Babi na 25—Dokar Allah Ba Ta Sakewa
Babban Jayayyar
- Contents- Gabatarwa
- Babi na 1—Hallakawar Urushalima
- Babi na 2—Tsanantawa a Karni na Farko
- Babi na 3—Riddan
- Babi na 4—Waldensiyawa
- Babi na 5—John Wycliffe
- Babi na 6—Huss da Jerome
- Babi na 7—Rabuwar Luther da Rum
- Babi na 8—Luther a Gaban Majalisa
- Babi na 9—Dan Canjin Switzerland
- Babi na 10—Ci Gaban Canji a Jamus
- Babi na 11—Yardar ‘Ya’yan Sarkin
- Babi na 12—Canjin Faransa
- Babi na 13—Netherlands da Scandinavia
- Babi na 14— ‘Yan Canjin Ingila na Baya.
- Babi na 15—Littafi da Juyin-Danwaken Faransa
- Babi na 16—Ubani Matafiya
- Babi na 17—Alkawuran Dawowan Kristi
- Babi na 18—Dan Canji America
- Babi na 19—Haske Ta wurin Duhu
- Babi na 20—Babban Falkaswa na Ibada
- Babi na 21—Gargadin da Aka Ki
- Babi na 22—Cikawar Annabci
- Babi na 23—Menene Haikalin?
- Babi na 24—Cikin Wuri Mafi-Tsarki
- Babi na 25—Dokar Allah Ba Ta Sakewa
- Babi na 26—Aikin Canji
- Babi na 27—Falkaswa na Zamani
- Babi na 28—Fuskantar Rahoton Rayuwa
- Babi na 29—Mafarin Mugunta
- Babi na 30—Gaba Tsakanin Mutum da Shaitan
- Babi na 31—Wakilcin Miyagun Ruhohi
- Babi na 32—Tarkokin Shaitan
- Babi na 33—Babban Rudi na Farko
- Babi na 34—Ko Mattatu Za Su Iya Magana da Mu?
- Babi na 35—Barazana ga Yancin Lamiri.
- Babi na 36—Yakin da Ke Zuwa.
- Babi na 37—Littafi, Mai-tsaro.
- Babi na 38—Gargadi na Karshe
- Babi na 39—Kwanakin Wahala
- Babi na 40—An Tsirar da Mutanen Allah
- Babi Na 41—Mayar da Duniya Kango
- Babi na 42—Karshen Jayayyar
Search Results
- Results
- Related
- Featured
- Weighted Relevancy
- Content Sequence
- Relevancy
- Earliest First
- Latest First
- Exact Match First, Root Words Second
- Exact word match
- Root word match
- EGW Collections
- All collections
- Lifetime Works (1845-1917)
- Compilations (1918-present)
- Adventist Pioneer Library
- My Bible
- Dictionary
- Reference
- Short
- Long
- Paragraph
No results.
EGW Extras
Directory
Babi na 25—Dokar Allah Ba Ta Sakewa
“Aka bude haikalin Allah da ke chiki sama, a chikin haikali na sa kuma aka ga sanduki na alkawalinsa.” Ruya 11:19. Sandukin alkawalin Allah yana cikin wuri mafi-tsarki ne. A hidimar haikali na duniya wadda alama ce da kwatancin al’amura na sama, akan bude wannan wuri na biyu a haikalin. Sabo da haka sanarwar cewa an bude haikalin Allah a sama, kuma an ga sandukinsa ya nuna cewa an bude wuri mafi-tsarki na haikalin sama ke nan a 1844, sa’anda Kristi ya shiga wurin domin aiwatar da aikin karshe na kafara. Wadanda ta wurin bangaskiya suka bi Babban Priest nasu yayin da ya shiga hidimarsa a wuri mafi-tsarkin sun ga sandukin alkawalinsa. Sa’anda suka yi nazarin batun haikalin, sun gane sakewar hidimar Mai-ceton, suka kuma ga cewa yanzu yana hidima a gaban sandukin Allah ne, yana anfani da jininsa a madadin masu zunubi.BJ 430.1
Sandukin cikin haikali na duniya ya kunshi alluna biyu na dutse da aka rubuta dokokin Allah a kai. Sandukin dai wurin ajiya ne na allunan dokar, kuma kasancewar dokokin ya ba sandukin darajarsa da tsarkinsa. Sa’anda aka bude haikalin Allah a sama, an ga sandukin alkawalinsa. Cikin wuri mafi-tsarki, a cikin haikali na sama, an ajiye dokar Allah cikin tsarki-dokan nan dai da Allah kansa Ya furta cikin tsawa na Sinai ya kuma rubuta da yatsansa a allunan dutse.BJ 430.2
Dokar Allah a haikali na sama shi ne asalin, wanda kuma dokokin da aka rubuta a allunan dutse, Musa kuma ya rubuta a cikin Littafin, hoton su ne. Wadanda suka kai ga fahimtar wannan muhimmin batun ta hakanan ne aka kai su ga ganin yanayin rashin sakewa na dokar Allah. Sun ga karfin kalmomin Mai-ceton cewa: “Har sama da duniya su shude, ko wasali daya ko digo daya ba za su shude daga Attaurat ba, sai dukan abu ya chika.” Matta 5:18. Da shike dokar Allah bayanin nufinsa ne, hoton halinsa kuma, dole zai dawama, amintacen shaida a sama. Ba a soke ko doka daya ba, ba a soke wasali daya ko digo daya ba. In ji mai-zabura: “Har abada ya Ubangiji maganarka ta kafu a sama.” “Dukan dokokinsa masu aminchi ne. Sun kafu har abada abadin.” Zabura 119:89; 111:7,8.BJ 431.1
A tsakiyar dokoki goma akwai doka ta hudu, yadda aka furta ta tun farko: “Ka tuna da ranar assabbat, domin a kiyaye ta da tsarki. Kwana shidda za ka yi aiki, ka kwa gama dukan aikinka; amma rana ta bakwai assabat ne ga Ubangiji Allahnka: cikinta ba za ka yi kowane aiki ba, da kai, da danka, da diyarka, da bawanka, da baiwarka, da bisashenka, da bakonka wanda ke chikin kofofinka: gama chikin kwana shidda Ubangiji ya yi sama da kasa, da teku da abin da ke chikinsu duka, ya huta kuma a kan rana ta bakwai; domin wannan Ubangiji ya albarkachi ranar assabbat, ya tsarkake ta kuma.” Fitowa 20:8-11.BJ 431.2
Ruhun Allah Ya shiga zukatan masu nazarin nan na maganarsa. Aka nuna masu cewa sun ketare dokan nan ta wurin rashin kulawa da ranar hutu ta Mahalicin. Suka fara binciken dalilan kiyaye rana ta fari ga mako maimakon ranan da Allah ya tsarkake. Ba su sami shaida a cikin littafin cewa an warware doka ta hudu ba, ko kuma an canja assabbat din ba, albarkan da ya fara tsarkake rana ta bakwai ba a taba cire ta ba. Da gaske suka rika neman sanin nufin Allah da aikata shi kuma; yanzu da suka ga cewa su masu ketare dokarsa ne, bakinciki ya cika zukatansu, suka kuma nuna biyayyarsu ga Allah ta wurin kiyaye assabbat dinsa da tsarki.BJ 431.3
An yi kokari sosai ta hanyoyi da bam dabam don kawas da bangaskiyarsu. Kowa ya gane cewa idan haikali na duniya hoto ne ko kwaikwayon haikali na sama, dokan da aka ajiye a cikin sanduki a duniya daidai hoton dokan da ke cikin sanduki na sama ne; cewa kuma an yarda da gaskiya game da cewa haikali na sama ya kunshi amincewa da dokar Allah da assabbat na doka ta hudu. Wannan ne asirin jayayya mai daci da aka yi game da fassarar nassosi da ta bayana hidimar Kristi a haikali na sama. Mutane suka so su rufe kofar da Allah Ya bude, su kuma bude kofan da Ya rufe. Amma Shi “wanda ya bude, ba mai-rufewa, ya rufe, ba mai-budewa,” Ya rigaya Ya ce, “Gashi na sa kofa a gabanka budaddiya, wadda ba mai-rufewa.” Ruya 3:7,8. Kristi Ya bude kofa ko kuma hidima ta wuri mai-tsarki, haske ya rika haskakawa ta wannan badaddiyar kofar haikali na saman, aka kuma nuna cewa doka ta hudu tana cikin kundin dokar; abin da Allah ya kafa ba wanda zai warware.BJ 432.1
Wadanda suka rigaya suka karbi haske game da tsakancin Kristi da dawamar dokar Allah sun iske cewa gaskiyan da aka gabatar cikin Ruay 14 ke nan. Sakonin wannan sura sun kunshi gargadi mai-sassa uku da zai shirya mazamanan duniya domin zuwan Ubangiji na biyu. Sanarwan nan “sa’ar hukuncin sa ta zo,” tana magana game da aikin karshe na hidimar Kristi ne domin ceton mutane. Yana shelar wata gaskiya da dole a dinga shelar ta har sai tsakancin Mai-ceton ya kare, ya kuma dawo duniya domin daukan mutanensa zuwa wurin kansa. Dole aikin hukumcin da aka fara a 1844 ya ci gaba har sai an gama jukumcin dukan mutane, rayayyu da matattu; sabo da haka aikin zai kai har rufewar gafara. Domin mutane su shirya tsayawa gaban shariar, sakon yana umurtarsu, su “ji tsoron Allah (su) ba shi daraja.” Su “yi sujada ga wanda Ya yi sama da duniya da teku da mabulbulan ruwaye.” An nuna sakamakon karban sakonin nan kamar haka: “Nan ga hankurin sarkaka, su wadanda ke kiyaye dokokin Allah da; imanin Yesu.” Domin a shirya ma hukumcin, wajibi ne mutane su kiyaye dokar Allah. Wannan dokan ne za a yi anfani da shi don hukumcin. Manzo Bulus ya ce: “Kuma dukan wadanda sun yi zunubi chikin shari’a bisa ga shari’a za a hukumta masu;… chkin rana da Allah za ya shar’anta asiran mutane, bisa ga bisharata, ta wurin Yesu Kristi.” Ya kuma ce, “masu aika doka za su kubuta.” Romawa 2:12-16. Bangaskiya muhimmin ne ga kiyayewar dokar Allah, gama “ba shi yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya.” Kuma “iyakar abinda ba na bangaskiya ba zunubi ne.” Ibraniyawa 11:6; Romawa 14:23.BJ 432.2
Tawurin malaika na fari ana kiran mutane su “ji tsoron Allah (su) ba shi daraja” su kuma yi masa sujada a matsayinsa na mahalicin sama da duniya. Domin su yi hakan, dole su yi niyya ga dokar sa. In ji mai-hikimar: “Ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kadai ne wajibin mutum.” Mai-wa’azi 12:13. Idan ba biyayya ga dokokinsa, ba sujadar da za ta gamshi Allah. “Gama kamnar Allah kenan, mu kiyaye dokokinsa.” “Wanda ya kawasda kunnensa daga jin shari’a, ko addu’atasa abin kyama ce.” 1Yohanna 5:3; Misalai 28:9.BJ 433.1
Dalilin sujada ga Allah shi ne cewa shi ne mahalici, kuma dukan sauran ababa ta dalilinsa suke kasancewa. Kuma ko ina, a Littafin, ana shaida bukatarsa ta cewa a yi masa sujada da bangirma, bisa allolin kafirai domin Shi kadai ne mai-ikon halitta. “Gama dukan alloli na alloli gumaka ne; amma Ubangiji ya yi sammai,” Zabura 96:5. “Ga wa fa za ku kamanta ni, da zan zama daidai da shi? in ji Mai-tsarki. Ku ta da idanunku sama, ku duba ko wane ne ya halichi wadannan.” “Gama hakanan Ubangiji ya fadi, shi wanda ya halichi sammai; shi ne Allah; mai-sifanta duniya. Mai yinta kuma, “Ni ne Ubangiji; babu wani kuma,” Ishaya 40:25,26; 45:18. In ji mai-zabura; “Ku sani Ubangiji shi ne Allah: shi ne ya yi mu, mu kwa nasa ne,” “Ku zo, mu yi sujada, mu yi ruku’u; mu durkusa a gaban Ubangiji mahalichinmu.” Zabura 100:3; 95:6. Kuma tsarkaka masu sujada ga Allah a sama suna cewa dalilin da suke masa sujada shi ne cewa “Kai ne mai-isa ka karbi daukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu; gama kai ka halici dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasanche, sabada nufinka aka haliche su.” Ruya 4:11.BJ 433.2
Cikin Ruya 14, ana bidar mutane su yi sujada ga Mahalici; kuma annabcin yana ambaton wata kungiya da ke kiyaye dokokin Allah, sakamakon sakon nan mai ressa uku. Daya daga cikin dokokin nan yana nunawa kai tsaye cewa Allah ne mahalicin. Doka ta hudu tana cewa; “Rana ta bakwai ‘assabbat ne ga Ubangiji Allahnka;… gama chikin kwana shidda Ubangiji ya yi sama da kasa, da teku, da abinda kechikinsu duka, ya huta kuma a kan rana ta bakwai: domin wannan Ubangiji ya albarkachi ranar assabbat ya tsarkake ta” Fitowa 20:10,11. Game da assabbat Ubangiji ya kuma ce, “shaida che tsakanina da ku, domin ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.” Exekiel 20:20. Dalilin kuma shi ne: “gama chikin kwana shidda Ubangiji ya yi sama da duniya, a chikin rana ta bakwai ya huta, ya lumfasa.” Fitowa 31:17.BJ 434.1
“Muhimmancin assabbat a matsayin abin tunawa da halitta shi ne cewa yana tuna mana da ainihin dalilin da ya sa Allah ne ya kamata a yi sujada gare shi.” Domin shi ne mahallici, mu kuma halitunsa ne “sabo da haka Assabbat ne tushen sujada ga mahalici da shike yana koyar da wannan muhimmiyar gaskiyar ta hanya mafi kayatarwa, ba kuma wani abin da ke koyas da hakanan. Ainihin dalilin sujada ga Allah, ba na assabbat ba kawai, dukan sujada, yana kunshe cikin bambanchin nan ne tsakanin mahalici da halitunsa. Wannan ba zai taba zama tsohon abu ba, kuma kada a taba manta shi.” Domin a dinga sa wannan a zukatan mutane ne Allah ya kafa assabbat a Adnin, kuma muddan dai kasanchewarsa mahalicin mu ne dalilin sujadarmu gareshi, assabbat kuwa zai ci gaba kasancewa alamarsa da abin tunawansa. Da duk duniya ta kiyaye assabbat, da tunanin mutum da sha’awoyinsa sun fuskanci Allah a matsayin wanda za a girmama a kuma yi masa sujada, kuma da ba a taba samun wani kafiri ko mai-cewa ba Allah ba. Kiyayewar assabbat alama ce ta biyayya ga Allah na gaskiya, “shi wanda ya yi sama, da duniya da teku, da mabulbulan ruwaye.” Saboda haka sakon da ke umurtar mutane su yi sujada ga Allah su kiyaye dokokinsa zai kira gare su musamman su kiyaye doka ta hudu.BJ 434.2
Sabanin masu kiyaye dokokin Allah suna kuma da imanin Yesu, malaika na uku ya ambaci wata kungiya kuma wadda aka ba da kashedi mai-nauyi game da kurakuranta cewa: “Idan kowane mutum ya yi sujada ga bisan da gunkinsa, ya karbi shaida kuma a goshinsa, ko a hannunsa, shi kuma za ya sha ruwan anab na hasalar Allah? Ruya 14:9,10. Kafin a fahimci sakon nan dole sai an fasara alaman da ke ciki daidai. Mene ne bisan da gumkin, da shaidan ke misaltawa?BJ 435.1
Jerin annabcin da ake iske alamun nan a ciki ya fara daga Ruya 12 ne, da dragon da ya so ya hallaka Kristi lokacin haifuwarsa. An ce Shaitan ne dargon din (Ruya 12:9) shi ne ya motsa Hirudus ya nemi kashe Mai-ceton. Amma babban wakilin Shaitan wajen yaki da Kristi da mutanensa a karnonin farko na kristanci mulkin Rum ne, inda kafirci ne addinin da ya mamaye ko ina. Sabo da haka ya yin da dragon ke misaltar Shaitan, a wata hanyar kuma alama ce ta Rum.BJ 435.2
Cikin sura 13 (aya 1-10) an bayana wani bisan kuma, mai-kama da damisa, wanda “dragon kuma ya ba shi ikonsa, da kursiyinsa, da hukumchi mai-girma. Yawancin masu kin ikon paparuma sun gaskata cewa wannan alamar mulkin paparuma ne, wanda ya gaji iko da kursiyi da hukumcin da mulkin Rum na da ta taba mallaka. Game da bisa mai-kama da damisan an ce: “aka ba shi baki kuma mai-yin ruba da saba-sabe … ya bude bakinsa kuma domin shi yi sabon Allah, shi sabi sunansa, da mazamninsa, watau wadanda ke zamne a sama nan. Aka yarda masa kuma shi yi yaki da tsarkaka, shi yi nasara da su: aka ba shi kuma hukumchi bisa kowache kabila da al’umma.” Wannan annabci da ya yi kama sosai da kwatacin karamin kaho na Daniel 7, ba shakka yana maganar tsarin paparuma ne.BJ 436.1
“Aka ba shi iko kuma da za shi dawama wata arba’in da biyu.” In ji annabin, Na ga dayan kawunansa sai ka che an yi masa bugun ajali.” Kuma: “Idan an kadara kowane mutum ga bauta ga bauta za shi: idan kowane mutum za ya yi kisa da takobi, da takobi za a kashe shi.” Wata arba’in da biyu din daidai suke da “wokachi da wokatai da rabin wokachi,” shekara uku da rabi ko kwana 1260 na Daniel 7, lokacin da mulkin paparuma zai dauka yana zaluntar mutanen Allah. Lokacin nan ya fara da samun fifikon paparuma ne a AD 538, wanda ya kare a 1798. A lokacin ne mayakan Faransa suka mai da paparuma kamame, ikonsa kuma ya karbi bugun ajalinsa, aka kuma cika annabcin nan cewa “Idan an kadara kowane mutum ga bauta, ga bauta za shi.”BJ 436.2
A wannan lokaci an kuma fito da wata alama. Annabin ya ce: “Na ga wani bisa kuma yana fitowa daga chikin kasa; yana da kafo biyu kamar dan rago,” Aya11. Kamanin bisan nan da yanayin tasowarsa suna nuna cewa al’umman da ta ke misaltawa ba ta yi kama da wadanda aka bayana a alamun da suka gabata ba. An misalta ma Daniel mulkokin da suka mallaki duniya da bisashe masu kisa ne da suka taso sa’an da “iskoki fudu na sama suka pasu daga bisa kan teku” Daniel 7:2. Cikin Ruya 17, malaika ya bayana cewa ruwaye suna misalta “al’ummai ne da taron jama’a, da dangogi da harsuna.” Ruya 17:15. Iska alamar tashin hankali ne. Pasuwar iskoki hudu na sama a kan teku yana misalta munanan yakoki da manyan tawaye da suka sa wadansu mulkoki suka sami iko.BJ 436.3
Amma an ga bisa mai kahoni irin na dan ragon “yana fitowa daga chikin kasa” ne. Maimakon hambare wadansu mulkoki domin ta kafa kanta wannan al’umma da aka misalta dole za ta taso daga wurin da mutane ba su taba zama a cikinta ba ne, ta kuma girma a hankali cikin salama. Ba za ta taso daga al’ummai masu jama’a masu fama kuma na Tshohuwar Duniya, watau tekun nan na “taron jama’a ne.BJ 437.1
Wace al’ummar Sabuwar Duniya ce ta yi tashen samun iko a 1798, wadda ta nuna alamar karfi da girma, ta kuma jawo hankalin duniya? Al’umma daya ce kadai ta cika bayanin annabcin nan, watau Amerika. Akai-akai ana anfani da kalmomin Littafin cikin rubuce rubucen tarihi don bayana tasowa da girman al’umman nan. An ga bisan yana “fitowa daga chikin kasa” ne, kuma ma’anar kalmar da aka juya zuwa “fitowa” ita ce yin girma ko kuma tsirowa kamar tsiro, kuma dai dole al’ummar za ta taso daga wurin da ba a taba kasancewa ciki ba ne. Wani shahararren marubuci, game da tasowar Amerika ya yi zancen “asirin tasowarta daga wofi,” ya kuma ce: “Kamar iri, shuru muka girma muka zama kasa mai-ikon kanta.” Wata majallar Turai a 1850 ta yi magana game da Amerika inda ta ce kasa ce mai-ban mamaki da ke “tasowa” kuma a cikin shurun duniyan nan ta na kara ikonta da alfarmarta.” Edward Everett, yayin da yake yabon wadanda suka kafa al’umman nan ya ce: “Sun nemi wuri ne a gefe inda ba hayanniya da shike ba sannanne ba ne, kuma mara hakuri sabo da nisan sa, inda karamar ekklesiyar Leyden din nan za ta mori ‘yancin ta na addini? Dubi manyan sassan da cikin nasara cikin salama,… suka rike tutocin giciyen!”BJ 437.2
“Yana da kafo biyu kamar dan rago.” Kahonin nan suna nuna yarantaka ne, da rashin laifi da tawali’u, daidai yadda Amerika ta ke sa’anda aka nuna ma annabawa cewa tana tasowa a 1798. Cikin Kirista masu hijiran da suka fara gudu zuwa Amerika suka nemi mafaka daga danniyar sarauta da zazzafar ra’ayin priestoci akwai da yawa da suka dukufa wajen kafa gwamnati bisa harsashen ‘yancin yangaranci da na addini. Ra’ayoyinsu sun sami shiga Furcin Mulkin-kai, wanda ya ambaci babban gaskiyan nan cewa “an halici dukan mutane daidai ne, kuma suna da ‘yanci da ba za a kwace ba, na rai da walwala da neman farinciki.” Kundin tsarin mulkin kuma ya na tabbatar ma mutane ‘yancin mulkin kai, cewa wakilai ne da mutane masu rinjaye suka zaba zasu kafa dokoki su aiwatarda su kuma. An kuma ba da ‘yancin addini, aka yarda kowane mutum shi yi sujada ga Allah bisa ga muradin lamirinsa. Jamhuriyanci da Kin ikon paparuma suka zama muhimman kaidodin al’ummar. Kaidodin nan ne asirin karfinta da ci gabanta. Wulakantattu da wadanda aka zalunce su cikin Kiristanci sukan zo wannan kasar cikin sha’awa da bege. Miliyoyi suna neman zuwa kasar, Amerika kuwa ta girma ta zama daya daga cikin al’ummai mafi-karfi a duniya.BJ 438.1
Amma bisan, mai-kaho irin na dan ragon, “yana kwa zanche kamar daragon. Dukan hukumchin bisa na fari kwa yana aiki da shi a gaban idon sa. Yana sa, duniya da mazamna a chiki su yi sujada ga bisa na fari wanda bugunsa na ajali ya warke,… yana che ma wadanda ke zamne a duniya, su yi gumki ga bisan wanda ya sha bugun takobi ya kwa yi rai.” Ruya 13:11-14.BJ 438.2
Alamun kaho irin na dan rago da murya kaman na dragon suna misalta sabanin da ke tsakanin da’awa da kuma ayukan al’umman da ake misaltawa ne: ayukan ta suna sabani da maganan ta. “Maganan” al’umman, abinda hukumomin majalisa da na shari’a ta ke yi ne. tawurin ababan da hukumomin nan biyu ke yi al’umman za ta karyata kyawawan kaidodin nan na ‘yanci da salama da ta bayana a matsayin harsashen hanyar tafiyar da al’ummaranta. Annabcin cewa za ta yi “zanche kamar dragon,” kuma “dukan hukumcin bisa na fari kwa yana aiki da shi,” annabci ne kai tsaye na ruhun rashin hakuri da zalunci da al’ummomin da dragon da bisa mai-kama da damisan anan ke misaltawa suka nuna. Batun nan kuma cewa bisa mai kaho biyu “Yana sa duniya da mazamna a chiki su yi sujada ga bisa na fari” a fili yana nuna cewa za a yi anfani da ikon al’umman nan don tilasta ibada da za ta zama aikin mubaya’a ga paparuma.BJ 439.1
Wannan abu zai saba ma kaidodin gwamnatin nan, da ‘yancin hukumominta, da furcin ‘yancin kanta da, da kuma kundin tsarin mulkinta. Wadanda suka kafa kasar sun yi kokarin hana yin amfani da ikon kasa a aikin ekklesiya, wanda dole zai jawo rashin hakuri da zalunci. Kundin tsarin mulkin ya ce “Majalisa ba za ta yi wata doka game da kafawar addini, ko hana ‘yancin yin addini ba,” kuma cewa “ba gwaji na addini da za a taba anfani da shi ya zama sharadin rike mukami na gwamnatin Amerika ba.” Sai dai in an ketare shingayen nan na ‘yancin al’umman ne za a iya anfani da ikon gwamnati don tilasta kiyayewar addini. Bisan nan mai-kaho kaman na dan rago, mai-tawali’u, mara cutaswa kuma, shi ne kuma yana magana kamar dragon.BJ 439.2
“Yana che ma wadanda ke zamne a duniya, su yi gumki ga bisan.” A nan, ana maganan wani tsarin gwamnati ne inda ikon yin doka yana wurin mutane ne, shaida cewa annabcin nan game da Amerika ne.BJ 439.3
Amma menene “gumki ga bisan?” kuma yaya za a yi shi? Ana kuma ce da shi gumkin bisan. Idan sansance bisan da yadda za a yi shi dole mu nazarci halayyan bisan kan sa, watau tsarin paparuma.BJ 440.1
Sa’anda ekklesiyar farko ta lalace ta wurin rabuwa da saukin kan bishara, ta kuma karbi al’adun kafirci, ta rasa Ruhun Allah da ikonsa, kuma domin ta mallaki lamirin mutane, sai ta nemi goyon bayan iko na duniya. Sakamakon shi ne tsarin paparuma, ekklesiya da ta mallaki ikon kasa da kuma yin anfani da shi don ci gaban manufofinta, musamman don horon “ridda.” Domin Amerika ta yi gumki ga bisan dole hukumar addini ta mallaki gwamnati ta yadda ekklesiya za ta kuma yi anfani da ikon gwamnati don cim ma manufofinta.BJ 440.2
Duk lokacin da ekklesiya ta sami ikon kasa, takan yi anfani da shi don horon masu jayayya da koyaswoyinta. Ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma da suka bi matakan Rum tawurin hada hannu da mulkokin duniya, sun nuna wannan irin hali na son takura ma ‘yancin addini. Misali shi ne zaluncin da Ekklesiyar Ingila ta yi ma masu kin yarda da ita, cikin karni na sha shida da na sha bakwai an tilasta dubban ma’aikatan ekklesiya masu kin yarda da ekklesiya suka gudu daga ekklesiyoyinsu, da yawa kuma, pastoci da sauran mutane, aka sa su biyan tara, ko zuwa kurkuku, ko shan zalunci ko kuma aka kashe su ma.BJ 440.3
Ridda ce ta sa ekklesiyar farko ta bidi taimakon gwamnati, wannan kuma ya shirya hanyar haifar da tsarin paparuma, watau bisan. In ji Bulus, “Wannan sai riddan ta fara zuwa, mutamen zunubi kuma ya bayanu”. Tassalunikawa II, 2:3. Sabo da haka ridda cikin ekklesiya ne zai shirya hanya domin gumkin bisan. BJ 440.4
Littafin ya bayana cewa kafin zuwan Ubangiji za a tarar da lalacewar addini irin na zamanai na farkon. “Amma sai ku san wannan, chikin kwanaki na karshe miyagun zamanu za su zo. Gama mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kurdi, masu-ruba, masu-girman kai, masu-zagi, marasa bin iyaye, marasa-godiya, marasa-tsarki, marasa-kamna irin na tabi’a, masu-bakar zuchiya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-chin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura, mafiya-son annishuwa da Allah; suna rike da surar ibada, amma sun musunchi ikonta.” Timothawus II, 3:1-5. “Amma Ruhu yana fadi a sarari, chikin kwanaki na karse wadansu za su yi ridda daga imani, suna mai da hankali ga ruhohi na rudani da koyaswar aljannu.” 1 Timothawus 4:1. Shaitan zai yi aiki “da dukan iko da alamu da al’ajibai na karya, da dukan rudani na rashin adilchi.” Kuma dukan wadanda “basu amsa kamnar gaskiya da za su tsira ba,” za a bari su karbi “aikawar sabo, har da za su gaskanta karya.” Tassalunikawa II, 2:9-11. Sa’anda aka kai wannan mataki na rashin imani irin sakamakon zamanai na farko zai samu.BJ 441.1
Da yawa suka gani kaman sabo da yawan bambance-bambancen koyaswoyi tsakanin ekklesiyoyi masu Kin tsarin paparuma ba za a taba yin yunkurin tilasta hadin kai ba. Amma shekaru da dama cikin ekklesiyoyi masu Kin ikon paparuma, ana kara goyon bayan hadewa bisa ga koyaswoyin da suka je daidai. Dan samun wannan hadin kan, dole a rabu da duk wani mahawara ko wata shawara game da al’amuran da aka bambanta akai.BJ 441.2
Charles Beecher cikin wani wa’azi a 1846, ya ce hidimar dariku masu Kin ikon paparuma ba an kafa ta duka kalkashin matsin tsoro na mutuntaka ba ne, amma suna raye, suna tafiya, suna lumfashi cikin yanayin lalatuttun al’amura ne, suna kuma kokari kowace sa’a domin su rufe gaskiyar, su kuma rungumi ridda. Ya ce: “Ba hakanan ne ya faru da Rum ba? Ba maimaita rayuwarta muke yi ba? Kuma me mu ke gani a gabanmu? Wata majalisa ta duka kuma! Taron duniya! Hadin kan dariku da koyaswa daya ta kowa da kowa!” Sa’anda wannan ya faru, domin kokarin samun cikakkiyar daidaituwa, jima kadan za a shiga anfani da karfi.BJ 441.3
Sa’anda manyan ekklesiyoyin Amerika suka hada kai bisa ga koyaswoyin da dukansu suka amince da su, idan sun rinjayi gwamnati ta tilasta bin umurnin su ekklesiyoyin da karfafa tsare-tsarensu, Amerika ta kafa gumki ga tsarin Rum ke nan, kuma za a fara horon masu kin yarda ke nan.BJ 442.1
Bisa mai-kaho biyu din “yana sa a ba dukan mutane kanana da manya, mawadata da matalauta, yaya da bayi, shaida chikin hannunsu na dama ko a bisa goshinsu; kada kowane mutum kuma shi sani iko kuma shi sayi ko sayas, sai wanda yana da shaidan, watau sunan bisan ko number na sunansa.” Ruya 13:16,17. Kashedin malaika na uku din shi ne: “Idan kowane mutum ya yi sujada ga bisan da gunkinsa, ya karbi shaida kuma a goshinsa, ko a hannunsa, shi kuma za ya sha ruwan anab na hasalar Allah.” Bisan da aka ambata a cikin sakon nan, wanda bisa mai-kaho biyu din ke tilastawa a yi masa sujada, shi ne bisa na fari, mai-kama da damisa, na Ruya 13 din nan, watau mulkin paparuma” Gunkin bisan yana misalta irin riddan kin ikon paparuma din nan ne da za a kafa sa’anda ekklesiyoyi masu kin ikon paparuma za su nemi taimakon gwamnati don tilasta biyayya ga koyaswoyinsu. Saura a fassara “lamban bisan.”BJ 442.2
Bayan gardadi kada a yi sujada ga bisan da gunkinsa, annabcin ya ce; “Nan ga su wadanda ke kiyaye dokokin Allah, da imanin Yesu.” Da shike an bambanta masu kiyaye dokokin Allah daga masu sujada ga bisan da gumkinsa suna kuma karban lamban sa, ya nuna cewa kiyaye dokar Allah a gefe daya da ketarewarta a daya gefen ne zai bambanta tsakanin masu sujada ga Allah da masu sujada ga bisan.BJ 442.3
Hali na musamman na bisan wanda shi ne gumkinsa, shi ne ketarewar dokokin Allah. Game da karamin kahon, watau tsarin paparuma, Daniel ya ce: “Za ya nufa ya sake zamanai da shari’a kuma.” Daniel 7:25. Bulus kuma ya ba mulki dayan suna “mutumen zunubi” wanda zai daukaka kansa gaba da Allah. Tawurin sake dokar Allah ne kadai mulkin paparuma zai daukaka kansa gaba da Allah. Duk wanda zai kiyaye dokan da aka sake hakanan da sanin sa, yana ba da mafificin bangirma ga mulkin da ya yi canjin ne. Biyayyan nan ga dokokin mulkin paparuma biyayya ne ga paparuma maimakon Allah.BJ 443.1
Mulkin paparuma ya yi yunkurin canja dokar Allah. An cire doka ta biyu da ta hana sujada ga gumaka daga dokar Allah, aka kuma sake doka ta hudu ta yadda ana umurta kiyaye rana ta fari maimakon ta bakwai a matsayin assabbat. Amma yan paparuma suna cewa dalilin cire doka ta biyu shi ne cewa ba ta zama lallai ba, da shike tana kunshe cikin ta fari, kuma cewa wai suna ba da dokar daidai yadda Allah Ya nufa a gane ta ne. Ba wannan ne sakewan da annabin ke magana akai ba. Yana magana game da canji ne gadan-gadan; wanda aka nufa a yi. “Za ya nufa ya sake zamanu da shari’a kuma.” Sakewar doka ta hudu ce ta cika annabcin daidai. An ce da ikon ekklesiya ne kadai aka yi sakewar. A nan mulkin paparuma kai tsaye ya aza kansa gaba da Allah.BJ 443.2
Yayin da za a iya bambanta masu sujada ga Allah tawurin girmama assabbat da su ke yi da shike shi ne shaidar ikonsa na halitta, dalilin da ya sa ya cancanci bangirma da biyayya, masu sujada ga bisan za a sansance su ta wurin kokarinsu na rushe abin tunawa na Mahalicin, don daukaka abin da Rum ta kafa. Game da Lahadi ne mulkin paparuma ya fara nuna girman kansa; kuma anfanin sa na farko da ikon gwamnati don tilasta sujada ranan Lahadi ne a matsayin “rana ta Ubangiji”. Amma Littafin yana cewa rana ta bakwai, ba ta fari ba, it ace rana ta Ubangiji. In ji Kristi: “Dan mutum Ubangiji ne har na ran assabbachi.” Ta bakin annabi Ishaya kuma Ubangiji ya che da assabbat “rana ta mai-tsarki.” Markus 2:28; Ishaya 58:13.BJ 443.3
Ikirarin da aka cika yi wai Kristi ya sake assabbat ya saba ma maganar Kristi da kansa. Cikin wa’azinsa a kan Dutsen ya ce: “Kada ku zache na zo domin in warware Attaurat da Annabawa; ban zo domin in warware ba, amma domin in chichika. Gaskiya fa ni ke fada maku, har sama da duniya su shude, ko wasali daya ko digo daya ba za ya shude daga, Attaurat ba sai dukan abu ya chika. Dukan fa wanda ya ketare guda daya ma-fi kakanta daga chikin dokokin nan, har ya koya ma mutane haka, za a che da shi mafi karamta a chikin mulkin sama, amma dukan wanda za ya aikata su har ma ya sanas, za a che da shi mai-girma a chikin mulkin sama.” Matta 5:17-19.BJ 444.1
Masu Kin mulkin paparuma sun amince cewa Littafin bai ba da dama a canja assabbat ba. Kungiyar wallafa majallu na Amerika da kungiyar Hadin kan “Sunday School” na Amerika sun wallafa wannan a sarari. Dayansu ta amince da cewa Sabon Alkawali gaba daya yayi shuru game da Lahadi, rana ta fari ko kuma umurni game da kiyaye ta.BJ 444.2
Wani kuma ya ce: “Har lokacin mutuwar Kristi, ba a canja ranan ba, kuma bisa ga abinda ke rubuce dai manzanin basu… ba da wani umurni cewa a yi watsi da Assabbat na rana ta bakwai, a kuma kiyaye ta a rana ta fari ga mako ba.”BJ 444.3
Roman Katolika sun amince cewa ekklesiyarsu ce ta sake assabbat, suna kuma cewa masu Kin ikon paparuma, ta wurin kiyaye Lahadi suna amincewa da ikon paparuma ne. A wata majallar Katolika mai suna a turance “Catholic Catechism of Christian Religion,” garin amsa tambaya game da ranar da za a kiyaye, don yin biyayya ga doka ta hudu, an ce: “A zamanin tshohuwar dokar, Asabar ne ranan da aka tsarkake, amma ekklesiya, wadda Yesu Kristi ya umurce ta, Ruhun Allah kuma ya bishe ta, ta sanya Lahadi a maimakon Asabar, sabo da haka yanzu muna tsarkake rana ta fari, ba ta bakwai ba, Yanzu Lahadi ne rana ta Ubangiji.”BJ 444.4
A matsayin shaidar ikon Ekklesiyar Katolika, marubutanta suna anfani da “canjawar Assabbat zuwa Lahadi, wanda masu Kin ikon paparuma suka yarda da shi,… domin ta wurin kiyaye Lahadi, sun amince da ikon ekklesiyar ta umurtawa a yi bukukuwa, wanda bai yi ba kuma ya yi zunubi.” Kenan mene ne sake Asabbat din, in ba alama, ko lamba, na ikon ekklesiyar Rum ba, watau lamban bisan?”BJ 445.1
Ekklesiyar Rum ba ta bar kirarinta na fifiko ba, kuma sa’an da duniya da ekklesiyoyi masu-kin ikon paparuma suka karbi assabbat din da ita ta kirkiro, suka ki Assabbat na Littafin, sun amince da wannan ikirarin ke nan. Suna iya cewa an yi canjin bisa ikon al’ada ne da na Ubanin ekklesiya, amma garin yin haka suna manta ainihin kaidar da ta raba su da Rum, cewa “Littafin, da Littafin kadai ne addinin masu-kin kon paparuma.” Dan paparuma ya gane cewa wadannan suna rudin kansu ne, suna rufe idonsu ga ganin gaskiyan. Yayin da aikin tilasta kiyaye Lahadi ke samun karbuwa, yana jin dadi, a ganin shi daga bisani aikin zai jawo dukan masu Kin ikon paparuma su zama a kalkashin tutar Rum.BJ 445.2
Romawa suna cewa; “Kiyaye Lahadi da masu Kin ikon paparuma ke yi, mubaya’a suke yi ga ikon ekklesiyar (Katolika).” Tilasta kiyaye Lahadi da masu Kin ikon paparuma ke yi tilasta yin sujada ga mulkin paparuma ne, sujada ga bisan. Wadanda, ko da shike sun san bukatun doka ta hudu, suka zabi kiyaye jebu maimakon ainihin Assabbat suna mubaya’a ga wannan mulkin ne wanda ke umurta shi. Amma tawurin tilasta ibada tawurin ikon gwamnati, ekklesiyoyin da kansu za su kafa gumkin bisan, sabo da haka tilasta kiyaye Lahadi a Amerika zai zama tilasta sujada ga bisan da gumkinsa ne.BJ 445.3
Amma Kiristan sararakin baya sun kiyaye Lahadi, suna gani kamar suna kiyaye Assabbat na Littafin ne, kuma yanzu ma akwai Kirista na kwarai a kowace ekklesiya, har da ekklesiyar Roman Katolika, da suke ba da gaskiya cewa Lahadi ne Assabbat da Allah ya kafa. Allah yana karban sahihancin manufarsu da amincinsu gare shi. Amma sa’anda kiyaye Lahadi ya zama tilas bisa ga doka, aka kuma wayar ma duniya da kai game da takalifin Assabbat na gaskiyan lokacin ne duk wanda ya ketare dokar Allah, ya kuma yi biyayya da dokan da an kafa bisa ikon Rum, yana girmama Rum fiye da Allah ke nan. Yana mubaya’a ga Rum da mulkin da ke tilasta yin abin da Rum ta umurta. Yana sujada ga bisan da gumkinsa. Yayin da mutane a lokacinsu ke kin abinda Allah ya bayana cewa shi ne alaman ikonsa, a maimakon shi kuma suna girmama abin da Rum ta zaba ya zama alaman daukakarta, tawurin wannan suna karban alamar biyayya ga Rum ke nan, watau “Lamban bisan.” Kuma sai an gabatar ma muane da batun a sarari hakanan, aka kuma bukace su su zaba tsakanin dokokin Allah da dokokin mutane, sa’an na wadanda suka ci gaba da ketarewa za su karbi “lamban bisan.”BJ 446.1
Barazana ma-fi ban tsoro da aka taba yi ma ‘yan Adam tana kunshe cikin sakon malaika na ukun, ne. Zunubi mai munin gaske ne zai jawo fushin Allah wanda ba a surka da jinkai ba. Ba za a bar mutane cikin duhu ba game da wannan muhimmin batun, za a ba duniya gargadi game da zunubin nan kafin zubowar horon Allah, domin mutane su san dalilin da ake azabtar da su, su kuma sami damar tsere ma horon. Annabci ya ce malaika na fari zai yi sanarwarsa “ga kowane iri da kabila da harshe da al’umma” ne. Gargadin malaika na ukun, wanda wani fanni ne na sako dayan, shi ma za a baza shi hakanan. Annabcin ya ce da babban murya za a yi shelarsa, ta bakin malaika mai-firiya a tsakiyar sararin sama, kuma za ya jawo hankalin duniya.BJ 446.2
Cikin batun hamayyan dukan Kirista za su kasu kashi biyu: masu kiyaye dokokin Allah da imanin Yesu, da masu sujada ga bisan da gumkinsa suna kuma karban lambansa. Ko da shike ekklesiya da gwamnati za su hada kai su tilasta “kanana da manyua, mawadata da matalauta, yaya da bayi” (Ruya 13:16), su karbi “shaidar bisan,” duk da haka mutanen Allah ba za su karbe shi ba. Annabin Patmos yana kallon “wadanda suka fito masu-nasara da bisan, da gumkin, da numba na sunansa, suna tsaye a bisa teku na madubi, suna da girayu na Allah.” Suna kuma raira wakar Musa da wakar Dan rago. Ruya 15:2,3.BJ 447.1