Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 21—Gargadin da Aka Ki

    Cikin wa’azin koyaswar zuwan Yesu na biyu. William Miller da abokansa sun yi aikin da niyyar falkar da mutane ne su shirya domin hukumcin. Sun so su falkar da masu addini ne ga ainihin begen ekklesiya da kuma bukatarsu ta kara zurfin Kiristancinsu; sun kuma yi aikin domin falkar da wadanda basu tuba ba don bukatarsu ta tuba ga Allah nan da nan. “Basu yi kokarin tubar da mutane zuwa wata darika ko kungiyar addini ba. Dan haka sun yi aiki cikin dukan dariku da kungiyoyi, ba tare da tsoma baki cikin tsarin su ba.”BJ 373.1

    Miller ya ce: “Cikin dukan aikina, ban taba sha’awa ko tunanin kafa wata kungiya dabam da darikun da suke nan ba, ko kuma in ba wani fifiko bisa wani ba. Na so duka su anfana ne. Da shike na zata cewa dukan Kirista za su yi murna game da zuwan Yesu, kuma cewa wadanda ba sa gani kamar yadda ni ke gani ba za su ki jinin wadanda za su rungumi koyaswar ba, ban zata za a taba bukatar tattaruwa dabam dabam ba. Nufi na kawai in tubar da mutane zuwa wurin Allah ne, in sanar da duniya cewa hukunci yana zuwa, in kuma motsa mutane su shirya zukatansu ta yadda za su iya saduwa da Allahnsu cikin salama. Yawancin wadanda suka tuba sakamakon aiki na, sun shiga ekklesiyoyin da ke akwai ne.”BJ 373.2

    Sa’an da aikinsa ya fara inganta ekklesiyoyi, an goyi baya sa. Amma sa’anda ma’aikatan bishara da shugabannin addini suka dauki mataki sabanin koyaswar zuwan Kristi din, suka kuma so su danne kowane kokari na ta da batun, ba daga bagadi kadai suka yi hamayya da shi ba, amma suka kuma hana membobinsu damar halartar wa’azi game da zuwan Yesu na biyu, ko ma yin magana game da begensu a cikin ekklesiya. Ta hakanan masu bada gaskiya suka iske kansu cikin mumunan gwaji da rudewa. Sun kaunaci ekklesiyoyinsu, ba sa kuma so su rabu da su; amma yayin da suka ga an danne shaidar maganar Allah aka kuma hana su ‘yancin su na bincike annabci, suka ga cewa biyayya ga Allah ya hana su amincewa. Suka ga cewa ba za su iya gani wadanda suka so su kulle shaidar magana kamar ekklesiyar Kristi, “madogara da dalilin dukan gaskiya ba.” Sabo da haka suka ji kawai ya kamata su rabu da kungiyoyinsu na da. Cikin bazarar 1844, wajen mutum dubu hamsin suka fice daga ekklesiyoyin. Wajen wannan lokacin an sami canji mai-yawa cikin yawancin ekklesiyoyi ko ina a Amerika. An yi shekaru da dama ana samun karin daidaituwa da ayukan duniya da alladunta, da kuma lalacewar ainihin rayuwa ta ruhaniya; amma a waccan shekarar an sami shaidar raguwa mai yawa na membobi cikin kusan dukan ekklesiyoyin kasar. Ko da shike ba wanda ya gane dalilin, ko ina an gane cewa hakan ya faru, aka kuma dinga sharhi a kan lamarin a masujadu da haridu.BJ 374.1

    A wani taron ekklesiya a Filadalfia, Mr. Barnes, wanda ya wallafa wani kundin sharhi da ko ina aka yi anfani da shi, kuma paston daya daga cikin manyan ekklesiyoyin birnin, “ya furta cewa yana aikin bishara har shekara ashirin, kuma ban da jibin da ya wuce, bai taba ba da jibi, a ce ba a sami karuwa ko raguwa a cikin ekklesiyar ba. Amma yanzu ba falkaswa, ba tuba, ba alamar ingantuwar alheri cikin masu bi, kuma ba wanda ke zuwa wurinsa domin hira game da ceton rayukansu. Idan jari da kasuwanci da masana’antu suka karu, son abin duniya yakan karu.BJ 374.2

    A watan Fabrairu na shekara dayan, shehun mallami Finney na Oberlin College ya ce: “Muna da tunanin nan a zukatan mu cewa ekklesiyoyin kasarmu masu Kin ikon paparuma, ko basu kula ba, ko kuma sun yi gaba da kusan dukan halayyan kirki na zamanin. Ban da wadansu dai, amma yawanci haka din ne. Muna kuma da wani tabbatacen dalili, watau rashin tasirin farkaswa cikin ekklesiyoyin, ko ina. Sanyin ruhaniya kusan ko ina ne, kuma ya yi zurfi da yawa; haka masu watsa labarum dukan kasar ke fadi.” Membobin ekklesiya da yawa suna zama masu bautar ado, suna hada hannu da marasa tsoron Allah suna shagulgulan jin dadi, da rawa da bukukuwa, da dai sauran su,… Amma bai kamata mu fadada wannan batu mai kawo bacin rai ba. Akwai shaida dai da ke karuwa cewa ekklesiyoyi suna kara lalacewa ne, abin bakinciki. Sun yi nisa da Ubangiji, shi kuma Ya janye kan sa daga gare su.”BJ 375.1

    Kamar yadda mawallafin majalla mai-suna Religious Telescope ya rubuta, “Ba mu taba ganin lalacewar addini irin na yanzu ba. Hakika, ya kamata ekklesiya ta falka, ta bincika dalilin wannan bala’in; gama dole kowane mai-kaunar Sihiyona ya gan shi kamar bala’i. Idan muka yi la’akari da yadda mutane kalilan ne suke tuba jefi jefi, da kuma rashin tuba da taurin kan masu zunubi, irin da ba a taba gani ba, za mu kusan ihu mu ce: “Ko Allah ya manta yin alheri ne? ko kuma, Ko an rufe kofar jinkai ne?BJ 375.2

    Irin wannan yanyin ba ya aukuwa sai in da dalili cikin ekklesiya kanta. Duhun ruhaniya da kan fado ma kasashe da ekklesiyoyi da mutane ba don janyewar alherin Allah ba ne yakan faru, amma don kyalewa ko kuma kin hasken Allah ne da mutane sukan yi. Akwai misalin wannan cikin tarihin Yahudawa a zamanin Kristi. Ta wurin mannewarsu ma duniya da mantawa da Allah da maganarsa, gamsuwarsu ta duhunta, zukatansu suka zama na duniya da son sha’awa. Ta hakanan suka jahilci zuwan Masiyan, kuma cikin fadin ransu da rashin bangaskiyarsu, suka ki Mai-fansar. Ko a wancan lokacin ma Allah bai datse al’ummar Yadudawan daga sani ko sa shiga cikin albarkun ceto ba. Amma wadanda suka ki gaskiyar sun rasa sha’awar kyautar Allah. Sun mai da duhu haske, haske kuma duhu, har sai da hasken da ke cikinsu ya zama duhu; duhu mai yawa kuwa!BJ 375.3

    Shaitan yana so mutane su rike alamun addini muddan dai ba su da ruhun ibada na kwarai. Bayan sun ki bisharar, Yahudawan suka ci gaba da rike al’adun su na da, suka kiyaye rashin cudanyansu da sauran mutane, alhali dukansu sun amince cewa kasancewan Allah ba ya tare da su kuma. Annabcin Daniel ba kuskure ya bayyana lokacin zuwan Masiyan, ya kuma yi annabcin mutuwarsa kai tsaye, ta yadda su kuma suka hana yin nazarinsa, a karshe kuma mallamansu suka furta la’ana kan dukan wanda ya yi kokarin sansance lokacin. Cikin makanta da rashin tuba mutanen Israila cikin sararaki na biye sun nuna halin kin kulawa da tayin ceto da ake masu, basu damu da albarkun bishara ba, ga kashedi mai ban tsoro kuma game da hatsarin kin haske daga sama.BJ 376.1

    Duk inda dalili yake, sakamako dayan ake samu. Duk wanda da gangan ya bice lamirin sa game da abinda ya kamata yayi, don kawai bi je daidai da muradin zuciyar sa ba, a karshe zai kasa bambantawa stakanin gaskiya da kuskure. Ganewarsa za ta duhunta, lamiri ya kangare, zuciyata taurara, har mutumin ya rabu da Allah. Idan aka yi banza da sakon Allah, ekklesiya takan nannadu cikin duhu, bangaskiya da kauna sukan yi sanyi, tsatsaguwa kuma takan shigo. ‘Yan ekklesiya sukan kallafa ransu ga kayan duniya, masu zunubi kuma su taurara cikin rashin tuba.BJ 376.2

    Sakon malaika na fari na Ruya 14 da ke shelar sa’ar hukumcin Allah, yana kuma kiran mutane su ji tsoron Allah, su yi masa sujada, an shirya shi ne ya raba mutanen Allah, su yi masa sujada. An shirya shi ne ya raba mutanen Allah daga tasirin lalacewa na duniya, ya kuma falkas da su su ga ainihin yanayinsu na zunubi da sanyin ruhaniya. A wannan sakon, Allah Ya aika ma ekklesiya gargadi wanda da an karba, da ya gyarta muguntan da yake raba su da shi. Da sun karbi sakon nan daga sama, suka kaskantar da kansu a gaban Ubangiji, suna kuma bidar shiri domin tsayawa a gabansa, da Ruhun Allah da ikonsa sun bayana a cikinsu. Da ekklesiya kuma ta sake samun hadin kai da bangaskiya da kaunan nan da ta kasance da su a zamanin manzanin, lokacin da masu bi suka kasance “zuchiyarsu da ransu kuma daya,” kuma “suka fadi maganar Allah da karfin zuchiya,” sa’an da Ubangiji kuma “yana tattarawa yau da gobe wadanda ake chetonsu,” Ayukan 4:32, 31; 2:47.BJ 377.1

    Idan mutanen Allah za su karbi hasken da ke haskaka su daga maganarsa, za su kai ga dayantakan nan da Kristi ya yi addu’a su samu, wadda manzon ya bayyana kamar “danyantuwar Ruhu chikin damrin salama.” Ya ce: “Akwai jiki daya, da Ruhu daya, kamar yadda aka kiraye ku kuma chikin begen nan daya na kiranku, Ubangiji daya, imani daya, baptisma daya.” Afisawa 4:3-5.BJ 377.2

    Irin sakamakon da wadanda suka karbi sakon zuwan Kristi suka samu ke nan. Sun fito dariku dabam dabam, aka kuma watsar da bambancin darika a kasa, aka kacancana bambancin koyaswa suka zama burbushi, aka yi watsi da begen nan na wadansu shekaru dubu a duniyan nan, aka grarta ra’ayoyin karya game da zuwan Kristi na biyu, aka share girman kai da sajewa da duniya, aka gyara kurakurai; zukata suka hadu cikin zumunci mafi dadi, kauna da murna kuma suka yawaita. Da shike koyaswan nan ta yi dukan wadannan ga kalilan da suka karbe ta, da kowa ya karbe ta ma da ta yi ma kowa hakanan ma.BJ 377.3

    Amma yawancin ekklesiyoyin basu karbi gargadin ba. Ya kamata da shugabanninsu ne suka fara gano alamun zuwan Yesu, amma suka kasa gane gaskiyar, ko daga annabci ko kuma daga alamun zamanai. Sa’anda buri da begen abin duniya suka cika zuciya, kaunar Allah da bangaskiya ga maganarsa sun yi sanyi, kuma sa’anda aka yi shelar koyaswar zuwan Yesu, ya ta da kiyayarsu da rashin bangaskiyarsu ne kawai. Da shike galibi masu sa kai ne suka yi wa’azin sakon, aka ce wannan ya nuna gazawar sakon. Kamar da, aka tare bayyananiyar shaidar maganar Allah da tambaya cewa: “A chikin hakimai, ko chikin Farisawa, akwai wadanda sun ba da gaskiya gare shi?” Kuma da shike an kasa karyata koyaswoyin da aka samo daga annabcin zamanun da yawa suka yi kokarin hana nazarin annabcin, suka koyar da cewa an kulle littattafan annabci, kuma ba za su fahimce su ba. Jama’a da yawa da suka amince da pastocinsu, suka ki jin gargadin annabcin, wadansu kuma, ko da shike sun gamsu da gaskiyar, basu iya furta ta ba, domin kada a fitar da su daga ekklesiya. Sakon da Allah ya aika domin gwadawa da tsarkakewar ekklesiya ya bayana, ba shakka, yawan jama’ar da suka ba da zukatansu ga duniyan nan maimamakon Kristi. Suka so su saurari muryar hikimar duniya suka juya daga sakon gaskiya.BJ 378.1

    Ta wurin kin gardadin malaika na farin, sun ki hanyar da Allah ya tanada don mayaswarsu. Sun ki dan sakon da ya kamata ya gyarta muguntar da ta raba su da Allah, suka kuma juya suka nemi abotar duniya. Dalilin son duniya da sanyin ruhaniya da mutuwa ta ruhaniya da suka kasance cikin ekklesiyoyi a 1844 ke nan.BJ 378.2

    Cikin Ruya 14, malaika na biyu ya bi na farkon yana shela cewa: “Ta fadi, Babila babba ta fadi, ita wadda ta sa dukan al’ummai sun sha ruwan anab na hasalar faskancin ta.” Ruya 14:8. Kalman nan “Babila” daga “Babel” ne, ma’anarsa kuma, birkicewa. Ana anfani da shi a Littafin don bayana yanayin dabam dabam na addinin karya ne. Cikin Ruya 17, an bayana Babibla kamar mace, Littafin kuma yana anfani da kalman nan “mace” kamar alamar ekklesiya, mace mai halin kirki ekklesiya mai-tsarki ke nan, mace mai halin banza kuwa ekklesiya mai-ridda.BJ 379.1

    Cikin Littafin, yanayi mai-tsarki mai jurewa kuma na dangataka da ke tsakanin Kristi da ekklesiyarsa ana kamanta shi da aure ne. Ubangiji ya hada mutanensa da shi kansa ta wurin alkawali mai-nauyi inda yake alakwalin zama Allahnsu, su kuma suna alkawalin zama nasa Shi kadai. Ya ce: “Zan damra alkawalin aure da ke har abada; I, chikin adilchi, da chikin shari’a, da rahama, dajin kai.” Hosea 2:19. Ya kuma ce; “Ni miji ne a gareku.” Irmiya 3:14. Bulus kuma ya yi anfani da wannan alamar a Sabon Alkawali inda ya ce: “Na damre amrenku ga miji daya domin in mika ku budurwa mai-tsabta ga Kristi.” Korinthiyawa II, 11:2.BJ 379.2

    Rashin amincin ekklesiya ga Kristi tawurin kawar da kaunar ta da amincin ta daga gare shi, da barin son kayan duniya ya mallaki rayuwar, ana kamanta shi da ketarewar alkawalin aure ne. Ana bayana zunubin Israila na rabuwa da Ubangiji da wannan alaman ne, ana kuma bayana kaunar Allah da suka rena hakanan: “Na rantse maki, na kwa yi alkawali da ke, in ji Ubangiji Yahweh, kin zama tawa.” “Kin zama kyakyawa kwarai da gaske kin yi arziki har kin kai matsayin sarauta. Sunanki ya tafi ko ina wurin al’ummai domin jamalinki; gama ya chika, tawurin daukaka ta da na sa maki.” Amma kin dogara ga jamalin ki, kin yi karuwanchi domin girman sunanki,” “kamar yadda mace maciyar amana ta kan bar mijin ta, hakanan kun chi amana da ni, ya gidan Israila, in ji Ubangiji.” “Matar aure mazinaciya, mai daukan baki maimakon mijinta.” Ezekiel 16:8, 13-15, 32; Irmiya 3:20.BJ 379.3

    Ana anfani da irin wannan magana cikin Sabon Alkawali game da Kirista masu neman abotan duniya fiye da alherin Allah. Manzo Yakub yace: “Ku mazinata, ba ku sani ba abutar duniya magabtaka che da Allah? Dukan wanda yake so ya zama abokin duniya fa yana mai da kansa magabcin Allah.”BJ 380.1

    Macen (Babila) na Ruya 17 an bayana cewa “tana yafe da shunaiya da mulufi, tana ado da zinariya da duwatsu masu tamani da lu’ulu’ai chikin hannunta tana da koko na zinariya chike da kazamche-kazamche, watau abubuwa masu - dauda, … bisa goshinta kuma da suna a rubuce, “ASIRI, BABILA BABBA, UWAR KARUWAI”. Annabin ya ce: “Na ga machen kuma tana maye da jinin tsarkaka, da jinin shaidu na Yesu.” An kuma bayana cewa Babila “babban birnin ne wanda ke mulki bisa sarakunan duniya.” Ruya 17:4-6,18. Mulkin da ya yi daruruwan shekaru yana yi ma sarakunan kasashen Kirista mulkin daniya shi ne Rum. Launin shunaiya da mulufi, da zinariya da duwatsu masu tamani suna bayana kyau da alfarman da Rum ta mallaka ne. Kuma ba wani mulkin da za a ce ya yi “maye da jinin tsarkaka” kamar mulkin nan da ya zalunci masu bin Kristi. Ana kuma zargin Babila da zunubin dangantaka ba bisa doka ba da “sarakunan duniya.” Ta wurin rabuwa da Ubangiji, da abuta da kafirai ne ekklesiyar Yahudawa ta zama karuwa; Rum kuma da shike ta lalata kanta hakanan tawurin neman hadin kan mulkokin duniya, ta sami hukumci dayan.BJ 380.2

    An ce Babila ce “uwar karuwai.” Ya nuna cewa ‘ya’yanta su ma dole ana misalta su da ekklesiyoyin da su ke rike da koyaswoyinta da al’adunta ke nan, suna kuma bin kwatancinta na sadakar da gaskiya da nufin Allah domin hada abuta ba bisa doka ba da duniya. Dole sakon Ruya 14 dake shelar faduwar Babila, yana magana kan kungiyoyin addini ne da suka taba kasancewa tsarkaka amma suka lalace. Da shike sakon nan yana bin gargadin hukukumcin ne, dole a kwanakin karshe ne za a ba da shi, sabo da haka ba ekklesiyar Rum kadai yake magana a kai ba, da shike wannan ekklesiyar ta kasance fadaddiya na daruruwan shekaru. Biye da haka, a Ruya 18 ana kira ga mutanen Allah su fito daga cikin Babila. Bisa ga nassin nan akwai mutanen Allah har yanzu a cikin Babila ke nan. Kuma a wadanne kungiyoyin addini ne yawancin masu bin Kristi suke yau? Ba shakka, a cikin ekklesiyoyi masu kin ikon paparuma ne. Lokacin da suke tasowa, ekklesiyoyin nan sun dauki matsayi mai kyau don Allah da gaskiya, kuma albarkansa ya kasance tare da su. Ko marasa bi ma sun yarda cewa sakamakon amincewa da kaidodin bishara ya haifar da sakamako masu anfani. Ta bakin annabi zuwa ga Israila: “Sunanki ya tafi ko ina wurin al’ummai domin jamalin ki, gama ya chika ta wurin daukaka ta da na sa maki, in ji Ubangiji Yahweh.” Amma sun fadi tawurin sha’awa dayan wanda ya zama la’ana da rushewar Israila - sha’awar kwaikwayon halayya da neman abutan marasa bin Allah. Kin dogara ga jamalin ki, kin yi karuwanci domin girman sunan ki.” Ezekiel 16:14, 16.BJ 380.3

    Yawancin ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma suna bin kwatancin Rum na dangantakar zunubi da “sarakunan duniya ne” - ekklesiyoyin kasa tawurin dangantakarsu da gwamnatocin duniya, sauran dariku kuma ta wurin neman goyon bayan duniya. Kuma za a iya kiran ekklesiyoyin nan “Babila,” watau birkicewa, ko da shike dukansu suna cewa suna samun koyasuyoyinsu daga Littafin ne, amma sun rarrabu zuwa dariku da ba a iya lisaftawa ba, da koyaswoyi daban dabam da ke saba ma juna. BJ 381.1

    Ban da abutan zunubi da duniya, ekklesiyoyin da suka rabu da Rum suna kuma nuna wadansu halayyan ta.BJ 381.2

    Wani littafin Katolika ya ce: “Idan ekkelsiyar Rum ta taba laifi game da tsarkaka, diyar ta, Ekklesiyar Ingila, ma ta yi laifi dayan domin tana da ekklesiyoyi goma da suka kallafa kansu ga Maryamu duk inda take da guda daya da ta kallafa kan ta ga Kristi.”BJ 382.1

    Dr. Hopkins kuma ya ce: “Ba dalilin da za a ce Ekklesiyar Rum ce kadai mai ruhu da ayukan sabani da Kristi. Ekklesiyoyin masu Kin ikon paparuma suna da sabani da Kristi a cikin su, kuma suna da nisa daga Canji daga… lalacewa da mugunta.”BJ 382.2

    Game da rabuwar Ekklesiyar Presbyterian daga Rum, Dr. Guthrie ya rubuta cewa: “Shekaru dari uku da suka gabata, ekklesiyarmu, da budadden littafi a tutarta, da kuma taken nan, “Binciken Littafin,” a kambinta, ta fice daga kofofin Rum.” Sa’an nan ya yi tambaya mai ma’ana: “ko sun fito sarai daga Babila?”BJ 382.3

    Spurgeon ya ce: “Ekklesiyar Ingila, kamar tsare-tsaren ibada sun cinye ta, amma rashin bin abin da aka saba, shi ma kaman yana fama da rashin aminci. Wadanda muka yi tsanamanin ababa mafi-kyau, suna juyawa daya daya daga asalin bangaskiyar. Na ba da gaskiya ainihin cibiyar Ingila ta cika da rashin aminchi wanda ke kiran kansa Kiristanci.BJ 382.4

    Menene tushen babban riddar? Yaya aka yi ekklesiya ta fara rabuwa da saukin kan bishara? Tawurin bin ayukan kafirci, domin Kiristanci ya sami karbuwar kafirai. Manzo Bulus ya ce, ko a zamaninsa ma “asiri na taka sharia yana ta aikawa ko yanzu.” Tassalunikawa II, 2:7. Lokacin rayuwar manzain, ekkesiya ta kasance da tsarki. “Amma zuwa karshen karni na biyu yawancin ekklesiyoyi sun dauki sabon kamani, saukin kai ya watse, kuma yayin da tsofofin almajiran suka mutu, yaransu, tare da sabobin tuba suka shigo suka sake salon aikin.” Domin a sami masu tuba sai aka rage ingancin imanin Kirista, sakamakon haka kuwa “ambaliyar kafirci ta shigo cikin ekklesiya tare da al’adun ta da gumakanta.” Sa’anda addinin Kirista ya sami goyon bayan shugabannin kasa, jama’a da yawa sun karbi addinin sama - sama; amma yayin da a ganin ido Kirista ne su, yawancinsu sun “kasanche ainihin kafirai, musamman ma suna bautar gumakansu cikin sirri.”BJ 382.5

    Ba a maimaita matakai dayan a kusan kowace ekklesiya mai Kin ikon paparuma ba? Sa’anda masu kafa ekklesiyar sun mutu zuriyarsu sukan guso su sabunta salon aikin. Yayin da suke manne ma koyaswar ubaninsu a duhunce, suna kuma kin karban karin gaskiyar, yaran masu-canjin sukan kauce daga kwatancin tawali’un iyayen, da musun kansu, da kin duniyansu. Ta hakanan saukin kan farko yakan bata. Ambaliyar duniya takan shigo cikin ekklesiya, “tare da al’adu, da ayuka, da gumakanta.BJ 383.1

    Abin tsoro ne kuwa abutan nan da duniya wadda gaba ce da Allah, wanda masu bin Kristi suke yi yanzu. Dubi yawan kaucewa da sanannun ekklesiyoyi suka yi daga koyaswar Littafin game da tawali’u da musun-kai, da saukin kai, da tsoron Allah! Game da anfani da kurdi yadda ya kamata, John Wesley ya ce: “Kada a yi barnar muhimmin talent din nan mai-daraja wajen biyan bukatar sha’awar ido, ko tufafi, masu tsada ko masu yawa, ko kuma kayan ado da ba a bukata. Kada a lalata shi wajen yawan kayan gida ko kuma tsadarsu, ko hotuna… kada a yi ajiya don biyan muradin alfarmar rai, ko neman sha’awar mutane ko kuma yabonsu. ‘Muddan kana aikata nagarta, mutane za su yaba maka.’ Muddan kana ‘sa sutura masu tsada’ kana kuma holewa mutane da yawa za su yabi adonka da yawan kyautanka da liyafarka. Amma kada ka sayi yabonsu da tsada hakanan. Maimaikon haka, ka gamsu da daukakan da ke zuwa daga Allah.” Amma ekklesiyoyi da yawa a zamaninmu, ba a kula irin koyaswan nan.BJ 383.2

    Da’awar cewa ana addini ya mamaye duniya. Shugabanni, ‘yan siyasa, lauyoyi, likitoci, ‘yan kasuwa, suna shiga ekklesiya don samun ban girma da amincewar jama’a, da kuma ci gaban kansu a duniya. Ta hakanan sukan so su rufe dukan laifofinsu da sunan Kiristanci. Kungiyoyin addini, da goyon bayan arziki da tasirin ‘yan duniyan nan da aka masu baptisma, sukan kara neman suna da samun sabobin membobi. Ana gina manyan majami’u da ake yi masu ado a yalwace, a manyan tituna. Masu sujada sukan yi ado mai tsada wanda ake yayi. Akan biya albashi mai-yawa ma wani mai-bishara wawnda ke da baiwa domin ya ba mutane nishadi ya kuma jawo hankulan mutanen. Wa’azinsa ba zai shafi zunuban da an cika aikatawa ba, amma wa’azin yakan zama mai sumul, mai gamsar da ‘yan zamani kuma. Ta hakanan akan sami ‘yan zamani su zama ‘yan ekklesiya, zunubansu na zamani kuma akan rufe su da imani na karya.BJ 384.1

    Game da halayyan Kirista yanzu, game da duniya, wata shaharariyar majalla, ba ta addini ba, ta ce: “Ba tunani, ekklesiya ta amince da ruhun zamanin, ta canja yanayin sujadar ta zuwa abinda zamani ke so.” “Hakika ekklesiya tana anfani da duk ababan da ke sa addini ya zama abin sha’awa.” Wani mawallafi a jaridar “New York Independent” kuma ya yi magana game da ekklesiyar Methodist, cewa: “Bambanci tsakanin masu addini, da marasa addini ya shude, masu himma a kowane gefen kuma suna kokari su share banbancin da ke tsakinin irin halayyansu da jin dadi.” Farin jinin addini yakan kara yawan masu son anfaninsa ba tare da cika bukatunsa ba.”BJ 384.2

    In ji Howard Crosby: “Abin damuwa ne kwarai cewa ekklesiyar Kristi ba ta cika nufin Ubangijita. Kamar yadda Yahudawa ne da suka bar sabawa da yin ma’amala da al’ummai masu bautar gumaka ya sace zukatansu daga Ubangijin…. Haka ekklesiyarmu yanzu, ta wurin hadin kansu da duniya mara ba da gaskiya, da barin hanyoyin Allah da kuma hada kanta da halayyan jama’a na rashin ibada, ko da shike suna da ban sha’awa, tana anfani da ra’ayoyin nan tana kuma samun sakamakon da sun bambanta da wahayin Allah, tana gaba kai tsaye kuma da batun girma cikin alheri.”BJ 385.1

    Cikin wannan malalar sha’awar duniya da neman jin dadi, musun kai da sadakarwa don Kristi sun kusa shudewa gaba daya. “Wadansu maza da mata masu kwazo a ekklesiyoyinmu yau an ilimantar da su tun suna yara su yi sadakarwa domin su iya bayaswa ko yin wani abu don Kristi.” Amma “idan ana bukatar kurdade yanzu,… bai kamata sai an ce ma wani ya bayas ba. Da ma a ce za a yi wata wasar kwaikwayo, ko liyafa, ko cin abinci, wani abu dai da zai ba mutane dariya.BJ 385.2

    Gwamna Washburn na Wisconsin, cikin sakonsa a shekara - shekara, ran 9 ga Janairu, 1873 ya ce: “Ya kamata a yi wata doka don wargaza makarantu inda ake haifar da yan caca. Suna ko ina, ko ekklesiya ma (ba da sanin ta ba dai) akan iske tana aikin iblis wani lokaci jari ko rehul na kyautattuka, wasu lokuta don taimakon addini ko aikin agaji, amma sau da yawa sabo da ababa da basu kai wadannan ba, ababan nan hanyoyi ne na samun kurdin banza. Ba abinda ya fi kashe jiki ko bugarwa, musamman ga matasa, kamar samun kurdi, ba tare da yin aiki ba. Mutane da ake ba su girma ma suna shiga irin ayukan nan, su kuma ba kansu hujja cewa abu mai kyau ne za a yi da kurdin. Ba abin mamaki ba ne kuwa a iske matasa suna shiga halayyan.BJ 385.3

    Ruhun daidaituwa da duniya yana shigowa ekklesiyoyi ko ina. Robert Atkins cikin wa’azinsa a London ya nuna munin lalacewar ruhaniya da ta mamaye Ingila, ya ce: “Masu ainihin dalci suna raguwa a duniya, kuma ba wanda ya kula, masu addini a zamanin nan, a kowace ekklesiya, masu kamnar duniya ne, masu daidaituwa da duniya, masu kaunar holewa da masu neman bangirma. An kiraye su su sha wahala don Kristi, amma suna gudun reni ma, … Ridda, ridda, ridda, aka zana a gaban kowace ekklesiya; kuma da sun sani, da akwai bege, amma ina! Suna cewa, “Na wadata, na sami dukiya, ban bukachi komi ba.”BJ 386.1

    Babban zunubin da aka zargi Babila da ita shi ne cewa “ta sa dukan al’ummai su sha ruwan annab na hasalar fasikancinta.” Kokon mayen nan da take mika ma duniya shi ne koyaswar karya da ta karba, sakamakon hada kanta da shugabanin duniya. Abota da duniya yana lalata imaninta, ita kuma tana mumunan tasiri ga duniya tawurin koyar da koyaswoyin da ke sabani da maganar Littafin.BJ 386.2

    Rum ta hana ma mutane Littafin, ta kuma bukaci kowa ya yarda da koyaswoyinta a maimako. Aikin canjin ne shi mayar da maganar Allah ma mutane, amma ko ba gaskiya ba ne, cewa a ekklesiyoyin zamaninmu ana koya ma mutane su dangana bangaskiyarsu kan koyaswoyin ekklesiyarsu maimakon Littafin ba? Game da ekklesiyoyin masu Kin ikon paparuma, Charles Beecher ya ce: “Suna tsoron fadin wata kalmar zargi game da koyaswa, daidai da yadda su Fada suke tsoron fadin wata kalmar zargi sabanin sujada ga tsarkaka da wadanda aka kashe don imaninsu,… Darikun masu Kin ikon paparuma sun daure hannuwansu da na juna ta yadda tsakaninsu duka, mutum ba zai zama mai-wa’azi ba a wani wuri sam sam, ba tare da karban wani littafi dabam da Littafi Mai-tsarki ba,… Ba karya ba ce cewa ikon koyaswa yanzu ya fara hana Littafin daidaida yadda Rum ta yi, ko da shike a hankali ne.”BJ 386.3

    Sa’anda amintattun mallamai suka bayana maganar Allah, wadansu masana, da pastoci masu cewa sun fahimci Littafin, da sukan yi sokar sahihiyar koyaswa cewa ridda ce, ta hakan kuma sukan hana bincike game da gaskiyar. Da ba don duniya ta yi maye da ruwan anab na Babila ba, da jama’a da yawa za su tuba tawurin bayananiyar maganar Allah. Amma addini ya rikice ta yadda mutane basu san abin da za su gaskata kuma ba, alhakin zunubin rashin tuban duniya yana kan ekklesiya ne.BJ 387.1

    An fara wa’azin sakon malaika na biyu na Ruya 14 da daminan 1844 ne, kuma lokacin ya fi cika kai tsaye ga ekklesiyoyin Amerika inda aka fi shelar gargadin game da hukumcin, aka kuma fi kin gargadin, inda kuma lalacewar ekklesiyoyin ya fi sauri. Amma sakon malaika na iyu din bai cika duka a 1844 ba. A lokacin, ekklesiyoyin sun sami faduwa na halayyan kirki, sakamakon kin hasken zuwan Kristi da suka yi, amma faduwar ba ta cika ba. Yayinda suke ci gaba da kin gaskiyar wannan zamani, suna ci gaba da faduwa ne. Amma har yanzu ba za a ce “Babila ta fadi,… ita wadda ta sa dukan al’ummai su sha ruwan anab na hasalar fasikanchinta” ba. Ba ta rigaya ta sa dukan al’ummai su yi haka ba. Ruhun dayantuwa da duniya da rashin kula da gaskiyar zamaninmu yana nan kuma yana ci gaba cikin ekklesiyoyi masu Kin ikon aparuma a dukan kasashen Kirista, kuma ekklesiyoyin nan suna cikin soka mai-tsanani da nauyin nan na malaika na biyu din. Amma aikin ridda bai rigaya ya kai cikar sa ba.BJ 387.2

    Littafin ya ce kafin zuwan Ubangiji, Shaitan zai yi aiki “da dukan iko da alamu da al’ajibai na karya, da dukan rudami na rashin adilchi,” kuma wadanda “basu amsa kamnar gaskiya domin su tsira ba,” za a barsu su karbi “aikawar sabo, har da za su gaskanta karya.” Tassalunikawa II, 2:9-11. Sai an kai wannan yanayin, aka kuma kamala hadewar ekklesiya da duniya ko ina a kasashen Kirista, kafin faduwar Babila ta cika. Canjin yana ci gaba ne, kuma Ruya 14:8 bai gama cika ba tukuna, sai nan gaba.BJ 387.3

    Duk da duhun ruhaniya da rabuwa da Allah da ke cikin ekklesiyoyin da Babila ta kunsa, akwai babban akwai jama’ar Kristi, watau amintattu masu binsa a cikinsu. Da yawa cikin su basu taba ganin muhimman gaskiya na wannan zamani ba. Da yawa basu gamsu da yanayin su na yanzu ba, suna kuma begen karin haske. A banza suke neman ganin surar Kristi a cikin ekklesiyoyinsu da suke ciki. Yayin da ekklesiyoyin nan suke kara rabuwa da gaskiya, suna kuma kara hada kansu da duniya, bambanci tsakaninsu zai kara fadi, zai kuma kai ga rabuwa daga bisani. Lokaci na zuwa da masu kaunar Allah fiye da komi ba za su kara kasancewa tare da wadanda su ke “mafiya son annishuwa da Allah; suna rike da surar ibada, amma sun musunchi ikonta” ba.BJ 388.1

    Ruya 18 yana nuna lokacin da, sakamakon kin gargadin Ruya 14:6-12, ekklesiya za ta kai cikar yanayin da malaika na biyu din ya yi annabcinsa; kuma mutanen Allah da ke cikin Babila za a bukace su su rabu da ita. Sakon ne na karshe da za a taba ba duniya, zai kuma cim ma manufarsa. Sa’anda za a bar wadanda basu gaskata gaskiya ba, amma suka kaunaci rashin adalci (Tasalunikawa II, 2:12), su karbi rudami mai karfi, har su gaskata karya, sa’an nan ne hasken gaskiya zai haskaka dukan wadanda zukatan su ke bude domin karbanta, kuma dukan ‘ya’yan Ubangiji da ke cikin Babila za su ji kiran: “Ku fito daga chikinta, ya al’ummata.” (Ruya 18:4).BJ 388.2

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents