Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 38—Gargadi na Karshe

    “Na ga wani malaika yana sabkowa daga sama, yana da hukumci da yawa; duniya kuma a haskaka domin daukakassa. Ya ta da murya da karfi, ya che, Fadadiya che, fadadiya che Babila babba, ta zama gidan aljannu, da madaurar kowane kazamin tsuntsu mai-ban kyama.” “Na ji wata murya daga sama ta che, Ku fito daga chikinta, ya al’ummata, domin kada ku yi taraya da zunubanta.” Ruya 18:1,2,4.BJ 599.1

    Nassin nan yana magana game da lokacin da za a maimaita sanarwar fadduwar Babila ne, da kari game da lalacewa da ke shiga kungiyoyi dabam dabam da suka hadu suka zama Babila, tun da aka ba da babban sakon nan da farko, da daminan 1844. An bayana munin yanayin addini ne anan. Duk sa’an da aka ki gaskiya, tunanin mutane zai kara duhunta, zukatansu za su kara tauri, har sai sun nutse cikin kangarar kafirci. Cikin tumbe ga gargadin da Allah Ya bayar, za a ci gaba da tattake daya daga cikin dokoki goma, har sai sun kai inda za su tsananta ma masu girmama dokar. Cikin rennin da ake yi ma maganar Kristi da mutanensa, ana wofinta Shi Kristi. Sa’an da ekklesiyoyi ke karban koyaswoyin sihiri, ana kawar da hanin da aka sa ma zuciyar mutumtaka, sa’annan addini zai zama alkyabbar da za ta boye zunubi mafi muni. Bangaskiya ga bayanuwar ruhohi ta kan bude kofa ga ruhohin lalata da koyaswoyin aljannu, ta hakanan kuma za a ji tasirin miyagun malaiku a cikin ekklesiyoyi.BJ 599.2

    Game da Babila a lokacin da annabcin nan ke magana akai, an ce: “Zunubanta sun kawo har ga sama, Allah kwa Ya tuna da muguntanta.” Ruya 18:5. Ta cika ma’aunin laifinta, hallaka kuma ta kusa fadowa a kanta. Amma Allah har yanzu yana da mutane a cikin Babila; kuma kafin zubowar hukumcin, dole za a fito da su domin kada su sa hannu cikin zunubanta, su kuma “sha rabon alobanta.” Don haka ne za a yi aikin nan da aka misalta da malaika da ya sauko daga sama, ya haskaka duniya da daukakarsa, da babbar murya kuma yana shelar zunuban Babila. Dangane da sakonsa, an ji: “Ku fito daga chikinta, jama’ata.” Sanarwoyin nan hade da sakon malaika na uku ne gargadi na karshe da za a ba mazamnan duniya. BJ 600.1

    Batun da duniya za ta fuskanta abin tsoro ne. Hukumomin duniya da suka hada kai don yaki da dokokin Allah za su umurta cewa “dukan mutane, kanana da manya, mawadata da mawadata da mataluta, yaya da bayi” (Ruya 13:16) su yi biyayya ga al’adun ekklesiya ta wurin kiyaye Assabbat na karya. Dukan wadanda sun ki yin biyayya za su gamu da horo daga gwamnati, a karshe kuma za a furta cewa sun cancanci mutuwa. A daya gefen kuma, dokar Allah game da ranar hutu ta Allah tana bukatar biyayya, tana kuma barazanar fushi kan dukan wadanda sun ketare umurninta.BJ 600.2

    Sa’anda an bayana batun a fili haka, duk wanda ya tattake dokar Allah domin ya yi biyayya ga dokar mutum, ya karbi shaidaar bisan ke nan; ya karbi alamar biyayya ga mulkin da ya yi biyayya gareta, maimakon Allah. Fadaka daga sama ita ce: “Idan kowane mutum ya yi sujada ga bisan da gumkinsa, ya karbi shaida kuma a goshinsa ko a hannunsa, shi kuma za ya sha rowan annab na hasalar Allah wanda an shirya chikin koko na fushinsa,” Ruya 14:9, 10. BJ 600.3

    Amma ba wanda za a sa ya sha fushin Allah sai an bayana masa gaskiya ga tunanin sa da lamirinsa, ya kuma ki. Akwai da yawa da basu taba jin gaskiya ta musamman don wannan zamanin ba. Ba a taba bayana masu doka ta hudu yadda ya kamata ba. Shi mai karanta kowace zuciya, yana kuma auna kowace manufa, ba zai bari a rudi wani mai-son sanin gaskiya game da batutuwan jayayyan ba. Ba za a tilasta ma mutane umurnin a duhunce ba. Kowa zai sami isashen haske da zai dauki mataki sa, da hankalinsa.BJ 601.1

    Assabbat ne zai zama babban magwajin biyayya da shike shi ne babban gaskiya da ake jayayya akai musamman. Sa’an da za a kawo gwaji na karshe ga mutane, sa’annan ne za a bamnamta tsakanin masu bauta ma Allah da marasa bauta masa. Yayin da kiyaye Assabbat na karya don biyayya ga dokar kasa sabanin doka ta hudu, zai zama shaidar biyayya ga wani mulki da ke jayayya da Allah. Kiyaye Assabbat na gaskiyar don yin biyayya ga dokar Allah shaida ce ta biyayya ga Mahalici. Yayin da wani bangare, ta wurin karban alamar biyayya ga ikokin duniya, take karban shaidar bisan, wani bangaren kuwa da ya zabi alamar biyayya ga ikon Allah, yana karban hatimin Allah ne.BJ 601.2

    Kafin nan, akan dauka cewa masu shelar sakon malaika na ukun nan masu ta da hankali ne kawai. Akan ce fadin da suke yi cewa rashin hakuri game da addini zai sake mamaye Amerika, kuma ekklesiya da kasar za su hada kai su tsananta ma masu kiyaye dokokin Allah, ba shi da tushe, kuma wai wauta ce, ana cewa wai kasan nan ba za ta taba zama wani abu dabam da abin da take ba, watau kasa mai-kare yancin addini. Amma yayin da ake baza zancen kiyayewar Lahadi, za a ga cewa lamirin da an dade ana shakkarsa yana tahowa, sako na ukun kuma zai haifar da sakamakon da kafin nan bai iya haifarwa ba.BJ 601.3

    A kowace sara Allah yakan aiko bayinsa su tsauta ma zunubi cikin duniya da cikin ekklesiya. Amma mutane suna so a fada masu ababa masu dadi ne, amma tsabar gaskiya ba ta karbuwa. Yan Canji da yawa, sa’an da suka shiga aikinsu, sun himmatu wajen anfani da dabara wajen tinkarar zunuban al’umma da na ekklsiya. Sun yi begen cewa ta wurin kwatancin rayuwa mai-tsabta ta Kirista za su dawo da hankulan mutane ga koyaswoyin Littafin. Amma Ruhun Allah Ya sauko masu yadda Ya sauko ma Iliya, ya motsa shi ya tsauta ma zunuban mugun sarki da jama’a mai-ridda; basu iya rabuwa da wa’azin bayanawan koyaswoyin Littafin ba, koyaswoyin da, da farko, sun yi shakkar bayanawa. Sun motsu su yi himmar bayana gaskiya da hatsarin da ke barazana ga rayuka. Suka furta kalmomi da Ubangiji Ya ba su, babu tsoron sakamakon yin haka, dole kuma mutanen suka saurari gargadin.BJ 602.1

    Ta haka aka yi shelar sakon malaika na ukun. Yayin da lokaci ke zuwa da za a ba da sakon da iko mafi girma, Ubangiji zai yi aiki ta wurin mutane masu tawali’u, ya jawo hankulan masu himmatuwa ga hidimarsa. Ikon Ruhunsa ne zai horar da masu aikin, ba koyaswar makarantu ba. Masu bangaskiya da addu’a za su motsu su tafi da himma mai-tsarki, suna shelar kalmomin da Allah ke ba su. Za a fallasa zunuban Babila. Sakamako masu ban tsoro na tilasta hidimomin ekklesiya ta wurin ikon gwamnatin kasa, da shigowar sihiri, da ci gaban ikon paparuma a sace, duka za a fallasa su. Ta wurin gargadin nan za a motsa mutane. Dubban dubbai wadanda basu taba jin irin kalmomin nan ba za su ji. Da mamaki za su ji shaida cewa ekklesiya ce Babila fadaddiya sabo da kurakuranta da zunubanta, sabo da ta ki gaskiyan da aka aika mata daga sama. Sa’an da mutane ke zuwa wurin mallaman su na da, da tambaya cewa, Ababan nan haka ne? Shugabannin addinin su kan ba da tatsuniyoyi, su yi annabcin ababa masu dadi, domin su kwantar da tsoronsu da lamirinsu da aka falkas. Amma da shike da yawa sun ki amincewa da ikon mutane, suka bidi “In ji Ubangiji,” sanannun shugabannin, kamar Farisawa na da, cike da fushi sabo da an rena ikonsu, za su ce sakon na Sahitan ne, su kuma ingiza masu son zunubi su rena su kuma tsananta ma masu shelar sakon.BJ 602.2

