Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 18—Dan Canji America

    Wani amintacen manomi da aka sa shi yayi shakkar cewa Littafin maganar Allah ne, amma kuma ya kasance da burin sanin ainihin gaskiyar, shi ne mutumin da Allah ya zaba ya zama shugaba wajen shelar zuwan Kristi ba Biyu. Kamar sauran ‘ya Canjin, William Miller a farko rayuwansa ya fama da talauchi, ta haka kuma ya koyi darussan kwazo da musun kai. ‘Yan iyalin da ya fito sun saba da dogaro da kai da son ‘yanci, da dauriya da kishin kasa, hallayan nan kuwa sun nuna a halinsa. Baban shi kaftin ne na mayakan Juyin Danwaken, kuma sadakarwan da ya yi cikin gwagwarmaya da wahalolin mawuyacin zamanin can ne suka haifar da irin yanayin rayuwar Miller a kurichiyarsa. BJ 315.1

    Lafiyayye ne shi, kuma ko a kuruciya ya ba da alamar bisira ta musamman. Yayin da yake girma, wannan ya kara bayanuwa. Yana da zurfin tunani kwarai, da marmarin samun sani. Ko da shike bai sami gatan zuwa jami’a ba, son nazari da zurfin tunani da halin sakewansa sun sa ya zama mutum mai-basira da ra’ayoyi masu tarin anfani. Ya kasance mai halin kirki mara abin raini, da suna mai ban sha’awa sabo da halin sa na aminci da tsimi da son mutane. Sabo da kwazo da hikimarsa, tun a kurchiya ya sami kwarewa, amma bai rabu da halin sa na son nazari ba. Ya rike matsayi dabam dabam na gwamnati da na soja da kyau, kuma kofofin samun wadata da suna sun bude masa sosai.BJ 315.2

    Uwarsa mace ce mai ibada kwarai, kuma a kurchiyarsa an koya masa addini sosai. Amma a samartakarsa ya kasance cikin jama’a da suka ba da gaskiya wai Allah bai damu da abinda ke faruwa da yan Adam ba, abin da ya burge su kadai shi ne cewa su masu halin kirki ne, da halayya masu-ban mamaki. Da shike suna tare da cibiyoyin Kirista, Kiristancin ne ya sifanta halayensu. Littafin ne ya sa suka mallaki halayyan da suka ba su martaba, amma aka lalata kyawawan baye bayen nan ta yadda suka saba ma maganar Allah kuma. Ta wurin chudanya da mutanen nan, Luther ya yarda da ra’ayoyinsu. Irin fasaran da aka rika yi ma Littafin a lokacin ya jawo matsalolin da kusan ba a iya magancewa ba; duk da haka, yayin da sabuwar bangaskiyarsa ta yi watsi da Liffafin, ba ta ba da wani abu a madadinsa ba, bai kuma sami gamsuwa ba. Amma ya ci gaba da ra’ayoyin nan har wajen shekara goma sha biyu. Amma da ya kai shekara talatin da hudu, Ruhu Mai-tsarki ya cika zuciyarsa da ganewar cewa shi mai zunubi ne. Bai sami tabbacin farin ciki bayan mutuwa ba daga bangaskiyarsa ta da. Gaba sai bakin ciki da duhu kadai. Game da yadda yaji a lokacin, daga baya ya ce:BJ 316.1

    “Hallaka ta zama abin tsoro, zancen ba da lissafi kuma ya nuna kowa zai hallaka kenan. Sammai suka kasance mini kamar inda ba shiga, duniya kuma kamar karfe ne ga sawaye na. Mene ne har abada? Mene ne dalilin mutuwa? Duk tunanin na ya kara nisantar da ni daga samun ganewa. Ina kara tunani, ina kara rudewa. Na yi kokarin dena tunani amma tunanin ya ki bari na. Na zama abin tausayi kwarai, amma ban san dalilin ba. Na yi ta gunaguni amma ban san ko da wa nike ba. Na san akwai kuskure da aka yi, amma ban san yadda, ko kuma inda zan sami na daidai din ba. Na yi bakin ciki amma ba bege.” BJ 316.2

    Ya kasance cikin wannan yanayi har sawon watanni, ya ce, “Nan da nan aka bayana mini halin Mai-ceto a sarari ga zuchiyata. Naga kamar akwai wani nagari mai-tausayi da har ya yi kafara da kansa, domin laifofinmu, ta haka kuma ya cece mu daga horo ta zunubi. Na ji kawai mutumin nan abin kauna ne matuka, na ji kawai da ma a ce na ga kaina a hannayensa, in dogara ga alherinsa. Amma tambaya ta taso, Ta yaya za a tabbatar cewa akwai wani haka? Ban da Littafin, na gane cewa ba inda zan sami shaidar cewa akwai wani Mai-ceto hakanan, ko ma wata kasancewa nan gaba….BJ 317.1

    “Na gane Littafin ya bayana daidai irin Mai-ceton da nike bukata. Na kuma kasa gane yadda za a ce Littafin da ba horarre ba ne zai haifar da kaidodi da suka dache daidai da bukatun duniya ta zunubi hakanan. Dole na yarda cewa Littafin ruya ce daga Allah. Nassosin suka zama abin marmari na. Yesu kuma ya zama mani aboki. Mai-ceto ya zama gareni mafi-girma duka; Nassosin da a baya suka kasance duhu-duhu yanzu suka zama fitilla ga sawayena, haske kuma ga tafarkina, zuchiyata ta kwanta ta kuma gamsu. Na iske cewa Ubangiji Allah dutse ne cikin tekun rayuwa. Yanzu kuma Littafin ya zama babban abin nazari na, kuma zan iya fadi da gaske cewa na bincika shi da marmari sosai. Na tarar cewa ko rabi ma ba a fada mini ba. Na yi mamakin yadda kafin nan ban ga kyaunsa da darajarsa ba. Na yi mamaki cewa har ma na taba kinsa. Na sami bayanin duk wani abin da zuchiyata ta taba bukata, da maganin kowane ciwo na rayuwa. Ban sake marmarin karanta wani abu dabam kuma ba, na kallafa zuciyata ga neman hikika daga Allah”BJ 317.2

    A gaban jama’a Miller ya bayana bangaskiyarsa ga addinin da ya rena a da. Amma kafin nan abokansa suka kawo masa dukan dalilan da shi kansa ya dinga bayarwa don nuna cewa Littafin ba daga Allah ba ne. Alokachin bai shirya amsa masu ba; amma ya yi tunani cewa idan Littafin daga Allah ne lallai ba za ya yi sabani da kansa ba; kuma cewa dashike an ba da shi don koya ma mutane ne, dole zai kasance abin da mutum zai iya ganewa, ya kudurta yin nazarin Littafin don kansa, domin shi kuma gane ko za’a iya daidaita kowane kamanin sabani.BJ 317.3

    Da kokarin rabuwa da dukan ra’ayoyin sa na da, da kuma kyale kowane sharhi, ya dinga gwada nassi da nassi, ya yi nazarin sa da fasali; tun daga Farawa, yana karanta aya bayan aya, bai wuce nassi ba har sai ya gane ma’anarsa sarai, sarai. Idan wani abu ya shiga masa duhu yakan gwada shi da kowane nassin da ya shafi abin da ake magana akai a wannan nassin. Yakan bar kowace kalma ta nuna anfaninta ga batun da ake yi a nassin, kuma idan tunaninsa game da shi ya daidaita da kowace nassi, matsalar takan warware. Ta haka duk sa’anda ya ga wata Magana mai wuyan ganewa, yakan sami fasara a wani fanni na Littafin. Yayin da ya rika nazari yana addu’a don samun haske daga Allah, abin da bai gane ba yakan zama a bayane. Ya dandana gaskiyar maganar mai-zabura cewa, “Bude zanttatukan ka yana ba da haske; yana ba da fahimi ga sahihai” Zabura 199:130.BJ 318.1

    Da marmari mai-yawa ya yi nazarin littafin Daniel da Ruya, yana anfani da ka’idodin fassara da ya yi anfani da su game da sauran nassosi, ya kuma yi murna sosai ganin cewa ana iya gane alamun annabce annabcen. Ya ga cewa annabce annabcen da aka cika zahiri ne, cewa an fassara dukan siffofin da kamancewa da misalai, da dai sauran su, daidai inda aka ambace su ne, ko kuma an bayana ma’amarsu a wani nassi dabam, kuma akan gane su a zahiri ne, wani lokaci ya ce, “Ta hakanan na gamsu cewa Littafin tsari ne na gaskiya da aka bayana su, aka ba da su a sarari kuma a saukake, ta yadda kowane mutum, ko wawa ne ma, ba zai yi kuskure ba.” Ya rika gano jerin gaskiya nan da can, yayin da ya rika bin muhimman matakan annabci daki-daki.. Malaikun sama sun rika bi da tunaninsa, suna bude nassosi ga ganewarsa.BJ 318.2

    Da shike ya dauka cewa yadda aka cika annabce annabcen a baya mizani ne na auna cikawar annabce annabce na nan gaba, sai ya gane cewa ra’ayin nan da ya cika wurin, cewa Kristi zai yi mulki cikin Ruhu a wannan duniya har Shekara Dubu kafin karshen duniya, ba shi da tushe daga maganar Allah. Wannan Koyaswa game da wadansu shekaru dubu na adalci da salama kafin zuwan Yesu kansa, ta jinkirta ababan ban razana na rana ta Ubangiji. Amma komi dadin koyaswar, ta yi sabani da koyaswoyin Kirsti da manzaninsa, wadanda suka ce dole a bar alkama da zawan su girma tare har sai lokacin girbi, watau karshen duniya; cewa “ miyagun mutane da masu-hila zasu dada mugunta gaba gaba” cewa “chikin kwanaki na karshe miyagun zamanu zasu zo;” kuma cewa mulkin duhu zai ci gaba har zuwan Ubangiji, kuma ruhun bakinsa zaya cinye mulkin duhu ya hallaka shi da walkiyar zuwansa. Matta 13:30, 38-41, Timothawus II, 3:13; Tassalanikawa II, 2:8.BJ 319.1

    Ekkelisiyar Manzanin ba ta koyar da cewa duniya zata tuba, Yesu kuma zai yi mulki cikin ruhu ba, Kirista basu yarda da wannan ba har sai kusan farkon karni na sha takwas, kamar kowane kuskure, sakamakon koyaswar sun yi muni. Ta koya ma mutane suka dauka cewa zuwan Ubangiji yana da nisa sosai, ta kuma hana su kulawa da alamun zuwanasa. Ta jawo gamsuwa mara tushe, ta kuma sa mutane da yawa suka dena shiri don saduwa da Ubangijinsu.BJ 319.2

    Miller ya ga cewa Littafin yana koyar da cewa Kristi zai zo zahiri ne da kansa. Bulus ya ce; “Gama Ubangiji da kansa zaya sabko daga sama, da kira mai-karfi, da muryar sarkin malaiku, da kafon Allah kuma” Tassalunikawa I, 4:14. Mai-ceton kuma ya ce “za su kwa ga Dan mutum yana zuwa a bisa gizagizai na sama tare da iko da daukaka mai-girma.” Gama kamar yadda walkiya takan fito daga gabas, ana kwa ganinta har yamma; hakanan bayanuwar Dan Mutum za ta zama” Matta 24:30,27. Dukan rundunan sama za su zo tare da shi, “Dan mutum zai zo chikin darajassa, da dukan malaiku tare da shi” Matta25:31. Kuma za ya aike malaikunsa da babbar karar to kafo, su kuma zasu tattara zabbaunsa” Matta 24:31.BJ 319.3

    Sa’anda ya zo za a tada mattatu masu adalci, a kuma wanzar da masu adalci da ke raye. Bulus ya ce “Ba dukanmu za mu yi barci ba, amma za a sake mu duka farap daya, da kyaptar ido, da karar kafo na karshe; gama kafo za shi yi kara, mattatu kuma za su tashi marasa rubuwa, mu kuma za mu sake. Gama dole mai wannan mai-rubuwa za shi yafa rashin ruba wannan mai-mutuwa kwa shi yafa rashin mutuwa.” Korantiyawa I, 15:51-53. Kuma cikin wasikar sa ga Tassalunikawa, bayan ya bayana zuwan Ubangiji ya ce, Mattatun da ke cikin Kristi za su fara tashi: sa’an nan mu da ke da rai, mun wanzu, tare da su, za a fyauce mu zuwa chikin gizagizai, mu tarbi Ubangiji a sararin sama; hakanan za mu zauna har abada tare da Ubangiji.” Tassalunikawa I, 4:16,17.BJ 320.1

    Sai Kristi da kansa ya zo kafin mutanensa su karbi mulkin. Mai-ceto ya ce “Amma sa’anda dan mutum za ya zo chikin darajassa, da dukan malai ku tare da shi, sa’an nan zaya zauna bisa kursiyin darajassa. A gabansa kuma za a tattara dukan alumai; shi kwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi yakan rarraba tumaki da awakai; kuma za ya sanya tumaki ga hanuin daman sa, amma awakai ga hagu sa’an nan shi sarkin za y ache ma wadanda ke hanun damansa, ku zo ku masu albarka na Ubana, ku gaji mulki da na shirya domin ku tun kafuwar duniya” Matta25:31-34. Daga nasosin nan mun ga cewa sa’anda Dan mutum ya zo za a tada mattatu ban da ruba a kuma wanzar da wadan da ke raye. Tawurin wan nan wanzuwar za a shirya su domin karban mulkin, domin Bulus ya ce: ” Nama da jini ba su da iko su gaji mulkin Allah ba; mai-rubewa kuma ba shi da gadon rashin ruba” 1Korantiyawa 15:50. Yanayin mutun yanzu mai-mutuwa ne, mai-ruba; amma mulkin Allah ba ruba, kuma na har abada ne. Sabo da haka a wannan yanayi na mutum ba zai iya shiga mulkin Allah ba. Amma sa’anda Yesu zai ba mutanensa rashin mutuwa, sa’annan zai kira su, su gaji mulkin nan da tun da ma abin gadon su ne.BJ 320.2

    Wadannan da wadansu nassosin kuma sun tabbatar ma Miller cewa al’amuran da ake ta cewa wai zasu faru kafin zuwan Kristi, kamar mulkin salama ga dukan duniya, da kafawar mulkin Allah a duniya, ashe bayan zuwan Kristi din ne kuma, dukan alamun zamanun da yanayin duniyan sun je dai dai da yadda anabci ya bayana kwanakin karshe. Dole ya gane daga binciken Littafin kawai cewa kwanakin duniyan nan a yanayinta yanzu sun kusa karewa. Ya ce; “Wata irin shaida kuma da ta taba zuciyata ita ce, yadda nassosin suka jeru bi da bi… Na gane cewa al’amuran annabci da suka riga suka cika sun auku ne a wani lokachi na musamman. Shekaru dari da ashirin din nan kafin ruwan tufana (Farawa 6:3); kwana bakwai din nan kafin ita ambaliyar, da kwana arba’in na ruwan sama da aka ce za a yi (Farawa 7:4); shekara dari hudu na bakunchin zuriyar Ibrahim (Farawa 15:13); kwana uku na mafalkan mai shayaswan Fir’auna da mai-tuyansa (Farawa 40:12-20); shekara bakwai na mafalkin Fir’auna (Litafin Lisafi) 14:34); Shekara uku da rabi na yunwa (Sarakuna I, 17:1) (Dubi Luka 4:25); shekara saba’in na kasancewa kamammu (Irmiya 25:11); wokatai guda bakwai na Nebuchadnezzar (Daniel 4:13-16); da kuma bakwai, bakwai, satin da biyu, da kuma bakwai guda, wadanda jimlar su ta kai bakwai saba’in, da aka kadara ma Yahudawa (Daniel 9: 24-27); al’amuran wokatan nan a baya da annabci ne kawai sun kuma cika daidai bisa ga annabchi.”BJ 321.1

    Sabo da haka sa’anda cikin binciken Littafin ya ga lokuta a jere a jere da bisa ganewarsa suka kai har zuwan Kristi na biyu, sai ya dauka cewa lokacin da aka ayyana kenan, wanda Allah ya bayana wa bayinsa. Musa ya ce; “Al’amura na asirin ga Ubangiji Allahnmu suke; amma wadanda am bayyana, a gare mu suke duk da yayan mu har abada;” kuma Ubangiji tawurin annabi Amos, ya ce, “Ba za ya yi komai ba, sai shi baiyana asirinsa ga bayinsa annabawa.” Kubawar Shari’a (29:29); Amos 3:7. Sabo da haka masu binciken maganar Allah za su yi begen samun bayani a sarari cikin Littafin, na abu mafi girma da zai faru cikin tarihin dan Adam. Miller ya ce, “Da shike na gamsu cewa kowane nassi horarre daga wurin Allah mai amfani ne (Timthawus II, 3:21), kuma cewa ba a taba kawo wani annabci bisa ga nufin mutum ba, amma an rubuta su yayin da Ruhu Mai-tsarki yana motsa su ne (Bitrus II, 1:21), an kuma rubuta su domin koyaswarmu, domin tawurin hakuri da ta’aziyar litattafai mu zama da bege” (Romawa 15:4), Sai na ga sassan Littafin da suka kunshi jeri jerin al’amura sun zama wajibi gare mu mu yi nazarinsu kamar kowane sashi na Littafin. Sai na ga cewa cikin kokarin fahimtar abin da Allah cikin jinkansa ya ga ya dace ya bayana mana, bani da yanci in tsallaka lokutan annabci.BJ 322.1

    Annabcin da yafi bayana lokacin zuwan Yesu na biyun shi ne Daniel 8:14: “Har yamma da safiya guda alfin da dari Uku; kana za a tsarkake wuri mai-tsarki.” Bisa ga kaidarsa ta barin Littafin ya fassara kansa, Miller ya ga cewa rana daya a annabci yana matsayin shekara daya ne (Lissafi 14:34; Ezekiel 4:6), ya ga cewa kwana 2,300 din nan na annabci, ko kuma shekaru a zahiri, zai wuce zamanin Yahudawa sosai ma, don haka hakika annabcin bai shafi haikalin wancan zamanin ba. Miller ya yarda da ra’ayin da aka fi yarda da shi cewa a zamanin Kirista, duniya ita ce haikalin, sabo da haka ya dauka cewa tsarkakewar haikalin da Daniel 8:14 ya ambata yana nufin tsarkakewar duniya ne da wuta lokacin zuwan Kristi na biyu. Idan kuwa za a iya sansance farkon kwana 2,300 din, a ganinsa za a iya gane lokacin zuwansa na biyu din. Watau ta haka ne za a bayana lokacin nan da yanayi na yanzu, da “dukan iko da shagulgulan sa da fahariyarsa da danniyarsa zai kai karshen;” lokacin da za a “cire la’anan nan daga duniya, a murkushe mutuwa, a ba bayin Allah lada, annabawa da tsarkaka da masu-tsoron sunansa, a kuma hallaka masu-hallaka duniya.”BJ 322.2

    Da karin himma, Miller ya ci gaba da binciken annabce annabcen dare da rana, yana binciken wannan al’amari mai-tarin muhimmanci. Bai sami haske daga Daniel 8, game da inda kwana 2,300 din ya fara ba. Ko da shike an umurci malaika Jibrailu ya ba Daniel fahimin wahayin, bai ba shi fasarar duka ba. Sa’anda aka bayana ma annabin muhiman tsananin da zai abka ma ekklisiya; karfin sa ya kare. Bai iya jimrewa ba kuma, sai malaikan ya bar shi tukuna. Daniel ya suma, ya yi chiwo kuma ‘yan kwanaki. Ya ce, “ Na yi mamaki da ruyan, amma babu wanda ya gane ta.”BJ 322.3

    Amma kuma Allah Ya rigaya Ya ce ma maliakan, “Ka sanas da mutanen nan da ruyan.” Dole a cika umurnin nan. Daga baya, malaikan ya dawo wurin Daniel ya ce, “Yanzu na fito domin in ba ka hikimar ganewa.” “Ka sani fa ka fahimta kuma.” Daniel 8:27,16; 9:22,23,25-27. Akwai abu daya muhimmin cikin ruyar sura 8 da ba a fassara ba, watau abin da ya shafi lokaci-kwana 2,300 din nan; don haka malaikan ya fi mai da hankali ga batun lokaci yanzu.BJ 323.1

    “An kadara bakwai, bakwai sau sabain domin mutanen ka da birninka mai-tsarki…. Ka sani fa, ka fahimta kuma, tun daga loton fitowar doka a mai da Urushalima, a ginata kuma, har zuwa loton Masiya sarki, za a yi bakwai bakwai; chikin bakwai sattin da biyu kuma za a sake gininta da karabku da ramin ganuwa, cikin kwanakin masifa ke nan. Bayan bakwai din nan sattin da biyu kuma, za a datse Masiyan, ba kwa za ya bar kowane nasa ba…. Za ya yi wa’adi mai-kwari kuma da masu-yawa domin bakwai daya; a tsakiyar bakwai din kuma za ya sa sacrifice da hadaya ta gari su fasa.”BJ 324.1

    An aiki malaikan wurin Daniel domin shi bayana masa abin nan da bai gane ba cikin wahayin sura ta takwas din na zancen lokacin nan; “Har yamma da safiya guda alfin da dari uku; kana za a tsarkake wuri mai-tsarki.” Bayan ya ce ma Daniel “Ka sani fa, ka fahimta kuma,” sai ya ce, “An kadara bakwai bakwai har saba’in domin mutanen ka da birninka mai-tsarki.” Ma’anar kalman nan “Kadara,” a nan “an yanke” ke nan. Malaikan ya ce an yanke bakwai saba’in, watau shekara 490, musamman domin Yahudawa. Amma daga ina aka yanke? Da shike kwana 2,300 din nan ne kadai aka ambata cikin sura 8, hakika daga cikin su ne aka yanke bakwai saba’in din; sabo da haka bakwai saba’in din zai fara daidai da kwana 2300 din ne. Malaikan ya ce bakwai saba’in din za su fara “daga fitowar doka a mai da Urushalima” ne. Idan aka gano ranan da aka ba da dokan nan, an gano inda kwana 2300 din sun fara ke nan.BJ 324.2

    Cikin Ezra 7, akwai wannan dokar. Dubi aya 12-26. Artaxexes, sarkin Persia ne ya ba da cikakkiyar dokar a 457 B.C. Amma cikin Ezra 6:14 an ce an gina gidan Ubangiji a Urushalima “bisa ga umurnin Cyrus kuma, da Darius da Artaxerxes sarkin Percia” ne. Sarakuna ukun nan ne, ta wurin farawa da kara tabbatarwa da karasa yin dokar suka kai ta cikar da annabcin ya bukata domin shi zama farkon shekara 2300 din. Idan aka dauki 457 B.C; shekaran da aka kamala yin dokar, a matsayin shekarar da aka yi dokar, za a tarar cewa kowane abin da annabcin ya ambata game da bakwai saba’in din ya cika.BJ 324.3

    “Tun daga fitowar doka a maida Urshalima, a ginata kuma, har zuwa loton Masiya sarki; za a yi bakwai bakwai: cikin bakwai sattin da biyu kuma,” watau bakwai sittin da tara, ko kuma shekara 483. Dokar Artaxerxes, sarkin Persia, ta fara aiki cikin kaka ne na 457 BC. Daga nan shekara 483 sun kai har kaka na A.D 27. Lokacin kuwa an cika wannan annabcin. Ma’anar “Masiya” it ce “Shafaffe”. A kakan A.D 27, Yohanna ya yi ma Kristi baptisma, ya kuma sami shafewa na Ruhu. Manzo Bitrus ya shaida cewa Allah ya zuba ma Yesu Ba-nazarat Ruhu Mai-tsarki da iko. Ayukan 10:38. Mai-ceton kansa kuma Ya bayana cewa: “Ruhun Ubangiji yana bisa gareni, gama ya shafeni da zan yi shelar bishara ga talakawa.” Luka 4:18. Bayan baptismarsa ya je Galili, “yana wa’azin bishara ta Allah, ya ce, Zamani ya chika” Markus 1:14,15.BJ 325.1

    “Zaya yi wa’adi mai-kwari kuma da masu yawa domin bakwai daya” (ko kuma har bakwai daya). Bakwi daya din nan shi ne na karshe cikin bakwai saba’in din nan; shi ne shekara bakwai na lokocin nan daga A.D 27 zuwa A.D 34, Kristi, da farko dai da kansa, daga baya kuma tawurin almajiransa, Ya mika ma Yahudawa gaiyatar bishara musamman. Yayin da manzanin suka tafi da albishiri din mulkin, umurnin mai-ceton shi ne: “Kada ku bita hanyar Alummai, Kada ku shiga kowane birni kuma na samariyawa; sai dai ku tafi wurin battatun tumaki na gidan Israila” Matta 10:5,6BJ 325.2

    “A tsakiyar bakwai din kuma za ya sa sacrifice da hadaya to gari su fasa.” A.D 31, shekara uku da rabi bayan baptimarsa, aka gichiye Ubangijin mu. Da babban hadayan nan da aka yi a Kalfari, tsarin nan na hadaya da har shekara dubu hudu ya rika misalta Dan-rago na Allah ya kai karshensa. Kamani ya sadu da abin da ya kamanta, aka kuma dena dukan hadayu na tsarin bukukuwan nan.BJ 325.3

    Kamar yadda mun rigaya mun gani, bakwai saba’in ko shekara 490 din sun kare a A.D 34 ne. A lokacin, tawurin kashe Istifanus da tsananta ma masu-bin Kristi. Sa’an nan aka ba duniya sakon ceton. Almajiran da zalunci ya tilasta su barin Urshalima, “suka tafi ko ina suna wa’azin Kalmar.” Filibus ya tafi birinin Samariya, ya yi masu wa’azin Kristi.” Bitrus, bisa ga bishewar Allah, ya bude bishara ga jarumin nan na Kaisariya, watau Karniliyus Mai-tsoron Allah, Bulus mai-kwazo kuma, aka aike shi ya kai albishirin “Chan nesa wurin al’ummai” Ayukan 8:4,5; 22:21.BJ 326.1

    Har wannan lokacin dai an cika kowane abin da annabci ya ambata, kuma an tabbatar da farkon bakwai saba’in din cewa 457B.C ne, kuma sun kare a A.D 34 ne. Daga wadannan, sansancewar karshen shekara 2,300 din ba abu mai-wuya ba ne. Bakwai saba’in din kwana 490 da aka yanke daga 2,300 din sun saurar kwana 490 da aka yanke daga 2300 din sun bar sauran kwana 1810. Bayan karshen kwana 490, za a dai cika kwana 1810 din. Daga A.D 34, shekara 1810 sun kai shekara ta 1844. Sabo da haka kwana 2,300 na Daiel 8:14 din nan sun kare a 1844 ne. A karshen wannan lokaci na annabcin, bisa ga shaidar malaikan Allah, “za a tsarkake haikalin” Ta haka kuwa an sansance lokacin tsarkakewar haikalin wanda ko ina an dauka cewa zai faru lokachin zuwan Kristi na biyu ne.BJ 326.2

    Da farko Miller da abokansa sun dauka cewa kwana 2300 din nan za su kare cikin bazarar 1844 ne, alhali annabcin yana maganar kaka ne. Wannan kuskuren ya jawo damuwa ga wadanda suka dauka cewa da bazaar ne Yesu zai dawo. Amma wannnan bai shafi koyaswar da ta nuna cewa 1844 ne karshen kwana 2300 din, kuma za a tsarkake haikali a lokachin ba.BJ 326.3

    Sa’ada Miller ya shiga nazarin Littafin don hakikance cewa wahayin ne daga Allah, da farko Miller bai za ta zai sami ganewa da ya samu yanzu ba. Shi kansa bai tabbatar da sakamakon bincikensa sosai ba. Amma shaidar Liffatin ta bayana a sarari ta yadda ba a iya kawas da ita ba.BJ 327.1

    Ya kebe shekara biyu don nazarin Littafin, a 1818 kuwa sai ya gane cewa shekara ashirin da biyar nan gaba Kristi za ya dawo don fansar mutanensa. Miller ya ce, “ Ba sai na fadi murnan da ta cika zuciyata sabo da abin faranta zuchiyan nan ba, ko kuma sabo da begena don kasancewa cikin farincikin fansassu. Littafin ya zama mani sabuwar littafi na. Hasken sa ya kawar da duk wani duhu da rashin fahimta daga kowace koyaswarsa; gaskiyar kuwa ta haskaka da daraja ainun! Kowane sabani da na gani a cikin maganar a da ya bata, kuma ko dashike ban gamsu da ganewata ta wadansu sassan ba, duk da haka haskensa ya wayar da duhun kai na har na sami marmarin binciken Littafin da ban sani za a taba samu daga koyaswoyinsa ba.” BJ 327.2

    “Da ganewar cewa Littafin ya yi annabcin aukuwar muhimman al’amuran nan cikin kankanin lokaci hakanan tambaya ta zo mani da karfin gaske game da alhakin da ke wuyana zuwa ga duniya, bisa ga shaidar da ta canja nawa tunanin.” Ya ji cewa wajibi ne gare shi ya mika ma wadansu hasken da shi ma ya samu. Ya san zai sami sabani daga marasa tsoron Allah, amma ya tabbata dukan Krista za su yi farincikin saduwa da Mai-ceton da suka ce suna kaunarsa. Tsoronsa kadai shi ne cewa cikin yawan murnarsa game da kusantowar kubutarwarsu, da yawa za su karbi koyaswar ba tare da bincika Littafin don gane gaskiyarsa ba. Sabo da haka ya jinkirta gabatar da shi, kada ya yi kuskure ya zama dalilin batar da wadansu. Wannan ya sa shi ya sake binciken ababan da suka goyi bayan ra’ayoyin da ya samu, ya kuma yi bimbini a hankali game da kowane abin da ya shiga masa duhu. Ya ga cewa hasken maganar Allah ya kawar da kowane jayayya. Cikin shekara biyar ya sami gamsuwa da masayin da ya dauka.BJ 327.3

    Yanzu kuma Alhakin sanar ma wadansu da abin da ya gaskanta ya sake dawo masa da karin karfi. “yayin da ni ke harka na, na rika ji a kunne na, ‘Je ka fada ma duniya hatsarinsu.’ Nassin nan ya dinga zuwa mani: ‘Kadan na che ma mungun mutum, Ya kai mungun mutum, lallai za ka mutu, kai kwa ba ka yi managa domin ka fadakadda mugun shi bar hanyassa; wannan mugun mutum za ya mutu domin laifinsa, amma zan bidi jininsa gare ka. Amma idan ka fadakadda mugun mutum domin shi juyo ga barin hanyanssa, shi kwa baya juya ga barin hanyassa ba; za ya mutu sabada laifinsa, amma ka cheche ranka.” Ezekiel 33:8,9. Na gane cewa idan aka fadakar da miyagun da kyau, da yawansu za su tuba; idan kuwa ba’a fadakar da su ba, za a bidi jininsu daga gareni.”BJ 328.1

    Ya fara bayana ra’ayoyinsa, ba cikin jama’a ba, duk sa’anda ya sami zarafi, yana addu’a cewa wani mai-bishara zai ga muhimmancinsu ya dukufa ga shelarsu. Amma bai iya rabuwa da sanin cewa shi kanshi yana da alhakin fadakarwar ba. Kalmomin nan sun dinga dawowa zuchiyarsa; “Je ka shaida ma duniya; zan bidi jininsu gareka” shekara tara yana jira, abin yana damunsa, har sai 1831 sa’an nan ya bayana dalilin bangaskiyarsa a gaban jama’a.BJ 328.2

    Kamar yadda aka kira Elisha daga bin shanun nomansa a jeji, ya karbi alkyabar tsarkakewa don zama annabi, haka aka kira William Miller ya bar garmarsa domin shi bude ma mutane asiran mulkin Allah. Da rawan jiki ya shiga aikinsa, yana bi da masu sauraronsa a hankali ta lokutan annabci har zuwan Yesu ba biyu. Kowane yunkurin ya kara masa karfi da jarumtaka yayin da ya ga marmarin da kalmominsa suka jawo.BJ 329.1

    Daga kalmomin ‘yan-uwan shi ne, inda ya ji kiran Allah, Miller ya yarda ya bayana ra’ayoyinsa ga jama’a. Yanzu shekarun haifuwarsa hamsin, bai saba da magana a gaban jama’a ba, kuma ya damu da cewa shi bai cancanci yin wannan aikin ba. Amma tun daga fari an albarkaci aikinsa sosai da ceton rayuka. Falkaswar addini ta biyo bayan laccar sa ta farko, har iyalai sha-uku suka tuba dukansu, banda mutum biyu kawai. Nan da nan aka roke shi ya yi magana a wadansu wurare kuma, a kowane wuri kuma, aikin sa ya kai ga falkaswar aikin Allah. Masu-zunubi suka tuba, Kirista suka kara dukufa da addinin Kirista. Shaidar wadanda ya yi aikin su ta ce; “Yana taba zukatan irin mutanen da sauran mutane basu iya masu komi ba.” Wa’azin sa yakan falkas da zukatan jama’a game da muhimman al’amura na addini, kuma yakan kawo ragewar sha’awar duniya na zamanin.BJ 329.2

    A kusan kowane gari mutane da yawa, daruruwa ma a wadansu garuruwa, suka tuba sakamakon wa’azinsa. A wurare da yawa aka bude masa ekklesiyoyi masu Kin ikon Paparuma, kuma pastocin ekklesiyoyin ne sukan gayyace shi wa’azin. Ya kudurta cewa ba zai yi aiki a wurin da ba’a gaiyace shi ba, duk da haka ya iske cewa baai iya zuwa rabin wurarren da aka gayyace shi ba. Da yawa da basu karbi ra’ayoyinsa game da ainihin lokacin zuwan Yesu na biyu ba sun yarda cewa hakika Yesu zai dawo, ba da jimawa ba, kuma ya kamata su shirya. A wadansu manyan birane, aikin shi ya yi tasiri sosai. Masu shagunan giya suka watsar da jarinsu, suka mai da shagunan nasu wuraren taruwa; aka tarwasa wuraren chacha; kafirai da masu cewa ba ruwan Allah da abinda mutane ke yi, har ma da gagararrun ‘yan iska, suka sake, wadansun su kuwa sun yi shekaru basu shiga gidan sujada ba ma. Dariku dabam dabam suka fara addu’oi a wurare dabam dabam, kusan kowace sa’a kuma masu jari sukan hadu da tsakar rana domin addu’a da yabo. Babu yawan ta da hankali, sai saduda ko ina cikin zukatan mutane. Aikinsa, kaman na yan canji na farko, ya shafi ganar da mutane ne da taba lamirinsu, maimakon ta da hankulansu.BJ 329.3

    A 1833, Miller ya sami lasin na yin wa’azi, daga ekklesiyar su ta Baptist. Pastocin darikarsa da yawa suka amince da aikinsa, kuma da yardar su ne ya ci gaba da aikin. Ya rika tafiya yana wa’azin ba fasawa, ko da shike ya fi kasancewa a New England ne da jihohin tsakiya. Shekaru da dama yana biyan bukatunsa daga aljihunsa, bai kuma taba samun isashen kurdi ma don tafiya wuraren da aka gayyace shi ba. Sabo da haka, aikinsa ga jama’a, maimakon kawo masa kurdi ma, ya janye ne daga dukiyar sa da ta dinga raguwa don haka, a wannan lokachin na rayuwarsa. Ya zama uba na babban iyali, amma da shike sun kasance masu tsimi da kuma kwazo, gonarsa ta isa biyan bukatunsu da na shi kansa.BJ 330.1

    Cikin 1833, shekara biyu bayan Miller ya fara bayana ma jama’a shaidu cewa Kristi Ya kusan zuwa, alama ta karshe daga alamun da Mai-ceton ya bayar na zuwan sa ta bayana. Yesu ya ce: “Tamrari za su fado.” Matta 24:29. Yohanna kuma, game da alamun rana ta Allah ya ce; “Tamrarin sama kuma suka fado a duniya, kamar itachen baure yakan kakabe yayansa da basu nuna ba, sa’anda babban iska ya raurawadda shi.” Ruya 6:13. Wannan annabcin ya cika sa’an da aka yi babban yayyafin taurari ran 13 ga Nuwamba, 1833. “Fadowar tamrari mafi yawa da ban mamaki da aka taba yi kenan;” “dukan sararin samaniya ko ina a Amerika, ya rude da haske kamar wuta! Babu wani abu da ya taba faruwa a sararin sama a kasan nan da aka kalle shi da sha’awa mai-yawa da kuma tsoro kamar wannan.” “Har yanzu kyaunsa yana zukatan mutane da yawa,… Ruwan sama bai taba zuba da kauri kamar yadda taurarin nan suka zubo a duniya ba, gabas da yamma, arewa da kudu, duk daya. A takaice, dukan sammai sai ka ce suna motsi ne,… kamar yadda Majallar Shehun Mallami Silliman ya ruwaito, an ga wannan al’amari ko ina a Amerika ta Arewa,… Daga karfe biyu har wayewan gari, sararin sama yana kwance shuru, kuma ba gizagizai, sai aka ajiye tarurari masu hasken gaske a dukan sararin sama.”BJ 331.1

    “Babu harshen da zai iya bayana kyaun wannan al’amarin,… wanda bai gani da idon shi ba, ba zai iya gane daukakar abin ba. Ya yi kamar dukan taurarin sama sun taru a wani wuri daya ne a sama kusa da tushen, suna kuma harbowa da sauri daidai da gudun haske, zuwa kowane bangon duniya, duk da haka kuma basu kare ba, dubbai suka bi bayan dubbai, sai ka ce an halice su don wannan al’amarin ne.” “Ba shi yiwuwa a sami wani kamanin itacen baure da ke kakkabe yayansa da basu nuna ba sa’anda babban iska ya raurawadda shi” kamar wannan.BJ 331.2

    A majallar kasuwanci ta New York ta ran 14 ga Nuwamba, 1833, an rubuta wani dogon sharhi game da wannan abu inda aka ce: “Babu mai-bin ussan ilimi ko kuma masanin da ya taba rubuta labari ko rahotun al’amari irin na safiyar jiya ba. Shekara dubu da dari takwas da suka wuce wani annabi ya yi annabcin wannan abin daidai,… idan za mu yarda cewa faduwar taurarin nan taurari ne suka fadi zahiri.”BJ 332.1

    Ta haka aka bayana alaman nan ta karshe ta zuwansa, game da shi kuwa Yesu ya ce ma almajiransa: “Lokacin da kun ga wadannan al’amura duka, ku sani ya yi kusa, har bakin kofa.” Matta 24:33. Bayan alamun nan, Yohanna ya ga babban al’amarin da ke biye, watau sararin sama ya shude kamar takarda yayin da duniya ta raunana, duwatsu da tsibirai kuma suka gusa daga wurarensu, miyagu kuma cikin tsoro suka so su gudu daga fuskar Dan mutum. Ruya 6:12-17.BJ 332.2

    Da yawa da suka ga fadowar taurarin sun gan shi kamar alamar hukumcin da ke zuwa ne, “mai-ban tsoro, alama tabbataciya ta jinkai, ta wancan babar rana mai-ban tsoro.” Ta haka aka jawo hankulan mutane zuwa cikar annabci, aka kuwa kai mutane da yawa ga jin kashedin zuwan Yesu na biyu din.BJ 332.3

    A shekara ta 1840, wata cikar annabcin kuma ta ja hankulan mutane sosai. Shekara biyu kafin nan, Josiah Litch, da ya daga manyan masu wa’azin zuwan Yesu na biyu, ya wallafa fasarar Ruya 9 da ya yi annabcin Mulkin Ottoman. Bisa ga lissafinsa, za a hambarar da mulkin nan “a AD 1840 ne, cikin watan Agusta,” kuma kwanaki kadan kafin hambararwar, ya rubuta cewa; “Idan sashen farkon, shekara 150, ya cika daidai kafin Deacozes ya hau gadon sarauta da izinin Turkawa, kuma shekara 391 da kwana goma sha biyar, sun fara a karshen sashe na farkon, za ya kare ran 11 ga Agusta, 1840 ne, sa’anda mulkin Ottoman a Constatinaple zai wargaje. Kuma na gaskata haka din ne zai faru.”BJ 332.4

    A daidai lokacin da aka ambata, Turkiya, tawurin jakadunta, ta amince da tsaron kungiyar kasashen Turai, ta haka kuma ta sa kanta kalkashin mallakar kasashen Kirista. Al’amarin ya cika annabcin daidai. Sa’anda aka sani, mutane da yawa suka yarda da sahihancin kaidodin fassara annabci da Miller tare da abokansa suka yi anfani da su, zancen dawowan Kristi din nan kuma ya kara ci gaba. Masana da masu matsayi suka hada kai da Miller wajen yin wa’azi da wallafa ra’ayoyinsa, kuma daga 1840, zuwa 1844 aikin ya ci gaba akai akai.BJ 333.1

    William Miller ya mallaki basira kwarai, ya kuma hada da horuwa da nazari; ya kuma kara da hikimar sama ta wurin hada kansa da tushen hikima. Mutum ne mai daraja, wanda dole ne a girmama shi a kuma daukaka shi, duk inda ake zancen aminci da halin kirki. Da shike ya hada halin kirki da tawali’un Kirista, da kuma kamewa, ya zama mai-sauraron kowa, yana sauraron ra’ayin sauran mutane tare da auna abin da suke fadi. Ba tare da fushi ko garaje ba, yakan gwada kowace koyaswa da maganar Allah, kuma bisirarsa da kyakyawar sanin sa na Littafin sun sa shi ya iya karyata kuskure ya kuma fallasa karya.BJ 333.2

    Duk da haka bai yi aikinsa ba tare da jayayya ba. Kamar ‘yan canji na farko mallaman addini basu karbi gaskiyan da ya koyar da soyayya ba. Da shike su basu iya kare ra’ayinsu ta wurin Littafin ba, sai suka shiga anfani da kalamai da koyaswoyin mutane, da al’adun ubani. Amma masu wa’azin gaskiyar sun yarda da maganar Allah ne kadai. “Littafin da Littafin kadai,” taken su ke nan. Rashin goyon bayan Littafin ya sa masu sabani da su suka shiga yi masu ba’a. aka yi anfani da lokaci da arziki da baiwa don wulakanta wadanda laifinsu kadai shi ne cewa sun yi begen dawowar Ubangijinsu da farinciki, suna kuma kokarin rayuwa mai-tsarki suna karfafa wadansu su ma su shirya domin bayyanuwarsa.BJ 333.3

    An yi kokari sosai don janye tunanin mutane daga zancen dawowan Yesu. Aka mai da shi kamar zunubi, abin duniya, a ce mutum yana binciken annabce annabcen da suka shafi zuwan Kristi da karshen duniya. Ta haka hidimar da aka fi sabuwa da ita ta raunana bangaskiya ga maganar Allah. Koyaswarsu ta mai da mutane kafirai, da yawa kuma suka shiga bin sha’awar zukatansu kawai. Sai kuma wadanda suka jawo matsalar suka masu begen zuwan Kristi laifin jawo matsalar.BJ 334.1

    Yayin da yake jan taron jama’a a gidaje suna jinsa, ba a cika ambaton sunan Miller ba, sai daita hanyar ba’a ko soka. Yan iska da kafirai, da karfafawa da suka samu daga ra’ayoyin mallaman addini, suka shiga zage zage, da maganganu na sabo cikin kokarin su na jibga zage zage da reni akansa da aikinsa. Mai furfuran nan da ya bar gidansa yana tafiya da kurdin aljihunsa daga birni zuwa birni, gari zuwa gari, yana aiki ba fasawa don kai ma duniya kashedi game da kusantowar hukunci, sai kuma aka soke shi cewa mai-tsananin ra’ayi ne, makaryaci, mai-rudu.BJ 334.2

    Ba’a da karya da zagi da aka jibga masa sun jawo masa fushin ‘yan jarida na duniya ma. Suka ce, “Mai da batu mai-girma da martaba mai-ban tsoro kamar wannan” abin wasa “ba wasa kawai ake yi da hankulan mutane ba” amma “ba’a ma ake yi da ranar hukumci, ana ba’a da Allah kansa, ana kuma rena ban razanar wurin hukumcinsa.”BJ 334.3

    Mai-zuga dukan mugunta ba ya so ne kawai ya karyata sakamakon sakon zuwan Yesu ba, amma ya hallaka dan sakon ma. Miller ya yi anfani da gaskiyar Littafin ga zukatan masu jinsa, yana tsauta ma zunubansu, yana kuma raunana gamsuwa da kansu da suke yi, kuma kalmominsa kai a waye sun jawo magabtaka gare shi. Jayayyan da ‘yan ekklesiya suka nuna ma sakonsa ta karfafa ‘yan iska kara sabani, magabta suka shirya kashe shi yayin da ya bar wurin taron. Amma malaiku masu-tsarki suna cikin taron, dayansu kuma, cikin kamanin mutum ya rike hannun bawan Allahn nan ya kai shi inda yan iskan basu gan shi ba. Bai rigaya ya gama aikinsa ba, shirin Shaitan da ‘yan sakon sa kuma bai yi nasara ba.BJ 334.4

    Duk da yawan sabani, sha’awar sakon zuwan Yesu ya ci gaba da karuwa. Daga ashirin ashirin da dari dari, jama’a suka karu har zuwa dubbai. An rika tuba ana shiga ekklesiyoyi, amma daga baya ruhun jayayya ya shiga, sabanin tubabbun nan, ekklesiyoyin kuma suka fara daukan matakan horon wadanda suka karbi koyaswar Miller. Wannan ya sa shi ya rubuta ma Kirista na dukan dariku jawabi inda ya ce idan koyaswoyinsa karye ne, a nuna masa kuskurensa daga Littafin.BJ 335.1

    Ya ce: “Mene ne muka gaskata da maganar Allah ba ta ce mu gaskata ba, kuma ku kanku kun ce Littafin ne kadai ka’idar bangaskiyarmu da ayukanmu? Menene, mun yi da ya jawo munanan soke soken da ake mana daga bagadi da kuma alkalami, ya kuma ba ku dalilin cire mu (Adventist) daga ekklesiyoyinku?” Idan mun yi kuskure, ku nuna mana inda muka yi kuskuren, ku nuna mana daga maganar Allah cewa mun yi kuskure; wulakancin ya ishe mu; wannan ba zai gamsar da mu cewa mun yi kuskure ba, maganar Allah ce kadai za ta sa mu canja ra’ayinmu. Ta wurin addu’a muka cimma matsayarmu, bisa ga shaida da muka gani a Littafin.BJ 335.2

    Daga sara zuwa sara gardadin da Allah ya aiko ma duniya ta wurin bayinsa an karbe su da shakka da rashin bangaskiya ma. Sa’an da zunubin mutanen zamanin Nuhu ya motsa Allah Ya kawo ambaliyar ruwa ga duniya, ya fara sanar masu da nufinsa domin su sami zarafin juyawa daga muggan halayyansu. Shekaru dari da ashirin ana jan kunnen su su tuba, kada Allah Ya bayana fushinsa ta wurin hallaka su. Amma sun ga sakon kamar tatsuniya ce, basu kuma gaskata shi ba. Cikin muguntarsu, sun yi ma dan sakon Allah ba’a, suka wofinta rokonsa, har ma suka zarge shi da tsageranci. Wane mutum daya ne ya tsaya yayi jayayya da dukan manyan mutanen duniya? Idan sakon Nuhu gaskiya ne, don me dukan duniya ba ta gan shi ta gaskata shi ba? Ra’ayin mutum daya sabanin hikimar dubbai! Ba za su ji gargadin ba, kuma ba za su fake a jirgin ba.BJ 335.3

    Masu ba’a suka nuna ababa na halitta, rani da damina ba sa fasawa, sararin sama bai taba zubo da ruwa ba, kullum raba ce tana kawo yabanya - suka ce: “Ba misalai ya ke yi ba kuwa? Da reni suka ce mai-wa’azin nan yana da yawan sha’awa ne kawai, suka kuma ci gaba da holewa, da muguntarsu fiye da da. Amma rashin bangaskiyarsu bai hana cikar annabcin ba. Allah Ya dade yana hakuri da muguntarsu, yana ba su damar tuba, amma daidai lokaci, hukumcinsa ya sauko kan masu kin jin kan sa.BJ 336.1

    Kristi ya ce za a yi irin rashin bangaskiyan nan game da zuwan sa na biyu. Kamar yadda a zamanin Nuhu “basu sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka, hakanan kuma bayanuwar Dan Mutum za ta zama,” in ji Mai-ceton. Matta 24:39. Sa’anda mutanen Allah ke hada kai da duniya, suna rayuwarsu, suna yin haramtattun ababa, sa’anda ekklesiya tana jin dadi irin na duniya yayin da ake aure-aure, kowa kuma yana begen shekaru da yawa na ci gaba irin na duniya, sa’an nan, faraf daya kamar walkiya, karshen burinsu da begen su zai zo.BJ 336.2

    Yadda Allah ya aiko bawan sa ya gardadi duniya game da rigyawa da ke zuwa, haka ya aiko zababbun yan sako su sanar da kusantuwar hukumci na karshe. Kuma kamar yadda mutanen zamanin Nuhu suka yi dariyan annabcin Nuhu, haka a zamanin Miller aka yi dariyan gargadinsa.BJ 337.1

    Don me ekklesiyoyin basu so wa’azin zuwan Yesu na biyu ba? Yayin da zuwan Ubangiji zai kawo ma miyagu wahala da hallaka, ga masu adalci yana cike da murna da bege ne. Wannan gaskiyar ce begen amintattu na Allah a dukan sararraki, don me ya zama “Dutsen tuntube” ga mutanensa? Ubangiji da kansa ne Ya yi ma alamajiran sa alkawali cewa: “Kadan na tafi na shirya maku wuri kuma, sai in sake dawowa, in karbe ku wurin kaina.” Yohanna 14:3. Mai ceton ne ma da ya hangi kadaici da bakincikin masu binsa, ya aiko malaiku su ta’azantar da su da alkawalin cewa zai sake dawowa da kansa, kamar yadda Ya hau sama, yayin da almajiran ke tsaye suna kallon haurawar kaunatacensu sama, hankalinsu ya koma ga kalmomin nan; “Ku mazajen Galili, don mi ku ke tsaye kuna duba zuwa sama? Wannan Yesu wanda aka dauke shi daga wurinku, aka karbe shi sama, kamar yadda kuka ga tafiyatasa zuwa chikin sama hakanan za shi dawo.” Ayukan 1:11. Sakon malaikun ya sake kawo bege. Almajiran “suka koma Urushalima da farinciki mai-girma: suna chikin haikali kullayaumi, suna albarkachi Allah.” Luka 24:52,53. Ba su yi farinciki don an raba su da Yesu aka bar su su yi ta fama da wahaloli da jarabobin duniya ba ne, amma domin tabbacin mai-ceton cewa zai sake zuwa ne.BJ 337.2

    Ya kamata shelar zuwan Kristi ta zama bishara ta farinciki mai-girma kamar wadda malaiku suka ba makiyayyan Baitalahmi. Masu kaunar Kristi da gaske dole za su marabci sanarwan nan mai-tushe daga maganar Allah cewa za Ya sake dawowa, ba domin a zage Shi, a rena Shi, a ki Shi, kamar zuwansa na farko ba, amma cikin iko da daukaka domin Ya fanshi mutanensa. Wadanda ba sa kaunar Mai-ceton ne suke so Ya kasance can; kuma ba abinda ya fi tabbatar da cewa ekklesiyoyin sun rabu da Allah kamar haushi da kiyayyar da sakon nan daga sama ke jawowa.BJ 337.3

    Wadanda suka karbi sakon zuwan Kristi sun ga anfanin tuba da kaskantar da kai a gaban Allah. Da yawa sun dade suna jinkiri tsakanin Kristi da duniya; yanzu sun ga cewa lokaci ya yi da za su dauki matsayi, “Ababa na har abada suka zama zahiri a gare su. An kawo sama kusa, suka kuma ga kansu masu-laifi ne a gaban Allah.” Aka motsa Kirista zuwa sabuwar rayuwa ta ruhaniya. Suka ga cewa lokaci ya kasa, cewa abinda ya kamata su yi ma mutane dole su yi shi da sauri. Suka hangi har abada a gabansu, duk wani abin duniya kuma ya dena burge su. Ruhun Allah Ya sauko masu, Ya kuma ba da iko ga rokerokensu ga yan’uwansu da masu zunubi, cewa su shirya domin rana ta Allah. Shaidar rayuwarsu ta yau da kullum ta rika tsauta ma ‘yan ekklesiya da basu tuba ba. Wadannan basu so a dame su cikin neman holewarsu, da son kurdinsu, da kuma neman sunan su ba. Shi ya jawo kiyayya da sabani da aka yi ma bangaskiya ga zuwan Kristi da masu shelarta.BJ 338.1

    Sa’anda aka iske cewa ba za a iya karyata koyaswoyin nan na wokatai na annabci ba, musu hamayya suka yi kokarin hana binciken tawurin koyar da cewa an hatimce annabce annabacen. Ta hakanan ‘yan Kin ikon paparuma suka bi sawun yan Rum. Yayin da ekklesiyar paparuma ke hana ma mutane Littafin, ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma sun ce wai wani muhimmin sashen maganar Allahn ma da ke koyar da gaskiyar da ta shafi lokacin mu, wai ba za a iya gane shi ba.BJ 338.2

    Masu aikin bishara da sauran mutane suka ce wai littafin Daniel da na Ruya asirai ne da ba za a iya ganewa ba. Amma Kristi Ya ja hankulan almajiransa zuwa maganar annabi Daniel game da al’amuran da za su auku a zamaninsu, Ya ce: “Bari mai-karantawa shi fahimta,” Matta 24:15. Kuma zacen cewa wai littaffin Ruya asiri ne da ba za a iya fahimta ba ya bambanta da sunan littafin kansa, watau, “Ruya ta Yesu Kristi wadda Allah ya ba shi domin shi bayana ma bayinsa, al’amura ke nan da za su faru ba da jinkiri ba,… mai-albarka ne shi wanda ke karantawa, da su kuma wadanda ke jin zantattukan annabcin, suna kwa kiyayae abin da an rubuta a chiki, gama sa’a ta kusa.” Ruya 1:1-3.BJ 339.1

    Annabin ya ce “Mai-albarka ne shi wanda ke karanatawa”- akwai wadanda ba za su karanta ba; albarkar ba tasu ba ce. “Suna kwa kiyaye abin da an rubuta a ciki.” Da yawa suna kinjin gargadi da umurni da ke cikin littafin Ruya; ba wanda a cikin su zai iya samun alabarkan da aka yi alkawalinsa. Dukan masu yi ma annabcin da alamun da aka bayar a nan ba’a, dukan wadanda suka ki canza rayuwarsu, su kuma shirya domin zuwan Dan mutum, ba za a masu albarka ba.BJ 339.2

    Bisa ga shaida daga Littafin, don me mutane ke koyar da cewa Ruyan asiri ne da ya fi karfin ganewar mutum? Asiri ne da aka bayana, littafin da aka bude. Nazarin Ruyan yana kai hankali mutum zuwa annabce annabcen Daniel, kuma dukansu suna ba da gargadi mafi muhimmanci daga Allah zuwa ga mutane game da al’amura da za su auku a karshen tarihin duniya.BJ 339.3

    Ga Yohanna aka bayana al’amura masu ban sha’awa cikin rayuwar ekklesiya. Ya ga matsayi da hatsarori da sabani, da kuma kubutawar karshe ta mutanen Allah. Ya rubuta sakonin karshe da za su nunar da girbin duniya, ko a matsayin dammuna don rumbun sama ko kuma yayi domin wutar halaka. An bayyan masa batutuwa masu tarin muhimmanci, musamman ga ekklesiya ta karshe, domin wadanda za su juyo daga kuskure zuwa gaskiya su sami gargadi game da hatsaruka da sabanin da ke gaban su. Bai kamata wani ya kasance cikin jahilci game da abin da ke zuwa duniyan nan ba.BJ 339.4

    Amma don me jahilci ya yi yawa game da muhimmin fannin Littafin hakanan? Don me ake kiwuyan binciken koyaswoyinsa? Sakamako ne na kokarin Shaitan don boye ma mutane abin nan da ke fallasa rudunsa. Don haka Kristi mai Ruyan, da shike ya hangi yakin da za a yi da nazarin ruyar, ya furta albarka kan dukan wadanda za su karanta, su ji su kuma aikata kalmomin annabcin.BJ 340.1

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents