Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 26—Aikin Canji

    Aikin canji na Assabbat da za a yi a kwanakin karshe an yi annabcinsa cikin annabcin Ishaya cewa: “Haka Ubangiji ya fadi, ku kiyaye sahri’a, ku yi adilchi; gama chetona ya kusa yana zuwa, adilchi na kuma shi bayana. Mai-albarka ne mutum wanda ya ke aika wannan, dan mutum kuma wanda ya lizimshe shi, wanda ya tsare assabbat, ba ya tozartadda ita ba, yana kwa tsare hannunsa ga barin yin mugunta.” “Baki kuma wadanda suka hadu ga Ubangiji, domin su yi masa hidima, su kaunachi sunan Ubangiji, su zama bayinsa, kowane wanda ya tsare assabbat, baya tozartadda ita ba, yana kwa rike da wa’adi na; su dai sai in kawo su wurin dutsena mai-tsarki, in faranta zuchiyassu a chikin gidana na addu’a.” Ishaya 56:1,2; 6,7.BJ 448.1

    Kalmomin nan sun shafi zamanin Kirista. Aya 8 ta ce: “Ubangiji Yahweh wanda yak e tattara warwatsatsu na Isaraila, ya che, Har wa yau, zan tattara masa wadansu, ban da nasa da an rigaya an tattara.” Wannan yana nuna tattarowar al’ummai tawurin bishara. Kuma bisa wadanda ke girmama Assabbat a lokacin an furta albarka. Ta haka bukatar kiyaye doka ta hudu ta zarce lokacin giciye, da tashi, da haurawan Yesu, har zuwa lokacin da bayinsa za su yi wa’azin sakon albishir ga dukan al’umma.BJ 448.2

    Ubangiji ya umurta ta wurin annabi dayan cewa; “Ka damre shaidan ka hatimche shari’a a wurin almajiraina.” Ishaya 8:16. Ana samun hatimin dokar Allah a cikin doka ta hudu ne. Shi ne kadai cikin dokoki goman ya kunshi suna da matsayin Mai-ba da dokar. Ya bayana cewa Allah ne Mahalicin sammai da duniya, ta haka kuma yana nuna cewa ya cancanci ban girma da sujada fiye da kowa. Ban da wannan dokar, ba komi cikin dokoki goma da ke nuna ko tawurin ikon wane ne aka ba da dokar. Sa’anda mulkin paparuma ya canja Assabbat an dauke hatimi daga dokar. Ana kira ga almajiran Yesu su mayar da hatimin ta wurin daukaka Assabbat na doka ta hudu zuwa matsayin da ya dace da shi na abin tunawa na Mahalici da alamar ikonsa kuma.BJ 449.1

    “A komo bisa shari’an da shaidan!” Yayin da koyaswoyi da ra’ayoyi masu sabani da juna suka yawaita, dokar Allah ce mizani madawami shi kadai da za a iya auna dukan ra’ayoyi da koyaswoyi da ita. Annabin ya ce: “Idan ba su fadi bisa ga wannan magana ba, hakika babu wayewan gari a gare sub a.” Aya 20.BJ 449.2

    An kuma ba da umurnin cewa; “Ta da murya, kada ka saukaka; daukaka muryarka kamar kafo, ka shaida ma jama’ata laifinsu, gidan Yakub kuma zunubansu.” Ba muguwar duniyar ba ce, amma wadanda Ubangiji ke kiransu “mutane na” ne za a tsauta masu sabo da laifofinsu. Ya kuma ce; “Lallai kwa suna nemana kowache rana, murnassu ne su san tafarkuna, sai kache al’umma mai-yin adilchi ne, wadda ba ta rabuwa da shari’ar Allahnsu ba.” Ishaya 58:1,2. A nan ana maganan wani sashin mutane ne masu ganin kansu kamar suna da adalci, suna kuma nuna marmarin hidimar Allah sosai; amma tsawa mai-tsanani na Mai-binciken zukata ya bayana cewa suna tattake umurnin Allah.BJ 449.3

