Babi na 30—Gaba Tsakanin Mutum da Shaitan
“Tsakaninka da machen kuma zan kafa magabataka, da tsakanin zuriyarka da zuriyatta kuma; shi za ya kuje kanka, kai kuma zaka kuje duddugensa. Farawa 3:15. Hukunchin da aka zartas ma Shaitan bayan faduwar mutum, annabci ne ma, wanda ya kunshi dukan sararaki har karshen lokaci, ya kuma bayana babban tashin hankalin da zai shafi dukan kabilun ‘yan Adam da za su taba rayuwa a duniya.BJ 502.1
Allah ya ce, “Zan sa gaba.” Gaban nan bai je daidai da yanayin halitta ba. Sa’anda mutum ya ketare dokar Allah, yanayinsa ya zama mungu, ya kuma sami jituwa, ba sabani ba, da Shaitan.BJ 502.2
Bisa yanayi, ba gaba tsakanin mutum mai-zunubi da wanda ya kago zunubin, dukansu sun zama miyagu ta wurin ridda. Mai-ridda ba ya taba hutawa, har sai ya sami tausayawa da goyon baya tawurin rudin wadansu su bi gurbinsa. Saboda wannan dalilin ne fadaddun malaiku da miyagun mutane ke hada kai cikin abota sosai. Da ba don Allah ya shiga tsakani ba, da Shaitan da mutum sun shiga wani hadin kai na sabani da Allah; kuma maimakon yin gaba da Shaitan, da dukan iyalin duniya sun hada kai wajen yin jayayya da Allah.BJ 502.3
Shaitan ya jarabci mutum ya yi zunubi, yadda ya sa malaiku su ka yi tawaye, domin ta wurin wannan shi sami hadin kai cikin yakinsa da Allah. Babu mahawara tsakaninsa da fadaddun malaikun game da kiyayarsu ga Kristi, yayin da suka sami rashin jituwa game da dukan sauran ababa, sun hada kai sosai wajen jayayya da ikon shugaban dukan halitta. Amma sa’anda Shaitan ya ji cewa gaba za ta kasance tsakaninsa da macen, da kuma tsakanin zuriyarsa da zuriyan macen, ya san cewa kokarinsa na lalata yanayin mutum zai sami cikas; cewa ta wata hanya za a ba mutum ikon kin yarda da ikonsa.BJ 503.1
Abin da ya ingiza magabtakan Shaitan da ‘yan Adam shi ne cewa tawurin Kristi, su masu cin moriyar kaunar Allah da jin kansa ne. Yana so ne ya rushe shirin nan na fansar dan Adam, ya jawo ma Allah rashin daraja, tawurin bata aikin hannunsa; zai jawo bakinciki a sama, ya kuma cika duniya da kaito da hallaka. Sa’an nan yana cewa dukan wannan sakamakon halitar mutum da Allah ya yi ne.BJ 503.2
Alherin da Kristi ya shuka cikin mutum ne yake haifar da magabtaka tsakaninsa da Shaitan. Ba domin wannan alherin tubarwa da ikon sabontawa ba, da mutum zai ci gaba da kasancewa kamammen Shaitan, bawan da zai kasance a shirye kullum ya bi umurnin Shaitan. Amma sabuwar kaidar a cikin mutum ya iya kin azalumin nan mai-kwace. Duk wanda aka ga yana kin zunubi maimakon sonsa, duk wanda ya ke ki yana kuma nasara da muradan zuciya da su ka mallaki zuciya a da, yana nuna aikin kaida ne daga sama dungum.BJ 503.3
Sabanin da ke tsakanin ruhun Kristi da ruhun Shaitan ya bayana a fili sa’anda duniya ta karbi Yesu. Ba lallai don ya bayana ba tare da arziki na duniya, ko fahariya, ko nuna isa ne Yahudawa su ka ki shi ba. Sun ga cewa Ya na da iko da ya fi arzikin duniya da duk wani abin fahariya muhimmanci. Amma kuma tsarkin Kristi da tsabtarsa sun jawo masa kiyayyar kafirai. Rayuwarsa ta musun kai da himma mara zunubi ta kasance soka na dindindin ga mutane masu fahariya da masu fasikanci. Wannan ne ya jawo ma Dan Allah kiyaya. Shaitan da miyagun malaiku suka hada kai da miyagun mutane. Dukan masu ridda suka hada baki sabanin jagoran gaskiya.BJ 503.4
Ana nuna ma masu bin Kristi daidai gaban da aka nuna ma Mai-gidan na su ne. Duk wanda ya ga munin zunubi, da taimako daga sama, kuma ya ki faduwa cikin jaraba, zai fuskanci fushin Shaitan da talakawansa lallai. Muddan akwai zunubi da masu aikata shi, kiyaya ga kaidodin gaskiya da tsananta ma masu gaskiya zai ci gaba. Masu bin Kristi da bayin Shaitan ba za su iya jituwa ba. Laifin giciyen nan bai kare ba. “I, kuma dukan wadanda su ke so su yi rai mai-ibada chikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” Timothawus II, 3:12.BJ 504.1
Wakilan Shaitan kullum suna aiki kalkashin umurninsa don tabbatar da ikonsa da gina mulkinsa sabanin gwamnatin Allah. Don haka suna kokarin rudin masu bin Kristi, su janye su daga biyayyarsu ga Kristi. Kamar mai-gidansu, suna tankware Littafin domin cimma manufarsu. Kamar yadda Shaitan ya yi kokarin jawo ma Allah reni, hakanan ne wakilansa su ke kokarin bata sunan mutanen Allah. Ruhun da ya kashe Kristi ne yana motsa miyagu su hallaka mutanensa. Dukan wannan yana kunshe cikin annabcin nan na farko cewa, “Tsakaninka da machen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyakka da zuriyatta kuma.” Wannan kuwa zai ci baga har karshen lokaci.BJ 504.2
Shaitan ya na tara dukan mayakansa, yana sa dukan karfinsa cikin fadan. Don me ba ya gamuwa da jayayya da yawa? Don me mayakan Kristi ke barci da kuma rashin kulawa? Domin dangantakarsu da Kristi ba shi da yawa; domin ba Ruhunsa a cikinsu. Zunubi ba abin kyama ba ne garesu, kamar yadda Mai-gidansu ke kyamarshi. Ba sa fuskantarsa da kiyayya mai-tsanani yadda Kristi ke yi. Basu gane matukar muguntar zunubi, kuma ba su san yanayin sarkin duhu da ikonsa ba. Gaban da a ke yi da Shaitan da ayukansa ba ta da yawa sabo da akwai jahilci ne game da ikonsa da muguntarsa, da kuma girman yakin da ya ke yi da Kristi da ekklesiyarsa. Jama’a da yawa sun rude a nan. Ba su san cewa magabcinsu babban janar ne, wanda ke mallakar tunanin miyagun malaiku ba, kuma cewa da ingantattun tsare tsare da matakai na gwamninsa ya na yaki da Kristi domin hana ceton rayuka. Cikin Kirista, har ma cikin masu aikin bishara, ba a cika ambaton Shaitan ba, sai dai wani lokaci a kan ambace shi a bagadi. Ba a kula alamun ayukansa da nasarorinsa; ana sakaci da gargadi kan gargadi game da dabarunsa, ana yin biris da kasancewarsa ma.BJ 504.3
Yayin da mutrane su ka jahilci dabrunsa, magabcin wand ba ya barci ya na binsu kowane lokaci. Yana tsoma baki cikin kowane fanni na iyali, a kowane titi na biranenmu, cikin ekklesiyoyinmu, a majalisun kasa, a kotunar, ya na rikitarwa da rudarwa, yana lalatarwa, ko ina ya na tatike rayuka da jikunan maza da mata da yara, ya na raba iyalai, ya na shuka kiyayya da rikici da hargitsi da kisa. Kuma Kirista su na gani kamar Allah ne ya shirya ababan nan, kuma dole su kasance.BJ 505.1
Kullum Shaitan ya na kokarin rinjayar mutanen Allah tawurin rushe shingayen da ke raba tsakaninsu da duniya. An rudi Israila ta da sa’an da suka shiga ma’amala da kafirai. Haka kuma a ke jawo Israila ta zamani ga batawa. “A chikinsu kwa allah na wannan zamani ya makantadda hankulan marasa-bada gaskiya, domin kada hasken bisharar darajar Kristi, wanda shi ke surar Allah, ya waye masu.” Korintiyawa II, 4:4. Dukan wadanda ba tsayayyun masu-bin Kristi ba ne bayin Shaitan ne. Cikin zuciyan da bai tuba ba, akwai son zunubi da son ba da juhhar yin zunubin. Zuciyar da ta sake ta na adawa da zunubi, tana kuma kinshi. Sa’an da Kirista su ka za bi dangantaka da kafirai da marasa ba da gaskiya ga Allah, su na jawo ma kansu jaraba ne. Shaitan ya kan boye kansa ya rufe idanunsu a sace da rudunsa. Ba za su iya gani cewa ma’amalan nan za ta cuce su ba, kuma yayin da su ke kusantuwa da duniya cikin hali da magana da ayuka, suna kara makancewa ne.BJ 505.2
Jituwa da halayyan duniya yakan tubar da ekklesiya ne zuwa duniya; ba ya taba tubar da duniya zuwa wurin Kristi. Sabuwa da zunubi yakan sa a dena ganin muninsa. Wanda ya zabi yin ma’amala da bayin Shaitan, ba da jimawa ba zai dena tsoron mai-gidansu. Sa’an da mu na cikin aikinmu idan aka jaracbe mu, kamar yadda a ka jarabci Daniel a fadar sarki, mu sani cewa Allah zai tsare mu, amma idan mu ka sa kanmu cikin jaraba, za mu fadi, ko a jima ko a dade.BJ 506.1
Magabcin ya cika aiki da nasara tawurin wadanda ba a tsammanin cewa ‘ya’yansa ne. Ana sha’awar masu gwaninta da masana, ana kuma girmama su, sai ka ce gwaninta da sani za su iya magance rashin tsoron Allah, ko su ba mutane ‘yancin samun karbuwa ga Allah. Gwaninta da ilimi kansu baiwa ne na Allah, amma idan aka sa su sun dauki matsayin ibada, idan maimakon jawo mutum kusa da Allah sun janye mutun ne daga Allah, sun zama la’ana ke nan da tarko kuma. Da yaya su na da ra’ayin cewa duk wani abu mai-kaman ladabi ko wayewa daga Krsiti ne. Ba kuskuren da ya fi wannan. Ya kamata kowane Kirista ya mallaki halayyan nan domin za su yi tasiri sosai ga ainihin addini, amma dole a sadakar da su ga Allah in ba haka ba kuwa su ma za su jawo mugunta. Mutane da yawa masu ilimi da ladabi, wadanda, ba za su taba yin rashin kirki ba, ‘ya’yan Shaitan ne. Tasirin halinsu mai-kama da nagarta ya sa sun zama magabta masu hatsarin gaske ga aikin Kristi, fiye da jahhilai marasa hankali. Ta wurin adu’a da naciya, da dagora ga Allah kuma, Solomon ya sami hikima da ta sa duniya ta yi mamaki da sha’awa. Amma sa’anda ya juya daga tushen karfinsa, ya shiga dogara ga kansa, ya fada cikin jaraba. Sa’anan gwanintan da aka ba sarkin nan mafi hikima su ka sa shi ya zama wakilin magabcin mutane.BJ 506.2
Yayin da Shaitan kullum ya ke nema ya makantar da tunaninsu, kada Kirista su taba manta cewa “Kokuwar mu ba da nama da jini ta ke ba, amma da mulkoki, da ikoki, da mahukumtan wannan zamani mai-dufu, da rundunai masu-ruhaniya na mugunta chikin sammai.” Afisawa 6:12. Fadakar ta na zuwa mana a zamaninmu cewa: “Ku yi hankali shimfide, ku yi zaman tsaro; magabcinku Shaitan, kamar zaki mai-ruri, ya na yawo ya na neman wanda za ya chinye.” Bitrus I, 5:8. “Ku yafa dukan makamai na Allah, domin ku sami ikon da za ku yi tsayayya da dabarun Shaitan.” Afisawa 6:11.BJ 507.1
Daga kwanakin Adamu zuwa na mu, zamanin, babban magabcinmu ya na amfani da ikonsa domin danniya da hallakaswa. Yanzu yana shiri domin harinsa na karshe a kan ekklesiya. Dukan masu so su bi Yesu za su fuskanci sabani da magabcin nan. Idan Kirista ya na kara kamanta halin Kristi, ya na kara jawo ma kansa hare-haren Shaitan ke nan. Dukan masu yin aikin Allah, su na kokarin bayana rudun mugun, su na kuma bayana Kristi ga mutane, za su iya hada kai da Bulus inda ya ke shaida batun bauta ma Ubangiji da dukan tawali’u na zuciya, da hawaye mai-yawa da jarabobi kuma.BJ 507.2
Shaitan ya jarabci Kristi da jarabobinsa mai-tsanani, amma an ka da shi ta kowace fuska. An yi yakokin nan a madadin mu ne, nasarorin nan sun sa mu ma za mu iya yin nasara. Krsiti zai ba da karfi ga dukan masu neman karfi. Shaitan ba za ya iya rinjayar wanda bai yarda masu ba. Majarabcin ba shi da iko ya mallaki tunani ko kuma ya tilasta mutum ya yi zunubi. Zai iya yin fitina, amma ba zai iya kazamtarwa ba. Zai iya jawo wahala amma ba zai iya lalatarwa ba. Da shike Kristi Ya yi nasara, ya kamata wannan ya motsa masu binsa su sami karfin hali su yi yaki da gaske sabanin zunubi da Shaitan.BJ 507.3