Babi na 34—Ko Mattatu Za Su Iya Magana da Mu?
Babban Jayayyar
- Contents- Gabatarwa
- Babi na 1—Hallakawar Urushalima
- Babi na 2—Tsanantawa a Karni na Farko
- Babi na 3—Riddan
- Babi na 4—Waldensiyawa
- Babi na 5—John Wycliffe
- Babi na 6—Huss da Jerome
- Babi na 7—Rabuwar Luther da Rum
- Babi na 8—Luther a Gaban Majalisa
- Babi na 9—Dan Canjin Switzerland
- Babi na 10—Ci Gaban Canji a Jamus
- Babi na 11—Yardar ‘Ya’yan Sarkin
- Babi na 12—Canjin Faransa
- Babi na 13—Netherlands da Scandinavia
- Babi na 14— ‘Yan Canjin Ingila na Baya.
- Babi na 15—Littafi da Juyin-Danwaken Faransa
- Babi na 16—Ubani Matafiya
- Babi na 17—Alkawuran Dawowan Kristi
- Babi na 18—Dan Canji America
- Babi na 19—Haske Ta wurin Duhu
- Babi na 20—Babban Falkaswa na Ibada
- Babi na 21—Gargadin da Aka Ki
- Babi na 22—Cikawar Annabci
- Babi na 23—Menene Haikalin?
- Babi na 24—Cikin Wuri Mafi-Tsarki
- Babi na 25—Dokar Allah Ba Ta Sakewa
- Babi na 26—Aikin Canji
- Babi na 27—Falkaswa na Zamani
- Babi na 28—Fuskantar Rahoton Rayuwa
- Babi na 29—Mafarin Mugunta
- Babi na 30—Gaba Tsakanin Mutum da Shaitan
- Babi na 31—Wakilcin Miyagun Ruhohi
- Babi na 32—Tarkokin Shaitan
- Babi na 33—Babban Rudi na Farko
- Babi na 34—Ko Mattatu Za Su Iya Magana da Mu?
- Babi na 35—Barazana ga Yancin Lamiri.
- Babi na 36—Yakin da Ke Zuwa.
- Babi na 37—Littafi, Mai-tsaro.
- Babi na 38—Gargadi na Karshe
- Babi na 39—Kwanakin Wahala
- Babi na 40—An Tsirar da Mutanen Allah
- Babi Na 41—Mayar da Duniya Kango
- Babi na 42—Karshen Jayayyar
Search Results
- Results
- Related
- Featured
- Weighted Relevancy
- Content Sequence
- Relevancy
- Earliest First
- Latest First
- Exact Match First, Root Words Second
- Exact word match
- Root word match
- EGW Collections
- All collections
- Lifetime Works (1845-1917)
- Compilations (1918-present)
- Adventist Pioneer Library
- My Bible
- Dictionary
- Reference
- Short
- Long
- Paragraph
No results.
EGW Extras
Directory
Babi na 34—Ko Mattatu Za Su Iya Magana da Mu?
Hidimar malaiku masu-tsarki, bisa ga Littafin, gaskiya ce mafi-ta’azantarwa mai-daraja kuma ga kowane mai-bin Kristi. Amma an duhunta koyaswar Littafin game da wannan batu aka kuma bata shi tawurin kura-kuran koyaswar yawancin masanan ilimin tauhidi. Koyaswar yanayin rashin mutuwa, wadda aka fara aronta daga kafirci, aka kuma shigar da ita cikin addinin Kirista a zamanin duhun nan na babban ridda, ya kawar da gaskiyanda Littafin ke koyarwa a bayane cewa “matattu ba su san komi ba.” Jama’a da yawa sun ba da gaskiya cewa ruhohin matattu ne “ruhohi masu-hidima ne, aikakku domin su yi hidima sabili da wadanda za su gaji cheto.” Wannan kuma duk da shaidar Littafin game da kasancewar malaiku na sama, da dangantakarsu da tarihin mutum, kafin ma mutuwar Habila.BJ 547.1
Koyaswar cewa matattu sun san abin da ke faruwa, musamman zancen cewa wai ruhohin matattu su kan dawo su yi ma masu rai hidima, ta shirya hanya domin sihiri na zamani. Idan ana shigo da matattu wurin Allah da malaiku masu tsarki, suna kuma da sanin da ya zarce wanda su ke da shi da, don ma baza su dawo duniya su koyar da masu-rai su kuma gargade sub a? idan ruhohin matattu sun a zagaya abokan su a duniya, don me baza a basu izini suyi sadarwa da su, su gargade su game da mugunta, ko kuma su ka’azantar da su cikin bakinciki ba? Ta yaya wadanda sun gaskata cewa matattu suna sane da abinda ke faruwa za su ki abin da ke zuwa masu a sunan hasken Allah wanda ruhohi ke kawo masu? Wannan hanya ce da a ke gani kamar mai-tsarki ce, wadda Shaitan ke anfani da ita don cim ma manufofin sa. Fadaddun malaukuda su ke bin nufin sa sukan bayyana kamar yan sako ne daga duniyar ruhohi. Yayin da su ke kirarin cewa suna hada adarwa tsakanin masurai da matattu, sarkin mugunta yana aikin rudarwar sa a zukatan mutansu.BJ 547.2
Yana da iko ya kawo ma mutane kamanin abokansu da suka mutu. Jabun yakan yi daidai da ainihin; kamanin da kalmomin, da muryarsu sukan yi daidai da na mamacin. Mutane da yawa su kan ta’azantu da cewa kaunatattun su suna jin dadin salamar sama, kuma su kan saurari “ruhohi na rudami da koyaswar aljannu.”BJ 548.1
Idan aka sa su sun gaskata cewa da gaske ne matattu suna dawowa su yi sadarwa da su, Shaitan yakan sa wadanda sun je kabari ba a shirye ba su bayana. Su kan ce suna murna a sama har ma suna da manyan matsayi a can, don haka ana koyar da kuskuren nan ko ina cewa ba a bambanta masu-adalci da miyagu. Bakin karyan nan daga duniyar ruhohi wani lokaci sukan yi kashedi da gargadi da kan kasance daidai. Sa’an nan, da sun sami karbuwa sai su gabatar da koyaswoyi da ke rage amincewan da ake yi ma Littafin. Da kamanin kulawa da lafiyar abokansu a duniya, su kan nuna kurakurai masu muni. Da shike su kan fadi abin da zai faru nan gaba daidai, wannan yakan sa a ga maganar su da kamanin gaskiya; jama’a kuma su kan yarda da koyaswoyinsu nan da nan; su kuma gaskata su gaba daya sai ka ce su ne gaskiya mafi-tsarki na Littafin. A kan kawar da dokar Allah, a rena Ruhun alheri, a kuma mai da jinin alkawalin abu mara tsarki. Ruhohin suna musun Allahntakan Kristi su kuma sa Mahalicin ma a matsayi daya da su kan su. Ta hakanan ta wurin sabuwar sake kama babban dan tawayen yana kan yakinsa da Allah, wanda ya fara a sama ya kuma ci gabada shi a duniya yanzu samada shekara dubu shi da ke nan.BJ 548.2
Wadansu sukan yi kokarin cewa ayukan ruhohin nan yaudara ce da dabo kawai. Amma ko da shi ke gaskiya ce cewa akan yi wani ba-duhu mai-kama da ayukan ruhohi, ana kuma nuna ainihin ikon da ya fi na mutum. Buge bugen ban mamaki da aka fara sihirin zamanin nan da shi ba sakamakon dabara ko wayon mutum ba ne, amma ayukan miyagun malaiku ne kai-tsaye, wadanda ta hakanan suka fito da rudi mafi-nasarar hallaka rayuka. Za a rudi mutane da yawa ta wurin gaskata cewa sihiri dabara ce ta mutane kawai; sa’anda suka sadu fuska da fuska da ayukan da dole su yarda cewa sun fi karfin mutum, sai a rude su, a kuma sa su karbe su a matsayin babban ikon Allah.BJ 549.1
Mutanen nan suna manta maganar littafi game da al’ajiban da Shaitan da wakilan sa su ka aikata. Tawurin taimakon Shaitan ne ‘yan dabon Fir’auna su ka iya yin kwaikwayon aikin Allah. Bulus ya shaida cewa kafin zuwan Kristi na biyu za a yi irin ayukan nan na nuna ikon Shaitan. Zuwan Ubangiji zai faru ne bayan “aikin Shaitan da dukan iko da alamu da al’ajibai na karya, da dukan rudami na rashin adalchi.” 2Tasalanukiyawa 2:9,10. Manzo Yohanna kuma, yayin da yake bayana iko mai-aika al’ajiban da za a bayana a kwanakin karshe, ya ce: “yana aika alamu masu girma, har ma yana sa wuta daga sama ta sabko a duniya a gaban idanun mutane. Yana rudin mazamnan duniya kuma saboda alamun da aka ba shi shi aika.” Ruya 13:13,14. Ba ‘yan rudi ake maganarsu a nan ba. Za a rudi mutane ta wurin al’ajiban da wakilan Shaitan za su aikata ne ainihi, ba wanda za su yi karyan cewa za su aikata ba ne.BJ 549.2
Sarkin duhu, wanda ya dade yana anfani da ikonsa don aikin yaudara, yana anfani da jarabobinsa kan mutane kowane iri kuma komi yanayinsu. Ga masana masu wayewa, yakan nuna sihiri cikin kamani mafi-haske da sani, ta haka kuma yakan yi nasara wajen jawo da yawa daga cikinsu zuwa cikin tarkon sa. Hakimar da sihiri ke bayarwa ita ce wadda manzo Yakub ya bayana cewa: “Ba hikima mai-sabkowa daga bisa ba, amma ta duniya che, ta jiki, ta Shaitan.” Yakub 3:15. Amma babban mai-rudin yana boye wannan muddan boyewan zai fi biya masa bukata. Shi wanda ya iya bayyana saye da hasken malaikun sama a gaban Kristi a jejin da ya jarabce shi a ciki, yana zuwa ma mutane cikin yanayi mafi-ban sha’awa kamar malaikan haske. Ya kan ja hankali ta wurin kawo batututwa masu kayatarwa; yakan fito da yanayi na ban sha’awa; yakan jawo soyayya tawurin furcinsa mai-dadi da ke nuna kauna da nagarta. Yakan kai tunanin mutane wasu wurare can sama, ya sa mutane su yi fahariya da hikimarsu ta yadda har za su rena madawami, a cikin zukatansu. Babban halittan nan da har ya kai Mai-fansar duniya kan dutse mai matukar tsawo, ya kuma nuna masa dukan mulkikin duniya da darajarsu, zai gabatar da jarabobinsa ga mutane ta yadda zai dauke hankulan dukan wadanda ikon Allah bai yi masu garkuwa ba.BJ 549.3
Shaitan yana rudin mutane yau yadda ya rudi Hawa’u a Adnin ta wurin balmar baka, ta wurin sa mata burin samun haramtacen sani, ta wurin burin daukaka kai. Son ababan nan ne ya jawo faduwarsa, tawurinsu kuma yana so ya jawo hallakar mutane. “Za ku zama kamar Allah,” in ji shi, “kuna sane da nagarta da mugunta.” Farawa 3:5. Sihiri yana koyar da “cewa mutum halitta mai-ci gaba ne; cewa an kadara shi ya ci gaba ne har ma zuwa har abada, zuwa wurin Allahntaka.” Kuma, wai “kowace zuciya za ta shar’anta kanta ne ba wata zuciyar ba.” “Hukumcin zai yi daidai, da shike hukumcin kai ne,… kursiyin yana cikin kai na.” Wani mallamin sihiri ya ce: “Yan-uwa na mutane, duka da alloli ne, da basu fadi ba.” Wani kuma ya ce: “Kowane adali mara kuskure Kristi ne.”BJ 550.1
Don haka, a madadin adalci da cikar Allah mara-iyaka, shi ainihin wanda ya kamata a so kwarai; a madadin cikakken adalcin dokarsa, ainihin ma’aunin mutum, Shaitan ya sa yanayin mutum na zunubi da kuskure a matsayin abu kadai da za a so kwarai, kaida na hukumci, ko misanin hali. Wannan shi ne ci gaba, ba sama-sama ba, amma kasa-kasa.BJ 550.2
Doka ce ta yanayin tunani da ta ruhaniya kuma, cewa tawurin kallo mu kan canja. Zuciya ta kan rika daidaita kanta a hankali da ababanda aka bari ta yi binbini a kai. Takan shaku da abin da ta saba so tana kuma girmamawa. Mutum ba zai taba zarce mizaninsa na tsabta ko nagarta ko gaskiya ba. Idan son kansa ne ya fi darajantawa ba zai taba zama wani abin da ya fi hakan mughimmanci ba. Maimako, zai dinga nutsewa kasa-kasa ne. Alherin Allah ne kadai ke da ikon daukaka mutum. Idan aka bar shi shi kadai zai dinga nutsewa kasa-kasa ne kawai.BJ 551.1
Ga mai-son anishuwa, mai-son jin dadi, mai-son sha’awa, sihiri yana nuna kansa a fili fiye da yadda yake nuna kan sag a wanda yafi wayewa, da tunani kuma. Cikin yanayin sa mafi-muni sukan sami abin da ya je daidai da ababan da su ke so. Shaitan ya kan yi nazarin kowace alamar gazawar yanayin mutum, yakan lura da zunuban da kowane mutum zai so ya aikata sa’an nan ya kan lura kada a rasa zarafin aikata zunubin. Yakan jarabci mutane su zarce kadada game da yin abinda ya halatta, ya sa su, tawurin rashin kamewa, su raunana karfin jiki da na ruhaniya. Ya hallaka, kuma yana kan hallaka dubbai ta wurin bin abin da zukatansu ke so kwarai, ta hakanan kuma yana wulakanta yanayin mutum dungum. Kuma domin shi cika aikinsa, ta wurin ruhohin cewa wai “sani na gaskiya yana aza mutum bisa kowace doka,” cewa “duk abin da yana nan daidai ne,” cewa “Allah ba ya hukuntawa,” kuma cewa “dukan zunuban da ake yi, babu laifi.” Idan aka sa mutane suka gaskata cewa marmari shi ne doka mafi-girma, cewa ‘yanci dama ce, cewa kuma mutum zai-ba da lissafi ma kansa ne kawai, me zai sa a yi mamakin cewa rashawa da lalacewa sun mamaye kowace kasa? Jama’a da yawa suna karban koyaswoyin da ke ba su ‘yancin biyayya ga muradan zukatansu ne. Ana makala linzamin kamewa a wuyar sha’awa, ana sa karfin tunani da na rayuwa a kalkashin halayya irin na dabbobi, Shaitan kuma yana tattara dubban masu bin Kristi cikin taronsa.BJ 551.2
Amma bai kamata yaudarar sihiri ta rudi wani ba. Allah ya ba duniya isashen hasken da zai sa su iya gane tarkon. Kamar yadda mun rigaya mun nuna, dabarar da ta kasance harsashen sihiri ta na yaki da maganar Littafin. Littafin ya ce matattu basu san komi ba, cewa tunaninsu sun lalace; ba su da rabo cikin komi da ake yi a duniya; ba su san komi game da farinciki ko bakincikin masoyansu da ke duniya ba.BJ 552.1
Bayan wannan, Allah Ya hana kowane irin kamanin sadarwa da ruhohi da suka tafi. A zamanin Ibraniyawa akwai wadansu irin mutane masu da’awa kamar masu sihiri na zamanin yau, cewa suna sadarwa da matattu. Amma Littafin yana kiran ruhohin nan ruhohin aljannu ne. (Dubi littafin Lisafi 25:1-3; Zabura 106:28; Korintiyawa I, 10:20; Ruya 16:14). Littafin ya ce yin zumunta da aljannu haram ne ga Ubangiji, an kuma haramta shi, da hukumcin kisa kan wanda ya aikata. Leviticus 19:31; 20:27. Sunan maita ma kawai abin kyama ne yanzu. Ana mai da zancen cewa mutane sukan iya yin ma’amala da aljannu, kamar tatsuniya ce ta zamanin Jahiliya. Amma zancen sihiri, wanda ke da miliyoyin mabiya, wadda kuma ta shiga cikin kimiya, ta kuma shiga cikin ekklesiyoyi, ta sami karbuwa kuma cikin majalisu, har ma a fadar sarakuna-wannan babban rudin falkasuwa ce, sabon bad da kma na maita da aka haramta tun da.BJ 552.2
Ko da ba wata shaidar ainihin yanayin sihiri ma, sanin cewa ruhohin ba sa bambanta akalci da zunubi, tsakanin manzani mafi martaba da tsarki na Kristi da bayin Shaitan mafi muni. Tawurin cewa wai mutane mafi mugunta suna sama, ana kuma daukaka su a can, Shaitan ya na ce ma duniya ne: “Komi yawan muguntanka, ko ka ba da gaskiya ga Allah da Littafin ko babu, yi rayuwarka yadda ka ga dama, sama gidan ka ne.” Mallaman sihirin suna cewa a takaice: “Kowane mai-aikata mugunta nagari ne a ganin Ubangiji, yana kuma farinciki da su; ko kuwa, ina Allahn hukunci?” Malachi 2:17. In ji maganar Allah: “Kaiton wadanda ke che da mugunta nagarta, nagarta kuma mugunta su ke che da ita, wadanda su kan sa dufu maimakon haske, haske kuma maimakon dufu.” Ishaya 5:20. BJ 552.3
Makaryatan ruhohin nan su kan shiga siffar manzani su karyata abin da manzanin su ka rubuta lokacin da su ke duniya. Su kan yi musun cewa Allah ne tushen Littafin, ta hakanan kuma su yaga harsashen begen Kirista su kuma bice hasken da ke bayana hanyar sama. Shaitan yana sa duniya ta gaskata cewa Littafin kage ne kawai, ko kuma dai Littafin da ya je daidai da mutanen da, amma yanzu ya kamata a rabu da shi a mai da shi tsohon yayi. Kuma yana sauya maganar Allah da maganganun ruhohinsa. Wannan hanyar ta na hannunsa ne; ta wurinta zai iya sa mutane su gasktata ba in da ya ga dama. Yana boye Littafin da ya kamata ya hukumta shi da masu bin sa; yana mai da Mai-ceton duniya kamar kowane mutum kawai. Kuma kamar yadda sojojin Romawa masu gadin nan su ka dinga b za karyan da priestoci da dattibai suka ce su baza don karyata tashin Kristi, hakanan ne masu gaskata zancen ruhohin nan ke kokarin nuna cewa babu wani abin al’ajibi game da rayuwar Mai-ceton mu. Bayan neman tura Yesu a gefe, suna jan hankula zuwa al’ajibansu, da cewa wai sun fi ababan da Kristi ke yi.BJ 553.1
Gaskiya ce cewa yanzu sihiri yana sake kamaninsa, kuma, ta wurin boye ainihin munanan fuskokinsa, yana daukan kamanin Kiristanci. Amma zatattukansa su na gaban jama’a da dadewa, kuma suna bayana ainihin halinsa. Ba za a iya boye koyaswoyin nan ko a boye su ba.BJ 553.2
Ko a kamaninsa a yanzu rudi ne mafi-mugunta domin da zurfin wayo a ke yinsa. Da dai, yana kayarta Kristi da Littafin, amma yanzu yana cewa wai ya amince da duka biyu din. Amma ana fassara Littafin da yadda masu zunubi ke so, ana kuma wofinta muhimman koyaswoyin sa. Ana nanata cewa kauna ce babban halin Allah, amma ana rage shi ta yadda ba a bambanta nagarta da mugunta kuma. A na boye adalcin Allah da yadda yake hukumta zunubi da sharuddan dokarsa mai-tsarki. Ana koya ma mutane su mai da dokoki goma kamar mataciyar doka. Tatsuniyoyi masu dadi, masu rudi suna jan hankula har su sa mutane su musunci cewa Littafin ne tushen bangaskiyarsu. Ana kin Kristi sosai kamar da, amma Shaitan ya makantar da idanun mutane ta yadda ba za a gane rudin ba.BJ 554.1
Mutane kalilan ne suna da kyakyawar ganewar ikon rudi da sihiri ke da shi da hatsarin shiga kalkashin tasirinsa. Da yawa su kan shiga cikinsa domin su ga yadda yake ne kawai. Ba su yarda da shi ba, kuma zasu yi kyamar tunanin ba da kansu kalkashin mulkin ruhohin. Amma su kan sa kafa cikin haramtacen wurin, mai-hallakaswan kuma yakan yi anfani da ikonsa a kan su ba da sonsu ba. Da zaran sun ba da zukatansu gare shi sau daya, sai ya rike su cikin bauta. Ba zai yiwu, ta wurin karfin kansu, su fita daga hannunsa ba. Ikon Allah da ake samu tawurin addu’ar naciya da bangaskiya ne kadai zai iya kubutar da kamammun mutanen.BJ 554.2
Dukan masu halayyan zunubi, ko masu sha’awar sanannen zunubi, suna neman jarabobin Shaitan ke nan. Suna raba kansu da Allah da kulawar malaikunsa, sa’an da mugun ya gabatar da jarabobinsa, ba su da kariya, kuma cikin sauki a kan kama su. Masu sa kansu cikin ikonsa hakanan ba sa gane inda za su karasa. Da zaran ya kama su, majarabcin ya kan yi amfani da su su jawo wadansu zuwa hallaka.BJ 554.3
In ji annabi Ishaya, “Sa’anda su ka che maku, ku bidi ga masu-mabiya, ga bokaye kuma, wadanda su ke kashe murya, suna magana da dan murya kamar tsuntsu; ba ya kamata mutane su yi bida ga Allahnsu ba? A bidi ga matattu sabada masu rai? A komo bisa shari’an da shaidan! Idan basu fadi bisa ga wannan magana ba, hakika babu wayewan gari a gare su ba.” Ishaya 8:19,20. Da mutane sun yarda su karbi gaskiyan da Littafin ya bayana a fili hakanan game da yanayin mutum da na matattu, da sun gane cewa sihiri aikin Shaitan ne da yake yi da kikonsa da alamu da al’ajiban karya. Amma maimakon rabuwa da zunuban da su ke so, mutane da yawa suka rufe idanunsu ga hasken su ci gaba, da sa kulawa da gargadi, yayin da Shaitan ke nannade su cikin takokinsa, har su zama nama gare shi. “Da shike ba su amsa kamnar gaskiya da za su tsira ba. Sabili da wannan fa Allah yana aike masu da aikawar sabo, har da za su gaskanta karya.” Tassalunikawa II, 2:10,11.BJ 555.1
Masu hamayya da koyaswoyin sihiri, ba da mutane kadai suke fada ba, har da Shaitan da malaikunsa ma. Sun shiga fada da mulkoki da ikoki da miyagun ruhohi a madaukakan wurare ne. Shaitan ba zai taba ba da kai ba sai dai idan ikon ‘yan sakon sama ya kore shi. Ya kamata mutanen Allah su iya tare shi yadda Mai-cetonmu Ya tare shi, da kalmomin nan: “An rubuta.” Shaitan zai iya maimaita Littafin yanzu kamar zamanin Kristi, kuma zai karkata koyaswoyinsa domin shi tabbatar da yaudararsa. Dole masu rai a wannan mawuyacin lokacin su gane shaidar Littafin domin kansu.BJ 555.2
Da yawa za su fuskanci ruhohin aljannu cikin siffar kamnatattun yanuwa da abokansu da suka mutu, masu baza ridda mai-hadarin gaske. Aljannun za su yi mana fadanci sosai su kuma aikata al’ajibai don tabbatar da karyansu. Dole mu shirya tare su da gaskiyan nan na Littafin cewa matattu basu san komi ba, kuma cewa su din da suke bayanuwa ruhohin aljannu ne.BJ 556.1
A gabanmu ga “Sa’ar jaraba, wannan da ke zuwa bisa ga dukan duniya, domin a jarabci mazamnan duniya.” Ruya 3:10. Dukan wadanda bangaskiyar su ba ta kafu sosai kan maganar Allah ba za a rude su a kuma rinjaye su. Shaitan yana aiki da dukan rudami na rashin adalci domin shi mallaki ‘ya’yan mutane, rudinsa kuma zai ci gaba. Amma ba zai cim ma burinsa ba sai dai in mutane sun amince da jarabobinsa. Wadanda da naciya suke neman sanin gaskiya, suna kuma kokarin tsarkake rayukansu ta wurin biyayya, ta hakanan kuma suna iyakar kokarinsu domin shiryawa don sabanin, Allah na gaskiya za ya zama tsaronsu. “Tun da ka kiyaye maganar hankuri na, ni ma zan kiyaye ka” (aya 10), alkawalin Mai-ceton ke nan. Zai iya aiko kowane malaika daga sama domin su tsari mutanensa, maimakon barin Shaitan ya rinjayi mutum daya mai-dogara gare shi.BJ 556.2
Annabi Ishaya ya bayana yaudaran da za ta abko ma miyagu, wadda za ta sa su dauka cewa Allah bazai hukumta su ba. Suna cewa: “Mun yi alkawali da mutuwa, muna kwa amana da Sheol, sa’anda bala’i mai-rigyawa za ya ratsa, ba za ya zo wurinmu ba; gama mun mai da karya mafakarmu, mun buya kuma kalkashin karya.” Ishaya 28:15. Cikin masu maganan nan akwai wadanda cikin taurin kai da rashin tuba su ke ta’azantar da kansu da tabbacin da ake yi masu cewa babu horo don mai-zunubi, cewa wai dukan ‘yan Adam, komi lalacewa, za a daukaka su zuwa sama, su zama kamar malaikun Allah. Amma fiye da wannan ma akwai masu yin yarjejjeniya da mutuwa, suna alkawali da lahira, wadanda ke kin gaskiyan da Allah ya tanada domin tsaron masu adalci a ranar wahala, suna kuma karban garkuwar karya da Shaitan ke bayarwa a maimako, watau rudin nan na sihiri.BJ 556.3
Abinda da ya fi ban mamaki shi ne makantar mutanen yanzu. Dubbai suna kin maganar Allah cewa bai kamata a gaskata shi ba, amma da marmari suna karban rudin Shaitan. Masu shakka da masu ba’a suna sokar masu goyon bayan imanin annabawa da manzani, suna kan cewa kuma su kansu ta wurin yin ba’a ga maganar Littafin game da Kristi da shirin ceto da horon da za a yi ma masu kin gaskiya. Suna cewa wai suna tausaya ma masu kankantan tunani mara karfi cike da camfi da ya sa har suna yarda da maganar Allah har suna biyayya ga dokarsa. Suna nuna tabbaci sosai sai ka ce sun dai yi yarjejjeniya da mutuwa, suka yi alkawali da lahira kuma, kaman sun gina shingen da ba za a iya wucewa ba ne tsakaninsu da ramuwar Allah. Ba abinda zai iya ba su tsoro. Sun ba da kansu ga majarabcin gaba daya, suka hada kai da shi, sun kuma amshi ruhunsa sosai, ta yadda ba su da iko ko niyyar tserewa daga tarkonsa.BJ 557.1
Shaitan ya dade yana shirya yunkurinsa na karshe don rudin duniya. Ya kafa harsashen aikinsa ta wurin tabbacin da ya ba Hawa’u a Adnin cewa, “Ba lallai za ku mutu ba.” “Ran da kuka chi daga chiki, ran an idanunku za su bude, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.” Farawa 3:4,5. Da kadan da kadan ya rigaya ya shirya hanya domin babban rudinsa mafi girma ta wurin tsarin sihiri. Bai rigaya ya kai karshen tsare tsarensa ba; amma zai kai a karshen ringin lokaci. In ji annabin: “Na ga kuma kazaman ruhohi uku, sai ka che kwadi,… gama ruhohin aljannu ne su, masu aika alamu; suna kwa fita zuwa wurin sarakunan duniya, garin su tattara su zuwa yakin babbar rana ta Allah mai-iko duka.” Ruya 16:13,14. Ban da wadanda ikon Allah ta wurin bangaskiya zai kiyaye su, dukan duniya za ta rude ta runtuma zuwa cikin rudinsa. Da sauri a ke ta rudin mutane zuwa cikin tsaro na karya mai-hadarin gaske, inda zubowar fushin Allah ne kadai zai falkas da su.BJ 557.2
In ji Ubangiji Allah: “Gaskiya kwa zan maishe ta igiya, adilchi kuma in maishe shi magwaji; kankara za ta share mafalkan karya, ruwaye kuma za su sha kan moboya. Za a warware alkawalinku da mutuwa, amanarku da Sheol ba za ta tsaya ba; lokacin da bala’i mai-rigyawa za ya ratsa, sa’an nan za ku sha takawa daga kalkashinsa.” Ishaya 28:17,18.BJ 558.1