Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    TUBA

    Yaya dan-Adam zai zama adili ga Allah? Yaya za a mai da mai zunubi adili? Sai ta wurin Kristi ne kadai za a iya kawo mu cikin sulhu da Allah, cikin sulhu da tsarkaka; amma ta yaya za mu kai ga Kristi? Dayawa suna yin tambaya daidai da wadda runduna masu yawa suka yi a ranar Pentecost, sa’anda suka ji zunubi ya kashe su, suka ta da murya, suka ce, “Me za mu yi?” Kalmar da ta fara fitowa daga bakin Bitrus game da amsa wannan tambaya ita ce “Tuba.” Ayukan Manzani 2:38. Ba a jima ba kuma, bayan ya ci gaba da jawabinsa, ya sake cewa “Ku tuba . . . ku juyo, domin a shafe zunubanku.”MK 19.1

    Bakin ciki sabo da zunubi a hade ya ke da tuba, da kuma juyawa ga barin aikata zunubi. Ba shi yiwuwa mu yi musun zunubi sai mun gane kazanta tasa, idan ba mun guje masa daga cikin zuciya ba, ba shi yiwuwa wani abu ya sake daga irin zamammu na da.MK 19.2

    Akwai mutane dayawa da ba su gane hakikanin azancin tuba ba. Dubbai suna bakin ciki sabo da sun yi zunubi, har ma su kan nuna sabon hali daga waje, domin suna jin tsoro cewa ayyukan da su ke aikatawa da ba daidai ne ba za su jawo masu wahala. Amma wannan ba shi ne ma’anar tuba kamar yadda ya ke a cikin Litafi Mai- tsarki ba. Wahalarsu suke kuka, amma ba suzubin ba. Irin wannan ne bacin ran da Isuwa ya yi sa’anda ya ga gadonsa na haifuwa ya bace masa har abada. Bala’am sabili da tsorata da ya yi sa’anda mala’ika ya tsare masa hanya ya hana shi wucewa da takobi a zare, ya fadi laifinsa domin gudun kada a kashe shi ne kawai; amma babu sahihin tuba na zunubin a gareshi, babu juyawa daga nufin da ya yi, babu dyamar mugunta. Yahuda Iskariyoti, bayan ya ba da Ubangijinsa, ya ce “Na yi zunubi, da shi ke jini mara-aibi ne na bashe shi.” Matta 27:4.MK 19.3

    Sanin la’ana na laifinsa da tsoron hakunci, su suka sa wannan furta laifi ya fito daga cikin ransa. Sanin abin da zai same shi sabili da abin da ya aikata shi ya cika shi da tsoro, amma fa ba wani zurfin bakin ciki na karayar zuciya a cikin ransa cewa ya ci amanar Dan Allah mara tabo, ya yi musun Mai-tsarki na Isra’ila. Sa’anda Fir’auna ya ke shan wahalar hukuncin Allah a kansa ya amsa laifinsa domin ya tsira daga hakuncin da ke gaba, amma ya koma kan kangara ga Allah nan da nan bayan an tsaida aloba. Su wadannan duka sun yi kukan abin da zunubi ya jawo, amma ba su yi bakin cikin ainihin zunubin kansa ba.MK 19.4

    Amma sa’anda zukata suka sada kansu ga ikon Ruhun Allah, nan da nan lamiri ya kan rayu, sa’annan mai zunubi zai iya rarrabewa da irin zurfin, da kuma irin tsarkin dokar Allah, wadanda su ke su ne tushen mulkinsa a cikin samaniya da duniya. “Wanda yana haskaka kowane mutum, yana zuwa chikin duniya.” Yohanna 1:9 ya kan haskaka asirtattun lollokai na ruhu, kuma yana nuna boyayyun abu- buwa na dufu a sarari. Tabbatawa ya kan kama hankali da zuciya. Mai zunubi ya kan gane adilcin Yahweh kuma ya kan ji fargaban tsayawa, cikin laifinsa da kazamtarsa, a gaban Mai-binciken zukata. Ya kan ga kaunar Allah, da jimalin tsarki, da farin cikin tsarkaka, ya kan yi marmarin a tsarkake shi, a maishe shi cikin zumunta da Allah.MK 21.1

    Addu’ar da Dauda ya yi bayan faduwa tasa tana kwatanta bakin ciki na gaske sabo da aikata zunubi. Tubansa sahihi ne mai zurfi kuma. Babu wani zukewa ko neman ba da hujja kan laifinsa. Ba neman tsira daga hukunci ne ya sa shi yin wannan addu’a ba, Dauda ya. ga kasaitar laifin da ya yi. Ya ga kazantuwar ruhunsa. Ya yi Kyamar zunubinsa. Ba sabo da gafara ne kadai ya yi addu’a ba, amma sabo da tsarkakewar zuciya. Ya yi marmarin farin ciki na tsarkaka — a maida shi cikin jituwa da zumunci da Allah. Ga kalmomin da suka fito daga zurfin zuciya tasa:MK 21.2

    “Mai-albarka ne mutum wanda an gafarta masa laifofinsa, wanda an rufi zunubinsa. Mai-albarka ne mutum wanda Ubangiji ba ya lissafta mugunta gareshi ba, wanda ba shi da algus chikin ruhunsa ba.” Zabura 32:1, 2.MK 21.3

    “Ka yi mani jinkai, ya Allah, bisa ga rahamarka, Bisa ga yawan jiyejiyenkanka ka shafe laifofina. Ka tsarkake ni daga zunubina. Gamma ina sane da laifofi na: Zunubi na yana gabana tutur. Ka tsarkake chikina da zofa, zan tsarkaka kuma. Ka wanke ni, zan kwa fi snow fari Daga chiki na ka halita zuchiya mai-tsabta, ya Allah: Ka sabonta dai-daitachen ruhu daga chiki na. Kada ka yashe ni daga gabanka, kada kuma ka dauke mani ruhunka mai- tsarki. Ka mayas mani da farinchiki na chetonka; Ka tokare ni da ruhu na yardan rai. Ka cheche ni daga alhakin jini, ya Allah, Allah na chetona; Harshena kuma zaya raira labarin adilchinka da karfi.” Zabura 51:1-14.MK 21.4

    Tuba irin wannan ya fi karfin ikon kammu ya sa mu kai gareshi. Daga wurin Kristi kawai ya ke samuwa, wanda ya hau bisa cikin sama, ya kuma ba da kyauta masu yawa ga ‘yan-Adam.MK 22.1

    Amma ga wani wuri inda mutane dayawa su kan yi kuskure, ta haka kuwa sai su rasa karbar taimakon da Kristi ya ke da nufi ya ba su. Suna tsammani ba za su iya zuwa ga Kristi ba sai sun fara tuba, kuma wai tuba shi ke shirya hanyar gafarar zunubansu. Lallai kam tuba shi ke gaba kafin gafarar zunubai, domin kuwa kar- yayyar zuciya mai tuba ce kadai za ta iya jin bukatar wani Mai-ceto. Amma dole ne mai zunubi ya dakata sai ya tuba kafin ya iya zuwa wurin Yesu? Ashe ya kamata a sa tuba ya zama abin tuntube tsakanin mai zunubi da Mai-ceto?MK 22.2

    Littafi Mai-Tsarki bai koyas da cewa sai dole mai zunubi ya tuba kafin ya kasa kunne ga kiran Kristi ba. “Ku zo gareni, dukan ku da ku ke wahala, da masu nauyin kaya, zan kuwa ba ku hutawa.” Matta 11:28. Alherin da ya ke fita daga Kristi shi ne ya ke bayaswa zuwa tuba na gaskiya. Bitrus ya baiyana abin a fili a cikin jawabinsa zuwa ga ‘ya’yan Isra’ ila sa’anda ya ce “Wannan Allah ya daukaka shi da hannun damansa shi zama sarki da Mai-cheto, domin shi bada tuba ga Israila, da gafarar zunubai kuma.” Ayukan Manzani 5:31. Ba shi yiwuwa mu tuba im ba tare da Ruhun Kristi ya farkad da lamirin mu ba kamar yadda ba shi yiwuwa mu samu gafara im ba tare da Kristi ba.MK 22.3

    Kristi shi ne masomin ko wane tunanin da ke dai dai. Shi ne kadai zai iya dasa kiyayya da zunubi cikin zuciya. Ko wane nufi domin gaskiya da tsarki, ko wane tabbatawa da sanin kasancewa zunubammu, shaida ne cewa Ruhunsa yana motsawa bisa zukatammuMK 22.4

    “Yesu ya ce, “Ni kwa idan an tada ni daga chikin kasa, zan jawo dukan mutane zuwa kaina.” Yohanna 12:32. Dole ne a baiyana Kristi ga mai zunubi kamar Mai-ceto wanda ke mutuwa domin zunuban duniya, kuma idan muna duban Dan Rago na Allah bisa giciye a Kalvari, asirin pansa zai komo ya soma bude hankulammu, sai kuma alherin Allah ya bishe mu zuwa ga tuba. A cikin mutuwa tasa domin masu zunubi Kristi ya nuna kauna wadda ba shi yiwuwa a gane ta, kuma idan mai zunubi ya ga wannan kauna, sai zuciya ta yi taushi, hankali ya ga shaida, ya jawo tarayan ruhu.MK 22.5

    Gaskiya ne wani lokaci ‘yan-Adam su kan ji kunyar irin zaman da su ke yi na zunubi, har ma su bar wadansu miyagun tabi’u nasu, kafin su farga cewa ana jan su ne a hankali zuwa ga Kristi. Amma fa a ko wane lokacin da suka yunkura domin ‘su sake zamansu, da sahihin nufi kuma su yi abin da ke daidai, ikon Kristi ne ya ke jawo su. Wani irin iko yana nan wanda ba za su farga da shi ba, shi ne ke aiki bisa zukatansu, sai lamiri ya farka, irin zama na waje ya gyaru. Kuma a lokacin da Kristi ya ke jawo su domin su dubi giciyensa a sa’ilin da ya ke jawo su su dube shi wanda zunubansu suka soke Shi, sai doka ta komo gida wajen lamiri. Irin mugun zaman da su ke yi, irin zurfin da zunubi, ya kafa gindinsa a cikin rayukansu, za su fito fili a gabansu. Sai su fara gane wani abu na adilcin Kristi, su ce “Mene ne zunubi, har da zai bukaci irin wannan baiko kafin a panshi wanda ya zama bawansa? Ashe, dukan kaunar nan, dukan wannan shan wahala, dukan wannan kaskanci, am bukace su ne domin kada mu hallaka, amma mu samu rai na har abada?”MK 23.1

    Mai zunubi yana iya tsayaiya da wannan kauna, yana iya ki a jawo shi zuwa ga Kristi, amma idan bai yi tsayayya ba, za a iya jawo shi zuwa ga Yesu, sanin shirin da aka yi domin ceto zai bi da shi zuwa ga kafafun giciye cikin tuba sabo da zunubansa, wadanda suka jawo radadi ga Dan Allah kaunataccensa.MK 23.2

    Wannan hali na sama mai aiki bisa abubuwan halitta shi ne dai ya ke zance da zukatan ‘yan-Adam, yana halittar wani irin marmari mai tsanani domin wani abu da ba su da shi. Abin da duniya ba za ta iya biya musu marmarin nan nasu ba. Ruhum Allah yana rokon su su bidi irin abubuwan da su kacfai ne za su iya ba da salama da hutu — alherin Kristi, da farin ciki na tsarki. Maicetonammu tutur yana aiki ta hanyoyi daban daban da ake gani da ido da wadanda ba a gani, domin ya jawo hankulan ‘yan-Adam daga nishatsi na zunubi wadanda ba su korsarwa zuwa ga albarka mara iyaka da zai zama nasu a cikinsa. Ga dukan rayukan da su ke kokari na banza su sha daga tuluna na wannan duniya, sako daga sama yana fada masu cewa Mai-jin kishi kuma, bari shi zo. Wanda ya ke so, bari shi diba ruwa na rai kyauta.” Ruya ta Yohanna 22:17.MK 23.3

    Ku wadanda a cikin zukatanku kuna da marmarin wani abu da ya fi wanda duniyar nan za ta iya bayarwa kuna gane cewa wannan marmarin muryar Allah ce zuwa ga zukatanku, ku roke shi ya ba kutuba, ya baiyana muku cikin kauna tasa mara iyaka, cikin cikakken tsarkinsa. A cikin zaman duniya na Mai-ceto ne aka nuna cikakkiyar shari’a ta Allah — kauna zuwa ga Allah da dan-Adam. Alheri da taimako da kauna mara son kai, su ne kurwar ruhunsa. Sai mun dube shi, sa’anda haske daga Mai-cetommu ya facfo bisa kanmu sa’annan za mu ga zunubin zukatanmu.MK 24.1

    Ya yiwu mu yabi kammu, kamar yadda Nikodimus ya yi, mu ce ai mu zamammu daidai ya ke, mu ce mu halayemmu na kirki ne, kuma mu yi tsammani cewa ba mu da bukatar mu kaskantar da zukatammu a gaban Allah kamar ko wane mai-zunubi, amma sa’anda hake daga Kristi ya haskaka cikin zukatammu za mu ga yadda ba mu da tsarki ko kadan; za mu gane son kai na nufi; za mu gane magabtaka da Allah wanda ya kazamtad da ko wane aiki na zaman duniya. Sa’annan za mu gane cewa hakika adilcimmu kamar daud an tsummoki su ke, sa’annan ne za mu gane jinin Kristi ne kadai zai iya tsabtace mu daga kazamtar zunubi, ya kuma sabonta zukatammu cikin kamannin kansa.MK 24.2

    Komai kankantar haske na darajar Allah, komai kankantar dan kyalli na tsarkin Kristi, wanda zai huda ya shiga rayukammu, ya isa ya baiyana a fili ko wane digo na kazamta, kuma ya baiyana a fili laifofuka na haleyemmu, Ya kan baiyana a fili rashin tsarki na muradodimmu, da rashin aminci na zukatammu, da rashin tsarkin lebunammu. Ayukan mai zunubi na cin amana wajen wofinta dokar Allah, za su tonu ga idanunsa, sai rai ya wahala karkashin ikon Ruhun Allah. Sai ya ji kyamar kansa sa’anda ya dubi tsarki da rashin tabo na halin Kristi.MK 24.3

    Sa’anda Annabi Daniel ya ga daukakar da ta ke kewaye da Manzo na sama da aka aiko wurinsa, ya cika da sanin rashin karfinsa da rashin cika tasa. Sa’anda ya ke kwatanta abin da ya gani mai ban mamaki, ya ce “Ba sauran karfin da ya rage a chikina kwa; gama jamalina ya juya a chikina, ya zama ruba, ba ni da ringin karfi.” Daniel 10:8. Ruhun da aka tabe shi haka zai yi kiyaiya da son kansa, zai ji kyamar kaunar kansa, zai kuwa nema, ta wurin adildn Kristi, ya samu tsarkin zuciya wadda ta ke cikin zumunci da dokar Allah da hallin Kristi.MK 24.4

    Bulus ya ce “Ga zanchen adilci da ke chikin shari’a.” Filibiyawa 3:6, amma sa’anda aka gane ruhaniyancin halin shari’a, ya ga kansa mai zunubi ne.MK 25.1

    Idan aka duba abin da shari’a ta shar’anta kamar yadda ‘yan- Adam suka dauka game da abubuwa na waje kawai, lallai ne Bulus ya yi nisa da zunubi; amma sa’anda ya duba ya ga zurfin sharudanta, ya kuma ga kansa kamar yadda Allah ya gan shi, ya sunkuya cikin ladabi da kaskantar zuciya ya fadi laifinsa. Ya ce “Ni ma da da rai ni ke da ba shari’a ba: amma sa’anda doka ta zo, zunubi ya sake rayuwa, na kwa mutu.” Romawa 7:9. Sa’anda ya ga ruhaniyancin tabi’ar shari’a sai zunubi ya baiyana a cikin muninsa, sai kuma yabon kai nasa ya bace.MK 25.2

    Allah ba ya daukan zunubi a kan cewa duk girmansu daya ne. Akwai bambantar girman laifi a wurinsa, haka kuma ga ‘yan-Adam; amma komai kankantar laifi a idanun ‘yan-Adam, ba zunubin da ya ke da kankanta a gaban Allah. Gani na dan-Adam ba cikakke ba ne, amma Allah yana jarraba komai daidai yadda ya ke. Ana raina mashayi, ana ce masa ba zai shiga sama ba, amma sau dayawa ba a tsautawa alfarma da son kai, da kyashi. Wadan nan kuwa su ne suka fi ba Allah haushi; gama su akasin alherin halinsa ne, su ne akasin kaunar nan mara son kai wadda ta ke kamar iskar da ta cika dukan halitta. Ya yiwu shi wanda ya fada cikin zunuban da suka fi girma ya ji kunya, ya kuma ji talauci, ya kuma ji bukatar alherin Kristi; amma alfarma ba ta kan ji irin wannan bukata ba, domin haka tana rufe zuciya ga Kristi da albarka tasa mara iyaka wadda ya zo ya bayar.MK 25.3

    Shi matalaucin nan mai karban haraji wanda ya yi addu’a ya ce “Ya Allah, ka yi mani jinkai, ni mai-zunubin.” (Luka 18:13.) ya ga kansa kamar kasaitaccen mugun mutum, a haka ne kuwa wadansu ke dubansa; amma ya ji bukatarsa a rai, da wannan kaya kuwa na laifinsa, da kunya, ya zo gaban Allah, yana bidar jinkansa. Am bude zuciya tasa domin Ruhun Allah ya yi aikin alherinsa, ya ‘yantad da shi daga ikon zunubi. Amma addu’ar da ba-Farisi ya yi, cike da ruba, da yabon kai, ta nuna cewa zuciya tasa a rufe ta ke kuble ta ji wani iko na Ruhu Mai-tsarki. Sabili da nisan da ke tsakaninsa da Allah, ba shi da wani ganewa na kazamta tasa, akasin cikakken tsarki na sama. Bai ji wani bukata cikin ransa ba, don haka bai karbi komai ba.MK 25.4

    Idan ka ga zunubinka, kada ka tsaya ka ce sai ka yi dama-dama. Ina misalin yawan wadannan da su ke tsammani ba su isa su zo ga Kristi ba! Kana tsammani ka iya kai kanka gaba da inda ka ke ta wurin kokarin kanka kadai? “Ba-kushi ya iya sake launin fatassa, ko damisa rodi rodinta? In hakanan ne, ku kuma ku a yi nagarta, ku da kuka saba da mugunta,” Irmiya 13:23. Sai a cikin Allah ne kadai taimakommu ya ke. Kada mu jira wai sai an ciwo kammu, ko sai mun samu dama wanda ya fi wanda mu ke ciki, ko kuma sai lokacin da muka ji mun yi tsarki. Ba za mu iya yin komai mu da kummu ba. Dole mu zo ga Kristi a matsayin da mu ke ciki.MK 26.1

    Amma fa kada wadansu su rudi kansu da tsammani cewa Allah, cikin kauna tasa da jinkansa masu girma, zai ceci ko su wadannan da suka ki karbar alherinsa. Sai ta wurin hasken giciye ne kadai za a iya gane rashin kyaun zunubi. Idan ‘yan-Adam suka tsaya a kan cewa nagartar Allah ta fi karfin ya jefas da mai zunubi, to, ya dubi Kalvari. Sabili da babu wata hanya ne da za a iya ceton dan- Adam, domin im ba da wannan hadaya ba, ba shi yiwuwa yan-Adam su tsira daga ikon kazantarwa na zunubi, har a mayar da su cikin zumunci da masu tsarki — ba shi yiwuwa a garesu su zama masu taraiya na zaman ruhaniya — Sabili da wannan ne Kristi ya dauka wa kansa laifin marassa biyayya, ya sha wahala madadin mai zu¬nubi. Kauna, da shan wahala, da mutuwar Dan Allah, duka suna shaida a kan kasaisar zunubi, kuma suna facfi cewa babu samun rai sai mun bada zuciyarmu ga Kristi.MK 26.2

    Wani lokaci marssa tuba su kan yi wa kansu hujja suna magana game da Mai-bin Kristi suna cewa, “ai ni ma daidai da su ni ke wajen nagarta. Ba su fi ni musun kai ba, ba su fi ni kamewa ba, ba su fi ni lura da twinkaya cikin irin zaman duniya ba. Ai su ma suna kaunar jin dadi da nishacfi kamar ni.” Ta haka su kan kawo hujja su ce laifin wadansu shi ya hana su yin abin da ya kamata su yi. Amma zu¬nubai da kasawa na wadansu ba shi yiwuwa su zama hujja ga kowa, domin Ubangiji bai sa mana dan-Adam mai kuskure ya zama abin da za mu yi koyi da shi ba. Dan Allah mara tabo ne aka bayar ya zama misali a garemu, kuma su wadannan da su ke ganin kuskure na masu bin Yesu su ne ya kamata su fi zaman kirki su kuma zama misalai nagari da za a kwaikwaya. Idan sun mai da matsayin zaman mai bin Yesu yana da girma haka, ashe wannan baya shaida girman zunubansu ba? Sun san abin da ke daidai amma sun ki aikatawa.MK 26.3

    Yi hankali da yin sakachi. Kada ka dakatad da aikin rabuwa da zunubinka da neman tsatstsarkar zuciya ta wurin Yesu. Ta nan ne dubbai bisa dubbai suka yi kuskure, har ya ja musu bata na har abada. Ba zan tsaya a nan kan zancen in nuna gajarta da rashin tabbatar zaman duniya ba; amma akwai hadari mai ban tsoro — hadarin da ba a gane shi yadda ya kamata ba — hacfarin jinkiri ga biyewa muryar roko ta Ruhu Mai-tsarki na Allah, hadarin zaben zama cikin zunubi, gama haka jinkirin ya ke. Zunubi, komai kan- kanta tasa, in aka dinga aikata shi zai jawo bata na har abada. Abin da ba mu ci nasara bisa kansa ba, zai ci nasara bisa kam mu, ya jawo mana hallaka.MK 27.1

    Adamu da Hauwa’u sun rinjayi kansu cewa don an ci dan itace kawai wanda aka hana ba zai jawo babban abin tsoro kamar yadda Allah ya fadi ba. Amma fa shi wannan abu kankani ketare doka ne mai tsarki na Allah wadda ba ta sakewa, ya kuwa raba dan-Adam da Allah, ya bucfe kofofin ruwaye na mutuwa da bakin ciki mara iyaka bisa duniya. Zamani bisa zamani, shekara bisa shekara, kuka da makoki suna tashi tutur daga duniya zuwa sama, duk halitta kuma ba hana ka juyowa kadai ya ke yi ba, amma yana sa ka kasa gaba da Allah. Kalvari a tsaye ta ke kamar shaida na wannan baiko mai ban mamaki da ake bukata domin a samu gafara sabo da ketare doka mai-tsarki.MK 27.2

    Ko wane aiki na ketare doka, ko wane kyaliya ko kin alherin Kristi yana komowa bisa kanka; yana taurare zuciya, da hankali, ga juyowa dungun zuwa ga kokarin nan da Ruhu Mai-tsarki na Allah, kuma ba hana ka juyowa ka dai ya ke yi ba, amma yana sa ka kasa ga rokon da ya ke yi dominka.MK 27.3

    Wadansu su kan kwantar da hankalin lamirin da ya damu da cewa sua iya sake hanyar mugunta duk sa’ad da suka ga dama, ko su yi wasa da kira na jinkai yadda su ke so. Suna tsammani bayan sun aikata abu gaba da alherin Ruhun, bayan sun ba da karfinsu ga Shaitan, za su iya sake hanyarsu. Amma ba abu ne mai sauki ba. Tabi’o’i da hanyar da aka bi duk cikin zaman duniya sun rigaya sun mulmula hali har zai zama kadan ne su kan so su karbi Yesu. Ko laifi guda daya ne kawai wanda ya shafi hali, ko marmari guda daya tak, idan aka nace yinsa, yana iya tsaida ikon bishara. Ko wane nishadi na zunubi yana dada karfafa rai gaba da Allah. Shi wanda ya nuna hali na kangarewa, ko rashin kula da gaskiya ta sama, girbin abin da ya shuka ya ke yi Cikin dukan littafi Mai- tsarki ba inda aka fi fadakarwa da kantata girman mugunta kamar kalmomin nan na mai-hikima cewa “Za ya riku da igiyoyin zunubinsa.” Misalai 5 :22.MK 27.4

    Kristi a shirye ya ke ya ‘yatand da mu daga zunubi, amma ba ya tilasa hankalimmu, kuma idan ta wurin ketare doka a ko wane lokaci, hankali ya kallafa ga aikata mugunta, har ba mu da marmarin a yantad da mu ko idan muka ki mu karbi alherinsa me kuma zai yi? Mun hallaka kammu ke nan ta wurin kuduri na kin karbar kauna tasa. “Gashi, yanzu ne lokaci na alheri; ga shi, yanzu ne ranar cheto.” “Yau, kadan kun ji muryatasa, kada ku taurare zukatanku.” 2 Korinthiyawa 6:2; Ibraniyawa 3:7, 8.MK 29.1

    “Gama mutum yana duban aini, amma Ubangiji yana duban zu- chiya.” 1 Samuila 16:7; zuciyar dan-Adam, cike ta ke da iskanci; raddadun tunane-tunanenta na farin ciki da bakin ciki; mazaunin rucfi da rashin tsarki. Ubangiji ya san tunaninta, da kulle- kullenta, da nufenufenta. Je ka wurinsa da ruhunka komai rashin tsabtarsa. Ka bude lollokin zuciyarka ga idanun mai ganin komai, kamar yadda Mai-zabura ya yi, ka ce, “Ka yi binchikena, ya Ubangiji, ka san zuchiyata, ka auna ni, ka san tunani na: Ka duba ko da wata hanyar mugunta daga chikina, ka bishe ni chikin tafarki na har abada.” Zabura 139:23, 24.MK 29.2

    Mutane da yawa su kan karbi wani irin imani wai shi addinini na cikin kwakwalwa, zuciya kuwa ba ta gyaru ba. Bari wannan ya zama addu-arka, “Daga chikina ka halitta zuchiya mai-tsabta, Ya Allah; ka tsabonta daidaitachen ruhu daga chikina.” Zabura 51:10. Ka yi wa ruhunka gaskiya. Ka yi anniya da naciya kamar yadda za ka yi in kana cikin hacfarin ranka na wannan duniya. Wannan matsala ce da ya kamata a daidaita ta tsakanin ruhunka da Allah, a dai- daita ta har abada. Bege mara tushe kawai zai zama hallaka gareka.MK 29.3

    Ka koyi kalmar Allah da addu’a. Wannan Kalma ta Allah tana baiyanawa a gabanka, ta wurin dokar Allah da zaman duniya na Kristi, jigajigai na zaman tsarkaka, wadanda im ba su “Babu mutum da zashi ga Ubangiji im ba tare da ita ba.’’ Ibraniyawa 12:14. Koyon kalma tasa tana sa mu tabbata da kasancewar zunubi, tana baiyana tafarkin ceto a fili. Kasa kunne gareta, karmar muryar Allah mai magana da ruhunka.MK 30.1

    Idan ka farga da girman zunubi, idan ka ga kanka kamar yadda ka ke, kada ka fid da zuciya. Masu zunubi ne Kristi ya zo ya ceta. Ba mu ne za mu sulhuntu ga Allah zuwa kammu ba — ya kauna mai ban al’ajibi — Allah ne cikin Kristi “yana sulhunta duniya zuwa kansa.” 2 Korinthiyawa 5:19. Shi ne ya ke panshe zukatan kangararrun ‘ya ‘yansa ta wurin kaunar tasa mai tsarki. Ba wani ma-haifi na duniya da zai yi hakuri da laifofin ‘ya’yansa, kamar yadda Allah ya ke yi da wa- cfanda ya ke nema ya ceta. Ba wanda ya fi shi mahawara da masu laifi. Ba lebunan dan-Adam da suka fi furta mahawara masu taushi ga batattu kamar Shi. Duk alkawaransa, da fadakunsa, numfashi ne na kauna tasa wadda ta fi gaban furta wa.MK 30.2

    Idan Shaitan ya zo ya fada maka cewa kai babban mai zunubi ne, ka daga ido ka dubi Mai-pansarka, ka yi zancen nagarta tasa. Duban haskensa shi ne zai taimake ka. Ka amsa zunubinka, amma ka ce wa abokin-gaban “Kristi Yesu ya zo chikin duniya domin cheton masu zunubi.” 1 Timothawus 1:15, kuma ya yiwu a cece ka ta wurin kauna tasa mara abin kwatantawa. Yesu ya tambayi Siman a kan mabarta biyu. Daya uban-gidansa yana binsa kudi kadan, dayan kuwa uban-gidansa yana binsa kucfi masu yawa, amma uban-gidansu ya yafe musu duka baki cfaya. Kristi kuwa ya tambayi Siman ya ce cikin su biyun nan wanne ne zai fi ka unar uban — gidansa. Siman ya amsa ya ce “Ina tsammani, shi wanda aka yafe masa mai-yawa.” Luka 7:43. Mu manyan masu zunubi ne, amma Kristi ya mutu domin a gafarta mana. Kyawawan abubuwa na baikonsa sun isa a mika su ga Uban sabili da mu. Wadanda aka gafarta musu zunubai masu yawa su za su fi kauna tasa, za su kuma fi tsayawa kusa da kursi- yinsa su yabe shi domin kauna tasa mai girma da baikonsa mara iyaka. Sai lokacin da muka fi gane kaunar Allah za mu gane kazantar zunubi. Idan muka ga tsawon sarka da aka zuraro domimmu, idan muka gane kadan daga cikin baikon da Kristi ya yi domimmu, sa’annan zuciya za ta narke, ta yi nadama sabo da zunubi.MK 30.3

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents