Cikin karni na sha shidda, Canjin da ta gabagtar da budediyar Littafi ga duniya, ya so ya shiga dukan kasashen Turai, wadansu kasashe suka karbe shi da murna, kamar dan sakon sama. A wadansu kasashe, tsarin paparuma ta hana Canjin shiga sosai, hasken sanin Littafi kuma da tasirinsa, kadan kawai aka samu. A wata kasar, ko dashike hasken ya shiga, duhu bai fahimce shi ba. Gaskiya da kuskure sun dinga fadan neman fifiko. A karshe mugunta ta yi nasara, aka kuma jefar da gaskiya waje. “Shari’a fa kenan, haske ya zo chikin duniya, amma mutane suka fi son dufu da haske.” BJ 263.1
Yakin da aka yi tsakanin Littafin a Faransa har tsawon daruruwan shekaru, ya kai ga Babban Tawayen nan. Mumunan al’amarin nan sakamoko ne kai tsaye na danne Littafin da Rum ta yi. Ya nuna a fili sakamakon manufar tsarin paparuma-kwatancin sakamakon da koyaswar ekklesiyar Rum ke shirgawa har tsawon shekaru dubu. BJ 263.2
Annabawa sun yi annabcin dannewar Littafin a lokacin daukakar paparuma; mai ruya kuma ya nuna sakamakon da danniyar “mutumin zunubi” za ta jawo musanman ga Faransa. BJ 264.1
Malaikan Ubangiji ya ce: “Gama an bayas ga al’ummai: za su tattake birni mai-tsarki kalkashin sawaye wata arba’in da biyu. Kuma zan ba shaiduna biyu iko, su yi annabci kuma kwana dubu da metin da sattin, a yafe chikin gwado…. Sa’anda suka gama shaidarsu kuma, bisan da ke fitowa daga chikin rami mara matuka za ya yi gaba da su, za ya rinjaye su, ya kashe su kuma. Gawansu kuma suna nan kwanche chikin karabkar babban birni, wand ake che da shi a ruahaniya Saduma da Masar, inda aka gichiye Ubangininsu kuma…. Kuma wadanda su ke zamane a duniya suna murna a kan su, suna ta nishatsi: za su aike da kyautai kuma zuwa ga junansu; domin wadannan annabawa biyu suka azabadda mazamnan duniya. Bayan kwana uku din da rabi, lumfashin rai daga wurin Allah ya shiga chikinsu, suka tsaya bisa kafafunsu; babban tsoro fa ya fada ma wadanda suka gan su.” Ruya 11:2; 11 BJ 264.2
Lokaci da aka ambata a nan - “wata arba’in da biyu” da “kwana dubu da metin da sattin” - daya ne, suna kuma matsayin likacin da ekklesiyar Kristi za ta sha danniya daga Rum. Shekaru 1260 na mulkin paparuma sun fara a AD 538 ne suka kuma kare a 1798. A wannan lokacin (1798) dakarun Faransa suka shiga Rum suka kuma mai da paparuma fursuna, ya kuma mutu cikin hijira, ko da shike an zabi sabon paparuma nan da nan, mulkin paparuma bai sake samun irin ikon da yake da shi da ba. BJ 264.3
Tsananta ma ekklesiya bata ci gaba cikin dukan shekaru 1260 din ba. Allah cikin jinkansa ya takaita lokacin wahalar mutanensa. Sa’anda yake annabcin “kunchi mai girma” da zai abko ma ekklesiya, Mai- ceton ya ce: “kuma da ba domin mun gajartadda wadanan kwanaki ba, da ba mai-rai da za ya tsira ba: amma sabili da zababbu, za a gajertadda su.” Matta 24:22. Tawurin tasirin Canjin, tsanantawar ta kare kafin 1798. BJ 264.4
Game da shaidu biyu din, annabin ya ce: “Wadannan su ne itatuwa noui na zaitun, da fitilla biyu suna tsaye a gaban Ubangijin duniya. “Maganarka fitilla che ga sawayena, haske ne kuma a tafarkina. Ruya 11:4; Zabura 119:105. Shaidu biyu din suna matsayin Tsohon Alkawali da Sabon Alkawali ne. Dukansu muhimman shaidu ne na tushen dokar Allah da dawamar ta kawai. Dukansu kuma shaidu ne na shirin ceto. Alamu da hadayu, da annabce annabcen Tsohon Alkawali suna nunawa zuwa ga Mai-ceto da za ya zo. Linjila da Wasikun Sabon Alkawali suna maganar Mai-ceto da ya zo daidai yadda alamu da annabci suka fada ne. BJ 265.1
Za “su yi annabchi kuma kwana dubu da metin da sattin a yafe chikin gwado.” Yawancin wannan lokacin shaidun Allah sun kasance yanayin duhu-duhu. Mulkin paparuma ya so ya boye ma mutane maganar gaskiya, ya kuma ajiye shaidun karya a gabansu don karyata shaidar maganar gaskiyar. Sa’anda masu iko na addini da na kasa suka hana bazawar Littafin, sa’anda aka tankware shaidarsa, mutane da aljannu kuma suka yi iyakar kokari don juya zukatan mutane daga wurinta; sa’anda wadanda aka rika farautarta, masu shelarsa, ana cin amanarsu, ana azabar da su, ana kuma bizne su a kurkuku da ramuka ko kogon kasa, ana kashe su saboda bangaskiyarsu, ko kuma a tilasta su gudu zuwa sansani na duwatsu, a lokacin ne amintattun shaidun suka yi annabci yafe da gwado. Duk da haka suka ci gaba da shaidarsu duk tsawon shakaru 1260 din. A zamanu mafi duhu akwai amintattun mutane da suka kaunaci maganar Allah, suka kuma yi kishin daukakarsa. Ga wadannan amintattun bayin aka ba da hikima, da iko da karfi don sanar da gaskiyarsa cikin dukan wannan lokacin. BJ 265.2
“Idan kwa kowane mutum yana so ya chiwuche su, wuta na fitowa daga bakinsu tana chinye makiyansu: idan kuma kowane mutum yana so ya chiwuce su, dole hakanan za a kashe shi.” Ruya 11:5. Mutane ba za su iya taka maganar Allah hakanan kawai ba sakamo ba. Surar karshe ta littafin Ruya ta bayana ma’anar wannan la’anar inda ta kai. “Ina shaida ma kowane mutum wanda yake jin zantattukan annabchi na wannan littafi, idan kowane mutum ya kara bisa garesu, Allah za ya kara masa alobai wadanda aka rubuta chikin wannan litaffi kuma idan kowanne mutum ya dauki wadansu daga chikin zantatukan litafin wannan annabchi, Allah za ya kawas da rabonsa daga chikin itache na rai, daga chikin birni mai-tsaarki kuma, watau daga chikin abin da aka rubuta chikin wannan litafi?” Ruya 22:18,19. BJ 266.1
