Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Gabatarwa

    Kafin shigowar zunubi, Adamu ya mori sadarwa kai tsaye da Mahalicinsa; amma tun da mutum ya raba kan shi da Allah ta wurin zunubi, an yanke jinsin ‘yan Adam daga wannan babban damar. Amma kuma ta wurin shirin fansa, an bude hanya ta yadda mazamnan duniya za su iya samun sadarwa da sama. Allah yana sadarwa da mutane ta wurin Ruhunsa, kuma an ba da hasken Allah ga duniya ta wurin wahayi ga zababbun bayinsa ne. “Mutane suka yi magana daga wurin Allah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” Bitrus I, 1:21.BJ v.1

    Cikin shekaru dubu biyu da dari biyar na fari na tarihin duniya, babu rubuce rubucen wahayi. Wadanda Allah Ya rigaya Ya koya masu, sun fada ma wadansu abin da suka sani, aka rika mika shi daga uba zuwa da, cikin sararakin da suka biyo. Shirya rubutaciyar maganar ya fara lokacin Musa ne. Sa’an nan aka rubuta horarrun wahayi a cikin horarren Littafi. Wannan aikin ya ci gaba cikin shekaru dari shida, daga Musa mai-tarihin halita da dokan, zuwa Yohanna, mai-rubuta gaskiya mafi-girma ta bishara.BJ v.2

    Littafin ya bayana cewa Allah ne Mawallafinsa, amma hannuwan mutane ne suka rubuta shi; kuma cikin bamabancin salo na litattafansa dabam dabam din, yana bayana halayyan marubutansa dabam dabam din. Dukan gaskiyan da aka bayana hurarru ne daga Allah (Timothawus II, 3:16); duk da haka cikin kalmomin mutane ne aka bayana su. Shi Mara-iyakan, ta wurin Ruhunsa Ya ba da haske cikin tunanin bayinsa da zukatansu. Ya ba da mafalkai da ruyai, da alamu da lambobi; kuma wadanda aka bayana masu gaskiyan hakanan, su ma kansu sun bayana tunanin nan a cikin harshen mutane.BJ v.3

    Allah da kan Shi ne Ya furta Dokoki Goma din nan, Ya kuma rubuta su da hannunsa. Allah ne Ya shirya su, ba mutum ba. Amma Littafin, da gaskiyan shi da Allah Ya bayar aka bayana cikin harshen mutum, ya kunshi hadin Allahntaka da mutumtaka. Irin wannan hadin ya kasance cikin yanayin Kristi wanda Shi Dan Allah ne da Dan mutum kuma. Ta hakanan, Littafin kamar Kristi ne. “Kalman ya zama jiki ya zamna a wurinmu.” Yohanna 1:14.BJ v.4

    Da shike mutanen da sun bambanta sosai a matsayi da sana’a, da kuma baiwan tunani da na ruhaniya ne suka rubuta Littafin, cikin sararaki dabam dabam, litattafansa suna nuna bambanci sosai na tsari da na yanayin batutuwan da aka bayana. Marubuta dabam dabam sun yi anfani da kalmomi dabam dabam; sau da yawa, wani yakan fi wani bayana gaskiya dayan, kuma sa’an da marubuta dabam dabam suka gabatar da batu kalkashin fannoni da yanayi dabam dabam, mai-karantawa sama sama da garaje, ko da wata manufa, zai ga kaman akwai sabani, inda mai-karantawa da tunani, da bangirma, da ganewa garai zai ga jituwa ne.BJ vi.1

    Ko da shike ta wurin mutane dabam dabam ne aka gabatar, an fito da kowane fannin gskiyar. Wani marubuci ya kula da wani fannin batun ne, yakan dauki ababan da sun je daidai da abin da ya sani, ko ganewarsa; wani zai dauki wani fanni dabam, kuma kowa, bisa ga bishewar Ruhu Mai-tsarki, yakan gabatar da abin da ya fi shiga zuciyarsa, fanni dabam dabam na gaskiyar, amma akwai cikakiyar jituwa tsakanin dukansu. Gaskiyan da aka bayana hakanan kuma sun hadu sun zama gaskiya guda cikakiya da aka shirya ta yadda za ta je daidai da bukatun ‘yan Adam cikin kowane yanayin rayuwa. BJ vi.2

