Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 1—Hallakawar Urushalima

    “Yace, Da ma kin sani a chikin wannan rana, har ke ma, abin da ya tabbata ga salama! amma yanzu a boye yake a idanun ki. Gama kwanaki za su abko maki, inda makiyan ki za su gina maki ganuwa, su sa ki a tsaka, su tsare ki daga kowane sasa, su fyade ki a kasa, da yayan ki a chikin ki, ba za su bar ko dutse daya a bisa wani a chikin ki ba; da shi ke ba ki lura da kwanakin ziyartanki ba.” Luka 19:4 -44.BJ 17.1

    Daga kan dutsen Zaitun, Yesu ya dubi Urshalima. Bai ga komi ba sai abin ban sha’awa da kuma salama. Lokacin Paska ne, kuma yayan Yukubu daga dukan kasashe sun tattaru a wannan wuri don wannan babban biki na al’umma baki daya. Cikin lambuna da gonakin anab, da kuma filaye masu ni’ima cike da bukokin maniyyata, akwai tuddai da kyawawan gidajen sarauta, da kuma manyan ganuwoyin cibiyar Israila. Sai ka ce diyar Sihiyona, cikin alfarma tana cewa ne, “Ni gimbiya ce, kuma ba zan ga bakin ciki ba;” da ban-sha’awan nan nata, tana kuma gani kamar Allah yana gayon bayan ta, kamar yadda a zamanun baya mawakan sarki suka raira cewa, “Mai-kyaun tsaye ne, abin murna ga duniya duka, Dutse Sihiyona kenan. “Birnin Madaukakin Sarki.” Zabura 48:2. A fili kuma ga kyawawan gineginen haikalin. Hasken rana ya haskaka dukan gine ginen nan, da kofar zinariyan da hasumiyar sa da kuma benen sa. A lokacin, haikalin nan abin fahariya ne ga al’ummar Yahudawa. Kowane dan kasa in ya bude shi yakan cika da murna da sha’awa! Amma wadansu ababa dabam ne suka cika tunanin Yesu a wannan lokaci. “Sa’anda ya kusa, ya hangi birni, ya yi kuka a kanta.” Luka 19:41. Cikin farin cikin da ya mamaye ko ina sabo da shigowar Sa Urshalima, yayin da ake nuna ganyen dabino, ana raira hosanna, dubbai kuma suna shelar cewa Yesu ne sarki, Mai-fansar duniya ya cika da bakincikin na ban mamaki, faraf daya. Shi Dan Allah, Dan Akawali na Israila, wanda ikon sa ya yi nasara bisa mutuwa, ya kuwa ta da matattu daga kabarbarun su, sai ga Shi ya cika da hawaye na azabar bakinciki sosai.BJ 17.2

    Hawayen Sa ba don kan Sa ba ne ko da shike ya sani sarai abin da zai faru da shi. A gaban sa yana ganin Gathsamani, inda za’a azabtar da Shi. Ga kuma kofar tumaki ta inda aka yi daruruwan shekaru ana shigowa da tumakin hadaya, ta inda kuma za a bi da Shi “kamar dan rago da aka kai wurin yanka” Ishaya 53:7. Kusa da wurin kuma akwai kalfari wuirn giciyewan. Dole mumunan duhu ya rufe hanyan da Yesu zai bi zuwa inda Ya mika ran Sa hadaya sabo da zunubi. Duk da haka ba tunanin wadannan ababa ne ya sa Shi bakinciki a wannan lokaci da ake murna ba. Ya yi kuka sabo da dubban mutanen Urshalima ne. Domin makanta da rashin tuban wadanda ya zo domin ya albarkace su, ya kuma cece su ne.BJ 18.1

    Tarihin shekaru fiye da dubu na alherin Allah da kulawan sa da nuna ma zababbun mutanen sa ya bayana ga idanun Yesu. Ya ga Dutsen Moriah inda aka daure dan alkawali mai-biyaya a a kan bagadin hadaya, alamar hadayar Dan Allah. Farawa 22:9. Can aka tabbatar ma uban masu bangaskiya alkawalin nan mai albarka, alkawalin zuwan Masiya. Farawa 22:16-18. Can ne kuma wutar hadaya da ke hawa zuwa sama daga wurin masussukar Ornan ta kawar da takobin malakan nan mai-hallakaswa. Labarbaru 1, 21 — alamar hadaya da tsakancin Mai-Ceto a madadin mutane masu laifi. Allah ya girmama Urushalima bisa dukan duniya. Ubangiji “ya zabi Sihiyona”, “ya yi marmarinta domin mazamninsa.” Zabura 132:13. Can fa tsarkakan annabawa suka rika furta sakonin su na kashedi. Can kuma priestoci suka rika mika hadayu, addu’o’in masu sujada kuma suka rika hawa zuwa gaban Allah. Can aka rika mika jinin yankakkun raguna, alamar Dan rago na Allah. Can ne Yahweh ya bayana kasancewar Sa a cikin girgijen daraja bisa dakalin jin kai. Can ne kuma tsanin nan wanda kansa ya kai har sama, ya kafu a kasa (Farawa 28:12; Yohanna 1:51) — tsanin nan da malaikun Allah suke hawa suna kuma sauka a kan sa, wanda ya bude ma duniya hanyar wuri mafi-sarki. Da al’ummar Israila ta yi ma Allah aminci, da Urushalima ta dawama har abada, zababbiya ta Allah. Irmiya 17:21-25. Amma tarihin kaunatattun nan, na ja da baya ne da tawaye. Sun ki alherin Allah, suka kuma wofinta alherai da zarafi da aka ba su.BJ 18.2

    Ko da shike Israila “suka yi ma manzanin Allah ba’a, suka rena maganatasa, suka yi ma annabawansa zunda” (Labarbaru II 36:16), duk da haka ya bayana kan Sa gare su, “Ubangiji, Allah ne chike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jin kai da gaskiya”. (Fitowa 34:6); duk da yawan bijirewar su, cikin jin kan Sa ya ci gaba da rokon su. Cikie da kaunar da ta fi ta uba zuwa ga dan sa, Allah ” ya aike gare su ta wurin manzaninsa, yana tashi da wuri yana aikassu domin yana jin juyayin mutanensa, da mazamninsa kuma” Labarbaru II, 36:15. Sa’anda lallashi da tsautawa da Allah ya aika masu da kyauta mafi-kyau da sama ke da shi, watau ya zubo masu dukan sama cikin Kyautan nan.BJ 19.1

    An aiko Dan Allah kan Sa domin shi roki kangararen birnin nan. Kristi ne ya fito da Israila, inabi mai-kyau da Masar. Zab. 8:8. Da hannun Sa ya kori kafirai daga cikin Israilan. Ya dasa ta a kan tudu mai-kyau, ya kuma kange ta. Aka aiki bayin Sa su ciyar da ita. Ya nome ta “a chikin wani tudu mai-albarka kwarai.” Mai lura masa da ita ya rigaya ya kewaye ta da shimge. An rigaya an aiki ma’aikata suka tsintsinche duwatsunta. Ya ce: “Me ya rage a yi ma ganata da ban yi a chikinta ba?” Ishaya 5:1-4. Ko da shike, sa’anda ya zata za ta haifi inabi, sai ta fito da inabi mara anfani, duk da haka, ya zo wurin gonar inabin nasa da begen samun ‘ya’ya, ko za a cece ta daga hallaka. Ya yi tono kewaye da inabin; ya gyara ressan ta. Bai gaji da kokarinsa na ceton inabin sa da ya dasa ba.BJ 19.2

    Ubangijin haske da daraja ya yi shekara uku yana ma’amala da mutanene Sa. Ya rika ayukan nagarta, yana warkar da dukan masu-aljannu, yana ta’anzantar da masu-bacin zuciya, yana kuma kubutar da dauraru, yana mayar da gani ga makafi, yana sa guragu su yi tafiya, kurame kuma su ji. Ya ta da matattu, yana kuma shelar bishara ga matalauta. Ayukan 10:38; Luka 4:18, Matta 11:5. Ya kira dukan mutane cewa: “ Ku zo gare ni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya, ni kuwa in ba ku hutawa” Matta 11:28BJ 20.1

    Ko da shike an rama masa adalcin Sa da mugunta, kaunar Sa kuma da kiyaya (Zabura 109:5), ya ci gaba da aikin Sa na jin kai. Bai taba koran mai-neman taimako ba. Ba shi da gidan kan Sa, ga reni, ga talauci, amma ya rika biyan bukatun mutane, yana rage wahalolin su, yana kuma rokon su su karbi kyautar rai. Cikin kauna ya rika maimaita ayukan Sa na jinkai da kangararu suka ki karba. Amma Israila ta ki babban abokin ta, wanda Shi ne kadai Mai-taimakon ta. Ta ki jin rokon Sa, ta ki karban kaunar sa, ta kuma ki jin shawarar sa da kashedin Sa.BJ 20.2

    Sa’ar bege da gafara ta kusan wucewa, kokon fushin Allah ya kusan cika. Hatsarin da ya rika taruwa a zamanin ridda da tawaye yana gaf da fashewa kan masu laifi; ga shi kuma sun rigaya sun ki wanda Shi kadai ne zai iya ceton su, suka wulakanta Shi, kuma ba da jimawa ba ma za a giciye Shi. Wannan giciyewan Kristi ne kuwa zai kawo karshen mastayin Israila na zababbiyar al’ummar da Allah Ya yi mata albarka. Mutuwar mutum daya ma kawai abin bakinciki ne, amma yayin da Kristi Ya dubi Urshalima, Ya ga hallakar birni guda ne, al’umma guda wadda da ita ce zababbiya ta Allah.BJ 20.3

    Annabawa sun rika kuka sabo da riddar Israila da munanan wahalolin da suka biyo baya. Irmiya ya so da idanun sa mabulbulolin hawaye ne, da ya yi ta kuka dare da rana, domin mutanen sa da aka karkashe, da garken Ubangiji kuma da aka tafi da su kamammu. Irmiya 9:1; 13:17. Yesu fa Ya fi dukan su bakinciki, da shike yana hangan zamanai can gaba. Ya hangi malaika mai-hallakan nan da takobin da zai hallaka birnin da Yahweh Ya dade yana kasancewa ciki. Daga gefen Dutsen Zaitun, daidai wurin da daga baya Titus da dakarun sa suka kama, Yesu ya hangi wurare masu tsarki, da hawaye a idanunsa kuwa, ya ga ganuwan da magabta za su kewaye. Ya “Ji surutun mayaka suna shirin yaki. Ya ji muryoyin uwaye da yara suna kukan neman abinci a cikin birnin da magabta suka kewaye. Ya hangi gidan nan mai-tsarki, da gidajenta na sarauta suna konewa, suka kuma zama kango kawai.BJ 21.1

    Sa’anda ya dubi sararaki nan gaba, ya hangi mutanen alkawali a warwatse cikin kowace kasa. Cikin horon da zai abko ma ‘ya’yanta, Ya hangi kashin farko na azaban da za ta sha daga kokon fushin, lokacin shari’a ta karshe. Sai Ya bayana tausayin Sa da kaunar Sa cewa: “Ya Urshalima, Urshalima, wadda ki ke kisan annabawa, kina jejjefe wadanda an aiko gare ki! So nawa ina so in tattara ‘ya’yanki, kamar yadda kaza takan tattara yan tsakinta kalkashin fikafikanta, amma, baku yarda ba!” da dai ke zababbiyar al’umman nan kin san lokacin wahalarki, da ababan da suka shafi salamar ki! Na dakatar da malaikan adalchi, na gayyace ki zuwa ga tuba, amma a banza. Ba barori da wakilai da annabawa ne kadai kika ki ba, amma Mai-tsarki na Israila, Mai-fansarki ne kika ki. Idan an hallaka ki kuwa laifin ki ne. amma ba ku yarda ku zo wurin na ba, domin ku sami rai.” Matta 23:37; Yohanna 5:40BJ 21.2

    A kan Urshalima Kristi ya ga alamar duniya kangarariya cikin rashin tawaye da rashin gaskatawa; da kuma hanzari zuwa ga saduwa da horon Allah. Kaito da wahalolin fadadiyar al’umman nan ne suka tilasta Shi furta wannan kuka mai-zafi. Ya ga zunubi a bayane cikin wahala da hawaye da jinin mutane; zuciyar Sa ta motsu da tausayi. Ya yi marmarin dauke masu wannan azabar. Amma ko hannun Sa ma ba zai kawar da azabar dan Adam ba. Kalilan ne masu bidar taimakon Sa. A shirye yake Ya mutu ma domin kawo masu ceto, amma kalilan ne masu zuwa wurin Sa domin su sami rai.BJ 22.1

    Sai ga Sarkin sama yana hawaye! Dan Allah Madaukaki Ya cika da bakinciki! Dukan sama ta cika da mamaki. Wannan abu yana bayana mana matukar munin zunibi; yana nuna yadda yake da wahala ainun, har ga Mai-cikaken iko ma, Ya ceci mai-laifi daga sakamakon ketare dokar Allah. Yesu Ya hangi cewa a zamanin karshe, duniya za ta shiga irin rudun nan da ya jawo hallakawar Urshalima. Babban zunubin Yahudawa shi ne kin Kristi da suka yi; kin dokar Allah wadda ita ce tushen gwamnatin Sa a sama da duniya, shi ne zai zama babban zunubin Kirista. Za a wofinta dokokin Allah. Miliyoyin masu zunubi da bautan Shaitan da ke fuskantar mutuwa ta biyu za su ki jin kalmomin gaskiya na zamanin su. Mumunar makanta ke nan.BJ 22.2

    Kwana biyu kafin idin Paska, bayan Kristi Ya yi fitar Sa ta karshe daga haikalin, bayan Ya tsauta ma riyar shugabanin Yahudawa, Ya sake komawa Dutsen Zaitun tare da almajiran Sa, ya kuma zauna da su a gefen dutsen da ke fuskantar birnin. Sai Ya sake duban ganuwar birnin, da hasumiyoyin sa, da manyan gine ginen sa. Ya sake ganin haikalin, gwanin kyau, abin ban sha’awa.BJ 23.1

    Shekaru dubu kafin wannan lokacin, mai-zabura ya bayana alherin da Allah Ya yi ma Israila inda Ya mai da haikalin ta mazamnin Sa. Ya ce, “A chikin Salem mazamninsa yake, wurin zamansa kuma chikin Sihiyona.” Ya zabi kabilar Yahuda Dutsen Sihiyona wanda yake kamna. Ya gina tsatsarkan wurinsa kamar tsawawa.” Zabura 76:2; 78:68,69. An gina haikali na fari a zamanin da Israila ta fi ci gaba ne. Sarki Dawuda ya tara dukiya a yalwace don wannan ginin, tsare-tsaren ginin kuma Allah ne ya bayar. Labarbaru I, 28:12,19. Solomon, mafi-hikima cikin sarakunan Israila, shi ne ya yi ginin. Duk duniya ba a taba ganin wani gini kamar haikalin nan ba. Duk da haka Ubangiji ya sanar tawurin anabi Haggai game da haikali na biyu din, cewa: “Daukaka ta baya ta wannan gida za ta fi ta farin.” “Zan raurawadda dukan dangogi; kuma muradin dukan dangogi za ya zo; zan chika wannan gida da daukaka, in ji Ubangiji mai-runduna.” Haggai 2:9,7.BJ 23.2

    Bayan da Nebuchsadnezzar ya rushe haikalin, mutanen da suka dawo kangon kasarsu daga bauta sun sake gina shi, shekara dari biyar kafin haifuwar Kristi. Cikin su akwai tsofofi da suka ga darajar haikalin Solomon na da, suka kuma yi kuka sa’anda aka kafa tushen sabon ginin, cewa ba zai yi kyau kaman na farin ba. Annabin ya bayana yadda suka ji inda ya ce: “Wa ya rage daga chikinku wanda ya ga gidan nan a chikin daraja ta da? Yaya kuke ganinsa yanzu kuma? A idanunku ba ya zama kamar babu ba?” Haggai 2:3, Ezra 3:12. Sa’an nan ne aka yi alkawalin cewa darajar sabon haikalin nan za ta fi ta farkon.BJ 23.3

    Amma haikali na biyu din bai kai na farkon kyau ba; kuma ba a tsarkake shi tawurin alamun kasancewar Allah a cikin kaman na farkon ba. Ba a nuna wani ikon Allah a bukin budewarsa ba. Ba’a ga girgijen daraja ya cika sabon haikalin ba. Wuta bai rika saukowa daga sama yana kona hadaya da ka bisa bagadinsa ba. Shekina bai sake kasancewa tsakanin cherubim na wuri mafi-tsarkin ba, sanduki da kujerar jin kai da tebur na shaida basu kasance cikinsa ba. Murya bai rika saukowa daga sama yana shaida ma priest nufin Allah ba.BJ 24.1

    Yahudawa sun kwashe daruruwan shekaru suna kokarin nunata yadda aka cika alkawalin da Allah Ya yi tawurin Haggai, a banza kuwa; amma girman kai da rashin bangaskiya sun rufe tunanin su daga ainihin ma’anar kalmomi annabin. Ba a girmama haikali na biyu din da girgijen darajar Allah ba, sai dai da zahirin kasancewar wanda cikin Sa akwai cikar Allahntaka cikin jiki — wanda Shi kansa Allah ne cikin jiki. “Marmarin dukan al’ummai” ne ya zo haikalinsa sa’anda Mutumin nan na Nazareth ya rika koyarwa da warkarwa a wuri mai-tsarkin. Ta wurin kasancewar Kristi ne kadai haikali na biyu din ya fi na farkon daraja. Amma Israila ta ki Kyautan nan na sama. Sa’anda Mai-koyarwan nan ya fita kofar zinariya ta haikalin, daraja ta rabu da haikalin har abada. Maganar Mai-ceto ta cika cewa: Ga shi, an bar maku gidan ku kango.” Matta 23:38.BJ 24.2

    Almajiran sun cika da mamakin annabcin Kristi cewa za a rushe haikalin, suka so su kara fahintar maganarsa. An yi sama da shekara arba’in ana anfani da dukiya da kwarewa na fasahar gine gine domin a kara ma haikalin kyau. Sarki Hiridus ya jibga arzikin Rum da wadatar Yahudawa a wurin, har sarkin dukan duniya ma ya arzunta haikalin da kyauta iri iri. Aka yi anfani da manyan duwatsu masu daraja a ginin, har ma almajiran suka jawo hankalin Yesu akan su cewa: “Ka duba, wadanne irin duwatsu kenan, wadanne irin ginegine kuma kenan!” Markus 13:1.BJ 24.3

    Yesu ya amsa wannan da cewa: “Hakika, ina che maku, Ba za a rage wani dutse bisa wani ba, da baza a rushe ba.” Matta 24:2BJ 25.1

    Almajiran sun danganta rushewar Urshalima da zuwan Kristi cikin daraja ta mutuntaka domin Ya karbi kursiyin mulkin duniya, ya kuma hori Yahudawa, ya kuma kubutar da al’ummar daga kangin bautar Romawa. Ubangiji ya rigaya ya fada masu cewa zai sake zuwa. Sabo da haka sa’anda ya ambaci hukunci da horo a kan Urushalima, tunaninsu ya je wurin wannan zuwan ne; kuma sa’anda suka taru kewaye da Mai-ceto a kan Dutsen Zaitun, suka tambaye shi: “Yaushe wadannan abu za su zama? Mi ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?’ Matta 24:3.BJ 25.2

    Cikin jinkai aka boye ma almajiran abin da zai faru nan gaba. A lokacin, da sun gane abu biyu din nan - azaba da mutuwar Mai-fansar, da kuma rushewar birnin da haikalin - da bakinciki ya fi karfinsu. Kristi ya bayana masu jerin muhimman ababa da za su faru kafin karshen lokaci. A lokacin ba a gane maganar sa gaba daya ba; amma za a bayana ma’anar sa yayin da mutanen sa za su bukaci umurnin da ke cikin maganan ne. Annabcin da Ya yi yana da ma’ana kashi biyu ne: yayin da ya nuna hallakawar Urshalima, ya kuma bayana ababan ban tsoro da za su faru a rana ta karshe.BJ 25.3

    Yesu ya fada ma almajiran matsalolin da za su abku ma Israila mai-ridda, musamman ma horon nan sakamakon kin Masiya da kuma giciyewarsa. Alamu za su rigayi horon. Sa’ar da ake tsoro za ta zo nan da nan, da sauri kuma. Mai-ceton kuma ya gargadi Masu bin Sa: “Sa’anda kun ga kyamar lalata, wadda aka ambace ta ta bakin annabi Daniyelu, tana tsaye a cikin tsatsarkan wuri (bari mai-karantawa shi fahimta), sa’annan wadanda ke chikin Yahudiya, su gudu zuwa duwatsu.” Matta 24:15,16; Luka 21:20,21. Sa’anda za a kafa gumakan Romawa a wuri mai-tsarki wanda ya zarce ganuwar birnin, to a wannan lokacin ya kamata masu bin Kristi su gudu. Idan aka ga wannan alamar, duk mai-neman tsira sai shi hanzarta. Dole cikin hanzari a yi biyayya ga wannan kashedi ko ina a kasar Yahudiya da Urshalima kanta. Wanda ya yi sa’a yana kan bene, kada ya sauka zuwa cikin gida, ko don ceton wani abin sa mafi-tamani. Wadandan ke aiki a gonaki ko lambu ba za su dawo don daukan rigan da suka tube kafin su fara aikin gonan ba. Kada wani ya yi jinkiri ko kadan, domin kada a hada da su cikin halakar.BJ 25.4

    A zamanin mulkin Hiridus, an yi ma Urshalima adon gaske aka kuma gina mata manyan gidaje da ganuwa da mafaka da suka kara mata tsaro, wanda ya yi annabci cikin jama’a cewa za a hallaka ta, za a mai da shi mahaukaci yadda aka yi ma Nuhu a zamaninsa. Amma Kristi Ya rigaya Ya ce: “Sama da kasa za su shude, amma zantattuka na ba za su shude ba.” Matta 24:35. Sabo da zunuban Urshalima, an kadara ma Urshalima fushi sosai. Urshalima da taurin kanta sun sa hallakawar ta ya zama dole.BJ 26.1

    Ubangiji, ta bakin annabi Mikah ya ce: “Ku ji wannan, ina rokonku, ku shugabannai na gidan Yakub, ku mahukunta na gidan Israila, ku da kuke kin shari’a kuna bata dukan gaskiya. Suna gina Sihiyona da jini, Urshalima kuma da sabo. Manyanta suna shari’a domin toshi, priest nata suna koyaswa domin ijara, annabawanta kuma suna duba domin kurdi; duk da wannan sai su jingina ga Ubangiji, su che, ubangiji ba shi chikinmu ba? Babu chiwuta da za ta same mu” Mikah 3:9-11BJ 26.2

    Kalmomin nan sun bayana halayen mazamnan Urshalima daidai. Yayin da suke cewa wai suna kiyaye dokokin Allah daidai, suna ketare dukan kaidodin dokokin. Sun ki jinin Kristi domin tsabtarsa da tsarkinsa sun bayana zunubansu. Suka kuma zarge shi da jawo dukan matsalolin da suka fuskanta sabo da zunabansu. Ko da shike sun san ba shi da zunubi, sun zartas da cewa dole Shi Ya mutu domin al’ummarsu ta sami zaman lafiya. Suka ce: “Idan mun bar Shi haka kurum, dukan mutane za su ba da gaskiya gare shi, Romawa kuma za su zo su amshi wurinmu duk da alummarmu.” Yohanna 11:48. Wai idan aka kashe Kristi, su za su sake zama al’umma kakarfa mai-hadin kai. Sai suka goyi bayan maganar babban priest nasu cewa zaifi kyau mutum daya ya mutu maimakon dukan al’umma ta hallaka.BJ 27.1

    Ta haka ne shugabannin Yahudawa suka gina “Sihiyona da jini, Urshalima kuma da sabo.” Mikah 3:10. Amma kuma yayinda suka kashe Mai-cetonsu domin ya tsauta zunabansu, sun mai da kansu kamnatattu na Allah, suka zata kuma cewa Ubangiji zai kubutar da su daga magabtansu. Inji annabin, “Domin wannan, sabada aikinku, za a hude Sihiyona kamar gona, Urshalima kuma za ta zama tuddai, dutsen gidan Ubangiji kuma za ya zama kamar tuddan kurmi.” Mikah 3:12. Kusan shekara arba’in bayan Kristi da kansa Ya yi annabcin hallakawar Urshalima, Ubangiji Ya jinkirta hallaka birnin da al’ummar. Jinkirin-fishin Allah zuwa ga masu kin bishararsa, masu kisan Dan sa kuma, abin al’ajibi ne. Misalin itace mara yayan nan ya bayana yadda Allah Ya yi da al’ummar Yahudawa ne. An umurta cewa: “ka sare shi; don mi yake tsare kasa banza.” (Luka 13:7) amma alherin Allah ya kyale shi har tsawon lokaci kadan. Cikin Yauhudawan akwai da yawa da basu san halin Kristi da aikin Sa ba tukuna. Yaran kuma basu sami zarafi ko hasken da iyayensu suka ki ba. Ta wurin wa’azin manzanin da abokansu, Allah zai ba su haske; za a yarda masu su ga yadda aka cika annabci, ba ta wurin haihuwar Kristi da rayuwarsa kadai ba, har ma tawurin mutuwarsa da tashinsa. Ba a kama yaran da zunuban iyayensu ba; amma sa’anda yaran suka ki karin hasken da aka ba su, bayan sun san hasken da aka ba iyayensu, sai suka zama masu tarayya cikin zunuban iyayensu, suka kuma cika ma’aunin zunuban su.BJ 27.2

    Jinkirin-fushin Allah zuwa Urushalima ya tabbatar da Yahudawa cikin rashin tubansu ne kawai. Cikin kiyayya da muguntar su ga almajiran Yesu, sun ki tayin karshe na jin kai ne. sai Allah ya janye kariyarsa gare su, ya kyale Shaitan da malaikunsa, sai al’ummar ta koma kalkashin mulkin shugaban da ta zaba. ‘Ya’yanta sun ki alherin Kristi, wanda da zai ba su ikon magance miyagun halayyansu, sai Shaitan ya ingiza munanan halayyen nasu; suka dena yin tunani, suna bin ta zuciya da kuma fushi mara-ma’ana. A cikin iyali da cikin al’umma, cikin manya da kanana, aka iske zato da kiyashi da kiyayya da rashin jituwa da tawaye da kisan kai. Ko in aba tsoro. Abokai da yan-uwa suka rika bashe da junansu. Iyaye da yan-uwa suka rika kashe juna. Shugabanni suka kasa yin mulkin kansu, suka zama azalumai. Yahudawa sun yarda da shaidar karya suka giciye Dan Allah, mara laifi. Yanzu kuma zarge zargen karya sun sa su cikin rashin tabbas. Ta wurin ayukansu sun dade suna cewa: “ku sa mai-tsarki na Israila shi dena shi bar mu.” Ishaya 30:11. Yanzu an biya bukatar su. Tsaron Allah bai sake domin su ba. Shaitan ya zama shugaban al’ummar, manyan shugabanni na gwamnati da na addini kuma suka kasance kalkashin ikon sa.BJ 28.1

    Shugabannin bangarori masu hamayya da juna sukan hada kai su tsotse mabiyan su su kuma wulakanta su, sa’annan su kuma su karkashe juna ba tausayi. Ko tsarkin haikalin ma bai hana su aikata muguntar su ba. Sukan kashe masu-sujada a gaban bagadi, aka kuma kazantar da haikalin da gawayen. Duk da haka cikin makantarsu da sabonsu, masu aikata muguntan nan sukan furta cikin jama’a cewa ba sa tsoron cewa za a halaka Urushalima, domin birnin Allah ne. Don kara tabbatar da ikonsu, suka ba annabawa toshi su shelata cewa mutane su jira kubutarwa da za ta zo daga wurin Allah, ko da dakarun Romawa suna kewaye da haikalin. Har karshe jama’a da yawa sun gaskata cewa Madaukaki zai sa hannu ya ba su nasara bisa magabta. Amma Israila ta rigaya ta bijire ma tsaron Allah, yanzu kuma ba ta da tsaro. Urushalima ta zama abin tausayi! Rashin jituwa ya nakasa ta, jinin yankakkun ‘ya’yanta ya mamaye tituna, mayakan magabta kuma suka rushe ganuwoyin tsaron ta suna karkashe mayakanta!BJ 29.1

    Kowane annabcin da Kristi Ya yi game da rushewan Urushalima ya cika. Yahudawa sun dandana gaskiyar kashedin Sa cewa: “Da mudun nan da kuke aunawa kuma da shi za a auna maku.” Matta 7:2.BJ 29.2

    Alamu da al’ajibai sun bayana, suna nuna cewa hallaka da kaito suna zuwa. Da tsakar dare, wani haske da ba a saba gani ba ya haskaka haikalin da bagadin. Da faduwar rana aka ga karusai da mayaka akan gizagizai suna shirye don yaki. Priestocin da ke aiki cikin haikalin da daren suka razana sabo da wasu surutai da basu gane ba; duniya ta girgiza, aka kuma ji muryoyi masu yawa suna cewa: “mu bar wurin nan.” Babban kofar gabas din nan da mutum ashirin ba sua iya rufe ta da sauki, wadda kuma aka tokare ta da manyan karafuna da aka dasa cikin dutse a kasa, ta bude da tsakar dare, ba kuma wanda ya bude ta.BJ 29.3

    Shekara bakwai wani mutum ya rika kai da kawowa a titunan Urushalima yana shelar munanan ababan da za su abko ma birnin. Dare da rana, ya rika shela cewa: “Murya daga gabas! Murya daga yamma! Murya daga kusurwoyi hudun! Murya sabanin Urshalima da haikalin! Murya sabanin angaye da amare! Murya sabanin dukan mutane!” Sai aka kame wannan mai-shelan da ba a gane ko wane irin halitta ne shi ba, aka kulle shi a kurkuku aka kuma yi masa bulala, amma bai ce komi ba. Idan aka zage shi ko an mare shi, yakan amsa kawai: “kaito, kaiton Urshalima.” “kaito, kaiton mazamna cikinta.” Bai dena shelar kashedin nan ba har sai da aka kashe shi cikin yakin da ya y i annabcinsa.BJ 30.1

    Ko Kirista daya bai mutu a hallakawar Urshalima ba. Kristi ya rigaya ya ba almajiran Sa kashedi, kuma dukan wadanda suka gaskata maganarsa sun jiraci alamun da aka ce za su zo. Yesu yace: “Amma sa’anda kun ga Urshalima tana kewaye da dagar yaki, sa’annan ku sani ribdewatta ta kusa. Sa’annan wadanda ke chikin tsakiyarta su fita waje.” Luka 21:20,21. Bayan da Romawa Kalkasin shugabancin Cestius suka kewaye birnin, sai haka kawai suka watsar da yakin a lokacin da ya kamata su kai hari. Israilawa suna gaf da sallama masu garin ke nan, sai janar din Romawa ya janye mayakansa, ba dalili. Amma Allah ne cikin alheri ya sa hakan ya faru domin mutanensa. An rigaya an ba Kirista alaman da aka yi masu alkawali, yanzu kuma an ba duk wanda ya yarda ya bi kashedin Mai-ceto. Aka shirya alamura ta yadda Yahudawa ko Romawa ba za su iya hana Kirista gudu ba. Sa’anda Cestius ya janye, sai Yahudawa daga Urushalima suka bi dakarun nasa; yayin da suke fada da juna, Kirista suka sami damar ficewa daga birnin. A lokacin kuma babu magabta a kauyuka da za su tare su. Lokacin kewayewar Urushalima, Yahudawa sun tattaru a Urushalima don Idin Bukkoki, ta haka kuwa Kirista ko ina suka iya gujewa ba matsala. Ba da jinkiri ba suka gudu zuwa birnin Pella, a kasar Perea, gaba da urdun.BJ 30.2

    Dakarun Yahudawa suka tasamma Cestius da mayakansa kamar za su hallaka su gaba daya. Dakyar Romawa suka iya tserewa. Yahudawa suka koma Urushalima da ganimar nasaran yakin da suka yi. Amma nasaran nan ta jawo masu wahalu ne kawai. Ta sa sun yi ma Romawa taurin kan da ya jawo ma birnin su hallaka nan da nan.BJ 31.1

    Sa’anda Titus ya dawo ya kewaye Urushalima da mayaka, matsalolin da suka fado ma Urushalima suna da yawa. Birnin ya cika da miliyoyin Yahudawa da suka zo idin Paska. Shaguna cike da kayan masarufi da ya kamata su isa anfani har tsawon shekaru, bangarori masu-gaba da juna a cikin birnin sun rigaya sun hallaka shagunan lokacin tashe-tashen hankulan su, yanzu kuma aka dandana azabar yunwa. Aka sayar da mudun alkama kan talent guda. Yunwa ta kai inda mutane suka cinye mazagin wandonsu da takalmin su da jakar su ma. Mutane da yawa sukan fita da dare a sace, su nemi ciyayi da ganyaye a bayan ganuwar garin, ko da shike an rika kashe wandansun su da azaba mai-tsanani, wadanda suka dawo lafiya kuma akan kwace abin da suka samu dakyar din nan. Azabtarwa mafi-muni shi ne wanda masu-mulki sukan yi don kwace dan abin da mayunwata suka boye. Yawancin masu muguntan nan kuma mutane ne masu koshi da kan yi kwacen nan domin su ajiye ma kansu ne don nan gaba.BJ 31.2

    Dubbai sun mutu da yunwa da annoba. Kauna kam ta kare. Mazaje sun yi ma matan su fashi, mataye sun ma mazan su fashi. Akan ga yara suna kwace abinci daga bakunan iyayen su tsofofi. Tambayan annabi cewa: “Ya yiwu mache ta manta da danta mai-shan mama?” ya sami amsa cikin wannan birnin: “Hannuwan mata masu-tabshin rai sun dafa ‘ya’yansu chikin ruwa, abinchinsu kenan a cikin hallakar diyar jama’ata.” Ishaya 49:15; Makoki 4:10. An kuma cika annabcin da aka bayar karni goma sha hudu da suka gabata, cewa: “Machen kuma da ke wurinku, mai-tabshi, mai-sanyin hali, wadda ba ta da karfin rai da za ta ko sa tafin sawunta a kasa domin sanyin hali dajin tabshi, za ta dubi mijin kirjinta da mugun ido, har da danta da diyarta kuma; ….. da yayanta wadanda take haifassu; gama a boye za ta chinye su domin rashin abu duka, chikin datsewar yaki da matsi, wadanda abokin gabanka za ya matsa ka chikin kofofinka.” Kubawar 28:56,57.BJ 32.1

    Shugabannin Romawan sun so su razana Yahudawa ta yadda dole za su sallamar. Fursunonin da suka yi taurin kai aka yi masu bulala da tsanantawa, aka kuma giciye su a cikin ganuwar birnin. Haka aka kashe daruruwan mutane kowace rana, aka kuma ci gaba har sai da gefen kwarin Jehoshaphat, a Kalfari kuma, an jera giciye da yawa ta yadda da kyar ma ake wucewa a tsakanin su. Ta haka aka cika la’anan nan da aka furta a gaban dakalin sharia’r Bilatus cewa: “Jininsa shi zamna a kanmu da ‘ya’yanmu.” Matta 27:25.BJ 32.2

    Titus ya so ya takaita yakin, ta haka kuma ya dauke ma Urushalima cikar azabarta. Tausayi ya cika shi sa’anda ya ga gawaye tuli tuli a cikin kwari. Daga kan Dutsen Zaitun kuma ya dubi haikalin nan mai-daraja, sai ya umurta cewa kada a taba ko dutse daya daga ginin. Kafin ya yi yunkurin kama haikalin sai da ya roki shugabannin Yahudawa kada su tilasta shi ya kazamtar da wuri mai-tsarkin da jini. Idan za su je a yi fadan a wani wuri dabam, Romawa ba za su bata tsarkin haikalin ba. Josephus da kansa ya roke su su sallamar domin su ceci kansu da birninsu da wurin sujadar su. Amma suka amsa masa da la’ana. Aka jejjefi mai-tsakancin nan na karshe yayin da yake rokon su. Yahudawa sun ki rokon Dan Allah, Yanzu kuma bayani da roko sun kara sa su nacewa ne cikin fadan, har karshe. Kokarin Titus domin ceton haikalin ya zama banza; wanda ya fi shi Ya rigaya Ya ce ba za a iske dutse daya a bisan wani dutsen ba.BJ 32.3

    Taurin kan shugabannin Yahudawan da, munanan laifukan da aka aikata cikin birnin, suka jawo fushin Romawan; sai kuma Titus daga baya ya kudurta kama haikalin a gurguje. Amma ya kudurta cewa ba za a hallaka haikalin ba. Amma ba a bi umurninsa ba. Bayan ya koma bukarsa da dare, Yuhudawa suka ruga daga cikin haikalin suka abka ma sojojin a waje. Cikin gwagwarmayar, wani soja ya jefa itacen wuta ta wani rami a ginin, nan da nan kuma dakunan ginin da aka yi masu ado da katako suka kama wuta. Titus ya ruga wurin tare da hafshoshinsa, ya umurci sojojin su kashe wutar. Ba a ji maganarsa ba. Cikin fushinsu, sojojin suka rika jefa wuta cikin dakunan da ke hade da haikalin, sa’an nan suka yanke dimbin mutane daga wadanda suka buya a wurin, jini ya kwarara a matakalan haikalin kamar ruwa. Dubban duban Yahudawa suka hallaka. Aka rika jin ihu cewa “Ichabod!” — darajar ta tafi.BJ 33.1

    Titus ya kasa tsayar da fushin sojoji, ya shiga da hafsoshin sa, ya dubi cikin ginin nan mai-tsarki. Darajar ginin ta ba su mamaki, kuma kafin wutar ta kai wuri mai-tsarki, ya yi yunkuri na karshe domin ya ceci haikalin, ya kuma umurci sojojin su tsayar da ci gaban wutar. Wani hafsa, Liberalis, ya yi kokarin tilastawa a yi biyaya bisa ga ikon matsayin sa; amma kiyayan da aka wa Yahudawa ya fi karfin buyayya ga sarkin Rum, ya kai ga marmarin yaki da bagen ganima. Sojojin suka ga komi kewaye da su zinariya ce da wutar ta haskaka; suka dauka cewa akwai dukiya mara iyaka a cikin haikalin. Wani soja a sace, ya tura wuta ta kofar wuri mai-tsarkin: nan da nan ginin gaba daya ya kama da wuta. Hayaki da wuta suka tilasta hafsoshin komawa, aka bar ginin ya kone “Abin bai yi kyaun gani ga Romawa ba — ga Yahudawa kuma fa? Dukan kan tudun da birnin yake ya haskaka kamar aman wuta. Gine gine suka rika rushewa daya bayan daya, wuta kuma ta cinye su. Jinkan katako suka zama kamar harsunan wuta; bene ya zama kamar igiyar jan haske, sorayen kofofin suka rika fitar da wuta da hayaki. Tuddai da ke kusa suka haskaka; aka kuma ga mutane sun tattaru suna kallon hallakar, cikin bakinciki. Mutane suka cika kowace ganuwa da tsaunuka suna fushi da tunanin ramuwa. Ihun sojojin Romawa da kukan mutane da ke konewa sun hadu da karar wutan da ke kona ginin, da kuma surutun katakai da ke faduwa. Kuwan duwatsu sun rika dawo da surutun mutane daga tsaunuka; mutanen da suna mutuwa da yunwa suka yi anfani da sauran karfin su don yin kukan bakinciki.BJ 33.2

    “Kisan cikin haikalin ya fi abin da ake gani a wajen muni. Maza da mata, tsofofi da yara, masu-tashin hankali da priestoci, masu-fada da masu-rokon jin kai duk an karkashe su barkatai. Wadanda aka kashe sun fi masu kashe su yawa. Dakarun suka rika tattaka tari tarin gawaye domin su ci gaba da kisa.” BJ 34.1

    Bayan hallakar haikalin, nan da nan dukan birnin ya fadi a hunnun Romawa. Shugababbin Yahudawa suka gudu daga mabuyansu; Titus kuma ya iske su, ba kowa ciki. Cikin mamaki ya ce Allah ne ya ba shi su cikin hannun sa; domin ba injin da ya isa ya rusa mabuyan nan komi karfin sa kuwa, aka kona birnin da haikalin har kasa, aka kuma kabce wurin da da haikalin ke tsaye, kamar gona. Irmiya 26:18. Daga kewayewar birnin har kisa da aka yi, sama da mutum miliyan daya sun hallaka; aka kwashe wadanda suka rage a matsayin kamammu, aka sayar da wadansu cikin bauta, wadansu kuma aka kai su Rum, aka jefa su ga namomin daji a wuraren shakatawa, wadansu kuma aka watsar da su barkatai cikin duniya.BJ 34.2

    Yahudawa sun yi ma kan su tarkoki; suka cika ma kansu kokon ramuwa. Cikin hallakan al’ummar su, da kuma wahalolin da suka bi su inda suka warwatsu, girbi suka yi na shukan da suka yi da hannunsu. In ji annabi: “Ka hallaka, ya Israila.” “gama ka fadi ta wurin sabon ka” Hosea 13:9; 14:1. An cika nuna cewa wai wahalolin su horo ne kai tsaye daga Allah. Ta haka ne babban mai-rudin nan ke so ya boye aikin sa. Tawurin bijire ma alheri da kaunar Allah, Yahudawa sun sa an janye kariyar Allah daga gare su, aka kuma bar Shaitan ya yi mulki bisan su yadda ya ga dama. Miyagun ababan da aka yi lokacin hallakar Urushalima kwatanci ne na ikon ramuwa na Shaitan a akan wadanda suka yarda da mulkinsa.BJ 34.3

    Ba za mu iya sanin bashin da Kristi ke bin mu sabo da salama da kariyan da muke moriya ba. Ikon kariyan Allah ne ke hana mutum shiga kalkashin ikon Shaitan dungum. Marasa biyayya da marasa godiya suna da dalili babba don godiya ga Allah sabo da jin kan Allah da jinkirin fushinsa yadda yake hana Shaitan anfani da ikonsa na mugunta. Amma idan mutane suka wuce iyakar hakurin Allah, akan cire wannan kariyar. Allah ba ya tsayawa kan mai-zunubi kamar mai-zartas da hukuncin laifin; amma yakan bar masu-kin jin kan Sa da kansu, su girbe abin da suka shuka. Kowane kashedi da aka bijire masa, kowace jaraba da aka yarda da ita, kowace ketarewar dokar Allah, shuka ake yi wadda kuwa za ta haifar da girbin ta. Daga bisani za a janye Ruhun Allah da aka yi ta kin Sa, daga mai-zunubin, sa’annan babu sauran ikon da zai danne miyagun halayyan mutum, ba kuma tsaro daga muguntar Shaitan da magabtakar sa. Hallakawar Urshalima kashedi ne ga dukan masu wasa da tayin alherin Allah, suna kuma bijire ma rokon da yake yi cikin jin kai. Ba a ta ba ba da wata shaidar kiyayyar Allah ga zunubi da kuma tabbacin horo da zai abku ma mai-laifi kamar wannan ba.BJ 35.1

    Annabcin Mai-ceto game da hukumci da aka aiwatar kan Urshalima zai sake cika ta biyu wadda ta farkon ma alamar ta ce kawai. Daga abin da ya faru da Urshalima za mu iya ganin rushewar duniyar da ta bijire ma alherin Allah, ta kuma tattake dokar sa. Duniya kam ta ga munanan wahaloli cikin daruruwan shekarunta na laifuka. Abin ba dadin tunawa. Sakamakon bijire ma ikon Allah sun yi muni sossai. Amma ana nuna cewa abin da zai faru nan gaba zai fi muni. Ababan da suka faru can baya — jerin tashe tashen hankula, tarzuma, juyin juye-hali, “mayaki chikin girman yaki, da tufafi mirginannu chikin jini” (Ishaya 9:5) mene ne su in aka gwada su da ababan ban razana na ranan can sa’anda za a jenye Ruhun sassauci na Allah gaba daya daga miyagu, ta yadda ba bin da zai sassauta muradin zuciyar mutum da fushin Shaitan! Lokacin ne duniya za ta ga sakamakon mulkin Shaitan yadda ba ta taba gani ba.BJ 35.2

    Amma a wannan ranar, kamar ranar rushewar Urushalima, za a kubutar da mutanen Allah, dukan wanda za a iske sunansa cikin masu rai. Ishaya 4:3. Kristi Ya rigaya Ya bayana cewa zai sake zuwa domin Ya tattara nasa zuwa wurin kansa. “Sa’annan kuma dukan kabilun za su yi bakin chiki, za su kuwa ga Dan mutun yana zuwa a bisa giza gizai na sama tare da iko da daukaka mai-girma. Kuma za ya aike malaikunsa da babbar kara ta kafo, su kuma za su tattara zababbunsa daga kusurwoyi fudu, daga wannan iyakar sama zuwa wannan.” Matta 24:30,31. Sa’an nan wadanda sun ki biyayya da bishara za a cinye su da ruhun bakinsa a kuma hallaka su da hasken zuwansa. Tassalunikawa II, 2: 8. Kamar Israila ta da miyagu ne za su hallaka kansu ta wurin zunubinsu. Ta wurin rayuwa ta zunubi, sun ware kansu daga Allah, har mugunta ta bata yanayin su ta yadda bayanuwar darajar Sa wuta ce mai hallakaswa.BJ 36.1

    Bari mutane su yi hankali, kada su manta darasin da Kristi Ya koya masu. Yadda Ya gargadi almajiran Sa game da hallakawar Urushalima, Ya kuma ba su alama, domin su tsira daga hallakar, hakanan ne Ya gargadi duniya game da ranan hallaka na karshe, Ya kuma ba da alamun zuwan wannan ranar, domin dukan wadanda sun yarda su guji fushin da ke zuwa. Yesu ya ce: “A chikin rana da wata da tamrari za a ga alamu; a kan duniya al’ummai suna chiwon rai.” Luka 21: 25; Matta 24:29; Markus 13:24-26; Ruya 6:12-17. Wadanda sun ga alamun nan “su sani ya yi kusa, har bakin kofa.” Matta 24: 33. Ya kuma yi kashedi cewa “Ku yi tsaro fa.” Markus 13:35. Wadanda sun ji kashedi ba za a bar su cikin duhu ba, har wannan ranar ta hume su. Amma wadanda basu yi tsaro ba, “ranan nan za ta tarshe [su] kamar barawo.” Tassalunikawa I, 5:2-5. BJ 36.2

    Yadda Yahudawa basu shirya karban fadakar Mai-ceton game da Urushalima ba, haka ne duniya bata shirya karban sako na wannan lokacin ba. Ko da yaushe ne ranar Ubangiji za ta zo, za ta humi marasa imani. Sa’an da rayuwa ke gudana kamar yadda ta saba, yayin da mutane suka nutse cikin nishadi da harka, da kasuwanci, da neman kurdi, sa’an da shugabannin addini suke daukaka ci gaban duniya da wayewar ta, mutane kuma sun shagala cikin yanayin tsaro na karya, lokacin ne, kamar yadda barawo da tsakar dare yake sata a cikin gidan da ba mai-gadi, hakanan ne hallaka faraf daya za ta abko ma marasa kula da marasa imani, “ba kwa za su tsira ba ko kadan.” Aya 3. BJ 37.1

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents