Kafin Lokacin Juyin juye-hali, yakan yi wuya a ga Littafi Mai-tsarki, amma Allah bai bari a hallaka maganar sa gaba daya ba. Yakan wadatar da maganar rai kamar yadda yakan bude kofofin kurkuku domin kubutar da bayinsa. A kasashen Turai, Ruhun Allah ya rika motsa mutane suka dinga neman gaskiya kamar masu neman boyayen tamani. Suka rika nazarin Littafi Mai-tsarki da marmari ainun. Sun yarda su karbi haske, ko da me zai faru da su. Ko dashike basu ga kowane abu sarai-sarai ba, aka ba su ikon fahimtar koyaswoyin gaskiya da yawa da aka dade ana boyewa. A matsayin su na aikakkun Allah, suka yi dukufa wajen warware sarkokin kuskure da na camfe camfe, suna kira ga wadanda an dade ana takura masu, cewa su tashi su kwace yancin su. BJ 78.1
Ba don Waldensiyawa ba kam, da masana harsuna ne kadai suke da Kalmar Allah; amma lokaci ya yi da za a juya maganar Allah a kuma kai ma mutanen kasashe daban dabam cikin yarurukan su. Lokacin duhu ya fara wucewa ga duniya, alamun wayewan gari kuma sun fara bayana a kasashe daban dabam. BJ 78.2
Cikin karni na goma sha hudu, jagoran Juyin juye-hali ya taso a Ingila. John Wycliffe ne ya fara juyin juye-hali a cikin Kiristanci ko ina, ba a Ingila kadai ba. Tawayen da ya fara yi ma Rum ne ya bude gwagarmayar da ta kai ga yantarwar mutane da ekklesiyoyin da al’ummai. BJ 79.1
Wycliffe ya sami isashen ilimi, kuma ya mai da tsoron Ubangiji mafarin ilimi. A makaranta an san shi da son addini da kuma baiwa iri iri ga kuma yawan ilimi. Don son ilimi, ya so ya koyi kowane fannin ilimi. Ya ilimantu ta fannin nazarin ussan ilimi, da kaidodin ekklesiya, da fannin doka, musamman dokar kasarsa. Muhinmincin horaswan nan da ya samu lokacin kuruciyarsa cikin gwagarmayarsa ya bayana can gaba. Sabo da kwarewarsa game da irin tunanin zamaninsa ne ya iya bayana kurakuran zamanin, tawurin sanin dokar kasa da ta ekklesiya kuma ya iya sa hannu cikin gwagwarmayar neman ‘yancin dan adam da na addini. Yayin da ya iya anfani da makamai daga Kalmar Allah, ya kuma sami horaswar makaranta, ya kuwa gane dabarun masana. Karfin iyawansa da kuma yawa da zurfin saninsa sun sa abokansa da magabtansa ma suka rika bashi girma. Mabiyansa suka ji dadin ganin cewa jagoransu yana daga cikin manyan masanan kasarsu; magabtansa kuwa basu iya rena aikinsa na neman canji ko kuma su nuna wani gazawa ko jahilci daga wurin jagoran canjin ba. BJ 79.2
Yayin da Wycliffe ke koleji, ya shiga nazarin Littafi sosai. A wancan zamanin da ba a rigaya an juya Littafi Mai-tsarki daga harsunan asalin ba, masu ilimi ne sukan sami sanin gaskiyar. Sabo da haka ilimin Wycliffe ya shirya shi domin aikin san a neman canji. Masana suka yi nazarin Maganar Allah suka, sami gaskiyar alherinsa a bayane. Suka rika baza gaskiyan da suka samu, wanda kuwa ya kai wadansu ga Maganar Rai. BJ 79.3
Sa’anda aka jawo hankalin Wycliffe zuwa Littafi Mai-tsarki, ya shiga bincikensa da irin kwazon da ya sa shi ya kware a ilimin da ya samu a makaranta. Kafin nan, ya dinga samun wani marmarin da ilimin sa da koyarswar ekklesiya basu iya gamsarwa ba. A cikin maganar Allah, ya sami abin da ya dade yana nema bai samu ba. Nan ne ya ga shirin ceto a bayane ga kuma Kristi kadai a matsayin Matsakancin mutane. Ya ba da kansa ga bautar Kristi, ya kuma kudurta yin shelar kowace gaskiya da ya gano. BJ 80.1
Kamar sauran masu neman canji da suka biyo bayan sa, Wycliffe da farkon aikin sa bai san inda aikin zai kai shi ba. Bai shirya kan sa gadan-gadan don hamayya da Rum ba. Amma dole ne rikon gaskiya ya kai shi ga magabtaka da karya. Duk sa’anda ya kara gane kuskeren paparuma, ya kan kara kwazo wajen bayana koyarswar Littafin. Ya ga cewa Rum ta rabu da maganar Allah, ta rungumi ala’adun mutane ba da tsoro ba, ya zargi priestoci da yin watsi da Littafin, ya kuma bidi cewa a dawo ma mutane da Littafin, a kuma mayar da muhinmincin sa ga ekklesiya. Shi kwararren mallami ne, shahararen mai-wa’azi, kuma rayuwar sa ta yau da kullum ta je daidai da wa’azinsa. Saninsa na Littafin da karfin koyaswarsa da rayuwarsa mai-kyau da karfin halinsa, sun kawo masa bangirma da amincewar mutane. Mutane da yawa basu gamsu da addininsu ba kuma, domin sun ga zunubin da ya mamaye ekklesiyar Rum, suka cika da fushi sa’anda suka ga cewa Wycliffe yana samun karbuwa fiye da su. BJ 80.2
Wycliffe mai-iya gane kuskure ne da sauri, ya kuma kushe kurakuran Rum ba tsoro. Yayin da yake aikin lura da ruhaniyar sarki, ya dauki mataki da karfin hali na hana sarkin Ingila biyan gandu ma paparuma, ya kuma nuna cewa ikon da paparuma ya ba kansa bisa shugabannin kasa ya saba ma hankali da Littaffin. Ababan da paparuma ya nema sun ta da haushi sosai, koyaswoyin Wycliffe kuma suka yi tasiri sosai ga manyan masanan kasar. Sarki da fadawansa suka hada kai, suka ki zancen nan na ikon paparuma bisa sarakuna da kuma cewa sarki ya rika biynasa gandu. Ta haka aka rage darajar paparuma a Ingila. BJ 81.1
Wani abin da Wycliffe ya ki akai shi ne zancen kungiyoyin kebabbun membobin ekklesiya da al’adar yan bara da ba a yarda su mallaki dukiya ba. Masu baran nan sun mamaye Ingila, suka kaskantar da kasar suka kuma rage ci gabanta. Kwazo, ilimi, da tarbiyya duka suka sami damuwa. Rayuwar yan kungiyoyin na zaman banza da bara, ba wai ya rika tsotse dukiyar mutane kawai ba, amma ya sa aka rena masu yin aiki mai-anfani kuma. Matasa suka rasa himmar su, suka zama malalata. Ta wurin tasirin yan baran, da yawa suka shiga rayuwar kadaici da zaman zuhudu, ba aikin komi, ba da yardar iyayensu ba, ba kuma da saninsu ba, sabanin umurnin iyayen ma. Wani uban ekklesiyar Rum na zamanin da, don nuna fifikon zaman zuhudu bisa kaunar yara ga iyaye, ya ce “ ko da babanka zai kwanta a gaban kofarka, yana kuka yana makoki, mamanka kuma ta nuna jikin da ya haife ka da nonon da ya rene ka, ka tabbata ka tattake su da sawayenka, ka kuma mike kai tsaye zuwa wurin Kristi” Ta wurin wannan “mugunta na rashin mutunci,” yadda Luther ya bayana abin nan, “wanda ya fi kama da kerkeci da azalumi ne, ba Kiristi da mutum ba,” aka taurara zukatan yara sabanin iyayensu. Haka shugabanin mulkin paparuma suka yi, kamar Farisawa na da, suka wofinta dokar Allah ta wurin al’adarsu. Ta wurin wannan aka warwatsar da iyalai, aka kuma raba iyaye da yayansu, maza da mata. BJ 81.2
Har daliban jami’o’i ma an rude su ta wurin karyan shugabannin addini, har aka sa suka shiga kungiyoyin nan. Da yawa daga baya sun tuba da daukan wannan mataki, ganin cewa sun bata rayuwarsu, suka kuma jawo ma iyayensu bakin ciki, amma da zaran sun shiga tarkon, basu iya samun yancinsu ba kuma. Iyaye da yawa don tsoron tasirin yan zuhudun, suka ki kai yaransu jami’a. Yawan dalibai da ke zuwa jami’a sai ya ragu sosai.Makarantu suka lalace, jahilci kuma ya karu. BJ 82.1
Paparuma ya rigaya ya ba yan zuhudun nan ikon sauraron furta laifukan mutane tare da yi masu gafara. Wannan ya jawo mugunta sosai. Domin kara ma kansu riba, masu ba da gafaran sun mai da gafara araha, ta yadda kowane irin mai-laifi yakan zo wurinsu, sabo da haka kuwa munanan laiuka suka karu. Aka bar mataulata da marasa lafiya cikin wahala, alhali baye-bayen da ya kamata su magance damuwarsu, yan zuhudu sun karbe, ta wurin rokon sadaka har da barazana ma, aka zargi wadanda basu ba da sadakar ba da rashin imani. Duk da cewa sun ce su matalauta ne, wadatar yan zuhudun nan ya dinga karuwa, manyan gidajensu da kyawawan teburansu sun kara nuna talaucin al’ummar. Yayin da suke kashe lokacinsu cikin holewa da shakatawa a madadin su kan su, suka rika aikan jahilai wadanda sun iya maimaita labaru, da tatsuniya, da ba’an da suka ji ne kadai, domin a ba mutane dariya kawai. Duk da haka ‘yan zuhudun sun ci gaba da rike jama’a da yawa, suka nuna masu cewa iyakar abin da addini ke bukata shi ne a yarda da daukakar paparuma, a girmama tsarkakansa, a kuma rika ba yan zuhudu kyautuka, kuma wai wannan ya isa ya samo masu wuri a sama. BJ 82.2
Masana masu imani sun yi kokari a banza don kawo canji a kungiyoyin nan na ‘yan zuhudu; amma Wycliffe, da ganewa mai-kyau, ya tinkari tushen zunubin ne, inda ya ce tsarin kansa na karya ne, kuma ya kamata a kau da shi. Aka fara shawara da bincike. Yayin da ‘yan zuhudun suka shiga ko ina a kasar suna tallen gafarar paparuma, mutane da yawa suka yi shakkar yiwuwar sayen gafara da kurdi, suka tambaya ko ba wurin Allah ya kamata su bidi gafara ba, maimakon wurin paparuma. Da yawa suka yi mamakin kwadayin ‘yan zuhudun, wadanda handamar su babu iyaka. “‘Yan zuhudun Rum da priestocin ta”, inji mutane, “suna cinye mu kamar ciwon daji. Dole Allah ya cece mu, im ba haka ba mutane za su hallaka.” Domin su boye handamar su, ‘yan zuhudun nan masu-bara, suka ce wai suna bin kwatancin Mai-ceto ne, cewa wai da kyautukan mutane ne aka taimaki Yesu da almajiransa. BJ 83.1
Wannan ikirarin ya jawo masu cikas, domin ya sa mutane da yawa komawa Littafi domin su ga gaskiyan da kansu, abin da kuwa Rum bata so ba kenan. Tunanin mutane ya koma ga Tushen gaskiya, wanda shi ne ta so ta boye. BJ 83.2
Wycliffe ya fara rubutu yana kuma wallafa majallu game da yan zuhudun, ba wai don yana neman jayayya da su ba, sai don jawo hankulan mutane ga koyaswoyin Littafin da kuma Tushen Littafin. Ya sanar da cewa ikon paparuma na yin gafara ko na cire mutum daga ekklesiya bai bambanta da na sauran priestocin ba, kuma cewa ba wanda za a iya cire shi daga ekklesiya ma ainihi, sai dai wanda ya rigaya ya kai kansa kalkashin hukuncin Allah. Babu wata hanyar sa da ta fi wannan kada mulkin paparuma wanda ya kama, ya kuma rike miliyoyin mutane. BJ 83.3
Kuma, an sake kiran Wycliffe domin shi kare ‘yancin sarkin Ingila daga fetsa da Rum ke yi masa, kuma da aka nada shi jakadan sarki, ya yi shekara biyu a Netherlands, yana shawarwari da kwamishinonin paparuma. Nan ya sami saduwa da masu aikin ekklisiya daga Faransa, da Italiya, da Spain, ya kuma samin damar duba bayan labulen, har ya sami sanin ababa da yawa da zamansa a Ingila kawai bai bar shi ya gani ba. Ya koyi ababan da za su taimake shi aiki nan gaba. Daga wakilan nan daga fadar paparuma ya gane ainihin hali da manufar mulkin ekklesiyar. Ya koma Ingila ya maimaita koyaswoyinsa na da a fili, da karin kwazo, yana cewa kiyashi, fadin rai, da rudu alloli ne na Rum. BJ 83.4
Cikin daya daga rubuce rubucensa game da paparuma da masu tara masa dukiya y ace: “Daga kasar Rum suna janye rayuwar matalauta, da kuma dubban lambobi daga kurdin sarki duk shekara, sabo da hidimomin ekklesiya da ababan ruhaniya, wannan la’antaciyar ridda ce ta cinikin gafara. Kuma hakika ko da kasarmu tana da babban tudun zinariya, kuma ba wanda ke dibawa sai masu tattara ma priest din nan dan duninya, a hankali wata rana tudun nan zai kare dole; domin kullum yana daukan kurdi daga kasarmu, kuma ba ya mayar da komi sai la’anar Allah sabo da sayar da gafara da yake yi”. BJ 84.1
Jima kadan bayan ya koma Ingila, sarki ya nada Wycliffe shugaban Lutterworth. Wannan ya tabbatar da cewa sarki bai sami damuwa da maganarsa, kai a waye ba. Tasirin Wycliffe ya shafi ayukan fada, ya kuma taimaka wajen tsara imanin al’ummar. BJ 84.2
Ba da jimawa ba paparuma ya fara jefa masa barazana, aka aika da dokokin har Ingila - zuwa jami’a, zuwa wurin sarki, zuwa wurin shugabannin ekklesiya kuma, duka ana umurtarsu su dauki matakan kawar da wannan mai-koyar da riddan maza maza. Kafin zuwan umurnin kuwa, bishop bishop din, cikin gaggawarsu, sun rigaya suka kira Wycliffe zuwa wurinsu don shar’anta shi. Amma biyu daga manyan yarimai mafi-iko a kasar suka bi shi zuwa wurin shari’ar; mutane kuma da suka kewaye wurin, suka kutsa ciki, wanda ya tsorata masu shari’ar har ya sa aka dakatar da shari’ar, aka bar shi ya tafi abinsa cikin salama. Jima kadan, Edward III, wanda cikin tsufarsa shugabannin ekklesiyar suka yi kokori su sa shi ya sami sabani da dan canjin, ya mutu, sai kuma wanda da yake kare Wycliffe ya zama mukaddashin sarkin kasar. BJ 84.3
Amma isowar wasikun dokokin nan na papruma ya aza ma dukan Ingila umurni na dole cewa a kama a kuma jefa mai riddan nan cikin kurkuku. Ya bayana a fili cewa tilas Wycliffe zai shiga hannun Rum, ba da jimawa ba. Amma Shi wanda Ya ce ma wani a zamanin da, “kada kaji tsoro…. Ni ne garkuwarka” (Farawa 15:1), ya sake mika hannunsa ya tsari bawansa. Mutuwa ta zo, ba kan mai-canjin ba, amma ga paparuma da ya umurta cewa a kashe shi. Gregory XI ya mutu, masu shari’an da suka taru don yi ma Wycliffe shari’a kuwa suka waste. BJ 85.1
Ikon Allah ya sake ba da dama domin ci gaban canjin. Bayan mutuwar Gregory aka zabi paparuma guda biyu masu hamayya juna, kowane dayansu yana cewa ba ya kuskure, yanzu kuma suna cewa a yi masu biyaya. Kowane daya ya bukaci masu-bi su taimake shi yaki da dayan, yana bin bayan kiran nasa da la’ana mai-muni ga magabtansa, da kuma alkawuran ladar sama ga masu binsa. Wannan al’amari ya rage ikon mulkin paparuma sosai. Bangarorin biyu suna da dukan bukata don kai ma juna hari, Wycliffe kuma ya sami hutu na wani lokoci. La’ana da zagi sun rika firiya daga paparuma zuwa paparuma, aka kuwa zubar da jini sosai don kare ikirarinsu, masu sabani da juna. Laifuka da ababan ban kunya suka cika ekklesiya. Lokacin kuwa dan canjin nan, a parish nasa a Lutterworth, ya rika aiki cikin natsuwa don mai da hankulan mutane daga paparuman nan biyu zuwa wurin Yesu, Sarkin Salama. BJ 85.2
Rabuwar, tare da rikici da lalacewan da ta jawo, sun shirya hanya domin canjin ta wurin nuna ma mutane har suka ga ainihin yadda mulkin paparuma yake. A wata majaila da Wycliffe ya buga mai-suna “On the Schism of Popes,” ya bukaci mutane su lura, su ga ko ba gaskiya ne priestocin nan biyu ke fadi game da juna, kowane dayansu yana ce da dayan dan hallaka ba? “Allah,” inji shi, “ba zai ci gaba barin magabcin ya ci gaba mulki cikin priest daya kadai a cikin su ba,…. Amma ya kawo rabuwa tsakanin su biyu din, domin mutane, a cikin sunan Kristi, su iya yin nasara bisa su biyu din cikin sauki.” BJ 85.3
Wycliffe, kamar Mai-gidansa, ya yi shelar bishara ga matalauta. Dashike bai gamsu da yada hasken a kananan gidajensu a Lutterworth ba, ya shirya cewa za a kai bisharar ko ina a Ingila. Don cimma manufan nan, ya kafa kungiyar masu wa’azi, mutane masu-saukin kai, masu kwazo da suke kaunar gaskiya, kuma ba abin da suke so kamar watsa shi. Mutanen nan suka je ko ina, suna koyarwa a kasuwanni, a titunan manyan birane, da kuma cikin kauyuka. Suka nemi tsofofi, da marasa lafiya, da matalauta, suka kuma bude masu labari mai ba da murna, labarin alherin Allah. BJ 86.1
A matsayinsa na shehun mallamin ilimin tauhidin Littafi a jami’ar Oxford, Wycliffe ya rika wa’azin maganar Allah a Jami’ar. Ya yi aminci wajen bayana gaskiyar ga dalibansa yadda har suka ba shi lakabin “likitan bishara”. Amma aikinsa mafi-muhimmanci shi ne juya Litaffi zuwa Turanci da ya yi. Cikin Littafinsa mai-suna “On the Truth and Meaning of Scripture,” ya nuna niyyar juya Littafi domin kowane mutum a Ingila ya karanta ayukan al’ajibin Allah cikin harshen da aka haife shi. BJ 86.2
Amma kuma faraf daya, aikinsa ya tsaya. Ko dashike bai rigaya ya kai shekara sittin da haihuwa ba, yawan aiki, da karatu, da fitinar magabtansa, sun shafi karfinsa har suka sa shi ya tsufa. Sai wani mumunan ciwo ya kama shi. Labarin ya faranta zuciyar ‘yan zuhudu. Sun dauka cewa yanzu zai tuba sabo da muguntar da ya yi ma ekklesiya, suka je kusa da dakinsa domin su ji tubarsa. Wakilan kungiyoyi hudu na addadin, tare da jami’ar kasa su hudu, suka kewaye mutumin da suka zata zai mutu. Suku ce “kana da mutuwa a lebenka, bari kurakuranka su taba ka, ka janye a idonmu, dukan ababan da ka fada na batanci game da mu.” Dan Canji ya saurare su shuru; ya ce ma mai lura da shi ya daga shi a kan gadonsa, sa’annan ya kalle su yayin da suke jiran janyewar maganganunsa, da babban murya kuma ya ce, “Ba zan mutu ba, zan rayu, in kuma sake bayana miyagun ayukan ‘yan zuhudun.” Cikin mamaki da kunya, suka tafi a gurguje. BJ 86.3
Maganar Wycliffe ta cika. Ya rayu domin shi ba ‘yan kasarsa makami mafi-karfi kan Rum, watau Littafin, abinda Allah Ya bayar don ‘yantarwa da wayewar mutane da kuma yi masu wa’azi. Aikin nan ya fuskanci manyan matsaloli da yawa. Wycliffe ya kamu da rashin lafya; ya san cewa shekarun aiki da sun rage masa ba yawa; ya ga hamayyan da zai fuskanta dole; amma bisa ga alkawuran maganar Allah, ya ci gaba ban da shakka. Da dukan karfin iliminsa, da kwarewarsa, Allah Ya rigaya Ya shirya shi don aikin nan mafi-girma. Yayin da addinin Kirista ke fama da rikici, Wycliffe a wurin aikinsa a Lutterworth, ya sa kai sosai cikin aikin nan da ya zaba, bai ko kula hayanniyan da ake yi ba. BJ 87.1
A karshe an gama aikin — juyin Littafi zuwa Turanci, na farko da aka taba yi. Aka bude ma Ingila maganar Allah. Yanzu Mai-Canjin ba ya tsoron kurkuku, ko mutuwa. Ya rigaya ya ba mutanen Ingila hasken da ba za a taba kashewa ba. Ta wurin ba mutanen kasarsa Littafin, ya yi abin da zai fi tsinke sarkokin jahilci da mugunta, ya kuma yantar da kasarsa, fiye da kowace nasara da aka taba yi a filin yaki. BJ 87.2
Da shike ba a rigaya an fara buga Littattafai na kusa ba, a hankali ne Littattafai suka yawaita. Marmarin samun Littafin ya yi yawa har mutane da yawa suka shiga yin kofen sa, amma da kyar suka iya gamsar da masu bukata. Wadansu mawadata suka so Littafin dungum. Wadansu suka sayi sashi sashi ne kadai. Wadansu lokuta iyalai da yawa ne sukan hada kurdi su sayi Littafi daya. Ta haka Littafin Wycliffe ya shiga gidajen mutane. BJ 87.3
Motsawar tunaninsu da Littafi ya yi, ya falkar da su daga yarda kuma da koyaswoyin paparuma. Yanzu kuma Wycliffe ya koyar da kaidodin rabuwa da ekklkesiya cikin Kristi, da kuma rashin kuskuren Litaffin. Masu wa’azin da ya aika suka rika sayar da Littafi tare da rubuce rubucen Wycliffe, har kusan rabin mutanen Ingila suka karbi sabuwar ibadar. BJ 88.1
Bayanuwar Littafin ya bata ma mahukuntan ekklesiya rai. Yanzu dole su sadu da abinda yafi Wycliffe karfi. Abin da makaman su ba za su iya yi masa kome ba. A wannan lokacin ba doka a Ingila da ta hana Littafin, domin ba a taba wallafa shi a harshen mutanen ba. Daga baya aka yi wadannan dokokin, aka kuma aiwatar da su sosai. Kafin nan, duk da kokarin priestocin, an sami zarafin baza maganar Allah, na wani lokaci. BJ 88.2
Kuma, shugabanin mulkin paparuma suka shirya rufe muryar Wycliffe. Aka gurbanar da shi a gaban hukumomi uku, daya bayan daya, duk a banza. Da farko wata majalisar bishops ta sanar da cewa rubuce rubucensa ridda ne, kuma da suka jawo matashin sarki Richard gefensu, suka sami dokar sarki da ta umurta jefa duk wanda aka samu da koyaswoyin nan cikin kurkuku. BJ 88.3
Wycliffe ya daukaka kara daga Synod zuwa Majalisar kasa; gurbanar da shugabannin gaban Majalisar kasa, ya bukaci a canza munanan cin mutunchi da ekklesiya ta ba da izinin yi. Da karfi sosai ya bayana kwace da muguntar ikon paparuma. Magabtansa suka rikice. An rigaya an tilasta abokan Wycliffe da magoya bayansa suka ja da baya. Kuma aka zata cewa shi kansa, mai-canjin sabo da tsufa da kadaici da rashin abokai, zai amince da hadadden ikon ekklesiya da na shugabaninta. Amma maimakon haka, suka ga an ka da su. Majalisa da jawabin Wycliffe ya ja hankalinta, sai ta sake dokan nan na zalunci, Wycliffe ya sake samun yanchi kuma. BJ 88.4
Sau na uku, aka kai shi gaban sharia, gaban hukuma mafi girma ta ekklesiya a kasar. Ba a tausaya ma ridda a nan. Nan aka zata Rum za ta yi nasara a kuma tsayar da aikin canji idan suka yi nasara , za a tilasta Wycliffe ya janye koyaswoyinsa, ko kuma daga kotun a kai shi inda za a kone shi kawai. BJ 89.1
Amma Wycliffe bai janye ba; ba tsoro ya manne ma koyaswoyinsa, ya kuma rushe zarge-zargen masu cin zalin sa. Sa’anda ya manta kansa, da matsayinsa, da inda yake, sai ya kai karar masu sauraronsa gaban hukumar sama, ya kuma auna rudunsu a ma’aunin gaskiya ta har abada. Aka ji ikon Ruhu Mai tsarki a cikin dakin majalisar. Masu ji suka harbu da jifa daga wurin Allah. Suka ji kamar ba su da ikon barin wurin. Kamar kibawu daga kwarin Ubangiji, kalmomin dan canjin nan suka rika sakar zukatansu. Ya juya zargin ridda da suka yi masa a kansu. Ye ce, don me suka baza kurakuransu? Sabo da neman riba sai a yi kasuwanci da alherin Allah? BJ 89.2
Daga baya ya ce, “Da wa, a ganinku, kuke jayayya? Da tsoho da ke bakin kabari? Babu! da gaskiya — Gaskiyar da ta fi karfinku, za ta ku ma yi nasara bisanku. Da ya fadi wannan, sai ya fita daga majalisar, ba wanda kuma ya gwada hana shi fita. BJ 89.3
Aikin Wycliffe ya kusa cika, tutar gaskiya da ya dade yana rikewa tana gaf da faduwa daga hannunsa; amma kuma zai dai sake ba da shaida ga bishara. Za a yi shelar gaskiya daga madogarar mulkin kure. Aka yi sammacin Wycliffe gaban kotun paparuma a Rum, wadda sau da yawa ta rika zub da jinin tsarkaka. Bai kasa ganin hasarin da yake fuskanta ba, duk da haka, ba don ciwon inna ya hana shi zuwa ba, da ya je wurin tuhumar. Amma ko da shike ba a ji muryarsa a Rum ba , zai iya magana tawurin wasika, ya kuma shirya yin hakan. Daga wurin aikinsa, Wycliffe ya rubuta ma paparuma wasika wadda tsautawa ce ga shagali da girma rai na mulkin paparuma. BJ 89.4
Ya ce, “hakika ina murna in bude in kuma shaida ma kowane mutum imanin da ni ke rike, musamman ma ga bishop na Rum: wanda, da shike na san na kwarai ne kuma ga gaskiya ce, za ya hakikance imanin nawa, idan kuma akwai kuskure, ya gyara mani shi” BJ 90.1
“Da farko, ina gani kamar bisharar Kristi dukan dokar Allah ne dungum…. A gani na bishop na Rum, da shike shi ne wakilin Kristi a nan duniya, shi ne dokar bisharar ta zama wajibi gare shi, fiye da dukan sauran mutane. Gama girma tsakanin almajiran Kristi, bai kunshi martaba ko daraja irin na duniya ba, amma ya kunshi bin Kristi kusa kusa daidai kuma da rayuwarsa da halayyansa ……. Kristi, a lokacin rayuwarsa a nan matalauci ne sosai, wanda yaki ya kuma yi watsi da dukan shugabanai da daraja na duniya….. BJ 90.2
“Ba amintace da ya kamata ya bi paparuma kansa, ko kuma wani daga cikin mutane masu-tsarki, sai dai idan shi ma ya bi Ubangiji Yesu Kristi; gama Bitrus da yaran Zabadi, ta wurin bidar daraja ta duniya, sabanin bin matakai na Kristi sun yi laifi, sabo da haka kuwa bai kamata a bi su cikin kura kuran nan ba….. BJ 90.3
“Ya kamata paparuma ya bar ma masu ikon duniya dukan mulki na duniya, ya kuma gargadi dukan ma’aikatan ekklesiyarsa su yi hakanan, gama haka ne Kristi ya yi, masamman ma manzaninsa. Sabo da haka, idan na yi kuskure game da wani abu cikin wadannan ababan, da tawali’u matuka zan mika kai na a yi mani gyara, har tawurin mutuwa ma, idan ta kama; idan kuma zan iya fama bisa ga nufin kai na dakai na, hakika zan gabatar da kai na wurin bishop na Rum; amma Ubangiji Ya ziyarce ni akasin hakan, Ya koya mani in yi biyayya ga Allah maimakon mutane.” BJ 90.4
A karshe, ya ce: “Bari mu yi addu’a ga Allahnmu, domin Ya motsa paparumanmu Urban VI, yadda ya fara, domin shi da ma’aikatansa na bishara su bi Ubangiji Yesu Kristi cikin rayuwa da halayya; kuma su koya ma mutane da kyau, su kuma hakanan su bi su cikin sa.” BJ 91.1
Ta haka Wycliffe ya nuna ma paparuma da manyan ma’aikatan ekklesiyarsa tawali’u da saukin kan Kristi, ya kuma nuna masu da dukan Kirista bambanci tsakanin su da Mai-gidan, wanda suka ce suna wakiltansa. BJ 91.2
Wycliffe ya sa rai lallai ransa zai zama farashin amincinsa. Sarkin, paparuman, da bishops din, sun hada kai don tabbatar da tatikewarsa, ya kuma ga kamar cikin watanni kalilan za a kashe shi. Amma karfin halinsa bai raunana ba. Yace: “Don me kake neman rawanin mutuwa sabo da addininka da nisa? Yi shelar bisharar Kristi ga priestoci masu alfarma, mututwa don addini kuwa ba za ta wuce ka ba. Mene! Ni in rayu sa’anan in yi shuru?.... ko kadan! Bari bugun ya fada, ina jiran zuwan sa.” BJ 91.3
Amma alherin Allah ya kuma tsare bawansa. Mutumin da duk rayuwarsa ya tsaya da gaske yana kare gaskiya, kullum cikin hadari ga ransa, ba zai fadi a hannun makiyansa ba. Wycliffe bai taba neman kare kansa ba, amma Ubangiji ne ya kasance mai-tsaron sa. Yanzu kuma da magabtansa suka ji kamar ya shiga hannunsu, hannun Allah ya cire shi daga gare su. Cikin ekklesiyarsa a Lutterworth, yayin da yana gaf da ba da jibin Ubangiji, ya fadi, gama ya harbu da ciwon shan inna, jima kadan kuma ya rasu. BJ 91.4
Allah ya shirya ma Wycliffe aikinsa. Ya sa maganar gaskiya a bakinsa, ya kuma tsare shi domin maganan nan ya kai wurin mutane. An tsare ransa, aka kuma tsawaita aikinsa, har sai da aka kafa harsashen babban aikin nan na canji. BJ 91.5
Wycliffe ya zo daga duhun Zamanin Duhun nan ne. ba shi da wadansu magabata da zai yi anfani da aikinsu don sifanta nashi aikin canjin. An tayar da shi kamar Yohanna mai-baptisma ne, domin shi cim ma wata manufa ta musamman, ya zama mai-gabatarwan sabon zamani. Duk da haka, cikin irin gaskiyan da ya bayana akwai daidaituwa da ‘yan canjin da suka bi bayansa basu wuce ba, wanda wadansu kuma basu kai ba, har bayan shekaru dari ma. Tushen ya yi fadi da zurfi, tsarin kuma mai-karfi ne da gaskiya kuma, ta yadda bai kamata na bayansa su sake shi ba. BJ 92.1
Babban aikin da Wycliffe ya fara, wato yantarwar lamiri da tunani, ya kuma kubutar da al’ummai da suka dade a daure a jikin mulkin Rum, ya taso daga Littafi ne. Wannan ne mabulbulan albarkan nan, wanda kamar ruwan rai, yana gudu cikin sararaki tun karni na goma sha hudu. Wycliffe ya karbi Littafi da cikakken bangaskiya, cewa hurarren bayanin nufin Allah ne, isasshiyar kaidar bangaskiya da aikatawa. An koya mashi ya ga ekklesiyar Rum kamar iko daga Allah wanda ba ta kuskure, shi kuma yarda, ban da tambaya, da koyaswoyi da al’adun da aka kafa fiye da shekara dubu; amma ya juya daga dukan wadannan, ya saurari magana mai-tsarki na Allah. Wannan ne ikon da ya roki mutane su yarda da shi. Maimakon ekklesiya da ke magana ta wurin paparuma, ya bayana cewa muryar Allah da yake magana ta wurin maganarsa ne ke da iko. Ya kuma koyar da cewa ba wai Littafi cikakken bayanin nufin Allah ba ne kawai, amma cewa Ruhu Mai-Tsarki ne kadai mai fasarta shi, kuma ta wurin nazarin koyaswoyinsa, ya kamata kowane mutum ya koya ma kansa abin da ya kamata ya yi. Ta haka ya juya tunanin mutane daga paparuma da ekklesiyar Rum zuwa maganar Allah. BJ 92.2
Wycliffe yana daga cikin fitattun yan Canjin. Game da yawan hikima, da kyakyawar tunani, da naciyar rikon gaskiya, da kuma karfin zuciya wajen kare ta, kadan ne daga cikin na bayansa sun kai shi. Tsabtar rai, naciyar himma wajen nazari da aiki, aminci, da kauna irin ta Kristi, da aminci cikin aikinsu, su ne halayyan yan canji na farko. Kuma duk da duhun tunani da rashin adalcin da suka mamaye zamanin nasu kenan fa. BJ 93.1
Halin Wycliffe shaida ce ta ikon ilimantarwa da sakewa na Littafin. Littafin ne ya sa shi ya zama yadda ya zama. Kokarin gane muhimman gaskiya da aka bayana yakan ba da sabuntawa da kuma kwazo ga kowane fannin jikin mutum. Yakan fadada tunani, ya inganta fahimi, ya kuma nunar da basira. Nazarin Littafin zai inganta kowane tunani, da buri fiye da kowane irin ilimi. Yana ba da karkon manufa, hakuri, karfin zuciya da dauriya; yana inganta hali, ya tsarkake mutum. Nazarin Littafi cikin kwazo da saduda, wanda ke sada tunanin dalibin da na Allah, zai ba duniya mutane masu tunani mai karfi da kuzari kuma, da kuma kaida mafi-kirki, fiye da wanda ya taba samuwa daga koyaswa mafi-inganci na mutane. In ji mai-zabura: “Buden zantattukanka yana ba da haske; yana ba da fahimi ga sahihai.” Zabura 119:130. BJ 93.2
Koyaswoyin Wycliffe sun ci gaba da yaduwa na wani lokaci; mabiyansa, da ake kira Wycliffawa da Lollards, ba wai sun shiga dukan Ingila ba ne kadai, amma suka bazu zuwa wadansu kasashe, suna kai sanin bishara. Yanzu da an cire shugabansu, masu wa’azin sun yi aiki da kwazo fiye da da ma, jama’a kuma suka rika taruwa domin jin koyaswoyinsu. Wadansu fadawa, har da matar sarkin ma, suna cikin tubabbun. A wurare da yawa aka sami kyakyawan canjin halayyan mutanen, aka kuma cire alamun gumakan ekklesiyar Rum daga majami’un. Amma nan da nan guguwar zalunci ba tausayi ta abko ma wadanda suka karbi Littafin a matsayin mai-bishewarsu. Sarakunan Ingila, don neman karfafa ikon su tawurin samun goyon bayan Rum, basu yi jinkirin sadakar da ‘yan canjin ba. Lokacin ne na farko a tarihin Ingila da aka taba umurtawa a kashe almajiran bishara. Kisa ta bi bayan kisa. Masu shelar gaskiya, da aka wulakanta, sun iya kai kukansu ga Ubangijin Assabbat ne kadai. Da aka yi farantarsu a matsayin magabtan ekklesiya da masu cin amanar kasa, suka ci gaba da wa’azi a wurare na boye, suna samun mafaka a gidajen matalauta, sau dayawa ma sukan buya a koguna ko ramuka. BJ 93.3
Duk da zafin zalunci, an ci gaba da nuna kin yarda da lalcewar imani cikin natsuwa da hakuri da naciya har tsawon daruruwan shekaru. Kiristan wancan zamanin sun mallaki karamin sanin gaskiya ne kawai; amma suka koyi yin kaunar maganar Allah da biyayya gare ta kuma, suka kuma jimre shan wahala domin ta. Kamar almajiran a zamanin manzanin, da yawa suka sadakar da mallakarsu ta duniya sabo da aikin Kristi wadanda aka yarda masu su kasance a gidajensu suka ba abokan famansu matsuguni, kuma sa’anda aka kore su su ma, sai su ma suka karbi yanayin korarrun. Dubbai kam, don tsaron fushin azalumansu, suka sayi yancinsu tawurin sadakar da imaninsu, suka fita daga kurkuku yafe da tufafin masu-tuba, don bayana janyewarsu daga imaninsu. Suna da yawa, kuma cikinsu akwai ‘yan gidajen sarauta da matalauta da suka yi ta shaida gaskiyar a cikin kurkuku, cikin azaba da wuta, ba tsoro, suna murna cewa su ma sun isa su san zumuntar wahalolinsa. BJ 94.1
Mutanen paparuma su kasa cim ma manufarsu game da Wycliffe lokacin rayuwarsa, kuma kiyayarsu ba ta kare ba yayin da gawarsa ke kwance shuru cikin kabari. Ta wurin dokar Majalisar Constance, sama da shekara arba’in bayan mutuwarsa, aka fito da kasusuwansa, aka kone su a gaban jama’a, aka kuma zubar da tokar cikin wani rafi da ke kusa. Wani tsohon mawallafi ya ce: “Wannan rafin ya kai tokansa Avon, daga Avon zuwa cikin Severn, daga Severn zuwa cikin kananan tekuna, daga nan kuma babban teku. Ta haka, tokan Wycliffe alama ce ta koyasuwarsa, wadda yanzu ake bazawa ko ina a duniya.” Ko kadan magabtansa basu gane ma’anar aikin muguntan nan nasu ba. BJ 94.2
Ta wurin rubuce rubucen Wycliffe ne John Huss na Bohemia ya kai ga watsar da kurakurai da yawa na ekklesiyar Rum, ya kuma shiga aikin canji. Ta haka, cikin wadannan karni biyu masu-nisa da juna, aka shuka irin gaskiya. Daga Bohemia aikin ya ci gaba zuwa wadansu kasashe. Aka jawo zukatan mutane zuwa ga maganar Allah da aka manta da ita da dadewa. Hannun Allah yana shirya hanya domin Babban Canji BJ 95.1