesiya da na kasa kuma ya bayana kin yarda mai-nauyi da aminci game da lalacewar shugabannin ekklesiya. Sa’an da aka bukace shi ya zaba tsakanin janye koyaswoyinsa ko mutuwa, ya gwammaci a kashe shi. BJ 106.2
Alherin Allah ya kiyaye shi. Cikin makonin wahalan nan da suka wuce kafin hukumcin sa na karshe, salamar sama ta cikka ran sa. Ya ce ma wani abokin sa: “Ina rubuta wasikan nan a cikin kurkuku na, kuma da dauraren hannu na, ina sa ran za a aiwatar Hukumcin kisa ta gobe.… Sa’an da, tare da taimakon Yesu Kristi, za mu sake saduwa kuma cikin salaman nan mai-dadi na rayuwa mai-zuwa, za ka ji yadda Allah Ya nuna mani jinkansa, yadda Ya goyi baya na a tsakiyar jarabobi na da kunci na.” BJ 106.3
Cikin duhun kurkukun shi, ya hangi nasarar ainihin bangaskiya. Sa’an da cikin mafalki ya koma majami’arsa a Prague inda ya yi wa’azin bishara, ya ga paparuma da bishop bishop dinsa suna shafe hotunan Kristi da shi ya zana a bangon. “Wahayin nan ya dame shi: amma washegari ya ga masu zane da penti da yawa suna mayar da hotunan nan, fiye da yawan na da, da hasken launinsu ma. Da zaran sun gama aikinsu, masu-zanen, wadanda wani babban taron jama’a ya kewaye su, suka ta da murya suka ce: “Yanzu bari su paparuman, da bishop bishop din su zo; ba za su kara shafe su kuma ba!” Sa’an da dan Canjin ke fadin mafalkin nasa, ya ce: “Na tabbata hakika, cewa ba za a taba shafe kamanin Kristi ba. Sun so da sun hallaka Shi, amma za a zana Shi sabo cikin dukan zukata, ta wurin masu-wa’azi da sun fi ni sosai.” BJ 107.1
Karo na karshe aka kawo Huss gaban majalisar. Babban taro ne mai-ban sha’awa — babban sarki da ‘ya’yan sarkin kasar, da wakilan sarki da cardinals da bishop bishop da priestoci, da kuma babban taron jama’a da suka zo kallon al’amuran ranan. Daga dukan fannonin Kirista aka taru don shaida babban hadayan nan ta farko cikin faman nan mai-tsawo, wadda ta wurin ta za a sami yancin lamiri. BJ 107.2
Sa’an da aka bukace shi ya fadi kudurin shi na karshe, Huss ya bayana cewa ba zai janye ba, kuma yana kallon idon sarkin nan da ba kunya aka ketare umurninsa, ya ce: “Na kudurta da yardar kai na, in bayana gaban majalisan nan, kalkashin tsaro da amincin babban sarkin nan da ke zaune a nan.” Jikin Sigismund ya yi sanyi sa’an da idanun kowa a wannan taron suka juya kansa. BJ 107.3
Da shike an rigaya an ba da hukiumci, sai aka fara hidimar aiwatar da horon. Bishop suka sa ma fursunan kayan priest, kuma yayin da ya karbi rigar sarautar, ya ce: “An sa ma Ubangijinmu Yesu Kristi farar riga ce, don cin mutunci, sa’an da Hiridus ya sa aka kai Shi gaban Bilatus.” Sa’an da aka sake bidar sa ya janye, ya juya ya kalli jama’a, ya ce: “Da wace fuska ke nan zan kalli sammai? Yaya zan kalli jama’a da yawa da na yi masu wa’azin tsabtar bishara? Babu; ina girmama cetonsu fiye da jikin nan mara-gata, wanda aka shirya mutuwarsa.” Aka cire rigunan, daya bayan daya, kowane bishop kuma yana tsine masa yayin da yake aikata nasa fannin hidimar. Daga baya, “suka sa masa har hular takarda da aka zana mata hotunan aljannu masu ban-tsoro, da kalman cewa ‘Babban mai-ridda’ a rubuce a gaban. ‘Da farin ciki sosai,’ in ji Huss, zan sa rawanin nan na kunya dominka, ya Yesu, Kai da Ka sa rawanin kaya sabo da ni.’” BJ 107.4
Sa’an da aka gabatar da shi, “priestocin suka ce: ‘Yanzu mun mika ranka ga iblis.’ ‘Ni kuma, in ji Huss, yayin da ya ta da idanun sa sama, ‘na mika ruhu na cikin hannayenka, ya Ubangiji Yesu, da shi ke kai ka fanshe ni.’” BJ 108.1
Sai aka mika shi ga hukumomin kasa, aka kai shi wurin da aka kashe shi. Babban taron jama’a suka bi, daruruwan masu rike da makamai, priestoci da bishop bishop cikin tufafin su masu-tsada, da mazauna Constance. Bayan an daure shi ga babban itacen, an kuma shirya komi don kunna wutar, sai aka sake shawartar Huss cewa ya ceci kan sa, ta wurin janye kurakuransa. “Wadanne kurakurai,” in ji Huss, “zan janye? Na san ban yi ko daya ba. Ina kira ga Allah Ya shiada cewa duk abin da na rubuta, na kuma yi wa’azin sa, da niyyar ceton rayuka ne daga zunubi da hallaka, kuma, don haka, da murna matuka za hakikance da jini na gaskiyan da na rubuta na kuma yi wa’azin ta.” Sa’an da harsunan wutan suka taso kewaye da shi, ya fara waka cewa: “Yesu, Kai dan Dawuda, yi mani jin kai,” kuma ya ci gaba hakanan har sai da muryar sa ta kare har abada. Har magabtansa ma sun yi mamakin jaruntakarsa. Wani dan papaaruma mai-matsanancin ra’ayi, game da mutuwar Huss da na Jerome wanda ya mutu jima kadan bayan Huss, ya ce: “Dukan su sun rike amincin zukatan su har sa’ar su ta karshe. Sun shirya ma wutar, sai ka ce za su bukin aure ne. Basu yi kuka domin zafi ba. Sa’an da harsunan wuta suka taso, sun fara raira wakoki ne; kuma ko zafin wutar bai hana su rairawa ba.” BJ 108.2
Bayan da wuta ta gama cinye jikin Huss, aka tattara tokan sa da kasar wurin da tokan ya kwanta, aka jefa cikin kogin Rhine, daga nan kuma ya wuce har teku. Masu zaluntar sa sun ga kamar ta wurin yin haka sun kawar da gaskiyar da ya koyar ke nan. Basu ko yi mafalkin cewa tokan da suka zubar har zuwa teku sun zama kamar iri ne da aka watsa cikin dukan kasashen duniya ba; cewa a kasashen da ba a rigaya an sani ba ma, zai haifar da ‘ya’ya a yalwace cikin shaidu na gaskiyar. Muryar da ta yi magana a babban zauren majalisar Constance ta falkas da muryoyin da za a dinga ji cikin dukan sararraki. Huss dai ya tafi, amma koyaswoyin gaskiyan da ya mutu sabo da su ba za su taba lalacewa ba. Kwatancin shi na bangaskiya da aminci ya karfafa jama’a da yawa su tsaya da karfi domin gaskiya, komi zalunci ko mutuwa ma. Kisan shi ya bayana ma dukan duniya zaluncin Rum irin na cin amana. Ko da shike magabtan gaskiya basu sani ba, sun kara ci gaban aikin da suka so a banza su lalatar ne. BJ 109.1
An kuma shirya wani wurin kisa a Constance. Dole jinin shaida ya shaida gaskiya. Sa’an da Jerome ya yi ban-kwana da Huss lokacin da zai tashi zuwa majalisar, ya karfafa shi ya yi karfin zuciya da naciya, yana cewa idan ya shiga wata damuwa, shi kan shi zai gudo ya taimake shi. Da zaran ya ji cewa an sa dan Canjin cikin kurkuku, nan da nan amintacen almajirin nan ya shirya domin cika alkawalin sa. Ba tare da wani alkawalin tsaro ba, ya kama hanya, tare da wani abokin tafiya, zuwa Constance. Daga isar sa wurin, ya gane cewa ya sa kansa cikin damuwa ne kawai, ba tare da wata yiwuwar yin wani abu domin kubutar da Huss ba. Ya gudu daga wurin, amma aka kama shi a hanyar sa zuwa gida, aka dawo da shi daurarre da sarkoki, kalkashin tsaron sojoji. A bayanuwar sa ta farko a gaban majalisar, kokarin sa na amsa zarge zargen da ake yi masa ya gamu da ihu cewa, “A kai shi wuta!” A kais hi wuta!” Aka jefa shi cikin kurkuku a daure, ta yadda ya wahala kwarai, ana ciyar da shi da burodi da ruwa. Bayan wadansu watanni, azabar kurkukun Jerome ta jawo masa ciwon da ya nemi ya dauke ransa, magabtansa kuma, sabo da tsoron cewa zai iya tserewa, suka rage tsananta masa, ko da shike ya kasance a kurkukun, har shekara guda. BJ 109.2
Huss bai mutu yadda yan paparuma suka so ba. Ketarewar alakwalin tsaron sa ya ta da guguwar fushi, kuma a matsayin hanyar da ta fi sauki, majalisar ta kudurta cewa, maimakon kona Jerome, a tilasta shi, idan ya yiwu, ya janye. Sai aka kawo shi gaban majalisar, aka kuma ba shi zabin janyewar, ko kuma ya mutu a daure a jikin itace. In da ya mutu a farkon zaman sa a kurkuku, da ya zama jinkai gare shi, idan aka gwada da munanan wahalolin da ya sha; amma yanzu da ya nakasa sabo da ciwo da wahalolin kurkuku, da kuma azabar taraddadi da rashiN sanin abin da zai faru, ga rabuwa da abokai, ga kuma bakin cikin mutuwar Huss, karfin zuciyar Jerome ya waste, ya kuwa yarda zai bi umurnin majalisar. Ya dauki alkawalin manne ma addinin Katolika, ya kuma amince da yadda majalisar ta sake koyaswoyin Wycliffe da Huss, sai dai “gaskiyar masu-tsarki” da suka koyar. BJ 110.1
Ta wurin matakin nan, Jerome ya yi kokarin rufe muryar lamiri, ya tsere kuma daga hallakar sa. Amma cikin kadaicinsa a kurkukun, ya ga abin da ya yi, a bayane. Ya yi tunanin karfin zuciyar Huss da amincinsa, sabanin haka kuma ya yi bimbini game da musun gaskiya da shi ya yi. Ya tuna Allah, Mai-gidan da shi ya yi alkawalin bauta masa, wanda kuma Ya jimre mutuwa ta giciye dominsa. Kafin janyewarsa, ya rigaya ya sami ta’aziya cikin dukan wahalolinsa, cikin tabbacin alherin Allah; amma yanzu juyayi da shakku suka azabtar da zuciyarsa. Ya san cewa akwai wadansu janyewa dole sai ya yi kafin ya sami salama da Rum. Matakin da yake daukawa zai karasa da ridda gaba daya ne kawai. Ya dauki kudurinsa: don gudun takaitacen lokaci na wahala, ba zai yi musun Ubangijinsa ba. BJ 110.2
Ba da jimawa ba, an sake kai shi gaban majalisar. Masu shari’an basu gamsu da jawabinsa ba. Kishin su na jini da mutuwar Huss ta tayar, ya sa sun rika marmarin karin wadanda za a kashe. Sai ta wurin yin watsi da gaskiya kwata kwata ne Jerome zai iya ceton ransa. Amma ya rigaya ya kudurta shaida bangaskiyarsa, ya kuma bi dan-uwansa Huss zuwa wutar. BJ 111.1
Ya fa fasa janyewan da ya yi, kuma a matsayin wanda ke fuskantar mutuwa, ya bukaci zarafin kare kansa. Sabo da tsoron sakamakon kalmominsa, shugabannin ekklesiyar suka nace lallai sai dai ya amnice ko kuma ya yi musun zarge zargen da ake tuhuman sa da su. Jerome ya ki wannan zalunci da rashin adalcin. “Kun rike ni kuka hana ni magana, kwana dari uku da arba’in, cikin kurkuku mai-bantsoro, a tsakiyar kazanta da surutu, da wani wari da rashin komi da komi; sa’an nan kun kawo ni gabanku, bayan kun saurari magabta na, sai ku ki ji na…. Idan za ku zama mutane masu hikima da gaske, haske ga duniya kuma, sai ku mai da hankali kada ku yi zunubi sabanin adalci. Ni dai kumama ne mai-mutuwa, rai na mai- kankantar muhimminci ne; kuma idan na fadakar da ku cewa kada ku ba da hukumci na rashin adalci, ina magana sabo da ku ne, fiye da sabo da ni kai na.” BJ 111.2
A karshe, an amince da rokon shi. A gaban masu shar’anta shi, Jerome ya durkusa ya yi addu’a cewa Ruhun Allah Ya bi da tunaninsa da kalmominsa, domin kada ya yi wata magana da ta saba ma gaskiya ko kuma wadda ba za ta cancanci Mai-gidan shi ba. Gare shi a ranan nan an cika alkawalin Allah ga almajiran farkon cewa: “I, kuma a gaban mahukumta da sarakuna za a kawo ku sabili da ni,…. Amma sa’an da sun bashe ku, kada hankalin ku ya tashi irin magana da za ku yi, ko kwa abin da za ku fadi. Gama ba ku ne kuna fadi ba, amma Ruhun Ubanku ne mai-fadi a chikinku.” Matta 10:18-20. BJ 111.3
Kalmomin Jerome sun jawo mamaki da sha’awa har cikin magabtansa ma. Shekara guda yana tsare a kurkuku, bai sami damar yin karatu ba, ba ya ko gani ma, cikin wahala mai-yawa da tarddadi mai-tsanani. Duk da haka ya gabatar da mahawararsa sarai sarai da karfi kuma kamar da ma ya sami damar yin nazari ne ba tare da tsangwama ba. Ya ja hankulan masu sauraron sa ga dogon jerin mutane masu-tsarki da masu-shari’a marasa adalci suka hukunta su. A cikin kowace sara akwai wadanda, yayin da suke kokarin daga mutanen lokacin su, an zarge su, aka kuma kore su, amma da ga baya kuma aka iske cewa sun cancanci girmamawa. Kristi kansa, an hukumta cewa Shi mai-laifi ne, a wani kotu na rashin adalci. BJ 111.4
Lokacin janyewar sa, Jerome ya rigaya ya yarda cewa hukumcin da ya iske Huss da laifi daidai ne. Yanzu kuma ya bayana tubarsa, ya kuma shaida tsarkin Huss da rashin laifinsa. “Na san shi tun kuruciyarsa,” ya ce: “Mutum ne cikakke mara-aibi, mai-adalci da tsarki; an hukumta shi, duk da rashin laifin shi…. Ni ma, ina shirye in mutu: ba zan ja da baya ba daga azaban da magabta na da shaidun karya suka shirya mani, wadnada wata rana dole za su ba da lissafin karyarsu a gaban Allah babba, wanda ba abin da zai iya rudin Sa.” BJ 112.1
Cikin zargin kansa sabo da musun gaskiya da ya yi, Jerome ya ci gaba cewa: “Cikin dukan zunuban da na yi tun ina saurayi, ba wanda ya fi damu na, yana kuma jawo mani nadama da yawa kamar wanda na aikata a wannan wurin mutuwar, lokacin da na amince da mugun hukumcin da aka yi ma Wycliffe, da kuma na mai-tsarkin nan Huss, mai-gida na da aboki na kuma. Hakika! Ina furta shi daga zuciya ta, ina kuma bayanawa da kyama cewa, da ban-kunya, nay i rashin karfin zuciya sa’an da, da tsoron mutuwa na kushe koyaswoyin su. Sabo da haka ina rokon…Allah madaukaki ya yi hakuri, Ya yafe mani zunubai na, kuma musamman wannan din, wanda ya fi dukan su muni.” Sai ya nuna masu-shari’an da yatsa, da karfi kuma ya ce: “Kun hukumta Wycliffe da John Huss, ba don sun raunana koyaswar ekklesiya ba, amma don kawai sun nuna rashin amaincewa da ababan fallasa da ke fitowa daga ma’aikatan ekklesiya - shagulgulansu na girman kai, da alfaharinsu, da dukan laifukansu. Ababan da suka fada, wadanda kuma ba za a iya karyatawa ba, kamar su, ni ma na yi tunani na bayana su.” BJ 112.2
Aka sa baki cikin maganarsa. Ma’aikatan ekklesiya, suna rawan jiki don fushi, suka ta da ihu cewa: “Akwai kuma bukatar wani tabbaci fiye da wannan? Da idanun mu muna ganin mai-ridda mafi-taurin kai!” BJ 113.1
Jerome bai kula holon su ba, ya ce: “Mene! Kuna tsammanin cewa ina tsoron mutuwa? Kun rike ni har shekara guda cikin kurkuku mai-ban tsoro. Kun wulakanta ni fiye da Baturki, ko Bayahudi, ko arne, nama na kuma, zahiri ya rube, ya rabu da kasusuwa na, da rai na kuwa; kuma duk da haka, ban nuna damuwa ba, da shike makoki bai yi kyau da mutum mai-zuciya da ruhu ba; amma dole in bayana mamaki na game da wannan irin babbauci da aka yi ma Kirista.” BJ 113.2
Guguwar fushi ta sake barkewa, aka kuma ruga da Jerome zuwa kurkuku. Duk da haka, cikin taron akwai wadanda kalmominsa suka taba zukatansu sosai, suka kuma so su ceci ransa. Masu martaba na ekklesiya sun ziyarce shi, suka roke shi ya ba da kan sa ga majalisar. Aka gabatar masa da hange mafi-ban sha’awa a matsayin ladar janye jayayyar sa ga Rum. Amma, kamar Mai-gidansa sa’an da aka yi masa tayin darajar duniya, Jerome ya nace da karfin halinsa. BJ 113.3
“Ku tabbatar mani daga Littafi Mai-tsarki cewa ina kuskure,” ya ce, “ni kuwa sai in rabu da shi.” BJ 113.4
Daya daga cikin masu-jarabtar shi ya ce, “Rubuce rubuce masu-tsarki! Watau da su za a gwada kowane abu ke nan? Wa zai fahimce su, idan ba ekklesiya ce ta fassara su ba?” BJ 113.5
“Ko al’adun mutane sun fi bisharar Mai-ceton mu cancantuwa a gaskata su?”, amsar Jerome ke nan. “Bulus bai bukaci wadanda ya rubuta masu su saurari al’adun mutane ba, amma ya ce, ‘Ku bincika Nassosin.’ ” BJ 113.6
Aka amsa cewa: “Mai-ridda! Na tuba da na dade haka ina rokon ka. Na ga cewa Iblis ne yake zuga ka.” BJ 113.7
Ba da jimawa ba, aka sanar da hukumci a kan shi. Aka kai shi daidai inda Huss ya sallamar da ransa. Ya tafi yana waka a hanyarsa, fuskarsa tana haskakawa da murna da salama. Ya kafa hankalinsa a kan Kristi ne, a gare shi kuwa, mutuwa ta rigaya ta rasa ban-razanar ta. Sa’an da mai-kisan, gaf da lokacin da zai kunna ma karmomin wuta, ya koma bayan sa, Jerome da karfi ya ce: “Taho gaba na kai tsaye; kunna wutar a gaban fuska ta. Da a ce ina tsoro da ba na wurin nan.” BJ 113.8
Kalmomin shi na karshe da ya furta sa’an da harsunan wutan suka taso a kan shi, addu’a ce. Ya ce: “Ubangiji, Madaukaki Uba, ka ji tausayi na, ka gafarta mani zunubai na; gama ka san ina kaunar gaskiyar ka kullum.” Muryar sa ta tsaya, amma lebunan sa suka ci gaba da motsi cikin addu’a. Sa’an da wutar ta gama aikinta, aka tara tokansa, da kasan da tokan ya kwanta a kai, kuma kaman na Huss, aka jefa su cikin Kogin Rhine. BJ 114.1
Hakanan ne amintattun masu-kai hasken Allah suka hallaka. Amma hasken gaskiyan da suka yi shelan ta - hasken kwatancin jarumtakarsu- ba a iya bicewa ba. Yunkurin mutane na hana wayewan garin da a lokacin ya zo ma duniya, daidai yake da yunkurin tura rana ta koma baya. BJ 114.2
Kashe Huss da aka yi ya kunna wutar fushi da kyama a Bohemia. Dukan al’ummar ta dauka cewa shi dai kiyayyar priestoci da cin amanansa da babban sarkin ya yi ne kawai suka sa an kashe shi. An bayana cewa shi amintacen mallami ne mai-koyar da gaskiya, aka kuma zargi majalisar da ta umurta kisansa da laifin kisa. Yanzu kuma koyaswoyinsa sun kara jawo hankula fiye da can baya. Ta wurin umurnin paparuma, an kone rubuce rubucen Wycliffe. Amma wadanda suka tsira daga kunar, yanzu an fito da su daga inda aka boye su, aka yi nazarinsu tare da Littafi, ko kuma fanonin Littafin da aka iya samu, ta haka kuma aka jawo mutane da yawa suka karbi sabuwar bangaskiyar. BJ 114.3
Masu kashe Huss basu tsaya a gefe suka kalli nasarar aikinsa ba. Paparuma da babban sarkin suka hada kai domin murkushe aikin, aka kuma tura ma Bohemia mayakan Sigismund. BJ 114.4
Amma fa an ta da mai-kubutarwa. Ziska, wanda daga farkon yakin ya makance, duk da haka ya kasance daya daga cikin kwararrun janar janar na zamaninsa, shi ne ya jagoranci yan Bohemia. Da dangana ga taimakon Allah da kuma adalcin aikinsu, al’umman nan ta nuna ma shahararrun mayakan nan karko. Akai-akai babban sarkin yakan ta da sabobin mayaka, ya kai ma Bohemia hari, amma sai a kuma kore su a saukake. Hussiyawan sun wuci inda za su ji tsoron mutuwa, kuma ba bin da ya iya karawa da su. Shekaru kalilan bayan farawan yakin, jarumin nan Ziska yam mutu; amma Procopius, wanda shi ma jarumin janar ne, kwararre mara-tsoro, wanda kuma a wdansu fannonin shugabanci ya fi Ziska, ya dauki matsayin sa. BJ 115.1
Magabtan Bohemiyawa, da sanin cewa makahon mayakin ya mutu, suka dauka cewa wannan zarafi ne da za su dawo da dukan abin da suka rasa. Sai kuma paparuma ya sanar da yakin addini kan mutanen Huss, ban da haka kuma aka ta da babban fada da Bohemia, amma kuma aka sha kaye mumuna. An sake sanar da wani yakin addinin. A dukan kasashen Turai masu-bin paparuma, aka tara mayaka da kurdi da makamai don yaki. Jama’a suka rika tururuwa don shiga rundunan mayakan paparuma, da tabbacin cewa a karshe dai za a kawo karshen masu riddan nan Hussawa. Da tabbacin nasara mayakan nan suka shiga Bohemia. Mutane suka taru domin su kore su. Rundunonin biyu suka fuskanci juna ta yadda kogi ne kadai tsakanin su. “Mayakan addinin sun fi na Hussawan karfi kwarai, amma maimako su kutsa cikin kogin su ketare domin su gwabza yaki da Hussawan, sai suka tsaya shuru suna kallon mayakan.” Sai kuma faraf daya, wata razana mai-ban al’ajibi ta abko ma rundunar. Ba tare da ko bugu daya ba, babban rundunan nan ta waste, kamar wani iko da ba a gani ba ne ya watsar da su. Mayakan Hussawan suka kashe magabtan da yawa sosai, suka kore su, kuma ganima da yawa ta shiga hannun masu-nasaran,don haka maimako yakin ya tsiyatar da Bohemiyawan, ya arzunta su ne kuma. BJ 115.2
Shekaru kaklilan bayan haka, kalkashin wani sabon paparuma, an sake shirya wani yakin addinin kuma. Kamar karon farko, an sake tara mutane da dukiya daga kasashen Turai yan paparuma. An kwadaita manyan lada ma masu zuwa wannan yaki mai-yawan hatsari. Aka tabbatar ma kowane mayaki cikakkiyar gafarar zunubai mafi muni. Dukan wadanda suka mutu a yakin an yi masu alkawalin babban lada a sama, wadanda basu mutu ba kuma za su girbe daraja da arziki a filin dagan ma. Aka kuma tara mayaka da yawa; kuma sa’an da suka ketare iyakar kasar, suka shiga Bohemia. Dakarun Hussawan suka ja baya, ta hakanan kuma suka rika jan magabtan zuwa ciki-cikin kasar. Suka kuma sa su sun dauka cewa sun rigaya sun yi nasara. A karshe dai, mayakan Procopius [shugaban Hussawan] suka tsaya, suka juya kan magabtansu, suka kuma ja daga da su. Masu yakin addinin, yanzu da suka gane kuskurensu, suka kwanta a sansaninsu, suna jira a fara fada. Da aka ji holon mayakan Hussawa, tun ma ba a gan su ba, rudewa ta sake abka ma mayakan addinin. ‘Ya’yan sarki da janar janar da sauran sojoji suka jefar da makamansu, suka waste barkatai. A banza wakilin paparuma, wanda ya shugabanci harin, ya yi kokarin tattaro firgitattun mayakan nasa. Duk iyakar kokarinsa, shi kan shi ma ya arce tare da sauran masu-gudun. Cikakkiyar nasara aka yi, haka kuma ganima da yawa ta sake shiga hannun masu nasarar. BJ 115.3
Haka kuwa, mayaka da dama a kasashe mafi-karfi na Turai suka tura rundunar horarru, da kayan yakinsu, suka gudu, kuma ba wanda ya taba su, daga gaban kankanuwar al’umma mara-karfi. Nan ga shaidar ikon Allah. An buge magabtan da razana ce wadda ta wuce ikon dan Adam. Shi wanda Ya hallaka rundunonin mayakan Fir’auna a Jan Teku, wanda Ya kori rundunonin mayakan Midian a gaban Gideon da mutanen sa dari uku, wanda cikin dare daya, Ya hallaka dakarun Assyria masu alfarma, Ya kuma mika hannunsa domin shanye ikon azalumin. “A chan fa suka ji tsoro mai-yawa, ba kwa abin tsoro ba: gama Ubangiji Ya watsadda kasusuwan wanda ya kewaye ka da sansani; ka kumyata su, domin Allah ya ki su.” Zabura 53:5. BJ 116.1
Sa’an da shugabannin yan paparuman suka kasa yin nasara ta wurin yin anfani da karfi, a karshe sai suka koma ga lallashi. Aka yi wata daidaitawa dai, wadda, yayin da ta ce ta ba Bohemiyawa yancin lamiri, a zahiri ma dai ta bashe su ne ga ikon Rum. Bohemiyawan sun rigaya sun ba da sharudda hudu don sulhuntawa da Rum, watau: yancin wa’azin Littafi; yancin dukan ekklesiya ga gurasa da ruwan anab lokacin cin jibi da kuma anfani da harshensu lokacin sujada ga Allah; raba ma’aikatan ekklesiya daga dukan makamai na gwamnati da ba na addini ba; sa’an nan game da aikata laifuka, kotunan kasa su kasnce da hurumi kan ma’aikatan ekklesiya dadai da sauran mutane. A karshe dai mahukumtan yan paparuman sun “yarda cewa a amince da sharudda hudu na Hussiyawan, amma kuma cewa yancin fassara su, watau bayana ainihin ma’anar su zahiri, ya kamata ya kasance a hannun majalisa ne, watau dai a hannun paparuma da babban sarkin.” Bisa ga wannan aka shiga yarjejjeniya, Rum kuma, ta wurin rudi da yaudara, ta sami abin da ta kasa samu ta wurin fada; gama, ta wurin ba sharuddan Hussawan ma’anan da ita ta so, kamar yadda ta yi da Littafi, za ta iya canja ma’anar su don cim ma manufofinta. BJ 117.1
Mutane da yawa a Bohemia da suka ga cewa yarjejjeniyar ta tauye hakinsu, basu yarda da ita ba. Gardama da rarrabuwa suka taso, suka kai ga tashin hankali da zub da jini tsakaninsu. Cikin hargitsin nan ne mai-martaban nan Procopius ya mutu, yancin Bohemiyawa kuma suka hallaka. BJ 117.2
Sigismund mai-bashe da Huss da Jerome, yanzu ya zama sarkin Bohemia, kuma duk da rantsuwar sa cewa zai goyi bayan yancin Bohemiyawa, ya ci gaba ya kafa tsarin paparuma. Amma bai yi riba mai-yawa ba ta wurin ba da kan sa kalkashin Rum. Shekaru ashirin rayuwar sa tana fama da wahaloli da hatsari. An rigaya an hallaka mayakan shi, baitulmalin shi kuma an tsiyaye ta wurin yaki mai-tsawo mara-anfani. Yanzu kuma, bayan ya yi mulki na shekara daya, ya mutu, ya bar kasarsa a bakin yakin basasa, ya kuma bar ma magada suna mara-kyau. BJ 117.3
Rigingimu da tashe tashen hankula da zub da jini sun tsawanta. Dakarun kasashen waje suka sake kai ma Bohemia hari, rashin jituwa na cikin kasar kuma ya ci gaba yana dauke hankalin al’ummar. Wadanda suka kasance da aminci ga bishara kuma an gallaza masu azaba mai-zub da jini. BJ 117.4
Yayin da yan’uwan su na da, da suka yi yarjejjeniya da Rum suka rungumi kurakuran ta, wadanda suka rike bangaskiya ta asalin sun kafa ekklesiyar su dabam, mai-suna “Yan’uwa Masu-Hadin kai.” Wannan ya jawo masu tsinewa daga dukan bangarori. Duk da haka basu raunana ba. Sa’an da aka tilasta su suka nemi mafaka a koguna da dazuka, sun ci gaba da tattaruwa suna karanta maganar Allah da hada kai cikin sujada gare Shi. BJ 118.1
Ta wurin ‘yan sako da suka aika a boye zuwa kasashe dabam dabam, sun gane cewa da can akwai “tsirarun masu rungumar gaskiya, kalilan a wannan birni, kalila a wancan, wadanda kamar su, masu shan tsanantawa ne; kuma cewa cikin duwatsun Alps din nan, akwai dadaddiyar ekklesiya da ta kafu bisa harsashen Littafi, tana kuma jayayya da lalacewar Rum, irin ta bautar gumaka. An karbi labarin nan da murna sosai; aka kuma shiga sadarwa da Kiristan Waldensiyawa.” BJ 118.2
Cikin aminci ga bisharar, Bohemiyawan sun jira har karshen daren zaluncinsu, cikin sa’a mafi-duhu, suna dai juya idanunsu zuwa sama, kamar masu-jiran safiya. “Sun kasance cikin mugun zamani ne, amma … sun tuna kalmomin da Huss ya fara fadi, Jerome kuma ya nanata, cewa sai bayan shekaru dari kafin gari ya waye. Kalmomin nan sun zama ma Hussawan kamar yadda kalmomin Yusufu suka zama ma kabilun Israila ne a kasar bauta, cewa: ‘Ina mutuwa: amma hakika Allah za ya ziyarche ku, ya fishe ku.’” “Lokacin karshen karni na sha biyar ya gamu da yawaitar ekklesiyoyin Yan’uwan a hankali, hakika kuma. Ko da shike an fitine su, duk da haka sun sami Karin hutu. A farkon karni na sha shida, ekklesiyoyin su sun kai guda dari biyu a Bohemia da Moravia.” “Masu daraja ne ringin nan da suka tsere ma fushin hallaka na wuta da na takobi, aka yarda masu su ga tahowar ranan nan da Huss ya ce tana zuwa.” BJ 118.3