    Ya gamshi Allah Ya aiko da gaskiyarsa ga duniya ta wurin mutane, da Shi kansa, da Ruhunsa Mai-tsarki, Ya shirya Ya kuma ba su kwarewar yin aikinsa. Ya bi da zuciyan game da zaben abin da za a fada, da abin da za a rubuta. An ba mutane ne amanar dukiyan nan, duk da haka dai daga sama yake. An ba da shaidar ta wurin harshen dan Adam ne da kurkuransa, duk da haka shaidar Allah ce, kuma ‘ya’yan Allah masu biyayya da ba da gaskiya za su ga darajar Allah cikinta, cike da alheri da gaskiya. Cikin maganarsa, Allah Ya ba mutane sanin da ya zama wajibi domin ceto. Sai a karbi Littafin a matsayin bayanin nufinsa, mai-iko mara-kuskure kuma. Shi ne ma’aunin hali, mai-bayana koyaswoyi, magwajin rayuwa kuma. “Kowne nassi horarre daga wurin Allah mai-anfani ne ga koyaswa, ga tsautawa, ga kwabewa, ga foro kuma da ke chikin adilchi: domin mutumen Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarchin aiki.” Timothawus II, 3:16,17.BJ vi.3

    Duk da haka, batun cewa Allah Ya bayana nufinsa ga mutane ta wurin kalmarsa, bai wofinta kasancewa da bishewar Ruhu Mai-tsarki ba. Akasin haka ma, Mai-ceton mu Ya yi alkawalin Ruhu Mai-tsarkin domin Ya bude Kalmar ga bayinsa, ya ba da haske, ya kuma yi anfani da koyaswoyin ta. Da shike Ruhun Allah ne Ya hura aka rubuta Littafin, ba shi yiwuwa koyaswar Ruhun ta taba sabani da ta maganar Allah. BJ vii.1

    Ba a ba da Ruhun, ba kuwa za a taba ba da shi, domin Ya sauya Littafin ba; gama Littafin ya fada a fili cewa maganar Allah ce ma’aunin da za a gwada kowace koyaswa da kowane al’amari da ita. Manzo Yohanna ya ce: “Masoya, kada ku ba da gaskiya ga kowane ruhu, amma ku gwada ruhohi, ko na Allah ne: gama masu-karyan annabchi da yawa sun fita zuwa chikin duniya.” Yohanna I, ,4:1. Ishaya kuma ya ce: “A komo bisa ga shari’an da shaidan! Idan basu fadi bisa ga wannan magana ba, hakika babu wayewan gari a gare su ba.” Ishaya 8:20.BJ vii.2

    An sa reni mai-yawa sosai kan aikin Ruhu Mai-tsarki ta wurin kurakuran wadansu masu cewa wai da shike suna da bishewar Ruhu Mai-tsarki, ba sa bukatar bishewar maganar Allah kuma. Suna biyayya ga abin da ya burge zukatansu ne, da suke gani kamar muryan Allah ne cikinsa. Amma ruhun da ke mulki cikinsu ba Ruhun Allah ba ne. Wannan bin tunanin zuciyarsu maimakon Littafin, zai iya kaiwa ga rudami da rudi da hallaka ne kadai. Yana kara ci gaban dabarun Shaitan ne kawai. Da shike hidimar Ruhu Mai-tsarki tana da muhimmanci kwarai ga ekklesiyar Kristi, wata dabarar Shaitan ita ce, ta wurin kura kuran masu matsanancin ra’ayi, ya sa a rena aikin Ruhun ya kuma sa mutanen Allah su rabu da wannan tushen karfi da Ubangijinmu Ya tanada.BJ vii.3

    Daidai da maganar Allah, Ruhun Shi zai ci gaba da aikinsa, duk tsawon lokacin zamanin bishara. Cikin sararakin da ake ba da nassosin Tsohon Alkawali da Sabon Alakwali, Ruhu Mai-tsarki bai dena ba da haske ga tunanin mutane ba, ban da ababan da aka bayana za a hada cikin Littafin. Littafin kansa ya bayana yadda, tawurin Ruhu Mai-tsarki mutane suka sami fadaka da tsautawa da shawara da umurni, game da al’amuran da basu shafi bayar da nassosin Littafin ba ko kadan. An kuma ambaci annabawa a sararaki dabam dabam da ba a rubuta komi game da ababan da suka fada ba. Haka kuma, bayan rufewar rubuta Littafin, Ruhu Mai-tsarki ya ci gaba da aikin Shi na wayarwa da fadakarwa da ta’azantarwa ga ‘ya’yan Allah.BJ vii.4

    Yesu Ya yi ma almajiransa alkawali, Ya ce: “Amma Mai-taimako, watau Ruhu Mai-tsarki, wanda za ya aiko chikin sunana, za ya koya maku abu duka, ya tuna maku kuma dukan abin da na fada maku.” “Amma sa’anda shi, Ruhu na gaskiya, ya tafo, za ya bishe ku chikin dukan gaskiya:…za ya bayana maku kuma abin da ke zuwa.” Yohanna 14:26; 16:13. Littafin yana koyarwa a fili cewa alkawuran nan basu tsaya kan zamanin manzani kadai ba, amma sun kai ga ekklesiyar Kristi cikin dukan sararaki. Mai-ceton Ya tabbatar ma masu-binsa cewa: “Ina tare da ku kullayaumi, har matukan zamani.” Matta 28:20. Bulus kuma ya bayana cewa baye baye da aikace aikacen Ruhu suna cikin ekklesiya, “domin kamaltawar tsarkaka, domin aikin hidima, domin ginin jikin Kristi: har dukanmu mu kai zuwa dayantuwar imani da sanin Dan Allah zuwa chikakken mutum, zuwa misalin tsawon chikar Kristi.” Afisawa 4:12,13.BJ vii.5

    Sabo da masu-bi a Afisus, manzon ya yi addu’a cewa: “Allah na Ubangijinmu Yesu Kristi, Uban daraja, shi ba ku ruhu na hikima da na bayani chikin saninsa; idanun zuchiyarku su haskaka, domin ku sani komine ne begen kiransa, … da ko mine ne mafifichin girman ikonsa zuwa garemu, mu masu ba da gaskiya.” Afisawa 1:17-19. Hidimar Ruhun Allah na wayar da ganewa da bude tunanin mutane ga zurfafan ababan magana mai-tsarki na Allah, ita ce albarkan da Bulus ya yi ma ekklesiyar Afisus.BJ viii.1

    Bayan bayanuwar Ruhu Mai-tsarki a ranan Pentecost, Bitrus ya kira mutanen zuwa tuba da baptisma cikin sunan Kristi, domin gafarar zunubansu; sa’an nan ya ce: “Za ku karbi Ruhu Mai-tsarki kyauta kuma. Gama alkawali dominku da yayanku, da dukan manisanta, iyakar wanda Ubangiji Allahnmu za ya kirawo.” Ayukan 2:38,39.BJ viii.2

    Dangane da al’amuran babban ranar Allah, Ubangiji ta bakin annabi Joel Ya yi alkawalin bayanuwa ta musamman ta Ruhunsa. Joel 2:28. An cika annabcin nan kadan, lokacin zubowar Ruhun a ranar Pentecost, amma zai sami cikakken faruwarsa lokacin da za a bayana alherin Allah wanda zai zo tare da aikin karshe na bisharan.BJ viii.3

    Babban jayayya tsakanin nagarta da mugunta za ta kara tsanani, gaf da karshen lokaci. Cikin dukan sararaki Shaitan ya nuna fushinsa game da ekklesiyar Kristi; Allah kuma Ya ba mutanensa alherinsa da Ruhunsa domin Shi karfafa su su yi tsayayya da ikon mugun. Lokacin da manzanin Kristi za su kai bishararsa ga duniya, su kuma rubuta shi domin dukan sararakin da ke zuwa, an ba su wayewa ta musamman daga Ruhun. Amma yayin da ekklesiya za ta kusanci tsiranta na karshe, Shaitan zai kara himman aikinsa. Zai sauko, “hasala mai-girma kwa gare shi, domin ya sani sauran zarafinsa kadan ne.” Ruya 12:12. Zai yi aiki “da dukan iko da alamu da al’ajibai na karya.” Tassalunikawa II, 2:9. Har shekara dubu shida mai-dabarun nan wanda da shi ne mafi-girma cikin malaikun Allah yana ta aikin rudi da hallaka kawai. Kuma duk zurfin kwarewa da wayon shaidanci da dukan zalunci da ya samo cikin lokacin faman nan na zamanai, zai yi anfani da su kan mutanen Allah cikin fada na karshen. A wannan lokacin wahala kuma, masu bin Kristi za su kai ma duniya gargadi game da zuwan Ubangiji na biyu; za a kuma shirya jama’a da za ta tsaya a gabansa lokacin zuwansa, “marasa aibi, marasa laifi.” Bitrus II, 3:14. A lokacin nan, za a bukaci zubowar alherin Allah bisa ekklesiya kamar zamanin manzanin.BJ viii.4

    Ta wurin hasken Ruhu Mai-tsarki an bayana al’amuran jayayyan nan mai-tsawo tsakanin nagarta da mugunta ga mai-rubuta wannan littafin. Lokaci lokaci, akan yarda mani in ga yadda a sararaki dabam dabam babbam jayayyan nan ke gudana tsakanin Kristi, Sarkin rai, Tushen ceto, da Shaitan, sarkin mugunta, tushen zunubi, wanda ya fara ketare doka mai-tsarki na Allah. Shaitan yana bayana kiyayyarsa ga Kristi a kan masu bin Kristi din. Kiyayyarsa ga kaidodin dokar Allah, tsarin rudin nan nasa wanda ke sa karya ta zama kamar gaskiya, wadda kuma ta wurinta ake sauya dokar Allah da dokar mutum, a kuma sa mutane su yi sujada ga halitace maimakon Mahalicin, za a iya ganinsu cikin dukan tarihi. Cikin dukan sararaki Shaitan yana kokarin batancinsa ga halin Allah, domin neman sa mutane su sami mumunan ra’ayi game da Mahilicin, ta hakanan kuma su kalle Shi da tsoro da kiyayya maimakon kauna. Kokarin shi na warware dokar Allah da yake sa mutane su ji kamar ba sa kalkashin sahruddan ta; da zaluncinsa da yake yi ma wadanda suka ki rudin na sa, yana nan kullum cikin dukan sararaki. Za a iya samun shi cikin tarihin ubani da annabawa da manzani da wadanda aka kashe, da ‘yan canji kuma. BJ ix.1

    A babban yaki na karshen, Shaitan zai yi anfani da manufa dayan, ya nuna ruhu dayan, ya kuma yi aiki domin manufa daya da ta dukan sararakin da suka gabata. Abin da ya faru da, zai faru kuma, sai dai cewa fadan da ke zuwa zai zama da zafi mai-tsanani irin wanda duniya ba ta taba gani ba. Rudin Shaitan zai zama da zurfin wayo, hare haren sa kuma da karin himma. In da zai yiwu, da zai batar da zababbun ma. Markus 13:22.BJ x.1

    Da shike Ruhun Allah Ya bayana ma zuciya ta manyan gaskiya na maganarsa, da al’amura na baya da na gaba, an umurce ni in sanar ma sauran mutane abin da aka bayana, in shaida tarihin jayayyar a zamanun baya, kuma musamman ma, in gabatar da shi ta yadda zan ba da haske game da yakin da ke zuwa a gurguje nan gaba. Domin cim ma manufan nan, na y i kokari na zaba, na kuma harhada al’amura cikin tarihin ekklesiya ta yadda zan bayana faruwar muhimman gaskiyan da a wokatai dabam dabam aka ba duniya, wadanda suka ta da fushin Shaitan, da kiyayyar ekklesiya mai-kaunar duniya, gaskiyan kuma da shaidar wadanda basu kaunaci ransu ba har mutuwa, suka rike. BJ x.2

    Cikin rahotanin, za mu iya ganin labarin yakin da ke gabanmu. Idan muka dube su bisa ga maganar Allah da haskakawar Ruhunsa, za mu ga an bayana dabarun mugun, da kowane hatsari wanda dole dukan masu so a iske su babu laifi a gaban Ubangiji sa’an da Ya zo, su guji hatsarin.BJ x.3

    Manyan al’amura da suka nuna ci gaban canji cikin sararakin baya, al’amura ne na tarihi da ke sanannu sosai ga masu Kin ikon paparuma; batutuwa ne da ba wanda zai iya karyatawa. Na gabatar da wannan tarihi a takaice ne bisa ga gajartar littafin, da yadda ya zama dole a bar shi da gajartar, da shike an matse batutuwan a kankanin wuri bisa ga yadda ya je daidai da kyakyawar ganewar anfaninsu. A wadansu wurare, inda mai-ba da tarihi ya tara al’amura wuri daya domin ya ba da takaitaccen cikakken ra’ayi game da batun, ko kuma ya takaita labaru da kyau, an ambata kalmomin na sa daidai; amma a wadansu wurare ba a ambaci ainihin wanda ya yi rubutun ba, da shike ba a ba da maganar da manufar nuna cewa wanda ya rubuta din masani ne ba, amma domin maganarsa ta ba da kwakwarar bayanin batun cikin sauki ne. Wajen bayana labaru ko ra’ayin wadanda ke aikin canji a zamanin mu, an yi anfani da rubuce rubucen su da aka wallafa hakanan ne ma.BJ xi.1

    Ba manufar littafin nan ne ya gabatar da sabobin gaskiya game da famar lokacin da ya rigaya ya wuce ba; muhimmiyar manufar ita ce a fito da batutuwa da kaidodi da ke da nasaba da al’amura da ke zuwa. Duk da haka idan aka dube su kamar sassan jayayyan nan tsakanin haske da duhu, dukan rahotanin ababan da sun rigaya sun faru a baya, za a ga cewa suna da sabuwar ma’ana; ta wurinsu kuma za a haskaka gaba, a haskaka hanyar wadanda , kamar ‘yan canji a sararaki na da, za a kira su, komi hatsari ga dukan ladarsu ta duniya, su shaida “domin maganar Allah da shaidar Yesu Kristi.”BJ xi.2

    Domin bayana al’amuran babban jayayya tsakanin gaskiya da kuskure; a bayana dabarun Shaitan da hanyoyin da za a iya nasarar kinsa; a gabatar da wadatacen maganin babban damuwar mugunta, ana kuma ba da haske game da tushe da kuma karshen zunubi, ta yadda za a ba da cikakken bayanin adalcin Allah da kaunarsa cikin dukan ma’amalansa da halitattunsa; a kuma nuna yanayin tsarki da rashin sakewar dokarsa, manufar littafin nan ke nan. Cewa ta wurin tasirinsa, a tsirar da rayuka daga ikon duhu, su zama “masu-tarayya na gadon tsarkaka chikin haske,” zuwa yabon Shi wanda Ya kaunace mu, ya kuma ba da kansa domin mu, babban addu’ar mai-rubutun ke nan.BJ xi.3

    Ellen G.White

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents