Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 13—Netherlands da Scandinavia

    A Netherlands, tun da wuri zaluncin paparuma ya jawo kin yarda. Shekaru dari bakwai kafin lokacin Luther, bishop biyu ba da tsoro ba, suka bayana kurakuran paparuma, domin sa’anda aka aike su jakadanci a Rum, sun gane ainihin halin tsarin paparuman: “Allah ya tanada ma amaryarsa ekklesiya kyakyawar guzuri don iyalinta, da gara mara shudewa ko lalacewa, ya kuma ba ta rawani da sandar sarauta na har abada … kana kuma anfani da dukan wadannan kamar taryen barawo. Ka aza kanka a haikalin Allah; maimakon makiyayi, ka zama kerkeci ga tumakin; … kana so mu gaskata cewa kai madaukakin bishop ne, amma kana yi kaman azalumi … maimako ka zama bawan bayi, yadda kake kiran kanka, kana kokarin zama Ubangijin iyayengiji. … kana jawo ma dokokin Allah raini …. Ruhu Mai-Tsarki ne mai gina dukan ekklesiyoyin duniya…. Birnin Allahnmu wanda dukan mu yan kasansa ne, yana kaiwa dukan yankunan sammai, ya kuma fi birnin da annabawa suka ba ta suna Babila, wadda ke da’awar cewa ita ta Allah ce, tana kai kanta sama, tana kuma yin alfaharin cewa hikimarta mara mutuwa ce; a karshe kuma, ko dashike ba dalili, tana da’awar cewa ba ta taba kuskure ba, kuma ba zata taba iya yin kurskure ba.”BJ 235.1

    Wadansu sun taso daga karni zuwa karni suna maimaita wannan kin yardan kuma, da suka bi kasashe dabam dabam, aka kuma san su da sunaye iri iri, suna da irin halin masu bishara na Vaudois, suka kuma baza bishara ko ina, sun kuma shiga Netherlands. Koyaswoyinsu suka bazu da sauri. Suka juya Littafin Waldensiyawa zuwa harshen Dutch. “Suka ce wannan ya yi anfani sosai; ba ba’a, ba tatsuniyoyi, ba wasa, ba rudu, sai kalmomin gaskiya; cewa akwai dai wurare masu wuyan ganewa amma ainihin dadin abin da ke da kyau da tsarki kuma yana da saukin ganowa daga cikinsa” Abin da abokan bangaskiya ta da suka rubuta kenan a karni na goma sha biyu.BJ 236.1

    Sai zaluncin Rum ya fara; amma a tsakiyar wuta da azaba masu ba da gaskiya suna ci gaba da yawaita; suna furta cewa Littafi ne kadai iko mara kuskure a sha’anin addini, kuma “bai kamata a tilasta wani ya gaskata ba, sai dai a ganar da shi tawurin wa’azi.”BJ 236.2

    Koyaswoyin Luther sun sami karbuwa a Netherlands, masu dukufa da aminci kuma suka shiga wa’azin bisharar. Daga wata lardin Holland, Meno Simons ya zo da iliminsa na Roman Katolika da shafewarsa priest duk da haka bai san Littafi ba, kuma bai yarda ya karanta shi ba don tsoron kada a yaudare shi ya yi ridda, sa’anda shakka game da koyaswar canja jibi zuwa ainihin jikin Yesu da jininsa ta dame shi, ya dauka jaraba ce daga Shaitan, kuma tawurin addu’a da furta zunubi ya yi kokarin kubutar da kansa daga jarabar; amma a banza. Tawurin zuwa cudanya a wuraren shakatwa ya yi kokarin danne muryar lamiri da ke zarginsa, amma a banza. Daga baya, ya shiga nazarin Sabon Alkawali, wannan kuwa tare da rubuce rubucen Luther, ya sa shi ya karbi sabuwar bangaskiyar. Bayan wannan, ya ga yadda a wani kauye kusa kusa aka yanke kan wani wai don an sake yi masa baptisma. Wannan ya sa shi binciken Littafi game da baptismar yara. Bai ga dalilinsa daga Littafi ba, amma ya ga cewa ko ina tuba da bangaskiya ake bukata kafin a yi ma mutum baptisma.BJ 236.3