    Sa’an da jayayyar ta kai har kauyuka, ana kuma jan hanulan mutane zuwa ga dokar Allah da aka tattake, Shaitan zai motsa. Ikon da ke cikin sakon zai haukatar da masu hamayya da shi sakon ne. Ma’aikatan bishara za su yi iyakar kokarin su don su rufe hasken, domin kada ya haskaka tumakinsu. Ta kowace hanya, za su yi kokarin danne kowace magana game da muhimman batutuwan nan. Ekklesiya za ta bidi taimakon karfin gwamnati, kuma a wannan aiki, ‘yan paparuma da masu Kin ikon paparuma za su hada hannu. Yayin da aikin tilasta kiyaye Lahadi ke kara karfi da hima, za a yi anfani da doka kan masu kiyaye dokar. Za a yi masu barazana da tara, da kurkuku, wadansu kuma za a yi masu tayin matsayi mai-tasiri da wadansu lada domin a sa su ki imaninsu. Amma amsarsu kullum ita ce: “Ku nuna mana kuskuren mu daga maganar Allah.” Magana dayan ne Luther ya yi. Wadanda za a gurbanar da su gaban kotuna za su nuna sahihancin gaskiyaar, wadansu da ke sauraronsu kuma za su kai ga daukan kudurin kiyaye dukan dokokin Allah. Ta hakanan za a kawo ma dubbai haske.BJ 603.1

    Biyayya ga maganar Allah bisa ga lamiri za a mai da shi tawaye. Da shike Shaitan zai makantar da su, iyaye za su tsananta ma ‘ya’yansu masu ba da gaskiya; mai-gida ko uwar gida za su muzguna ma bara mai-kiyaye dokar. Za a manta da soyayya; za a hana ma ‘ya’ya gado a kuma kore su daga gida. Kalmomin Bulus za su cika zahiri cewa: “I, kuma dukan wadanda su ke so su yi rayuwa mai-ibada chikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” Timothawus II, 3:12. Sa’anda masu gaskiya suka ki girmama assbbat na Lahadi, za a jefa wadansu cikin kurkuku, a kori wadansu daga kasarsu, a kuma maida wadansu kamar bayi. Ga hikimar mutum duk wannan yanzu kamar ba abu ne mai yiwuwa ba; amma sa’an da an janye Ruhun Allah daga mutane, suka kasance kalkashin mulkin Shaitan makiyin dokokin Allah, za a yi ababa da ba a saba gani ba. Zuciya za ta iya cika da keta idan aka cire kaunar Allah da tsoronsa.BJ 604.1

    Yayin da guguwar ke tahowa, jama’a da yawa da ke cewa sun gaskata sakon malaika na ukun, amma basu tsarkaku ta wurin biyayya ga gaskiya ba, za su rabu da matsayinsu, su shiga jerin ‘yan adawa. Ta wurin hada kai da duniya da samun rabon ruhun duniya, yanzu suna ganin al’amuran kusan yadda duniya ke kalonsu; kuma sa’an da aka kawo gwaji, suna shirye su zabi gefenda yawanci suke. Masu baiwa da iya magana wadanda ke son gaskiya za su rudi mutane su batar da su. Za su zama magabtan ‘yan’uwansu na da. Sa’an da aka kawo masu kiyaye Assabbat gaban kotuna sabo da bangaskiyarsu, ‘yan riddan nan ne za su zama wakilai mafi anfani ga Shaitan da za su yi masu karya su zarge su kuma, tawurin rahotanin karya kuma su fusata shugabani game da su.BJ 604.2

    A lokacin zaluncin nan, za a gwada bangaskiyan bayin Ubangiji. Da aminci suka ba da gargadin, su na duban Allah da maganarsa kadai. Ruhun Allah Ya motsa zukatansu, suka yi magana. Sa’an da himma mai-tsarki ta motsa su, sun shiga aikinsu ba tare da lissafta skamakon furta ma mutanen maganan da Allah Ya ba su ba. Basu dubi anfanin kansu na duniya ba, ko kuma su yi kokarin kare sunansu ko rayukansu ba. Duk da haka, sa’an da guguwar hamayya da reni ta abko masu, wadansu za su firgita har su ce: “Da mun hangi sakamakon kalmominmu, da mun yi shuru.” Matsaloli sun kewaye su. Shaitan ya na kai masu hari da jarabobi masu tsanani. Aikin da suka kama kaman ya fi karfin iyawarsu. Ana yi masu barazanar hallaka. Marmarin da su ke da shi a da, ya tafi; duk da haka ba za su iya juyawa baya ba. Sa’an nan, idan suka gane kasawarsu, za su gudu zuwa wurin Madaukaki domin neman karfi. Za su tuna cewa kalmomi da suka furta nasu ba ne, amma na Shi wanda Ya umurce su su ba da gargadin ne. Allah Ya sa gaskiya cikin zukatansu, kuma ba su iya kin shekar ta ba. BJ 604.3

    Mutanen Allah sun fuskanci gwaji dayan a sararrakin baya. Wycliffe, Huss, Luther, Tyndale, Baxter da Wesley, sun koyar da cewa a gwada kowace koyaswa da Littafin, suka bayana cewa za su rabu da duk wani abin da Littafin ya hana. An tsananta ma mutanen nan da fushi sosai; duk da haka basu dena bayana gaskiyar ba. Lokuta dabam dabam a tarihin eklesiya sun kasance da wata gaskiya ta musamman da aka shirya don bukatun mutanen Allah a lokacin. Kowace gaskiya ta yi nasara bisa kiyayya da adawa; wadanda suka karbi hasken gaskiyar, an jaarabce su, aka kuma tsananta masu. Ubangiji yakan ba da gaskiya ta musamman domin mutane a lokacin tashin hankali. Wa ya isa ya ki baza ta? Ya umurci bayinsa su bayana gayyatar jinkansa ta karshe ga duniya. Ba za su iya yin shuru ba, sai dai su rasa rayukansu. Jakadun Kristi basu damu da batun sakamako ba. Dole za su cika aikinsu, su bar sakamakon a hannun Allah. BJ 605.1

    Yayin da adawa ke kara tsanani, bayin Allah za su kara rudewa, domin za su ga kamar su suka jawo tasin hankalin. Amma lamiri da maganar Allah suna tabbatar masu cewa basu yi kuskure ba, kuma ko da shike wahalolinsu suna ci gaba, ana karfafa su su jimre. Hammayyar ta na kara marmatsowa, ta na kara tsanani kuma, amma bangaskiyarsu da karfin halinsu, suna karuwa daidai da damuwar. Shaidarsu ita ce cewa: “Ba mu isa mu taba maganar Allah ba, mu raba dokarsa mai-tsarki, muna ce da wani bangare mai—muhimmanci, wani kima mara muhimmanci, domin mu sami karbuwa ga duniya. Ubangij da mu ke bauta masa Ya isa Ya kubutar da mu. Kristi Ya rigaya Ya yi nasara da duniya, kuma sai mu ji tsoron duniya da an rigaya an yi nasara da ita?”BJ 606.1

    Zalunci iri iri abu ne da zai ci gaba da kasancewa muddan akwai Shaitan, kuma Kiristanci yana da ikon sa na musamman. Ba wanda zai iya bauta ma Allah ba tare da jawo ma kansa adawar rundunonin duhu ba. Miyagun malaiku za su kai masa hari, da shike sun damu cewa yana kwace abinci daga hannunsu. Miyagun mutane wadanda kwatancinsa ke tsauta masu, za su hada kai da miyagun malaiku wajen kokarin raba shi da Allah ta wurin jarabobi. Sa’an da wadannan basu yi nasara ba, za a yi anfani da wani iko domin a tilasta lamirin. Amma muddan dai Yesu Ya kasance Matsakancin mutum a haikali na sama, za a ji tasirin hani na Ruhu Mai-tsarki kan shugabanni da mutane. Har yanzu yana mulki kan dokokin kasar. Da ba domin dokokin nan ba, da munin yanayin duniya ya fi yadda yake yanzu. Yayin da shugabannin mu da yawa wakilan Shaitan ne, Allah ma yana da wakilansa cikin shugabannin kasar. Magabcin yana motsa bayinsa su shawarta a dauki matakan da za su hana ci gaban aikin Allah, amma manyan kasar, masu tsoron Allah, malaikun Allah su kan motsa su su yi jayayya kan shawarwarin nan ta yadda ba za a iya kin maganarsu ba. Ta hakanan mutane kalilan za su iya tare babbar rigyawar mugunta. Za a hana adawar magabtan gaskiya domin sakon malaika na ukun ya yi aikinsa. Sa’an da an ba da fadaka ta karshen, za ta jawo hankulan shugabannin nan da Ubangiji ke aiki ta wurinsu, wadansunsu kuma za su karbe shi, su kuma tsaya da mutanen Allah a lokacin wahala.BJ 606.2

    Malaikan da ya hada kai cikin shelar sakon malaika na uku zai haskaka dukan duniya da darajarsa. Aikin da zai mamaye dukan duniya ake nunawa a nan. Aikin zuwan Yesu na 1840-1844 ya nuna ikon Allah da daraja; aka kai sakon malaika na farin kowace cibiyar mishan a duniya, kuma a wadansu kasashe an sami marmarin addini mafi yawa da aka taba gani a wata kasa tun Canjin karni na sha bakwai; amma marmarin babban himman nan an lokacin fadaka na malaika na ukun zai fi wannan.BJ 607.1

    Aikin zai yi kama da na Ranar Pentecost. Kamar yadda aka ba da “ruwan fari,” ta wurin zubowar Ruhu Mai-tsarki a farkon bisharar, domin kawo tohuwar irin, haka kuma za a ba da ruwan bayan a karshe domin nunar da girbin. “Bari mu sani fa, mu nache bi kuma garin mu san Ubangiji; fitarsa tabbataciya che kamar wayewar gari; za ya zo wurinmu kamar ruwan sama, kamar ruwan karshe mai-damsasa kasa.” Hosea 6:3. Ku yi murna fa ku ‘ya’yan Sihiyona, ku yi farin zuchiya chikin Ubangiji Allahnku: gama ya na ba ku ruwan fari daidai bukatarku, ya na sa ruwa ya sabko maku, da na fari har na karshe, kamar da.” Joel 2:23. “Za ya zama a chikin kwanakin karshe, in ji Allah, zan zuba maku Ruhu na bisa mai-rai duka.” “Za ya zama kuwa dukan wanda ya kira da sunan Ubangiji za ya tsira.” Ayukan 2:17, 21.BJ 607.2

    Babban aikin bishara ba zai kare da bayanuwar ikon Allah a kasa wadda aka bude aikin da ita ba. Annabce annabcen da aka cika ta wurin zubowar ruwan farko a farkon bisahra za a kuma cika su lokacin ruwan karshen a karshen aikin. Lokutan warsakewan kenan da manzo Bitrus ke begen sa,lokacin day a ce: “Ku tuba fa ku juyo domin a shafe zunubanku domin hakanan wokatan wartsakewa daga wurin Ubangiji su zo; domin kuma Shi aiko Kristi.” Ayukan 3:19, 20.BJ 607.3

    Bayin Allah da fuskokin su sama, suna walkiya da tsarkakewa mai-tsarki, za su yi sauri nan da can su yi shelar sakon nan daga sama. Ta wurin dubban muryoyi, ko ina a duniya za a ba da gargadin. Za a aikata al’ajibai, za a warkar da marasa lafiya, kuma alamu da al’ajibai za su bi masu ba da gaskiya. Shaitan ma zai bi da al’ajiban karya, har ma zai kawo wuta daga sama, mutane suna gani. Ruya 13:13. Ta hakanan za a kai mazamnan duniya ga daukan matsayinsu.BJ 608.1

    Za a kai sakon, ba lallai ta wurin mahawara ba, kamar ta wurin aikin Ruhun Allah. An rigaya an gabatar da dalilan. An rigaya an shuka irin, yanzu kuma zai tohu ya haifi ‘ya’ya. Majallun da ma’aikatan bishara ke bazawa za su yi nasu tasirin, duk da haka da yawa da zukatansu suka motsu an hana su samun cikakiyar fahimtar gaskiyar, ko kuma yin biyayya. Yanzu tsirkiyoyin hasken suna shiga ko ina, ana ganin gaskiya cikin haskenta, amintattun ‘ya’yan Allah kuma su na yanke madauran da suka rikesu. Gaskiya ta fi dukan ababa daraja. Duk da akilan da su ka hada kai domin su yaki gaskiyar, mutane da yawa za su dauki matsayinsu a gefen Allah. BJ 608.2

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents