Babi na 8—Luther a Gaban Majalisa
Babban Jayayyar
- Contents- Gabatarwa
- Babi na 1—Hallakawar Urushalima
- Babi na 2—Tsanantawa a Karni na Farko
- Babi na 3—Riddan
- Babi na 4—Waldensiyawa
- Babi na 5—John Wycliffe
- Babi na 6—Huss da Jerome
- Babi na 7—Rabuwar Luther da Rum
- Babi na 8—Luther a Gaban Majalisa
- Babi na 9—Dan Canjin Switzerland
- Babi na 10—Ci Gaban Canji a Jamus
- Babi na 11—Yardar ‘Ya’yan Sarkin
- Babi na 12—Canjin Faransa
- Babi na 13—Netherlands da Scandinavia
- Babi na 14— ‘Yan Canjin Ingila na Baya.
- Babi na 15—Littafi da Juyin-Danwaken Faransa
- Babi na 16—Ubani Matafiya
- Babi na 17—Alkawuran Dawowan Kristi
- Babi na 18—Dan Canji America
- Babi na 19—Haske Ta wurin Duhu
- Babi na 20—Babban Falkaswa na Ibada
- Babi na 21—Gargadin da Aka Ki
- Babi na 22—Cikawar Annabci
- Babi na 23—Menene Haikalin?
- Babi na 24—Cikin Wuri Mafi-Tsarki
- Babi na 25—Dokar Allah Ba Ta Sakewa
- Babi na 26—Aikin Canji
- Babi na 27—Falkaswa na Zamani
- Babi na 28—Fuskantar Rahoton Rayuwa
- Babi na 29—Mafarin Mugunta
- Babi na 30—Gaba Tsakanin Mutum da Shaitan
- Babi na 31—Wakilcin Miyagun Ruhohi
- Babi na 32—Tarkokin Shaitan
- Babi na 33—Babban Rudi na Farko
- Babi na 34—Ko Mattatu Za Su Iya Magana da Mu?
- Babi na 35—Barazana ga Yancin Lamiri.
- Babi na 36—Yakin da Ke Zuwa.
- Babi na 37—Littafi, Mai-tsaro.
- Babi na 38—Gargadi na Karshe
- Babi na 39—Kwanakin Wahala
- Babi na 40—An Tsirar da Mutanen Allah
- Babi Na 41—Mayar da Duniya Kango
- Babi na 42—Karshen Jayayyar
Search Results
- Results
- Related
- Featured
- Weighted Relevancy
- Content Sequence
- Relevancy
- Earliest First
- Latest First
- Exact Match First, Root Words Second
- Exact word match
- Root word match
- EGW Collections
- All collections
- Lifetime Works (1845-1917)
- Compilations (1918-present)
- Adventist Pioneer Library
- My Bible
- Dictionary
- Reference
- Short
- Long
- Paragraph
No results.
EGW Extras
Directory
Babi na 8—Luther a Gaban Majalisa
Sabon sarki Charles V ya hau gadon sarautan Jamus ke nan, ‘yan sakon Rum kuma suka yi sauri suka je su yimasa barka, su kuma lallabe shi ya yi anfani da ikonsa ya hana Canjin. A wancan gefen kuma mai-zaben Saxony, wanda ya taimaki Charles samun rawaninsa, ya roke shi kada ya dauki wani mataki game da Luther har sai ya saurare shi. Wannan ya sa mai-zaben cikin halin rudewa da rikicewa. Babu abin da zai gamsar da ‘yan paparuman nan sai umurnin da zai sa a kashe Luther. Mai-zaben ya rigaya ya furta da karfi cewa, “Ko mai-martaba sarki, ko kuma wani mutum da bam, babu wani mutumin da ya nuna cewa an karyata rubuce rubucen Luther,” sabo da haka ya bidi “cewa a ba Likita Luther tsaro, domin ya bayana gaban hukuman nan na masana, masu ibada, masu-sahri’a marasa son kai kuma.”BJ 144.1
Hankalin dukan mutane kuma yanzu ya koma ga majalisar kasashen Jamus da suka taru a Worms jima kadan bayan Charles ya hau gadon mulki. Akwai muhumman batutuwa da wannan majalisar za ta duba; na farko ke nan da ‘ya’yan sarautan Jamus za su fara saduwa ta shawarar majalisa da matashin sarkin nasu. Daga dukan bangarorin kasar, masu martaba na ekklesiya da na kasa, suka zo. Manyan kasa da ‘ya’yan sarauta da masu iko, masu-kishin yancin gadonsu; shugabannin ekklesiya, cike da sanin fifikonsu da ikonsu; fadawa masu-matsayin jarumtaka tare da barorinsu, rike da makaman su; da jakadu daga kasashen waje masu nisa - duka suka taru a Worms. Duk dai babban abin da ya fi daukan hankalin taron nan shi ne mai-canjin nan na Saxony, watau Luther. BJ 144.2
Charles ya rigaya ya umurci mai-zaben ya zo majalisar tare da Luther, ya kuma tabbatar masa da tsaro, da alkawalin yin mahaware cikin sauki tare da masana, game da batutuwan da ake mahawara akai. Luther ya yi taraddadin bayanuwa gaban sarkin. Lafiyarsa a wannan lokacin ta ragu sosai; duk da haka ya rubuta ma mai-zaben cewa: “Idan ba zan iya zuwa Worms da koshin lafiya ba, zan je da rashin lafiyan nan nawa. Domin idan sarki ya kira ni, ba ni da shakka cewa kiran Allah ne da kansa. Idan suna so su yi anfani da karfi a kai na, wanda kuwa mai yiwuwa ne (domin ba don fadakarwarsu ne suka umurce ni in je ba), na bar batun a hannun Ubangiji. Har yanzu Yana da rai, Yana kuma mulki, Shi wanda Ya kiyaye samari ukun nan a cikin tanderun wuta. Idan ba zai cece ni ba, rai na ba komi ba ne. Mu dai mu kare bishara daga renin miyagu, mu kuma zub da jininmu domin bisharar, domin kada miyagun su yi nasara, ba ni ne zan zabi ko rayuwa ta ko mutuwa ta ce za ta fi kawo ceto ga duka ba.... za ku iya begen komi daga wuri na ...amma ba gudu ko janyewa ba. Ba zan iya gudu ba, balle ma janyewa.”BJ 145.1
Sa’an da labari ya yadu a Worms cewa Luther zai bayana a gaban Majalisa, hankalin mutane ya tashi sosai. Aleander, wakilin paparuma da aka ba shi yin sahri’an, ya yi mamaki da fushi kuma. Ya ga cewa sakamakon zai bata aikin paparuma. Ta da binciken sahri’an da paparuma ya rigaya ya ba da hukumcin warewa akai zai zama reni ne ga ikon paparuma din. Biye da haka ya ji tsoron cewa kaifin harshe da karfin mahawaran mutumin nan za su iya janye hankulan ‘ya’yan sarki daga ra’ayin paparuma. Sabo da haka, cikin hanzari, ya nuna haushin sa ga Charles game da zancen zuwan Luther Worms. Kusan lokacin nan ne aka wallafa umurnin da ya ware Luther; wannan kuwa hade da fadan da jakadan ya yi ma sarkin ya sa shi sarkin ya yarda. Ya rubuta ma mai-zaben cewa idan Luther ba zai janye ba, sai dai ya kasance a Wittenberg.BJ 145.2
Da shi ke bai gamsu da nasaran nan tasa ba, Aleander ya yi iyakar kokarinsa ya tabbatar an hukumta Luther. Da naciyar da ta cancanci abu mafi kyau, ya jawo hankulan ‘ya’yan sarkin, da prietocin, da wadansu membobin majalisar, ya zargi Luther da “ta da hargitsi, tawaye, rashin ibada, da sabo.” Amma zafi da mumunan fushin da jakadan ya nuna a fili haka ya bayana irin ruhun da ya motsa shi. Mutane suka rika cewa: “Fushi da ramuwa ne su ke motsa shi, maimakon himma da ibada.” Yawancin yan Majalisar suka fi yarda da matsayin Luther.BJ 146.1
Da karin himma, Aleander ya matsa ma sarkin cewa wajibi ne gare shi ya aiwatar da umurnin paparuman, amma a kalkashin dokokin Jamus ba za ya iya yin wannan ba sai da yardar ‘ya’yan sarkin; sa’an nan da matsin wakilin paparuman da ya fi karfinsa, Charles ya ce ma Luther ya gabatar da maganarsa ga Majalisar. “Ranar alfarma ce ga jakadan. Majalisar mai-girma ce: dalilin ma ya fi girma. Aleander aka zaba zai yi Magana a madadin Rum, .... uwa da uwargijiyar dukan ekklesiyoyi. Zai nuna yarimancin Bitrus a gaban taron nan na shugabannin Kirista. Yana da baiwar kaifin harshe, ya kuwa shirya ma babban zaman nan. Allah Ya shirya cewa Rum ta zo gaban taro mafi girma ta bayana kanta, ta bakin jami’inta mafi iya magana, kafin a hukumta ta.” Cikin shakka masugoyon bayan Luther suka so su ga sakamakon maganar Aleander. Mai-zaben Saxony ba ya wurin, amma bisa ga umurnin, wadansu fadawansa suka hallara domin su rubuta abin da jakadan zai fada.BJ 146.2
Da dukan ikon sani da kaifin harshe, Aleander ya shirya rushe gaskiya. Ya dinga jefa ma Luther zagi daya bayan daya, cewa Luther magabcin ekklesiya ne da na kasa kuma, da na masu rai da matattu, masu aikin bisahara, majalisu da Kirista daya dayansu. Ya ce: “A cikin kurakuran Luther, akwai isassun dalilan kona yan ridda dubu dari.”BJ 147.1
A karshe, ya yi kokarin nuna reni ga magoya bayan sabuwar gaskiyar. Ya ce: “Ina yan Luther din? Kungiyar mallamai masu zagi, priestoci masu-rashawa, ‘yan zuhudu marasa halin kirki, jahilan lauyoyi da fadawa marasa kunya, tare da talakawan da suka batar. Ina yawan fifikon yawan jama’ar Katolika, da fifikon iyawa, da iko! Wata doka ta bai daya daga wannan babban Majalisar za ta wayar da marasa hikima, ta gargadi marasa hankali, ta ba da tabbaci ga masu shakka, ta kuma karfafa marasa karfi.” BJ 147.2
Da irin makaman nan ake kai ma masu shelar gaskiya hari a kowace sara. Dalilai dayan ne ake anfani da su a kan dukan wadanda suka yi shelar bayananiyar maganar Allah sabanin sanannun kurakurai. Masu-son addini na yayi sukan ce: “wadanne ne wadannan masu wa’azin sabobin koyaswa?” “Ba su da ilimi, basu da yawa, kuma marasa wadata ne. Duk da haka suna cewa suna da gaskiya, kuma wai su ne zababbun mutanen Allah. Jahilai ne su, rudaddu kuma. Dubi yadda ekklesiyaar mu ta fi tasu yawan jama’a da tasiri kuma! Dubi yawan manyan mutane da masanan da ke cikinmu! Dubi yawan ikon da ke cikinmu!” Dalilan da ke jan hankulan duniya kenan; amma kamar yadda ba su da nasara a zamanin Luther, haka kum ba su da nasara yanzu ma.BJ 147.3
Canji fa bai tsaya kan Luther ba yadda mutane da yawa su ke zato. Zai ci gaba har karshen tarihin duniyan nan. Luther ya yi babban aiki na bayana ma sauran mutane hasken da Allah Ya haska masa; amma bai karbi dukan hasken da ya kamata a mika ma duniya ba. Daga wancan lokacin zuwa yanzu, sabon haske yana haska Littafin kullayaumin, sabobin gaskiya kuma suna bayanuwa. BJ 147.4
Jawabin jakadan ya yi tasiri sosai a kan Majalisar. Ba Luther awurin da zai rushe jarumin paparuman nan da gaskiyar maganar Allah mai-saukin ganewa. Ba a yi wani yunkurin kare dan Canjin ba. A fili aka nuna shirin hukumta shi da koyaswoyinsa, idan ya yiwu ma a tumbuke ridda. Rum ta sami dama mafi-kyau don kare matsayin ta. An fadi duk abin da ta iya fadi don kare kanta. Amma kamanin nasaran ne ya zama shaidar kasawarta. Daga nan za a kara ganin bambancin gaskiya da kuskure a fili, sa’an da suka ja dagar yaki a bayane, daga ranan Rum ta dena rashin tsoron da take da shi da.BJ 148.1
Yayin da yawancin yan majalisan ke marmarin mika Luther ga ramuwar Rum, da yawa cikinsu sun gani suka kuma yi kyamar lalacewan da ke cikin ekklesiya, suka kuma so a hana wulakncin da mutanen Jamus ke sha ta dalilin lalacewa da handaman shugaabannin ekklesiya. Jakadan ya nuna kyaun mulkin paparuma sosai. Yanzu kuma Ubangiji ya motsa wani dan Majalisa ya ba da ainihin sakamakon zaluncin tsarin paparuma. Da karfi cikin martaba, sarki George na Saxony ya tashi tsaye a wannan taron, ya bayana daidai rudi da ayukan ban kyama na tsarin paparuma da munin sakamakon su kuma. A karshe ya ce: BJ 148.2
“Wadannan ne wadansu daga cin mutuncin da ke nuna kasawar Rum. An ajiye dukan kunya a gefe, kuma manufarsu kadai it ace ...kurdi kurdi kurdi,... ta yadda masu wa’azi da ya kamata su fadi gaskiya ba abin da suke fadi sai karya, kuma ba barin su ake ba, lada ma ake ba su, da shike yawan ribar su daidai da yawan karyar su. Daga wannan mumunar mabulbulan ne mumunan ruwan nan ke kwararowa. Lalata ta sadu da son kurdi.... Abin kunyan da ma’aikatan ekklesiya ke yi ne yake jefa mutane da yawa cikin hallaka. Dole a yi canji gaba daya.”BJ 148.3
Luther kansa ba zai iya yin sokan da ya fi wannan game da cin mutunci da tsarin paparuma ke yi ba, kuma da shi ke mai-maganan ma sanannen magabcin Luther ne, wannan ya kara ma maganar sa tasiri. BJ 149.1
Da an bude idanun yan Majalisan, da sun ga malaikun Allah a tsakaninsu, suna aika tsirkiyoyin haske cikin duhun kuskure suna kuma bude zukata da tunani don karban gaskiya. Ikon Allahn gaskiya da hikima ne ya mallaki har magabtan Canjin ma, ta haka kuma ya shirya hanya domin babban aikin da za a yi, ba d a jimawa ba. Martin Luther ba ya wurin; amma an ji muryar Wani wanda Ya fi Luther a wannan taron. BJ 149.2
Nan take Majalisar ta kafa komiti da zai kirga, ya jera kowane cin zarafi da paparuma ke danne mutanen Jamus da shi. Jerin nan da ya kunshi ababa dari da daya, aka ba sarki, aka kuma bukace shi ya dauki mataki nan da nan don magance cin zarafin nan. Masu rubuta takardar karar suka ce: “Ga fa babban hasarar rayukan Kirista, ga barna ga kwace sabo da ababan kunya da suka kewaye shugaban ruhaniyar Kirista! Aikin mu ne wajibi mu hana hallaka da wulakantarwar mutanenmu. Don haka cikin tawali’u amma da hanzari, mu ke rokon ka ka umurta canji na duka, ka kuma dauki nauyin aiwatar da shi.”BJ 149.3
Yanzu kuma Majalisar ta bukaci dan Canjin ya bayana a gaban su. Duk da roko da kin yarda, da barazanar Aleander, daga baya dai sarkin ya yarda, aka kuma yi sammacin Luther ya bayana gaban Majalisar. Aka hada sammacin da takardar izinin tafiya da tabbacin tsaronsa. Aka ba wani dan sako da aka zaba ya kawo shi Worms daga Wittenberg.BJ 149.4
Abokan Luther sun tsorata kwarai. Da sanin kiyayya da gaban da ake masa, sun ji tsoro cewa ba za a kula da takardar izinin tafiyarsa ba ma, suka kuma roke shi kada ya sa ransa cikin hatsari. Shi kuwa ya amsa: “Yan paparuma ba sa so in je Worms, hukumci na da mutuwa ta suke so. Ba komi ba ne. Kada ku yi mani addu’a, amma ku yi ma maganar Allah addu’a.... Kristi zai ba ni Ruhunsa don nasara da wadannan ‘yan sakon kuskuren. Ina rena su tun ina da rai, zan yi nasara kan su ta wurin mutuwata. Suna kai da kawowa a Worms game da tilasta ni in janye; kuma ga yadda janyewata za ta kasance: da na ce paparuma wakilin Kristi ne; yanzu ina cewa shi magabcin Ubangijinmu ne, manzon Iblis kuma.”BJ 149.5
Luther bai yi tafiyan nan shi kadai ba. Ban da dan sakon sarkin, uku daga cikin abokansa na kusa kusa sun nace za su je tare da shi. Melanchthon ya nace zai bi su. Zuciyar sa ta hadu da ta Luther, ya kuwa so ya bi shi, in ta kama, har kurkuku ko mutuwa. Amma ba a yarda masa ba. Idan Luther ya hallaka dole begen Canjin ya rataya a kafadar abokin famarsa. Yayin da Luther ke rabuwa da Melanchthon, ya ce: “Idan ban dawo ba, kuma abokan gabana suka kashe ni, ka ci gaba da koyaswa, ka kuma tsaya da karfi cikin gaskiyar. Ka yi aiki a madadi na.... Idan ka rayu, mutuwa ta ba komi ba ne.” Dalibai da ‘yan kasa da suka taru domin su ga tafiyar Luther, sun motsu sosai. Jama’a da bishara ta taba zukatansu suka yi masa bankwana da kuka. Haka Luther da abokan tafiyarsa suka kama hanya daga Wittenberg.BJ 150.1
Cikin tafiyar, sun ga cewa zukatan mutane sun damu da tsoron munanan ababa. A wadansu garuruwa ba a ba su girmansu ba. Sa’an da suka tsaya domin su kwana, wani priest aboki ya nuna damuwar sa ta wurin nuna ma Luther hoton wani dan canji, mutumin Italiya da aka kashe. Washegari suka ji cewa an haramta rubuce rubucen Luther a Worms. ‘Yan sakon sarki suka rika shelar dokar sarkin, suna bidar mutane su kawo ma majistarori rubuce rubucen. Dan sakon sarki da ke tare da Luther, sabo da shakkar tsaron Luther a majalisar, da kuma zaton cewa karfin zuciyar sa ya raunana, ya tambaye shi ko yana da niyyar ci gaba. Ya amsa: “Ko da za a hana aiki na a kowane birni, zan ci gaba.”BJ 150.2
A Erfort, an karbi Luther da daraja. Jama’a masu sha’awarsa suka kewaye shi har ya wuce ta titunan nan da ya sha bi da zabirar barar sa. Ya ziyarci dakin da ya taba zama ciki a unguwar masu zaman zuhudu, ya kuma tuna famar da ta kawo masa hasken da yanzu ya mamaye Jamus. An roke shi ya yi wa’azi. Wannan kuwa an hana shi yi, amma da sakon sarkin ya ba shi izini, sai Luther, wanda da an taba mai da shi bawan unguwar, yanzu kuma ya hau bagadin unguwar. BJ 151.1
Ga taron jama’a ya yi anfani da kalmomin Kristi, “Salama gare ku.” Ya ce: masu bin ussan, ilimi, likitoci, da marubuta sun yi kokarin koya ma mutane hanyar samun rai madawami, kuma ba su yi nasara ba. Yanzu zan fada maku shi:... Allah Ya ta da Mutum daya daga matattu, Ubangiji Yesu Kristi, domin Ya hallaka mutuwa, Ya tumbuke zunubi, Ya kuma kulle kofofin lahira. Wannan shi ne aikin ceto. Kristi ya yi nasara! Wannan shi ne labari na farin ciki; kuma an cece mu ta wurin aikinsa, ba ta wurin aikinmu ba, ..... Ubangijinmu Yesu Kristi Ya ce, “Salama gare ku; dubi hannuwana; watau kenan, Duba, Ya mutum! Ni ne, ni kadai, wanda na dauke zunubanka, na fanshe ka; yanzu kuma kana da salama, in ji Ubangiji.”BJ 151.2
Ya ci gaba yana nuna cewa ana nuna ainihin bangaskiya ta wurin rayuwa mai-tsarki ne. “Da shi ke Allah Ya cece mu, bari mu yi ayukan mu domin su karbu gare Shi. Kana da arziki?, bari dukiyarka ta tanada domin bukatun matalauta. Kai matalauci ne? Bari hidimomin ka su zama karbabbu ga masu-arziki. Idan aikinka yana da anfani gare ka kai kadai ne, aikin da kake cewa kana yi ma Allah karya ne.” BJ 151.3
Mautanen suka ji shi kamar ya rike su da dabo. Ya ba mayunwatan mutanen nan gurasa ta rai. Aka daga Kristi a gabansu bisan su paparuma da priestoci da sarakuna manya da kanana. Luther bai ambaci hatsarin yanayin da shi kansa yake ciki ba. Bai nemi ya sa a yi tunaninsa ko a ji tausayinsa ba. Garin tunanin Kristi, ya manta da kansa. Ya boye a bayan Mutumin Kalfari, yana kokarin nuna cewa Yesu kadai ne Mai-fansar mai-zunubi. BJ 151.4
Yayin da Luther ya ci gaba da tafiyarsa, ko ina an so ganin shi sosai. Jama’a sukan kewaye shi, masu kaunarsa kuma suka yi masa kashedi game da manufar Romawan game da shi. Wadansu suka ce: “Za su kona ka, su mai da jikin ka toka, yadda suka yi da John Huss.” Luther ya amsa: “Ko da za su kunna wuta daga Worms zuwa Wittenberg, har harshen wutan ya kai har sama, ni zan yi tafiya cikin wutar, cikin sunan Ubangiji; zan bayana a gabansu; zan shiga mukamukan dorinan nan, in karye hakoran sa, ina dogara ga Ubangij Yesu Kristi.” BJ 152.1
Labarin kusantowar shi Worms ya ta da rudewa sosai. Abokansa sun damu da tsaron lafiyarsa; magabtansa sun damu game da yiwuwar nasarar aikinsa. An yi kokari sosai don hana shi shiga birnin. Bisa shawarar ‘yan paparuma, aka roke shi ya je gidan wani jarumi mai-goyon bayansa, inda aka ce za a magance dukan matsaloli cikin salama. Abokai sun yi kokarin nuna masa abin ban tsoro da yake fuskanta. Dukan kokarinsu ya kasa. Luther dai bai damu ba. Ya ce: “Ko da yawan aljannun da ke Worms ya kai yawan fallayen jinkan dukan dakunan da ke birnin, duk da haka zan shige shi.”BJ 152.2
Da shigowarsa Worms, jama’a da yawa suka kewaye kofofin, domin su marabce shi. Ko sarki kansa jama’a ba su taba taruwa da yawa hakanan domin su gaishe shi ba. Ya ja hanakula sosai, kuma daga cikin jama’ar aka ji wata murya mai-karfi tana wakar biso don yi ma Luther kashedin abin da zai faru da shi. Luther ya ce: “Allah zai zama Garkuwa ta,” sa’an da yake saukowa daga karusarsa.BJ 152.3
Mutanen paparuma basu gaskata cewa Luther zai dauki kasadar bayanuwa a Worms ba, zuwan sa kuwa ya cika su da mamaki. Babban sarkin nan da nan ya kirawo yan majalisarsa domin su yi sahwara kan matakin da za su dauka. Wani bishop, mai-tsananin ra’ayin paparuma, ya ce: “Mun dade muna shawara kan wannan batu. Bari mai-martaba ya gama da wannan mutumin gaba daya. Ba Sigismund ya sa an kone John Huss ba? Ba lallai ne mu bayar ko kuma mu tabbatar da kariyar mai-ridda ba.” Babban sarkin kuwa ya ce: “Babu, dole ne mu cika alkawalinmu.” Sabo da haka aka yarda cewa a saurari Luther.BJ 152.4
Dukan birnin sun kosa su ga kwararren mutumin nan, jama’a da yawa kuwa suka cika masaukinsa. Luther bai gama murmurewa daga ciwonsa ba; tafiyarsa ta sati biyu kuma ta gajiyar da shi; dole ne zai shirya domin muhimman ababan da za a yi washegari, yana kuma bukatar wuri shuru da hutawa ma. Amma marmarin ganin shi ya kai inda ‘yan sa’o’i kadan ne kawai ya samu ya huta kafin fadawa da jarumawa, da priestoci da ‘yan kasa suka kewaye shi. Cikinsu akwai fadawa da yawa da suka dade suna rokon babban sarkin cewa a canja daga cin mutunci da eklesuya ke yi, kuma, ta bakin Luther , “dukan su an yantar da su ta wurin bishara ta.” Magabta da abokai suka taru domin su ga dan zuhudun nan mara tsoro; amma ya karbe su a natse, yana amsa ma kowa da girmamawa da hikima kuma. Babu alamar kumamanci ko tsoro a jikinsa. Fuskarsa cike da alamun gajiya da ciwo ya nuna nagarta da farin cikin da ke cikinsa. Saduda da hikimar maganarsa sun ba shi ikon da ko magabtansa ma basu iya tsayayya da shi ba. Abokai da magabta suka cika da mamaki. Wadansu sun gaskata cewa akwai ikon Allah cikinsa; wadansu kuma suka ce: “Yana da aljannu,” kamar yadda Farisawa suka fada game da Kristi.BJ 153.1
Rana ta biye aka kira Luther domin ya halarci Majalisar. Aka hada shi da wani hafsan babban sarki wanda zai kai shi zauren da za a yi zaman; amma da kyar ya kai wurin. Kowane titi ya cika da ‘yan kallo suna marmarin ganin dan zuhudun nan da ya ki ikon paparuma.BJ 153.2
Da ya zo zai shiga wurin shari’an, wani tsohon janar wanda ya yi yake yake da yawa, ya ce masa: “Ya mai-zaman zuhhudu, yanzu za ka dauki matakin da ya fi nawa da wanda kowane kyaftin ya taba dauka cikin dukan yake yakenmu da aka fi zub da jini. Amma idan dalilin ka daidai ne, kuma ka tabbatar da shi, ci gaba cikin sunan Allah, kuma kada ka ji tsoron komi. Allah ba za ya rabu da kai ba.” BJ 153.3
Daga bisani Luther ya bayana gaban majalisar. Babban sarkin ya zauna bisa kujerar sarautar. Manyan mutane mafi girma a kasar suka kewaye shi. Ba mutumin day a taba bayana gaban taron day a fi wanda Luther ya bayana a gaban sa, don kare bangaskiyar sa. “Wannan tuhumar ma babban nasara ce a kan tsarin paparuma. Paparuma ya rigaya ya hukumta mutumin, yanzu kuma yana tsaye a gaban wata hukuma, wannan ma kawai ya nuna cewa hukumar ta aza kan ta isa paparuma. Paparuma ya rigaya ya ware shi ya raba shi daga dukan ya Adam; duk da haka an yi sammacin sad a harshe mai- ban girma, aka karbe shi a gaban majalisa mafi mafi martaba a duniya. Paparuma ya rigaya ya hukumta masa yin shuru har abada, yanzu kuma ga shi zai yi magana a gaban dubban masu sauraron sa a natse da suka zo daga kasashen Kirista masu nisa. An yi wani babban canji kenan tawurin aikin Luther. Rum ta fara saukowa kenan daga gadon sarautan ta, kuma muryar mai-zaman zuhudun ne ta jawo wannan kaskantarar.”BJ 154.1
A gaban wannan majalisar mai-iko da martaba, Luther dan Canji ya cika da tsoro da rudewa kuma. Da yawa cikin yarimomin, da suka gane yadda yake ji, sai suka je wurinsa, dayan su kuma ya ce masa a kunne: “Kada ka ji tsoron wadanda ke kashe jiki, amma ba za su iya kashe ruhu ba.” Wani kuma ya ce: “Sa’an da za a kai ku gaban gwamnoni da sarakuna sabili da ni, Ruhun Uban ku za ya ba ku abin da za ku fada.” Ta haka manyan mutanen duniya suka kawo kalmomin Kristi domin karfafa bawan Sa a lokacin jaraba. BJ 154.2
An kai Luther ya zauna fuska da fuska da wurin zaman babban sarkin ne. Sai wuri ya yi shuru. Sa’an nan wani jami’in babban sarkin kasar ya tashi yana nuna yatsa ga wani tarin littattafan Luther, ya bukaci dan Canjin ya amsa tambayoyi biyu: ko ya yarda littattafansa ne, da kuma ko yana sirye ya janye ra’ayoyin da ya bayana a cikinsu. Da shi ke an rigaya an karanta sunayen littattafan, Luther ya amsa cewa game da tambaya ta farko littattafan nasa ne. Ya kuma ce: “Game da tambaya ta biyu din, da shi ke tambaya ce da ta shafi bangaskiya da ceton rayuka, wadda kuma ta safi maganar Allah, dukiya mafi daraja a sama ko duniya, zan yi rashin hankali idan na amsa ba tare da yin tunani ba. Ina iya kasa abin da ya cancanci yanayin, ko kuma fiye da abin da gaskiya ke bida, wanda zai zama zunubi bisa ga furcin Yesu cewa: ‘Amma dukan wanda za ya yi musun sani na a gaban mutane, shi zan yi musunsa a gaban Ubana wanda ke chikin sama kuma.’ [Mata 10:33.] Sabo da haka, ina rokon martabar sarautar ka, da dukan saukin kai, ka ba ni lokaci domin in amsa ba tare da ketare maganar Allah ba.”BJ 154.3
Rokon nan na Luther hikima ce. Matakin sa ya nuna cewa ba cikin fushi ko gaggawa yake aikinsa ba. Irin natsuwa da kamewan nan wanda ba a zata za a samu wurin mai- karfin hali da rashin daidaituwan nan ya kara mashi karfi, ya kuma taimake shi daga baya ya amsa da hankali, da tabbaci, da hikima da martaba da suka ba magabtansa mamaki, ya yanke masu buri, ya kuma tsauta ma rennin su da fahariyar su.BJ 155.1
Washegari ne ya kamata ya bayana ya ba da amsarsa ta karshe. Da farko zuciyar sa ta yi sanyi, ganin irin ikokin da suka hada kai sabanin gaskiya. Bangaskiyarsa ta raunana; tsoro da rawan jiki suka abka masa, kyama ta cika shi. Sai ya ga hatsarukan da yawa a gabansa; ya ga kamar magabtan sa suna gaf da yin nasara, ikokin duhu kuma su rinjaya. Duhu ya rufa shi Kaman zai raba shi da Allah. Ya yi marmarin tabbacin cewa Ubangijin runduna zai kasance tare da shi. Cikin bakin ciki kwarai ya jefa kansa a kasa, ya yi rub da ciki, ya kuma kai kukansa mai-zafi ga Allah wanda Shi kadai ne mai gane irin kukan nan. BJ 155.2
Ya roka cewa: “Ya MAdaukaki, Allah na har abada, wace irin muguwar duniya kenan! Duba ga shi ta bude bakinta za ta hadiye ni, kuma dogara ta gare ka kadan ne. Idan a kan karfin duniyan nan ne kadai zan dogara, an gama komi.... sa’a ta ta karshe ta zo, an furta hukumci na.... Ya Allah, ka taimake ni da dukan hikimar duniya. Ka yi wannan kai kadai, gama akin nan ba nawa ba ne, naka ne, ba ni da abin yi a nan, ba abin mahawara da wadannan manya na duniya.... Amma aikin naka ne,... kuma aikin adalci ne, na har abada kuma. Ya Ubangiji ka taimake ni! Allah Mai-aminci Mara sakewa kuma, ba mutumin da na dogara gare shi.... Kowane abu na mutum ba shi da tabbaci; duk abin da ya fito daga mutum yana faduwa.... Kai ka zabe ni domin wannan aikin.... Ka tsaya a gefe na sabi da Kaunatacen Ka Yesu Kristi, wanda Shi ne kariya ta, garkuwa ta, da mabuya ta mai-karfi.”BJ 155.3
Allah mai-cikakken hikima ne Ya yarda Luther ya gane hadarin da ke gabansa, domin kada ya dogara ga karfin kansa, ya yi gaggawar shiga damuwa da ganganci. Amma ba tsoron wahala kansa ko tsoron azaba ko mutuwa, wadda da alama ta kusa, suka dame shi ba. Ya iso wurin tashin hankalin, sa’an nan ya ji rashin isansa ya fuskance shi. Ta wurin kumamancinsa gaskiya za aa iya yin nasara. Ba don tsoron lafiyarsa ba, amma don nasarar bishara ne ya yi kokawa da Allah. Kamar ta Israila a kokawar daren nan a gefen rafi, haka damuwa da tashin hankalinsa suka kasance. Kamar Israila kuma, ya rinjaya tare da Allah. Cikin kumamancinsa, bangaskiyarsa ta manne ma Kristi, babban Mai-kubutarwan. Aka karfafa shi da tabbacin cewa ba zai bayana gaban majalisar shi kadai ba. Salama ta dawo zuciyarsa, ya kuma yi murna cewa an yarda mashi ya girmama maganar Allah a gaban shugabanin al’ummai.BJ 156.1
Da wannan tunani da ya dogara ga Allah da shi, Luther ya shirya don faman da ke gabansa. Ya yi tunanin tsarin amsarsa, ya yi nazarin wadansu ababan da ya rubuta, ya kuma samo tabbaci daga Littafi da ya dace da matsayinsa. Sa’an nan, da hannunsa a kan Littafin da ke bude a hannun damansa da ya daga sama, ya yi alkawali cewa zai “kasance da aminci ga bishara, ya kuma sanar da bangaskiyarsa kai tsaye, ko da zai hatimce shaidarsa da jininsa ne.”BJ 156.2
Sa’an da aka sake shigo da shi cikin Majalisar, fuskarsa ba ta nuna alamar tsoro ko rudewa ba. Cikin natsuwa da salama, amma kuma cikin martaba da rashin tsoro, ya tsaya a matsayinsa na shaidan Allah cikin manyan mutanen duniya. Hafsan sarkin kuma ya yi masa tambayan nan, ko yana so ya janye koyaswoyinsa. Luther ya ba da amsarsa cikin natsuwa da murya mai-ladabi, ba fada ko haushi. Ya nuna kunya da rashin tsoro da murna da ta ba Majalisar mamaki.BJ 157.1
Luther ya ce, “Ya sarki mai-hankali kwance, manyan ‘ya’yan sarki, masu-sarauta da alheri, na bayana a gabanku yau bisa ga umurnin da aka ba ni jiya, kuma da jin kan Allah ina rokon mai-martaba, da ku masu girma, ku saurari kariyar matsayin da na tabbata daidai ne kuma gaskiya ce. Idan, ta wurin jahilci, na ketare al’adu da kaidodin fada, ina rokonku ku yafe ni; domin ba a girmar da ni a fadar sarakuna ba, amma a ware cikin unguwar masu zaman zuhudu.”BJ 157.2
Sa’an nan, game da tambayan, ya ce rubuce rubucensa da aka wallafa ba iri daya ba ne. A wadansu ya yi magana kan bangaskiya da kyawawan ayuka ne, kuma ko magabtansa ma sun ce suna da anfani, bayan ba su da illa. Janye wadannan zai zama rushe gaskiyan da duka aka yarda da shi. Kashi na biyu din rubuce rubuce ne da suka bayana lalacewa da kuma cin zarafin da tsarin paparuma ke yi. Janye wadannan zai karfafa zaluncin Rum, ya kuma kara bude babbar kofa ga manyan rashin ibada masu yawa. A kashi na ukun, ya zargi mutane da suka goyi bayan muguntan da ake yi ne. Game da wadannan ya yarda cewa ya yi anfani da karfin da ya wuce kadada. Bai ce ba shi da laifi ba, amma ko wadannan litattafan ma ba zai iya janyewa ba, domin yin haka zai karfafa magabtan gaskiya, sa’an nan za su yi anfani da zarafin nan su murkushe mutanen Allah da zalunci mafi muni.BJ 157.3
“Duk da haka, ni mutum ne kawai, ba Allah ba,” Luther ya ce; “sabo da haka zan kare kai na yadda Kristi Ya yi: ‘Idan na fadi mugunta, ku ba da shaidar muguntar.... Ta wurin jinkan Allah, ina rokonku, ya sarki mai-hankali shifidadde, da ku, masu sarauta da alheri, da dukan mutane kowane iri, ku nuna daga rubuce rubucen annabawa da manzani cewa na yi kuskure. Da zaran na gamsu da wannan zan janye kowane kuskure, in kuma zama na farko da zan dauki littattafai na in jefa su cikin wuta.”BJ 158.1
“Abin da na fada yanzun nan, ina fata ya nuna cewa a hankali na yi la’akari da hatsarin da nake jefa kai na ciki, amma maimakon karaya, ina farin ciki ganin cewa bishara yanzu, kamar da, ta zama sanadin damuwa da gardama. Wannan shi ne yanayi da kadarar maganar Allah. Yesu Ya ce, ‘Ban zo domin in kawo salama a duniya ba, sai dai takobi.’ Allah Mai-al’ajibi ne da ban tsoro cikin al’amuransa; a yi hankali kada garin neman murkushe gardama ku tsananta ma maganar Allah, har ku jawo ma kanku ambaliyar matsaloli na matsifu da hallaka ta har abada.... Zan iya ambaton misalai daga maganar Allah. Zan iya magana game da su Fir’auna da sarakunan Babila, da na Isaraila, wadanda ayukan su na neman karfafa mulkinsu sun taimaka wajen jawo hallakarsu. ‘Allah yana tura manyan tsaunuka amma su basu sani ba.’ ”BJ 158.2
Luther ya yi magana da harshen Jamusanci ne; yanzu kuma aka ce ya maimaita kalmomi dayan da Helenanci. Ko da shike maganan da ya fito yi ta gajiyar da shi, ya yarda dai, ya kuma yi jawabinsa sarai, da karfi kaman na farkon. Ikon Allah ne ya bi da wannan al’amarin. Da farko kuskure da camfi sun rufe idanun mutane da yawa daga ‘ya’yan sarki da yadda basu ga ma’anar maganar Luther ba; amma maimaitawar ta sa sun gane sarai abin da ya fada.BJ 158.3
Wadanda cikin taurin kai suka rufe idanunsu daga hasken, suka kuma nace cewa ba za su karbi gaskiyar ba, sun fusata da karfin maganar Luther. Da ya gama magana, mai-magana a madadin Majalisar, cikin fushi ya ce: “Ba ka amsa tamabayar da aka yi maka ba.... Ana bukatar ka ka ba da amsa sarai gajeruwa kuma.... za ka janye ko babu?”BJ 159.1
Luther ya amsa: “Da shike mai-martaba da ku masu girma kuna bidar amsa sarai mai sauki, gajeruwa kuma, zan ba ku, kuma ita ce: ba zan ba da bangaskiya ta ga paparuma ko majalisu ba, domin a bayane yake cewa sau da yawa sun yi kuskure, suka kuma yi sabani da juna. Sabo da haka in ba an gamsar da ni ta wurin shaidar Littafi ko fasara mafi-saukin ganewa ba, in ba an fahimtar da ni ta waurin nassosi da na ambata ba, sa’an nan kuma in ba ta wurin haka sun daura lamirina da maganar Allah ba, ba zan iya janyewa ba, kuma ba zan janye ba, domin kasada ce ga Kirista ya yi magana sabanin lamirinsa. Nan na tsaya ba zan iya yin wani abu dabam ba; bari Allah Ya taimake ni. Amin.”BJ 159.2
Hakanan adalin nan ya tsaya kan tabbatacen tushe, watau maganar Allah. Hasken sama ya haskaka fuskarsa. Girman sa da tsabtar halinsa, salamar sa da murnar zuciyarsa, sun bayana ga kowa yayin da yake ba da shaida sabanin kuskure ya kuma shaida fifikon bangaskiyan nan da ke da nasara bisa duniya.BJ 159.3
Dukan majalisar ta yi shuru na wani lokaci sabo da mamaki. A amsar sa ta fari, Luther ya yi magana da murya mara-karfi, da ban girma kuma. ‘Yan Rum din suka mai da wannan alamar cewa karfin halinsa ya fara kasawa kenan. Sun dauka cewa rokon karin lokaci da ya yi da farko hanya ce da za ta kai ga janyewarsa. Charles da kansa da ya lura cikin reni cewa da gajiya a jikin Luther, da suturar sa mara tsada, da kuma saukin jawabinsa, ya ce: “Mai zaman zuhudun nan ba zai ta ba mai da ni mai-ridda ba.” Jaruntaka da naciya da ya nuna, da kuma karfi da saukin ganewar maganarsa, sun cika kowa da mamaki. Babban sarkin, cike da yabawa, ya ce: “Wannan mai-zaman zuhudun yana magana da karfin zuciya.” Da yawa daga cikin yayan sarkin Jamus suka kalli wannan wakilin na kasar su da alfarma da farin ciki kuma.BJ 159.4
An yi nasara bisa masu goyon bayan Rum; an nuna munin tasirinsu. Sun so su rike ikonsu ba ta wurin anfani da Littafin ba, amma ta wurin anfani da barazana, yadda Rum ta saba. Kakakin Majalisan ya ce: “Idan ba ka janye ba, babban sarki da jihohin kasar za su yi shawara su ga matakin da za a dauka game da mai-ridda da ya ki tuba.”BJ 160.1
Abokan Luther da suka saurari kariyarsa cikin farinciki, suka yi rawan jiki da jin maganan nan; amma Luther kansa, cikin kwanciyar hankali ya ce: “Bari Allah Ya zama mai-taimakona, gama bazan janye komi ba.” BJ 160.2
Aka umurce shi ya fita daga Majalisar, yayin da ‘ya’yan sarkin suka shiga shawara. An dauka cewa babban tashin hankali ya zo. Nacewar Luther cewa ba za ya janye ba zai iya shafar tasirin ekklesiya har sararraki. Sai aka yarda cewa za a ba shi dama ta karshe domin ya janye. Aka kawo shi cikin Majalisa, kawowa na karshe. Aka sake tambayarsa ko zai janye koyaswoyinsa. Ya ce: “Ba ni da wata amsa da zan bayar, da bam da wadda na rigaya na bayar.” Ya bayana a fili cewa ba za a iya lallabar sa, ko ta wurin alkawura ko barazana, cewa shi amince da tsarin Rum ba.BJ 160.3
Shugabannin tsarin paparuman suka fusata domin wani mai-zaman zuhudu kawai ya rena ikon nan nasu da yakan sa sarakuna da fadawa su yi rawan jiki; suka yi begen sa shi ya gane fushinsu tawurin azabtar da shi har mutuwa. Amma Luther, duk da sanin wannan hatsari, ya yi magana da dukansu da martaba, cikin kwanciyar hankali. Maganarsa babu girman kai ko fushi ko rudewa. Ya rigaya ya manta kansa, da manyan mutanen da suka kewaye shi, ya kuma ji kawai cewa yana tare da wanda Ya fi su paparuma, da priestoci da sarakuna, da manyan sarakuna. Kristi Ya rigaya Ya yi magana ta wurin jawabin Luther, da iko tare da martaban da ya kawo ma abokai da magabta ma bangirma da mamaki. Ruhun Allah Yana cikin wannan Majalisar a lokacin, Yana aiki cikin zukatan manyan kasar. Da yawa cikin ‘ya’yan sarkin sun yarda da matsayin Luther, ba tsoro. Da yawa sun amince da gaskiyar; amma ga wadasu, koyaswan da suka samu bai jima a cikinsu ba. Akwai wadansu kuma da basu bayana amincewarsu a lokacin ba, amma bayan sun bincika Littafin da kan su, daga baya suka nuna nasu goyan bayan Canjin ba da tsoro ba.BJ 160.4
Mai-zabe Fredrick ya yi ta begen bayanuwar Luther a gaban Majalisar, kuma da marmari ya saurari jawabinsa. Da alfarma da farincki ya ga karfin hali da naciya da kwanciyar hankalin likitan, har ma da kasancewarsa a shirye ya kara kare kansa. Ya bamabanta masu jayayyar, ya kuma ga cewa an wofinta hikimar paparuma da sarakuna da prietoci ta wurin karfin gaskiya. Tsarin paparuma ya sha kaye ta yadda dukan al’ummai a dukan sararraki kuma za su sami labari.BJ 161.1
Sa’an da jakadan ya ga sakamakon da jawabin Luther ya haifar, ya ji irin tsoron da bai taba ji ba, sabo da tsoron ikon Rum, ya kuma dauki kuduri zai yi duk abin da zai iya domin tabbatar da cewa an kawar da Luther. Da duk iya magana da kwarewar jakadanci da ya yi fice akai, ya nuna ma babban sarkin wauta da hadarin sadakar da abota da goyon bayan mulkin Rum wai don wani mai-zaman zuhudu kawai da bai isa komi ba.BJ 161.2
Maganar sa ta yi tasiri. Bayan amsar Luther, washegari Charles ya sa aka kai ma Majalisar sako cewa shi zai ci gaba da tsarin magabatansa na tabbatarwa da kuma kare addinin Katolika. Da shike Luther ya ki janye kurakuransa, za a yi anfani da matakai mafi tsanani a kansa da riddan da yake koyarwa. “Mutum daya mai-zaman zuhudu wanda wautarsa ta batar da shi, ya ta da jayayya stakanin sa da dukan Kirista. Domin hana wannan rashin ibadar, zan sadakar da mulkoki na, da dukiya ta, da abokai na, da jiki na, da rai na, da ruhu na. Ina gaf da wofinta Luther, in hana shi jawo ma mutane rikici; zan kuma tuhume shi da masu binsa, masu ridda da laifin rena hukuma, a hukumta su da warewa, da horo da kowace hanya da za ta hallaka su. Ina kira ga dukan membobin jihohi su yi kamar amintattun Kirista.” Duk da haka babban sarki ya ce dole a cika da alakawalin nan na tsaron Luther, kuma kafin a fara tuhumarsa, dole a yarda mashi ya shiga gidan shi lafiya. BJ 161.3
Membobin Majalisan fa suka fito da ra’ayi biyu masu sabani da juna. Yan sako kuma wakilan paparuma, suka sake cewa a yi watsi da zancen alkawalin tsaron lafiyar Luther. Suka ce, “Ya kamata Kogin Rhine ya karbi tokarsa, yadda ya karbi tokar Huss karni guda da ya wuce.” Amma ‘ya’yan sarkin Jamus, ko da shike su ma ‘yan paparuma ne, magabtan Luther kuma, suka ce ba za su yarda su jawo ma Jamus da babban sarkin su maimaicin wadannan matsalolin ba.BJ 162.1
Amsar Charles kan sa ga mumunan ra’ayin nan it ace, “Ko da an kawar da girma da aminci daga dukan duniya, dole girma da aminci su sami mafaka a zukatan ‘ya’yan sarki.” Magabtan Luther dai suka kara matsa cewa ya yi ma Luther abin da Sigismund ya yi ma Huss, ya ba da shi a hannun ekklesiya; amma sa’an da ya tuna lokacin da Huss a gaban jama’a ya nuna ma kowa sarkokin, sa ya kuma tuna ma sarki matsalar imaninsa, Charles ya ce: “Ba zan so in yi ajiyar zuci kamar Sigismund ba.”BJ 162.2
Amma kuma Charles ya rigaya ya ki gaskiyan da Luther ya bayana. Ya rubuta cewa: “Na dauki kuduri zan bi kwatancin ubani na.” Ya kudurta cewa ba zai kauce daga al’ada ba, ko domin ya bi hanyoyin gaskiya da adalci ma. Da shike ubaninsa sun goyi bayan tsarin paparuma, shi ma zai goyi baya, da dukan zaluncin ta da lalacewar ta. Hakanan ya ki karban duk wani haske da ya fi wanda ubaninsa suka karba, ko kuma ya yi wani abin da su basu yi ba.BJ 162.3
Akwai mutane da yawa yanzu da ke manne ma al’adun iyayensu. Sa’an da Ubangiji ya aika masu Karin haske, sukan ki karban shi, domin da shi ke ba a ba iyayen su ba, iyayen basu karba ba. Ba a ajiye mu inda iyayen mu suke ba; sabo da haka aikinmu da bukatunmu ba daidai ne da nasu ba. Allah ba zai gamsu da cewa muna duban kwatancin ubaninmu domin mu san aikin da ya rataya a wuyanmu, maimakon binciken maganar gaskiya ma kanmu ba. Aikin da ke kanmu ya fi wanda yake kan iyayenmu. Za mu ba da lissafin hasken da suka karba, wanda aka mika mana gado, kuma za mu ba da lissafin Karin hasken da ke haskaka mu daga maganar Allah. BJ 163.1
Game da Yahudawa marasa ba da gaskiya Kristi Ya ce: “Da ban zo na yi masu magana ba, da ba su da zunubi ba, amma yanzu ba su da hujjar zunubinsu ba.” Yohanna 15:22. Ikon Allah dayan ya yi magana ta wurin Luther zuwa ga babban sarki da yaran sarkin Jamus. Kuma yayin da hasken ya haskaka daga maganar Allah, Ruhunsa Ya yi roko na karshe ga mutane da yawa a Majalisar. Yadda Bilatus, daruruwan shekaru da suka gabata, ya bar fahariya da farin jini suka rufe zuciyarsa daga Mai-fansar duniya; yadda firgitacen Filikus ya ce ma dan sakon gaskiya: “Tafi dai yanzu, sa’an da na sami zarafi, na kirawo ka,” yadda Agaribas ya amsa, “Da kankanuwar rinjayaswa kana so ka maishe ni Christian” (Ayukan 24:25; 26:28), duk da haka suka juya ma sakon Allah baya, haka Charles V, sabo da alfarmar duniya da manufofin tafiyar da gwamnati, ya ki hasken gaskiya. BJ 163.2
An yayata jita jitan shirye shiryen da ake yi game da Luther, wanda ya jawo rashin kwanciyar rai ko ina a birnin. Luther ya rigaya ya yi abokai da yawa wadanda, da sanin zaluncin Rum ga dukan masu jayayya da halayyanta, suka dauki kuduri cewa ba za a sadakar da shi ba. Daruruwan fadawa suka dauki alkawalin tsaron sa. Da yawa suka kushe sakon sarkin a matsayin nuna amincewa da kasancewa kalkashin ikon Rum. Aka rika manna sakoni a kofofin gidaje da gine ginen gwamnati, wadansu suna yabon Luther, wadansu kuma suna sokar sa. Waninsu ya rubuta maganar mai-hikiman nan ne, cewa: “Kaiton ki kasa, sa’an da sarkin ki yaro ne.” Mai-wa’azi 10:16. Karbuwan da aka nuna ma Luther ko ina a Jamus ya tabbatar ma babban sarkin da Majalisar cewa duk wani rashin adalci da aka nuna masa zai lalata salamar kasar da karkon gadon sarautan ma.BJ 163.3
Fredrick na Saxony ya kame kansa, a hankali kuma ya boye son Luther da yake da shi, yana kuma tsaronsa sosai ba ja da baya, yana lura da take taken sa da na magabtansa. Amma da yawa basu boye goyon bayansu ga Luther ba. ‘Ya’yan sarki da hakimai da masu unguwa da sauran sanannun mutanen ekklesiya da na waje, sun rika ziyartarsa. Spalatin ya rubuta cewa: “Dan kankanin dakin likitan bai iya daukan dukan masu ziyartar sa ba.” Suka rika ganin sa kaman ya fi dan Adam ma. Ko wadanda basu gaskata koyaswarsa ba dole suka yi sha’awar amincin da ya sa shi ya gwammaci mutuwa maimakon ketare lamirinsa.BJ 164.1
An yi kokari sosai a sa Luther ya sasanta da Rum. Fadawa da ‘ya’yan sarki suka ce masa idan ya nace yana gwada ra’ayin sa da na ekklesiya da na majalisu, ba da jimawa ba za a kore shi daga kasar, kuma ba zai sami kariya ba.... Luther ya amsa cewa: “Ba za a iya shelar bisharar Kristi ba tare da bata ma wani rai ba.... Don me tsoron hatsari zai raba ni da Ubangiji, kuma daga maganarsa wadda it ace kadai gaskiya? Babu, gwamma in sadakar da jiki na, da jini na, da rai na.”BJ 164.2
An kuma sake matsa mashi ya amince da ra’ayin babban sarkin, sa’an nan ba abin da zai same shi. Ya kuwa amsa: “Na yarda da dukan zuciya ta cewa babban sarkin, da ‘ya’yan sarkin, har ma da Kirista mafi mugunta su bincika, su kuma auna rubuce rubuce na; amma bisa sharadi daya, cewa maganar Allah ta zama ma’auninsu. Mutane ba su da abin yi sai dai biyayya ga maganar Allah. Kada ku bidi ketarewar lamiri na wanda ke daure da sarka cikin Littafi Mai-Tsarki.”BJ 165.1
Game da wata sahwarar ya ce: “Na yarda in sallamar da alkawalin tsaro na, na sa jiki na da rai na a hannun babban sarki, amma ba zan taba sallamar da maganar Allah ba!” Ya ce yana shirye ya amince da hukumcin majalisar, amma fa idan majalisar za ta yanke hukumcin bisa ga Littafi. “Game da abin da ya shafi maganar Allah da imani, kowane Kirista ya isa ya yanka hukumci daidai da paparuma, ko da majalisu miliyan guda ne suke goyon bayan paparuma din.” Da abokai da magabta duka suka gane dai duk wani kokarin sasantawa ba zai yi anfani ba.BJ 165.2
Da Luther ya yarda da abu daya, da Shaitan da rundunansa sun yi nasara. Amma naciyar sa ce ta zama hanyar yantarwar ekklesiya da farawar sabuwar sara mafi kyau. Tasirin mutum dayan nan wanda ya yi tunani don kansa game da addini ya kuma aikata, ya shafi ekklesiya da duniya, ba a zamaninsa kadai ba, amma har dukan sararraki da suka biyo baya. Naciyarsa da amincinsa za su karfafa kowa, har karshen lokaci, duk wanda zai wuce ta irin yanayin nan kuwa. Ikon Allah da martabansa sun tsaya fiye da shawarar mutane, fiye da yawan ikon nan na Shaitan ma.BJ 165.3
Ba da jimawa ba, babban sarki ya umurci Luther ya koma gida, ya kuma san cewa za a bi wanna da hukumtawarsa maza maza. Ya fuskanci barazana, amma yayin da ya tashi daga Worms, zuciyar sa ta cika da murna da yabo. Ya ce: “Iblis kansa ne tsare dakin yakin papruma, amma Kristi Ya huda shi, aka kuma tilasta Shaitan ya yarda cewa Ubanfiji Ya fi shi.” BJ 165.4
Lokacn tafiyarsa, don dai kada a ga naciyarsa kamar tawaye ne, Luther ya rubuta ma babban sarkin cewa: “Allah wanda Shi ne Mai-karanta zukata Shi ne Shaida na, cewa ina shirye da gaske in yi biyayya gare ka mai-martaba, cikin daraja da cikin rashin daraja, cikin rai ko cikin mutuwa, kuma in ceci maganar Allah, wanda tawurin sa mutum yake rayuwa. Cikin dukan al’amuran rayuwan yanzu, aminci na ba zai raunana ba, domin a nan yin nasara ko riba ba wani abu ba ne game da ceto. Amma idan ana zancen al’amura na har abada, Allah ba Ya so mutum ya dogara ga mutum. Da shike dogara ga mutum a sha’anin ruhaniya ainihin sujada ne, kuma Mahalici ne kadai Ya cancanta a yi masa sujada.”BJ 166.1
Cikin tafiyarsa daga Worms, Luther ya sami karbuwa fiye da wanda ya samu lokacin tafiyarsa can. Manyan ma’aikatan ekklesiya suka marabci mutumin nan da ekklesiya ta ware, shugabannin gwamnati kuma suka girmama mutumin da babban sarki ya hukumta. Aka roke shi ya yi wa’azi kuma, ko da shike babban sarkin ya hana, ya sake hawa bagadi. “Ban taba yin alkawalin kulle maganar Allah ba, kuma ba zan taba yi ba.”BJ 166.2
Bai dade da barin Worms ba, ‘yan paparuma suka sa babban sarkin ya ba da doka game da shi. Cikin dokar, an ce Luther “Shaitan ne da kansa cikin kamanin mutum, yafe da tufafin mai-zaman zuhudu.” Aka umurta cewa da zaran alkawalin tsaron sa ya kare, sai a dauki matakan tsayar da aikinsa. Aka hana kowane mutum yin harka da shi, ko ba shi abinci ko abin sha, ko taimaka masa ta wurin magana ko ayuka, cikin jama’a ko a boye. Aka kuma ce a kama shi duk inda yake, a mika ma hukuma. A kuma sa masu bin sa a kurkuku, a kwace dukiyarsu. A hallaka rubuce rubucensa, a karshe kuma, dukan wadanda suka ketare wannan doka suna kalkashin hukumcin dokar. Mai-zaben Saxony da ‘ya’yan sarki masu goyon bayan Luther sun bar Worms jima kadan bayan tafiyar Luther, dokar babban sarkin kuma ta sami goyon bayan Majalisar. Yanzu kuma yan paparuma suka yi murna. Sun dauka cewa karshen Canjin ya tabbata.BJ 166.3
Allah Ya rigaya Ya tanada ma bawansa hanyar tsira a wannan sa’ar hatsarin. Idon da ba ya barci ya dinga bin Luther duk inda ya je, wani mai-zuciyar gaskiya da martaba ya dauki kudurin kubutar da shi. Sanin kowa ne cewa Rum ba za ta gamsu da komi ba sai mutuwarsa; ta wurin boye shi ne kadai za a iya raba shi da bakin zaki: Allah Ya ba Fredrick na Saxony hikimar yin tsarin da ya kiyaye Luther. Da goyon bayan abokai na gaskiya aka aiwatar da manufar mai-zabe Fredrick, aka kuma boye Luther daga abokai da magabta. Cikin tafiyarsa zuwa gida aka kwace shi, aka raba shi da masu rakiyarsa, aka kuma bi da shi ta jeji maza maza zuwa babban sansanin Wartburg. Al’ajibai sun bi kwacewan nan nasa da boyewar sa, ta yadda har shi Fredrick kan sa ya dade yana tababar inda aka kaishi. Rashin sanin nan ma daidai ne, domin muddan dai mai-zaben bai san inda Luther yake ba, ba zai iya fada ma wani ba. Ya dai gamsu cewa Luther yana cikin tsaro, wannan kuma ya ishe shi.BJ 167.1
Bazara da damina da kaka suka wuce, rani kuma ya zo, Luther dai yana tsare. Aleander da magoya bayansa suka ji dadi suna gani kamar hasken bishara ya kusan mutuwa. Amma maimakon haka, Luther ya yi ta cika fitilarsa ne daga rumbun gaskiya; haskenta kuma zai kara karfi.BJ 167.2
A sansanin tsaron nan na Wartburg, ya ji dadin sakewarsa daga zafin yaki da hayaniyarta. Amma bai dade yana jin dadin hutun ba. Da shi ke ya saba da aiki da kuma zafin jayayya, bai iya jimre hutu ba. A wannan lokacin kadaicin, yanayin ekklesiya ya zo zuciyarsa, sai ya ta da murya ya ce: “Kash! Babu wani a wannan ranar karshe ta fushinsa, da zai tsaya kamar ganuwa a gaban Ubagiji, ya ceci Israila!” sai tunaninsa ya dawo wurinsa kuma, ya ji tsoron cewa za a zarge shi da cewa matsoraci ne shi, da shike ya gudu daga fadar. Sai ya tsauta ma kansa sabo da kiwuyarsa da son kansa. Duk da haka kowace rana ya rika yin ababan da mutum daya ba zai iya yi ba. Alkalaminsa bai taba hutawa ba. Yayin da magabtansa ke rudin kansu cewa an rufe bakinsa, sun yi mamaki suka kuma firgita ganin alamun cewa yana kan aikinsa. Rubuce rubucensa sun yadu ko ina a Jamus. Ya kuma yi ma ‘yan kasarsa babban hidima ta wurin juya Sabon Alkawali zuwa harshen Jamusanci. Daga dutsensa, misalin Pathmos, ya kusa shekara guda yana shelar bishara, yana kuma tsautawa game da kura-kuran zamanin.BJ 167.3
Amma ba domin kare Luther daga fushin magabtansa ne kadai, ko kuma domin a ba shi lokaci don yin muhumman ayukan nan ne kadai, Allah Ya janye bawan Shi daga rayuwa cikin jama’a ba. Akwai manufofin da suka fi wadnnan. A boyayyen wurin nan na kadaici, an dauke Luther daga taimako na duniya, aka boye shi daga yabo na duniya. Ta hakanan aka cece shi daga alfarma da dogara ga kansa, wanda nasara takan iya jawowa. Ta wurin wahala da kaskantarwa, an shirya shi domin ya sake tafiya kan tafarkin da an rigaya an kai shi. BJ 168.1
Yayin da mutane ke murna cikin yancin da gaskiya ke kawo masu, sukan so su daukaka wadanda Allah Ya yi anfani da su domin su tsinke sarkokin kuskure da camfi. Shaitan yana kokarin janye tunanin mutane daga Allah, ya kai su kan mutane. Yakan sa su girmama kayan aikin, su kuma manta da Hannun da ke bi da kowane al’amari. Sau da yawa shugabannin addini da ake yaba masu ana kuma daukaka su, sukan manta dogararsu ga Allah har su dogara ga kansu. Sakamakon wannan, sukan so su mallaki zukata da lamirin mutanen da ke so su nemi bishewa daga gare su, maimakon meman bishewa daga maganar Allah. Aikin canji yakan sami koma baya sabo da irin ruhun nan. Allah Ya tsare aikin Canji daga wanan hatsarin. Ya so aikin ya sami hatimin Allah ne, ba na mutum ba. Zukatan mutane sun koma wurin Luther a matsayin mai-bayana gaskiyar; an cire shi domin dukan idanu su koma ga Tushen gaskiya na har abada.BJ 168.2