    Menno ya janye daga ekklesiyar Rum, ya kallafa ransa ga karya da gaskiyan da ya samu. A Jamus da Netherlands, wadansu masu matsanincin ra’ayi suka taso, suna koyaswoyi na wauta da hadasa hargitsi, suna bata oda da hankali, har ma suna jawo gwada karfi da bare. Meno ya ga munanan sakamakon da ayukan nan za su haifar, sai ya shiga hamayya da koyaswoyin kuskuren nan da munanan dabarun masu matsanancin ra’ayin. Amma sun rigaya sun rudi mutane da yawa, ko da shike mutanen sun watsar da munanan koyaswoyin; akwai kuma zuriyar Kirista na da da yawa, sakamakon koyaswar Waldensiyawan. Meno yayi aiki da nasara mai-yawa cikin wadannan kungiyoyin.BJ 237.1

    Ya yi shekara ashirin da biyar yana tafiye tafiye tare da matarsa da yaransu, suna jimre manyan wahaloli da talauci, kullum kuma ran shi na ciki musamman cikin marasa gata, amma yana tasiri ko ina. Yana da baiwar iya magana, ko dashike iliminsa ba yawa, shi kuwa mai cikakken aminci ne, mai tawali’u da halayyan kirki, da ainihin himmar ibada, yana ba da kwatancin koyaswarsa ta wurin rayuwarsa, ya kuma sami karbuwa ga mutane. Masu binsa a warwatse suke, kuma ana kuntata masu. Sun wahala kwarai daga gigicewar masu matsanancin ra’ayi. Duk da haka dai jama’a da yawa sun tuba sabo da aikinsa.BJ 237.2

    Ba inda aka karbi sabobin kowasoyin kamar Netherlands. A kasashe daya daya ne kawai aka fi tsananta ma masu kiyaye su. A Jamus, Charles V ya hana canjin, kuma son sa ne da ya hallaka dukan masu kiyaye sabobin koyaswoyin, amma ‘ya’yan sarakuna suka yi tsayayya da zaluncinsa. A Netherlands ikonsa ya fi yawa, kuma dokokin zalunci suka rika bin juna akai akai. Karanta Littafi, ko ji ko wa’azin Littafi, ko ma yin Magana game da shi, yakan jawo horon kisa ne, yin addu’a ga Allah cikin sirri, kin sunkuya ma gunki, ko raira zabura, duk hukuncinsu kisa. Ko da ana ce an bari, har da rantsuwa ma, akan hukunta laifinsu, in maza ne, a kashe su da takobi; in mata ne, a bizne su da ransu. Dubbai sun hallaka a zamanin mulkin Charles V da na Philip II.BJ 237.3

    A wani likaci iyali guda aka kawo gaban masu binciken, aka zarge su da rashin zuwa mass da kuma yin sujada a gida. Sa’anda aka tambayi autan dan game da ayukansu cikin sirri sai ya amsa: “Mukan fadi a gwiwarmu ne, mu yi addu’a cewa Allah ya haskaka zukatanmu, ya kuma gafarta zunubanmu; mukan yi addu’a don sarkinmu; muna addu’a don majitarorinmu, cewa Allah ya kiyaye su?” Wadansu masu shari’an suka kadu, duk da haka an kashe uban da daya daga cikin ‘ya’yansu.BJ 238.1

    Bangaskiyar wadanda aka yi wa zaluncin ta je daidai da fushin azaluman. Ba maza kadai ba, mata da ‘yan mata ma sun nuna karfin zuciya mara kaduwa. “Mata sukan tsaya a gefen katakon da ake kashe mazasu, kuma yayinda yake jimre wutar, takan rada masa kalmomin ta’aziya, ko kuma ta raira zabura don karfafa shi.” “Yan mata sukan kwanta cikin kabarinsu da ransu kamar suna cikin dakinsu da suke barci a ciki kowane dare; ko kuma su je dakalin katakon nan da wutan, suna saye da tufafinsu mafi kyau, kamar za su bukin aurensu.”BJ 238.2

    Kamar lokacin da kafirci ya so ya hallaka bishara, jinin Kirista ya zama iri. Zalunci ya kara yawan shaidu na gaskiya. Shekara bayan shekara, sarkin da ya haukace da himmar mutane da ta ki mutuwa, ya ci gaba da muguntarsa; amma a banza. Kalkashin William bafaden Orange, canjin ya kawo ma Holland ‘yancin sujada ga Allah.BJ 238.3

    A duwatsun Piedmont, a filayen Faransa, da gaban tekun Holland, ci gaban bishara ya sami bayanuwa ta jinin almajiranta. Amma a kasashen Arewa ya shiga cikin salama. Dalibai a Wittenberg da suke dawowa gidajensu, suka kai sabuwar bangaskiyar har Scandinaviya. Wallafawar rubuce rubucen Luther ma ya baza hasken. Mutanen arewan nan masu saukin kai suka juya daga lalacewa da shagali, da kuma camfe camfen Rum, suka rungumi saukin kai da gaskiyar Littafi masu kawo rai.BJ 238.4

