Yayin da Luther ke bude rufaffen Littafin ga mutanen Jamus, Ruhun Allah ya motsa Tyndale ya yi ma Ingila haka ma. An rigaya an juya Littafin Wycliffe daga na Latin, wanda ke da kurakurai da yawa. Ba a taba buga shi ba, kuma kurdin sayen rubutaciyar ya yi yawa ta yadda mawadata da fadawa ne kadai za su iya sayen shi, kuma da shi ke ekklesiya ta haramtadda shi, bai yadu sosai ba. A 1516, shekara daya kafin bayanuwar ra’ayoyin nan na Luther, Erasmus ya rigaya ya wallafa Sabon Alkawali da harshen Latin da na Helenanci. Yanzu, na farko kenan da aka buga maganar Allah cikin harshensa na asali. A wannan Littafin an gyara kurakurai da yawa daga juyin harsunan da aka fara bugawa, wanda ya fito da ainihin ma’anar. Wannan ya kai mutane da yawa ga sanin gaskiyar, ya kuma kara karkon Canjin. Amma yawancin talakawa basu sami maganar Allah kai tsaye ba tukuna. Tyndale ne ya kamala aikin Wycliffe na ba da Littafi ga yan kasarsa. Shi natsatsen dalibi ne mai kwazon neman gaskiya, ya kuma sami bisharar daga Sabon Alkawali na Hellennanci da Erasmus ya wallafa ne. Ya yi wa’azin ra’ayoyinsa ba tsoro, yana cewa a gwada dukan koyasuwoyi da Littafin. Game da kirarin yan paparuma cewa ekklesiya ce ta ba da Littafin, kuma ekklesiya ce kadai za ta iya fasarta shi, Tyndale ya amsa; “Kun san wanda ya koya ma gaggafa neman abincinsu? Haka kuwa Allah dayan ke koya ma mayunwata ‘ya’yansa neman Ubansu cikin maganarsa. Maimakon ba mu Littafin, ku ne kuka boye mana shi, ku kuke kone wadanda ke koyar da shi, kuma da kun iya ma da za ku kone Littafin kansa.” BJ 243.1
Wa’azin Tyndale ya jawo marmari sosai, da yawa sun karbi gaskiyar. Amma Priestocin basu yi soke ba, kuma da zaran ya bar filin, suka yi kokarin rushe aikinsa ta wurin barazana da rudu. Sau da yawa sun yi nasara. Ya ce: “Me za a yi? Yayin da nike shuka a waje daya, magabcin yana tarwasa wurin da na bari yanzu. Ba zan iya kasancewa ko ina ba. Kash! Da Kirista suna da Littafin a harsunansu da sun iya yin jayayya da makaryatan nan da kansu, in babu Littafin ba zai yiwu a karfafa mutane cikin gaskiyar ba.” BJ 243.2
Wata manufa kuma ta shiga tunaninsa yanzu. Ya ce; “Da harshen Israila ne aka raira zabura a haikalin Yahweh; ashe bishara ba za ta yi yaren Ingila a cikinmu ba? … Ko ya kamata ekklesiya ta kasance da hasken tsakar rana da bai kai na wayewan gari ba? Dole Krista su karanta Sabon Alkawali ciki harshensu.” Likitoci da mallaman ekklesiya suka sami sabanin ra’ayi tsakaninsu. Ta wurin Littafin ne kadai mutane za su san gaskiya. “Wannan ya yarda da wannan likitan, wani kuma ya yarda da wani likitan…. Yanzu fa likitocin nan suna sabanin ra’ayi da juna. Ta yaya kenan za mu iya bambanta mai fadin gaskiya da mai kuskure?.... Ta yaya? ….Hakika tawurin maganar Allah.” BJ 244.1
Ba da jimawa ba ne bayan wannan da wani masani, likitan Katolika, cikin mahawara da shi yace; “Gara mu kasance ba dokar Allah da mu kasance ba dokar paparuma.” Tyndale ya amsa: “Na kangare ma paparuma da dukan dokokinsa, kuma idan Allah ya kiyaye raina, cikin shekaru kadan zan sa yaron da ke rike garma ya san Littafin fiye da kai.” BJ 244.2
Manufar da ya fara sha’awarta, ta ba mutane Sabon Alkawali cikin harshensu, yanzu ta tabbata, kuma nan da nan ya shiga aikin. Da zalunci ya kore shi daga gidansa, sai ya je London, can kuma ya ci gaba da aikinsa babu tashin hankali. Amma kuma nuna karfi na ‘yan paparuma ya sake tilasta shi ya gudu. Sai ka ce dukan Ingila ta tasam masa, sai ya kudurta neman mafaka a Jamus. Nan ne ya fara buga Sabon Alkawali cikin harshen Ingilishi, sau biyu aka tsayar da aikin, amma sa’anda aka hana shi bugawa a wani birni, yakan tafi wani birnin. Kuma a karshe ya je Worms, inda, shekaru kalilan da suka gabata, Luther ya kare bishara a gaban majalisar. A wannan birnin akwai abokan Canjin da yawa, can kuma Tyndale ya yi aikinsa, ba abu mai hanawa. Nan da nan Sabon Alkali guda dubu uku suka kare, wani sabon bugun kuma ya biyo baya cikin shekarar. BJ 244.3
Ya ci gaba da aikinsa da himma sosai, duk da cewa hukumomin Ingila sun tsare tashoshin jiragen ruwansu sosai, maganar Allah ta shigo London ta hanyoyi daban dabam daga nan kuma aka bazu ko ina a kasar. Yan paparuma sun yi kokarin danne gaskiyar, amma a banza. A wani lokaci bishop na Durham ya sayi kowane Littafin da ke shagon wani abokin Tyndale da niyyar kone su, yana zato cewa wannan zai ja aikin baya. Amma, sabanin haka, kurdin da ya biya ne aka buga wani sabon bugun Littafin da shi, ingantace kuma wanda ba don kurdinsa ba, da ba a iya buga sabon ba. Sa’anda daga baya aka mai da Tyndale fursuna, an yi masa tayin samun yancinsa bisa sharadin cewa zai bayana sunayen wadanda suka taimake shi biyan kurdin buga littafansa. Ya amsa cewa bishop na Durham ya fi kowa, domin tawurin biyan kurdi mai yawa don littatafan da ba a saya ba ya taimake shi ya ci gaba da karfin hali sosai. BJ 245.1
An bashe Tyndale a hannuwan magabtansa, a wani lokaci kuma ya sha kurkuku na watanni da yawa. Daga baya ya shaida bangaskiyarsa tawurin mutuwan don bangaskiyar, amma makamai da ya shirya sun taimaki wadansu sojoji yin yaki cikin dukan sararaki har zuwa lokacin mu ma. BJ 245.2
Latimer ya rika wa’azi daga bagadi cewa ya kamata a rika karanta Littafin da harshen mutane. Ya ce ai mawallafin Littafin, “Allah ne da kansa,” kuma Littafin yana da girma da dawamar shi mai wallafa ta din. “Kowane sarki, da majistare, da mai mulki…. Wajibi ne su yi biyayya ga …. Maganarsa mai-tsarki.” “Kada mu bi wata barauniyar hanya, amma bari maganar Allah ta bishe mu: kada mu yi tafiya kamar kakanin mu, ko mu bidi abin da suka bida, amma mu yi abin da ya kamata da sun yi.” BJ 246.1
Barnes da Frith, amintattun abokan Tyndale, sun tashi domin su kare gaskiyar. Su Ridley da Cranmer suka bi. Shugabannin nan na Canjin Ingila masane ne, an kuma kakame yawancinsu sabo da himma ko ibada a ekklesiyar Rum. Sabaninsu da tsarin paparuma sakamakon sanin su na tsarin ne. Sanin su na asiran Babila ya bada karin iko ga shaidarsu game da Babila din. BJ 246.2
Latimer ya ce: “yanzu zan yi wata tambaya da ba a saba yi ba. Wane ne bishop mafi himma a dukan Ingila?... Na ga kana ji, kuma kana sauraro cewa in fadi sunansa…. Zan fada maku: Shaitan ne…. Ba ya taba barin diocese dinsa; a kira shi duk lokacin da aka ga dama, yana gida kullum: kowane lokaci yana wurin aikinsa… Ba za a taba samun shi yana zaman banza ba, ina tabbatar maku. Inda Iblis ke da zama, can fa ban da littafai, sai dai kyandir, banda littafi, sai dai cazbi, ban da hasken bishara, sai dai hasken kyandir, I, da tsakar rana ma; banda giciyen Kristi, sai dai yankan aljihu na purgatory;… ban da suturta marasa tufafi, da matalauta da mara lafiya, sai dai yi ma gumaka ado da shafa ma wuraren horon mutane kayan ado; daukaka al’adun mutum da dokokinsa, kasa da al’adun Allah da maganarsa mafi tsarki .…da dai priestocin mu za su zama da himmar shuka masarar koyaswa mai kyau, kamar yadda Shaitan ke himmar shuka ciyayi da zawan.” BJ 246.3
Baban kaidan da ‘yan Canjin nan suka rike - wadda Wycliffe da John Huss da Luther da Waldensiyawa da Zwingli suka rike - ita ce iko mara kuskure na Littafin a matsayinsa na ka’idan bangaskiya da ayuka. Sun ki yancin paparuma da majalisu da ubani da sarakuna su mallaki lamirin mutane a sha’anin addini. Littafi ne ikonsu, kuma da koyaswarsa suka rika gwada kowace koyaswa. Bangaskiya ga Allah da maganarsa ne suka rike mutanen nan da suka ba da rayukansu aka kashe su. Latimer ya ce ma abokan famansa: “Ku kasance da kyakyawar ta’aziya, yau za mu kunna kyandir a Ingila wadda, da yardar Allah ba za a taba bicewa ba.” BJ 247.1
A Scotland, ba a taba rushe gaskiyan da Columba da abokan aikinsa suka baza kwata kwata ba. Daruruwan shekaru bayan ekklesiyoyin Ingila suka yarda da Rum, na Scotland suka rike yancinsu. Amma a karni na sha biyu an kafa tsarin paparuma a nan, inda ya fi na kowace kasa tsananin iko kuwa. Ba inda duhun ya fi baki. Duk da haka tsirkiyoyin haske suka rika ratsa duhun suna ba da begen zuwan rana. Yan Lellard da suka zo daga Ingila da Littafi tare da koyaswoyin Wycliffe, sun yi aiki sosai don kiyaye sanin bishara, kuma kowane karni an sami shaidu da wadanda aka kashe don bangaskiyarsu. BJ 247.2
Budewar Babban Canjin ta zo tare da rubuce rubucen Luther, sa’annan da Sabon Alkawali na Turanci na Tyndale. Ba da sanin yan ekklesiyar Rum ba, yan sakon nan suka rika ketare duwatsu da kauyuka suna kunna tocilar gaskiya da aka kusa kangewa a Scotland, suna kuma warware aikin danniyar Rum na karni hudu. BJ 247.3
Sa’annan jinin masu bangaskiya ya kara ma aikin karfi. Da shugabannin yan paparuman suka gane hadarin da ke barazana ga aikinsu, sai suka rika kashe wadansu ‘ya’yan Scotland mafi martaba da daukaka. Amma wannan bagadi ne suka kafa daga inda aka ji kalmomin shaidun nan da ke mutuwa, ko ina a kasar, wanda ya motsa rayukan mutanen da niyyar tube sarkokin Rum. BJ 247.4
Hamilton da Wishart, ‘ya’yan sarauta masu halin martaba tare da almajirai talakawa da yawa sun ba da rayukansu aka kashe su. Amma daga tarin itache wutan da aka kona Wishart, wani ya taho wanda wutan ba za ta kashe shi ba, wanda a kalkashin Allah zai yi ma tsarin paparuma a Scotland bugun ajali. BJ 248.1
John Knox ya juya daga al’adu da shirin ekklesiya, ya shiga ci daga gaskiyar maganar Allah, kuma koyaswoyin Wishart sun tabbatar da kudurinsa na barin ekklesiyar Rum. Ya kuma hada kansa da ‘yan Canjin da ake wa zalunci. Sa’anda abokansa suka roke shi ya zama mai wa’azi, ya yi sanyin gwiwa saboda nauyin aikin, kuma sai bayan kwanaki na ware kansa cikin bimbini da kansa sa’anan ya yarda. Amma da zaran ya karbi matsayin, ya ci gaba da himman tare da karfin zuciya ainun duk tsawon rayuwarsa. Wannan tsayayyen dan Canjin bai ji tsaron mutum ba. Wutar mutuwa dan bangaskiya ta dinga kara ingiza himmarsa ne ma. Ga gatarin azalumi da aka daga ta kusa da shi don a kashe shi, amma ya ci gaba yana rushe bautar gumaka dama da hagu. BJ 248.2
Sa’anda ya zo fuska da fuska da sarauniyar Scotland, wadda a gabanta himmar shugabannin Kin ikon paparuma da yawa ta rika karewa, John Knox ya shaida gaskiya ba tantama. Lallashi bai canja shi ba; bai raunana sabo da barazana ba. Sarauniyar ta zarge shi da ridda. Ya koya ma mutane su karbi adinin da kasa ta hana, ta ce, kuma wai ta hakanan ya ketare umurnin Allah cewa talakawa su yi biyayya ga yayan sarakunansu. Knox ya amsa: “Kamar yadda addinin na kwarai bai sami karfinsa daga ‘ya’yan sarakunan duniya ba ne, amma daga madawamin Allah kadai, haka ne bai wajaba ma talakawa su sifanta addininsu bisa ga marmarin yayan sarakunansu ba. Gama sau da yawa ‘ya’yan sarakuna ne suke fin kowa rashin sanin addinin gaskiya na Allah…. Da dukan zuriyar Ibrahim yan addinin Fir’auna ne, wadda sun dade suna masa bauta, ya uwargida, da wane addini ne ke duniya a lokacin? Ko kuma da dukan mutane a zamanin manzanin yan addinin sarakunan Rum ne, da wace addini ne ya kasance a fuskar duniya?... Sabo da haka, uwargida, za ki iya ganewa cewa ba wajibi ne ga talakawa su bi addinin yayan sarakunansu ba, ko da shike an umurce su su yi masu biyayya.” BJ 248.3
Mary kuma ta ce: “Kana fassara Littafin ta wata hanya, su kuma (mallaman Roman Katolika) suna fassara shi ta wata hanya, wa zan gaskata; kuma wa zai yi hukumci? Dan Canjin ya amsa: “Ki gaskata Allah, wanda ke maganarsa a bayane, kuma ba wani abin da ya fi wanda maganar ke koya maki, kada ki gaskata wannan ko wancan. Maganar Allah a bayane take da kanta; kuma idan akwai shakka a wani wuri, Ruhu Mai-Tsarki, wanda ba ya taba jayayya da kansa, yakan fassara wurin a bayane a wadansu wuraren, ta yadda ba za a iske wata shakka kuma ba sai ga wadanda suka nace ma jahilci.” BJ 249.1
Irin gaskiyan da dan Canjin nan mara tsoro ya furta a kunnen sarauniya, a bakin ransa. Da wannan karfin halin ne ya rike manufarsa yana addu’a, yana kuma yake yaken Ubangiji, har sai da aka ‘yantar da Scotland daga tsarin paparuma. BJ 249.2
A Ingila, kafawar Kin ikon paparuma a matsayin addinin kasa ya rage zalunci, amma bai kawar da shi kwata kwata ba. Yayin da aka yi watsi da koyaswowi da yawa na Rum, an kuma rike kamaninsu da yawa. An ki daukakar paparuma, amma a madadinsa an daukaka sarki a matsayin kan ekklesiya. A cikin hidimar ekklesiya an iske bambanci mai yawa daga tsabta da saukin kan bishara. Ba a rigaya an fahimci babban kaidan nan na yancin addini ba lokacin. Ko da shike jefi jefi ne shugabannin ‘yan Kin ikon paparuma suka yi anfani da irin muguntan da Rum ta yi anfani da su kan masu ridda, duk da haka ‘yancin kowane mutum ya yi sujada ga Allah bisa ga lamirinsa bai karbu ba. An bukaci kowa ya karbi koyaswa ya kuma bi matakan sujada da ekklesiyar da aka sani ta tsara. Waddanda basu bi ba sun sha zalunci har tsawon daruruwan shekaru. BJ 249.3
A karni na sha bakwai an sallami dubban pastoci daga matsayinsu. An hana mutane halartar duk wani taro na addini sai dai wand ekklesiya ta amince da shi, in bah aka ba kuwa a fuskanci tara ko fursuna ko kora daga kasar. Amittantun mutanen nan da ba su iya rabuwa da taron sujada ga Allah ba ya zama masu tilas suka rika saduwa da sakon tsakanin gidaje da benen gidaje, wadansu lokuta ma a kurmi da stakar dare. A kurmin haikalin da Allah ya gina da kansa, ‘ya’yan nan na Ubangiji da aka warwatsar aka kuma tsananta, sukan taru don yin addu’a da yabo. Amma duk kokarin buyansu, da yawa sun wahala sabo da bangaskiyarsu. Gidajen kaso suka cika. Aka rarraba iyalai. Da yawa aka kore su zuwa wadansu kasashe dabam. Duk da haka Allah yana tare da mutanensa, kuma zalunci bai tsayar da shaidar su ba. Aka kori wadansu zuwa ketare can Amerika inda suka kafa harsashen yancin addini da ya zama ginshiki da abin daukakar kasar nan Amerika. BJ 250.1
Kuma, kamar zamanin manzani, zalunci ya kara ci gaban bishara ne. A wani kurkuku mai ban kyama, cike da masu manyan laifuka, John Bunyan ya shaki iskar yanayin sama, kuma nan ne ya rubuta littafin nan nasa da ya kamanta tafiyar Kirista daga kasar hallaka zuwa birni na sama. Har sama da shekara dari biyar wannan littafin daga kurkukun Bedford ya rika magana ga zukatan mutane da iko na ban mamaki. Littattafan Bunyan, “Pilgrims Progress” da “Grace Abounding to the Chief of Sinners,” sun bi da mutane da yawa zuwa hanyar rai. BJ 250.2
Baxterm Florrel, Alleine da wadansu kuma masu baiwa da ilimi da kwakwaran dandanon Kristoci sun tashi tsaye don kare bangaskiyar da aka taba ba sarkaka, aikin da mutanen nan da suka yi, wanda masu mulkin duniyan nan suka haramta, ba zai taba lalacewa ba. Littattafan Florrel, “Fountain of Life” da “Method of Grace” sun koya ma dubbai yadda za su mika ma Kristi tsaron rayukansu. Littafin Baxter, “Reformed Pastor,” ya zama albarka ga masu marmarin falkaswar maganar Allah, wani littafin sa kuma, “Saint’s Everlasting Rest” ya jawo mutane zuwa “hutun” da ya rage don mutanen Allah. BJ 250.3
Bayan shekaru dari, Whitefield da yaran Wesley suka fito a matsayin masu kai hasken Allah. A kalkashin shugabancin ekklesiyar kasar, mutanen Ingila sun rigaya sun shiga yanayin sanyin addini da ya zama da wuya a bambanta shi da kafirci. Addini na halitta ya zama abin da masu bishara suka fi so su yi nazarinsa, kuma ya kunshi yawancin tauhidinsu. Manyan mutane suka rena ibada suna alfaharin cewa sun fi karfin tsanancin talakawa, kuma jahilci ya sha kansu, suka zama masu mugunta, ekklesiya kuma ta rasa karfin zuciyar da za ta goyi bayan aikin gaskiya. BJ 251.1
Muhimmin koyaswar barata ta wurin bangaskiya da Luther ya koyar, an kusan mantawa da ita gaba daya, koyaswar Rum ta dogara ga kyawawan ayuka kuma ta dauki wurin. Whitefield da yaran Wesley, membobin ekklesiyar kasa ne, amma amintattun masu neman yardar Allah, kuma an koya masu cewa za su sami aminciwar Allah tawurin rayuwa na halin kirki ne da kiyaye hidimomin addini. BJ 251.2
Sa’anda Charles Wesley ya kamu da rashin lafiya, ya kuma ga kamar mutuwa tana zuwa, an tambaye shi a kan me ya dangana begensa na rai madawami. Ya amsa da cewa: “Na yi iyakar kokari na in bauta ma Allah” Sa’anda abokin da ya yi tambayar ya nuna kamar bai gamsu da amsar ba, Wesley ya yi tunani cewa: “Kai! Watau kokari na bai isa ya ba ni bege ba kenan? Yana so ya kwace kokarin nawa ne? Ba ni da wani abu dabam da zan dogara a kai kuma”. Yawan duhun da ya mallaki ekklesiya kenan, ya boye kafara, ya kwace ma Kristi daukakarsa, ya kuma juya zukatan mutane daga begensu kadai na ceto, watau jinin mai fansa giciyayye. BJ 251.3
An nuna ma Wesley da abokansa cewa addinin gaskiya yana cikin zuciya ne, kuma cewa dokar Allah ta shafi tunani har da kalmomi da ayuka kuma. Da suka amince cewa tsabtar zuciya da kyawawan halayyan da ake gani wajibi ne, sai suka dukufa neman sabuwar rayuwa. Ta wurin kwazo da addu’a suka yi kokarin danne muguntar zuciya ta mutumtakar; sun yi rayuwa ta musun-kai, da kauna, da kaskantar da kai, suna himma sosai wajen bin kowane matakin da suka ga kaman zai taimake su samun babban abin marmarinsu, watau tagomashi daga Allah. Amma basu sami abin da suka nema ba. A banza suka yi kokarin yantar da kansu daga hukumcin zunubi ko kuma su karya ikonsa. Fama dayan da Luther ya sha kenan a dakinsa a Erfurt. Tambaya dayan kenan da ta dami zuciyarsa. “Amma kaka mutum za shi barata wurin Allah? ” Ayuba 9:2. BJ 252.1
Wutan gaskiyar Allah da ta kusan mutuwa ta sake kunnuwa daga tocilan nan na da, wanda aka mika ma Kiristan Bohemia. Bayan Canjin, Kin bin ikon paparuma ya fatattaka a hannun dakarun Rum. Aka tilasta dukan wadanda suka ki rabuwa da bangaskiyarsu, suka gudu. Wadansun su suka sami mafaka a Saxony inda suka ci gaba da bangaskiya ta da din. Daga muryar wadanan Kiristan ne haske ya zo ma Wesley da abokansa. BJ 252.2
Bayan an shafi John da Charles Wesley cikin aikin bishara, aka aike su aikin mishan a Amerika. cikin jirgin akwai ‘yan Moravia an fuskanci munanan guguwa cikin tafiyar, sai John Wesley, da ya zo fuska da fuska da mutuwa, ya ji kawai ba shi da tabbacin salama da Allah. Akasin haka, Jamusawan suka nuna kwanciyar hankali da danganan da shi bai sani ba. BJ 252.3
Ya ce: “Da dadewa kafin nan na lura da irin halayyansu. Sun nuna saukin kai kowane lokaci, ta wurin yi ma sauran fasinja irin ayukan bauta da yan Ingilishi ba za su yarda su yi ba, basu kuma ce a biya su ba, suna cewa abinda suke yi yana da kyau don zukatansu na fahariya, kuma Mai-cetonsu mai kauna, ya yi masu abinda ya fi haka. Kowace rana kuma ta ba su damar nuna tawali’un da babu laifin da ke rage shi. Ko da an tura su, ko an buge su ko an jefar da su, sukan tashi ne su tafi abinsu, ba a ji kara daga bakinsu ba. Sai kuma zarafi ya zo don gwada ko an kubutar da su daga ruhun tsoro, da na girman rai ko fushi ko ramuwa. A tsakiyar wakar budewar sujadarsu sai teku ya rikice, ya tarwasa babban abin da ke sa iska ya sa jirgin ruwan ya ci gaba da tafiya, ya rufe jirgin, sa’anan ruwa ya fara zubowa cikin jirgin, sai ka ce tekun ya rigaya ya hadiye mu ne. Yan Ingila suka fara ihu mai yawa. Jamusawan nan suka ci gaba da wakarsu. Daga baya na tambayi dayansu, Ba ka ji tsoro ba? Ya amsa cewa, “Godiya ga Allah, babu! Na tambaye shi, “Amma matanku da ‘ya’yanku basu ji tsoro ba?” Ya amsa a hankali cewa, ‘Babu; matanmu da ‘ya’yanmu ba sa tsoron mutuwa.’” BJ 253.1
Sa’anda suka iso Savannah, Wesley ya zauna da yan Maravian nan na guntun lokaci, ya kuma yi sha’awar halayyansu na Kristanci sosai. Game da wata hidimarsu ta addini da ta bambanta da ta Ekklesiyar Ingila, ya rubuta; “Yawan saukin kai da kuma yin dukan hidimar ya kusa sa ni in manta shekaru dubu da dari bakwai da ke tsakani, na ga kaina kamar ina cikin taron nan da Bulus mai yin tent da Bitrus masunci suka shugabanta: ga Ruhu ga kuma iko.” BJ 253.2
Da ya koma Ingila, Wesley, tawurin koyaswar wani mai wa’azi dan Moravia, ya kara fahimtar bangaskiya ta Littafi. Ya gane cewa dole ne ya dena dogara ga ayukan kansa don ceto, ya kuma dogara ga “Dan rago na Allah mai dauke da zunubin duniya” kadai. A wani taron kungiyar yan Moravia a London, an karanta wata maganar Luther inda yake bayana Canjin da Ruhun Allah ke haifarwa cikin zuciyar mai bi. Yayin da Wesley ke sauraro, bangaskiya ta zo cikinsa, ya ce, “Na ji zuciya ta ta dimu sosai, na ji kawai na amince da Kristi, Kristi kadai, don ceto na: na kuma sami tabbaci cewa Kristi ya dauke zunubai na, ya kuma cece ni daga dokar zunubi da mutuwa.” BJ 253.3
Wesley da farko ya kwashe shekaru yana fama da musun kai da shan zargi da cin mutunci cikin kokarinsa na neman Allah. Yanzu ya same shi, ya gane kuma cewa alherin da ya yi ta faman nema ta wurin addu’a da azumi da ba da sadaka da musun kai, ashe kyauta ce, ba da kurdi ba, kuma ba da farashi ba. BJ 254.1
Da ya kafu cikin bangaskiyar Kristi, ruhun sa ya motsu da marmarin baza sanin bisharar alherin Allah. Ya ce: “Ina ganin dukan duniya kamar coci na ne, duk inda nike, ina gani ya dace, kuma daidai ne, aiki na ne in shaida ma dukan wadanda suke so su ji labari mai dadi na ceto.” Ya ci gaba da rayuwarsa ta musun kai, a matsayin sakamakon bangaskiya; ba tushen tsarkakewa ba, amma sakamakonsa. Alherin Allah cikin Kristi shi ne tushen begen Kirista, kuma za a nuna wannan alherin tawurin biyayya ne. Wesley ya ba da ransa ga wa’azin muhimman gaskiya da ya karba ne barata tawurin bangaskiya cikin jinin kafara na Kristi, da kuma ikon sabontawa na Ruhu Mai-tsarki kan zuciya wanda ke haifar da ‘ya’ya ga rayuwar da ta yi daidai da kwatancin Kristi. BJ 254.2
An shirya Whitefield da su Wesley domin aikinsu, tawurin ganewarsu da dadewa cewa su kan su batattu ne, kuma cewa za su iya jimre wahala kamar sojojin Kristi, sun rigaya sun sha ba’a da raini da zalunci, a jami’a da kuma sa’anda suke shiga aikin bishara. Su da wadansu kalilan da suka tausaya masu, yan’uwansu dalibai, marasa sanin Allah, suka rada masu sunar ba’a wai Methodist, sunan da a zamanin nan ake gani da daraje ga daya daga dariku mafi girma a Ingila da Amerika. BJ 254.3
A matsayinsu na yan Ekklesiyar Ingila, sun manne ma tsare tsoranta na sujada sosai, amma Ubangiji ya nuna masu hanya mafi inganci cikin maganarsa. Ruhu Mai-Tsarki Ya umurce su su yi wa’azin Kristi giciyayye. Ikon Madaukaki ya bi aikinsu. Dubbai suka amince suka kuma tuba. Ya zama wajibi a tsare tumakin nan daga kerketai. Wesley bai yi tunanin kafa sabuwar darika ba, amma ya shirya su kalkashin abin da ya kira “Methodist Connection.” BJ 255.1
Hamayyar da masu wa’azin nan suka fuskanta daga hannun ekklesiyar kasa babba ce mai ban mamaki kuma, duk da haka Allah cikin hikimarsa Ya canja alamura Ya sa canji ya fara daga cikin ekklesiyar kanta. Da daga waje kadai canjin ya zo, da bai shiga inda aka bukace shi sosai ba. Amma da shike masu wa’azin falkaswan yan ekklesiyar ne, kuma sun yi aiki cikin ekklesiyan ne duk inda suka sami zarafi, gaskiya ta sami shiga ta inda da kofofin sun kasance a kulle. Wadansu masu aikin bishara an falkas da su daga barcin ruhaniya suka zama masu wa’azi a ekklesiyoyin da suke mulki. Ekklesiyoyin da suka kangare cikin rashin ruhaniya suka falka. BJ 255.2
A zamanin Wesley, kamar dukan sararakin tarihin ekklesiya mutane masu baye baye dabam dabam suka yi aikin da aka basu. Basu sami ra’ayi daya game da kowace koyaswa ba, amma Ruhun Allah Ya motsa kowa, suna kuma hada kai wajen ribato rayuka domin Kristi. Bambance bambance tsakanin Whitefield da yaran Wesley sun so su jawo rabuwa a wani lokaci, amma yanzu da suka koyi tawali’u a makarantar Kristi, hakuri da juna da kauna sun sasanta su. Ba su da lokacin jayayya yayinda kuskure da zunubi ke habaka ko ina, masu zunubi kuma suna nutsewa cikin hallaka. BJ 255.3
Bayin Allah sun yi tafiya a mawuacin hanya ne. Masana da masu martaba suka yi anfani da ikonsu don sabani da su. Daga baya wadansu ma’aikatan bishara suka nuna magabtaka kwarai, aka kuma rufe kofofin ekklesiyoyi daga bangaskiya mara aibi da masu shelarta. Zarginsu daga bagadi da ma’aikatan bishara suka rika yi ya falkas da duhu da jahilci da zunubi. Akai akai John Wesley ya rika tsere ma mutuwa tawurin al’ajibin alherin Allah. Sa’anda aka ta da fushin yan iska a kansa, kuma ba alamar hanyar tsira, malaika cikin kamanin mutum yakan zo kusa da shi, yan iskan kuma sukan ja da baya, sai bawan Allah ya wuce lafiya daga wurin hatsarin. BJ 256.1
Game da kubutarwarsa daga yan iska a wani lokacin, Wesley ya ce, “Da yawa sun yi kokarin tura ni a kasa yayin da muke gangarawa wata hanya mai-tsantsi zuwa garin, da sanin cewa idan har na kai kasa, ba zan tashi kuma ba. Amma ko tuntube ban yi ba, ko tsantsi ma bai ja ni ba, har na tsere gaba daya daga hannunsu … ko dashike da yawa sun so su kama kwala ta ko riga na, su ja ni kasa, basu iya rikewa ba sam: mutum daya ne kadai ya iya rike shafin kwat di na, na kuma bar mashi a hannunsa; daya shafin, inda akwai takardar kurdi, ya yage rabi ne kawai, wani mutum daga baya na ya yi ta duka na da katon sanda, wadda in da ya buga ni sau daya a keyata, da bai sha wani wahala kuma ba. Amma kowane lokaci, akan kawar da bugun, ban san ta yaya ba, don ban iya kaucewa dama ko hagu ba. Wani kuma ya zo a guje, ya kutsa ta cikin jama’ar, ya kuma daga hannu zai kai duka, amma kuma ya saukar nan da nan, sai dai ya shafa kai na ne kawai, yana cewa: “Ji laushin sumansa!” … Wadanda zukatansu suka fara tuba jarumawan garin ne, shugabannin yan iskan, dayansu kuwa shahararren mai fada ne a mashaya.… BJ 256.2
“A hankali Allah ke shirya mu don nufinsa! Shekara biyu da suka wuce, wani gutsuren tubali ya kuje mani kafada, shekara daya bayansa, dutse ya buge ni a sakanin idanu na. Watan da ya wuce an naushe ni sau daya, da yamman nan ma na sami saushi biyu, daya kafin mu shigo gari, daya kuma bayan mun fita; amma dukansu biyu kamar ba komai ba ne: gama ko dashike wani mutum ya buge ni a kirji da dukan karfinsa, dayan kuma a baki da karfin da ya sa jini ya bulbulo nan da nan, ban ji zafin kowane bugun ba, kamar ma da tsinke suka taba ni.” BJ 257.1
Yan Methodist na kwanakin farko, pastoci da membobi, sun sha wulakanci da zalunci a hannun membobin ekklesiya da marasa addini wadanda karyar membobin ta fusata. An gurbabar da su a gaban kotunan kasa, inda ba a cika samun adalci ba a wancan zamanin. Sau da yawa sun sha duka a hannun masu tsananta masu. ‘Yan iska sun dinga bi gida gida suna lalata kayan daki, da dukiya, suna kwasar ganiman duk abinda suka ga dama, suna kuma cin zarafin maza da mata da yara. A wadansu lokuta an rika manna sanarwa ga jama’a, ana kira ga masu so su taimaka wajen fasa tagogi da yin fashi a gidajen yan Methodist, su taru a wani wuri daidai wani lokaci. Ketarenwar dokokin mutum da na Allah hakanan sun rika faruwa ba tare da ko tsautawa ba. Aka rika cin zalin mutanen da laifinsu kadai shi ne kokarin da suka yi na kau da masu zunubi daga hanyar hallaka zuwa hanya mai-tsarki. BJ 257.2
Game da zarge zargen da aka yi ma John Wesley da abokansa, ya ce: “Wadansu suna cewa koyaswoyin mutanen nan karya ne, kuskure ne, kuma sha’awa ce kawai; wai sabobi ne da ba a ta ba ji b a sai kwanan nan, cewa kowane bangaren koyaswan nan ainihin koyaswar littafi ne da ekklesiyarmu ta fasarta. Sabo da haka ba za ta zama karya ko kuskure ba, muddan dai Littafi gaskiya ce. “Wadansu suna cewa: ‘koyaswarsu ta cika tsanani; suna sa hanyar sama ta zama matsatsiya da yawa. ‘Da gaske kuma wannan ne ainihin zargin, kuma shi ne ginshikin zarge zarge dubu da ke daukan kamani dabam dabam. Amma tana kara matsuwar hanyar sama fiye da yadda Ubangijinmu da manzaninsa suka tsara ta? Ko tasu koyaswa ta fi Littafin tsanani? A dubi nassosi kalilan kawai: ‘Ka yi kamnar Ubangiji Allahnka da dukan zuchiyarka, da dukan ranka, da dukan azanchinka; ‘kowace maganar banza da mutane ke fadi, a chikin ranar shari’a za su ba da lissafinta.’ ‘Ko kuna chi fa, ko kuna sha, ko kwa iyakar abinda ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.’ BJ 257.3
“Idan koyaswarsu tafi wannan tsanani, laifinsu ne; amma kun sani cikin lamirinku cewa ba ta fi ba. Kuma wa zai yi karancin tsananin, komi kankanta, ba tare da lalata maganar Allah ba? Ko za a iske wani wakilin Allah da aminci idan ya canja wani fanni na ajiyan nan mai-tsarki? Babu. Ba zai iya rage komai ba, ba zai iya sassauta komai ba, ana bukatar shi ya sanar ma dukan mutane cewa, “Ba zan iya saukar da Littafin zuwa inda kuke so ba. Dole ku hau zuwa wurinsa, ko kuma ku hallaka har abada. Wannan ne ainihin dalilin abin da ake ta fadi game da rashin kauna da mutanen nan suke da shi. Rashin kauna, haka suke? Ta wace hanya? Ba sa ciyar da mayunwata, ba sa kuma suturta marasa tufafi? “Babu, ba maganan kenan ba: suna dukan wadannan: amma suna da rashin kauna wajen shar’anta mutane! Suna gani kamar ba wanda zai iya samun ceto sai ‘yan kungiyarsu.” BJ 258.1
Lalacewar ruhaniya da ta mamaye Ingila gaf da lokacin Wesley sakamako ne na koyaswar cewa ta wurin bangaskiya kadai ake samun ceto, kuma wai ayukan kiyaye doka ba su da wani anfani ma game da ceto. Da yawa sun koyar da cewa Kristi ya warware dokoki goman anan, sa’an nan wai ba wajibi ne ga Kirista su kiyaye doka ba, cewa wai an yantar da mai ba da gaskiya daga “bautar nagargarun ayuka.” Wadansu da suka amince da dawamar dokar, suka koyar da cewa wai ba lallai ne ma’aikatan bishara su bukaci mutane su yi biyayya ga kaidodinta ba, da shike wadanda Allah ya zabe su sami ceto, tawurin alherin Allah wanda, ba za su iya ki ba, za a bishe su zuwa ayukan ibada da halayyan kirki, yayin da wadanda aka kadara zuwa ga hallaka ta har abada kuwa ba su da ikon yin biyayya ga dokar Allah.” BJ 258.2
Wadansu da suka gaska ta cewa “zabbabu ba za su iya faduwa daga alherin Allah ko kuma su rasa tagomashin Allah ba,” sun kuma koyar da cewa “miyagun ayukan da su ke aikatawa ba zunubi ne ainihi ba, ko kuma abin da za a ce da su ketarewar dokar Allah, kuma cewa, saboda haka, ba su da dalilin furta zunubansu ko kuma su rabu da su ta wurin tuba.” Saboda haka suka sanar cewa ko daya daga zunubai mafi muni “wanda ko ina ana gani babban ketarewar dokar Allah ne, ba zunubi ne ba a ganin Allah,” idan daya daga cikin zabbabu ne ya aikata, “domin, daya daga cikin muhimman halayyan zababbu kenan da ya bambanta su, cewa ba za su iya yin wani abin da Allah ba ya so ko kuma doka ta hana ba.” BJ 259.1
Wadannan munanan koyaswoyin daidai suke da koyaswar sananun mallamai da masanan hauhidi - cewa ba wata dokar Allah mara canjawa a matsayin ma’aunin cancanta, amma cewa jama’a ne kansu suke tsara ma’aunin cancanta, kuma a kullum ana canja shi. Dukan wadannan ra’ayoyi ruhu dayan ne ke ba da su - shi wanda ko cikin mazamnan sama marasa zunubi, ya fara aikinsa na neman rushe kaidodi masu tsarki na dokar Allah. BJ 259.2
Koyaswar cewa umurnin Allah yana kafa halayen mutane yadda ba za’a iya canjawa ba, ta kai mutane inda kusan sun ki dokar Allah ma. Wesley ya yi jayyaya da kurakuran masu koyar da zancen ceto tawurin alheri kawai, kuma doka ba ta da anfani, yak uma nuna cewa koyaswar ta saba ma Littafin. “Alherin Allah ya bayana, mai-kawo ceto ga dukan mutane” “Wannan mai-kyau ne abin karba kwa ga Allah mai chetonmu; shi wanda yake nufi dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya. Gama akwai Allah daya, matsakanchi daya kuma tsakanin Allah da mutane, shi kwa mutum ne, Kristi Yesu wanda ya ba da kansa pansar dukan mutane.” Titus 2:11; 1 Timothawus 2:3-6. Ana ba da Ruhun Allah kyauta domin kowane mutum shi iya kama hanyar ceto. Don haka, Kristi, hasken gaskiyan, “yana haskaka kowane mutum, yana zuwa chikin duniya.” Yohanna 1:9. Mutane suna rasa cetonsu tawurin kin kyautar rai da su kansu suke yi ne. BJ 259.3
Don amsa koyaswan nan cewa wai daga mutuwar Kristi an kawas da dokoki goman tare da dokokin bukukuwa, Wesley ya ce; “Dokoki goma din nan, wanda annbawa suka kiyaye, Allah bai kawar ba. Bai zo don warware su ba ne. Wannan kundin doka ne da ba za a iya karya shi ba, wanda ya tsaya sosai a matsayin amintacen shaida a sama… Wannan tun kafuwar duniya, aka rubuta shi, ba kan allon dutse ba, amma a zukutan dukan ‘ya’yan mutane, sa’anda suka fito daga hannuwan mahalicin. Kuma komi yawan sharewa da zunubi ke yi ma bakaken da Allah ya rubuta da yatsansa, duk da haka ba za a iya share su gaba daya ba, muddan muna da sanin nagarta da mugunta. Dole kowane sashin dokan nan ya kasance da iko kan mutane duka, a dukan sararaki, cewa basu dangana ga lokaci ko wuri ba, ko kuma wani yanayi da kan iya canjawa ba, amma kan yanayin Allah, da yanayin mutum, da dangantakarsu da juna, mara sakewa. BJ 260.1
“Ban zo domin in warware ba, amma domin in chichika.” … Ba shakka, nufinsa a nan shine, Na zo domin in tabbatar da ita ne duk cikar ta, duk dai da dukan kyaliyar da mutane ke yi: na zo ne in bayyana a fili duk wani abinda ke da wuyan ganewa a ciki; na zo ne in bayyana ma’anar kowane bangarenta, in nuna tsawo da fadin kowane doka cikin kundin, da kuma bisa da zurfinta, tsarki da ruhaniyarta cikin kowane fanninta.” BJ 260.2
Wesley ya sanar da rashin sabanin doka da bishara. “Sabo da haka awai dangantaka mafi karfi tsakanin doka da bishara. A bangare guda dokar tana ba bishara fifiko, tana kuma nunawa zuwa ga bishewar, a daya bangaren kuma, bishara tana bishemu kullum zuwa ainihin cikawar dokar. Misali, dokar tana kai mu ga kaunar Allah ne, mu kaunaci makwabcin mu, mu zama masu tawali’u da saukin kai, ko tsarki. Muna gani kamar ba za mu iya yin wadannan ba, hakika kam, ga mutum, ba mai yiwuwa ba ne mamma Allah Ya yi alkawain ba mu kaunan nan, zai kuma mai da mu masu saukin kai da tawali’su da tsarki; sai mu kama bisharan nan, labarin nan mai dadi; akan yi mana bisa ga bangaskiyarmu ne; kuma adalcin dokar yana cika cikin mu tawurin bangaskiya da ke cikin Kristi Yesu ne. BJ 261.1
Wesley yace: “Cikin mafi magabtaka da bisharar Kristi, akwai wadanda a fili suke shar’anta dokar kanta, suna neman zargin dokar; suna koya ma mutane su ketare dokokin gaba daya…. Mafi ban mamaki aikin Yahuda ya yi ne lokacin da ya ce, ‘A gaishe ka, Rabbi’, ya yi ta yi masa sumba, kuma Yesu zai iya ce ma kowane dayansu, ‘Da sumba ka ke chin amanar Dan mutum?’ Cin amanarsa da sumba ne idan an yi zancen jininsa, amma aka dauke rawaninsa, a rage karfin wani bangaren dokarsa, da sunan taimakon bishara. Kuma ba wanda zai kauce ma zargi nan idan yana wa’azin bangaskiya ta hanyar da ke soke zancen biyayya, idan yana wa’azin Kristi ta yadda yana soke mafi kankantar dokar Allah, ko rage karfinta. BJ 261.2
Ga masu wa’azin cewa “wa’azin bishara yana amsa kowace doka,” Wesley ya amsa: “Ba mu yarda da wannan ba, sam. Bai amso manufar farko na dokar ma, watau, nuna ma mutane zunubin su, falkas da wadanda ke cikin barci gaf da lahira. “Manzo Bulus ya bayana cewa ta wurin doka ake sanin zunubi, kuma sai mutrun ya gane zunubinsa zai ji bukatarsa t jinin kafara na Kristi…. Ubangijinmu kansa ya ce: “Masu lafiya ba su da bukatar mai-magani ba; sai dai masu chiwuta.” Saboda haka ba daidai ba ne a mika ma masu lafiya mai-magani. Za ka fara tabbatar masu ne cewa suna da ciwo, in ba haka ba, ba za su gode maka da wahalar ka ba. BJ 262.1
“Haka kuma kuskure ne a mika ma masu tsabtar rai Kristi, su kuwa basu ta ba ba,” sabo da haka yayin da yake wa’azin alherin Allah, Wesley, kamar mai-gadonsa, ya so ya dadada dokar ne ya girmama ta. Da aminci ya aiwatar da aikin da Allah ya ba shi, kuma sakamako masu daraja aka ba shi zarafin gani. A karshen rayuwarsa mai tsawon shekara tamanin - wanda yafi rabin karni yana aikin bishara - wadanda suka bayana goyon bayansu sun zarce mutum rabin miliyan. BJ 262.2
Amma jama’a da tawrin aikinsa aka fitarda su daga hallakar zunubi zuwa rayuwa mafi inganci da tsarki, da wadanda tawurin koyaswarsa suka sami dandano mafi anfani da inganci, ba za a taba iya sanin yawansu ba, sai an tara dukan iyalin fansassu a mulkin Allah. Rayuwarsa darasi ne mai tamani mara iyaka ga kowane Kirista. Da dai ya iske irin bangaskiya da saukin kai, da himma da sadakar da kai da daukufar wannan bawan Allah cikin ekklesiyoyi na yau! BJ 262.3