Duk da duhun da ya mamaye duniya a zamanin mulkin paparuma, ba a iya bice hasken gaskiya kwatakwata ba. A kowace sara akwai shaidu na Allah - mutane da suka ba da gaskiya cewa Kristi ne kadai Matsakanci tsakanin Allah da mutu., suka mai da Littafi kadai kaidar rayuwar su, suka kuma tsarkake Assabbat na gaskiya. Aka lakaba masu suna masu-ridda, aka zargi manufofinsu , aka bata masu suna, aka hana yaduwar rubuce rubecensu, ko kuma a canza rubucerubucen, a sake manufofinsu. Duk da haka suka jimre daga sara zuwa sara, suka rike bangaskiyarsu da tsarki, domin sararakin baya su gada. BJ 60.1
Tarihin mutanen Allah a zamanun duhu da suka biyo bayan mulkin Rum yana rubuce a sama. Amma a duniya da wuya a same su a rubuce, Rum takan murkushe kowace alamar bambancin ra’ayi game da koyaswoyin ta da umurnin ta. Takan hallaka masu ridda har da rubuce rubucen su. Ko sau daya mutum ya nuna shakka game da sahihancin koyaswar Rum, wannan kawai yakan sa a kashe mutumin, komi girma ko kankantar sa. Rum ta yi kokarin hallaka kowace shaidar muguntar ta. Ga masu bambancin ra’ayi. Majalisun ekklesiya sukan umurta cewa a kone litattafai da rubuce rubucen da suka kunshi labarin muguntar. Kafin a kirkiro buga littattafai, littattafai ba su da yawa, kuma ba sa cikin yanayin da za su yi dadin ajiya; don haka bai zama ma Rumawan da wahala su cika nufin su ba. BJ 60.2
Ba a bar wata ekkelesiya da ke kalkashin Rum ta dade tana morar ‘yancin addinin ba. Da zaran mulkin paparuma ya sami iko, nan da nan ya mika hannuwan sa don murkushe dukan wadanda suka ki bin umurnin sa, kuma daya bayan daya ekklesiyoyin suka yarda da mulkinsa. BJ 61.1
A Birtaniya ainihin Kiristanci ya dade da kahuwa. Sa’an nan bisharan da mutanen Birtaniyan suka karba a karni na farko ba ta lalace da riddar Rum ba. Kirista da yawa masu gudun zalunci a Ingila sun sami mafaka a Scotland; daga nan aka kai gaskiyar a Ireland, kuma a dukan kasashen nan an karbi ainihin kiristacin da farin ciki. BJ 61.2
Sa’an da Saxons suka shiga Birtaniya da yaki, kafirci ya yi nasara. Masu nasaran suka ki karban koyaswa daga bayin su, don haka aka atilasta Kirista suka gudu zuwa duwatsu da dazuka. Duk da haka hasken da aka boye na wani lokaci ya ci gaba yana haskakawa. A Scotland bayan shekaru dari, ya haskaka da hasken da ya kai kasashe masu nisa sosai. Daga Ireland, Columba da abokan aikin sa suka taso, kuma da suka tattaro masu-bi da ke warwatse a tsibirin Iona, sai suka mai da tsibirin cibiyar aikin bishararsu. Cikin wadannan masu wa’azi akwai mai-kiyaye Assabbat na Littafi, ta haka kuma aka shiga da gaskiyan nan cikin mutanen. Aka bude makaranta a Iona, daga nan kuwa masu bishara suka dinga zuwa Scotland da Ingila da Jamus, da Switzerland, har da Italiya ma. BJ 61.3
Amma Rum ta sa ma Birtaniya ido, ta kuma kudurta kawo ta kalkashi ikonta. Cikin karni na shida, masu wa’azin ta suka shiga tubar da kafiran Saxony. Barbarians suka karbe su da marmari, suka kuma zuga dubban mutane suka rungumi koyaswar Rum. Sa’an da aikin ya ci gaba, shugabannin ekklesiyar Rum da tubabbun su suka sadu da Kiristan nan na ainihi. Bambanci tsakanin su ya bayana. Kiristan ainihin nan masu kamewa ne, da tawali’u da ruhaniya a hali da koyaswa da tsabi’a, alhali wadacan sun nuna camfi da girman kai da bankaman nan nasu. Dan sakon Rum ya ce ma ekklesiyoyin Kiristan nan su yarda da mulki da daukakar paparuma. Kiristan Birtaniyan nan suka amsa a natse cewa suna marmari su kaunaci dukan mutane, amma paparuma bai cancanci daukaka cikin ekklesiya ba, kuma za su yi masa ban girma irin wanda ake yi ma kowane mai-bin Kristi ne kadai. Aka yi kokari akai akai domin su yi biyayya ga Rum; amma Kiristan nan talakawa masu tawali’u, da suka yi mamakin girman kan yan sakon ekklesiyar, suka nace cewa basu san wani mai-gida ba ban da Kristi. Yanzu kuma aka bayana ainihin ruhun mulkin paparuma. Sai ya ce: “Idan baza ku karbi yan-uwa da ke kawo maku slama ba za ku karbi magabta da za su kawo maku yaki. Idan ba za ku hada kai da mu wajen nuna ma Saxons hanyar rayuwa ba, za ku karbi mutuwa daga wurin su.” Wannan ba barazanar banza ba ce. An yi anfani da yaki da dabara, da rudi a kan shaidun nan na addini na Littafi, har sai da aka hallaka ekklesiyoyin Birtaniya ko kuma aka tilasta su yarda da ikon paparuma. BJ 61.4
A kasashen da Rum ba ta da hurumi, an iske rukunonin Kirista da lalatar ekklesiyar Rum bai shafe su ba, har tsawon daruruwan shekaru. Kafirci dai ya kewaye su har kurakuran sa sun shafe su; amma suka ci gaba suna daukan Littafi a matsayin ma’auni tilo na bangaskiya, suka kuma rike yawancin koyaswoyin Littafin. Kiristan nan sun gaskata dawamar dokar Allah suka kuma kiyaye Assabbat na doka ta hudu. Ekklesiyoyin da suka rike wannan bangaskiya da ayuka sun kasance a Afirka ta Tsakiya da cikin Armeniyawan Asia ne. BJ 62.1
Amma Waldensiyawa sun yi fice wajen tsayayya da mulkin paparuma. A kasar da paparuma ya dasa kursiyin sa, nan ne karyarsa da lalacewarsa suka gamu da matukar tsayayya. Ekklesiyoyin Piedmont sun rike yancinsu har daruruwan shekaru; amma lokaci ya kai daga bisani da Rum tan nace cewa su ba da kai. Daga nan bayan sun ki na wani lokaci, shuabannin ekklesiyoyin nan suka yarda da wannan mulkin da duniya ke biyayya da shi. Amma akwai dai wadanda suka ki yarda da ikon paparuma, sun kudurta za su rike biyayar su ga Allah, su kuma kiyaye tsabtar ibadar su da saukin kan ta. Rabuwa fa ta shigo. Wadanda suka manne ma bangaskiya ta farko suka janye; wadansu suka kaura daga kasar su a Alps, suka daga tutar gaskiya a kasashen waje; wadansu suka koma cikin koguna da kewayen tsaunuka, inda suka kiyaye yancin su na sujada ga Allah. Bangaskiyan nan da Waldensiyawan nan suka rike, suka kuma koyar har daruruwan shekaru ya bambanta da koyaswoyin karyan nan na Rum. Bangaskiyar addinin su ta kafu kan rubutaciyar maganar Allah ne. Amma wadannan Kiristan a inda suka buya daga sauran duniya, suna noman inabi da rike dabbobi ne, tukuna basu sami gaskiyar, sabanin bidi’ar ekklesiyan nan mai-ridda ba. Gaskiyar su ba sabuwa suka karba ba. Sun gaji addinin nan daga ubanin su ne. Suka yi tsayayya domin imanin ekklesiyar manzani, “imani wanda aka bayas ga tsarkaka so daya dungum” Yahuda 3. “Eklesiyar cikin jeji,” amma ba mai girman kai din nan da aka kafa a Rum ba, ita ce ainihin ekklesiyar Kristi, mai lura da muhimman gaskiya da Allah Ya ba mutanen Sa, su ba duniya. BJ 63.1
Daya daga manyan dalilan rabuwar ekklesiyar gaskiya da Rum shi ne kiyayyar Rum ga Assabbat na Littafi. Kamar yadda annabci ya ce, mulkin paparuma ya yar da gaskiya har kasa. Aka tattake dokar Allah cikin kura, yayin da aka daukaka al’adun mutane. Tun da farko aka tilasta ekklesiyoyi da ke kalkashin paparuma su girmama Lahadi a matsayin rana mai-trsarki. Cikin yawan camfi da kuskure, yawanci, har da ainihin mutanen Allah, suka rikice ta yadda, yayin da suke kiyaye Assabbat, suka dena aiki ran Lahadi. Amma wannan bai gamsar da shugabannin ekklesiyar Rum ba. Suka umurta cewa a tsarkake Lahadi a kuma bata Assabbat; suka kuma yi soka mai-karfi game da masu-kiyaye Assabbat din. Ta wurin tserewa daga ikon Rum ne kadai aka iya yin biyayya ga dokar Allah cikin salama. BJ 63.2
Waldensiyawa suna cikin mutanen farko a Turai da suka sami Littafi da aka juya zuwa harshensu. Daruruwan shekaru kafin zamanin gyare gyaren nan, sun mallaki Littafi rubutaciya cikin harshensu. Suka kasance da gaskiya tsaba, wannan kuma ya sa suka zama abin kiyaya da zalunci musamman. Suka sanar cewa ekklesiyar Rum ce Babila mai-riddan nan na Ruya ta Yohanna, kuma a bakin ran su suka tashi tsaye domin tsayayya da kurakuran ta. Yayin da sakamakon matsin zalunci wadansu suka sassauta imanin su, sannu a hankali kuma suka rabu da muhimman kaidodin sa, wadansu kuwa sun manne ma gaskiya. Cikin sararakin duhu da ridda akwai Waldensiyawa da suka ki daukakar Rum, suka ki bautar sifofi cewa bautar gumaka ne, suka kuma kiyaye Assabbat na gaskiya. Cikin kiyaya mafi-muni sun rike imaninsu. Ko da shi ke an zalunce su, sun tsaya da gaske ma maganar Allah da daukakar Sa. BJ 64.1
A cikin kogunan duwatsu, Waldnesiyawa sun sami wurin buya. Nan fa aka rike hasken gaskiya cikin duhun nan da ake kira a Sararakin Tsakiya. Nan kuma shaidun gaskiya suka kwashe dubban shekaru suna rike da imanin zamanin da. BJ 64.2
Allah Ya rigaya Ya tanada ma mutanen Sa haikali mai-daraja ainun wanda ya dace da muhimman gaskiya da ya ba su amana. Ga korarrun amintattun nan, duwatsu alamu ne na adalcin Yahweh. Suka nuna ma yayansu tsayin duwatsun nan kewaye da su suna ba su labarin Shi wanda ba Ya sakewa, wanda maganar Sa tana dawama kamar duwatsun. Allah Ya kafa duwatsun, Ya kuma tokare su da karfi; ba mai iya gusar da su sai Shi Mai-cikaken iko. Haka kuma Ya kafa dokar Sa, harsashen gwamnatinsa na sama da na duniya. Hannun mutum zai iya samun yan-uwan sa mutane ya kuma hallaka rayukan su; amma wannan hannun ba zai iya tumbuke duwatsun daga gindin su, ya jefa su cikin teku ba, kamar yadda ba za su iya canza dokar Allah ba ko daya, ko kuma su share alkawalinsa daya ga masu aikata nufinsa ba. Cikin amincinsu ga dokar Allah, ya kamata bayin Allah su tsaya da karfi kamar tuddai da ba sa sakewa. BJ 65.1
Duwatsun da suka kewaye garin su shaida ce kullum na ikon halita na Allah, tabbaci kuma na tsaronsa da kulawansa. Matafiyan nan suka kawunaci al’ammun nan na kasancewar Allah tare da su. Basu dinga gunaguni don wahalolin su ba; a tsakanin duwatsun nan ba basu ji kamar su kadai ne ba. Suka gode ma Allah domin Ya tanada masu mafaka daga fushi da zaluncin mutane. Sun yi murna don yancin su na sujada gare Shi. Sau da yawa idan magabtansu suka kai masu hari, duwatsun ne sukan zama kariyarsu. Daga tsaunukan nan sukan raira yabon Allah, mayakan Rum kuma basu iya tsayar da wakokin godiyarsu ba. BJ 65.2
Ibadar masu-bin Kristi din nan mai tsabta ce, mai-sauki kuma. Sun girmama kaidodin gaskiya fiye da gidaje da filaye, abokanai, yan-uwa da su kan su ma. Suka yi kokari wajen koya ma matasa kaidodin nan. Akan koya ma yara nassosin tun suna kanana, ana kuma koya masu su daukaka dokar Allah. Littafi bai yi yawa ba a hannun mutane, don haka aka rika hadace nassosi akai kawai. Mutane da yawa sukan iya maimaita dogayen nassosin Tsohon Alkawali da na Sabon Alkawali daga kai, ba sai sun karanta ba. Aka danganta Allah da kyawawan ababan da Ya halita da kuma albarkun Sa na yau da kullum. Kananan yara suka koyi yin godiya ga Allah Mai-bayar da kowane alheri da kowane jin dadi. BJ 66.1
Iyaye sun kaunaci yayan su da hikima ta yadda basu bata su da jin dadi ba. Gabansu akwai rayuwar tsanani da wahala, ko mutuwa ma. Aka koya masu tun suna yara su jimre wahala, su yi biyayya, amma kuma su yi tunani su kuma aikata don kansu. Tun da wuri aka koya masu daukan nauyin kansu, yin hankali da maganarsu, su kuma gane hikimar yin shuru. Idan magabtansu suka ji mumunan kalma daya kawai daga wurinsu, wannan zai iya jawo hallaka ga ran mai-maganar, har da rayukan daruruwan yan-uwan sa, gama kamar yadda dabbobi sukan yi farautar naman da za su ci, haka abokan gaban gaskiya suka rika neman wadanda suka yi yunkurin rike yancin addini. BJ 66.2
Walsensiyawa sun sadakar da ci gaban su na duniya, sabo da gaskiya da naciya cikin hakuri kuma, suka rika fama don neman abincinsu, suka rayar da kowane wurin da za a iya noma a duwatsun; aka so kowane kwari da gefen dutse ya zama gona mai ba da anfani. Tsimi da hakuri suka kasance ilimin da yaran suka samu a matsayin abin gadon su kadai. An koya masu cewa Allah Ya shirya cewa rayuwa ta zama abin koyo ne, kuma za a iya biyan bukatunsu ta wurin aikin kansu ne da hangen gabansu, da kulawansu, da bangaskiyar kansu kuma. Koyaswan nan mai wahala ne da gajiyarwa, amma kuma mai-kyau ne, wanda mutum da ke bukata, makarantar da Allah ya tanada don koyaswar mutum da ci gabansa. Yayin da ake koya ma matasa jimre wahala, ba a manta zancen inganta tunanin su ba. Aka koya masu cewa kowace baiwarsu ta Allah ce, kuma ya kamata a inganta ta don yi masa hidima. BJ 66.3
Ekklesiyoyin Waldensiyawan nan, cikin tsabta da saukin kansu, sun yi kama da ekklesiyar zamanin manzani. Da suka ki daukakar paparuma, sai suka rike Littafi cewa shi kadai ne kaida mara-aibi. Pasocinsu, ba kamar priestocin Rum masu son girma ba, suka bi kwatancin Mai-gidansu wanda “Ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta ma wadansu.” Suka ciyar da garken Allah, suna kai su makiyaya mai-danya da mabulbulan ruwayen maganarsa Mai-tsarki. Ba kamar masu-shagalin nan da girman kai, masu-tattaruwa a manyan majami’u ba, sun rika sujada a kalkashin inuwar duwatsun Alps, ko kuma a lokacin hadari sukan rika taruwa a kogunan duwatsun ne don jin maganar gaskiya ta bakin bayin Kristi. Ban da wa’azin bishara, pastocin sun rika ziyarar marasa lafiya, suna koyar da yara, da gargadi ga wadanda suka yi kuskure, da yin kokarin sasanta masu-sabani da juna, suna karfafa jituwa da kaunar yan-uwa. Lokacin salama sukan dogara ga baye bayen mutane ne don rayuwa; amma kamar Bulus mai-yin tentuna, kowa ya koyi sana’an da yakan dogara da ita in ta kama. BJ 67.1
Matasa sun sami koyarwa daga pastocinsu. Yayin da aka mai da hankali ga fannonin sani iri dabam dabam, an mai da Littafi abin nazari mafi-muhummanci. Aka hadace bishara ta Matta da ta Yohanna, da kuma da yawa cikin wasikun Bulus. An kuma yi anfani da wadansu cikin matasan wajen yin kofen nassosin. Wadansu rubuce rubucen sun kunshi dukan Littafi, wadansu kuma zababbun nassosi ne kawai da akan hada da fassara ta bakin wadanda suka iya bayyana Littafin. Ta haka aka kawo tamanin gaskiya da masu neman daukaka kansu fiye da Allah suka dade suna boyewa. BJ 67.2
Ta wurin kokari cikin hakuri, wani lokaci ma cikin duhun koguna, da hasken tocilan, aka rubuta nassosi masu-tsarki, aya bayan aya, sura bayan sura. Ta haka aikin ya ci gaba, bayyanannen nufin Allah kuma yana haskakawa kamar zinariya mara aibi; ya kara haske da karfi ma sabo da jarabawa da aka sha dominsa, wanda masu yin aikin ne kadai ke iya ganewa. Malaiku daga sama sun kewaye amintattun ma’aikatan nan. BJ 68.1
Shaitan ya bukaci priests da shugabannin su su bizne maganar gaskiya kalkashin karmomin kuskure, da ridda, da camfi, amma ta hanya mai-ban mamaki, an kiyaye shi ban da aibi duk tsawon sararakin duhu. Ba shi da hatimin mutum, sai amincewar Allah. BJ 68.2
Mutane ba sa gajiya da kokarin su na duhunta bayananiyar ma’anar maganar Allah, da kuma neman sa nassosi su saba ma juna, amma kamar jirgin kan teku, maganar Allah takan fi karfin kowace guguwar da ke so ta rushe ta. Yadda ma’adini yakan kasance da jerin zinariya da azurfa a boye a kalkashin kasa, domin duk mai-so dole sai ya tona da karfi, haka ne Littafi yana da tamanin gaskiya wanda ake bayana ma wanda ya nema ta wurin naciya cikin addu’a da tawali’u kadai. Allah Ya ayyana Littafi ya zama littafin koyaswa ne ga dukan yan Adam, yara da matasa da manya, a kuma yi nazarin sa kowane lokaci. Ya ba mutane maganarsa domin ta bayana Shi. Kowace sabuwar gaskiya da aka fahimta, sabuwar bayani ce ta halin Mai-ba da ita. Nazarin Littafi ne Allah Ya kadara ya zama hanyar jawo mutane zuwa ga Mahalicinsu, a kuma ba su Karin sanin nufinsa. Hanyar sadarwan ken nan tsakanin Allah da mutum. BJ 68.3
Yayin da Waldensiyawa suka mai da tsoron Ubangiji mafarin ilimi, basu rufe ido ga muhimmancin sanin duniya ba, sanin mutane da na ruhaniya, inganta tunani da basira kuma. Daga makarantunsu a cikin duwatsun aka tura wadansu matasa makarantu a biranen Faransa ko Italiya, inda akwai fili mai fadi don karantarwa da tunani da kulawa fiye da na Alps. Matasan da aka aika sun fuskanci jaraba, sun ga mugunta, sun sadu da wakilan Shaitan wadanda suka matsa masu su karbi ridda da rudi mafi-muni. Amma ilimin su daga yaranta irin wanda ya rigaya ya shirya su don jarabobin nan ne. BJ 68.4
A makarantun da suka je, basu yi abokan shawara da kowa ba. An dinka masu rigunansu ta yadda za su iya boye rubutatun maganar Allah a ciki. Sun rika tafiya da maganan nan duk inda za su, ba tare da tayar da zato ba, a hankali kuma sukan ajiye wadansu rubutattun nassosin inda masu-alamar son gaskiya za su gani. Tun yarantakan su an hori matasan Waldensiyawan nan da wannan manufan ne; sun gane aikinsu,suka kuma yi shi da aminci. An sami masu-tuba zuwa imani na gaskiya a makaranun nan, kuma sau da yawa kaidodin imanin nan sukan mamaye dukan makarantar; duk da haka shugabannin ekklesiyar Rum ba su iya gane tushen kaidodin nan ba, komi binciken su. BJ 69.1
Ruhun Kristi ruhun shelar ishara ne. Wanda ya tuba yakan fara so ya ja wadansu zuwa wurin Mai-ceton ne su ma. Irin ruhun Waldesiyawan ke nan. Sun ji a jikin su kawai cewa Allah Ya bida daga gare su abin da ya wuci kiyaye gaskiya cikin tsarkin ta kawai a cikin ekklesiyoyin su; cewa nawaya ta rataya a kan su, su haskaka haskensu ga wadanda ke duhu; ta wurin ikon maganar Allah suka so su karya bautan da Rum ta kafa. An horar da pastocin Waldeniyawan, aka kuma bukaci duk mai-son aikin pasto ya sami horaswa na mai-bishara. Kowane dayansu ya kan yi aikin shekara uku yana lura da wata ekklesiya a wani wuri a gida. Wannan aiki da ya bukaci sadakarwa, gabatarwa mai-dacewa ne zuwa rayuwar pasto a wancan zamani mawuyaci, matasan da aka shafe su pastoci su ga ba rayuwa ce ta wadata da daukaka ba, amma rayuwa ta wahala da hatsari, mai yiwuwa ma har da mutuwa. Masu bisharan suka rika tafiya su biyu biyu, yadda Yesu Ya aiki almajiransa. Akan hada kowane matashi da wani dattijo mai-kwarewa mai yi ma matashin jagoranci da horaswa, aka kuma bukaci matashin ya yi biyayya. Ba kowane lokaci ne sukan kasance tare ba, amma sukan dinga saduwa don addu’a da shawara, ta haka kuma suka rika karfafa juna cikin imanin. BJ 69.2
Da a ce sun bayyana manufar aikinsu, lallai da an hana aikin, sabo da haka suka boye ainihin manufarsu. Kowane pasto ya iya wata sana’a ko aiki, suka kuma yi aikin su da sunan sana’a. Yawanci sukan zabi jari ne ko talla. “Suka sayar da yaduna ko kayan ado, ko dai wadansu ababa wadanda ba a cika samu ba sai a kasuwanni masu nisa, aka kuwa marabce su a matsayin yan kasuwa inda da an ki su a matsayin sun na masu-wa’azi.” Kullum sukan bidi hikima daga wurin Allah, domin su iya gabatar da tamanin nan da ya fi zinariya ko lu’alu’ai. A boye sun rika tafiya da Littafi ko kuma nassosinsa, kuma sa’an da dama ta samu, sukan jawo hankulan abokan cinikinsu ga Littafin. Sau da yawa ta wurin haka akan jawo hanlkali zuwa maganar Allah, akan kuma bar masu Littafin ko nassosin idan sun nuna suna so. BJ 70.1
Aikin masu bisharan nan ya fara a wuraren da ke kewaye da duwatsun da suke da mazamnin su ne, amma ya yadu daga wurin. Da kafafun su ba takalma, da kuma tufafi tsofofi sabo da yawan tafiya, kaman na Mai-gidansu, suka dinga ratsawa ta manyan birane, suka shiga kasashe masu-nisa. Ko ina sun watsa irin. Ekklesiyoyi suka taso duk inda suka wuce, jinin amintattu da aka kashe kuma ya dinga ba da shaidar gaskiyar. Ranar Allah za ta bayana rayuka da yawa da amintattun nan suka jawo. A boye, shuru kuma, maganar Allah ta dinga shiga cikin Kirista, ana kuma karban ta da murna a gidaje da zukatan mutane. BJ 70.2
Ga Waldaelsiyawan, Littafi ba labarin abin da Allah Ya yi da mutane ne a da can kawai, da bayanin aikin da ya rataya a kafadar su yanzu ba, amma ya hada har da bayanin matsaloli da daukaka na nan gaba. Sun gaskata cewa karshen komi ya kusa, kuma yayin da suke nazarin Littafi cikin addu’a da hawaye, maganar sa ta burge su sosai, suka kuma kara ganin aikin da ya rataya a kafadar su na sanar ma sauran mutane gaskiyar Littafi mai-kawo ceto. Suka ga shirin ceto a bayyane sarai cikin Littafin, suka kuma sami ta’aziya da bege da salama cikin ba da gaskiya ga Yesu. Yayin da hasken ya kara masu ganewa, ya kuma faranta masu zukata, suka yi marmarin isar da hasken nan ga wadanda ke cikin duhun kuskuren ekklesiyar paparuma. BJ 71.1
Sun ga cewa kalkashin shugabancin paparuma mutane da yawa suna faman neman yafewa ta wurin azabtar da jikunansu, sabo da zunubin su. Da shi ke an koya masu dogara ga kyawawan ayukan su don samun ceto, sai suka rika duban kansu, suna tunanin yanayinsu na zunubi, suna ganin kansu fuska da fuska da fushin Allah, suna azabar da ruhu da jiki, duk da haka ba magani. Ta haka ne koyaswoyin Rum suka daddaura ruhaniyar mutane. Dubbai suka rabu da kasashe da yan-uwa, suka yi rayuwar su cikin kulle na covent. Ta wurin azumi akai akai da bulala na zalunci, da kwana-gani, da durkusawa na sa’o’i da yawa cikin sanyi a kan duwatsu, ta wurin tafiya mai-nisan gaske, ta wurin wahalar da jiki ta hanyar wulakanci da tsanani mai-ban tsoro, dubbai suka nemi damar samun salamar lamirinsu, amma a banza. Duk da damuwa game da zunubin su da tsoron fushin Allah, da yawa suka ci gaba da shan wahalar su, har sai da suka mutu, ba kuma wanda ya ba su bege. BJ 71.2
Waldensiyawan su yi marmarin mika ma mutanen nan gurasar rai, su bude masu sakonin salama cikin alkawuran Allah, su kuma nuna masu cewa Kristi ne kadai begen cetonsu. Suka nuna cewa koyaswar cewa wai kyawawan ayuka za su iya yin kafara don ketarewar dokar Allah karya ce. Dogara ga kokarin mutum ya kan hana ganin kaunar Kristi mara-iyaka. Yesu Ya mutu a matsayin hadaya sabo da mutum, domin yan Adam fadaddu ba za su iya yin komi don gamsar da Allah ba. Anfanin giciyewar Mai-ceto da tashinsa su ne tushen imanin Kirista. Dogarar mutum ga Kristi tabbas ne, kuma dole mannewar sa da Kristi ta zama kamar ta hannu ko kafa da sauran jiki, ko kuma mannewar reshe da kuringar anab. BJ 72.1
Koyaswoyin su paparuma da priestoci sun sa mutane suka rika gani kamar halin Kristi zalunci ne da bakin ciki, hali mara-kyau. Suka nuna kamar Mai-ceton ba ya tausaya ma dan Adam, ta yadda har ya zama dole sai an nemi tsarkaka su shiga tsakani. Wadanda maganar Allah ta rigaya ta wayar masu da kai sun yi marmarin nuna ma mutanen nan cewa Yesu Mai-ceton su mai-tausayi ne da kauna, kuma yana tsaye, hannuwansa a mike, yana gayyatar kowa ya zo wurinsa da nauyin zunubinsa, da damuwarsa, da gajiyarsa. Sun yi marmarin warware matsalolin da Shaitan ya tara ma mutane domin kada su ga alkawuran har su zo kai tsaye wurin Allah, suna furta zunuban su, suna kuma samun gafara da salama. BJ 72.2
Da marmari sosai Waldensiyawan nan masu wa’azin bishara suka bayana ma duk mai-tambaya gaskiyar bisharar. A hankali mai-wa’azin ya kan fitar da rubutacen nassin. Farin cikin shi ne ya ba da bege ga mai-lamiri wanda zunubi ya buga shi, wanda yana ganin Allah kamar mai-ramuwa ne kawai, wanda kullum yana jira ne kawai Ya zartas da hukumci. Da harshen tausayi, idon sa cike da hawaye, yawancin lokaci a durkushe ma, mai-bisharan yakan bude ma mutanen alkawuran da ke bayana begen da mai-zunubi ke da shi kadai. Ta haka hasken gaskiyan ya shiga tunanin mutane da yawa, ya kawar da girgijen duhu, har sai da ranar adalci ta haskaka da warkarwa cikin haskensa. Sau da yawa akan karanta wani fannin Littafi akai akai, mai-ji kuma ya rika cewa a sake maimaitawa, kamar yana so ya tabbatar ma kansa cewa ya ji da kyau. Musamman an rika cewa a maimaita kalmomin nan: “Jinin Yesu Dan Sa yana tsarkake mu kuma daga zunubi duka.” Yohanna I, 1:7. “Kuma kamar yadda Musa ya ta da maciji bisa cikin jeji, hakanan kuma dole za a ta da Dan mutum bisa, domin dukan wanda yana ba da gaskiya shi sami rai na har abada a chikinsa.” Yohanna 3:14,15. BJ 72.3
Da yawa basu yarda da rudin Rum ba. Suka ga rashin anfanin aikin tsakanci da aka ce mutane ko malaiku ke yi a madadin mai-zunubi. Yayin da hasken gaskiya ya haskaka tunanin su, suka ta da murya da murna suka ce: “Kristi ne priest di na, jinin Sa ne hadaya ta; bagadin Sa ne wurin tuba na.” Suka sallamar da kansu gaba daya ga aikin Yesu, suna maimaita kalaman nan cewa: “Ba shi kwa yiwuwa a gamshe shi sai tare da bangaskiya.” Ibraniyawa 11:6. “Babu wani suna kalkasin sama, da aka bayas wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” Ayukan 4:12. BJ 73.1
Tabbacin kaunar Mai-ceto ya zama ma wadansu wulakantattun mutanen nan da wuya su gane. Saukin da wannan ya kawo mai-yawa ne sosai, aka haska masu hasken nan mai-yawa, har suka ji kamar ana kai su sama ke nan. Suka sa hannun su cikin hannun Dutsen Sararraki. Dukan tsoron mutuwa an kawar. Yanzu ma suka so kurkuku, idan har ta wurin wannan za su daukaka sunan Mai-fansarsu. BJ 73.2
A boye aka rika kawo maganar Allah ana karantawa, wani lokaci don mutum daya ma, wani lokaci don wata kingiyar mutane kalilan da ke begen samun haske da gaskiya. Sau da yawa akan kwana ana karatun nan sabo da mamaki da sha’awar masu ji, har ma sau da yawa akan roki mai-karatun ya dakata tukuna, har sai an gama fahimtar tarihin ceton. Sau da yawa kuma akan ji kalmomi kamar: “Ko Allah zai karbi bayaswa ta? Za ya gafara mani kuwa?” Sai a karanta amsar cewa: “Ku zo gareni dukanku da ku ke wahala, masu nauyin kaya kuma, ni kwa in ba ku hutawa.” Matta 11:28. BJ 73.3
Bangaskiya takan amice da alkawalin, akan kuma ji amsa cewa: “Ba damuwar tafiya kuma, ba tafiya mai-wahala zuwa wurare masu-tsarki. Zan iya zuwa wurin Yesu yadda ni ke, mai-zunubi, mara tsarki kuma, kuma ba zai ki addu’ar tuba ta ba. ‘An gafarta zunuban ka’ nawa, har nawa ma za a gafarta!” BJ 74.1
Farin ciki yakan cika zuciya, akan kuma girmama sunan Yesu ta wurin yabo da godiya. Wadannan masu-murnan sukan koma gidajen su su bayana haske, suna ba kowa labarin abin da ya faru da su; cewa sun sami Hanyar gaskiya, mai-rai kuma. Akwai iko da ba a saba da shi ba, cikin maganar Littafi da ke zuwa kai tsaye cikin zukatan wadanda ke begen samun gasiyar. Muryan Allah ne kuma yakan taba zukatan dukan wadanda suka ji. BJ 74.2
Dan sako na gaskiya yakan tafi abinsa; amma tawali‘unsa, gaskiyarsa, himmarsa da kwazonsa sukan zama abin labari. Lokuta da dama masu jinsa ba sa tambayan inda ya fito da inda za shi. Da farko sukan cika da mamaki, daga baya kuma sukan cika da murna da godiya har ma ba sa tunanin tambayan shi ababan nan. Sa’an da suka roke shi ya bi su zuwa gidajen su, yakan amsa cewa tilas ne ya ziyarci batattun tumakin garken. Su kan tambaya, Ko shi malaika ne daga sama? BJ 74.3
Sau da yawa ba a sake ganin dan sakon nan kuma. Ya tafi wadansu kasashe kuma, ko kuma yana fama a wani kurkuku daba a sani ba ma, ko kuma kasusuwan sa suna shudewa a wurin da ya shaida kalmomin gaskiyan. Amma ba za a iya hallaka kalmomin da ya bari a baya ba. Suna aikin su a zukatan mutane; lokacin hukumci ne kadai za a san sakamakon. BJ 74.4
Waldensiyawa masu wa’azin nan sun kai ma mulkin Shaitan hari ne, ikokin duhu kuma suka taso suna tsaro ba barci. Shaitan ya dinga lura da kowane yunkuri na ci gaba da gaskiyar, ya kuma tsoratar da wakilansa. Shugabannin ekklesiyar Rum suka ga hadari ga ekklesiyarsu daga aikin matafiyan nan. Idan aka bar hasken gaskiya ya ci gaba da haskakawa, zai share gizagizan kuskure ya kuma rinjayi mutane. Zai kai tunanin mutane wurin Allah kadai, ya kuma rushe daukakar Rum daga bisani. BJ 75.1
Kasancewar mutnen nan masu rike imanin ekklesiyar farko shaida ce ta riddar Rum, kuma don haka suka janyo kiyayya da zalunci mafi tsanani. Kin sallamar Littafi da suka yi ma ya zama laifin da Rum ba ta iya yafewa ba. Ta dauki kudurin shafe su daga duniya. Lokacin nan ne aka fara yake yake mafi-muni kan mutanen Allah a gidajen su cikin duwatsu. Aka tura masu masu-bincike, sau da yawa aka rika maimaita irin abin da Kayinu ya yi ma Habila. BJ 75.2
Akai akai aka rika lalata gonakin su, aka kawas da gidajen su da majami’un su ta yadda inda da akwai gonaki masu-albarka, da gidajen jama’a da basu yi laifi ba, masu kwazon nema, ba abin da ya rage sai hamada. Kamar yadda dabba mai-barna yakan kara hasala in ya taba jini, haka fushin ‘yan paparuma ya kara tsanani sabo da wahalolin masu-wa’azin nan. Aka hori masu wa’azin imani mai-tsarkin nan har ketaren duwatsun, aka yi farautar su cikin kwari inda suka buya, cikin manyan dazuzuka da tsaunuka kuma. BJ 75.3
Ba a iya zargin kungiyan nan da wani hali na rashin kirki ba. Ko magabtan su ma sun ce mutanen nan masu salama ne marasa hayaniya, masu imani kuma. Babban laifin su shi ne cewa basu yarda su yi sujada ga Allah bisa ga nufin paparuma ba. Sabo da laifin nan kowane wulakanci da zagi da zalunci da mutane ko aljannu ke iya kirkirowa an yi masu. BJ 75.4
A wani lokaci, sa’an da Rum ta yi niyyar rushe kungiyan nan da ta ki jini, paparuma ya kafa dokar da ta mai da su masu ridda da ya kamata a kashe su. Ba a zarge su da zaman banza ko rashin gaskiya ko tashin hankali ba, amma aka ce suna da kamanin imani da tsarkin da ke rudin “tumakin ainihin garken.” Don haka paparuma ya umurta cewa “muguwar haramtaciyar kungiyar kangararrun nan,” da suka “ki rantsewa cewa sun bar akidar su, sai a murkushe su kamar macizai masu dafi.” Ko paparuma ya san zai sake saduwa da kalmomin nan nasa? Ko ya san cewa an rubuta su a litattafan sama, domin a nuna masa su a ranar shari’a? “Da shi ke kuka yi wannan ga guda daya a chikin wadannan yan-uwana,” in ji Yesu, “ni kuka yi ma.” Matta 25:40. BJ 76.1
Dokan nan ta kirayi sukan membobin ekklesiya su shiga yaki da masu riddar. Ladar shiga mugun aikin nan it ace an “yafe masu dukan wahaloli da horo na ekklesiya, na kan su da na duka; ta yafe ma dukan wadanda suka shiga yakin kowace rantsuwa da suka taba yi; ta halarta masu duk wata gona ko fili ko gida da suka mallaka ba bisa doka ba; ta kuma yi alkawalin yafe zunuban dukan wanda ya kashe mai-ridda. Ta soke duk wata yarjejjeniya mai-anfani ga Walddensiyawa, ta umurci masu yi masu aiki a gida su rabu da su, ta hana kowa ba su kowane irin taimako, ta kuma ba kowa dama ya kwace dukiyarsu.” Wannan ya bayana ainihin ruhun da ke aiki a boye. Rurin dragon ne, ba muryar Kristi ake ji a cikin dokar ba. BJ 76.2
Shugabannin ekklesiyar Rum ba su yarda su daidaita halayen su da babban ma’aunin dokar Allah ba, amma suka kafa ma’aunin da ya gamshe su, suka kuma so kowa ya bi su domin haka Rum ta so. Aka aikata mugunta mafi-muni. Miyagun priestoci da paparuma sun yi aikin da Shaitan ya ba su. Babu jinkai a cikin su. Ruhu dayan da ya giciye Kristi ya kuma kashe manzanin, ruhun da ya kuma motsa Nero ya saba ma amintattu a zamanin sa, shi ne ya motsa a raba duniya da kamnatattu na Allah. BJ 76.3
Zaluncin da aka yi ma masu tsoron Allahn nan, su sun jimre cikin hakuri da naciyar da ta girmama Mai-fansarsu. Duk da yakokin da aka yi da su, da kisan wulakanci da aka yi masu, sun ci gaba da aika masu-wa’azi su baza gaskiyan. Aka yi farautar su har mutuwa; duk da haka jininsu ya yi ma irin da aka shuka ban-ruwa, kuma bai kasa ba da ‘ya’ya ba. Ta hakanan Waldensiyawan suka shaida Allah, har daruruwan shekaru kafin haihuwar Luther. A warwatse cikin kasashe dabam dabam suka shuka irin Canjin nan da ya fara a lokachin Wycliffe, ya habaka a zamanin Luther, za a kuma ci gaba da shi har karshen lokaci ta hanun wadanda ke shirye ma su sha wahala “sabili da maganar Allah da shaidar Yesu.” Ruya 1:9. BJ 77.1