    Tausen, “mai-canjin Denmark,” dan talaka ne. Yaron ya nuna alamar yawan bisira; ya yi kishin samun ilimi, amma yanayin iyayensa ya hana shi samu, sai ya shiga zaman zuhudu. Nan fa tsabtar ransa da amincinsa sun burge mai gidansa. Da aka gwada shi sai aka ga cewa yana da baiwar da za ta zama da anfani ga ekklesiya nan gaba. Aka kudurta za a ba shi ilimi a wata jami’a a Jamus ko Netherlands. Sai aka ba dalibin nan damar zaben jami’ar da zai je, amma ban da Wittenberg. Ba a so a sa dalibin cikin hatsarin gubar ridda ba, in ji priestocin.BJ 239.1

    Tausen ya je Cologne, daya daga biranen da koyaswar Rum ta fi karfi. A nan, ba da jimawa ba, ya yi kyamar dabon masu makarantar. A lokaci dayan, ya sami rubuce rubucen Luther. Ya karanta su da marmari da mamaki kuma, ya kuma so da dan canjin da kansa ya koyar da shi. Amma kafin hakan ya faru, dole ya bata ma maigidansa zuciya har ma ya dena taimakonsa. Ba da jimawa ba, ya dauki kudurinsa, ba da jimawa ba kuwa aka yi rajistarsa a matsayin dalibi a Witternberg.BJ 239.2

    Sa’an da ya dawo Denmark, sai ya koma zaman zuhundu kuma. Ba wanda ya zata cewa yana Luthanci tukuna; bai bayana asirinsa ba, amma ya yi kokari, ba tare da ingiza kiyayar abokansa ba, don jawo su zuwa bangaskiya mafi tsabta da rayuwa mafi tsarki. Ya bude Littafi ya kuma bayyana ainihin ma’anarsa, daga bisani kuma ya yi wa’azin Kristi gare su a matsayin adalcin mai zunubi, da begensa na ceto. Mai gidansa a wurin zaman zuhudun nan ya fusata kwarai, domin ya yi bege mai yawa cewa Tansen zai zama gwarzon mai kare Rum. Nan da nan aka cire shi daga inda yake aka sake masa wuri inda aka tsare shi cikin dakinsa, ana duba shi ba sakewa.BJ 239.3

    Sabobin masu lura da shi sun razana sa’anda masu zaman zuhudu da yawa suka tuba suka zama masu Kin ikon paparuma. Daga dakin da aka tsare shi, Tausen ya rika shaida ma abokansa gaskiyar. Da a ce priestocin Denmark din nan sun kware a tsarin ekklesiya na magance ridda da ba a sake jin muryar Tansen ba kuma, amma maimakon tura shi wani kurkuku na kalkashin kasa, sai suka kore shi daga gidan zaman zuhudun. Yanzu ba su da iko. Wata sabuwar doka ta ba da kariya ga masu koyar da sabuwar koyaswar. Tansen ya fara yin wa’azi. Aka bude masa majami’un, mutane kuma suka rika taruwa suna ji. Wadansu ma suka rika wa’azin maganar Allah, aka baza Sabon Alkawali na harshen Denmark ko ina. Kokarin ‘yan paparuma don hambarar da aikin ya fadada shi ne, ba da jimawa ba kuma Denmark ta sanar da cewa ta karbi sabuwar bangaskiyar.BJ 240.1

    A Sweden ma, samari da suka rigaya suka sha daga rijiyar Witternberg sun kai ma yan kasarsu ruwan nan na rai. Biyu daga cikin shugabaninin canjin a Sweden, Olaf da Laurantius Petri, ‘ya’yan wani makeri a Orebro sun yi makaranta kalkashin Luther da Melanchton, suka kuma koyas da gaskiyar da suka koya. Kamar Luther, Olaf ya motsa mutanen da himmarsa da kaifin bakinsa kuma, yayin da Laurentius kuma, kamar Melanchthon, mai sani ne mai zurfin tunani, natsetse kuma. Dukan su mutane ne masu zurfin ibada, kwararrun masanan tauhidi da karfin zuciya wajen fadada gaskiya. Sun gamu da jayayyar yan paparuma. Prestoci ‘yan paparuma suka zuga jahilai da masu camfi. Yan iska sun rika kai ma Olaf Peteri farmaki, sau da yawa kuma da kyar ya tsira da ransa. Amma sarki ya goyi bayan ‘yan canjin nan, ya kuma tsare su.BJ 240.2

    Kalkashin shugabancin ekklesiyar Rum mutanen sun nutse cikin talauci da danniya. Basu san Littafin ba; kuma da shike addininsu na alamu da bukuwa ne kawai, mara haskaka tunani, suka fara komawa zuwa bangaskiyar arnanci da ayukan kafirci na iyayensu. Kasar ta rabu ta yadda tashe tashen hankulansu suka kara ma kowa wahala. Sarkin ya kudurata yin canji a kasa da ekklesiya, ya kuma marabci kwararrun masu taimakon nan cikin yaki da Rum.BJ 241.1

    A gaban sarki da shugabanin Sweden, Olaf Pedri ya kare koyaswoyin sabuwar bangaskiyar, sabanin jarumawan Rum. Ya ce ya kamata a karbi kyaswoyin ekklesiya idan sun je daidai da Littafin ne kawai; cewa Littafin ya bayana muhimman koyaswoyin addini a fili da sauki kuma, domin dukan mutane su iya fahimtarsu. Kristi ya ce “Abin da ni ke koyarwa ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni.” Yohanna 7:16; Bulus kuma ya ce: “idan har ya yi wa’azin wata bishara daban da wadda ya karba zai zama la’anne (Galatiyawa 1:8). Dan canjin ya ce; “Don me wadansu zasu kafa koyaswoyin da suka ga dama sa’annan su ce wajibi ne a kiyaye su don samun ceto?” Ya nuna cewa dokokin ekklesiya basu da iko idan suka saba ma dokokin Allah, ya kuma manne ma babban kaidan nan cewa “Littafin da Littafin kawai” shi ne ma’aunin bangaskiya da ayuka.BJ 241.2

    Wannan hamayyar tana nuna mana “irin mutanen mayakan canjin. Ba jahilai ba ne, ko yan darika, ko masu tada rudani, ko kusa; mutane ne da suka yi nazarin maganar Allah, suka kuma san yadda za su yi anfani da makaman da Littafi ya ba su. Game da sani, sun yi fice a zamaninsu. Idan muka mai da hankulan mu ga sunannun cibiyoyi kamar Witternberg da Zurich, da sannanun sunaye kamar Luther da Melanchthon, da Zwingli da Oecolampadius, nan da nan za a ce mana wadannan ne shugabannin aikin, kuma ya kamata su nuna iko mai girma da nasarori masu yawa; amma ba haka na kasa da su ba. Bari dai mu koma lungun fagen faman nan na Sweden, wanda ba a saurin ganewa, da kuma sunayen nan Olaf da Laurentius Petri, da ba a san su sosai ba — daga iyayen gida zuwa almajiran kenan - me za mu gani? … Masana da kwarraru na tauhidi; wadanda suka kware a sanin dukan tsarin bishara ta gaskiya, kuma suna nasara kan masannan makarantun Rum da masu martabar ta.BJ 241.3

    Sakamakon wannan jayyayar, sarkin Sweden ya karbi bangaskiyar Kin ikon paparuma, jima kadan kuma majalisar kasar ta bayana cewa ta goyi baya ita ma. Olaf Petri ya rigaya ya juya Sabon Alkawali zuwa harshen Sweden, sarki kuma ya roke shi da dan’uwansa suka shiga juya dukan Littafin. Ta hakanan mutanen Sweden suka sami maganar Allah cikin harshensu. Majalisa ta umurta cewa ko ina a kasar, masu aikin bishara su bayana Littafin, a kuma koya ma yan makaranta karanta Littafi.BJ 242.1

    Sannu a hankali aka kori duhun jahilci da canfi ta wurin hasken bishara. Da shike an yantar da ita daga danniyar Rum, kasar ta sami karfi da girman da ba ta taba samu ba. Sweden ta zama babbar cibiyar Kin ikon paparuma. Shekaru dari daga bisani, a lokacin kunci sosai, wannan karamar kasa mara karfi wadda ita ce kadai a Turai ta taimaka — sai ga ta ta ceci Jamus a mumunan yakin shekaru Talatin din nan. Dukan Turai ta Arewa ta kusan sake nutsewa kalkashin zaluncin Rum kuma. Mayakan Sweden ne suka taimaki Jamus ta juya ci gaban Rum, ta samo yanci ma masu kin ikon Rum - Calvinawa da Luthawa - ta kuma dawo da yancin lamiri ga kasashen da suka karbi Canjin.BJ 242.2

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents