Babi na 10—Ci Gaban Canji a Jamus
Babban Jayayyar
- Contents- Gabatarwa
- Babi na 1—Hallakawar Urushalima
- Babi na 2—Tsanantawa a Karni na Farko
- Babi na 3—Riddan
- Babi na 4—Waldensiyawa
- Babi na 5—John Wycliffe
- Babi na 6—Huss da Jerome
- Babi na 7—Rabuwar Luther da Rum
- Babi na 8—Luther a Gaban Majalisa
- Babi na 9—Dan Canjin Switzerland
- Babi na 10—Ci Gaban Canji a Jamus
- Babi na 11—Yardar ‘Ya’yan Sarkin
- Babi na 12—Canjin Faransa
- Babi na 13—Netherlands da Scandinavia
- Babi na 14— ‘Yan Canjin Ingila na Baya.
- Babi na 15—Littafi da Juyin-Danwaken Faransa
- Babi na 16—Ubani Matafiya
- Babi na 17—Alkawuran Dawowan Kristi
- Babi na 18—Dan Canji America
- Babi na 19—Haske Ta wurin Duhu
- Babi na 20—Babban Falkaswa na Ibada
- Babi na 21—Gargadin da Aka Ki
- Babi na 22—Cikawar Annabci
- Babi na 23—Menene Haikalin?
- Babi na 24—Cikin Wuri Mafi-Tsarki
- Babi na 25—Dokar Allah Ba Ta Sakewa
- Babi na 26—Aikin Canji
- Babi na 27—Falkaswa na Zamani
- Babi na 28—Fuskantar Rahoton Rayuwa
- Babi na 29—Mafarin Mugunta
- Babi na 30—Gaba Tsakanin Mutum da Shaitan
- Babi na 31—Wakilcin Miyagun Ruhohi
- Babi na 32—Tarkokin Shaitan
- Babi na 33—Babban Rudi na Farko
- Babi na 34—Ko Mattatu Za Su Iya Magana da Mu?
- Babi na 35—Barazana ga Yancin Lamiri.
- Babi na 36—Yakin da Ke Zuwa.
- Babi na 37—Littafi, Mai-tsaro.
- Babi na 38—Gargadi na Karshe
- Babi na 39—Kwanakin Wahala
- Babi na 40—An Tsirar da Mutanen Allah
- Babi Na 41—Mayar da Duniya Kango
- Babi na 42—Karshen Jayayyar
Search Results
- Results
- Related
- Featured
- Weighted Relevancy
- Content Sequence
- Relevancy
- Earliest First
- Latest First
- Exact Match First, Root Words Second
- Exact word match
- Root word match
- EGW Collections
- All collections
- Lifetime Works (1845-1917)
- Compilations (1918-present)
- Adventist Pioneer Library
- My Bible
- Dictionary
- Reference
- Short
- Long
- Paragraph
No results.
EGW Extras
Directory
Babi na 10—Ci Gaban Canji a Jamus
Bacewar Luther ta jawo damuwa ko ina a Jamus. An rika jin tambayoyi game da shi ko ina. An yayata jita-jita, mutane da yawa kuma suka dauka cewa an kashe shi ne. Aka yi makoki sosai, ba sanannun abokan sa kadai ba, har da dubbai da basu bayana matsayin su game da Canjin ba. Da yawa suka rantse za su rama mutuwarsa.BJ 183.1
Shugabannin Romawa cikin tsoro suka ga yawan munin kiyayar da ake masu. Ko da shike da farko sun yi murna cewa Luther ya mutu, nan da nan suka so su buya daga fushin mutanen. Magabtansa basu taba damuwa da manyan ayukan karfin halinsa kamar yadda suka damu da bacewarsa ba. Wadanda cikin fushinsu suka so su hallaka dan Canjin nan kuwa suka cika da tsoro yanzu da ya zama kamamme mara taimako. Wanin su ya ce: “Hanya daya tak da ta rage mana don ceton kanmu ita ce mu kunna fitillu, mu nemi Luther ko ina a duniya, mu mayar da shi ga al’ummar da ke bidar sa.” Dokar babban sarkin ta kasa aiki. Wakilan paparuma suka cika da haushi, ganin cewa dokar ba ta jawo hankula kamar yadda yanayin da Luther ke ciki ya jawo ba.BJ 183.2
Labarin cewa yana lafiya ko da shike fursuna ne shi, ya kwantar da hankulan mutane, ya kuma kara yawan sha’awarsa da suke yi. An rika karanta rubuce rubucen sa da marmari fiye da da. Yawan masu goyon bayan mutumin nan, wanda a cikin kasada mai ban tsoro ya tsare maganar Allah, ya karu sosai. Canjin ya ci gaba da kara karfi. Irin da Luther ya shuka ya tsiro ko ina. Bacewar sa ta yi aikin da kasancewarsa da ba ta yi ba. Wadansu ma’aikata ma suka ji sabon aiki ya kama su, yanzu da babban shugabansu ba ya nan. Da sabuwar bangaskiya da kwazo kuma, suka yi iyakar kokarinsu, domin kada aikin da aka fara da kyau ya sami koma baya.BJ 183.3
Amma Shaitan bai huta ba. Yanzu kuma ya gwada abin da yakan gwada a kowane kokari na canji: ya rudi mutane ya kuma hallaka su ta wurin rudinsu da jabu a maimakon aiki na gaskiyan. Kamar yadda aka sami Kristi na karya a karnin farko na ekklesiyar Kirista, haka annabawan karya suka taso a karni na goma sha shida.BJ 184.1
Mutane kalilan da suka motsu ta wurin abin da ke faruwa a sha’anin addini suka ga kamar sun sami ruya ta musamman daga sama, suka kuma ce wai Allah Ya aiko su su ci gaba har karshe da Canjin da Luther ya fara da kumamanci, in ji su. Gaskiyar ita ce, sun rika warware aikin da shi ya yi ne. Suka ki babban kaidar da ta kasance harsashen Canjin, cewa maganar Allah ce kaidar gaskiya da ayuka; kuma suka sanya wannan mai bishewar da ra’ayinsu da tunanin kansu kuma. Ta wurin kawar da babban abin da ke bayana kuskure da karya aka bude ma Shaitan hanyar mallakar zukata yadda ya ga dama.BJ 184.2
Daya daga annabawan nan ya ce wai malaika Jibrailu ne ya aiko shi. Wani dalibi da ya bi shi, ya watsar da makaranta yana cewa wai Allah da kan Shi ya ba shi hikimar bayana maganarsa. Wadansu da suka saba da tsananin ra’ayi suka hada kai da su. Aukan wadannan mutanen sun ta da hankula sosai. Wa’azin Luther ya falkas da mutane ko ina, suka ji a jikinsu cewa canji ya zama dole, yanzu kuma annabawan karya suka rudi mutane masu ainihin gaskiya. BJ 184.3
Shugabanin sabuwar kungiyar suka ci gaba zuwa Wittenberg. Suka dami Melanchthon da abokan aikinsa da ra’ayoyinsu. Suka ce: “Allah Ya aiko mu mu koya ma mutanen. Mun ji sahwarwari kai tsaye daga Ubangiji; mun san abin da zai faru; a takaice, mu manzani ne da annabawa, muna tare kuma da Luther.” BJ 185.1
Yan Canjin sun yi mamaki sosai. Basu taba gamuwa da irin wannan ba, kuma basu san matakin da za su dauka ba. Melanchthon ya ce: “Hakika, akwai ruhohi na musamman cikin mutanen nan; amma wadanne ruhohi?... A gefe daya, mu yi hankali da bice Ruhun Allah, a daya gefen kuma, mu yi hankali kada mu bar ruhun Shaitan ya batar da mu.” Sakamakon sabuwar koyaswar ya bayana nan da nan. Ya sa mutane suka kyale Littafi, ko ma suka ajiye shi a gefe gaba daya ma. Makarantu suka shiga rudami. Dalibai suka watsar da makaranta, suka janye daga jami’ar. Mutane da suka ga kamar suna da kwarewar da za su falkas da aikin Canjin, sun kai aikin kusa da hallaka ne kawai. Masu bin Rum din suka dawo da kwarin gwiwansu, suka ce: “Fama daya na karshe kawai sa’an nan komi zai zama namu.”BJ 185.2
Luther a Wartburg, da jin abin da ya faru, ya ce: “Da ma na san Shaitan zai aiko mana wannan annobar” Ya gane ainihin halin annabawan karyan nan ya kuma ga hadarin da ke barazana ga gaskiyar. Jayayyar paparuma da ta babban sarkin basu jawo masa irin damuwa da rudewa da ya shiga a wannan lokacin ba. Daga masu cewa su abokan Canjin ne, magabtansa mafi-muni suka fito. Gaskiyan nan da ta ba shi murna da kwanciyar rai ne aka yi anfani da ita don ta da hargitsi da rudewa cikin ekklesiya.BJ 185.3
Cikin aikin canjin nan, Ruhun Allah ne Ya dinga ingiza Luther. Bai shirya daukan matakai da ya dauka ba, ko kuma ya yi canje canjen da ya yi ba, shi dai ya kasance kayan aiki ne a hannun Iko mara iyaka. Duk da haka yakan yi rawan jiki game da sakamakon aikinsa. Ya taba cewa: “Idan an san cewa koyaswata za ta yi ma wani mutum daya rauni, komi kankantansa, wanda kuwa ba zai taba yiwuwa ba, da shike bishara ce kanta, zan gwammaci mutuwa sau goma maimakon kin janye koyaswar.”BJ 186.1
Yanzu kuma Wittenberg kansa, cibiyar Canjin, ta fada cikin tsananin ra’ayi da rashin bin doka. Wannan mumunan yanayi ba daga koyaswoyin Luther ba ne; amma ko ina Jamusawa, magabtansa sun rika tura masa laifin. Cikin bacin rai, wani lokaci yakan tambaya: “Ko wannan zai iya zama sakamakon Canjin?” idan kuma ya koma ga Allah cikin addu’a, salama takan shigo zuciyarsa. Yakan ce: “Aikin ba nawa ba ne, naka ne. Ba za ka bari ya lalace ta wurin camfi ko tsananin ra’ayi ba.” Amma tunanin ci gaba da rabuwa da jayayyar har wannan tsawon lokacin a wannan yanayi ba daidai ba ne. Sai ya shirya zai koma Wittenberg. BJ 186.2
Ba da jinkiri ba, ya kama hanyarsa mai yawan hadari. Yana dai kalkashin takunkumin kasar. Magabta suna da yanci su dauke ransa; an kuma hana abokai taimaka masa, ko kuma ba shi masauki. Gwamnatin kasar ta dauki matakai masu tsanani game da masu goyon bayansa. Amma ya ga cewa aikin bishara ya sami matsaloli, cikin sunan Ubangiji kuma ya fita ba tsoro, domin yin yaki sabo da gaskiya.BJ 186.3
Cikin wasikarsa zuwa ga mai-zaben, inda ya fada masa niyyar sa ta barin Wartburg, Luther ya kara da cewa: “Ina shirye in sadu da rashin gamsuwar ka ya mai-girma, game da zuwa na Wittenburg, kalkashin tsaron da ya fi na yarima da na sarakuna. Ba na tunanin neman goyon bayan ka, kuma maimakon neman tsaron ka ma gara ni kai na in tsare ka. Idan na sani kai mai-girma za ka tsare ni, ba zan je Wittenburg ba ma sam. Babu takobin da zai iya ci gaba da wannan aikin. Dole Allah ne zai yi komi ba tare da taimako ko yardar mutum ba. Shi wanda Ya fi bangaskiya Shi ne Ya zai fi iya tsaro.”BJ 186.4
Cikin wasika ta biyu da ya rubuta a hanyarsa zuwa Wittenburg, Luther ya kara da cewa: “Ina shirye in fuskanci rashin jin dadin ka, ya mai-girma, da fushin dukan duniya ma. Yan Wittenberg ba tumaki ba ne? Ba Allah ne ya ba ni amanarsu ba? Bai kamata ni, in ta kama, in ba da kai na ga mutuwa sabo da su ba? Ban da haka, ina tsoron ganin mumunar annoba a Jamus, wadda Allah zai hori al’ummarmu da ita.”BJ 187.1
Cikin lura da bangirma, amma kuma da gaske, ya shiga aikinsa. “Ta wurin maganar za mu rushe, mu kuma hallaka abin da aka kafa da karfi. Ba zan yi anfani da karfin yaki masu camfi da rashin bangaskiya ba.... Ba wanda za a tilasta. Yanci shi ne ainihin bangaskiya.” BJ 187.2
Jima kadan aka labarta a Wittenberg cewa Luther ya dawo kuma zai yi wa’azi. Mutane suka kwararo daga kowane gefe, majami’a kuma ta cika makil. Da ya hau bagadi, cikin hikima da natsuwa ya umurta, ya karfafa, ya kuma tsauta. Game da aikin wadansu da suka yi anfani da karfi don kawas da mass, ya ce: BJ 187.3
“Mass mumunan abu ne, Allah ba ya son shi; ya kamata a kau da shi; kuma fata ta ce a duk duniya a sauya shi da jibi na bishara. Amma kada a raba wani da shi karfi da yaji. Dole mu bar batun a hannun Allah. Maganarsa ce za ta yi aiki ba mu ba. Don me kuwa? Domin zukatan mutane ba a hannuna su ke ba, yadda mai-yin tukwane ke rike da yumbu. Muna da yancin yin magana; ba mu da yanci game da aikatawa. Bari mu yi wa’azi, sauran na Allah ne. Idan na yi anfani da karfi mene ne riba ta? Gatsine, kwaikwayo, al’adun mutane, da riya.... Amma ba za a iske zukata na gaskiya ko ainihin bangaskiya ko kauna ba. Inda ba abu ukun nan, ba komi kenan, kuma ba zan dami kai na da wannan ba.... Allah Ya na yin abu da yawa da maganarsa fiye da abin da ni da kai da dukan duniya ke yi da karfin dukan mu. Allah Yana kama zuciya ne; kuma sa’an da aka kama zuciya, an sami komi kenan...” BJ 187.4
“Zan yi wa’azi, da mahawara da rubutu, amma ba zan tilasta ma wani ba, da shike bangaskiya yardar rai ne. Dubi abin da na yi. Na yi jayayya da paparuma da cinikin gafara da masu goyon bayan paparuma, amma babu nuna karfi ko tashin hankali. Maganar Allah na sa a gaba; na yi wa’azi, na yi rubutu; abin da na yi kenan kadai. Duk da haka yayin da nike barci,...maganar da na yi wa’azin ta ta hambarar da paparuma, ta yadda babu yarima ko babban sarki da suka yi ma maganar wata illa sosai. Kuma ban yi komi ba, maganar kadai ta yi komi. Da na so in yi anfani da karfi watakila da dukan Jamus ta jike da jinni. Amma da mene ne sakamakon? Hasara da kango na jiki da na ruhu. Sabo da haka ne na yi shuru, na bar maganar ta shiga duniya ita kadai.”BJ 188.1
Kowace rana, har mako guda, Luther ya ci gaba da yi ma jama’a wa’azi. Maganar Allah ta karya makarin matsanancin ra’ayi. Ikon bishara ya sa wadanda aka rude su suka dawo hanyar gaskiya. Luther bai yi marmarin saduwa da masu matsanancin ra’ayin nan da aikinsu ya haifar da masifa sosai ba. Ya san su marasa tunani mai-kyau ne, da rashin tarbiyya kuma sosai, wadanda yayin da suke cewa sun sami wayarwa daga sama, ba za su jimre jayayya mafi kankanta ko ma gargadi ko shawara mafi anfani ba. Da suka mallaka ma kan su mafificiyar daukaka, suka bukaci kowane mutum ya yarda da ikirarinsu, ban da tambaya. Amma sa’an da suka nemi yin ganawa da shi ya, yarda zai sadu da su; kuma ya tone karyarsu sosai, ta yadda nan da nan ‘yan sojan gonan suka fice daga Wittenberg. BJ 188.2
An tsai da matsanancin ra’ayin, na wani lokaci; amma shekaru kalilan daga baya ya bullo da karin karfi da munanan sakamako kuma. Game da shugabannin masu wannan ra’ayin, Luther ya ce: “Gare ku Littafi mataciyar magana ce; dukansu kuma suka far ihu, ‘Ruhun! Ruhun!’ Amma hakika ba zan bi inda ruhun su ke kai su ba. Bari Allah cikin jinkansa Ya kiyaye ni daga ekklesiyar da babu kowa sai tsarkaka. Ina so in kasance tare da masu twali’u, marsa karfi, marasa lafiya, wadanda sun san zunubansu, suna kuma kuka ga Allah kullum daga tsakiyar zuciyarsu don samun taimakonsa da goyan bayansa.”BJ 188.3
Thomas Munzer, mafi zafi cikin masu matsanancin ra’ayin, mutum ne mai-kwarewa sosai, wanda da ya yi anfani da kwarewarsa daidai, ya yi abu mai-kyau; amma shi bai koyi kaidodin addinin gaskiya ba tukuna. “Ya shaku da marmarin canza duniya, kuma ya manta, kamar yadda dukan masu tsananin sha’awa sukan yi, cewa ya kamata canjin ya fara daga shi kansa ne.” Ya yi burin samun matsayi da tasiri, kuma bai yarda ya zama na biyu ga ko Luther kansa ba. Ya ce ta wurin sauya ikon Littafi a maimakon ikon paparuma suna kafa wani tsarin paparuma ne dabam kawai. Ya ce shikansa an aiko shi ya fito da canji na gaskiya ne. “Wanda ke da irin wannan ruhun,” in ji Munzer, “yana da bangaskiya ta kwarai, ko da ba zai taba ganin Littafi ba duk tsawon rayuwarsa.”BJ 189.1
Mallamai masu matsanancin ra’ayi sun bar zato ya mallake su, suka mai da kowane tunani ko tsammani kamar muryar Allah ce; sabo da haka suka kai makura sosai game da dukan al’amura. Wadansu ma sun kona Littafinsu, suna cewa: “Harafi yana kisa, amma ruhu yana bada rai.” Koyaswar Munzer ta je dadai da sha’awar al’ajibai da mutane ke da shi, yayin da ya kuma gamsar da alfarmar su ta wurin ba ra’ayin mutum da tanninsa fifiko bisa maganar Allah. Dubbai suka karbi koyaswarsa. Jima kadan ya yi watsi da duk wani tsari ko oda cikin sujadar jama’a, ya kuma ce yin biyayya ga yarima kokari ne na bauta ma Allah da Belial tare.BJ 189.2
Zukatan mutane da suka rigaya suka fara watsar da kangin paparuma sun kuma damu sabo da takurar mahukmta na gwamnati. Koyaswoyin Munzer na juyin dan wake da ya ce Allah ne Ya ba shi, sun sa mutane suka bijire ma kowane iko, suka dogara ga wariyarsu da tunaninsu. Munanan ayukan tawaye da tashin hankali suka fara aukuwa, har kasar Jamus ta jike da jini.BJ 189.3
Damuwan da Luther ya fuskanta da dadewa a Erfurt ya taho masa yanzu da karin karfi, yayin da ya ga sakamakon matsanancin ra’ayi da aka zargi Canjin da yi. Mahukunta ‘yan tsarin paparuma suka ce, kuma da yawa suka so su yarda, cewa gawayen da aka yi sakamakon koyaswar Luther ne. Ko da shike zargin nan ba shi da tushe ko kankani, duk da haka ya jawo ma Luther damuwa babba. Bai iya gane yadda aka daidaita aikin gaskiya da muguntar matsanancin ra’ayi ba. Ta wani bangaren kuma shugabannin tawayen sun ki jinin Luther domin, ban da jayayyar sa ga koyaswarsu, ya kuma ki amincewa da ikirarinsu cewa Allah ne Ya aiko su. Domin ramuwa su kuma suka yi sokar sa cewa sojan gona ne shi. Kaman dai ya jawo ma kansa kiyayyar mahukumta da na mutane ne.BJ 190.1
Yan Rum din sun yi murna, suna jira su ga faduwar Canjin; suka kuma ba Luther laifi har game da kurakuran da ya yi ta kokarin gyarawa. ‘Yan matsanancin ra’ayin da suka yi zargin cewa ba a yi masu adalci ba, suka yi nasarar samun goyon bayan jama’a da yawa, kuma, kamar yadda aka cika yi game da masu kuskure, sai aka kuma mai da su kamar wadanda aka wulakanta sabo da banaskiyarsu. Sabo da haka wadanda suka rika yin iyakar kokarin yin sabani da Canjin su ne aka tausaya masu, aka kuma yaba masu cewa su ne aka yi masu mugnta da danniya. Aikin Sahitan ke nan ta wurin ruhun tawaye dayan da ya fara nunawa tun a sama.BJ 190.2
Shaitan kullum yana kokarin rudin mutane domin ya sa su kira zunubi adalci, adlci kuma zunubi. Kuma yana yin nasara! Sau da yawa akan yi ma amintattun bayin Allah horo da reni domin sun tsaya ba tsoro suna kare gaskiya! Amma a kan yabi wakilan Shaitan a kuma yi masu balmar baka ko lallaba, har ma ana ganinsu kamar wadanda aka azabtar sabo da bangaskiyarsu, alhali wadanda ya kamata a girmama a kuma karfafa sabo da amincinsu ga Allah, akan bar su su tsaya su kadai, kalkashin zato da rashin amincewa. BJ 190.3
Jabun tsarki, da tsarkakewa ta karya suna aikin su na rudi har yanzu. Kalkashin kamani dabam dabam yana nuna ruhu dayan kamar zamanin Luther, kawar da tunanin mutane zuwa bin ra’ayin kansu da kuma yadda suke ji kawai, maimakon yin biyayya ga dokar Allah, daya daga dabarun Shaitan ne na jawo reni ma tsarki da gaskiya.BJ 191.1
Da rashin tsoro, Luther ya kare bishara daga hare haren da suka zo daga kowane gefe. Maganar Allah ta nuna kanta makami mai-girma cikin kowace fada. Da wannan maganar ya yaki paparuma, da koyarwar sassauci ta masu-makaranta, yayin da ya tsaya da karfi kamar dutse, ya yaki matsanancin ra’ayi da ya so ya hada kai da Canjin. BJ 191.2
Kowane daya daga cikin bangarorin nan masu sabani ya rika sake Littafin ne, yana daukaka mutum a matsayin tushen gaskiya da sani da addini. Addinin Rum da ke cewa wai ruhun paparuma ya sauko masa ne tawurin manzani, kuma ba ya sakewa har abada, yana ba da isashen zarafi ya boye kowane irin almubazzaranci da lalacewa a kalksahin tsarin sakon manzanin. Karfafawar Munzer da abokansa ta fito daga abin da zuciyarsu ta gani ne kawai, kuma tasirin ta ya kaskantar da kowane iko, na mutum da na Allah. Kiristanci na gaskiya yana karban maganar Allah a matsayin babban gidan dukiya na gaskiya da ma’aunin kowane motsuwa ko horuwa.BJ 191.3
Da ya dawo daga Watburg, Luther ya kamala juya Sabon Alkawali, ba da jimawa ba kuma aka ba mutanen Jamus bishara cikin harshensu. An karbi wannan juyin da farinciki sosai ga masu kaunar gaskiya; amma wadanda suka zabi al’adun yan Adam da dokokin mutane, suka ki shi da reni ma. BJ 191.4
Priestoci suka tsorata, ganin cewa yanzu kowane mutum zai iya yin mahawara ma da su game da maganar Allah, kuma ta haka za a tone jahilcinsu. Makaman tunanin su na mutumtaka sun rasa iko kan takobin Ruhu. Rum ta yi iyakar kokarinta don hana yaduwar Littafi; amma dokoki da tsinewa da azaba duk sun zama banza. Yayin da yake kara karanta Littafni, sai mutane kuma suka kara samun marmarin sanin ainihiin abin da Littafin ke koyarwa. Dukan wadanda sun iya karatu suka yi marmarin karanta maganar Allah don kansu. Sun dinga tafiya ko ina da shi, suna kara karantawa, basu gamsu ba kuwa har sai da suka hadace nassosi da yawa masu tsawo kuma. Ganin farin jinin da Sabon Alkawali ya yi, ya sa Luther nan da nan ya fara juya Tsohon Alakwali yana wallafa shi bangare bangare da zaran ya juya.BJ 192.1
An ji dadin rubuce rubucen Luther a birni da kauye. “Abin da da abokan sa suka rubuta, wadansu suka baza. Masu zaman zuhudu da suka gane rashin cancantar takalifansu, suka kuma so sauya doguwar rayuwar kiwuya da rayuwar aiki tukuru, amma kuma ba su da sani da za su iya shelar maganar Allah, suka rika zuwa dukan lardunan, suna ziyartar kauyuka da unguwanni, inda suka sayar da littattafan Luther da abokansa. Nan da nan Jamus ta cika da masu sayarda litattafan nan.”BJ 192.2
Mawadata da matalauta, masana da jahilai, sun dinga nazarin littattafan nan da marmari sosai. Da dare mallaman makarantun kauyukan sukan karanta su ga kananan kungiyoyi a gefen wuta. Da iyakar, kokari wadansu sukan gane gaskiyar, kuma bayan sun karbi maganar da murna, su kuma sukan fada ma wadansu kyakyawar labarin. BJ 192.3
An tabbatar da gaskiyar maganar Allah: “Buden zantattukanka yana ba da haske; yana ba da fahimi ga sahihai.” Zabura 119:130. Nazarin Littafin ya rika kawo babban canji cikin tunani da zukatan mutane. Mulkin paparuma ya rigaya ya aza ma masu binsa karkiya ta karfe da ta daure su cikin jahilci da kankantar girma. An rika bin kamanni da sifa a hankali; amma cikin dukan hidimarsu, ba su yi anfani da zuciya ta tunani kuma ba. Koyaswoyin Luther da suka bayana ainihin gaskiyar maganar Allah, da kuma ita maganar Allahn kanta da aka sa a hannun mutane marasa gata, ya falkas da kwarewarsu, ya tsarkake ya kuma girmama yanayin ruhaniyarsu, wannan kuwa ya ba da karfi da kuzari ga tunaninsu. BJ 193.1
An rika ganin mutane kowane iri da Littafin cikin hannuwansu, suna kare koyaswoyin Canjin. ‘Yan paparuma da suka rigaya suka bar nazarin Littafin a hannun priestoci da ‘yan zaman zuhudu, yanzu kuwa suka fara kiran su priestocin su zo su karyata sabobin koyaswoyin. Amma da shike priestocin basu san maganar Allah ba, wadanda an rigaya an ce da su jahilai masu ridda suka ka da priestoci. Wani marubucin Katolika ya ce: “Abin bakinciki, ya rigaya ya ce ma mutanensa kada su sa bangaskiyarsu ga wani abu dabam da Littafin.” Jama’a sukan taru domin su ji gaskiya daga mutane masu karamin ilimi, har ma suna mahawarar maganar Allahn da masana masu iya magana. Jahilcin mutanen nan ya bayyana sa’an da aka tare hujjojinsu da koyaswoyi masu sauki na maganar Allah. Leburori da sojoji da mata, har da yara ma, suka fi priestoci da likitoci fahimtar koyaswar Littafi.BJ 193.2
Bambanci tskanin almajiran bishara da magoya bayan camfin paparuma ya bayana cikin masana da kuma cikin marasa gata. “Sabanin tsofofin jarumawan sarautar, wadanda suka ki koyon harsuna da sanin littattafai, suna kuma koya ma kansu sani mafi inganci na da. Da shike sun mallaki tunani mai-kuzari, da ruhu mai-daukaka, da zukata marasa tsoro, matasan nan suka sami sanin nan da ya dade ba a sami mai-takara da su ba.... Sabo da haka, sa’an da wadannan matasa masu kare Canjin suka sadu da likitocin Rum a kowane taro, sukan fada masu a saukake gabagadi kuma, ta yadda jahilan nan suka ja baya, suka sha kunya, suka kuma fada cikin renin da ya cancance su.”BJ 193.3
Sa’an da ma’aikatan Rum suka ga jama’an su suna raguwa, suka bidi taimakon majistarori kuma ta kowace hanya da suka iya bi, suka yi kokarin dawo da masu jinsu. Amma mutanen sun sami abin da ya gamsar da ruhunsu a cikin sabobin koyaswoyin, suka kuwa rabu da wadanda sun dade suna ciyar da su da buntun banza na camfi da al’adun mutane. BJ 194.1
Sa’anda aka ta da zalunci kan masu koyar da gaskiyar, sai suka ji maganar Kristi cewa: “Amma sa’anda sun tsanance ku chikin wannan birni, ku gudu zuwa na kusa.” Matta 10 :23. Hasken ya shiga ko ina. Yayin da suke gudu, akan karbe su a wani wuri, nan kuwa sukan yi wa’azin Kristi, wani lokaci cikin majami’a, ko kuma, idan an hana su damar, a cikin gidaje ko a fili ma. Duk wirin da za a iya jin su yakan zama tsarkakakken haikali. Gaskiyar da aka yi shelar ta da karfi da tabbaci kuma hakanan, ta yadu ta yadda ba za a iya ki ba. BJ 194.2
A banza aka nemi mahukuntan ekklesiya da na kasa su murkushe riddar. A banza suka yi anfani da kurkuku da azabtarwa da wuta da takobi kuma. Dubban masu bi suka hatimce bangaskiyarsu da jininsu, duk da haka kuma aikin ya ci gaba. Zalunci ya kara fadada gaskiyan ne ma, kuma tsanancin da Shaitan ya so ya hada da zaluncin ya kai ga kara bayana bambanci da ke tsakanin aikin Shaitan da aikin Allah ne.BJ 194.3