Irin kashedin da Allah ya ba mutane kenan don tsaronsu daga canja abin da Shi ya bayana ko kuma ya urmurta. Wannan la’anar sun shafi dukan wadanda tawurin tasirinsu suke sa wadansu su yi wasa da dokar Allah. Ya kamata kashedin nan su ba da tsoro ga masu cewa wai kiyayya ko rashin biyayya ga dokar Allah wani muhimmin abu ba ne. Dukan masu daukaka ra’ayinsu bisa abinda Allah ya bayana, dukan masu canja ma’anar maganar Allah don cim ma burin kansu, ko kuma domin daidaituwa da duniya suna jawo ma kansu sakamako mai ban tsoro ne. Rubuttaciyar Kalmar dokar Allah, za ta gwada halin kowane mutum ta kuma hukumta wadanda ta iske da laifi. BJ 266.2
“Sa’anda suka gama [suke karasa] shaidarsu.” Lokacin da shaidu biyu din za su yi annabci yafe da gwado ya kare a 1798 ne. Yayinda suka kusa karshen aikinsu cikin yanayin duhu-duhu, ikon da aka kamanta da “bisan da ke fitowa daga rami mara matuka,” zai yake su. A kasashen Turai da yawa, ikokin da suka yi mulkin ekklesiya da na kasa Shaitan ya yi daruruwan shekaru yana mulki kansu ta wurin tsarin paparuma. Amma a nan ana maganar bayanuwar wani iko ne na Shaitan. BJ 266.3
Da manufar Rum ne ta kulle Littafin cikin wani harshe da ba a sani ba, a kuma boye shi daga mutane. Kalkashin mulkin ta shaidun sun yi annabci “yafe da gwado,” Amma wani ikon kuma — bisan nan daga rami mara matuka — zai taso, yay i yaki a fili kai tsaye ka maganar Allah. “Babban birnin,” “wadda a karabkar ta aka kashe shaidun, kuma inda gawansu suna kwance, a ruhaniya” shi ne Masar. A dukan al’ummai na tarihin Littafin, Masar ce ta fi musun kasancewar Allah Mai rai ta kuma yi tsayayya da umurninsa ba tsoro. Ba sarkin da ya taba gwada tawaye a fili da girman rai kuma sabanin ikon Allah kamar yadda sarkin Masar ya yi. Sa’anda Musa ya kawo masa sakon, a cikin sunan Ubangiji, Firauna ya amsa da alfarma cewa; “Wane ne Ubangiji, har da an ji muryatasa in saki Israila kuma? Ni ban san Ubangiji ba, ba kwa zan saki Israila ba.” Fitowa 5:2. Wannan kafirci ne, kuma al’ummar da aka misalta da Masar za ta furta irin bijirewan nan ma. Allah Mai-rai, ta kuma nuna wannan irin ruhun, na kafirci da tumbe. An kuma kamanta babban birnin na ruhaniyan da Saduma [Sodom]. Lalacewar Saduma wajen ketare dokar Allah ya fi bayanuwa musamman ta wajen fasikanci ne. Kuma wannan zunubin zai zama babba cikin halayyan al’ummar da za ta cika wannan nassin. BJ 267.1
Bisa ga maganar annabin, sa’an nan, gaf da shekara ta 1798 wani mulki mai asali daga Shaitan da kuma irin halinsa, zai taso ya yi yaki da Littafin. Kuma a kasar da za a bice maganar Allah hakanan, za a ga kafircin Fir’auna da fasikancin Saduma. BJ 267.2
Wannan anabcin ya cika daidai a tarihin Faransa. Lokacin Juyin danwaken, cikin 1793, “sau na fari duniya ta ji taron mutane, wadanda aka haife su aka kuma ilimantar da su cikin wayewan kai, masu cewa kuma wai suna da ‘yancin yin mulkin daya daga al’ummai mafi kyau a Turai, suka ta da muryarsu, suka ki gaskiya mafi girma da mutum ke karba ba hamayya, suka kuma ki bangaskiya da sujada ga Allah.” Faransa ce kadai al’ummar duniyan nan da maganar ta dace da ita, cewa kamar al’umma, ta daga hannun ta, ta yi tawaye a fili sabanin mahalicin dukan halitta. Akwai masu sabo da yawa, da kafirai da yawa, da kuma har yanzu akwai su a Ingila da Jamus, da Spain, da sauran wurare, amma Faransa ta yi suna a tarihin duniya a matsayin kasa daya tilo da, tawurin dokar Majalisar Dokokinta, ta furta cewa wai babu Allah, wadda kuma dukan mutanen da ke babban birnin kasar, tare da yawancin sauran mutanen, mata da maza, suka yi rawa suna waka da murna wajen amincewa da sanarwar.” BJ 267.3
Faransa ta kuma nuna irin halayyan da suka bambanta Saduma. Lokacin juyin danwaken, an nuna yanayin fasikanci da lalacewar hali irin wadanda suka kawo hallaka ga biranen Saduma da Gomorrah. Mai-tarihin yana bayana kafirci da fasikancin Faransa yadda aka bayana a annabcin cewa; “Itace da dokokin nan game da addini, akwai dokar da ta rage dawamar aure-dangangaka mafi tsarki da yan Adam za su iya samu, wadda dawamar ta ke jawo karfafawar zaman tare, an rage ta, ta zama yarjejjeniya kawai mara dadewa, wadda mutum biyu za su iya sa hannum su kuma warware shi yadda suka ga dama. Ko da aljannu ne suka hada kai don gano hanya mafi tabbaaci don hallaka duk wani abu mai-tsarki, mai ban sha’awa ko mai dawama a rayuwar iyali, su kuma sami tabbaci cewa illar da suke so ta samu za ta dawama daga sara zuwa sara, aljannun nan da basu iya kirkiro wani shiri kamar rage darajar aure ba… Sophie Arnnoult, mai wasan kwaikwayo da ta yi suna tawurin ababan nuna hikima da takan rika fadi, da bayana irin auren nan “bukin zina mai-tsarki.” BJ 268.1
“Inda aka giciye Ubangijinmu kuma” Faransa ta kuma cika wannan fannin annabcin. Ba kasar da aka fi nuna ruhun magabtaka da Kristi a fili. Ba kasar da gaskiya ta fuskanci jayayya mafi daci da mugunta. Cikin zaluncin da Faransa ta yi ma masu goyon bayan bishara, ta giciye Kristi tawurin giciye almajiransa. BJ 269.1
Karni bayan karni aka rika zub da jinin tsarkaka. Sa’anda Waldensiyawa suka ba da rayukansu a kan duwatsun Piedment “domin maganar Allah da shairdar Yesu Kristi, yanuwansu Albigensiyawan Faransa ma sun ba da irin wannan shaidar na gaskiya. A zamanin Canjin an yi ta kashe almajiransu da azaba mai-tsanani. Sarakuna da fadawa, manyan mata da kananan ‘yan mata, abin alfarma da mutuncin kasar, sun kalli azabar wadanda aka kashe don Yesu. Hugeunots masu karfin zuciyan nan da suka sha fama don ‘yancin dan Adam mafi muhimanci, sun zub da jininsu a fagen fama da yawa. Aka mai da masu Kin ikon paparuma marasa bin doka, aka sa farashi a kansu, aka kuma yi farautarsu kamar namomin jeji. BJ 269.2
“Ekklesiyar cikin Hamada,” watau tsirarun zuriyar Kiristan da suka rage a Faransa a karni na sha takwas, da suka buya a duwatsun kudu, sun rike sha’awarsu ta bangaskiyar Ubaninsu. Idan suka gwada saduwa da dare a gefen dutse ko cikin ciyawa, muggan dabbobi sukan kore su, ko kuma a ja su a kai wurin bauta har tsawon rayuwarsu. Yan Faransa mafi tsarki, mafi wayewa, mafi hikima kuma aka rika daure su da sarka cikin azaba mai-tsanani, a tsakanin mafasa da masu kisan kai. Wadanda aka tausaya masu aka rika harbinsu da bindiga har lahira yayinda suna durkushe suna addu’a, ba komai a hannunsu. Daruruwan tsofofi da mata da yara aka rika kashewa a wurin saduwarsu. Yayinda suke ketare wurin saduwansu, ba abin mamaki ba ne a iske “kasarsu da aka kankare da takobi da gatari da wutan yayi aka mai da shi wani babban daji mai fadi mara haske.” An tabka muguntan nan fa ba a zamanin jahalliya ba ne, amma a zamanin haske na Louis XIV. A lokacin, kimiyya ta yadu, ilimi ya habaka, shugabannin kotu da na kasa masana ne masu kaifin baki, kuma suna yawan nuna cewa su masu tawaliu da kauna ne.” BJ 269.3
Amma mafi muni cikin laifuka da ayukan munanan sararakin shi ne kisan kiyashi na St. Batholomew. Har yanzu duniya tana tuna wannan mumunar mugunta mai ban kyama kuwa. Sarkin Faransa, da zugin Priestocin Rum, ya ba da yardarsa aka aikata wannan danyen aikin. Kararrawa aka rika bugawa da tsakar dare, alamar fara kashe kashen. An rika jan dubban masu Kin ikon paparuma daga barcinsu a gidajensu, ba zato ba tsamnni, aka dinga kashe su cikin ruwan sanyi. BJ 270.1
Kamar yadda Kristi ya shugabanci mutanensa daga bautar Masar, haka kuma Shaitan ya shugabanci mutanensa cikin wannan mumunan aiki na kisan masu bangaskiya. Kwana bakwai ana kisan kiyashin nan a Paris, kuma ba a birnin kadai aka yi shi ba, amma bisa ga umurnin sarki musamman, an yi shi a larduna da garuruwan da aka iske ‘yan Kin ikon paparuma ma. Ba a damu da shekaru ko jinsi ba. Ba a bar jinjiri ko tsoho ba. Atajiri da talaka, tsofafi da matasa, uwa da ‘ya’ya, aka karkashe su duka. An ci gaba da kashe kashen nan ko ina a Faransa har tsawon wata biyu. Mutum dubu saba’in aka hallaka. BJ 270.2
“Sa’anda labarin kisan ya kai Rum, ma’aikatan ekklesiya suka yi murna ba iyaka. Dan majalisar paparuma daga Lorraine ya ba dan sakon da ya kawo labarin ladar rawani dubu; shugaban St. Angelo ya yi ihun gaisuwar bangirma; aka buga kowace kararrawar coci, hasken wuta da aka rika kunnawa na tayoyi da sauransu ya mai da dare rana, kuma Gregory X111, tare da ‘yan majalisa da wadansu shugabannin ekklesiya, suka yi jerin gwano zuwa majami’ar St. Louis, inda dan majalisar Lorraine ya raira yabon Allah.… aka manna lambar yabo don tuna kisan kiyashin, kuma a Vatican ana iya ganin zanen Vasari guda uku da ke bayyana harin a kan shugaban jiragen teku, da na sarkin a cikin majalisa yana shirya kisan, da kisan kan ta. Gregory ya aika ma Charles Furen Zinariya; wata hudu bayan kisan kuma, … ya saurari wa’azin wani priest dan Faransa inda ya yi magana game da ranan nan cike da murna da farinciki da uba mafi tsarki ya sami labarin, ya kuma shiga yanayin saduda don yin godiya ga Allah da St. Louis.” BJ 270.3
Ruhun da ya zuga kashe kashen St. Louis shi ne ya ruhu dayan da ya zuga ababan da aka yi lokacin juyin danwaken. Aka ce Yesu Kristi sojan gona ne, kuma taken kafiran Faransa a lokacin shi ne, “A murkushe Dan Banzan,” watau Kristi kenan. Sabo na raini ga Allah, da mugunta na ban kyama, aka dinga yi tare, kuma aka girmama ‘yan iska da ‘yan banza da miyagu sosai. Cikin dukan wannan, Shaitan ne aka daukaka shi, amma Kristi cikin halayyansa na gaskiya da tsarki da kuma mara son kai, aka giciye Shi. BJ 271.1
“Bisan da ke fitowa daga chikin rami mara matuka za ya yi gaba da su, za ya rinjaye su, ya kasha su kuma.” Ikon kafirci da ya yi mulki a Faransa lokacin Juyin danwaken da mulkin razana, ya yi yaki da Allah da maganarsa da ba a taba ganin irinsa ba. Aka haramta sujada ga Allah. An kawas da ranar hutu ta mako makon a maimakon ta kuma aka kebe kowace rana ta goma don shaye shaye da sabo. Aka haramta baptisma da cin jibi. Sanarwa da aka manna a wuraren biso suka rika nuna cewa mutuwa barci ne na har abada. BJ 271.2
Sun ce tsoron Allah mafarin wauta ne ba mafarin ilimi ba. Aka haramta yin sujada na addini sai dai sujada ga ‘yanci da kuma kasar. “Bishop na Paris bisa ga dokan kasa ne aka gabatar domin ya shugabanci wannan raini da abin kunya mafi muni da wata kasa ta taba aikatawa.… An kawo shi gaba da dukan girmamawa domin shi sanar ma taron cewa addinin da ya yi shekaru da yawa yana koyarwa rudu ne na priestanci wanda ba shi da tushe ko a tarihi ko a gaskiya mai tsarki. Ya musunci kasancewar Allahn da aka shafe shi ya yi masa sujada, ya kuma kebe kansa don sujada ga ‘yanci da daidaito da nagarta da halin kirki. Sa’an nan ya aza lambobinsa na aikin ekklesiya a kan tebur, ya karbi rungumar yan-uwantaka daga shugaban Taron. Priestoci da yawa masu ridda suka bi kwatancinsa.” BJ 272.1
“Kuma wadanda suke zamne a duniya suna murna a kansu, suna ta nishatsi: za su aike da kyautai kuma zuwa ga junansu; domin wadannan annabawa biyu suka azabadda mazamanan duniya.” Faransce shiru a titunan kasar, wadanda kuma suka ki jinin takura da bukatun dokar Allah suka ji dadi. Mutane suka rika kangare ma sanin sama a gaban jama’a. Kamar masu zunubi na da, suka ce; “kaka Allah ya sani? Da wani sani kuma a wurin madaukakin?” Zabura 73:11. BJ 272.2
Da karfin zuciya irin na sabo, mai ban mamaki, daya daga cikin priestocin sabuwar kungiyar ya ce: “Allah, idan kana nan, ka rama ma sunanka da aka bata. Na kangare maka! Kana shiru; ba ka isa ka ture tsawanka ba. Bayan wannan wa zai gaskanta cewa kana nan?” Wannan daidai yake da maganar Fir’auna cewa: “Wane ne Ubangiji har da zan ji muryatasa?” “Ni ban san Ubangiji ba:” BJ 272.3
“Wawa ya fadi chikin zuchiyatasa, Babu Allah.” Zabura 14:1. Ubangiji kuma yana cewa game da masu kangare ma gaskiya: “Gama wautassu za ta bayana a sarari ga dukan mutane.” II Timotawus 3:9. Bayan Faransa ta rabu da sujada ga Allah Mai-rai, madaukaki, madawami kuma, ba da jimawa ba kuwa ta shiga bautar gumaka, tawurin sujada ga allahr Basira, wata fasika kawai. Wannan kuma a majalisar wakilai na kasar, kuma mahukumta mafi girma na kasa da na dokoki suka yi! Mai tarihi ya ce: “daya daga bukukuwan wannan mahaukacin lokacin ba shi da makamanci wajen wauta hade da rashin ibada. Aka shigo da kungiyar wake wake da raye raye wajen Taron, bayan yan majalisan suka shigo ta jerin gwano suna raira wakar yabon ‘yanci, suna kuma rakiyar abin sujadarsu nan gaba, watau wata mace cikin lullubi, wadda suka ba ta suna Allar Basira. Sa’anda aka kawo ta cikin wurin shaye shayen, aka bude ta, budewa na musamman, aka kuma ajiye ta a hannun daman shugaba, sai aka gane ta, cewa wata yarinya ce mai-rawa a wasannin kwaikwayo, macen nan da suka ce ta fi dacewa a matsayin wakiliyar basiran nan ce suke yi mata sujada, majalisar kasa ta Faransa ta yi mata mubaya’a. BJ 273.1
“Wannan buki mara ibada ne, wanda isa a yi masa ba’a kuma, ya kasance da wani kamani, aka kuma sabonta nadawar Allar Basiran, ana kwaikwayon nadin, ko ina a kasar, a wuraren da mutanen suka so nuna cewa sun cika yan Juyin danwake ta kowace fuska.” BJ 273.2
Mai shelan da ya gabatar da sujada ga Basira ya ce: “Masu yin dokoki! tsanancin ra’ayi ya kauce ya ba basira wuri. Idanunsu basu iya jimre walkiyar hasken ba. Yau jama’a da yawa sun taru a kalkashin rufin daki, suka nanata gaskiyar,” abin da ba a taba yi ba. A can Faransa mun yi bukin sujada ta gaskiyar - sujada ta yanci, sujada ta hikima. Can muka tsara fatar ci gaban Jamhurriyar. Can muka rabu da gumaka marasa rai, muka rungumi Hikima, gunkin nan da aka rayar; halitta mafi-kayu.” BJ 273.3
Sa’anda aka kawo allar cikin Taron, mai-shelar ya rike ta a hannu, ya kuma juya ga jama’ar, ya ce: “Ya masu mutuwa, ku dena rawan jiki a gaban tsawan Allah mara iko da tsroron ku ya halita. Daga yanzu, kada ku yarda da wani Allah sai Basira. Ina mika maku gunkinsa mafi tsarki da martaba; in ya kama dole ku yi gumaka, ku yi hadayar ku ga irin wannan gunkin ne kadai.… ku fadi a gaban majalisar ‘yancin kai! Mayafin Basira!” BJ 274.1
“Bayan shugaban ya rungumi allar, sai aka aza ta a kan wata mota mai-ban sha’awa, aka kewaye da ita cikin babban taron jama’a, zuwa babban majami’ar Notre Dame, domin ta dauki wurin Allah. Can aka aza ta kan babban bagadi, ta kuma karbi yabon dukan wadanda ke wurin.” BJ 274.2
Jima kadan bayan wannan, aka bi da konawar Littafin. A wani lokacin, “Shahararriyar Kungiyar Ma’adanar Kayayyakin Tarihi” ta shiga babban dakin taron garin, tana cewa, “Lale Basira!” suna kuma dauke da guntayen burbushin littattafai da yawa da aka kona, ciki har da littattafan addu’a da na wakoki, da Tsohon Alkawali, da Sabon Alkawali “da cikin wuta suka yi kafara dukan wautan da suka sa ‘yan Adam suka aikata,” in ji shugaban. BJ 274.3
Tsarin papaaruma ne ya fara aikin da kafirci ke karasawa. Manufafin Rum ne suke tanada yanayin jama’a da na siyasa da na addini da suka hanzarta rushewar Faransa. Yayin da marubuta ke rubutawa game da ababan ban kyama na Juyin Danwanken, sukan ce sarauta da ekklesiya ne ke da alhakin jawo laifukan nan. Ainihin gaskiya ma, alhakin yana wuyar ekklesiya ne. Tsarin paparuma ya rigaya ya bata tunanin sarakukan game da Canjin, cewa magabcin sarutasa ne, abin da kuwa ya jawo rashin jituwa da ya kashe salamar kasar da jituwarta. Rum ce ta haifar da mugunta mafi muni da duniya mafi daci da sarakuna suka rika aikatawa. BJ 274.4
Ruhun ‘yanci ya tafi tare da Littafi. Duk inda aka karbi bishara, an falkas da tunanin mutanen. Suka fara watsar da sakokin da sun dade suna danne su cikin bautar jahilci da mugunta da camfi. Suka fara tunani da ayuka kamar mutane. Sarakunan sun ga wannan, suka fara rawan jiki saboda danniyarsu. BJ 275.1
Rum ba ta yi jinkirin zuga tsoronsu mai-kishi ba. Paparuma ya ce ma mukaddashin sarkin Faransa a 1525, “Wannan haukan (watau Kin ikon paparuma) ba kawai zai rikitar da addini ya kusa rushe shi ba ne, amma har da dukan ikoki da masu sarauta, da dokoki da kungiyoyi, da mukamai ma.” Shekaru kalilan bayan haka, wani jami’in ‘yan paparuma ya gargadi sarkin cewa: “Mai-gida, kada a rude ka. ‘Yan Kin ikon paparuman nan za su wargaje dukan kaida ta kasa da ta addini,… Sarauta tana fuskantar hatsarin da ekklesiya ke fuskanta ne.… Dole kirkirowar sabon addini ya haifar da sabon gwamnati.” Masanan tauhidi kuma suka zuga kiyayyar mutanen ta wurin koyar da cewa wai koyaswar Kin ikon papruma tana “jan hankalin mutane zuwa sabobin ababa da wauta, tana kuma lalata ekklesiya da kasa ma.” Ta haka Rum ta yi nasarar hada gaba tsakanin Faransa da Canjin.” Don girmama sarauta da kiyaye fadawa da karfafa dokoki ne aka zare takobin zalunci a Faransa. BJ 275.2
Shugabannin kasar basu hangi sakamakon wannan matakin ba. Da koyar da Littafin ya shuka kaidodin nan na adalci da kamewa da gaskiya da nagarta da soyayya wadanda kuwa su ne ginshikin ci gaban kasar “Adilchi yakan daukaka al’umma,” Gama kursiyi bisa adilchi yake kafuwa.” Misalai 14:34; 16:12. “Aikin adilchi kuma salama ne.” Sakamakon kuma, “kwanciyar rai da sakankanchewa har abada,” Ishaya 32:17. Wanda ya yi biyayya ga dokar Allah zai girmama ya kuma yi biyayya ga dokokin kasar sa. Wanda ke tsoron Allah zai girmama sarki cikin anfani da ikonsa yadda ya kamata. Amma Faransa ta haramta littafi, ta hana almajiransa anfani da shi. Karni bayan karni, mutane masu kaida da aminci, masu kaifin hikima da halin kirki, wadanda ke da kwarin gwiwan bayana ra’ayinsu, su kuma sha wahala saboda gaskiya, sun rika aikin bauta suka yi ta mutuwa ko kuma rubewa a cikin kurkuku ma. Dubban dubbai suka rika gudun hijira; hakan ya ci gaba fa har shekaru dari biyu da hamsin bayan farawar Canjin. BJ 275.3
“Da wuya a sami wata sarar ‘yan Faransa da ba ta ga almajiran bishara suna gudu daga haukar fushin azalumin suna kuma tafiya tare da hikima da fasaha da kwazo da ado da suka kware a kai ba, don arzunta kasashen da suka ba su mafaka. Kuma daidai yadda suka inganta wadansu kasashe da baye baye masu kyau, daidai haka kuma suka raba kasarsu da baye bayen. In da dukan abin da aka kora daga Faransa sun kasance a kasar, da cikin shekaru dari uku din an yi anfani da kwarewar korarun game da masana’antu don aikin noma; kuma in da kwarewarsu ta fasaha ta ci gaba da inganta masan’antun kasar, in da cikin shekaru dari uku din nan, basirar su ta kirkirowar ababa ta ci gaba da habaka littattafai da inganta kimiyar, da hikimarsu ta ci gaba da ba da bishewa ga majalisun kasar, da karfin zuciyarsu kuma wajen yakokin kasar, da adalcin su wajen tsara dokokinta, addinin Littafin kuma yana karfafa kangado yana kuma mallakar lamirin mutanenta, ina yawan daukakan da da ya mamaye Faransa yau! Ina girma da yawan ci gaba da farincikin da ya kamata da kasar ta samu, kwatanci ga sauran al’ummai? BJ 276.1
“Amma makauniyar rashin sassauci ta kori kowane mai koyar da nagarta, kowane jarumin oda, kowane amintacen mai-kare gadon saruta; ta ce ma mutane da da sun mai da kasarsu sananniya maidaukakiya a duniya, zabi wanda za ka samu: mutuwa ko gudun hijira. A karshe, rushewar kasar ta cika; ba sauran addinin da za a kai wurin kisa kuma, ba sauran kishin kasa da za a bi zuwa kora daga kasar. Kuma Juyin Danwaken da dukan muguntansa, shine ya zama sakamako. BJ 277.1
u“Sa’anda Huguenots saka gud, Faransa ta rika lalacewa sosai. Birane masu ci gaba wajen masana’antu suka fara lalacewa, larduna masu yawan anfanin gona suka koma dazuzuka; rashin bisira da lalacewar halayen kirki suka dauki wurin ci gaba. Paris ya zama wani gidan bara mai fadi, an kuma kiyasta cewa sa’anda Juyin Danwaken ya fara, miskinai dubu dari biyu sun rika rayuwa ta wurin sadaka daga hannun sarkin. Yan Jesuits ne kadai suka sami ci gaba a kasar, yayinda ta ke rubewa, suka kuma yi mulki da zalunci na ban tsoro bisa ekklesiyoyi da makarantu da kurkuku. BJ 277.2
Ya kamata da bishara ta kawo ma Faransa maganin matsalolin nan na siyasa da zamantakewa da suka razana kwarewar ma’aikatanta na addini da sarkinta, da masu yin dokokinta, a karshe suka kuma jefa kasar cikin rudani da hallaka. Amma kalkashin bishewar Rum, mutanen sun rasa darussan sadakar da kai da kauna mara son kai. An rigaya an janye su daga ayukan musun kai don anfanin wadansu. Mawadata basu sami tsautawa game da danniyar da suka yi ma matalauta ba, matalauta kuma basu sami taimako game da bautarsu da wulakancinsu ba. Son kan mawadata masu iko ya yi ta ci gaba akai akai a bayane. An yi daruruwan shekaru handama da almubazzarancin mawadata ya kai ga mumunar tsotsewar talaka. Masu arziki sun yi ma matalauta laifi, matalauta kuma suka ki jinin masu arziki. BJ 277.3
A yawancin larduna, masu sarauta ne suka mallaki gidaje, talakawa kuma ‘yan haya ne kawai, sai abin da masu gidajensu suka ce masu, kuma dole su amince da abin da masu gidajen suka bukata daga wurinsu. Nawayar tokarar ekklesiya da kasa ta rataya a kafadar ma’aikata ne da talakawa da mahukuntan kasa da na ekklesiya suka aza masu haraji mai yawa sosai. “Gamsuwar masu sarauta ce aka mai da ita doka mafi daukaka; ko da manoma da talakawa sun fama da yawa, ba damuwar masu yi masu danniya ba ne…. Dole kowane lokaci mutanen su nemi sanin abin da mai gidan ke so. Rayuwar manoman ta kasance rayuwar aiki ne kullum cikin talauci kawai; idan har suka nuna damuwa ma, akan amsa masu da zagi ne da raini kuma. A kullum kotuna sukan saurari mai sarauta ne sabanin talaka; masu shari’a suka yi kaurin suna wajen karban cin hanci; kuma duk abin da mai sarauta ke so yakan sami goyon bayan doka a wannan tsarin. Daga harajin da jami’an kasa da na ekklesiya suka rika karba, ko rabi bai rika shiga baitulmalin kasa ko na ekklesiya ba ma. Sauran akan kashe wajen almubazzaranci ne da holewa kawai. Wadanda kuwa suka tsotse yan’uwansu hakanan an ware su daga biyan haraji, kuma doka da al’ada sun ba su ‘yancin samun kowane aiki a kasar. Masu gatan sun kai mutum dubu dari da hamsin kuma don gamsar da su miliyoyi suka kasance masu rayuwar kaskanci da rashin bege.” BJ 277.4
Fada ta cika da holewa da almubazzaranci, tsakanin mutane da shugabbi babu yarda. Kowane matakin gwamnati akan dauka cewa dabara ce ta son kai kawai. Har sama da shekara hamsin kafin Juyin Danwaken, Louis XV ne ke kan gadon sarauta, wanda kuma ko a wadancan zamanu na mugunta an san shi sarki ne mai kiwuya da shashanci da fasikanci. Inda akwai lalatattun masu sarauta azalumai, da kuma matalautan talakawa jahilai, ga kasa cikin rashin kurdi, mutanen kuma kullum suna fushi, ba sai da idon annabci ba, za a hangi barkewar mumunar damuwa ba da dadewa ba. Game da gargadin mashawaransa sarkin yakan amsa: “A yi kokari a sa al’amura su ci gaba duk tsawon rayuwata; bayan mutuwata abinda zai faru ya faru.” A banza aka rika nuna cewa akwai bukatar canji. Ya ga matsalolin amma ba shi da karfin hali ko ikon fuskantarsu. Amsarsa cewa “Bayana, ambaliyar!” ta bayyana ainihin matsalar da ke jiran Faransa. BJ 278.1
Tawurin anfani da kishin sarakuna da masu shugabanci, Rum ta sa su suka rike mutane cikin bautan, da sanin cewa wannan zai nakasa kasar, ita Rum kuma za ta daure shugabannin da mutanen cikin bautarta. Ta hangi cewa idan har za a rike mutane cikin bauta sosai, dole ne a takura ma tunaninsu; cewa hanya mafi tabbaci ta hana su tsere ma bautarsu ita ce a hana su iya samun ‘yanci. Munin lalacewar halin kirkinsu ya fi wahalarsu ta jiki muni sau dubu. Dashike an hana su Littafi an kuma bar su da koyaswar rashin sassauci da son kai, mutanen sun kasance cikin jahillci da camfi, suka kuma nutse cikin mugunta ta yadda ba su cancanci mulkin kansu ba. BJ 279.1
Amma abida wannan ya haifar ya bambanta gaba daya daga abinda Rum ta nufa. Maimakon rike talakawa cikin amincewa da koyaswarta a makance, aikin ta ya mai da su kafirai ne ‘yan juyin danwake. Suka yi kyamar Romanci cewa tsarin priestoci ne kawai, sun ga masu aikin bishara suna da hannu cikin danniya da ake masu. Basu san wani Allah ba sai allan Rum, koyaswarta ne kadai addininsu. Sun dauka cewa handamarta da zaluncinta sakamakon Littafin ne, kuma ya ishe su. Rum ta yi karya game da halin Allah, ta kuma wofinta dokokinsa, yanzu kuma mutane suka ki Littafin da Mai-wallafa shi ma. Ta bukaci biyayya ga koyaswarta ko ta halin kaka, cewa haka Littafin ya ce. Saboda haka Voltaire da abokansa suka yi watsi da maganar Allah gaba daya, suka kuma baza dafin kafirci ko ina. Rum ta murkushe mutane kalkashin duddugenta na karfe; yanzu kuma mutane wulakanttattu, rusassu suka watsar da ka’ida. Sun fusata game da macucin da suka dade suna masa mubaya’a, suka kuma ki gaskiya da karya baki daya; bayin mugunta suka yi murna game da abin da suka ga kamar ‘yanci ne. BJ 279.2
Da farkon Juyin Danwaken, da yardar sarki aka ba mutanen wakilci da ya fi na masu sarauta da ma’aikatan bishara gaba daya. Ta haka iko ya koma hannunsu, amma basu shirya anfani da shi da hikima da sassauci ba. Da marmarin magance laifukan da suka yi masu, suka kudurta sake tsarin zamantakewar jama’a. Jama’a cike da fushi, wadanda tutaninsu ke cike da muguntan da aka masu, suka kudurta cewa za su juya yanayin wahala da ta kai makura, su kuma yi ramuwa a kan wadanda suka dauka cewa su ne sanadin wahalarsu. Wulakanttatun sun yi anfani da darasin da suka koya lokacin zalunci sai suka zama masu danniya ga wadanda suka yi masu danniya. BJ 280.1
Faransa ta girbe jinin da ta shuka. Sakamakon amincewarta da mulkin Rum ya yi muni sosai. Wurin da Faransa a farkon Canjin nan, kalkashin tasirin Rum, ta kafa wurin kisa nan ne Juyin Danwaken ya kafa injin yanke kawunan mutane. Daidai inda aka kone masu Kin ikon paparuma na farko, a karni na sha shidda, nan aka fara yanke kawunan mutane da inji a karni na sha takwas. Ta wurin kin bishara, wadda da ta kawo warakar ta, Faransa ta bude kofar kafirci da hallaka. Sa’anda aka kawar da sassaucin dokar Allah, dokokin mutum suka kasa sassauta fushin ‘yan Adam, kasar kuma ta ci gaba zuwa tawaye da hargitsi. Yaki da Littafin ya shigo da zamanin da a tarihin duniya aka ce da shi Mulkin Razana. Aka kori farinciki da salama daga zukatan mutane. Babu wanda ke da tsaro. Wanda ya yi nasara yau, gobe akan zarge shi, a hukumta shi, gwada karfi da sha’awa suka mamaye kasar. BJ 280.2
An tilasta sarakuna da masu bishara da fadawa suka amince da muguntar mutanen da suka haukace. Kashe sarki da aka yi ya ta da marmarin su na ramuwa ne kawai; wadanda kuma suka umurta aka kashe shi, su ma an kashe su ba da jimawa ba. Aka kudurta kisar dukan wandanda aka zata ba sa goyon bayan Juyin Danwaken. Kurkuku suka cika, a wani lokacin ma akwai kamamu fiye da dubu dari biyu a cikinsu. Biranen kasar suka cika da al’amura masu ban kyama. Wata kungiyar ‘yan Juyin Danwaken sukan yi sabani da wata kuma, kuma Faransa ta zama babbar fagen talakawa masu jayayya da juna, cike da fushi kuwa. “A Paris, wata rigima takan bi bayan wata, ‘yan kasan kuma suka rarrabu cikin bangarori da yawa da burinsu kadai shi ne su murkushe juna.” Domin kara masu damuwar kuma, kasar ta shiga mumunan yaki mai tsawo da manyan kasashen Turai. “Kasar ta kusa tsiyacewa, mayakan suka rika kukan cewa a biya su albashin baya da ba a biya su ba, ‘yan Paris suna fama da yunwa, mafasa suka mai da larduna kango, wayewa kuma saura kadan kawai ta kare cikin rashin zaman lafiya.” BJ 281.1
Mutanen sun rigaya sun koyi darusan mugunta da zaluncin da Rum ta koyar. Ranar sakamako ta zo. Yanzu kuma ba almajiran Yesu aka jefa cikin kurkukum aka kuma kai su wurin kisa ba, wadannan sun hallaka ko an kore us daga kasar da dadewa. Yanzu Rum ta ji ikon kisa na wadanda ta koya masu su ji dadin zub da jini. “Kwatancin zaluncin da masu aikin ekklesiya a Faransa suka nuna na tsawon sararaki da yawa, shi ne yanzu kuma aka mayar masu babu sassauci. Katakai na kisa suka zama jajaye da jinin priestoci. Kurkuku da can baya suka cika da Huguenots yanzu suka cika da azalumansu. Ma’aikatan Roman Katolika suka dandana dukan azaban da ekklesiyarsu ta gana ma masu ridda.” BJ 281.2
“Sai kuma ga kwanakin suka zo da wata hukuma mafi jahilci ta aiwatar da kaidodi mafi muni, sa’anda ba wanda ya iya gaisuwa da makwabtansa ko kuma yin addu’a….ba tare da yiwuwar aikata laifin da horonsa kisa ne ba. Sa’anda yan lekan asiri suka buya a kowane lungu; sa’anda injin yanke kawuna ya rika aiki kowace safiya, sa’anda kowane kurkuku ya cika makil kamar jirgin daukan bayi; sa’anda lambatu suka cika da kumfar jini da suka rika kwararowa zuwa cikin kogin Seine…. Yayin da aka rika wucewa da tarago bayan tarago cike da wadanda za a kashe, ana bi ta titunan Paris, jami’an da babban komiti ya aika zuwa bangarorin, suka rika tabka zaluncin da ko a babban birnin ma ba a taba ganin irinsa ba. Wukar injin yankan yi ta yi masu jinkirin yanka da yawa. Aka dinga yanke kamammu da yawa. Sai aka huda ramuka a gindin kowane kwalekwale cike da mutane. Aka mai da birnin Lyons Hamada. A birnin Arras kuma ko jinkai na mutuwa da wuri ba a ba fursunonin ba. Duk tsawon kogin Loire, daga Saumur zuwa teku, garkunan tsuntsaye suka rika buki akan gawaye a tattare. Ba a damu da jinsi ko shekaru ba. Yawan samari da ‘yan mata ‘yan wajen shekara sha bakwai da gwamnati ta karkashe ya kai daruruwa. Jarirai da aka fizge su daga nonon uwaye, akan dinga wurga su ana yayanke su da takobi akan ciyawa.” Cikin shekara goma kadai jama’a da yawa suka hallaka. BJ 282.1
Duk wannan yadda Shaitan ya so ke nan. Abin da ya yi sararraki yana so ya tabbatar an yi kenan. Hanyarsa rudu ne daga farko har karshe, kuma nufinsa ne kullum ya kawo ma mutane kaito da talauci, ya lalata ya kuma kazantar da aikin Allah, ya bata manufan Allah na kauna da halin kirki, ta haka kuma ya jawo bakinciki a sama. Sa’an nan tawurin karyarsa, yana makantar da tunanin mutane, ya sa su jefa laifin aikinsa a kan Allah, sai ka ce dukan wahalolin nan shirin Allah ne. Hakanan kuma, sa’anda wadanda aka wulakanta su aka kuma zalunce su ta wurin ikon sa suka sami ‘yanci, yakan zuga su zuwa wuce gona da iri da kuma aikata laifuka. Sa’annan azalumai sukan nuna kamar hoton nan na rashin sassauci shaida ce ta sakamakon ‘yanci. BJ 282.2
Sa’anda aka gane wani salon kuskure, Shaitan yakan sake masa kama ne, jama’a kuma sukan karbe shi da marmari kamar karon farkon. Sa’anda mutanen suka gane cewa Rumanci rudu ne, ya ga kuma ba zai iya kai su ga ketare dokar Allah tawurin wannan hanyar ba, sai ya zuga su suka mai da kowane addini wai zamba ne, littafi, tatsuniya kuma; kuma sa’anda suka watsar da dokokin Allah, suka ba da kansu ga zunubi ba sassauci. BJ 283.1
Babban kuskuren da ya jawo ma mazaman Faransa kaiton nan shi ne kyale gaskiya dayan nan da aka yi: cewa ainihin ‘yanci yana cikin kaidodin dokar Allah ne. “Da ma ka yi sauraro ga dokoki na! da hakanan ne da salamakka ta yi kamar kogi, adilchinka kuma kamar rakuman teku.” “Babu lafiya, in ji Ubangiji, ga masu mugunta.” “Amma dukan wanda ya saurara gare ni za ya zamna da rai a kwanche, ba tsoron masifa ba.” Ishaya 48:18, 22; Misalai 1:32. BJ 283.2
Kafirai da masu ridda suna jayayya da dokar Allah; amma sakamakon tasirinsu yana nuna cewa zaman lafiyan mutum ya danganta ga biyayyarsa ga dokokin Allah ne. Wadanda ba za su karanta darasin daga maganar Allah ba, ana shawarta su su karanta shi cikin tarihin al’umma. BJ 283.3
Sa’anda Shaitan ya yikokari tawurin ekklesiyar Rum ya kawar da mutane daga biyayya, ya boye wakilinsa, aikin sa kuma ya badda kama ta yadda ba a ga rage daraje da bakinciki da ya haifar kamar sakamakon ketare doka ne ba. Aikin Ruhun Allah kuma ya yi gaba da shi ta yadda aka hana manufofinsa haifar da dukan sakamakon da sanadinsa don gane tushen bakincikinsu ba. Amma a Juyin Danwaken, majalisar kasa ta kawar da dokar Allah kai tsaye a fili. Kuma cikin mulkin Razana da ya biyo baya, kowa ya ga yarda, sanadi ya jawo sakamako. BJ 283.4
Sa’anda Faransa ta ki Allah a fili ta kuma kawas da Littafin, miyagun mutane da ruhohin duhu sun yi murnar samun mulkin da suka dade suna so - mulkin da babu hane hanen dokar Allah. Domin ba a aiwatar da hukumci nan da nan ba, “saboda haka zukatan yayan mutane suka ji karfin aika mugunta.” Mai-wa’azi 8:11. Amma ketare doka mai-adalci dole yakan kai ga bakinciki da hallaka. Ko da shike ba a hukunta muguntar mutane nan da nan ba, muguntar ta ci gaba da shirya hallakarsu. Daruruwan shekarun ridda da laifuka sun yi ta tattara fushi don ranar ramako; kuma sa’anda zunibinsa ya cika, masu raina Allah suka gane a makare cewa kure hakurin Allah da suka yi abin tsoro ne, Ruhun Allah wanda ke takura ma ikon muguntar Shaitan an cire shi, kuma shi wanda abin sonsa kadai shi ne bakincikin mutane ya sami damar aikata nufinsa. Wadanda suka zabi tawaye aka bar su su girbe ‘ya’yansa har sai an cika kasar da laifuka da ke da munin da ya fi karfin rubutawa. Daga rusassun larduna da birane aka ji mumunan kuka mai-daci, mai-zafi kuma. Faransa ta girgiza sai ka ce an yi rawan duniya. Addini, doka, oda, iyali, kasa, da ekklesiya, dukansu hannun nan na kafirci da aka daga don sabani da dokar Allah ya rusar da su. Mai-hikima ya ce: “Mugu za ya fadi tawurin muguntar kansa.” “Mai-zunubi ya yi mugunta so dari, har ma ya dade a duniya, duk da haka na sani lallai, wadanda ke tsoron Allah za su zama lafiya, masu ibada ke nan: amma babu lafiya ga miyagu.” Misalai 11:5. Mai-wa’azi 8:12,13. “Gama suka ki ilimi, basu zabi tsoron Ubangiji ba:” “Zasu fa chi alhakin hanyassa, su koshi da nasu dabarbaru.” Misalai 1:29, 31 BJ 284.1
Amittantun shaidun Allah da iko mai-sabon nan da ke tasowa daga rami mara matuka, ba za su dade suna shuru ba. “Bayan kwana uku din da rabi, lumfashin rai daga wurin Allah ya shiga chikinsu. Suka tsaya bisa kafafunsu; babban tsoro fa ya fada ma wadanda suka gansu” Ruya 11:11. Cikin 1793 ne dokokin da suka haramta addinin Kirista suka kuma kawar da Littafin, suka sami wucewa a Majalisar Faransa. Shekaru uku da rabi daga baya wani kudurin majalisa dayan ya warware wadancan dokokin, don haka aka ba Littafin dama. Duniya ta yi mamakin yawan girman laifin da ya taso daga kin Magana mai-tsarki, mutane kuma suka gane muhimmancin bangaskiya ga Allah da maganarsa a matsayin harsashen nagarta da halin kirki. In ji Ubangiji, “Wane ne ke nan ka yi masa zargi, ka sabe shi kuma? A kan wane ne kuma ka daukaka muryarka ka ta da idanunka sama kuma? Mai-tsarki ne na Israila.” Ishaya37:23. “Shi ya sa fa, yanzu so dayan nan zan sanashe su hannu na da iko na; za su kwa sani sunana Yahweh ne.” Irmiya 16:21. BJ 285.1
Game da shaidu biyu din, annabin ya kuma ce: “Suka ji babban murya daga sama ta che masu, ku hau daga nan. Suka hau kuma zuwa chikin sama chikin girgijen: makiyansu kuma suna duban su.” Ruya 11:12. Tun da Faransa ta yi yaki da shidun Allah biyu din nan, an daukaka su fiye da duk yadda aka taba yi. A 1804 aka kafa kungiyar Littafin na Birtaniya da kasashen waje (British and Foreign Bible Society). Aka bi da kungiyoyi irin sa da ressa da yawa, a nahiyar Turai. A 1816 aka kafa “American Bible Society.” Sai aka buga aka kuma baza Littafin cikin harsuna hamsin. Yanzu ma an rigaya an juya shi zuwa daruruwan harsuna. BJ 285.2
Cikin shekaru hamsin kafin 1792 ba a mai da hankali sosai ga aikin mishan na kasashen waje ba. Ba a kafa sabbin kungiyoyi ba, kuma ekklesiyoyi kalilan ne suka yi kokarin baza Kiristanci a kasashen kafirai. Amma kusa da karshen karni na sha takwas an sami babban canji. Mutane suka gane muhimmancin wahayin Allah da addini na tabbatar da abin da aka ji. BJ 285.3
Daga wannan, lokacin aikin mishan na kasashen waje ya ci gaba sosai. Karin ingancin harkar buga littattafai ya kara ma aikin baza Littafin kwarin gwiwa. Karin hanyoyin sadarwa tsakanin kasashe dabam dabam, da rushewar shingayen wariya, da rashin ikon kasa da paparuma ya yi, sun bude hanya don shigowar maganar Allah. Shekaru da dama ana sayar da Littafin a titunan Rum ba takura, kuma yanzu an kai shi ko ina a duniya. BJ 286.1
Kafirin nan Voltaire ya taba buga kirji ya ce: “Na gaji da jin mutane suna cewa wai mutum sha biyu ne suka kafa addinin Kirista. Ni zan nuna cewa mutum daya ya isa ya hambarar da shi.” Sararraki sun wuce bayan mutuwarsa. Miliyoyi sun sa hannu cikin yaki da Littafin. Amma maimakon hallaka shi, in da akwai Litattafai guda dari a zamanin Voltaire, yanzu akwai dubu goma, I, Littafin Allah guda dubu dari ma. Ta bakin wani dan Canji, game da ekklesiyar Kirista: “Littafin make ra ce da ta shude guduma da yawa.” In ji Ubangiji: “Babu alatun da aka halitta domin chiwutanki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gaba da ke, a shari’a za ki koyas da shi.” Ishaya 54:17. “Maganar Ubangiji za ta tsaya har abada.” “Dukan dokokinsa masu-aminchi ne. Sun kafu har abada abadin an gudana su chikin gaskiya da adalchi.” Ishaya 40:8; Zabura 111:7,8. Duk abin da aka gina bisa ikon mutum za a hambarar, amma abinda aka kafa bisa Dutsen maganar Allah zai tsaya ha abada. BJ 286.2