    Saboda haka annabin ya bayana dokar da aka rabu da ita; ya ce: “Za ka sake ginin gindaye na sararaki da yawa; za a che da kai mai-gyaran kufai, mai-mayasda tafarkun da za a zamna a chiki. Idan ka kawas da kafa ga barin aikin garalin kanka a ranar assabbat, rana ta mai-tsarki, ka kuma che da assabbat, abin marmari ne; mai-tsarki na Ubangiji, abin girmamawa; idan kwa ka girmama ta, ba ka aika sha’anin kanka ba, ba ka bidi naka nishadi ba, ba ka kwa fadi zanchen kanka ba; sa’an nan za ka faranta zuchiyarka chikin Ubangiji.” Ishaya 58:12-14. Wannan annabcin yana aiki a zamaninmu. An ketare dokar Allah sa’anda mulkin Rum ta canja Assabbat ne, amma lokaci ya yi da za a mayasda wannan hutun Ubangijin. Za a gyara kufai din a kuma sake gina gindaye na sararakin.BJ 449.4

    Da shike Allah Ya tsarkake Assabbat ta wurin hutawarsa da albarkasa, Adamu ya kiyaye Assabbat din bayan an kore shi daga gidansa na farinciki. Ubani daga Habila har mai-tsarki Nuhu, zuwa Ibrahim, zuwa Yakubu sun kiyaye ta. Sa’an da zababun mutanen ke bauta a Masar, da yawa a tsakiyar rinjayen bautar gumaka, sun manta dokar Allah; amma sa’anda Ubangiji Ya kubutar da Israila, Ya bayana dokarsa da martaba mai-ban tsoro ga taron jama’ar, domin su san nufinsa, su kuma ji tsoronsa, su yi biyayya gare shi har abada.BJ 450.1

    Daga wancan ranan har yau an kiyaye sanin dokar Allah a duniya, kuma ana kiyaye dokana hudu. Ko da shike “mutumin zunubi” ya tatteka rana mai-tsarki na Allah, duk da haka har a lokacin daukakarsa akwai amintattu a boye da suka girmama ranar. Tun lokacin Canjin nan kowace sara akwai masu kiyaye ta. Kullum akwai masu shaida dawamar dokar Allah da takalifin kiyayae Assabat na halitta, sau da yawa ma ko cikin zalunci da reni.BJ 450.2

    Gaskiyan nan, yadda ake gabatardasu cikin Ruya 14 game da bisara ta har abada za su bambanta ekkesiyar Kristi a lokacin bayyanuwarsa. Gama sakamakon sakon nan mai sassa uku za a sanar da cewa: “Ga su wadanda ke kiyaye dikokin Allah, da imanin Yesu.” Kuma sakon nan ne na karshe da za a bayar kafin zuwan Ubangiji. Da zaran an yi shelarsa, annabin ya ga Dan mutum yana zuwa cikin daraja domin ya yi girbin duniya.BJ 450.3

    Wadanda suka karbi haske game da haikalin da rashin sakewar dokar Allah sun cika da farinciki da al’ajibi yayin da suka ga ban sha’awar tsarin gaskiya da ta bayyana garesu. Sun so a ba dukan Kirista hasken nan da suka samu. Suka kuma ba da gaskiya cewa za a karbi hasken da farinciki. Amma koyaswoyin gaskiya da za su sa mutane sabani da duniya ba su karbu ga mutane da yawa masu cewa su masu bin Kristi ne ba. Biyayya ga doka ta hudu ta bukaci hadaya wadda da yawa ba su so ba.BJ 451.1

    Sa’anda aka bayana batun Assabbat, mutane da yawa suka ce: “Mu Lahadi mu ke kiyayewa tun farko, iyayenmu sun kiyaye shi, kuma nagargaru da yawa masu ibada har sun mutu suna kiyaye shi. Idan daidai suka yi, mu ma daidai muke yi. Kiyayewar sabon Assabbat din nan zai sa mu rashin jituwa da duniya, kuma ba za mu yi tasiri bisan su ba. Mene ne ‘yar karamar kungiyar masu kiyaye rana ta bakwai za su samu sabanin dukan duniya da ke kiyaye Lahadi?” Ta wurin wannan irin maganar ne Yahudawa suka so su ba da hujjar kin Kristi da su ka yi. Allah ya karbi ubaninsu da suka mika hadayu gareshi, don me su yaran ba za su sami ceto ta hanya dayan ba? Haka ma a zamanin Luther ‘yan tsarin paparuma suka ce Kirista na kwarai sun mutu cikin imanin Katolika, sabo da haka wannan addinin ya isa ceto. Irin tunanin nan yakan hana ci gaban imani ko ibada.BJ 451.2

    Da yawa suka koyar da cewa kiyaye Lahadi dadaddiyar koyaswa ce, kuma ekklesiya ne na daruruwan shekaru. Amma sabanin wannan, an nuna masu cewa Assabbat ya fi dadewa da kuma yaduwa, tun kafuwar duniya kanta ne ma, kuma yana da hatimin malaiku da na Allah ma. Sa’anda aka kafa harsashen duniya, sa’anda tauraren safiya suka raira tare, dukan ‘ya’yan Allah kuma suka ta da murya don murna, lokacin ne aka kafa harsashen Assabbat. Ayuba 38:6,7; Farawa 2:1-3. Wajibi ne Assabbat ya bukaci bangirman mu; ba mutum ne ya kafa shi ba, kuma bai dangana ga al’adun mutane ba; Mai-zamanin da ne ya kafa shi, maganarsa ta har abada kuma ta umurta shi.BJ 451.3

    Sa’anda ana jawo hankulan mutane ga batun sabontawar Assabbat, shahararrun ma’aikatan bishara suka kangare ma maganar Allah, suna ba ta fasarar da za ta hana binciken batun. Wadanda kuma ba su bincika ma kansu Littafin ba suka gamsu da ra’ayoyin da sun je daidai da abin da su ke so. Ta wurin musu da al’adun Ubanni, da ikon ekklesiya, da yawa suka so su hambarar da gaskiyar. Masu goyon bayan gaskiyar suka koma ga Littafin domin kare sahihancin doka ta hudun. Talakawa, tawurin maganar gaskiya kadai, suka yi nasara bisa hare haren masana wadanda, cikin mamaki da fushi, suka ga cewa duk da iya maganansu da wayon su, ba su iya yin nasara bisa magana mai-sauki kai tsaye na mutanen nan da suka san Littafin sosai ba.BJ 452.1

    Da shike ba su da goyon bayan Littafin, da yawa suka ce: “Don me manyan mutanen mu ba su gane batun Assabbat din nan ba? Ai kalilan ne sun gaskata wannan batun. Ba shi yiwuwa a ce ku ke da gaskiya sa’annan dukan masanan duniyan nan suna kuskure.” Sun manta cewa irin maganar da aka yi ma Yesu da manzaninsa ke nan.BJ 452.2

    Don wofinta irin maganan nan, an bukaci anfani da koyaswoyin Littafin ne da tarihin yadda Allah yana aiki tawurin wadanda ke jin maganarsa suna kuma biyayya da ita ne, wadanda in ta kama za su fadi maganan da ba a so a ji, wadanda ba sa tsoron tsawata zunuban da ake yayinsu. Dalilin da ya sa bai cika zaben masana su shugabanci canje canje ba shi ne cewa su kan dogara ga koyaswoyinsu da ra’ayoyinsu da tsare-tsaren ekklesiyoyinsu ne, su kuma ji kamar ba sa bukatar Allah ya koya masu. Wadanda ke da alaka da Tushen hikima, kai tsaye ne kadai za su iya gane ko kuma su bayana Littafin. Wani lokaci akan kira masu kankantar sani na makaranta su bayana gaskiya, ba don basu da ilimi ba, amma domin ba su cika dogara ga iyawar kansu ta yadda za su ki Allah ya koya masu ba. Su kan koya a makarantar Kristi, tawali’unsu da biyayyar su kuma sukan sa su zama manya. Ta wurin ba su sanin gaskiyar, Allah yakan ba su girman da ya fi na duniya.BJ 452.3

    Yawancin Adventist da sun ki gaskiya game da haikali da dokar Allah, da yawa kuma sun rabu da bangaskiyarsu game da batun zuwan Kristi, suka rungumi ra’ayoyi masu sabani da juna game da annabce-annacben da suka shafi aikin. Wadansu sun shiga kuskuren tsai da takamammen ranar zuwan Kristi a kai a kai. Ya kamata da hasken da ke haskakawa game da batun haikalin a lokacin ya nuna masu cewa babu lokacin annabci da ya kai har lokacin zuwan Yesu na biyu; cewa ba a yi annabcin daidai lokacin zuwan ba. Amma da suka juya daga hasken, sai su ka yi ta tsaida lokaci bayan lokaci da Ubangiji zai zo, kuma sun rika gamuwa da yankan buri.BJ 453.1

    Sa’anda ekklesiyar Tassalunikawa ta sami ra’ayiyoyin da ba su dace ba game da zuwan Kristi, manzo Bulus ya shawarce su su gwada begensu da maganar Allah. Ya tuna masu da annabce annabcen da ke bayana al’amuran da za su faru kafin Kristi ya zo ya kuma nuna cewa ba su da hujjar yin tsammanin cewa zai zo a zamanin su. “Kada ku bari kowane mutum shi rude ku da ko kaka.”( Tasalunikawa II, 2:3). Kalmominsa na fadaka ke nan. Idan suka yarda da zance-zance da littafi bai amince da su kam, za su kai ga rudun marasa ba da gaskiya, za su kuwa shiga hadarin katsewar hanzari su kuma jarabtu ga yin shakkar gaskiyan da suka wajibta domin cetonsu. Gargadin manzon zuwa ga Tassalunikawan ya kunshi wani muhimmin darasi domin wadanda ke raye a kwanakin karshe. Adventist da yawa sun dauka cewa in ba sun kafa bangaskiyarsu ga wani takamammen lokacin da Ubangiji zai zo ba, ba za su iya yin himma da kwazo cikin aikin shiryawa ba. Amma yayin da begensu yana tashi akai akai yana kuma yankewa, bangaskiyarsu tana gigicewa ta yadda yana zama masu da wahala su yi sha’awar muhimman gaskiya na annabci.BJ 453.2

    Allah ne Ya sa aka koyas da batun takamammen lokacin hukumci sa’anda aka ba da sakon malaika na farin. Lissafin lokutan annabcin da suka shafi sakon, wanda ya aza karshen kwana 2300 a kaka na 1844, babu kuskure a cikinsa. Kokarin da aka dinga yi don samun sabobin ranakun farawa da na karewan lokutan annabcin, da kurakuran dalilan da ake bayarwa don amincewa da wadannan ranakun suna janye tunanin mutane daga gaskiya ta yanzu, su kuma sa a rena duk wani kokari na bayyana annabce annabce. Manufofin Shaitan su kan cika idan ana yawan aza takamammen lokacin zuwan Kristi na biyu ana kuma koya ma mutane hakanan. Bayan lokacin ya wuce, yakan sa a rika rena masu wannan koyaswar ana yi masu ba’a kuma, ta hakanan kuma ya sa a rena babban aikin 1843 da 1844 din nan game da zuwan Kristi na biyu. Masu nacewa da kuskuren nan a karshe za su aza wani lokaci can gaba da nisa da a ganinsu Kristi za ya zo. Ta hakanan za su yi sake, za su rudi mutane da yawa kuma har lokaci ya kure.BJ 454.1

    Tarihin Israila ta da, kwatanci ne na abinda ya faru da Adventist. Allah ya shugabanci mutanensa cikin aikin nan game da zuwan Yesu na biyu, yadda ya shugabanci ‘ya’yan Israila daga Masar. A babban yankan burin nan an gwada bangaskiyarsu yadda aka gwada na Ibraniyawa a Jan Teku. In da sun ci gaba da amincewa da hannun da Ya dinga bishe su cikin rayuwarsu can baya, da sun ga ceton Allah. Da dukan wadanda suka yi aiki tare a 1844 sun karbi sakon malaika na uku, suka kuma yi shelarsa cikin ikon Ruhu Mai-tsarki, da Ubangiji Ya yi aiki sosai cikin kokarinsu. Da ambaliyar haske ta mamaye duniya. Da tun shekaru da suka gabata mazamnan duniya sun sami gargadin, an kamala aikin karshen, Kristi kuma da Ya dawo don fansar mutanensa.BJ 454.2

    Ba nufin Allah ne Israila suka yi ta yawo a jeji har shekara arba’in ba; ya so ya jagorance su kai tsaye ne har kasar Kan’ana, ya kafa su a wurin, jama’a mai-tsarki, mai-farinciki kuma. Amma ba su iya shiga ba saboda rashin bangaskiya; Ibraniyawa 3:19. Saboda koma-bayansu da riddarsu, sun hallaka a hamadar, aka kuma ta da wadansu suka shiga kusar Alkawalin. Hakanan kuma, ba nufin Allah ne a jinkirta zuwan Kristi da yawa haka, mutanensa kuma su kasance shekaru da yawa hakanan a wannan duniya ta zunubi da bakinciki ba. Amma rashin bangaskiya ya raba su da Allah. Sa’anda suka ki yin aikin da ya ba su, sai aka ta da wadansu da su ka yi shelar sakon. Cikin jin kai ga duniya, Yesu yana jinkirta zuwansa, domin masu zunubi su sami zarafin jin gargadin, su kuma sami mafaka cikinsa kafin a zubo da fushin Allah.BJ 455.1

    Yanzu, kamar a sararraki na da, bayana gaskiyan da ke sokar zunubai da kurakuran zamanin yakan jawo jayayya. “Gama kowanne wanda ya ke aika mugunta kin haske ya ke yi, kuma ba shi zuwa wurin haske, domin kada ayukansa su tonu.” Yohanna 3:20. Sa’anda mutane sun ga cewa ba za su iya tabbatar da ra’ayinsu daga Littafin ba, da yawa sukan nace da rikon ra’ayin dai ko ta halin kaka, da ruhun mugunta kuma su kan dinga zargin halaye da manufofin wadanda ke kare gaskiya. A dukan sararaki haka abin yake. An ce ma Iliya wai shi ne mai wahal da Israila, an kira Irmiya mai-cin amana, aka ce da Bulus mai-kazantar da haikalin. Daga zamanin can zuwa wannan, wadanda ke biyayya ga gaskiya akan zarge su cewa su masu cin amana ne, masu-ridda, ko masu kawo tsatsaguwa. Jama’a da yawa marasa ba da gaskiya ga maganar annabci tabbataciya nan da nan za su yarda da zargin da za a yi ma wadanda ke kwaban zunuban da ake yayinsu. Wannan ruhun zai dinga karuwa. Littafin kuma yana koyarwa a sarari cewa lokaci yana zuwa da dokokin kasa za su saba ma dokar Allah ta yadda dukan wanda zai yi biyayya ga dukan umurnin Allah dole ya shirya fuskantar zargi da horo cewa, shi mai-aikata mugunta ne.BJ 455.2

    Saboda haka, me ya kamata dan sakon gaskiya ya yi? Zai ce ne bai kamata a bayana gaskiya ba, da shike sau da yawa mutane suna kin ta? Babu; ba shi da dalilin barin yin shelar maganar Allah wai don tana jawo jayayya. An rubuta furcin bangaskyar tsarkaka domin anfanin sararrakin baya ne. Rayayyun masu kwatanta tsarki da aminci suna karfafa wadanda yanzu ake kira su tsaya a matsayin shaidun Allah. Sun karbi alheri da gaskiya, ba don kansu ba kadai, amma domin, ta wurinsu, sanin Allah ya haskaka duniya. Ko Allah Ya ba da haske ga bayinsa na wannan sarar? Sai su hakaka shi ga duniya.BJ 456.1

    Da can Ubangiji Ya ce ma wani mai-magana a cikin sunansa. “Amma gidan Israila ba za su kasa kunnne gare ka ba; gama ba za su kasa kunne gareni ba.” Duk da haka Ya ce: “Za ka fada masu maganata, ko su a ji, ko su ki ji.” Ezekiel 3:7; 2:7. Ga bawan Allah a wannan zamani ana umurta cewa: “Ka ta da murya kamar kaho, ka nuna ma mutanen nan laifinsu, gidan Yakub kuma zunubansu.” Annabin Israilan nan da kalmar Allah ta ce masa: “Hakanan kai fa dan mutum, na sanya ka mai-tsaro ga gidan Israila; domin wannan ka ji Magana ga bakina, ka yi masu fadaka daga gareni. Kadan na che ma mugun mutum, Ya kai mugun mutum, lallai za ka mutu, kai kwa ba ka yi magana domin ka fadakadda mugun shi bar hanyassa; wannan mugun mutum za ya mutu domin laifinsa, amma zan bidi jininsa gareka. Amma idan ka fadakadda mugun mutum domin shi juyo ga barin hanyassa, shi kwa bai juya ga barin hanyassa ba, za ya mutu sabada laifinsa, amma ka chechi ranka.” Ezekiel 33:7-9.BJ 456.2

    Babban matsala ga karban gaskiya da shelarta it ace cewa ta kunshi rashin jin dadi da zargi. Amma wannan ba ya hana ainihin masu bin Kristi na gaskiya. Ba sa jira wai sai gaskiya ta karbu ga mutane. Sa’anda sun gane takalifin da ya rataya a wuyansu, sukan karbi giciyen, tare da manzo Bulus suna dauka cewa “kunchinmu mai-sauki, wanda ke na lokachi kadan, yana aika dominmu nauyin daraja madawami gaba gaba kwarai,” tare da wani na da suna “mai da zargi domin Kristi wadata ne mafi-girma bisa ga dukiyar Masar.” Korinthiyawa II, 4:17; Ibraniyawa 11:26.BJ 457.1

    Ko da menene suke fadi, masu son duniya a zuchiyarsu ne su ke bin sauki maimakon kaida da al’amuran addini. Ya kamata mu zabi abin da ke daidai domin shi daidai ne, mu bar abin da zai biyo baya a hannun Allah. Ga masu aminci da bangaskiya da karfin zuciya, dole duniya ta gode masu saboda manyan canje canjen da suka kawo. Wadannan mutanen ne za su ci gaba da aikin canji.BJ 457.2

    In ji Ubangiji: “Ku kasa kunne gareni, ku masanan adilchi, mutane wadanda shari’a ta tana chikin zuchiyarku; kada ku ji tsoron zargin mutane, kada ku yi fargaba domin zaga zagensu kuma. Gama asu za su chinye su kamar riga, tsutsa kuma za ta chi su kamar ulu; amma adkilchina za ya dawama har abada, chetona kuma har dukan tsararaki.” Ishaya 51:7,8.BJ 457.3

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents